Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa yake 'dan mammatsawa yana murmushi, shi kansa fa ya gaji da kwanciyar nan kawai 'karfin hali yake yi...ba'a jima ba sai yaji wayar sa ta 'dauki 'kara.

Hannu ya kai ya 'dago wayar sai ya saki wani sabon murmushin ganin sunan Ammi..gyara muryar sa yayi tarwai sannan yayi mata sallama daka ji muryar sa zaka san lafiya cikakka gare shi ba wani alamun jinya tattare da shi, abinda yasa kullum Ammi bata damuwa kenan domin haka kullum take jin sa idan suna waya da shi.



A lokacin Noor ta tsagaita da kukan ta illah ajiyan numfashi dan haka itama taji 'karan wayar tasa.


Tana amsa sallamar yace" Ammi na..!"
" Kayi min shiru! me ke damun ka tell me?"
" Ni bakomai Ammi".
Ya bata amsa yana murmushi.
" Yanzun nan fa matar ka ke ce min ko motsi baka iyawa shine nake jin muryar ka haka nd u ar still telling me bakomai...wai meke faruwa ne dan Allah Mu'een?"

" Lafiya ta qalau Ammi..kawai fa wasa nake yi mata".
" Baka da hankali!.."
" Thank u Madame"
Ya bata amsa yana murmushi.
Tace
" Idan ka sake rikita min yarinya Allah ni da kai Mu'een zaka zo ka same ni ne"
Yana 'yar dariya yace
" Sorry Ammi..yarinyar taki ne bata ji shiyasa"
" Haka ma kace ko to wallahi ka yadda ta sake 'kira na kan hakan ka gani..kasan hali naai ba sai na sake gaya ma ba, this time around idan na dawo da ita gaba na har abada tsakanin ka da ita sai dai hange..ai kasan wace ni".
" Ai kuwa da mutuwa zan yi Ammi...itace bugun numfashi na fa..".
" Ka gwada ka gani kana wasa da ni ne..."
Dariya sosai yayi sannan yace
" Kiyi ha'kuri Ammi insha Allahu baza'a sake ba...daga yau na daina".


Noor dake parlour jin muryar sa yana waya garau ya sanya ta tahowa da sauri dan ta ganewa idanun ta shin kunnuwan ta 'karya suke yi mata ko kuwa dagske shi 'dinne har da dariya.
Zaune ta hange shi kunnan sa ma'kale da waya yana dariya.


Mutuwar tsaye tayi tana duban sa da tsananin mamaki take cigaba da sauraran surutun da yake yi.


Mutum da ko hannun sa ma baya iya 'dagawa shine kuma yanzu take gani zaune har yake wannan uban surutun?







Comment
Vote
Share









*Salmerh ce* 😍

πŸ’• *NOORUL* πŸ’•
(Haske nah)



By
*Salmerh MD*


*Wattpad @*
*Serlmerh-md*



πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
πŸ’«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*



_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_



*Last Page* πŸ’―


*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*



πŸ…Ώ *94*


Mamaki 'karara ya bayyana kan fuskar ta, sai ta rasa shin kuka zata yi ne ko kuma dariya...yana cire wayan daga kunnan sa suka ha'da idanu da ita.


Murmushi kawai yayi gami da cire duvet daga saman jikin sa ya tashi ya nufi bayi tsab kamar bashi babu wani dafe 'kirji da ri'ke bango bai ko sake kallon inda take ba ma.


Tana ganin ya shige bathroom da kansa taji wani 'kululun takaici ya kamata ashe dama lafiyar sa 'kalau shine yake ta wahal da ita.


Komawa tayi jikin window ta dafe 'karfen windown tana hawaye..babu tunanin da bai zo ranta ba, sam ta rasa dalilin da yasa yayi mata hakan.


Fitowar sa daga bayin sai yaga bata inda take tsaye..bai tsaya ba sai ya bi bayan ta inda ya hango ta jikin window tana kuka mayafin dake kanta ya 'dan zamo yana iya hango tsefaffen gashin kanta dake nan 'daure cikin ribbom guda.


A hankali.ya tako zuwa inda take ya matso daf da ita da kansa yasan be kyauta mata ba dan wahala sosai ya bata ya ringa yi mata wasa da hankali.

.. ..kusa da kanta ya kawo fuskar sa yana sha'kan 'kamshin da kanta ke fitar wa...a hankli ya maida idanun sa ya lumshe tare da matsawa jikin ta sosai.

Tana jin motsin sa kusa da ita kawai sai ta juya gami da sar'ke hannun ta a wuyan sa bai wani 6ata lokaci ba ya ha'de musu baki ya fara kissing 'din ta irin wanda ta manta a rayuwar ta cewa ana yin irin sa...lumshe idanu tayi tana kar6an sa'kon nasa gami da jin zuciyar ta wasai musamman da yake yanzu ta fahimci cewa mijin ta lafiya 'kalau yake babu abinda ke damun sa.


Tsawon lokaci kafin ya rabu da ita wanda kamar jira take kuma sai tayi saurin juya masa baya tana fuskantar windown.


Murmushi mai 'kayatarwa yayi gami da kai hannun sa gefen wuyan yana yi mata tafiyar tsutsa yace" What kuma?...bayan kin gama cinye min baki shine kuma zaki juya min baya?"
Ya 'karasa maganar da sau'kar da kansa saman wuyan ta.
Kafa'da ta no'ke tana lumshe idanu amma bata ce da shi komai ba.

Abubuwan
da taji yana fa'dawa Ammi cikin waya sune suke dawowa 'kwa'kwalwar ta...murmushi tayi tana jin 'kaunar mijin ta na ratsa mata zuciya.


Ganin baza ta juyo ba ya sanya shi cire hannun sa daga jikin ta ya 'dan matsa baya ka'dan yana murmushi...'kirjin sa ya dafe gami da fa'din" Wash..!"
Ai da sauri ta waigo tana zare idanu har ta ma manta da cewa ciwon 'karya yake yi.


Da ganin ta juyo 'din sai ya tuntsire dariya yana nuna ta...kicin-kicin tayi da fuska tamkar zatayi kuka.." Ba gashi kin juyo ba yanzu ai na gano maganin masu taurin kai cikin sau'ki".


Shagwa6e fuska tayi ta taho da sauri zata gifta gefen sa ta wuce sai yayi saurin kamo hannun ta fa'da jikin sa ya rungume ta.

Dukkan su ajiyan zuciya suka sau'ke mai cike da ma'anoni da dama.




*****
Cikin lokaci 'kan'kani suka daidaita zaman auren su har ma sun fara shirye-shiryen komawa gida inda Deen yace da zarar sun koma zasu wuce Umrah dan cika burin Jasmine 'din su kamar yadda yayi al'kawari.



Yanayin 'kaunar da yake nuna mata ita kanta yanzu tasan ba irin na baya bane...sannan ko ita kanta ma bata yadda ta sake yin wani sakaci kamar yadda ta aikata abaya ba.


Sosai ta ri'ke mijin ta hannu bibbiyu ta jashi a jiki.
Sam yanzu bata kuskuren hana shi hakkin sa dake kanta dan ta fahimci ko abubuwan da suka ta faruwa abaya ma ciki harda laifukan ta.


Darasin rayuwa kala-kala yanzu ta koya.
Wani sa'in har ji take kamar yanzu ne suka yi sabon aure da shi domin sai yanzun ne suka yi sha'kuwar da ya kamata ace sun yi ta tun a baya amma sai suka kasa fahimtar junan su wancan lokacin.


Ko lokacin da suka koma gida ma ba 'karamin farin ciki Ammi tayi da ganin su ba, jikin Deen ya 'dan koma sai dai har yanzun ba kamar baya can da yake rayuwar sa cikin farin ciki ba.


Sai dai da yake har yanzun bai daina kar6ar magunguna ba ya sanya basu wani damu ba domin sun san with time komai zai daidaita ne, balle ma sun san yanzu ya riga ya samu abinda yake so in ba wani ikon Allah kam tafiya mai nisa ciwon zai yi.
Yana zuwa kuma ana sake duba shi a duk lokacin da bu'katar hakan ta taso...sannan baya sa6a dokar shan maganin sa bisa 'ka'ida yake shan su, da ya 'dan kuskure lokaci ma Noor zata tunatar da shi.


Ummah kanta ji tayi kamar ta goya su saboda farin ciki sai dai kunya bai barta ta bayyana hakan a fili ba...Albarka ta ringa sa musu tana yi musu fatan Alkhairi cikin rayuwar su da samun zuri'a 'dayyiba.


Satin su biyu da dawowa suka wuce Umrah...Yah Deen da ya gansa gaban ka'abah sosai jikin sa yayi sanyi...Noor kuwa kasa jurewa tayi sai da ta zubda hawaye, bata ta6a manta kalaman Jasmine da kuma burin ta na son zuwa Makkah da Madinah taga 'dakin Allah ba, yau gashi Allah ya nufe su da zuwa amma babu ita.


Addu'ah sosai suka yi kafin su dawo...ko a Madinah sai da suka 6ata lokaci sosai dan kusan satin su uku kafin suka juyo gida.


Ginin da ake yi na gidan mai 'din Ammi ma ba'a jima da kammala shi ba... *T. Manga and sons* aka sanya wa gidan man.

...Ishaq Alhaji Baba ya 'dora matsayin manager na gidan mai 'din dama a kullum burin sa bai wuce yaga yayi wa Ishaq wani abin da zai taimaki rayuwar sa ba domin yanda Ishaq ke son zuri'ar sa ka'dai ya sa yake birge shi balle tuni ya koma yi masa kallon 'da kamar su Muhammad, har cikin zuciyar sa yake jin sa.

Sosai Ishaq ya nuna tsantsan farin cikin sa da wannan karramawa da Alhaji yayi masa dama aikin da yake yi ba wani ku'din kirki ake biyan sa ba 40k ne duk 'karshen wata ake bashi, sai ga shi tashin farko matsayin manager ya fito inda za'a biya shi maku'dan ku'dade...amfanin zama da mutane masu karamci kenan.


Hatta Sani da ke can jihar Plateau Alhaji Baba sai da ya nemo shi shima ya bashi aiki agidan man, cikin sa'a kuwa albarkar Allah tuni ta sau'ka akan sa...sosai suke samun 'karuwa abin ba'a cewa komai.


Saif ma anan yake aiki sai dai bai kai Ishaq matsayi ba Sani kuwa dama dake be yi wani karatun kirki ba a matsa mai kawai ya tsaya...Zaidu kuwa na can wurin Uncle Ja'afar shima a shekarar nan yayi retire daga aikin sa sai dai babu ranar dawowa gida, dan kuwa acan ya samawa Zaidu aiki shima a wani bankin daban mai suna Gt ba wanda yayi nasa aikin ba.


Tuni anyi bikin Ishaq ya tare da amaryar sa anan Azare, nuna mata matsayin da gidan Alhaji Taheer Manga ke da shi a wurin sa yayi koda wasa baya nuna mata wani bambamcin da zai sa taji ta raina wani daga cikin familyn, matsayin iyaye ya basu ita ma kuma kan hakan ya 'dora ta.

Imrana kam na can tun da 'yan drugs suka tafi da shi ba'a sake jin 'duriyar sa ba...ashe wai sai da 'kwayoyi yake yi da manyan abubuwan maye shiyasa har yanzun ba'a sake shi ba.


Mu'een duk ya manta da shi sai ranar yana wucewa ya hango wasu 'yan shaye-shaye shine Imrana ya fa'do ransa da yake ya jima da sanin cewa inda Imrana yafi kauri kenan amma duk da hakan yake abota da shi da kansa ya sha bashi ku'da'de yana zuwa yana sayen kayan mayen sa da shi, tun lokacin da suka zo gidan sa ne shikenan yaji ya fita ransa bai kuma neman sa ko shiga harkar sa ba.

Sake kallon su yayi sai ya girgiza kansa, yara 'kanana ne amma duk sun lalata rayuwar su da shaye-shaye.
Cikin zuciyar sa ya furta Allah ya sauwa'ka ya shirya mu baki 'daya...Allah ya baku baki amma 'karfi da yaji kun maida shi salansa kuna ta 'karawa duniya hazo...manyan ku ma basu ci nasara ba balle ku... *_Allah Ubangiji ka raba mu da aikin dana sani da mu da Zuri'ar mu da ma Al'ummar Musulmai baki 'daya_ .*


Anan gidan man Sani ya samu wata me sai da goro suka daidaita ta kuma amince da shi duk da yake tasan yana da matsalar hannu 'daya amma bata 'ki shi kamar yadda 'yan can garin su suka guje shi ba.


Sai dai bai tashi sanin wace ya aura ba sai bayan auren nasu nan ya fahimci sauran gardawan ya kwasa...bai ce da ita komai ba domin yasan duk cikin hukuncin sa ne da Allah ya tanadar masa badan hakan ba ba zai ta6a ha'da shi da ita ba balle har yaji tayi masa cikin zuciya.


Yasan alhakin Jasmine bazai ta6a barin sa ba,
kuma da yake yasan ba'a yiwa Allah wayo shiyasa be wani damu kansa ba domin yasan komai na tafiya ne bisa tsarin mahalicci, koda yace zai rabu da ita be kuma san wace kala zai sake karo da ita ba...hakan yasa dole ya watsar da komai ya ja matar sa ajiki suka yi zaman su lafiya lau dan biyayya ne da ita sosai.
*_Allah ka raba mu da kusantar Zina balle har mu aikata shi_*

Kusan lokaci guda matar Ishaq da matar Sani suka sau'ka dan tsakanin su bai fi 3weeks ba...Matar Ishaq ce ta fara haihuwa inda ta haifi 'yar ta mace mai kyan gaske...sunan Ammi Ishaq ya sanyawa Babyn inda suke 'kiran ta da Nana.
Matar Sani ma mace ta haifa shima kuma ya sanyawa Babyn sa suna Aisha amma bai sanar da kowa sunan da ya sanya ba, kunya yake ji ya furta cewa sunan Jasmine ya sanya, hakan yasa ya bar abin sa aran sa shika'dai...Baby ake ce da yarinyar Sani.


Noor ce dai shiru har yanzu..Deen tuni ya koma bakin aikin sa shima sun koma Abujan gaba 'daya da zama..zaman su suke mai cike da so da 'kaunar juna basu yadda su 6ata lokaci wajen tuno abinda ya riga ya wuce musu.


Husnah sai da ta shekara goma da aure kafin a shekarar Allah ya nufe ta da samun ciki, murna kamar zata ha'diye kanta, Hisham ma kamar ya goya ta, Husnah kam banda godiya ga Allah babu abinda take yi ga yaran Hisham duk sun yi wayo suna makaranta...Mummyn ta tafi kowa farin ciki dan abinda ta jima tana jira ne yau Allah ya bata, daga Husnah bata da kowa sai yanzu da Allah ya nufe ta da samun rabo...itama yanzu da'di take ji zata zama kaka na asali.

Koda lokacin haihuwa tayi sai ta sam6alo 'danta namiji 'katoto da shi.

Sunan mahaifin ta aka sanya wato Hamza amma Daddy suke 'kiran sa...Husnah sau da dama agaba take sa yaron tayi ta kallo tana murmushi.
*Ashe in da rai da rabo...Bai kamata 'dan Adam ya cire rai da rahamar Allah ba.*




*****
Zaune yake yayin da Noor ke kwance tayi matashi da 'kafar sa...yanzun nan ya gama cire waya a kunnan sa Anas ya 'kira shi da Albishir 'din matar sa ta haifa masa Baby girl karo na biyu...da farin ciki ya sa albarka gami da fa'din sai munzo suna yana dariya ya cire wayar a kunnan sa.


Duban ta yayi ta wani lumshe idanu...sai ya kai hannu jikin ta a 'ko'karin sa na son 'dago ta amma ta sake narkewa..." Tashi mana albishir zan yi miki fa..?"
" Na riga naji ai..Allah ya raya mana ita.."
Ta bashi amsa da idanun ta a lumshe.

" To tashi muyi magana please...nifa na fara 'kosawa...3yrs fa yanzu da dawowar ki amma shiru har yanzu..gaskiya dole ne na duba ki in san abinda ke faruwa...".
" Ni dai a a...".
" Ni kuma nace Erh...so nake nima na fara raino...kin ganin yarinyar Ishaq har ta fara 'kiran Daddy fa..gaskiya da sake dole in san abin yi...".
Har yanzun idanun ta a lumshe tace" Ka kar6o mana aron ta kawai mu zauna da ita shikenan ka samu abin rainon ka...ni kaga dama ba so nake in sake haihuwa ba..".

'Bata rai yayi nan take..da 6acin rai yace" Baki da hankali...".
" Dagaske ban so ni".
" Nuree ban son shirme..."
Zatayi magana yayi saurin dakatar da ita.

'Karfi yasa ya 'dago ta zaune sai gata daf da dashi sosai, ta firgita ma she thought marin ta zai yi sai kuma taji shiru hannun sa taji yakai 'kasan marar ta yana yawo da shi wanda hakan yasa tayi saurin bu'de idanun ta ta sau'ke su akan fuskar sa.


Murmushi taga yana yi memakon 6acin rai da taji cikin muryar sa, da mamaki sai tsaya duban sa..bakin sa ya sau'ke saman la66an ta ya sumbata gami da matsa marar tata da 'dan 'karfi sai ta saki 'kara.

A kunne ya ra'da mata" Naki albishir 'din kenan...".

" Me hakan ke nufi wai?"
Ta tambayi kanta mamaki 'karara kan fuskar ta...hannun ta ta kai kan nasa itama ta shafo cikin sai yace mata" Kinga ikon Allah ko..dama mugunta kike so kiyi min baki san Allah na so na ba...ba tun yau na fahimci kina 'dauke da ciki ba kawai gudun ruwan ki nake son gani dan naga alamar baki da mu da rashin cikin ba ke ashe ban sani ba dagaske baki 'kauna ta..".


Shiru tayi tana jin tsananin fargaba na kamata, ita fa ba wai bata son haihuwa bane kawai tsoro take ji kar labari ya sake maimaita kansa akan abinda zata kuma haifa, shiyasa ta tilastawa kanta ha'kura da haihuwa gaba 'daya.


Allah ma sai ya dubi zuciyar ta ya ja mata lokaci har cikin eanta take jin ta ha'kura da haihuwa indai zasu yi rayuwar su a hakan dashi bazata ta6a damuwa ba koda kuwa basu da 'da ko 'ya agaban su har abada..shiyasa tun yanzu take jin tausayin abinda ke cikin cikin ta.


Hawaye ne da bata shirya musu ba taji sun gangaro saman kuncin ta..Yah Deen kam tsayawa kallon ta ma yayi sosai take bashi mamaki.


Wasa-wasa Noor sosai ta 'daga hankalin ta akan cikin duk ta tashi hankalin ta ta hana shi natsuwa, sosai yake kwantar da murya ya mata nasihar amma abanza, tsakanin ta da Allah take nuna rashin son cikin, har sai ma ya rasa yadda zai yi da ita.

Ya fahimci so take ta rabu da cikin cikin ko wani irin hali, sai da ya fito a Mu'een 'din sa ya nuna mata cewa hauka zai mata idan ta kuskura ta salwantar masa da cikin sa...kafin ta 'dan rage haukan da take yi.


Amma kullum tana cikin kuka, tunda labarin cikin ya bayyana mata basu 'kara walwala a gidan ba.

Daga 'karshe sai da batun ya kaisu har wajen iyayen su, da 'kyar Noor ta ha'kura akan zata haifi cikin bayan Anty tayi mata nasiha sosai da al'kawarin da ta haifa zata 'dauke a wurin ta...misalai da dama Antyn ta bata inda tace" Ni kaina ma babban misali nake Noor idan kin bada hankali, rana guda aka 'daura auren mu da Ammin ku amma Allah cikin ikon sa har yau bai ta6a bani haihuwa ba, nayi kuka munyi Addu'ah 'karshe dole muka ha'kura muka fawwala Allah komai, yanzu haka na riga na cire raina da samun rabo shiyasa kika ga ina ruyuwa ta cike da walwala domin ban isa in ce da Allah miye dalili ba....amma ke gashi kin samu cikin sau'ki amma kina wasa da damar ki ta hanyar ki maidawa Allah babban kyautar da yayi miki, a kaf 'din rayuwa babu abinda yakai kyautar 'da da kuma lafiya da Allah yake yi mana domin duk dukiyar ka baka isa ka siya ba har sai yaga dama, godiya ya kamata kiyi baki nuna ba fushin ki ba Noor.
Banda kuka babu abinda Noor ke yi dan a ganin ta har yanzu basu fahimce ta bane shiyasa, ita da kanta tana son taga 'ya'yan ta amma bazata juri ganin ba'ka'ken ta6o ajikin su saboda uban su ba shiyasa ta ha'kura kawai, hala sun manta da abinda ya faru da Baby ne.
Ganin ta kasa kwantar da hankalin ta ne ya sanya Ammi ta hana ta komawa Abujan ta zauna da ita tana bata kulawar da ta dace...shi kansa ma hakan yafi masa dan 'daga masa hankali take yi idan tana kusa da shi.


Kwanaki na ta tafiya cikin Noor na sake girma, sai dai zuwa yanzun Alhamdulillah ta kwantar da hankalin ta sosai saboda yawan nasihar da ake yi mata, ita kanta yanzu tasan cewa kuskure ta aikata domin kuwa duk abinda Allah ya tsara kai baka isa ka canza shi ba, wayon ta bai isa ya kawar da shirin Allah ba matu'kar ya riga yace sai ya faru.


Bayan wata tara da 'yan satikai ta haifo yaranta kyawawa guda biyu mace da namiji...inda yaron yaci sunan Alhaji Baba amma ana 'kiran sa da _Affan_ macen kuma sunan Anty Zainab aka sanya mata se ake 'kiran ta da suna _Farrah_ .


Tunda ta haife su kuma saj taji 'kaunar abinta ya sake kamata, haka ta cigaba da rainon abinta bata 'kara nuna musu 'kyama ba Addu'ar ta ayanzu kawai shine Allah ubangiji ya raya mata su ya kuma basu kariya a duk inda suke...





*****
_Bayan shekaru biyu_
Tsaye take a kitchen da tu'ke'ken cikin ta hannun ta wu'ka ne tana slizing green beans a hankali dan kar ta kuskure.


Gidan shiru cuz yaranta duk basu nan, Affan na can wurin Ammi yayin da Farrah aka yi can gaba da ita wurin Anty Zainab tuni an tattara mata kayan ta can, hakan yasa banda 'karar T.v dake aiki a parlour baka jin komai sai ko kuma idan kayo hanyar kitchen kaji kwarabniyar da take yi.


Tana daga kitchen 'din tajiyo muryar sa yana 'kiran sunan ta kamar wanda akace masa bata gidan ne.
" *Nureen-Deen* !"
Ya sake anbata a karo na uku.
Noor bata amsa ba illah murmushin da take yi daga inda take tsaye tana mai cigaba da aikin ta.
Yanzun fa ya fita zuwa masallaci kuma yasan aiki take a kitchen amma yake ta fama 'kwala 'kiran sunan ta.


Kitchen 'din ya nufo sai ya tsaya daga bakin 'kofa ya wani kama kunkumi..gira ya 'dage da alamun 'kosawa yace" Ya ina ta 'kiran Nureen-Deen amma bata amsa ni ba?"

Tana murmushi ta bashi amsa da fa'din" May be bata ji ka ba ne shiyasa ".
Tayi maganar ne batare da ta waigo ta dube shi ba.
Gaba tayi zuwa wajen sink tana wanke hannu yayin da ya 'karaso ta bayan ta ya sarke hannuwan sa a wuyan ta yana sau'ke numfashi.
" *_Nuree na_* "!
Ya ra'da mata a kunne gami da sumbatar bayan wuyan ta.
Fuskar ta 'dauke da murmushi ta sake fa'din" _Ni ban ji ba_ ".
" *Hasken Deen* ".
Ya 'kara fa'da yana mai gangarawa da hannun sa zuwa saman cikin ta.
" _Har yanzun ni banji ba_ ".
Ta sake fa'da tana mai 'ko'karin kwatan kanta daga jikin sa tayi gaba zuwa gaban Gasscooker ta sa hannu tana juya ha'din kayan miya da take soyawa...fuskar ta cike da murmushi.

Sosai ya sake matso ta ya rungume ta a jikin sa ta baya tsam sannan ya sake ra'da mata" *Ciwon zuciyar Deen* ". Cikin kunne.


Wannan karan dariya ya bata sosai ai kuwa tana fara dariyar shima ya taya ta yana jan baya yace" Ai gaskiya ne...." *Nuree na itace ciwon zuciya ta...*".
Kai ta girgiza masa sannan ta cigaba da abinda take yi murmushi ya kasa bariΓ± fuskar ta.


_They live happily ever after....._


*_Tammat bi hamdil-lah_*


*Me na manta?* πŸ€”
*Idan ma akwai kuma kuka tuna to ku jefa shi nan inda ya dace da shi...sai kuma ayi min afuwa domin ba laifi na bane laifin Brain 'dina ne* πŸ€—




*Alhamdulillah!!!...*πŸ–ŠοΈ
_Anan na kawo 'karshen wannan labari mai suna *NOORUL (Haske nah)...* wannan duk abubuwan dake cikin sa yake 'kir'kira ta ce ba da sunan wani ko wata nayi shi bs, in ma yayi kama da labarin ki/ka ayi min afuwa kuskuren al'kalami na ne bada niyya na aikata ba, ina ro'kon Allah ya yafe min dukkan kura-kuran dake cikin sa ya kuma sa a fahimci sa'kon da labarin ya 'kunsa...(Ameeen Yah Allah)_

_Duk Abinda aka tsinta ciki na kuskure kuma ayi min afuwa ba dan ni ba, duk abinda be yi miki ko maka cikin labarin ba shima dan Allah a watsar da shi kawai kunsan 'dan Adam Ajizi ne ba lallai ne in iya farantawa kowa dake bin labarin ba._


_Masoya na dake wattpad da whatsapp ina gaisuwa ina kuma mi'ka 'dumbin godiya ta, bazan iya lissafo sunayen ku anan ba amma ku sani wallahi ina 'kaunar ku irin unlimited 'din nan._
_Musamman 'yan group 'din_
*DA BAZARMU WRITTERS ASSOCITAION.*
*SALMERH MD PALACE.*
*NOORUL FANS GROUP* *UNIQUE ONLINE HAUSA NOVELS* _....Alherin Allah ya cimmaku a duk inda kuke 'yan uwa na...Allah ya kare ku daga sharrin CORONA, cututtukan zamani da ma dukkan wani abin 'ki._ πŸ™

~*Salmern ku nayi muku fatan Alkhairi*~ 😍
_Sai wani lokacin kuma idan Allah ya kaimu in ma zan iya kenan kun san sai a hankali rubutun ba sauqi wahala yake bani sosai_.πŸ€—
πŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”š




*Taku har kullum Miss Salmerh MD*.







©️ *2020*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu

Please Login or Register in order to submit comment