Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

'kara fa'da daga 'karshe.

Sau 'daya kawai ya kalle ni sai ya maida idanun sa kanta yace " Asma'u...ina son ki".

Jin maganar nayi tamkar sau'kar ruwan sama gatsau wani iri hakan ya sa na kalle shi sannan na kalli Ma'u.

Sai yanzun Ma'u tayi magana bayan ha'de goshi da tayi da jin wai yana son ta a yatsine tace da shi" Hum-um ni dai bana son ka waccan na gidan nake so"!
Ido Imrana ya zaro yana duban ta yace
" Wa wai kike nufi?...Deeni?"
Sai ta 'dage kanta.

Murmushin gefen baki yayi ya cusa hannun sa cikin aljihun wandon jeans dake jikin sa gami da fa'din " wahallalliya, angaya miki shi 'din zai so irin ki ne? Da manyan yara yake tarayya ba da 'yan mata irinki ba, gara ma ki tsaya ki fuskanci rayuwar ki...ni nan nine kalar ki....".

Bai kaiga rufe bakin sa ba nace " Ma'u ni kam zan tafi kar Ammi tace na da'de".

" A a mu tafi nima gida zani".
Ma'u tayi maganar gami da kaucewa daga gaban sa.
Daga haka muka ra6i gefen sa muka yi wucewar mu.

Imrana kam juyowa yayi ya biyo mu da idanu yana smiling, saboda wani tunani da ya 'darsu cikin ransa.

Kafin mu rabu ne da mamaki nace da Ma'u " Wai ke Yah Deen kike so?"
Sai tamin shiru tana kallo cikin idanu na...Baki na ta6e sannan nace " Indai wannan ne marin sa ka'dai ma zai kashe ki Ma'u...mugu ne fa shi sosai".

" Ni dai inason shi"!
Abinda Ma'u tace ka'dai kenan kanta a 'kasa.
Baki na 'kara ta6ewa nace " Allah ya yaye miki".
Bata 'kara tanka ni ba har muka rabu.

Ni kuwa har na isa gida ina mamakinΒ  ta a zuciya ta, wai ita tarasa wa za tace tana so sai Yah Deen " Ta6"...har sai ma naji tana bani tausayi.

Ko da naje gida kuwa Ammi fa'da sosai ta fara yimin inda tace na da'de daga raka ta kuma sai inje in zauna, ni banga ita bata da'de agidan mun ba shine ni zan bita har gidan su, kenan ta fini wayo tunda jana tazo yi tace ai da tasan zan da'de da ba zama ta barni in bita ba..daga 'karshe sai tace idan ina yawo irin haka zata saka Mu'een ya zane ni".
Ammi ta fa'di haka ne saboda ta san ina tsoron sa wai ko idan naji hakan zan kiyaye gaba...bata san cewa tsoron nawa ya zarce misali ba...dan kuwa tunda naji tace zai zane ni nayi narai-narai da idanu ina kallon ta nace " Dan Allah Ammi kiyi ha'kuri..bamu gama sharar bane da wuri fa shiyasa muka da'de..ni dai kar kice masa ya zane ni".
Na 'karasa maganar hawaye na sa'k'ko min.
Da mamaki Ammi tace " Shara kuma ta me kuma a ina?"


Β 

Comment
Vote
Share



*Salmerh ce* 😍

πŸ’• *NOORUL* πŸ’•
(Haske nah)


By
*Salmerh MD*


*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
πŸ’«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

🀞🏻

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*


πŸ…Ώ *39*

" Ai shine ya sani sharar"!
Wannan karan ina share hawaye na nayi maganar.
" Waye?".
Ammi ta sake tambaya ta tana mai bada dukkan hankalin ta gare ni.
" Yah Deen 'din ?"
Na bata amsa hawaye na na sake gangarowa.

Salati Ammi ke zubawa da jin abinda na fa'di, tana tafa hannuwa tace "
Hudah dagaske shine ya saki shara?"
Da kai na bata amsa alamar " Erh"
Wannan karan Ammi baki ta ri'ke cike da mamaki tace" Allah Buwayi...Ina gidan nan ya akayi har yazo ya aikata hakan batare da na sani ba?".
Ina tura baki nace
" Ai ya da'de da fa'da min kuma yace kar ingaya miki in ba haka kashe ni zaiyi".

Dariya ma maganar tawa ta bata amma yanda Yah Deen ya ninke ta abaibai ya yaudaretan sai ya sa ta jin 6acin rai sosai, " Wato barazana yayi miki da kisa"
Ta fa'di a fili"..hmm lalle!... shiyasa ya daina neman atura masa kowa...munafiki ashe ya san munafurcin da ya 'kulla...zaizo ya same ni ai"

Ni kuwa ina daga tsaye sai goge idanu nake yi kamar zan cire su, a lokacin tsoro biyu ne suka ha'du min, ga na kar Ammi ta sashi ya zane ni ga kuma tunowa da nayi cewa ya hana ni sanar da ita wanda hakan ya sanya hawayen nawa kasa tsayuwa.

Zama tayi ta gyara tare da janyo hannu na zuwa gaban ta kusa da ita, kafin ta furya komai na 'dago jajayen idanu na sauke au kan fuskar ta nace " Ammi kar ki ce masa na gaya miki dan Allah cewa yayi kashe ni zai yi"
Na 'karasa cikin kuka.

...Cikin lallami da kwantar da murya tace
" Haba uwata ina nan din kike tunanin zai kashe min ke kuma in barshi, 'kyale ni da shi zai zo ya same ni ne...kinji?"
Kaina na 'dage alamar Erh naji.
" Yanzu gaya min me ya faru duk karki 6oye min kinji ".
....Daki-daki na hau bawa Ammi duk amsar tambayar da ta min.

Takaici ne sosai ya kama Ammi jin yanda tsawon lokaci yake wasa da hankalin ta kamar 'kwallo...ya muzanta ta ya nuna mata bata isa ba, sannan ya girgiza mata igiyar al'kawarin da ta 'dauka kafin ta kar6o Noorul Hudah da wani irin fuska yake so iyayen na su dube ta ?"
Ran Ammi sosai ya 6aci da shi.
Abinda kawai ta iya 'karfin halin furta min a fili shine" Rabu da shi zai zo ya same ni"!

Ni kam take sai na marairaice fuska tuno irin kashedin da ya zayyana min gashi na warware wa Ammi komai, cikin kuka da marairaita nace " Ammi dan Allah kar kice na gaya miki Allah kashe ni zai yi".

Dai-dai nan Zaidu ya shigo 'dakin yana ta6e baki jin abinda nake fa'dawa Ammi, shi haka yake sam bai damu da damuwar kowa ba har ma sai nake ganin gara kowa ma akaina, domin iya tsawon zama na a gidan bai mun sha'ku da shi ya fara yi min kallon 'yar uwa ba yayin da ni nake jin su tamkar 6angaren jiki na.

Daga can hanyar corridor Saif dake biyo bayan Zaidu yake fa'din " ...Wai Zaid anya kuwa ka tuna siyan wannan...."

Cak maganar tasa ta yanke sakamakon ganin yanda nake rusa kuka...Ammi ya kalla sai yaga itama hankalin ta na kaina.
Take akalar tambayar tasa ta canza daga kan Saif zuwa Ammi inda ya karasa shigowa parlourn da sassarfa yake tambayar.." Lafiya Ammi me ya same ta?"
Ammi bata tanka shi ba kawai ta cigaba da duba na...shi kuma Saif ya 'karaso ya zauna daga gefen Ammi yana min duba a tsanake da son karantar yanayin da nake ciki.

Ammi kuwa 'dan takaitaccen murmushin takaici ta saki gami da kamo hannu na tana share min hawaye tace " Ki kwantar da hankalin ki, ba na gaya miki ba, ai be isa ya kashe ki ba matu'kar ina nan kar ki damu kinji?"
Sai na 'dage kaina sama.
" Yauwa...sannan daga yau ki daina 6oye min abu kinji..koma miye ya faru kar ki 6oye min bana son irin haka ni...ko me ya miki ki zo ki sanar dani, zanyi maganin sa, yanzu wannan da kin gaya min tuntuni ai da hakan ba zai faru ba, da ba zan ta6a bari ya ringa bautar da ke ba balle har su lattin zuwa makaranta, munafukin kuma ya sani amma ya basar...zai zo ya same ni ne...ni ina nan na saki baki ina tunanin ramar girma ce ta kamaki ashe ba haka bane..wani abin ne daban...hmm yaron nan na wasa da ni Allah".

Daga yanda Ammi ke furta maganar ma zaka san cewa ranta a tsananin 6ace yake hakan yasa da mamaki Saif ya 'kara jefa mata tambayar" Ammi wai meke faruwa ne na kasa ganewa".

Sai yanzun Ammi ta 'daga idanu ta kalle shi sai tace da shi " me ke faru kuwa Saif a gidan banda matsalar Yayan ku, fisabilillahi nawa yarinyan take da zai maida abokiyar hamayyar sa? ace tsawon lokaci ina gidan nan ban sani ba ashe kullum sai taje tayi masa bauta acan gidan ko makaranta bata zuwa a lokacin da ya dace, kuma abin haushi ma wai sai yayi mata barazanar kisa idan ta sanar da kowa...ji min hauka fa? Bansan me Mu'een ya 'dauki kansa ba gaskiya".
Ta 'karashe maganar da yaren su tare da watsa hannu.

Ajiyar zuciya Saif ya sau'ke tare da fa'din" Haba!..ai nima wallahi sai da na zargi wani abu tuntuni, Allah Ammi da Hudah fa ba haka take ba, amma kwanan nan naga duk ta canza bata fiye son shiga mutane ba, kuma fa ko makaranta idan nace zan rakata hanya 'kin yadda take yi...ko'ina zata bata son araka ta sam, ashe dan kar aga inda zata je ne shiyasa".

Tsaki Ammi taja tana kallon Saif cikin ido tace" See you, tun farko me yasa baka gaya min hakan ba to?"

Yana shirin sake yin magana ta Ammi ta kwa6e shi da fa'din" Shut up please ya ishe ni..ai kaima harda laifin ka Saif...wancan wawan kan ma nasan koda ya sani he won't tell saboda mugun hali".
Ta 'karashe tmaganar tana nuna Zaidu.
Da haushin ance mai wawa yace " Nima fa Ammi bansani ba".
" Kai ka sani ai.. useless kawai".
Ta fa'di cike da takaici.
Saif kam cikin kwantar da murya yace" Ammi sorry ni dai bansan haka bane Allah da kinsan bazan 6oye miki ba".
Shiru Ammi tayi bata sake tanka shi ba.
Ni kam kuka na na cigaba da yi bayan na kwantar da kaina bisa cinyar Ammi..ban 'kara fa'din komai ba cikin haka har bacci yayi gaba dani.

Ta shi na daga baccin kuwa sai na tashi da zazza6i mai zafi saboda tsoron abinda zai biyo baya tsakanin ni da shi, cuz koka'dan ban yadda cewa Ammi zata iya hana shi ta6a lafiya ta ba.


*****
Tun a ranar ba'a kwana ba Imrana yaje gidan su Ma'u da sunan zance ita kuwa ta 'kara jaddada masa wanda take so da yake tana tare da yarin ta itama shi yasa sam bata damu da bayyana sirrin dake cikin ranta ba, domin dududu shekarun ta sha biyar ne a lokacin.

Mahaifin ta ma daya ga Imrana tare da 'yar sa ai sai hankalin sa ya tashi sosai, ba zato ba tsammani kawai washe gari yasa ta shirya ya tura ta can wurin dangin mahaifiyar ta a Lanzai ko ita kanta Ma'un kuwa bata san dalilin tafiyar tata ba balle wani daban...dan a cewar sa sam be yaba da tarbiyar Imrana ba.

Ana gobe su Saif zasu tafi zazza6i na yayi tsanani sosai....hankalin Ammi kuwa ba 'karamin tashi yayi ba.

Ko lokacin da su Saif zasu wuce ma kuka na dingayi Ammi duk sai ta 'kara rikicewa har suka tafi basu samu natsuwar Ammi ba.

Bayan tafiyar su ne suka sake 'kiran ta awaya lokacin ina bacci.....sai a sannan hankalin su ya kwanta da suka ji tayi musu Addu'ah cikin natsuwa...anan Saif ya sake tambayar ta jiki na ta ce da shi " Alhamdulillahi da sau'ki".
Jin hakan ne ya 'kara kwantar da hankalin Saif har ya saki ransa a makaranta.

Kwana uku ina kwance ban zuwa ko'ina, Alhaji Baba da kansa ya 'kira likita ya dubani ya bani magunguna da Allura, ni kaina wannan karan ban san me yasa banji tsoro ba akayi min har guda biyu, sai dai magungunan kam ban iya na sha ba illah kuka da nake tayi wanda ganin haka yasa Alhaji Baba yace abarni kawai.

'Bangaren Yah Deen kuwa sai da ya kwana biyar cif bai sa ni a idanun sa ba, koma ba dan sharar da nake yi masa ba atleast idan ya ganni ya kanji natsuwa har cikin zuciyar sa, amma sai gashi yanzu ko gidan yazo baya gani na haka ban zuwa can gidan nashi, shine ranar ya ku'duri aniyar tambayar Ammi dalilin daina gani na da yayi.

Zaune suke kan Dinning daga shi sai ita da yake dama babu kowa gidan, Ammi ce da Alhaji da ni, Alhaji Baba kuwa tuni ya fita, ni kuwa ina 'daki ina bacci, shi ma 'din breakfast yazo yi shine suke zaune tare da Ammi, abinda yayi sosai yake bata haushi amma dan takaici ma sai ta tarasa me zata ce da shi...sai dai ko ba'a fa'da masa komai ba shi kansa yasan sakin fuskar da take yi masa kaso mafi yawa daga ciki babu shi yanzu, hatta gaisuwar sa a yatsine take amsawa kuma daga gaisuwar bata 'kara wani hira mai tsayi da shi sai dai be san dalilin faruwar hakan ba sam kuma bai tambaye ta ba.

Yah Deen ya saci kallon inda take a 'kalla kusan sau uku amma ya kasa furta abinda ke ransa, musamman dan ganin yanayin da fuskar ta yake ma...sai ana hu'dun ne kafin ya iya dauriyan 'kiran sunan ta cikin tsohuwar shagwa6ar da jima bai yi mata ba.

Da idanu kawai ta iya kallon shi sai ta kuma sau'ke idanun batare da ta furta komai ba.

Ganin hakan ya sanya shi yin gyaran muryfa tare da gyara zaman sa da kyau ya wani buga uban tagumi sannan yace" Dan wai ni Ammi laifin me nayi kwata-kwata yanzu bakya 'kauna ta..ko dan na daina zama a gidan nan ne?"

Ammi bata kula shi ba kawai ta cigaba da abinda takeyi koma kallon inda yake bata sake yi ba.

Bai 'dau abin wani serious ba dan iya tunanin sa bai hango laifin da yayi mata ba, hakan yasa yayi saurin kauda wancan zancen da fa'din" Ba ma wannan ba Ammi ni kwana biyu ban ganin 'yar kin nan ko tayi tafiya ne?"
Kamar ba zata yi magana ba sai can kuma tace" Wace 'yar ta wa kenan?"

Yah Deen cire tagumin yayi jin ta kula shi, har da 'dan ha'de gira as if tilasta shi akayi yin maganar yace..."..Nu..Noor ce wai ko ya ma sunan ne na manta".
Ya 'karashe da yatsina fuskar sa.
Cikin kwantar da murya Ammi tace" Baka gaji da bautar min da ita ba kenan?"
Tayi magnaar tana ajiye spoon 'din da ke hannun ta tare da gyara zaman ta.

Yah Deen kam ido ya zaro da mamaki yace " Ni kuma Ammi?"
" a a Ubanka...!"
"Toh ni Ammi wani irin bautar da ita zanyi?"
" Ka fini sani ai.. ko in ba hakan ba me yasa ka tambayar ta...ko kashe tan kazo yi har gida kamar yadda ka yi niyya?"
'Dan 6ata rai yayi dan ya fahimci inda zancen ya dosa a hankali yace
" Nifa Ammi ba haka bane...kawai danna tambaye ta laifi ne?"
"....Babba ma kuwa!....kai yanzu ko kunya baka ji sai kasa yarinya 'karama irin wannan agaba bacin kasan lokacin zuwa makaranta ce kai haka akayi maka?"
Shiru yayi ya 'dan lumshe idanu yana sauraran ta.
A tsawace tace " I'm asking haka akayi maka?"
Bu'de idanun nasa yayi da tuni har sun canza launi zuwa ja bai kalle ta ba kawai ya zubawa table 'din dake gaban sa idanu.
Yayin da Ammi ta cigaba da fa'din"...kai me yasa ka koma can gidan ba cewa kayi dan kayi karatu bane...shine dan iskanci ita kake 'ko'karin hanata nata zuwa nata makarantar karatu yafi karatu ne?...ko kuwa tsabar ka raina ni ne yasa hakan?"
Ta 'karashe maganar tana kallon sa.
A hankali ya 'daga idanu ya kalle ta tare da fa'din
"...Dan Allah Ammi kiyi ha'kuri..nifa ba nufi na kenan ba".
Kwafa tayi gami da fa'din
" Ohh nufin ka 6ata raina ko?"
" Haba Ammi?"
" Yi min shiru da Allah, me kuma zaka sake fa'da min tunda duk girman baka san kayi abinda ya dace da kanka ba har sai an tunatar da kai, and this is my last warning Mu'een wallahi ka kiyaye ni, idan ka kuskura na sake jin abu makamancin hakan ya faru zaka sha mamaki na, ni da kaina zan 'dauki mataki tunda ba kai ka kawo ta gidan ba, kaje kayi rayuwar ka acan babu ruwan ka da yarinya ta, ka bar min ita sha iska, ai kaima babu wanda ya takuraka dan haka ka ka bar min yarinya ba ita ta turaka can 'din ba so babu dalilin da zaka 'daura mata nauyin da ko ni ban 'daura mata ba ..."
Taran ta yayi da fa'din"..Ni dai kiyi ha'kuri Ammi.."
" Sai yanzu kasan da ha'kurin ai...kwanan yarinyar nawa ba lafiya amma baka ta6a tambayar ta ba sai yau da kake so tayi maka bauta kafin ka iya tambayar ta har ka bada ha'kuri ko..?..i thought ni dai muka rufe zancen tun da 'da'dewa..dan munafurci shine ka zagaya da yake isheshshe ne kai shiyasa ka nuna min ban isa ba, jibi yanda yarinyan duk ta 'kare ta lalace, ko tausaya mata baka yi dan mugunta....".

Murmushin dole ya 'ka'kalo ya sanyawa fuskar sa, dan ya fahimci masifar Ammin ba mai 'karewa bane...in dai akan wanna 'yar ne Ammi gwana ce wurin masifa...balle shi da ta kama dumu-dumu da laifin da acewar ta bautar mata da 'ya yake yi..." ko itan ba mace bace oho.." Yayi maganar cikin ransa.

A fili kuwa cewa yayi
"...Ai ban sani bane Ammi shiyasa...ina take in duba ta".
Tsaki Ammi taja ta kawar da kanta gefe, Yah Deen kam wani murmushin ne ua kubce masa sai ya mi'ke ya nufi 'dakin Ammin....tura 'kofar yayi a hankali sai ya hango ni zaune ina shirin sau'ka daga kan bed.

Tsaye yayi a 'kofa yana 'kare min kallo, koka'dan baiyi regretting abinda ya aikata ba, bai ma ji cikin ransa cewa laifi ya aikata ba in ka 'dauke abu 'daya shine lattin schhol da nake yi bayaga haka kuwa zuciyar sa fes.

Ni kam ina ganin sa sai zuciya ta ta tsinke da 'karfi take nayi narai-narai da idanu tamkar zanyi kuka..jiki na ya fara 6ari.

Sai da ya kuma waigawa ya kallo baya bansan abinda yake dubawa ba kafin a hankali ya 'karaso ciki ya iso gaba na ya tsaya yana kallon duk yanayin da na shiga.

Ni kam tausayin kaina ya sani zubda hawaye ina sunkuyar da idanu na 'kasa..farar shimi ce a jikina da wani skirt 'yar kanti da Ammi ta siya min, kaina ba ko hula sai tsefaffen gashi na da jinyar da nake yi ya hana ai min kitso har ranar.

Sai da ya gama 'kare min kallo wai ko zai hango ramar da yaji Ammi tace nayi amma shi kam bai fahimta ba ko dan bai san yanayin jiki na kafin faruwar hakan bane oho, iya abinda ya sani game da jikina tun farko dama shine banda wani jiki, to ko yau din ma iya abinda zai iya fa'di kenan bai ga sauyi ba, yana folding hannun sa a 'kirji yace
" Miye hakan kuma ?"
In da yayi maganar cikin natsuwa..sai na 'dago kaina na kalle shi..take kuma na sake yin 'kasa da kaina hawaye na gangaro min.
Sau'ke hannun yayi a 'kirjin sa ya cusa cikin aljihun wandon sa kafin yace
"... Ba cin kin riga ki fa'da har ta yi min masifan kuma miye na kuka? ko zazza6in ne ya tashi da gani na?"
Girgiza mai kai nayi alamar a a.
" To ya akayi?"
Ya sake tambaya ta.
Da muryar kuka nace
"..Dan Allah Yaya kayi ha'kuri kar ka kashe ni..ba zan sake ba, bazan sake gaya mata ba"!
Bai bi ta kan wancan maganar tawa ba kawai yace
" Me ke damun ki wai?"

Kafin nayi magana naga yayi saurin zama gefe na wanda sai da ga zauna 'din kafin nima na jiyo takun tafiya, take kuwa sai naji da'di har cikin raina dan nasan Ammi bazata bari ya cutar da ni ba kamar yadda take fa'da min kusan kullum.

Yah Deen kam harda kama hannu na tare da maimaita tambayar da ya min da farko kafin ya zauna...inda ya sake yin tambayar yana ta6a jiki na zuwa wuya na.

Ganin haka yasa nayi saurin bashi amsa da fa'din
"..Zazza6i"!
" Sannu.." Yace dai-dai sallamar Ammi da shigowar ta cuz batare da ta jira an amsa ba kawai ta 'karaso ciki.

Yah Deen kuwa har shigowar Ammi bai saki hannu na ba shi nan adole ya nuna mata cewa he cares for me..but ni ka'dai na san me yake min da hannun nawa, palm 'dina ya ri'ke cikin nashi dan haka sai ya cusa yatsan sa 'daya cikin tsakiyar hannu na a hankali yake yawo da shi wanda babu ta yadda mutun zai fahimci hakan in ba ni da shi da muke zaune ba..cuz ko Ammi da ta shigo bata lura da hakan ba idanun ta kan fuska ta batare da ta ko kalli inda yake ba ma tace " Kin tashi ko?"
Kaina na 'daga mata sama sai tace " To ki samu ki watsa ruwa sai ki same ni can parlour...magungunan ki basu 'kare ba..idan kin yi breakfast sai ki sha ko?"
Kai na 'daga mata ina marairaice fuska.
Wayar ta wuce zata 'dauka acan gaban mirror ganin haka yasa nayi yun'kuri nima da niyyar tashi cuz Allah-Allah nake ya bar inda nake, sai dai wani kallo da ya watsa min ya sanya nayi saurin komawa na zauna kamar yadda nake da farko still kuma bai saki hannun nawa ba bansani ba ko mancewa yayi da ni 'din wacece.

Har Ammi ta 'daukp wayar ta juya bai ce da ita komai ba haka nima, ganin tana shirin fita bata tanka shi ba ne yasa shi tambayar " Ammi wai meke damun ta ne?"
" Ka tambaye ta mana gata gaban ka ai".
Ta bashi amsa batare da ta ko kalle shi ba kawai tayi waje abin ta.

Murmushi ya saki batare da damuwar komai ba, dama ya san ba amsa mai kyau Ammi zata bashi ba kawai ya tambaya ne dan rasa abin fa'da shi a dole kar tace bai damu da jinyar tawa bane dagaske.

Ni kam baiwar Allah, idanu na 'kur akan connection 'din da yayi da hannu na nawa hannun 'dumi ne da shi yayin da nashi yake sanyi 'kalau, ji nake kamar in wafci hannu na in zura da gidu amma tsoro bazai barni ba, ban kuma san manufar hakan da ya yayi ba sam.

Idan kinga hannu na a cikin nasan abin tausayi, duk yadda nake fallin nafi su Addah Saudah Hasken fata compared to him ba'ka na dawo, idan ina tare da Yah Deen sai dai a 'kira ni da mai choculate skin, hasken sa tas ne shi irin na Ammi ya 'debo, dan shima sosai yafi su Saif hasken fata.

'Dan motsi nayi da hannu na dake cikin nashi sai yayi saurin sake min hannun tare da mi'kewa tsaye bai sake fa'din komai ba har ya juya ya kusa fita daga 'dakin sannan yace " Allah ya sauwa'ka".
Inda yayi maganar ciki-ciki tamkar dole aka sa shi furtawa.

Nima ban ko amsa shi ba kawai na bishi da idanu har bar 'dakin ya maida 'kofar ya rufe.

Da ganin haka kuma sai na maida idanu na kan hannu na da ya ri'ke 'din ina mai jin wani farin ciki na ratsani na ganin bai kashe nin ba, da yake dama fargaba ceke 'kara narkar da ni shiyasa da na ga bai kula ba kawai sai naji wani sanyin da'di har zuciya ta..zakiyi mamaki Hafsat kamar wanda ciwon ya cire min take naji ni garau illah rashin 'karfin jiki.

Kafin washegari kuwa har na warware abina kamar bani ba, Ammi kanta sai da tayi mamaki.

Haka kuwa na cigaba da rayuwa ta cikin kwanciyar hankali..ba na tare da damuwa yanzu dan zuwa ko'ina illah makaranta da Islamiya...ga shi Ma'u ma bata nan balantana ta dame ni...sabuwar rayuwa na fara mai cike da 'yan cin kai da walwala.



γ€°γ€°γ€°
_*Bayan sati biyu.....*_
Zaune muke ni da Ammi tana tsife min kaina sai wayar ta tayi ringing...tana gefe na wayar game na keyi da na gaji na ajiye ta gefe na.
Baki na ta6e da ganin suna mai 'kiran nata, bai jima da barin gidan ba kuma miye na 'kiran waya na fa'di cikin zuciya ta tare mi'ka mata wayar.

" Wa alaikissalam..."
Naji Ammi tace cikin kulawa.
" Ammi akwai wasu kaya na da na bawa Zaidu ya wanke min bai kawo ba tuntuni...na manta kuma 'dazu ban tambaya ba, please ki bayar akawo min".
Daga 'dayan 6angaren aka fadi hakan cikin natsuwa.
Ammi sai tace" Bani da 'dan aike ai ka sani ko?"
Dariya kawai yayi sannan ya yanke 'kiran.

Ammi sai da ta gama min tsifan tana mitar mantuwar karya me yasa da ya tuna bai dawo ya duba ba.

Kusan shu'dewar mintina a'kalla arba'in har mun kammala tsifan ta kame min da ribbom dan nace kitson sai da yamma zanje idan na huta da yake ranar bani da Islamiya.

Muna zaune wayar Ammi ta sake yin 'kara sai ta'ki 'dagawa, sau biyu aka kuma 'kira duk bata 'daga ba, sai da na ukun ya tsinke kafin ta ja tsaki gami da fa'din inyi ha'kuri in kai masa kayan in dawo kafin

Please Login or Register in order to submit comment