Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

man of his word bashi magana biyu.

Sanin haka ya sanya shi fatan Allah dai yasa ba Husnah bace Alhajin yake shirin aura masa ya kuma sa ba irinta bace ma kwata-kwata, bashi da mafita a yanzu illah komawa ga mahalicci ya ro'ke sa..ko zai tausaya masa ya canza ra'ayin mahaifin nasa.

Da isar sa gida sai ya sa6i jakar sa a kafa'dar sa ya fito tare da kulle ko'ina na gidan yayi gaba abin sa zuwa bakin titi dan samun abin hawan da zai shigar da shi Azare...sai fatan Allah ya tsare hanya kuma.


*****
Kafin cikar sha biyu na rana ya dira Jihar jigawa inda direct ya wuce gidan sa da yake zama bai tsaya 6ata lokaci a ko'ina cikin garin ba, balle ma yanda yake jin sa cikin 'kunci ya sa yafi bu'katar jin sa kawai a muhallin sa shi ka'dai inda babu hayaniyar kowa.

Gidan ya 'danyi 'kura ka'dan ba laifi dan haka bayan ya 'dan huta kafin lokacin sallar Zuhr tayi har ya 'dan kimtsa nasa 'dakin ya watsa ruwa sannan ya wuce masjid...sauran aikin ya barwa isowar Husnah ne idan ta iso sai ta 'karasa duk dama ya riga ya yanke cikin ransa cewa zaman su da ita zai cigaba tare ne bayan ya tabbatar da cewa babu wani ala'kar da taji yake shirin faruwa tsakanin sa da ita da ya danganci maganar aure, amma hakan bazai sashi hana ta kimtsa masa gidan sa ba...koma dan kar ta barshi da uban aikin da bai san yadda zai yi da shi ba.

Koda ya dawo daga masallacin ma 'dakin sa ya kuma shigewa yayi kwanciyar sa dan hutawa, bai ko nemi abinda zai sa a cikin sa ba ya bari sai zuwa yamma idan ya fita...kafin bacci ya 'dauke sa ne sai yaji 'karan Vibration na wayar sa dake gefen kansa.

Tsaki ya saki tare da 'dago wayar yana duban fuskar wayar gami da karanto sunan wanda ke 'kiran sa.

Sai a lokacin ma ya tuna ashe bai 'kira mahaifan sa ya sanar da su isowar sa ba...shaf ya sha'afa ma gaba 'daya.

Tsayawa tunanin da yayi ne ya sanya 'kiran da akayi masa yankewa nan ya ci karo da missedcall 'din da akayi masa 'dazu da yake tunanin fitar sa masallaci ne akayi 'kiran, na Ammi 3missedcall sai na Husnah kuma biyu yayin da na Is'haq kamar yanda yayi saving yake 'daya...sai dai kafin yayi wani yun'kuri take wani 'kiran Ishaq 'din ya sake shigowa while wayar na ri'ke a hannun sa.


*****
Ishaq da Imam abokan juna ne irin na 'kut da 'kut 'din nan su yan asalin jihar Borno ne haifaffun 'karamar hukumar Beinishek.

Sun kasance course mate 'din Mu'een ne dake matu'kar son ganin sun 'kulla abota dashi, musamman saboda ajin sa da kuma sanin yanda brain 'din sa ke kawo light ba da wasa ba.

Hakan yasa suke matu'kar shishshige masa a mafi yawan lokuta sukan so suga sun sako shi cikin shirgin rayuwar su, babu laifi kuma ya 'dan sake musu fuska cuz dama a makaranta ba'a ta6a gudun mutane, dole ne ko kana gudun wasu a wani 6angaren zaka saba da wasu, hakan yasa Mu'een sabawa da su Ishaq a hankali suna 'dan gaisawa, babu laifi har wataran ma sukan 'dan zauna da shi su ta6a hira ka'dan musamman a irin lokutan da ya kasance suna jiran lecturer ya zo ne, ga shi kuma sai akayi sa'a group 'din su yazo 'daya.

Tun lokacin da zasu tafi hutun semester Ishaq ya kar6i phone numbern sa sai dai basu ta6a yin waya da shi ba, babu wanda ya ta6a 'kiran wani cikin su, Ishaq bai 'kira shi ba ko da sau 'daya ne kamar yanda shi da kansa ya san cewa Mu'een ba zai yi 'kiran sa wai dan kawai su gaisa ba, su kan ha'du dai a whatsapp su gaisa sama-sama kuma hakan ma ba kullum ba.

Yau shine rana ta farko da Ishaq ya gwada 'kiran layin Mu'een da bayan yankewar 'kira na farkon ya kuma sake dialling karo na biyu.

Tsaki Deen yayi tare da jan recieve button ya danna wayar a speaker tare da ijiye ta gefen kansa...yana wani cic-cin magani.

" Ya akayi Ishaq?"
Ya fa'di yana ha'de gira, ko daga sautin muryar sa ka'dai zaka iya fahimtar ba'a son ransa yake maganar ba balle idan ka dubi yanayin fuskar sa.

Ishaq kuwa bai damu da yayanyin da ya jishi ba kawai ya cigaba da fa'din" Normal fa Gaye, ka iso ne?"

" No ban taho ba...but may be tomorrow or day after...ban gama kintsawa ba tukunna".
Hankalin sa kwance ya shirga 'karyar hakan cikin ransa yake ayyana" ban son damuwa ni daga dawowa ta".
'Kasa-'kasa ya saki tsuka yana gyara kwanciyar sa.

Ishaq da bai san cewa 'karya bace Mu'een ya shirga masa sai ya saki murmushi tare da fa'din" Kana sha'anin ka Gaye, girman ka ne...mu kam mun diro muna cikin school ma yanzu haka..."
Fa'din Ishaq yana 'yar dariya.

Deen kuwa sai yace" Yayi kyau ya hanya kuma?"
" Alhamdulillah za'a ce gaskiya".
Sai yace
" Owk yayi kyau".
A takaice yana wani lumshe idanun gajiya gami da 'kosawa da yayi da amsa wayar.

Yana so ma ya tambayi Imam amma sai ya mance sunan sa kuma ma bai son hirar tayi tsayi tsakanin su shiyasa kawai ya basar, hakan yasa yayi shiru yayin da Ishaq ya yanke wayar da fa'din" Sai ka iso to".

Ishaq na kashe 'kiran ya 'dago wayar yana mita cikin ransa wai" Mutum sai nacin tsiya..wannan in maye ne shi ha'dama zai yi".

Ammi ya 'kira ya sanar da ita isowan sa, sai Uncle Ja'afar da Alhaji Baba, daga nan bai kuma 'kiran kowa ba kawai ya mi'ke yai bacci abin sa.

*****
Sai bayan sallar la'asar Husnah ta iso, da isowan ta kuwa bai fi hutun 20mins tayi ba kawai ta tashi ta fara aikin gidan zuciyar ta 'daya.

Wanda tun lokacin isowan ta daga" sannu da hanya" babu abinda ya ha'da ta da shi tun isowar tata har izuwa kammala kimtsa gidan bata ga wani annuri tattare da shi ba.

Husnah bata damu ba cuz ta san dama shi tamkar wahainiya yake, launin halayyar sa canzawa take a duk lokacin da ya ga dama....maganar sa kuwa juju ne da ita, idan yaso yin rowar muryar sa kuwa har sai kunyi mamakin yanda yake yin 'dif...in kuwa yan surutun sa na nan ko ita sara masa take yi ta zama 'yar sauraro...'dan ra'ayi ne Mueen ba na wasa ba kuwa.

Sanin halin sa da tayi ne ya sanya sam bata ko damu da sharetan da yake yi ba, mafi yawan lokuta ma sai dai ta saki murmushi kawai ita ka'dai, musamman idan ta tuna irin 'dokin da yake yiwa ha'duwar su da kuma da'da'dan kalaman da yai ta zuba mata cikin satin kafin tahowar su amma ganshi yanzu tamkar ba shi ba yazo yana wani ha'de mata gira...

Bata samu damar kammala gyaran gidan ba har sai kusan sallar Maghrib saboda ba laifi gidan nada 'dan girma sosai, amma sosai tayi 'ko'kari cuz cikin lokaci 'kan'kani gidan ya dawo fes da shi yana walwali tamkar ba shi ne yayi futu-futu 'dazun ba...harda burner ta kunna a palourn ta saka musu turare mai da'din 'kamshi saboda kawai ta sanyaya ransa, cuz ta san shi da son 'kamshi.

Shi kam tun da ya fita sallar Maghrib bai dawo ba har sai da akayi sallar Isha'i sannan ya dawo gidan da ledan take-away da ya musu a hannun sa.

Husnah hutun Sallah take yi dan haka a palour ya same ta kishingi'de tana amsa waya daga mahaifiyar ta.

Ledan ya ajiye tare da zama facing da inda take ya tsura mata idanu yana jiran ta kammala wayar ji yake tamkar yaje ya rungumeta ya bayyana mara irin kewar ta da yayi.

Amma deep down his heart yake tsana ta na taso masa ka'dan, maganar aure ka'dai da akace mahaifin sa na shirin yi masa ya sanya tsanar yin tsiri cikin zuciyar sa inaga kuma ance auren akayi gaba 'daya..kunga ai sai cin mutunci da hantara ne zai biyo baya ko.
_'Kalubalen mu 'yaya mata, darajar ki, itace kimar ki, mutuncin ki, gadarar ki, alfaharin ki, har ma da kwanciyar hankalin ki a ko ina, mu daure mu kula da kare mutuncin mu ko dan gudun abinda kan iya zuwa ya dawo, babban ma shine tsoron Allah...Ubangiji Allah ka 'kara tsare mana kawunan mu ka raba mu da sharrin masu sharri...AM33N._

Ai kuwa tana gama amsa wayar ta juyo gare shi tana murmushi tace" Ka dawo?"
Da" Umm" kawai ya amsa ta a takaice tare da 'dago ledan da ya shigo da shi ya ciri abinda yaga zai iya ci sannan ya tura mata sauran batare da ya furta mata komai ba.

Shima 'din yunwa yake ji sosai shiyasa bai ko saurari Husnah sun ci tare ba kamar yanda suka saba kawai ya fara aikawa cikin hanjin sa.

Murmushi Husnah tayi tana kallon sa tace" ba zaka jira ko plate na 'dauko maka ba yau 'din?"

" Barshi kawai".
Yace bayan ya taune chips 'din dake bakin sa.

Husnah murmushi tayi tare da mi'kewa ta je ta 'dakko plate ta zuba iya abinda zata iya ci ta koma gefe ta fara ci, shiru 'dakin ya 'dauka kowa na cin abincin sa jifa-jifa ta kan 'dan saci kallon sa yayin da shi kuwa baya ko kallon inda take tamkar ma ya manta da kasancewar ta cikin 'dakin illah Television da yake kallo lokaci zuwa lokaci a haka har suka 'kare cin abincin baki 'daya.

Husnah ce ta ta shi ta tattare komai harda wanda yayi amfani da shi duk ta fitar zuwa kitchen sannan ta dawo palourn, sai dai bata zauna ba kawai ta tunkari 'kofar da zai sada ta da 'dakin ta tana mai shafo kyawawan siraran kitson da ke kwance a fatar kanta.

Daf da zata shige taji muryar sa ya 'kira sunan ta" Husnah"! Cikin dakiya da mugun hali.

Waigowa tayi batare da ta yi niyyar tahowa ba cuz zuwa lokacin 'dan iskan banzan halin nasa ya fara isanta itama, ganin babu wani abinda ya ha'da su amma sai faman share ta yake yi, tun zuwan ta gidan zuwa yanzu in bata manta ba bai fi sau biyu kacal magana ta shiga tsakanin su ba.

Ganin ta tsaya batare da ta taho zuwa inda yake ba ya sanya shi ha'de gira yana sake fa'din" Magana nake so muyi please".

Baki ta ta6e sannan ta taho a hankali ta zauna kan kujerar da ke nesa ka'dan da shi.

Sai da ya saki numfashi kafin ya ha'de hannayen sa wuri guda yana duban ta yace" Husnah me kika ji yake shirin faruwa tsakani na da ke?"

Da mamaki tace da shi" Ni kuma me zanji Mu'een babu abinda naji ni"
Tayi maganar tana kallon fuskar sa.

Sai ya 'dage gira 'daya tare da zuba mata idanu a hankali ya furta" Mahaifina ya san ala'kar da ke tsakani na dake, akanki Husnah har mari mahaifina yai min da tun haihuwa ta har girma na hakan bai ta6a faruwa tsakani na da shi ba..kin san kenan ransa ya 6aci sosai kenan ko?"
Ya 'karashe yana duban ta sannan ya koma ya zauna da kyau still yana kallon ta da itama 'din shi take kallo...Cigaba yayi da fa'din" Ina jin tsoron hukuncin da zai yanke akan hakan ne shiyasa nake tamabayar ki".

Husnah sai tace" Babu komai, ni banji komai ba gaskiya".
Yace" Kin tabbatar ko Husnah?"
" Me yasa kake tunanin zan maka 'karya to".
"Hmm"
ya saki ajiyar zuciya afili yana jin 'dan natsuwa ka'dan na shigan sa.
Baya ya koma ya jinginu sosai da jikin kujerar yana lumshe idanu.

" To ni ka 'daure min kai sam ban fahimci inda maganar taka ta dosa ba, me kake nufi da wannan tambayar? Me yasa kake tunanin hukuncin da za'ayi maka zai shafe bacin ko sani na bai yi ba ni".

Idanun sa a lumshe yana shafa saman 'kirjin sa da left hand 'din sa ya bata amsa da fa'din
" Bazaki gane bane Husnah abar zancen kawai...fata na dai kawai shine Allah yasa abinda kika fa'da min ya zam iya gaskiyar kenan, kuma ya sanya iyakar abinda zai iya faruwa tsakani na dake ya kasance iya nan...."

Husnah kam ido kawai ta tsura masa cike da matu'kar mamakin kalaman nasa, sosai ya 'daure mata kai ya sa ta cikin tunanin manufar hakan da ya furta mata.

Yayin da cikin ransa yake ayyana cewa matu'kar Husnah tayi kuskuren da har ta bari aure ya kasance tsakanin sa da ita..." Hmm"
Kawai ya furta illah bayyana murmushin sa da yayi a fili still idanun sa a rufe.

Husnah kam zuciyar ta cike fal da tunani ta tashi ta shige 'dakin da ya kasance mallakin ta ne a gidan, sosai take so ta san me maganganun nasa ke nufi amma sanin da tayi cewa matu'kar ba ra'ayin kansa yayi ba to ko hauka zata yi bazata ta6a jin yanda take so daga bakin sa ba.

Ranar haka kowa ya kwana 6angaren sa babu wanda ya nemi 'dan uwan sa, Husnah kam 'kullin dake cikin maganar sa ne ya dame zuciyar ta..kwana tayi tana tunanin tambayar da yayi mata, to me yake tunanin zai faru tsakani na da shi wanda yake tsammanin zan ji shi a gidan mu?
Tambayar da take yawan yiwa kanta kenan abin ya dame ta sosai har hakan yasa ta 'kagara gari ya waye ta 'kira mahaifiyar ta taji, tsoron ta kar dai ahalin ta sun san da batun 'kazamar tarayyar da ke tsakanin ta da shine suke ganin ta da abin kawai...yayin da Yah Deen yayi baccin sa cikin kwanciyar hankali jin cewa babu wani labari daga 6angaren Husnah.

Gari na wayewa da yake ba sallah zata yi ba, tana watsowa jikin ta ruwa ko gama kimtsawa bata bari tayi ba kawai ta rarumo wayar ta, sosai ta 'kagara taji abinda ke faruwa cuz ba 'karamin duhu Mu'een ya shimfi'da cikin tunanin ta ba.

" Hello Mummy"!
Husnah ta fa'di jin an 'daga wayar da ta 'kira 'din.
" Haba Husnah...sau nawa wai zan miki kashedi akan wannan Hello 'din da kike yi a waya, sallamar ce da wahala ko kuwa menene?"
Mahaifiyar Husnah ce ta furta hakan tana mai jin 'daci har cikin ranta na rashin jin maganar ta da Husnah bata yi.

" Sorry Mummy na daina...Fatan an tashi lafiya?"
Husnah ta fa'di tana mai zama bakin gadon ta yayin da ta folding left hand 'din ta a 'kirjin ta tana mai cigaba da sauraran wayar tare da bada dukkan hankalin ta akai.

Mahaifiyar ta sai tace" Lafiya lau Alhamdulillah...ya makarantar?"

" Qalau Mummy gamu nan duk ma ba'a dawo sosai ba ba wani da'di school 'din".

Tayi maganar tana wani yatsina fuska kamar gaske.

Mummyn sai tace" Zasu dawo ai ba abin damuwa bane may be ma duk yau ku gansu".
" Hakane Mummy".
Husnah tace tana 'dan sosa tsakankanin kitson dake kanta.
Bu'dan baki tayi kamar zata fa'di abinda ke cikin ranta
"..umm Mummy"
Sai kuma tayi shiru.
Da kulawa Mummyn tace" Me ke faruwa ne Husnah sanar da ni mana".

Sai da ta sanya dauriya cikin maganar ta kafin ta iya furta" Mummy dama tambayar ki zanyi"
" Ina jinki, me yafaru?"
" Mummy akwai abinda ya faru ne bayan tahowa ta?"
" Wani abu kamar me kenan?"
" Wai nace ko kinji wani abin, amma shikenan kawai ya wuce".

A masifance Mummyn Husnah tace" Kamar ya shikenan ya wuce, ni 'din sa'ar ki ce ko kuwa 'kawar ki ce da zaki sa ni gaba da guntayen magana ko kuwa tsabar kin raina ni?"

Cikin shagwa6a tace
" Afuwan..ba haka bane fa Mummy, dama nayi tunanin ko kin sami labari ne amma shikenan ya wuce".

" Husnah...ban son iskanci fa..."
Saurin taran ta tayi da fa'din" Allah Mummy ba komai in akwai ai kin san zan sanar dake".

" Kin tabbatar?"
" Erh Mummy"
" To shikenan ayi karatu banda wasa ko".
" Uhmm".
Daga haka suka yi sallama kowa ya ajiye wayar.

Sai dai wannan wayar da Husnah ta 'kira 'din sosai ya 'daga hankalin mahaifiyar ta, tayi saurin nuna mata ta saki ranta ne dan tana so ta binciko dalilin da yasa Husnah yi mata wannan tambayar.

Yayin da 6angaren Husnah abin ya sake 'daure mata kai, ta tabbata kalaman da Mu'een yai mata jiyan nan da akwai dalilin yin su, sai dai kuma tana tunanin maganar daga 6angaren sa ta taso bai shafe ta ba....to ko dalilin kenan da yasa shi 'dauke min wuta tun isowa ta garib nan?"
Ta tambayi kanta, take kuma ta bawa kanta tabbacin erh hakan ne ma.

To in kuwa hakane ya zam dole ta nemo dalilin daga wajen sa, batare da 6ata lokaci ba ta ci alwashin hakan cikin zuciyar ta...dole ne tasan abinda yake 'ko'karin 6oye mata.

Sai dai ga mamakin ta tun a safiyar ranar Mu'een ya dawo mata a yanda ta saba ganin sa, wannan ba'kin halin duk ya kau, yazo mata ne a asalin masoyin ta Mu'inuddeen.

Husnah kam taji da'din hakan sosai har ma ya sanya ta manta duk damuwoyin da take ciki da al'kawarin da ta yiwa ranta....haka suka cigaba da rayuwar su cikin farin ciki kamar da can baya.

Lokacin da ta samu tsarki kuwa batare da 6ata wani dogon lokaci ba suka 'dora daga inda suka yi madakata, balle dama gashi duk sunyi missing junan su...ai hikenan.


*****
'Bangaren Alhaji Baba kuwa tun washe garin tafiyar Yah Deen ya tura wani amintaccen yaron sa Yusha'u can cikin garin Azare da sunan mahaifin Husnah da yake shima yayi zaman garin so bai wani sha wahalar gano inda Alhajin ya turasa ba, inda yaje domin yai masa kyakkyawan binciken da ya dace game da ita.

Cikin kwanaki biyu kacal ya kammala ya dawo, akan 'dan wannan tafiyar Alhaji Baba sadaukarwar 100k yayi saboda tafiyar, hatta da hotel 'din da Yusha'u yayi masau'ki da sauran abubuwa duk cikin ku'din yayi su, hakan ma lokacin dawowar sa ya dawo da canjin kusan 30k amma Alhaji Baba ya bar masa saboda jin da'din labarin da ya zo masa da shi.

Dama can mahaifan Husnah mutanen kirki ne na gaske basu da abokin gaba balle 'yan tsama, sai dai mahassada.

Duk iya binciken Yusha'u bai ci karo da komai da ya danganci 6atanci ga iyayen Husnah ba, ita ka'dai suka haifa daga ita Allah bai sake basu wata haihuwar ba, sannan mahaifin Husnah ri'ka'k'ken 'dan kasuwa ne da ya shahara ta 6angagori da dama, ya tara dukiya fiye da zaton mai karatu, sai dai Allah bai bar shi ya rayu cikin iyalan sa ba da mafi soyuwa cikin zuciyar sa wato Husnah.

Yawan takurawar da wani wansa ke yi masa ne kan ya bashi kaza yau kaza gobe kaza yafi damun sa, ya gina masa gida mai girman gaske kwatankwacin wanda yake ciki da iyalen sa, ya kai sa Hajji har sau uku wanda shi kansa mamallakin dukiyar ma zuwan sa Hajjin sau biyu ne, matar sa kuma sau 'daya amma dan kawai ya faranta ma Yayan nasa rai ya sanya shi biya masa har sau uku, ya kuma biyawa uwargidan sa ma taje sau 'daya, ya 'dau nawin karatun 'dansa Hisham har Cyprus yaje ya kammala kuma cikin saa yanzu haka yana aiki a Abuja...amma duk wannan abin bai sa wan mahaifin Husnah Alhaji Mamman ya bar 'kanin sa ya sake da dukiyar sa ba.

Ya kan zo da bu'kata ta ku'di a duk lokacin da ya ga dama kuma ku'di masu nawin gaske, haka mahaifin Husnah zai bashi check idan bashi da cash a hannun sa, bai ta6a nuna masa 6acin ransa game da hakan ba.

Amma duk ranar da ya kuskure yace ya bashi lokaci idan ya tambayi ku'di to kuwa ranar mahaifin Husnah ya taro march har da August ma kuwa, domin masifa zai sashi a gaba yanayi kamar 'dan cikin sa da ya haifa, duk wasu alkhairan da yai ta masa abaya mantawa da su yake yi ya dinga ya6a masa maganganu son ransa kan cewa yana yi masa wula'kanci dan yaga Allah ya hore masa dukiya.

Sosai irin wannan abin ke 6ata wa mahaifin Husnah rai amma sai yake dannewa kawai yake dauriyar bashi duk yawan ku'din da ya bu'kata.

Mummyn Husnah bata ta6a saka musu baki cikin maganar su ba illah idan taga yayi shiru yana tunani sai ta bashi ha'kuri da kalamai masu da'di da kwantar da hankali tana kuma sake nuna masa muhimmancin dangin sa agare shi.

Musamman ma da yake tasan cewa lafiya ba isan sa tayi ba.
Ciwon hawan jini yake da ga kuma Diabetes duk shi ka'dai.

Shekarun Husnah 15 lokacin tana Ss1 aka yi kidnapping 'din ta...imaging fa tashin farko 50million aka nema daga wurin iyayen ta, sosai hankalin mahaifin Husnah ya tashi...hakan yasa ya tattaro duk abinda ya san mallakin sa ne ya dun'kula ya samo million hamsin.

Tun faruwar abin sau 'daya tak wansa yazo yayi masa jaje, waya ma sai sai dai mahaifin Husnah ya 'kira shi idan ya matsu, lokacin da ya tattara ku'da'dan kwanan Husnah hu'du a hannun kidnappers 'din, amma idan kaga mahaifan ta sai ka tausayawa yanayin yanda suka koma saboda damuwa.

A bayan mota ya jefa jakar da ku'din ke ciki, yana tunanin hana shi sako hukuma da akayi cikin lamarin, haka yaja mota da kansa ya nufi gidan wansa da nufin sanar da shi cewa ku'din sun kammalu zai kai.

A gida ya same shi a can 6angaren sa dake da girman gidan da wasu iyalai kimanin mutane goma zasu iya rayuwa cikin farin ciki a ciki...kishingi'de yake idanun sa a lumshe, a haka mahaifin Husnah yaje ya tarar da shi, bayan sun gaisa sai yake sanar da shi cewa ku'din sun samu zai kai yanzu ya kar6o Husnah.

Fuskar sa babu alamun alhini yace" To shikenan sai ka dawo, gashi sun ce kai ka'dai suke bu'kata ba dan haka ba ai da na raka ka mun je tare"

" Bakomai Yayah..."

Bai kai ga rufe bakin sa ba Alhaji Mamman ya tare shi da fa'din" Amma ka tabbatar ba ka sa hukuma cikin lamarin ba kamar yanda suka bu'kata ko? dan banaso a salwantar min da rayuwar 'ya a banza ".

Mahaifin Husnah cikin sanyin jiki yace
" A a Yayah ban sa da su ba ni ka'dai zani"
" To to je ka Allah ya bada sa'a, idan ka kar6o ta ka kawo min ita nan gidan dan na lura ku jin da'din ku kawai kuka sa agaba baku damu da rayuwar ta ba, idan baku so ni ina son kaya na".
Ya 'karashe maganar a masifance.

Mahaifin Husnah fita kawai yayi yana fa'din" sai na dawo" Tare da ayyana wai har wani ne zai iya kwatanta irin son da yake yiwa Husnah ya kuma ce wai baya son ta bai damu da ita ba?...shi kansa sa yasan soyayyar da yake yi mata ya rinjayi wanda yake yiwa kansa ma.

Da wannan tunanin ya fice daga 6angaren ya nufi inda yayi parking motar sa..wan nasa ko irin ya biyo shi yaga ku'din ma bai yi ba.

Har ya bu'de mota zai shiga kuma sai yaji tsoro ya diran masa nan take, rufe motar yayi ya koma 6angaren Yayan nasa da nufin ro'kon sa akan ya taimaka suje tare ko zai 'dan ji 'kwarin gwiwa ajikin sa.

'Kofar babban parlour a bu'de take sai labile da ke sau'ke hakan yasa shi 'dagawa ya shige ya tunkari bakin sitting room da ya samu Yayan nasa aciki 'dazu.

_Sai dai me?_







Comment
Vote
Share




*Salmerh ce* 😍
💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*_Marubuciyar littafin CAPTAIN ABBAS_*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *45*

Irin kalaman da yaji Yayan nasa na furtawa ne suka matu'kar jijjiga shi, take ya 'dimauce idanun sa suka firfito waje, jijiyoyin kansa suka yi ru'du-ru'du....

Da hannu ya nuna inda Alhaji Mamman ke tsaye ya juya masa baya yana amsa waya bai ma san da cewa ya dawo 6angaren ba...dan haka sai ya cigaba da amsa wayar sa cikin kwanciyar hankali yana sake bada orders 'din yanda yake so abin ya kasance.

Bai san meke faruwa ba kawai sai jin fa'duwar abu yayi a 'kasa wanda ya sanya shi waigowa a rikice cikin hanzari da firgicin kar wani ne ya jisa har bai san lokacin da wayar ta fa'di a hannun sa ba ta tarwatse a 'kasa.

Ai kuwa ganin 'kanin sa Alhaji Hamza kwance a wurin ya matu'kar 'dimauta shi, ga dukkan alamu ma suma yayi, gumi ne ya fara karyo masa nan take saboda tashin hankali.

Kafin ya gama tantance abinda ya kamata yayi sai ga uwar gidan sa Hajiya Kareemah ta shigo 6angaren nasa da sallamar ta, ganin baya

Please Login or Register in order to submit comment