Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamar yadda suka yi buri duk cikin sati 'daya, harma sun fara 'ko'karin dawowa da tunanin barin Kano su koma Kaduna da zama gaba 'day musamman ma da suka ga yanayin garin yayi musu ba laifi sai suke ganin zasu dasa sabuwar rayuwa a can 'din.


Ana jibi zasu tafi ne da safe lokacin Aishatu na 'dan fama da zazza6i ko Tahir ma bai san da zancen zazza6in ba yayin da ya shiga cikin gari tun safe ya manta wayar sa a hotel 'din da suke 'din.....Aishatu kuwa zafin zazza6i da ciwon kai da take ji bai barta ta iya koda motsawa ba, tana jin wayoyin su na faman ringing amma bata iya ta 'daga ko guda 'daya ba, duk kuwa da tayi mamakin yanda wayoyin ke faman ruri lokaci guda amma hakan bai sa ta 'dauki 'kiran ba.


'Ko'karin da tayi ma shine tashin da tayi ta kakkashe wayoyin batare da tabi ta kan 'kira ko 'daya ba.


Tsawon lokaci sannan ya dawo kusan shabiyu na rana sai da ma yayi sallahr Zuhr kafin yabi ta kan wayar inda ya tarar da ita a kulle... Yaso yayi mamaki amma kuma tuna cewa Aishatu ce ka'dai zatayi hakan ya sanya shi kunnawa kawai ya bar batun mamakin.


Kunnawar sa
keda wuya kuwa sai ya tsinci 'kiran Manager cikin wayar kamar dama jira yake yi ya kunna.. ...'dauka yayi da tunanin zai masa bayani na 'karshe dan zaton sa ko har yanzu akan komawar sa bakin aiki ne dan haka cikin ransa ya shirya maganar da zai gaya masa akan cewa shi ba zai iya sake yin aiki da su ba har abada......sai dai ga mamakin sa bai kai ga furta abinda ke cikin ransa ba shima 'din hankalin sa ya tashi, cuz yanda yaji muryar Manager cikin damuwa sosai ya sanya shi shiga firgici lokaci guda.


Jikin sa sanyi yayi da ya sau'ke wayar daga kunnen sa, koda Aishatu ta tambaye shi ma bai iya yace da ita komai ba dan gudun 'daga hankalin ta.

Wannan dalilin ne ya sanya shi mantawa da duba sauran tarin missedcalls 'din da akayi masa.


Aranar ya wuce Kano batare da ta sani ba.


Manager ne yayi masa kwatancen inda zai same shi batare da 6ata lokaci ba kuwa ya wuce gurin saboda har yanzun baiji hankalin sa ya kwanta ba tun bayan da suka yi waya da manager a Kaduna.


Ba 'karamin mamaki yayi ba da yaji abinda Manager yace cikin 6oye ko wanene ke abin yayi masa bayani a ta'kaice kan cewa babban abokin sa ke neman ran Tahir 'din da iyalan sa ma gaba 'daya.
Tun jiya wai ake zarya a gidan sa har wayewar garin yau amma basu samu kowa a gidan ba kuma rashin ganin ahalin gidan ya sanya su fahimtar cewa basa kusa ne shiyasa, dan haka da safiyar yau suka sanya wa gidan wuta kuma ya 'kone 'kurmus.....


Cikin matu'kar razani Tahir ke kallon manager jin cewa an 'kona masa gidan sa a wayewar garin yau 'din nan.....kenan da bamu tafi ba da ikon Allah ne ka'dai zai iya ku6utar da mu a hannun su.
"..... Yah Rabbi.. "
Ya furta gami da dafe kansa.... Sai ga hawaye sun sau'ko masa take idanuwan sa sukayi jajur, bai san me ze ce kan wannan lamarin ba sam....musamman da yake ba sanin mai neman halaka shin yayi ba, mamakin sa kawai shine ta ina suka ha'da ala'ka yayin da tambayar abinda ya ha'da su ya tsaya masa a zuci.


Bakin sa har rawa yake yake wajen godewa Allah da ya basu ikon tafiya Kaduna cikin kwanakin nan...ya san ba komai bace hakan face kariya daga wurin sa in ba dan yaso kare su ba da babu abinda zai sasu yin tafiyar.
Duk dama ya san sun yi asara sosai a gidan wanda shi kansa ba zai iya irga su ba amma ba zai ta6a fasa furta Alhamdulillah ba.
Duk cikin zuciyar sa yake wannan tunanin yayin da hawayen sa ke sake gangara a hankali.


Manager ne ya dafa kafa'dan sa gami da cigaba da fa'din " ni kaina ina cikin matsala Tahir ta dalilin haka domin rashin samun ka ya sanya shi zargin ni na kawo maka labarin zuwan su, shiyasa ka gudu amma ban damu ba dan nasan babu wanda zai ta6a gujewa 'kaddarar sa ko a ina take shiyasa bazan 'daura ma laifi ba... Amma tun lokacin da na cire ka cikin wancen zargin ni kuma na cusa kaina ciki dumu-dumu batare da na sani ba...... Yanzu haka Tahir wannan ha'duwar tamu da kai babu wanda ya san da ita.... Na tausaya maka sosai jin cewa an 'kona gidan ka fargaba ta shine Allah yasa baka ciki domin ban samu dama na nemi yafiyar ka ba har yanzu, Tahir dan girman Allah kayi ha'kuri ka yafe min 6ata maka suna da nayi duk kuwa da nasan cewa baka da laifin komai amma naso biyewa son zuciya ta... ban cancanci kasancewa shugaba sama da kowa ba saboda na ci amana Tahir....
Sai dai gashi nima ban tsira ba domin yace naci amanar sa kuma zai 'dauki akaina.....please Tahir forgive me, sai daga baya nasan ban kyauta ba sam ban yi maka adalci ba"

Kallon sa kawai Tahir yake yi bai yi wani mamaki ba da yake tun farko ya san cewa sune suka bada report 'din a kamashi, in ma mamakin zai yi bai wuce na ji da yayi cewa shima saboda wani yayi hakan ba, babbar damuwar sa a yanzun kuwa bai wuce yaji ko waye wancen 'din ba mecece kuma ala'kar su.


Manager bai damu da shirun Tahir 'din ba sai kawai ya cigaba da maganar sa inda yace.
" Naji da'di sosai Tahir da ka kasance araye ma'ana baka 'kone cikin wannan gidan ba..... Dan haka ga wannan ka tafi can da nisa inda babu wanda zai takuraka kaje ka gina sabuwar rayuwar ka ka ingan ta rayuwar iyalin ka, nasan yanzu haka abubuwa da yawa ka rasa kuma nasan bazan iya biyan ka ba amma duk da haka bazan barka haka ba Tahir.... Ka tafi da nisa domin *Kido* ba zai barka ba matu'kar ya san kana raye. "

Yana gama fa'din hakan kawai ya cusa masa check 'din yayi gaba....
Tahir kam bai iya yace dashi komai ba.... Mutuwar tsaye yayi yana tunanin sunan da yaji manager ya fa'da.

.........Me yake nufi wai, *Kido* inkiyar Lawyern mahaifin Aishatu ne wanda suka sanshi da shi tun asali sai ma da yaje bincike ne ya samu bayanin cikakken sunan sa.....kenan barrister shine yake neman ransa?... Shine ya sa aka 'kone gidan sa? Shine.... Shine...yasa aka kama shi da laifin da bai aikata ba? Duk dan saboda dukiya ko me?
Ashe gaskiyan Aishatu ne... Gaskiyan tane da ta hana shi tunkarar sa tun abaya.... "


Har manager ya 6ace bai dawo daga tunanin da ya lula ba.


Tafiya manager yakeyi cikin sanyin jiki yana jin dad'in ya sau'ke nauyin da yake kanshi... Tsakanin sa da abokin san bai wani dameshi sosai ba duk kuwa da ya riga yasan kalan mugunta da rashin imanin sa amma yasan bai isa yayi masa abinda ba Allah bane ya tsara dan haka bai damu sosai ba.... Gudun kar Tahir ya'ki amincewa da batun tafiyan ne ma ya Sanya shi 6oye masa cewa ance ne ko ya kawo shi ko kuma shi abakin ransa..... Yaso ya kai report gun 'yan sanda amma yin hakan dai-dai yake da salwantar da rayuwar iyalan sa cuz dasu akayi masa baraza na kan kar ya yadda ya fara sako jami'an tsaro cikin lamarin.


Dan haka sai ya wuce gida kawai yana jiran yaga yadda Allah zai yi dashi.



'Bangaren Tahir kuwa lokacin da ya dawo daga tunanin a lokacin ya fahimci cewa Manager ya jima da barin wajen dan haka a hankali shima ya taka ya isa gaban motar sa da niyyar komawa Kaduna, har zai bu'de motar ya shiga sai kuma ya fasa.

Rufe ta yayi ya koma bakin titi ya tari taxi zuwa unguwar tasu inda ya ringa nuna wa mai taxi 'din hanya har kan layin nasu.


Nesa da gidan ka'dan ya tsaya ya dubi yanda gidan duk ya lalace bai 'kara mintina biyar masu kyau ba ya umarci mai taxi 'din fa'din su tafi kawai bai samu numbern wanda yazo gurin sa ba, ko mai taxi 'din Tahir bai yi saken da har ya gane abinda ya kawo shi layin ba kuma koda suka koma daga can bakin titi ya sau'ka inda ya gangaro da 'kafar sa ya dawo ya shiga motar sa take ya wuce Kaduna, Sallar la'asar ma a Zaria ya tsaya yayi ta daga nan ya wuce abinsa.


Yanzun kam da ya koma bai 6oyewa Ammi komai ba duk ya bata labari inda take ta sanya kuka tana dafe kai jin cewa ana neman su ne kunsan mata da tsoro.


Sai da yayi ta kwantar mata da hankali kafin ya samu tayi shiru amma ta kasa sakewa dan ko da dare ma kasa bacci tayi saboda tsoro.


Washegari ya fita bayan sun gama yaje ya saida motar dake hannun sa, sannan ya biya Bank ya ciro ku'da'den da Manager ya bashi check jiya na dubu 'dari 'daya daga ya koma masau'kin su kusan la'asar a lokacin inda yaje ya samu Ammi zazza6i sosai ya rufe ta.


Batare da 6ata lokaci ba suka wuce asbiti.
Inda bayan gwaje-gwaje da 'yan tambayoyin da likita yayi mata sai ya bisu da albishir 'din cewa tana 'dauke da juna biyu na kusan wata uku.


Murnar da sukayi har sai da ya kusan mantar da su damuwar da suke ciki.


Da komawar su sai Tahir ya 'kira Ja'far ta landline 'din dake gidan sa ganin lokacin ba lokacin aiki bane, anan ya sanar dashi komai duk abinda ke faruwa.

Shima Ja'afar 'din sosai ya damu da jin abinda ya farun....ganin kamar zai ja maganar cikin tashin hankali ne ya sanya Tahir dakatar dashi da albishir 'din cikin da Ammi ke 'dauke da shi.....ai kuwa take yanayin sa ya canza amma duk da haka farin cikin bai hana shi tambayar inda suke ba.

Jin cewa suna Kaduna a dai-dai lokacin ya sanya hankalin sa kwantawa gami da yiwa mahalicci godiya.


Bayan kwana uku da faruwar hakan suka tattara suka wuce can jihar Bauchi batare da sun sake tsayuwa cikin gari Kano ba.


Sai da suka sau'ka a gurin Ja'afar suka 'dan huta kafin suka 'karaso garin Shuwarin mahaifar su ta asali.....inda Ja'afar yayi-yayi da shi akan ya bari kawai su zauna tare amma Tahir ya'ki amincewa sam dole tasa Ja'afar ya ha'kura badan ya so ba da kansa ya shigo dasu suka sau'ka gidan mahaifin su dake can bayan makaranta.
Su biyu kawai suka taho batare da su Ammi ba sobada gidan na matu'kar bu'katan gyara dan an jima ba'ayi amfani da shi ba.


Nan Ummah taja dogon numfashi tace " to kunji dalilin dawowar Alhaji Baba garin nan da zama, bakomai bane face sharrin ma'kiya".

Dukkan mu shiru mukayi ni kam harda tagumi duk muna kallon Ummah yayin da fuskokin mu ya cika da tausayin su jin irin yadda suka sha fama da rayuwa.

Ummah bata bi ta kan mu kawai ta ci gaba da labarin ta.

" Sai da suka nemi masu aiki suka bada aikin gyaran gidan bisa jagorancin mahaifin ku sannan suka koma Azare.


Cikin sati guda aka gyare gidan tsab kamar bashi ba da yake ma 'karamin gida ne ba babba ba shiyasa gyaran bai 'dauki lokaci ba, ai kun gane gidan ko....wancen gida mai fenti dake nesa ka'dan da makaranta?"
Ta 'karashe maganar da sigar tambaya.


Nanne kai ta 'daga yayin da ni.kuma nace " ehh Ummah nagane shi kullum idan zani makaranta ai ina ganin sa a rufe".

Ummah sai tace " Yauwa to wannan shine gidan da Alhaji Baba ya fara zama bayan dawowar sa garin nan, kuma anan Ammi ta haifi 'yan biyun ta wato....Saifullahi da Zaidullahi".
Murmushi Ummah tayi tace min " abokan wasan Hudallahi".

Nima 'din murmushin nayi jin sunan da ta 'kira ni dashi.....kuma ya min da'di...dan bata cemin hakan ba sai yau.


"......Sai dai koda Alhaji Baba ya dawo nan bai taho da 'dan sa dake gurin 'kanin sa Ja'afar ba, dan Ja'afar hana musu shi yayi musamman saboda karatun sa shiyasa har yanzu baku san shi ba....."
kallo na Ummah tayi tace " ko ke dake zuwa gidan kin ta6a ganin sa?"

Da sauri na girgiza kaina gami da fa'din " ah ah".

Sai ta cigaba da fa'din ko hutu ma ba'a kawo shi idan sunzo tare suke komawa da iyayen nasa basa barin sa anan koda ana hutu sai suce akwai makarantar islamiya....Alhaji Baba ma bai damu ba dan yasan ilimi shine hasken rayuwar 'dan Adam, Ammi kuwa da take ganin 'yan biyun shikenan sai suka 'dauki hankalin ta bata damu sosai da shi babban ba, musamman ma da yake tana tausaya musu saboda rashin samun haihuwar su shiyasa take ganin dama a bar musu shi kawai su ri'ke shi.


Tun zuwan Alhaji Baba garin nan bashi da abokin da ya wuce Baban ku, shine ka'dai suke zama suyi hira wanda har hakan yasa da kansa ya bashi labarin duk abinda ke faruwa da rayuwar sa, Baban ku ya tausaya masa sosai.

Koda ya nemi shawarar abinda zai rin'ka yi yana juya ku'd'den sa sai Baban ku yace bari yayi tunani.


Ganin ba zai iya noma kamar yadda su suke yi ba ya sanya washegari da suka ha'du ya bashi shawarar yayi gidan gona tunda shi rani da damina ana cin moriyar sa in yaso sai yayi na dukkan 6angarorin biyu, wato lambu da kuma kiwo za'a fa'da'da gurin sosai ta yadda babu wanda zai cutar da wani acikin su.


Sosai Alhaji Baba ya ji da'di shawarar Baban ku, dan kuwa kafin sati uku su cika har an nemi filin gona mai girman gaske an siya har an katange shi sauran aikin cikin.


A hankali ake yin komai kafin 3month kuwa komai ya kammala an raba filin 6angare biyu.


Kaji kala suka zuba farko guda dubu biyu...sannan suka yi shuke-shuke aka dasa wasu kama daga kan albasa, carrots sweets potato, abubiwa da dama suka fara dasu, gefe guda kuma aka daddasa su ayaba da sauran su wa'danda zuwa yanzun sun girma sun zama bishiyoyi masu masifar ni'ima a wurin.


Ma'aikata kusan talatin aka zuba kowa da 6angaren sa.

Karon farko da Alhaji Baba ya fitar da kajin sa ba 'karamin riba ya samu ba wanda hakan ya sanya shi 'karo wasu masu yawan gaske kamar da wasa sai gashi yana samun alkhairi da dama.


Lokacin da kajin sa na 'kwai suka fara 'kwai abin ba'a cewa komai....'diba kawai suke yi safe da yamma babu 'ka'k'kautawa.


Dalilin hakan ne ya sanya shi yiwa mahaifin ku alkhairi na zunzurutun ku'di har dubu hamsin, wanda da 'kyar Baban ku ya amshi ku'din....dubu goma ka'dai ya 'dauka ciki ya dam'ka sauran hannun yayan ku Usman yace ya 'kara akan sana'ar sa.


Wani filin Alhaji Baba ya 'kara siya ya tada ginin na zamani kafin a shekara kuwa ya gini ya kammala gaba 'daya.....sai da ya gama zuba komai aciki na amfani kafin suka tattaro suka dawo ciki inda aka kulle wancan gidan shiyasa har yau kuke ganin sa a kulle babu kowa ciki.

A dai-dai lokacin ne kuma Alhaji Baba ya samu labarin rasuwar Manager inda a lokacin ma ya kai kusan wata shida da rasuwa, Ja'afar ne da yaje Kano ya samo labarin.


Alhaji Baba ya tausaya masa musamman da yaji cewa wai cikin sa aka soka da wu'ka har cikin gidan sa yasan babu mamaki aikin *Kido* ne wannan, addu'ar dacewa ya bisa dashi sannan ya ro'ki Allah ya tsare masa marayun 'ya'yan sa dama shi kansa da abin ya kasance sanadin sa ne.

Sai dai bai gayawa
Ammi ba dan baya son hankalin ta ya tashi, ganin yanzu ta kwantar da hankalin ta baya son sabuwar damuwa kuma...dan haka sai ya ri'ke abin cikin ransa bai 'kara sanar da kowa ba.


Gidan gonar Alhaji Babba sosai albarkar Allah ya sau'ka a kansa shiyasa a kullum take 'kara habbaka da yin suna a fa'din garin Bauchi.


Bai yi 'kasa a gwiba wurin siyan manyan motoci guda biyu ya bayar ana zirga-zirga da su jahohin kudanci shiyasa a kullum ka ganshi bazakace mazaunin 'karamin gari kamar nan bane.....gashi da karamci da son mutane ga kyautatawa jama'ah gaskiya halin Alhaji Baba sai godiyar Allah........."
Ummah na kaiwa nan sai ta dubeni tace " kinji ko Hudah, ai yanzu kam kin fahimci dalilin da ya sanya rayuwar Alhaji Baba da iyalan sa ta banbanta da ta mu ko?"


" ehh Ummah na fahimta yanzu".
Nace cikin sanyi.


Sai tace kunga ba dan wani ikon Allah ba ma da nasan babu abinda zai sa shi dawowa nan garin da zama amma rayuwa ta kan juyawa mutum ne a duk lokacin da taso shiyasa ake son bawa ya ri'ki imani da 'kaddara cikin kowani hali na rayuwa".

Nanne ce tace hakane Ummah Allah yasa mu dace".

Dukkan mu muka amsa da " Amin".

Baban mu dake tsaye tun da jimawa wada bamu san ma da tsayuwar shi wurin ba murmushi yayi shima gami da jijjiga kansa sannan ya 'karaso ciki da sigar wasa yace da Ummah " kinyi mantuwa".

Kallon shi mukayi gaba 'daya da mamaki yayin da Ummah cikin sauri tace
" Me na manta kuma?"

Sai Baban mu yace " Riba ta mana.....kin manta nike kula da 6angaren Kajin ne?"


Dariya mukayi dukkan mu har Ummah sannan muka mi'ke muka bar wurin.





*****
Ban san me yasa ba amma tun ranar da naji tarihin Alhaji Baba sai na 'kara jin mutumin ya shiga raina sosai, duk da 'karamcin shekaru na amma hakan bai hanani fahimtar labarin nasu ba.


Bazan ta6a mantawa ba ranar wata Alhamis da na je gidan da safe, Ummah ce ta aikeni in kaiwa Alhaji Baba sa'kon gidan sa kamar yadda na saba kullum.....





Comment
Vote
Share







*Salmerh ce*😍
[12/27/2019, 8:16 AM] 🌸Salmerh🌸: πŸ’• *NOORUL* πŸ’•
(Haske nah)



By
*Salmerh MD*



*Wattpad @*
*Serlmerh-md*



πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
πŸ’«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*


This page is specaially dedicated toπŸ‘‰πŸ» *Ummien Diga* naki ne ke ka'dai kiyi yadda kike so da shi...πŸ‘ŒπŸ»



*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*



πŸ…Ώ *20*


Koda naje banji muryar Alhaji Baba ba....haka ma sai naga Ammi duk ta zama wata iri kana ganin ta zaka san tana tare da damuwa, ni kaina sai da naji babu da'di a raina cuz ba haka na saba ganin ahalin gidan ba.


Tun da Ammi ta kar6i abin hannu na ta ajiye akan dinning gami da fa'din " Zaid in kun gama ga breakfast anan".
" toh" yace da ita shikenan ta koma ciki ban 'kara ganin ta ba.


Hatta su Saif ma da kansu suka yi serving breakfast 'din su suka ci...har suka kammala ina gidan kuma Ammi bata fito ba.


Tashi nayi da niyyar tafiya ganin kowa ba kulani yake yi ba yau 'din.


Har zan tafi sai kuma na dawo 6angaren da Zaid yake zaune, nesa ka'dan dashi na tsaya nace masa " wai ina Alhaji Baba yake yau?"

" me ya faru?"
Yace dani cuz dama ba wani shiri sosai mukeyi da shi kamar da Saif ba.


Jin ya sake tambaya ta madadin amsata sai na 'dan ja 'karamin tsaki ciki-ciki, sai na koma gefen Saif a hankali nace " Saif yau me ya samu Ammi?"

Kallona yayi kawai batare da ya bani amsa ba sai kuma ya 'dauke kansa yaci gaba da abinda yake yi.
" Zakiyi late fa better kije kiyi shirin makaranta yafi miki dan bazan hana kowa dukan ki ba yau kam".

Jin hakan ne ya sanya ni ta6e baki gami da mi'kewa na fara tafiya a hankali sai kuma na waigo nace dashi " to ina Alhaji Baba yake ni yau duk ban ganshi ba? Kuma ban gaishe shi ba ma".

Saif ne ya bani amsa da fa'din " sassafe ya wuce Azare Yayan mu bai da lafiya".

" yayan ku?"
Na sake tambayar sa da mamaki dan ni har ga Allah mantawa nake da batun wani wai shi Mu'een a gidan.

Da " erh ai baki san shi ba".
Saif ya sake bani amsa gami da mi'kewa tsaye ya rataya jakar makarantar sa.


Ganin hakan ne ya sanya ni fita nima da 'dan hanzari na na koma gida dan shirin zuwa makaranta ta.



Kwanan Alhaji Baba uku a Azare sannan ya dawo gida bayan ya tabbatar jikin Mu'een 'din da sau'ki.


Wannan karan kam abakin Baban mu mukaji takaitaccen labarin cewa wai ai 'dan Alhaji Baban ciwon zuciya ke damun sa wanda afa'dar likitocin ma wai da abinsa ya girma cuz ciwon ya da'de a jikin sa amma wannan ne karo na farko da ciwon ya ta6a motsa masa dalilin 6ata masa rai da akayi a school abin sai ya bashi haushi sosai, ga kuma club 'din su da sukeyi ma suka sake 'dora wani a madadin sa da yake ya 'danyi zazza6i na kwana kusan tara sanadin targa'de da ya samu a'kafa wajen wasan Ball shine ya ha'da masa harda zazza6i.

Su kuma kamar jira suke dama ya kauce duk sai suka maye gurbin sa da wasu, ya juri wancen bai nuna 6acin ransa ba har suka zana jarabawa.....abinda yafi 'kona ranshi ma shine debate 'din da za'ayi na 'karshen zango wanda duk da yana fama da targa'da'd'den 'kafar amma hakan bai hana shi mai da hankali wajen karancewa da kyau ba tunda jimawa yake bibiyar abin....... abin mamaki ranar ma zazza6i na damunsa amma haka ya matsawa Uncle Ja'afar akan zai zo yaji labarin debate 'din saboda gobene yake saka ran za'a fita na jaha ne kuma, zuwan sa sai ya tarar har an maye gurbin sa da wani tuntuni duk da yake kuwa wancan 'din bawai ya kai sa 'ko'kari bane amma dai mahaifin sa babban mutum ne shiyasa yaron ya maida Mu'een tamkar abokin hamayyar sa a makarantar dan sam baya 'daga masa 'kafa a komai kuma bai isa yace ya kamo 'kafar Mu'een a karatu ba amma haka yake kishi da shi....sai gashi wannan karon yaron na 'daga masa doro dan ya maye gurbin sa wurin debate.....karo na farko kenan da Hayatuddeen yaci nasara a takarar da yake yi da Mu'een.


Koda Mu'een ya nemi ji daga bakin jagoran nasu sai yace dashi ai ya 'dauka ko shi 'din ya fasa ne ganin lokaci na tafiya kuma basu ji daga gareshi ba".
Inda yayi maganar batare da nuna damuwar komai ba.


Mu'een bashi da tsoro shi tun tasowar shi haka Allah yayi sa, dan haka batare da fargabar komai ba yace da malamin " haka mukayi da kai? Ko ni nace maka na fasa?"
Idanun sa har jajaye suka koma lokacin da yake maganar dan tsananin 6acin rai.

Take sai malamin ya juyo gami da dafa gefen kafadar sa yace " kayi ha'kuri zuwa wani lokacin kaji....me kake so kai kam ma yanzu, me kake nema Muhammad?, i thought duk inda ya kamata ace burinka ya cika akan fita debate to ka kai matsayin, in ban manta ba tun kana junior classes ake fita debate da kai toh ina laifi dan ka bawa wani chance wannan karon?
Mahaifin Hayatuddeen da kansa yazo ya ro'ki a sanya Hayat 'din for the first time kaga kuwa da girman sa bazamu bijirewa batun saboda kai ba ko?"

Cikin ido yake kallon malamin tankar wani sa'an sa wanda jin wai Hayat ne ma akasa a madadin sa ya ta6a ransa sosai, yasan kuma ba dan komai hakan ya faru ba sai dan cewa mahaifin Hayat 'din mai yaga Naira ne.....kenan 'karfin ikon Naira aka nuna masa.

Hafsat wannan abin ya 6ata ran Deen sosai fiye da zaton ki....

" Allah sarki"
Hafsat tace cikin sanyin murya yayin da Noor taci gaba da bata labarin da fa' din.....

" Hannun malamin ya sau'ke daga kan kafa'dar sa sannan ya juya batare da ya ce da shi komai ba kawai ya koma gida".

Haushi sosai abin ya bashi fiye da zaton mai karatu sannan bai sanar da kowa halin da yake ciki ba ko Uncle Ja'afar da ya tambaye shi ma cewa yayi dashi kawai wai ai an fasa ne gaba 'daya.

Sai dai ya 'kudura cikin ransa cewa bazai ta6a barin Hayat haka ba sai ya rama, sai ya

Please Login or Register in order to submit comment