Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafe da batun aure, shi mahaifin 'ya mace wanda shi yakamata azo gareshi neman aure sai gashi abin ya juye masa, gashi ma a yanda yasan Taheer yasan waye shi yana da ya'kinin ko da ace Jiddah ce mace ka'dai da ta rage a duniya yasan Taheer ba ze ta6a yadda ya ha'da jini da shi ba...in dai har ya gano waye shi cuz yasan abu me mai wahala ya manta wancan lamarin.


Cikin zuciyar sa ya fara tunanin mafita, a ganin sa gara kawai ya tashi ya tafi tun kafin asirin sa ya 'karasa tonuwa in yaso sai yaje yasan me ze ce da Jiddah...
Tunanin sa ya yanke ne lokacin da ya tuno irin tashin hankalin da Jiddah ta shiga kafin tahowar sa, me kuma ze iya faruwa idan ya koma mata da batun da ba shi take tsammani ba....Innalillahi wa inna ilaihi raji'un...hakan ya furta a fili batare da ya farga ba...goshin sa ya dafe da yake jin kamar kansa na juyawa.

Amsa kuwwa sunan Taheer yake masa cikin 'kwa'kwalwa, yasan Taheer ya kuma san irin kafiyar sa, yasan taurin rai da yake da shi, ya kuma san muddin Taheer ya gama fahimtar waye shi ba zai bar shi ya tafi haka nan ba..me ya kamata inyi?
ya tambayi kansa.
Duk yadda yake ji da kansa da dukiyar sa yau gashi gaban Taheer komai ya kunce masa, ji yake kamar ba shi ne wannan me fa'da ajin ba.
Sosai kwarjinin Taheer ya cika masa idanu, tsoro da fargaba duk sun mamaye shi...sai dai duk wannan ba damuwa bane kamar idan yayi kuskuren da Taheer ya 'dago waye shi dole yasan abinyi kafin faruwar hakan,


Cikin zuciyar sa ya gama yanke shawarar da yake ganin itace mafita agare shi.

Duk wannan abin da ke faruwa Alhaji Baba bai ce da shi 'kala ba, tsawon lokaci yana zaune yana jira ne yaji abinda ke tafe dashi amma hakan ya kasa faruwa, fuskar Alhaji wasai banda bayyananniyar murmushi dake kwance a fuskar bakaka fahimci komai daga 6angaren sa ba....


Duban.sa yake yana 'karawa cike da mamakin sa, yanda yaga ya rikice in sosai yake bashi mamaki, har zuwa lokacin da yaga ya 'dan sawa zuciyar sa natsuwa..duban Alhaji Baba yayi cikin dakiya da nuna alamun kuskure yace" Alhaji afuwa dan Allah..wallahi ina jin kuskuren fahimta muka yi muka zo gare ka....sai yanzun na fahimci ba kai in nake nema ba...".
Yana gama fa'din hakan ya mi'ke tsaye gami da bawa Alhaji Baba hannu.


Mi'ka masa nasa hannun yayi yana murmushi me 'kayatar wa suka yi musabahar bankwana.


Abban Jiddah be jira komai ba kawai ya sa kai yayi gaba abinsa cikin sauri da fatan Allah yasa kar Taheer ya gane sa...shaf ya manta da cewar tun farkon ganin Alhaji Baba da yayi ya ambaci sunan sa, zaton sa ko duk cikin zuciyar sa ne yayi hakan.

Tsaye Alhaji Baba ya mi'ke yana duban bayan sa da mamakin sa, maganar sa 'karshe 'din sam bata gamshi Alhaji ba, sam sai yaji bai yadda da shi ba, 'kila wani shirin zai koma yi akansa tun da har ya gano inda yake rayuwa, mamakin sa Alhaji Baba ke yi domin ya fahimci Barrister tamkar mara hankali ya 'dauke shi, me yasa yake tunanin shi ba zai gane sa ba, in har shi da yayi abin ma bai manta kammanin sa ba me yasa kuma shi zai iya mantawa da nashi kamannin.


Taku biyar yayi ana shidan Alhaji Baba dake kallon bayan sa bai bari ya 'karasa ba ya furta" _Barrister Kido_ ...!"
Yana murmushi ya fa'di hakan da muryar da ya tabbatar zai ji sa.

Cak Abban Jiddah ya tsaya dai-dai da harbawan da zuciyar sa tayi, salati ya maimaita atake kusan sau uku da be masan yayi su ba.


Takowa Alhaji Baba yayi ya dawo gaban sa hannuwan sa duk na cikin babbar rigar jikin sa yayin da Abban Jiddah ya sake rikicewa jikin sa na rawa ya kauda idanun sa gefe abinka da marar gaskiya.
Alhaji Baba kam be damu ba bayan kallon 'yan da'ki'ku da yayi masa sai yace da shi yace da shi" Barrister kenan...bayan tsawon lokaci da rabuwar mu sai gashi kallon farko da kayi min ka fahimci waye ni me yasa kake zaton ni bazan iya gane kamannin ka ba..? U thought haka kawai zan iya mantawa da kai ne bayan duk abubuwan da suka faru abaya?"

Shiru Abban Jiddah yayi ya kasa furta komai, 'kafafun sa yake jin tamkar baza su iya 'daukan sa ba.
Alhaji Baba ne ya cigaba da fa'din" Ai in har zaka iya fahimtar ko ni waye tsawon wannan shekarun nima kasan bazan gaza fahimtar waye kai ba...amma yanzu duk ba wannan ba i know wani abin muhimmi ne ya kawo ka gare ni kuma bamu kai ga tattaunawa ba ka tashi...dan Allah ka manta da baya mu koma mu 'karashe maganar da ta kawo ka".
Zai yi magana Alhaji Baba yayi saurin dakatar da shi da fa'din" Please Barrister...".
Inda yayi maganar tare da nuna mai hanya fuskar sa ba yabo ba fallasa bazaka ta6a tunanin ganin Barrister ya ka'da shi ba.


Haka badan yaso ba Abban Jiddah ya juya suka koma suka sake zama, shiru ya 'dan biyo baya kowa tunanin da yake sa'kawa daban ne, sai da Alhaji Baba ya sake ce mai ina jin ka kafin ya bu'di baki, madadin ya fa'di abinda ke tafe da shi a a sai ya fara ro'kon Alhaji Baba gafara kamar zai yi kuka...sosai nadamar bazata ta kama shi, yanzu ne ya fahimci cin amana bata da rana sam.


Gashi tun ba'a je ko'ina ba Allah ya kama shi da dasawa 'yar sa 'kaunar yaron da yaci amanar mahaifan sa da da'dewa...bai 6oye komai ba duk ya sanar da Alhaji Baba hadda batun da ya kawo shi, nan ma ya 'karashe da ha'dawa da neman afuwar su.


Duk abubuwan da ya fa'di 'din babu ba'ko wurin Alhaji Baba, amma batun Jiddah sosai ya ka'da shi.


Cikin.zuciyar sa ya furta ' _karshen zamani_ sosai yayi mamakin wannan lamari, yasan a haife Barrister ya girme masa dan ko lokacin da ya sanshi ma ya san yafi shekaru talatin a lokacin kawai haihuwa ce Allah bai bashi da wuri ba amma sam bai ji da'din jin wannan labarin ba.



Zurfafa tunani yayi a lokacin, a zahiri shiru Abban Jiddah yaga yayi har sai ya fara tabbatar da tunanin sa na cewa Taheer ba zai amince da wannan batun ba.

Alhaji Baba kam can cikin rayuwar Deen ya tafi da tunanin sa, idan bai manta ba akwai sunan Jiddah cikin labarin sa da ya basu, kenan itama tana 'daya ne daga cikin irin 'yan matan da yayi abaya.


Murmushin gefen baki Alhaji yayi, sai kuma yaji tausayin iyayen nata ya kama shi, abin takaici ne ace ga abinda 'dan ka ko 'yar ka suke aikatawa musamman abu dangin Zina sa6on mahalicci shi ya san ciwon hakan ya kuma yasan Abban Jiddah ba zai so jin wannan batun ba, baya ga haka ma a idanun sa zaka fahimci zallar 'kaunar da yake yiwa 'yar sa, babu mamaki itace mafi soyuwa a zuciyar sa cikin 'ya'yan sa shiyasa ma har ya iya amince mata kan wannan batun da yazo masa da shi wanda ya tabbatar ba kowa ne zai iya irin hakan ba.

Muhammad 'dansa ne na cikin sa amma zai iya rantsuwa akan bai bar Jiddah haka nan ba, matu'kar ya ta6a neman ta to kuwa babu mamaki itama tabi sahun su Husnah ne...kuma abu ne me wahala ya amince da auren ta....

Bai kai ga 'karasa tunanin ba ya jiyo muryar Barrister na sake ro'kon sa, wannan karon kam mamakin sa 'karuwa yayi akan na baya musamman saboda ganin gwiwoyin Barrister da yayi zube a 'kasa, fuskar da muryar da muryar sa duk sunyi rauni da alamun ro'ko yake fa'din" Taheer dan Allah kar ka tuna abinda na aikata muku abaya..kaji 'kaina ka amince da wannan ha'din, wallahi Jiddah ba hali ne da ita ba halin mahaifiyar ta tayi..kuma basu san komai game da hakan ba a yanzu idan ka 'ki amincewa bansan yadda zanyi da ita ba, tsoro nake ji kar na rasa ta Taheer ita ka'dai Allah ya bani bani da kowa sai ita..idan dukiyar ku ne i promise u zan dawo maka da ita gaba 'daya ni dai ka amince kawai shine damuwa ta...".


Alhaji Baba bai yi mamakin jin hakan daga bakin Barrister ba, domin da kanshi ma ya zargi hakan bayaga haka me ze sashi biyewa batun yara har ya iya yada girman sa haka nan.



Ro'kon sa yayi akan ya tashi ya koma ya zauna amma Barrister ya'ki cuz shi a ganin sa ai bashi da sauran girma kuma tunda har ya kasance maciyin amana, ko da kwanciya ne zai iya yi a wannan lokacin matu'kar zasu yafe masa su kar6i batun Jiddah.


Da 'kyar Alhaji yasa shi ya koma ya zauna sannan ya tabbatar masa da cewa shi bashi da matsala ta 6angaren shi kar ya damu in har Muhammad ya amince bakomai.






comment
Vote
Share






*Salmerh ce* 😍
💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)



By
*Salmerh MD*


*Wattpad @*
*Serlmerh-md*



💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*



_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_


*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*



🅿 *88*


Alhaji Baba zuciyar sa 'daya ya 'dauke shi ya kai gidan sa wanda kafin hakan sai da ya 'kira Ammi ya sanar da ita cewa suna ba'ki dan ta shirya musu wani abin kafin isan su.


Sai da suka tsaya suka sallaci la'asar a masallaci kafin su isa cikin gidan da su Zaidu da suma suka je masallacin.


Cikin girmamawa kuwa suka gaida ba'kin Alhajin a tare suka isa gidan har parlour Alhaji ya shigar da shi da yake sauran 'yan tafiyan nasa daga wajen gidan suka tsaya suna daga harabara gida, sukan sosai suke jin da'din komai da ya shafi wannan bawan Allah, gashi da sanyin hali, komai nasa ma mai sanyi ne, gidan sa ma ni'ima sosai sassanyar iska ke ka'dawa ta ko'ina.



Parlourn babu kowa dan haka Alhaji Baba yayi mai iso sannan ya umarci Saif da ya 'kira Ammin su yayin da ya tura Zaid 'kiran Mu'een a 6angaren sa.


Koda yaje kuwa Sallah ya same shi yana yi cuz baccin da yayi ya makarar da shi zuwa masjid.
Zama yayi ya jira shi ya idar kafin ya bashi sa'kon Alhajin.


Mu'een kai ya jinjina masa da tunanin me ya kawo Alhaji gida kuma da wannan yammacin?..wanda sai bayan da ya gama addu'o'in sa kaf kafin ya tashi ya fito.


Already Saif ya cika gaban Barrister da duk abubuwan da yaga Ammi ta ha'da na tarar ba'kin so ko da Zaidu ya dawo ma ba wani sauran abu kawai sanar da Alhajin yayi cewa Yayan yana sallah ne amma yana fitowa.


Kai Alhaji ya jinjina sannan ya sallame su dan aganin sa abin bai wani shafe su ba.


Saif kam sam hankalin sa bai kwanta da ba'kon Alhajin ba, musamman ma daya ga yana wani sussunkuyar da kai 'kasa kamar marar gaskiya.


Ko da suka fitan Saif 'kin tafiya yayi ya tsaya daga jikin 'kofa dan ya saka cikin ransa cewar sai yaji abinda ke faruwa.


Ammi ce ta fara fitowa jikin ta lullu6e da mayafin ta, murmushi tayi ganin yaran nata sun hutar da ita sun gama mata komai da ya dace tayi.


Zuwa kawai tayi ta zauna gefen Alhaji Baba sannan ta gaida Barrister, sau 'daya tak ya iya duban ta har suka 'kare gaisuwan bai sake ba kallon fuskarta ta ba.


Ammi kam sam bata gane shi ba..dan haka sai ta dubi Alhaji Baba tana murmushi..ganin hakan ya sashi murmushin shima...gyara zaman sa yayi gami da fa'din" Sirkin ki ne fa..".
Idanu Ammi ta 'dan zaro zaton ta ko sirkin ta ta 6angaren Hudah ne, da yake tasan yanzu ba matar kowa bace tana da damar kula duk wanda taso.


" Alhaji kar dai Hudah ta..?"
Ta tambaya da mamaki.
Sai ya girgiza kansa sannan yace" Mu'een dai".
Tsuke fuska tayi nan take fuskar ta ta nuna alamun tambaya.

Alhaji Baba bai damu ba sai ya dubi Barrister sannan ya dubi Ammi sannan yace" Wai baki gane shi ba ne har yanzu?"
Kai ta girgiza masa duk kanta ya 'daure ma.

Deen ne tafe a hankali kamar yanda ya saba tafiyar sa, yana zuwa sai yaci karo da Saif nan tsaye da mamaki ya dube sa da alamun tambayar me kake anan kuma.
Saif kunya yaji dan haka sai ya sosa kansa yana murmushi yayi gaba.


Gyara zama Alhaji Baba yayi sannan ya furta" Daga Abuja yake tafe kan batun auren 'yar sa...
Dai-dai nan Mu'een yayi sallama ya shigo wanda ya dakatar da Alhaji Baba daga maganar da yake yi.

Wuri ya zo ya samu ya zauna daga 'kasa sannan ya gaida su Alhaji Baba da ba'kon na sa daya gani zaune.


Cigaba Alhaji Baba yayi da bayanin sa wanda ya fara da yi musu bayanin farkon abinda ya kawo Barrister wajen sa...Mu'een na jin batun ya 'daure fuska tamau dan shi har ga Allah baya son wata damuwa yanzu balle Jiddah da yake ganin itace farkon tubalin rushe masa farin cikin rayuwar sa.
Ammi kam ba'ki ta ta6e jin abin sam bai yi wani tsari ba.

Daga hakan Alhaji Baba ya gangara da yi musu bayanin waye asalin Barrister.


Atare Ammi da Mu'een suka mi'ke tsaye suna duban Barrister da idanun su kamar zasu cinye shi 'danye.

Ammi kam mamakin kanta ma tayi da har ta kasa gane shi tun farkon shigowar ta, sai da ma Alhaji yayi bayanin kafin ta gane shi sarai.


Idanun ta ne suka cika da 'kwalla hannu ta 'dago ta nuna shi da yatsa amma ta kasa fa'din komai, tsoron ta kar ya sake dawowa cikin rayuwar su da niyyan sake tarwatsa musu farin cikin su, hawaye ne ya fara gangaro mata tana share su....

" Aishatu ki yafe min dan Allah ha'ki'ka ban kyautawa rayuwar ku ba dana kasance mai son zuciya ta..."
Ciki kawai Ammi ta wuce batare da ta kai ga jin 'karshen maganar tasa ba, 'dakin ta ta shiga ta kullo 'kofan ta dinga kuka, bata son abinda zai sake 'daga mata hankalin iyalan ta sam, bata son dawo da abinda ya wuce, me yasa Barrister zai dawo cikin rayuwar su a wannan lokacin..me kuma ya rage musu da zai dawo dan sake mallakewa?


Hankalin Ammi sosai ya tashi da ganin Abban Jiddah, bazata ta6a manta rashin imanin da ya gwadawa rayuwar su abaya ba wanda dalilin sa suka guji zama cikin gari suka ha'kura da duk wani jin da'di, don su tseratar da rayuwar su yasa suka dawo nan da zama sai gashi da 'kafafun sa ya sake biyo su da wani batun kuma.


Ammi na shigewa Mu'een ma ya kama hanyar barin 'dakin shima a fusace batare da ya furta ko kalma ba, ji yake badan Alhaji Baba ne ya kawo shi gidan ba da babu abinda zai hana shi tara masa mutane...Alhaji Baba na ganin cewa shima barin su zai yi yasa shi saurin ambatan sunan sa.

Cak ya tsaya sannan ya waigo ransa a matu'kar 6ace fuskar sa babu alamun fara'a ko ka'dan..yace" Alhaji ni bazan auri 'yar sa ba..kawai ya koma inda ya fito".

Yayi maganar ne batare da ya ko kalli inda Abban Jiddah yake ba, a ganin sa bashi da ko arzi'kin da zai samu kallo mai kyau daga gare shi.


Yana shirin juyawa yajiyo muryar sa na fa'din" Haba Muhammad ka dubi girman Allah kayi ha'kuri, kai fa musulmi ne..."
" Kai kuma kafiri kake ai a lokacin da ka zalunci iyaye na ko..."
ya furta hakan ne a matu'kar fusace wanda yasa Barrister saurin 'kasa da kansa.. cigaba yayi da fa'din.
" Kai har kana da bakin magana ne? ka ro'ke ni, ni in auri 'yar ka? in ba ma rasar kunya ba har ka isa ka zo gaban mahaifi na ka ce wani kana so ka ha'da jini da shi bayan duk zaluncin dakayi masa?
bani da wayo fa a lokacin amma har yau 'din nan ban ta6a mantawa da kwanan cell da ka sa mahaifi na ba na tsawon kwanaki bacin babu abinda ya aikata..ciwon hakan nake ji sosai..haushin kaina nake ji da ban canza ma kamanni ba..."
Abban Jiddah kam duk yayi laushi da raunin murya ya fara fa'din" Kayi ha'kuri...."
" Bazan yi ba..."
Mu'een sam baya bari ya kai ga jin 'karshen furucin Abban Jiddah sai ya yanke maganar tasa.
A zafafe har jijiyoyin kan sa na nunawa yayin da idanuwan sa suka fito sosai suka yi ja.

"...bazan yi ha'kurin ba.."
Ya sake maimaitwa...har ya juya sai Alhaji Baba ya sake 'kiran sunan sa.

Wannan karon bai waigo ba cike da dakiya yace da Alhajin" Ni bazan auri 'yar sa ba har abada Alhaji, idan Jiddah ta kasance mace 'daya da ta rage ne a duniya ni bazan ta6a auren ta ba...".
" Kana so ka nuna cewa ni ban isa da kai ba ne ko?"
Da jin hakan sai yavjuyo yacdawo gaban Alhaji Baba ya dur'kusa kansa 'kasa yace" Kayi min afuwa Alhaji amma harga Allah bazan iya auran 'yar sa ba...Alhaji kai mahaifi na ne kuma ka isa da ni kana da damar da zaka za6a min kowace irin mace kuma ni me biyayya ne agare ka zan aure ta in zauna da ita amma dan Allah Alhaji kar ka tilastawa kanka ha'da jini da wannan tsohon azzalumin domin har abada bazan ta6a iya yafe masa cutarwar da yayi wa rayuwar ku ba...".

Shiru Alhaji yayi ya lumshe idanu yana sauraran sa.
Da gama fa'din hakan sai ya tashi bai sake bi takan Alhaji ba kawai ya wuce gaban Abban Jiddah ya tsaya ido cikin ido yake duban sa kafin yace" Fatan ka fahimce ni?...ni bana ha'da jini da maciya amana masu zalunci irin ka...kasan halin da muka shiga ta dalilin ka ne abaya? ko kuwa kasan 'kuncin da ka jefa mahaifa na aciki saboda son zuciyar ka? dalilin ka muke rayuwa a wannan garin ba dan muna so ba duk kasan hakan ne? sanadin ka mahaifa ne ke rayuwa a 6oye kamar basu da 'yancin kai basu shiga mutane, ka haramta mana rayuwa a inda muke so ka rufe mana duk wani hanyar jin da'din mu, lokacin da ka zalunci iyayena kayi tunanin yadda rayuwa zata kasance musu ne baka yi ba...kayi tunanin halin rashi da zasu fa'da ne? d answer is no..duk baka yi wannan tunanin ba saboda son dukiya ya riga ya rufe maka idanu ka manta da farin cikin wasu sai naka..mutum ya gina gidan sa baka san ta yadda aka yi ya samu hakan ba amma kasa an 'kone shi, baka yi tunanin abubuwan sa muhimmi dake gidan da zai iya rasawa ba duk ka sa an 'kone su gaba 'daya, zaton ka ma ko duk muna gidan, sai Allah ya nuna maka gazawar ka ya tseratar da mu,...duk a lokacin baka yi tunanin rashin imanin da ka aikata ba, baka yi tunanin farin cikin wasu da ka da'kile ba sai yanzun da kake farautan naka farin cikin shine zaka kwaso 'kafafun ka ka zo mana gida? hadda kwantar da kai na munafurci ko?"


Baya ya 'dan ja ka'dan ya bar gaban Barrister sannan ya cigaba da fa'din"...as u can see Allah na son mu ya kuma rufa mana asiri ya sake bamu wani farin cikin kwatankwacin wanda ka zalunce mu akansa, bamu rasa komai na rayuwa ba duk da nasan ba haka ka so ba...dukiya kuma kaje da ita ai wanda ya tara ta ma tafiya yayi ya barta bansani ba ko kai 'din har kabarin ka za'a kaika da shi..wannan duk matsalar ka ce ba damuwa ta ba ce amma malam ka sani wancan farin cikin daban yake da wanda kake barar sa a yanzu nd in har ni 'dan halak ne bazaka ta6a samun sa daga gare ni ba idan arzi'kin ka zai iya siya maka kuma bismillah... in kuwa zuwa kasake yi musamman dan ka zalunce mu ne bismillah mu zuba ni da kai.. amma for now mintina biyar bana bu'katan ka sake yi cikin gidan nan ko gurbin 'kafafun ka bana so in sake in sake gani ka fice ka bar mana gida kafin inci maka maka mutunci, in kuma baka yadda ba try me..".
Yana gama fa'din hakan ya juya ya kama hanyar 6angaren sa.

Barrister bin bayan yayi da kallo har ya 6acewa ganin sa, ha'ki'ka duk abinda yaron ya fa'di kan hanya suke, lokacin da yayi nasan zaluncin bai yi tunanin halin da su zasu shiga ba, yayi ne dan farin cikin kansa da kansa sai gashi kuma yanzu a gaban su yana neman taimakon su da kansa yasan bai kyauta ba cuz har attempting na kashe su yayi Allah ne tseratar da su amma duk da haka sanadin sun ya sa an kashe mutane kusan guda uku kafin ya samu natsuwa dan yana ganin kamar asirin sa ya gama rufuwa ne a lokacin.


A yanzu kam bashi da wata kalma da zai iya sake ce da su, ha'kurin ma yana ganin sam bai cancanci ro'ka daga wajen su ba..amma ya zanyi da Jiddah? ya tambayi kansa.
Ya sani a yanzu Jiddah bata da wani farin cikin da ya wuci ta ga ta mallaki Mu'een, burin ta ka'dai kenan a yanzu nd yayi al'kawarin sama mata farin ciki ta kowani irin hali saboda soyayyar da yake yi mata ashe yaudaran kansa yake...
Sum sum ya 'daga 'kafafun sa ya kama hanyar barin 'dakin...Alhaji Baba ne ya sha gaban sa zai yi magana Barrister ya dakatar da shi tare da girgiza kansa..." yaron ka gaskiya ya fa'da Taheer kuma na gamsu da shi...ban cancanci a yafe min haka cikin sau'ki ba ni kaina na sani, Jiddah ma zan bata ha'kuri ta ha'kura da shi amma nayi al'kawarin next week zan dawo, kuma Insha Allahu zanzo muku da dukkan dukiyar ku ba wai dan inaso Muhammad ya auri Jiddah ba a a, karamcin da kayi min ma na gode sosoi Taheer..ha'ki'ka kai 'dan halak ne...abaya nabi son zuciya ta na yaudari kaina da kwa'dayin dukiyar da take mallakin ku ne....na ji babu da'di Taheer har a zuciya ta naji haushin kaina domin gashi a zahiri son zuciya ta na barazanar hana 'yata farin cikin rayuwar ta...".
Kasa 'karasa maganar tasa yayi illah kafa'dar Alhaji Baba da ya dafa sannan yayi gaba yana share hawayen da suka gangaro mai...


Fita yayi direct ya nufi wajen motar su ya shiga tare da basu umarnin tafiya.


Alhaji Baba kam shiru yayi jim a tsaye duk komai ya kwance masa...yana jin dirin tashin motar su wanda har ya daina jin dirin motar amma bai motsa daga inda yake tsaye ba.


Ajiyan numfashi ya sau'ke bayan tsawon wani lokaci sannan ya nufi 'dakin Ammi da 'kyar ya shawo kanta tayi shiru ta daina kukan da take yi, wanda tana kukan ne hadda tunawa da tayi da mahaifin ta da 'kannan ta.

Nasiha sosai Alhaji yayi mata sannan ya baro inda take bai sake bi takan Mu'een ba dan yasan shi baya sa'k'kowa da wuri idan yayi fushi....


'Bangaren sa ya koma ya lulu6o layin Uncle J yayi masa bayanin komai, shi kansa da yaji abinda ke faruwa hankalin sa tashi yayi sosai abinda shima ya furta shine" Mu'een ba zai auri 'yar sa ba har abada, yaje ya nema mata wani mijin..."
Jin da yayi cewa yace next week zai dawo yasa Uncle Jafar ma 'daura aniyar zuwa kafin satin dan ayi komai akan idanun sa.





*****
Barrister da komawan sa gida batare da 6ata lokaci ba ya tara iyalan sa ya sanar da su komai dake faruwa, hatta mahaifiyar Jiddah bata san wannan labarin ba sai yau, gata mace mai hankali da natsuwa sosai take gujewa duk abinda wani abinda zai ja ta izuwa sa6on Allah, kuka ma ta sanya ita kam tana jimamin tsawon lokacin da ta 'dauka tana 'durawa cikin ta haramun, ta sha haramun ta sitirta jikin ta da haramun.
Wannan abin shi yafi komai tsayawa a ranta, hankalin ta ya tashi sosai ta ja masa Allah ya isa fin cikin kwando.

Bata sake yadda ta 'kara shan koda ruwan gidan bane ta tattara kayan ta bar gidan sa tana kuka.


Jidda ma binta tayi tana kukan itama dan

Please Login or Register in order to submit comment