Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

TUN'KAHO*


_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*


🅿 *74*


Da kaina kuma na fahimci jin da'din da yayi da wannan canjin nawa ya kuma bani wani babban muhimman cin da har yau 'din nan nasan ina da shi a wurin sa.

Domin ko yanzu Yah Deen kusance ni sai yayi min sumbatu, ya yaba min, ya samin albarka, ya kuma nuna min cewa ni ta dabance, Hafsat yanzu har na saba, inajin kaina ne tamkar Zahra cikin taurari saboda irin riritawar da yake yimin, saboda shi nake duk wasu abubuwan da mata ke yi dan kula da jikin su dan jin da'din mazajen su, babu abinda bansa kaina na koya ba sabo shi da soyayyar sa, duk wani abu da zai kawo mana farin ciki indai bai sa6awa addini ba Hafsat a hankali na sawa raina shi na koya duk dan saboda Yah Deen.

Da kaina na ringa neman ilimi kan zamantakewa, ha'kuri juriya da biyayya hatta kwanciyar aure duk sai da na nemi 'karin ilimi akan su, duk wani styles na kwanciyar aure na koya dan kawai in faranta masa.

Na kan ji kaina kamar zai fashe idan Yah Deen ya yaba min bisa wani abin da na yimasa musamman a shimfi'dar mu, zuciya ta duka na bashi yake sarrafawa, na bashi rayuwa ta na bashi duk wani abu da ya shafe ni, yayin da shi kuma ya dinga cika ni da 'karyar yana so na yana 'kauna ta, ashe duk 'karya ne, Yah Deen ba zai ta6a so na ni ka'dai ba, ban san ya zanyi da shi ba, wallahi na 'kwammaci da auren sa yayi ya cika gidan sa da mata da zai fi min akan a ringa yiwa yara na kallon 'ya'yan Mazina ci mai neman mata.

     Allah be yoni mai tsananin san a kusance ni ba amma dole nasawa raina tun ban saba ba har nazo na saba kawai saboda shi da farin cikin sa...duk da hakan fa Yah Deen ya raina 'ko'kari na Hafsat ya zanyi masa...ya zanyi masa ya fahimci ciwon da yake 'ko'karin yi min cikin zuciya ta?

Sosai abin nan yake damuna a zuci wanda ni ka'dai na na ri'ke ban sanar da kowa ba ciki kuwa har Ammi na da kullum take cikin tuna min cewar matu'kar naga abinda bai game ni ba tare da shi in sanar da ita, amma bazan iya ba Hafsat ina matu'kar son shi, ina 'kaunar sa, sosai nake tausayin ranar da 6acin ran iyayen sa zai sau'ka kansa, shiyasa ma na kasa sanar da kowa hatta ke da kike matar abokin sa ban ta6a sanar miki ba kin sani, Ummah ta, Anty Zainab da Addah na Maryam duk babu wanda ya sani.

Duk yanda na so zama na da shi yayi kyau amma da zarar mun fara 'daukan hanya sai kiga ya sako wani al'amarin sa daban ya gusar mana farin cikin mu, domin harga Allah ni 'kwa'kwalta 'karama ce, ban iya ha'da abu biyu lokaci guda ba, bazan iya danne kishi na akan sa ba balle in rayu cikin walwala kamar yadda na saba while nasan zahiri ga halin da ya cusa kansa.

Nakan zurfafa tunani wani lokacin sai kuma inga ai kyautata zato ya kamata inyi masa ba munanawa ba, domin ban tabbatar da wacce irin ala'ka bace tsakanin sa da Jiddah...dole na kawar da kaina da sunan basarwa ko ince gudun zato haka na cigaba da rayuwa ta ni da yarinya ta...amma bazan miki 'karya ba Hafsat na dai danne ne kawai amma sanin asalin halin sa yasa na kasa cire batun cikin raina, haka muka koma rayuwar mu kamar baya bana iya wani sakin jiki da shi, duk yadda yaso yaji abinda ke damuna kuma ban iya sanar masa.



*****
    Tun bayan tafiyar sa sai muka raba hanya da su Baby domin nima na fara tafiya makaranta da kaina yanzu nake driving, yayin da Sani kuma yake sau'ke baby ita ka'dai yake yake kuma 'dakkota.

Tun a lokacin abubuwa suka fara ta6ar6arewa ta 6angaren Jamsine, domin ganin ya samu ishshen damar da zai ke6e da Jas ne shai'dan ya fara yi wa Sani muguwar sa'ka azuci, cikin lumana ya fara lalata min tarbiyar yarinya batare da na farga da hakan ba, sau da dama Baby na so ta gaya min wani abu amma sam bana bata hankali na domin asali ni ba gwanar zama in saurari surutan Baby ba ce, baya ga haka ma kuma nima 'din a kullum ina tafe ne da tawa damuwar.

Kwata-kwata sai Allah ya toshe min kwakwalwa ta ya kawar min da tunanin wani abu a raina...sam ban ta6a sa hankali na ga canjin da rayuwar Baby ya shiga ba, dan duk yanda naga ta canza sai in ga kamar damuwar rashin mahaifin ta ne kawai ba komai ba.

Daga baya ma sai bata ko gwada kawo min wata magana, sau tari kuma sai dai in ga ta dawo fuskar ta wata iri ba fara'a sam..cikin raina sai ince" Gado".
Nufi na ta gaji halin ubanta ne wurin rashin fara'a, ban sani ba ashe Jasmine cikin tsananin damuwa take, a hakan ma sosai Sani yake garga'din ta akan kar ta fa'dawa kowa, duk ranar da ya san yayi kissing 'din ta ko wani abu ya kan yi mata garga'di sosai akan kar ta sanar da kowa...hakan kuwa yake faruwa domin bata gaya min, amma duk da haka nasan da ace tana samun damar yin hira da ni da wani lokacin dole zan 'dan ji hint daga bakin ta, amma da kaina na toshe wannan damar.

Kuma Allah da ikon sa sai kiga duk ranar da ta yi su6ul da baka ma tayi niyyan sanar da ni sai kiga wani abin yazo ya shiga tsakanin maganar  dole maganar ta yanke ko kuma kiga ni 'din na kasa sauraran ta har batun ya wuce...kinsan idan Allah yaso jarabtan bawa gaba 'daya 'dauke hankalin sa yake yi akan abin shiyasa koda wasa ban ta6a tunanin wani abu makamancin hakan ba game da Baby.

Da kaina kuma sai na fara experiencing wani abu, bakin Baby jan sa ya 'karu gashi sai ya zama wani iri ba kamar baya ba da yake 'dan cukul amma yanzu ya fito sosai kullum sai kiga kamar a kumbure, duk da nasan bakin dama asali ja ne saboda hasken ta amma sosai ya 'karu a lokacin.

Ranar ma ina mata wanka ne nake tambayar ta ina shafa bakin nace" Wai meke damun ki ne baby abakin ki?"

Rau-rau naga tayi da idanu tamkar zata yi min kuka tana kallon cikin idanu na.
Sai nace" Yana ciwo ne yanzu?"
Kai ta girgiza min alamar a a still tana kallon cikin idanu na.
Sai nace" Shikenan to..na 'karasa da fa'din" Kallon fa? Bana hanaki yi min irin kallon nan ba Baby...yana sa rashin kunya ki daina kinji Ammi na?"
Kai ta 'dage min kawai alamar to.

Allah sarki baiwar Allah ashe zuciyar ta magana ce a 'kunshe amma tana tsoron fa'di saboda garga'din Sani da kuma tsoron hantarar da zan mata akai...wallahi yau ka'dai nayi dana sanin tsangwamar da nake yi mata yafi sau hamsin cikin zuciya ta...wanda na tabbatar da na yi ta ne a kurarran lokaci.

Ranar Baby bata iya tace da ni komai ba nima kuma ban sa komai aka ba har na kammala yi mata wankan...
Damuwar halin da ubanta ke neman shigar da mu ne duk ya dame ni.

Shima 'din da kansa yazo ya fara fahimtar rashin walwala daga Jasmine, dan idan ya dawo yanzu ba kamar da take walwala ba, amma sai yace ai dama yasan rashin kulawar da nake yi matan nan dole zai yi mata illah watarana, a fa'dar sa wai ai dan bana jan ta ajiki ne shiyasa take 'dan shiga damuwa kuma gashi shi baya nan, a lokacin har zama yayi yai min nasiha akan hakkin yaro da Allah ya 'dora akan iyaye...yace min kin hana kanki farin ciki kuma kin.kasa sanar dani abinda ke damun ki Nuree gashi kuma abin naki har ya shafi Baby, idan haka kika ce zaki cigaba da rayuwa Nuree dukkan mu hakan zai cutar mu ne".
Cikin raina nace" Ai kaine ka ja mana".
Kwantar da kansa yayi yai min nasiha wanda daga 'karshe ya 'kara da fa'din idan ban saki raina ba da Ammi zai ha'da ni ta min bulala.

Dariya ma ya bani dan haka sai nayi murmushi kawai.
Sosai na gamsu da baya nan sa amma ina damuwar dake cikin zuciyata ta ishe ni ta hana ni bada hankali na akan 'ya ta, ni kaina yanzu ba walwalar nake da ita ba balle in iya dawo da farin cikin Baby da take neman rasawa.

Bazan manta ba wani hutu da su Baby suka yi a lokacin na so in dawo da jigilar Baby hannu na saboda na fahimci Sani ba mutunci ne da shi ba musamman da naga yanda yake yawan takurawa yarinyar da ke taya ni aikace-aikace abin sosai yake bani haushi, ga kuma baya dawo min da Baby gida akan lokaci 'karshe ma wai sai ya fara bata kyautar ku'di, wa'dannan dalilan su suka 'kara cire min shi a raina har na sanar da Yah Deen bayan wata tafiya da yayi Jos jinyar mahaifin sa, amma Yah Deen ya 'ki ya goya min baya dole Sani ya cigaba da aikin sa badan raina ya so ba.

Haka muka cigaba da rayuwar mu kowa baida  walwalar kirki, har a lokacin Addu'ah ta be wuce Allah yasa 'karamar ala'ka ce tsakanin miji na da wannan Jiddahn ba, kuma na sani ko ba'a fa'da min ba nasan acan Abuja suka ha'du, kuma ai ina jin yanda ake labarin 'yam matan Abuja shiyasa tsoro da fargaba kullum 'kara hauhawa suke min cikin zuciya ta.

Kwatsam watarana ina zaune sai gashi an 'kira ni da wata new number kamar bazan 'dauka ba ma sai kuma na 'daga, sallamar kirki bata yi min ba kawai ta hau yi min tuhuma akan miji na, wai sai na gaya mata dalilin da ya sa Mu'een yake ikirarin ni ka'dai na ishesa rayuwa har mutuwar sa, tace wani irin ri'ko nayi masa har haka da ko bayan idanu na ma baya iya kushe ni".

Sosai naji haushin wannan rainin hankalin nata dan haka sai na nace da ita ta tambaye sa mana tunda saurayin ta ne ai zai gaya mata dalilin.

Daga haka na yanke 'kiran ban 'kara sauraren komai ba daga gare ta.

Allah ya sani naji babu da'di har raina dan har na fara tunanin bakin su 'day ne da shi, amma yanda ta bayyana min irin yanda nake da muhimmanci a wurin Yah Deen shi yafi komai yi min da'di har ma sai ya wanki takaicin 'kiran da ta yi min..kusan kowacce mace naso ta samu irin wannan matsayi wurin mijin ta, abu 'daya ne ni 'din na rasa shine cikakkiyar 'kaunar sa daya kasa bani ni ka'dai, sannan kafar da ya bari har wasu matan ke samun daman shiga tsakani na da shi shima yana bani haushi.

Duk da haka ban bar 'kiran da Jiddah ta yimin ya zauna cikin raina ba dan ko da wasa ma ban sanar da shi ba, da kansa ya dawo yake bani ha'kuri akan maganar tare da yimin bayanin ala'kar dake tsakanin su, ban gamsu ba da bayanan sa ba sam domin nasan indai ba tana da wani marsayi a wurin sa ba da bazata ta6a samun daman ta6a wayar sa ba balle har ta bincika ta 'dauki pin 'dina ta kuma samu guts 'din 'kira na ta tuhume ni akan sa ba,  dole akwai wani abu da nasan ba zai iya sanar da ni ba... amma dole na sawa raina yadda da miji na na watsar da waccen batun.

Cikin sa'a sai na ga duk ya dawo da hankalin sa wurin mu, ya kan 6ata lokaci sosai fiye da baya yana hira da ni, ya kan kuma dawo akai-akai ba kamar baya ba da yake 'daukan wata guda be zo ba, kuma ma sai na daina ganin 'kiran Jiddahn ko da yazo gida, sosai na saki raina na watsar da komai kawai na ri'ki karatu na kullum cikin raina da kuma salloli na nake addu'ar Allah ya kare min miji na ya shirya min shi ya dawo da hankalin sa gare ni.


Sai gashi kwatsam rana tsaka ban zata ba ban yi tsammani ba kawai naci karo da wani mummunan abu cikin waya ta, Hafsat mijina yana aikata zina da wata macen da ban ma santa ba kuma aka 'dauka aka tura min dan na gani.

Ya kike ganin zan 'dauki wannan lamarin Hafsat? Yah Deen da na 'dauki soyayyar duniya na 'dora masa na 'dauki duk wata kulawa ta na bashi amma da abinda ya saka min kenan ya munafurce ni ya 'dauki hankali na da kalaman sa 'karya ya kautar da tunani na akan halayyar sa ta hanyar nuna min zallar soyayya.

Lokaci guda na fahimci Yah Deen ba zai ta6a canzawa ba, banga alamun zai iya canza halayyar sa ba, hakan yasa na yanke shawarar tafiya in barshi tafiya ta har abada, na riga na gama ji cikin raina cewar bazan ta6a samun cikakken farin ciki tare da shi ba illah ba'kin ciki a koda wani lokaci, yaushe zan rayu a kullum  idanuwa na na cin karo da abinda hankali na ba zai iya 'dauka ba kuma akan mijina, wallahi koda ace bana jin 'kaunar sa cikin raina dole zanji zafi ballantana Hafsat ina matu'kar son shi, ni da kaina bazan iya misalta miki irin 'kaunar sa dake raina ba.

Na gama yanke shawaran rabuwa da shi,  tun a jiyan na so inyi tafiya ta domin lokaci yayi da zan fuskanci rayuwa ta in daina yaudarar kaina da sunan ina zaman soyayya da miji na, ko da rabuwa da shi zai illah tani na gwammaci hakan da acecin zauna hallayar sa ta yi sanadin kumburin zuciya ta,  amma sai aka samu akasi Baby bata dawo gida da wuri ba, hankali na gida-gida ya kasu, wanda ganin lokaci ya tafi sosai ne na nemi mayafi na na tafi har makarnatar neman ta amma babu labari, na yi tafiyar da tunda mahaifiya ta ta haife ban ta6a yin irin ta ba, nayi kuka kukan da ko lokacin mutuwar mahaifina ban yi irin ta ba Hafsat, da wanne zanji, na rasa farin ciki na tako wani fanni, bayan 'kuncin dake zuciya ta akan Yah Deen sai gashi wani babban al'amarin ya sake faruwa na rasa inda zanga Baby.

Tamkar wata mahaukaciya haka nake jin kaina a lokacin, ta ya zan iya rayuwa babu Yah Deen babu Baby, Jasmine itace sanyin idaniya ta, na gama shirya mana yanda zamu rayu bayan bashi amma ko'ina naje bana samun cikakken bayanin inda zanga 'ya ta.

Hankali na sosai ya tashi fiye da zaton ki Hafsat, ban ta6a sanin yanda ake jin zafin 'da a zuci ba sai jiya da na ga alamun rasa Baby zan yi,  domin kaf na bincika amma ba Sani ba labarin su shi da Jasmine...babu tunanin da bai zo raina ba dan gani nake tamkar Sani saida min yarinya yaje yayi.

Daga 'karshe da wannan mummunan labarin naci karo Baby kwance wai ba lafiya a gadon asbiti.

Hankali na ya 'dan kwanta da na ganta, saboda bata ji wani mummunan rauni ba kuma ganin nata koda cikin wani hali ne yafiye min ace ban ganta ba kwata-kwata.

Abin takaici abin ba'kin ciki wai sai Safwan ke sanar da mu abinda ya so waka na koma ince ya faru, Sani ya raping min yarinya...
Kuka sosai ta fashe da shi a wannan ga6ar yayin da tausayin ta duk ya mamayi zuciyar Hafsat.

Hafsat bata ce da ita komai ba, domin abin kuka ne ya same ta da ya kamata ace ta zubda hawayen ta, ko case 'din Jiddah ka'dai ma ya kamata abarta tayi kuka akai ballantana abinda aka yiwa 'yar ta kuma Allah da ikon sa abin duk sai yazo mata cikin rana guda, ha'ki'ka wannan ba 'karamin tada hankalin ta zai yi ba.

Da 'dauki tsawon mintina uku tana kukan kafin ta fara magana.
" Zuciya ta tafasa take yi Hafsat duk da nasan da kaina ina da laifi cikin lamarin cuz da na bawa Jas cikakakken lokaci da natsuwar da zan zauna inji damuwar ta nasan da baza'a kawo wannan lokacin ba za'ayiwa tufkar hanci, amma duk da hakan nasan nawa laifin ragagge when it comes to halin Yah Deen, zato na komai ya wuce abaya, duk da nasan yana tare da Jiddah ahalin yanzun amma ban sawa raina cewar mummunan ala'ka ke tsakanin su ba sau da dama koran wannan tunanin nake yi cikin raina, ashe yaudaran kaina kawai nake yi, yau gashi da kansu suka tabbatar min da abinda suke aikatawa wanda nake da ya'kinin shine ya so faruwa da Baby.

'Kwalla ne masu zafi suka sake gangaro mata...ta sa hannu ta share su da wuri sannan ta cigaba da fa'din" Da kaina nake jin cewar rayuwa ta tazo 'karshe dan bazan iya da halin sa ba Hafsat, yaushe zan cigaba da rayuwa while ina ganin Baby da wani mummunan tabon da na tabbatar sakayyar halin mahaifin ta ce? Bazan iya ba sam, bani da hakkin kowa, in akwai ma sai dai ta Baby ka'dai amma rayuwar Yah Deen cike take da tarin abubuwan Allah wadai wanda nasan a duk lokacin da na kalli Baby sai na tuno da su, duk 'yammatan sa sai da yayi lalata da su daga 'karshe kuma ya guje su...Na tabbata da Yah Deen bai lalata rayuwar 'ya'yan wasu ba da 'kila Allah zai ji 'kaina ba zai 'dora min wannan abin ba, wata 'kil da Allah zai bawa Baby kariya amma kinga da yake alhaki ne sai da aka lalata ta aka 'daura mata wannan mummunar 'kaddarar...taya kike tuanin bazan yanke ala'kar da ke tsakanin sa da Baby ba? ta ya kike tuanin zan bar Baby ta cigaba da kallon sa matsayin mahaifin ta?
Idan na yi hakan sam ban yiwa rayuwar Baby adalci ba...ta 'karashe da shashshe'ka mai cin zuciya.

Cikin kukan tace" Dana sani nake ji masu yawan gaske Hafsat, dana sanin yadda da auren sa da nayi tun farko, da nasanin rayuwa da shi, haihuwar da nayi da shi da kuma cigaba da barin sa yana kusanatata bayan nasan halin sa.
       Ji nake dama rayuwa ta bata kawo i yanzu ba nasan da duk hakan basu faru ba, 'kila da ko haihuwa da shi ma bazan yi ba, wallahi da nasan hakane da ranar da su Imrana suka zo da da kaina zan ro'ke shi ya barsu su aikata abinda ya kawo su koda kuwa hakan zai yi sanadin raina ne tunda dama burin sa kenan 'kila da yanzu labarin bai iso nan ba da duk hakan bai faru ba.

" Da ya zama 'kaddarar ki kuma fa Noor? Haba dan Allah, kar ki bari tashin hankali ya gusar miki da tunanin ki mana, ina ilimin ki ina ha'kurin ki? Haba Noor ya zaki rin'ka fa'din maganganu tamkar baki san ciwon kanki ba? kar ki manta fa abar halitta ce ke, kinfi 'karfin Allah ya jarabce ki ne ko me? Hala kin manta cewa Allah yana tsarawa bawa rayuwar sa ne tun kafin zuwan sa duniya.."

"Nasa ni Hafsat ban manta ba, amma har abada ni nasan wannan sakayya ce ba 'kaddara ba ce, Allah ne ka'dai yasan yawan rayukan da banzan halin Yah Deen ya cutar ya lalata kuma yayi dumping in su, wanda gashi kina gani 'karshe ya 'kare ne akan Jasmine, kuma wallahi har abada bazan ta6a yafe masa ba, kuma baby ma bazata yafe masa ba koda kuwa abu ka'dai da ya rage masa da zai sa asashi a aljanna kenan baza mu ta6a yafe masa cutar da zuciyoyin mu da yayi ba".

Hafsat goshi ta dafe cike da damuwa da 'kuncin zuciya, sam bata san me zata sake fa'diwa Noor ba da zai kwantar mata da hankali...cikin hakan taji Noor 'din na fa'din" Babu yadda Alhaji Baba bai yi da shi ba, haka ma Ammi hadda Uncle Ja'afar amma duk ya watsar, an nuna masa illolin aikata zina, an gaya masa sakamakon mai yin ta, an kwatanta masa zabar da Allah yake yiwa mai aikata ta amma duk abanza after all ma da kansa yasan komai tunda yayi karatu dai-dai gwargwado amma ya take, ni dai nasan ban ta6a yi masa magana akai ba saboda banga fuskar hakan ba, amma ai nasan Ammi sun yi masa fa'da da kansa kuma shima 'din ya sani, kuma yasan dalilin hakan ne ya hana auren mu 'daukan hanya har yau amma ya share, ko Sani ma na sha nuna masa cewa halin Sani bai min ba amma yayi banza da magana ta ya cigaba da nunanwa Sani 'kauna ya bashi muhimman ci ya 'daukaka darajar sa sama da mai gadin gidan sa da tun zuwan mu Bauchi muke tare da shi...'karshe suka cutar min da yarinya, suka lalata min rayuwar yarinya...insha Allahu duk sai sunga sakayya domin Allah bazai bar su ba, zama da Yah Deen kam daga yanzu ya 'kare, mun bar rayuwar sa kenan har abada..zanje in rayu da yarinya ta in kula da ita da tarbiyar ta, zanyi 'ko'kari wajen ganin na goge duk wasu munanan tabo da yayi mata...ko babu shi tana da Alhaji Baba, tana da Saif ga Zaidu sannan ga ni ga Ummah ta da 'yan uwana mu ka'dai mun ishe ta ba sai da shi ba...daga yau matsayin _babu_ yake a wurin Baby insha Allahu...sai na mantar da ita shi da duk wani abu da ya shafe shi.








Comment
Vote
Share







*Salmerh ce*😍

💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)


By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*


_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*


🅿 *75*

Ha'kika Mu'een ya aikata son ransa a duniya ya manta cewar Allah yana hukunta mutum ne dai-dai da abinda ya aikata a duk lokacin da yaso, ya manta cewar tun a duniya Allah yake sakayya musamman irin wannan zunubin, Mu'een yaci mutuncin 'kauna, ya ci mutuncin yarda da kuma amana, ya zarafin aure 'karshe ya 6ige da yaudarar mahaifan sa ya 6oye musu asalin waye shi.
Allah da kansa ya toni asirin sa wajen mahaifan sa amma duk da haka bai watsar da banzan halin sa ba...'karshe wa gari ya waya?..rayuwa sau'ki ne da ita sosai matu'kar ka tsarkake zuciyar ka ka sanya tsoron Allah a cikin ta, sa6anin hakan kuwa a kullum bazaka ta6a ganin dai-dai ba...Allah ka rufa mana asiri ka yafe mana zunuban mu badan halin mu ba".

Hafsat ce ke wannan tunanin cikin zuciyar ta tana mai jin zafin abin, ga kuma Noor da ke kuka a gefen ta wanda tasan ko ita ce haka ya faru da ita abinda yafi kuka ma zata yishi domin wannan abin kuka ne, abin ba'kin ciki ne sosai, bata da bakin da zata furta wata kalma da take ganin zai taushi zuciyar Noor ko kuma ya hana ta zubda hawaye, to koma ta daina hawayen ai bata isa ta kankare tabon abin cikin zuciyar ta ba, domin kuwa a zahiri an zalunce ta iya zalunci, an ci mata fuska an kuma 'kunsa mata ba'kin cikin da har 'karshen rayuwar ta bazata iya mantawa da shi ba, ina ma laifin ace aure yayi ya cika gidan sa da mataye ta tabbata da sai yafi ma Noor sau'ki fiye da ji da ganin irin wannan lamarin.

Sosai Yah Deen yaci amanar masu son shi, yayi wasa da tunanin su, yayi amfani da 'karfin soyayya duk ya yaudare su da ita ya lalata musu rayuwar su.

Farko rayuwar *Rahma* yaso ya 6atawa tun tana cikin 'kuruciyar ta, sai Allah ya taimake ta ya bata kariya ta hanyar sako yayan ta cikin lamarin 'karshe Allah ya ha'data da miji mai so da 'kaunar ta duk da yasan cewa ga abinda ya so faruwa amma ya kawar da kansa ya aure ta ya zauna da ita da amana...yanzu haka tana nan da yaran ta biyu mace da namiji.

'Kaddara ce ta sake ha'da shi da *Husnah* na biyu wacce ta so shi da dukkan zuciyar ta, ta nuna masa 'kauna, amma shi koda wasa bai ta6a jin soyayyar ta cikin zuciyar sa ba, amfani yayi da hakan yayi rayuwa da ita irin wacce yake so ya maida ita tamkar

Please Login or Register in order to submit comment