Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

waya daga baya kinji..?"

" Uhum" nace da ita sannan na ajiye wayar raina ba'ki'kirin, ni ba haka naso ba sam.

Ko da na sanar da Addah ta ma da mamaki ta tambaye ni cewa da kansa kuma yace ki koma?"
Nace mata" Erh shi ne ya 'kira ni jiya ya fa'da min".
Ina maganar kamar zan fasa ihu saboda haushi.
Sai naji tace
" To ai shikenan tafiya ta kama ki".
" Ni wallahi Addah banso.in tafi yanzu".
Na yi maganar kamar zan saki kuka sai tace" Dolen ki ai, kinsan ni ba goya miki baya zanyi ki aikata son ranki ba".
Da fa'din.hakan.sai ta fice ta barni cikin 'dakin.

Haka ina ji ina gani Addah ta shirya min kaya na na taho ba dan raina ya so ba.

Ai kuwa gidan Ummah ta na sau'ka waya kawai nayi da Ammi na sanar da ita dawowa ta, ko Anty Zainab ban 'kira ba dan haushin yau bata goyi baya na ba.
Shi 'din kuwa 'kin 'kiran sa nayi duk da kuwa yace da ni idan na dawo in 'kirasa amma na share shi har sai can bayan sallahr Isha'i kafin na 'kira sa lokacin ma har na gama shirin bacci zan kwanta.

Da ganin ya 'dauka na gaida shi tare da fa'din" Na dawo".
A ta'kaice.

" Dan baki da sence kuma sai kika jira har dare sannan zaki taho?"
Take sai nace
" a a fa ni tun 'dazu na dawo".
Yace
" Kuma shine yanzu zaki gaya min?"
Nace
" Mantawa nayi ne..."
Tsaki yaja sannan ya kashe wayar sa.

  Ni kam baki na ta6e a fili na furta" _Almasifatu_ "
A hakan ne Addah take tunanin watarana zaka canza? Hmm so take in mutu kawai a hannun sa wannan me kai biyun kam ba canzawa zai yi ba...cikin zuciya ta nayi wannan tunanin a fili kuwa baki kawai na ta6e.

Washe gari kuwa na shirya naje na gaida Ammi na da Alhaji Baba.

Yini nayi da Ammi sannan da yamma na koma gida.

Sai da na kwana biyu da dawowa kafin na fara zuwa makarantar har ranar kuwa ban kuma waya da shi ba...ai kuwa karatu ya barni sosai a makaranta balle gashi SS class muke yanzu abin ba sau'ki dole na na dukufa da karatu dan kar abar ni abaya...gefe guda kuma Ammi na yawan cewa da ni na 'ki ta yanzu, wanda ni kaina bansan me yasa yanzu na fi jin da'din zama a gidan mu ba..gidan Ammin ne yazama shiru yanzu ba da'di ba su Saif gidan shiru ita ka'dai take yini abin kuma ya fara isanta.

Da kaina na fara jin tausayin ta kuma sai na yi tunanin dawowa gidan kawai, banyi maganar da kowa ba na dai bar shi cikin raina, kafin in sanar da Ummah ta kuma sai Ammi ta riga ni, ai kuwa Ummah ta tace maza in shirya in koma gidan miji na, dama ai rasuwa ce kuma ta jima da shu'dewa, tace zaman mace 'dakin mijin ta shine darajar ta.

Ni dai bance da Ummah ta komai ba, tunani nake cikin rina, cewar indai wancan 'dakin da yaci sunan nawan ne ma take tunanin zan koma ni kam har abada na yafe shi, bana jin zan iya sake rayuwa cikin wannan gidan da ya kasance wurin aikata masha' a tun kafin zuwa na..ina.babkashevkaina nake son yi ba bazan koma can ba cuz ni ka'dai nasan me nake ji cikin zuciya ta game da gidan, to tuno shi nayi ballnatana ace in sake rayuwa cikin sa, abu ne da har yau banga alamun zan iya mantawa da shi ba.

Duk da yake ita ma Ummahn nasan ba can 'din take nufi ba amma cewa da tayi gidan mijina ya sa ni zurfafa tunani akai tunda nasan can 'din shine gidan mijin nawa, kuma nasan Ummah ta baza ta6a cewa dani in koma wancan gidan ni  ka'dai ba dan haka ko da na shirya kaya na sai na koma gidan Ammi muka cigaba da zaman mu.

Ko guda daga cikin kulan da take min kuwa bata daina ba, sai abinda ma ya 'karu...Alhaji Baba ma kan yawaita yi min kyauta ta musamman ni da kaina nasan iyayen Yah Deen na 'kauna ta sosai.

Kwanaki na goma sha uku da dawowa gidan Ammi sai ga Yah Deen ma ya dawo wai ya kammala karatun sa gaba 'daya.

Ni dai bazan ce ga yanayin da na shiga da dawowar tasa ba amma har zuciya ta na taya shi farin cikin kammala makarantar da yayi.

Tun dawowar sa kuwa maganar kirki bata ha'da ni da shi ba, saboda bai ma wani zauna ba, ya kan yawaita yin 'kananun tafiye-tafiye amma duk da hakan ranar da akace yana gari kuwa ranar bana yin yinin farin ciki, na kan tsinci kaina cikin rashin sukuni musamman saboda wani salon tsareni da ya fara wanda ban san dalilin sa ba, Allah ma ya taimaka ni 'din ma ba gwanar shiga sabgar da bata shafe ni ba ce shiyasa ba kasafai lamari ke ha'da mu ba.

A yanda na fahimta ma sai naga tamkar ni ka'dai yake wa hakan, tamkar mai jin haushi na, duk dama ko a wurin Ammi yake ba kasafai zaki ga suna hira kamar da ba amma da sau'ki akan innice tare da shi sai na rasa dalilin wannan canjin.

Gani na abin farin ciki ne ya same shi daya kamata ace yafi kowa nuna farin ciki amma 6angaren sa kam abin ba haka bane.

Sai nake tunanin ta6 ashe kuwa zamu da'de mafarkin Addah bai tabbata ba in dai Yah Deen ne, mutun da kullum halayen sa canzawa suke yi gaba 'daya sai ka kasa gane inda ya dosa.

Ban sani ba ashe hakan na faruwa ne sanadiyyan tsintan kansa da yayi dumu-dumu cikin so da 'kauna ta, sai yake ganin in ba haka yake min ba tamkar abin zai girmama ne a zuciyar sa shi kuma baya so kowa ya fahimce shi domin ayanda yake ji 'din idan yace zai bayyana soyayyar da yake min kowa dariya zai masa musamman su Anty Zainab hatta Ammi yasan sai ta masa dariya bayan duk iyayin da yai ta musu akaina.

Kafin cikar 3weeks da dadowar sa kuwa wai sai  ji muka yi har zai fara aiki da wani abokin Uncle Ja'afar cikin garin Bauchi.






Comment
Vote
Share






*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)


By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*


_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *67*


Sosai nayi farin ciki da samun wannan aikin nasa dan ko ba komai zan huta da ganin sa, nima in sake kamar kowa ma.

Abin mamaki da lokacin tafiyar tasa tayi kuma sai  Alhaji yace wai dole tare da matar sa zai tafi jin wannan labarin sosai ya 'daga hankali na bada wasa ba.

Kamar wasa sai gani nayi Ammi ta fara shiri gadan-gadan, ragowar akwatina na da kayayyaki na dake can gidan tasa wai akwaso, da tace ma wai da ni za'a je can 'din amma tun daga lokacin kuka na ya 6alle ina fa'din ni bazani gidan ba, duk yadda Ammi ta so aje da ni wai ko zan duba wani abin amfani na 'kin zuwa nayi sai turawa tayi akwai aka 'debo mata kayan bisa jagorancin Yah Deen.

Shi kam da yake yana zargin kansa ne bisa  dalili na na 'kin zuwa sai bai damu da shiga maganar ba gudun kar allura ta tono garma.

Ni kuwa sam kuka na sai ya kasa tsayawa yinin ranar kuwa kaf haka na sa Ammi gaba da kuka ina fa'din ni ba matar sa bace bazan bisa ba.

Ammi ko kula ni ba tayi ba har sai yamma sannan ta zaunar da ni tayi ta lallashi na da ban baki harda al'kwarurruka tayi min akan wai da kanta watarana ma zataje ta duba ni in tana raye...tace kuma koda wasa naga abinda bai min ba ko kuma ya aikata wani abin wanda raina bai kwanta da shi ba in 'kira in gaya mata uban sa zata ci...taceckovwaya naga yana yi da wata macen in sanar da ita sai taji dalili.

Ni kam bance da ita komai ba, damuwa ta ni kawai a yanzu shine inji ance bazan bishi ba.

Abakin Ammin ma nake jin wai za'a kwashe kayan kitchen 'din mu na wancen gidan a tafi mana da shi can Bauchin, ni kam baki na ta6e na kauda kaina.

Ko ranar da za'a 'dibi kayan ma ba yadda Ammi bata yi da ni akan muje ba sam na'ki, Yah Deen ne ya sau'ke ta gidan dama lokacin da Ammi zata tafin da na'ki binta sai naga ya sa kai yayi gaba inda ya jira ta a waje har ta fito.

Yana sau'ke ta ba'ajima ba ya dawo gidan, da shigowar sa kuwa bai zame ko'ina ba sai cikin 'dakin Ammi da yake bai ganni a parlour ba.

Lokacin da ya shigo ina bayi ban san ya shigo 'dakin ba dan haka skirt 'di na a sama na fito ban sau'ke shi ba, da fitowa ta ne sai na ganshi tsaye ya wani cika iska cikin bakin sa take kuwa na sau'ke skirt 'din nawa cikin sauri har da jan shi sosai zuwa 'kasa.

Yana daga tsayen ya furzo da iskan bakin sa sannan ya ta6e baki gami da buga min wata  harara da ban ta mecece ba.

Kawar da kaina gefe nayi ina tunanin me kuma ya kawo shi, me yake nema.

'Ko'karin fita na fara daga 'dakin inda na tunkari hanyar fita.
Sai ji nayi ya ri'ko hannu na gami da fa'din" Zonan".
Take na waigo a 'dan firgice na kalle inda ya ri'ke hannu na kafin na ankara sai ji nayi ya janyo jikin sa kusa da shi sosai ya ha'da bayana da jikin sa still yana ri'ke da hannaye na, cikin kunne ya ra'da min" Kin raina ni ko?"
Sai nayi saurin girgiza kaina.
Yah Deen sai yace
" Erh mana kin raina ni..yau ma ko gaida ni ma 'kin yi kika yi".
" mancewa nayi".
Yace" Me yasa to kullum kike wa Ammi gardamar zuwa gidan can?"

Shiru nayi na nayi narai-narai da idanu kamar zan yi kuka.
Jin nayi shiru ya sanya shi juyo da ni na fuskance shi take nayi 'kasa da idanu na sai ga hawaye ya gangaro saman kuncina.

Kaina ya 'dago da hannayen sa amma ban iya duban sa ba.." Har yanzu baki mance wancen abin ba ko?"
Shiru nayi sai ma nayi 'ko'karin cire kaina daga hannun sa amma bai sake ni ba sai ya maida min kannawa saman 'kirjin sa ya rungume ni...ni kam sai na cigaba da kuka na.

Bayan kamar sakan sha biyar sai naji yana fa'din suna na" Noor!"
Ya fa'di cikin sanyin murya mai hankali.
Ban amsa shi ba illah hawaye na da na cagaba da gogewa.
" Kina jin kishi na dama sosai har haka ne?"
Girgiza kai nayi da sauri alamar" a a.."
" To menene yake damun ki ki gaya min kinji?"
" Ni bakomai kawai ban son zuwa ne".
" Kin tabbatar bakomai?"
Nace" Umm".
'Kasan ma'koshi.
Sai yace" Zan tafi Bauchi yanzu kimin addu'ah..."
" Allah ya tsare hanya".
"Murmushi yayi sanna yace" Ameen"
A takaice.
Cire ni yayi daga jikin sa amma bai saki hannu na 'daya daya ri'ke ba yace" Barin je sai na dawo ko?"
" Uhumm".
Na bashi amsa da shi
Daga haka ya sake min hannu yayi waje.

Ko bayan fitar sa ma kuka na nasha na na 'koshi sannan nayi shiru.
Lokacin da Ammi ta dawo kuwa bacci nake yi ban ma sani ba sai da na farka kusan Azahar sannan na ganta.

Washe gari Yah Deen ya dawo Bauchin ko damuwa da kamarin sa ma banyi ba, shima 'din kuma bai damu da shiga sabga ta ba.

Bayan kwana biyu kuwa sai ya kasance gidan Ummah ta zan yini da sunan wai muyi sallama da su, Yah Deen ma Ammi tasa ya sau'ke ni, haka kuwa tunda ya 'dauko ni har ya sau'ke ni babu wata kalmar da ta shiga tsakani na da shi domin haushin sa yanzu nake ji sosai, musamman saboda tafiyar nan, baya ga haka ma gashi jiya ya 'kara tunatar dani batun sa da Husnah sai haushin sa ya 'karu sosai cikin zuciya ta.

Har na fita cikin motar na rufo ta bance da shi 'kala ba kawai na juya na yi cikin gida, da shiga ta na cire mayafi na na shige 'dakin Ummah ta na kwanta na cigaba da zubda hawaye na.

Ummah ta data ga yanda na shiga sai bata kula ni ba ta cigaba da sabgogin gaban ta domin ba yau tasan da batun tafiyar ba kuma tasan babu mamaki akai ne nake kukan.

Ina daga cikin 'daki kamar daga sama najiyo sallamar sa, Ummah ce ta amsa shi tare da yi masa iso sannan ta umarci Ummie da ta shinfi'da masa abin zama..inda ta 'kara da fa'din" Ke kuma Hudah kinsan bake ka'dai bace shine kuma kika wucewar ki ciki dan shegantaka ko?"
Ina daga inda nake kwancen nake gungunin" Ni nasan zai shigo ne, mutun kullum yanayin sa daban-daban ina zan gane masa"
Bazan manta masifar da ya zabga min lokacin da naje Darazau ba...amma ji shi kamar ba shi ba a 'yan kwanakin nan, sai daga baya ma nayi mamakin me yasa be tada zancen ba musamman yanda naga ya 'dauki zafi a lokacin har tsoro ya sani.

Murmushi kawai Yah Deen yayi da jin furucin Ummah ta..haka ya zuna fuskar sa wasai tamkar wanda dama can yayi sabo da gidan sosai...in kinji yadda ya nutsar da murya yake gaida Ummah ta bazaki ta6a zaton yana da wani hali daban ba.

Da kansa ya 'kara yi mata bayanin tafiyar ayanda tazo Ummah tace" Ai bakomai Allah ubangiji ya tsare ya bada sa'a"
Yace" Ameen-Ameen".
Bai wani da'de ba ya tashi ya fita bayan ya ajiyewa Ummah ta ku'di, duk yanda tayi da shi ya tafi da ku'din nan 'ki yayi, da yake shima yasan ba fitowa zan yi ba yasa da fitowar sa yaja motar sa yayi gaba abin sa.

Ina daga cikin 'daki nake mita da zagin sa cikin raina..mutun sai munafurci da fuska biyu, idan ka ganshi bazaka ta6a zaton zai iya aikata abinda yake aikatawa ba, kuma Allah sai ya sakawa Ma'u kashe ta da kayi..tuno Husnah da nayi yasa ni fa'din 'yan iskan banza kawai".
Cikin 'dacin rai nake tuno duk 6oyayyun halin nasa na ina kuma jin ciwon su cikin zuciya ta.

Ummah ko ka'dan bata yi niyyan tanka ni ba har sai da na gama zaman 'dakin da kaina na fito sannan gani na haka a hargitse ya sa ta tambaya ta abinda ya same ni, take kuwa na bata labarin tafiyar tare da nuna mata rashin amincewa ta ina fa'da ina kuka, dan ni harga Allah bana son inbisa wani gari mutun cikin garin iyayen sa ma bai ji shakkan kawo mata gidan sa ba inaga inya ke6e gefe kuma?" Cikin zuciya ta na 'karasa wannan tunanin ni ka'dai.

Ummah kam shiru tayi ta gama saurara ta sai da na dasa aya sannan tace" Yanzu Uwata akan wannan tafiyar kike faman 'daga hankalin ki har haka? Miye abin damuwa aciki to?"

Shiru nayi mata bance da ita 'kala ba...cikin zuciya ta na ayyana" Ai Ummah bazaki ta6a ganewa ba, 'kilan nima sai an kawo miki gawata ya kashe nima kafin zaki fahimci abinda ke damu na a lokaci na da kuma dalilin 'kin binsa da naso yi".
Ummah kam tsura min idanu tayi tamkar mai tunani daga 'karshe tashi tayi ta barni a wurin,m zaune, da kaina na gaji da kukan na watsar da batun na cigaba da harkoki na.

Sai can har bayan azahar ma da taga na nutsu sannan ta zaunar da ni tayi min Nasiha, garga'di, ban ha'kuri da kuma jan kunne game da aure na, sosai ta nuna min cewa irin nawa auren natsuwa yake bu'kata dole in bada hankali na, in kula da hakkokin aure na kar inje inbiye wa shirme har wata 6araka ta sake 6ullowa, tace" kowa da kike gani a duniyan nan Hudah da aure ya ginu, aure ne nasarar kowa, da yawan mutane kuma auren na riskan su ne cikin rashin amincewar su amma sai suka yi ha'kuri gagarumar nasara kuma ta cimma su sanadin ha'kurin su, dalilin hakan ma sai kiga sun dace ranar gobe alkiyama, kema ina miki kwa'dayin wannan nasara matsayina na mahaifiyar ki Uwata, ko kukan da kike yi a yanzu da kanki kinsan ba amfani ne da shi ba, domin ba tun yau aka 'daura auren ki ba, bani da ikon sawa ko hanawa a yanzu kinsan yanzu ke mallakin su ce, su ke da iko akanki bani ba, ni kuma bazan ta6a saki ki bijirewa auren ki ba har abada sai dai in wani abin na nagani wanda ya sa6awa shari'a sannan, amma yanzu kam sai dai ince kiyi ha'kuri ki bi mijin ki, kuma ki sani yanzu ne rayuwar aure na sali ya tunkaro ki ba shirmen da kika kusan shekara kina yi ba, domin zaki jene inda babu kowa naki sai ke sai Allahn ki sannan mijin ki abu na uku da zai kasance tare da ke shine halayyar ki, dan haka ki yi 'ko'kari ki tsarkake zuciyar ki ki zauna da kowa lafiya ki yiwa mijin ki biyayya ki kuma ri'ke sirrin ki, mijin ki ka'dai ne abokin hirar sirrin ki da ya shafi auren ki, Hudah har yanzu nasan da sauran ki amma watarana da kanki zaki fahimci cewa ba 'kinki muke yiba inma kinsa hakan cikin zuciyar ki, sannan ki daure ki koyawa zuciyar ki kar6an 'kaddara kowace iri ce kinji? ki cigaba da yiwa mijin ki addu'ah Allah ya nutsar da hankalin sa wuri guda insha Allahu watarana komai zai zam tarihi kamar ba'a yi ba,  abinda kuma ya riga ya faru ya wuce kar ki yadda ki barshi cikin zuciyar ki balle ya dame ki, domin Allah shi ka'dai yasan dalilin ha'da auren ku, tace bazan 6oye miki ba Hudah ni kaina raina ba son wannan auren yake yi ba amma ba yadda zanyi dan ban isa inja da yin Allah ba, sai dai fatan Allah ya baku zaman lafiya mai 'dorewa, idan ancutar dake Allah yana gani kuma zai miki sakayya amma dan Allah kiyi min al'kawari bazaki ta6a cutar da kowa ba".
" Insha Allahu Ummah na"
Na yi maganar siraran hawaye na gangaro min.
Ta sake fa'din" Kiyi min al'kawarin zaki zauna da mijin ki lafiya kiyi masa biyayya da ha'kuri cikin ko wani irin hali".
Wannan karan ina share hawaye nace" Insha Allahu Ummah na".

" Yauwa Uwata kuma banda zargi kinji? domin Zargi na da matu'kar muhimmanci wajen lalata darajar aure, komai da yafaru ya wuce kar ki saka cikin ranki balle ki tuno da shi har ya gur6ata miki tunani, kowa da kike gani.yana da nasan mugun.halin a 6oye bambancinnkawai na wani yafi na wani.ne shiyasa ba'a fiya gane wa ba".
Nace
" Hakane Ummah".
Sai ta cigaba da fa'din" Ma'u kam 'kaddara ya riga ya hau kanta sai dai muyi fatan Allah ya ji'kan ta da Rahama Allah ya tsare 'yan baya..ke ma kici gaba da Addu'ah ubangiji Allah ya kawo miki shiriya cikin gidan ki..wannan karon kam matu'kar naga da cutar wa bazan bari a salwantar min da rayuwar ki ba da kaina zan 'dau mataki, Ke de ki kwantar da hankalin ki, ki nutsu ki bi mijin ki kinji Uwata?".

Kuka na rushe da shi sosai tuno Ma'u da nayi, yanzu har abada wannan ba'kin fentin bazai barni ba, a kulluma za'a dinga kallona ne matsayin matar Deen wanda yayi sanadin ciki ga Ma'u daga 'karshe ma ta rasa ranta gaba 'daya..bana so in dinga yawan tuno wannan incidence 'din domin.gaba 'daya yake tunamin da dukkan rayuwar Yah Deen da na sani tun abaya har zuwa zama na da shi agidan sa, ji nake tamkar idan na 'kara cin karo da irin hakan daga gare shi mutuwa zanyi...cikin kukan na bawa Ummah ta tabbacin" Insha Allahu bazan bata kunya ba".

Sarai nasan gaskiya itama take fa'da min, amma Ummah bata san ni abinda na gani da idanu na ba cikin halayyar Yah Deen da na tabbata ba kowa ke da irin ta ba, ita kanta Ummah da tasani nasan da bazata fa'di wasu abubuwan ba, to ma ta ina zan fara gaya mata sam bazan iya ba..hakan yasa na 'kara sunkuyar da kaina kawai na cigaba da kuka na...rayuwar Yah Deen kacokam 'din ta wata iri ce, a yanda nake.jin zuciya ta ji.nake da ba Ammi bace ta haifi Yah Deen da ko Soyayyar shi zata yi ajali na ne da kuwa zan sadaukar da zuciya ta in mutu da in amince yin zaman aure da shi..amma ina Ammi da Alhaji Baba sunfi 'karfin hakan awaje na.

Jikin ummah na kwantar da kaina sai ta 'dago hannun ta ta 'dora saman kaina sannan tace" Allah ubangiji ya albarkaci rayuwar ki Uwata, Allah ya baki zaman lafiya da mijin ki, ya ha'de kanku ya kawar da shai'dan tsakanin ku".
Ban iya na amsa ta koda da kalma ba kawai na cigaba da aikin kuka na.


Ummah kam daga haka bata 'kara fa'din komai ba shiru muka zauna na tsawon lokaci, tana sake lallashi na ganin Ummie ta dawo daga gidan Yayah Usman da ta je ne ya sata fa'din maza inyi shiru in shiga ciki in huta kafin anjima dan kar Ummie ta fahimci yanayin da nake ciki.

Da yamma kafin azo 'dauka ta Ummah ta bani wani magani ha'di da kindirmo tace inshanye, haka na 'daga na sha ina 6ata raina na goge baki na.

Wata 'yar roba ta bani mai 'dauke da ha'din zuma tace insa cikin jaka ta sai mun tafi can Bauchin sai in ringa sha ka'dan-ka'dan nace to.

Ba'a jima ba sai aka zo 'dauka ta daga nan muka yi sallama da Ummah ta na tafi, banje gidan kowa bama hatta Addah Saudah banje nayi mata sallama ba haka ma gidan Yah Usman...duk na bari ajan zan 'kira su daga baya.

Wannan karan kam" ina yini" Nace da shi jin ya amsa sai na kawar da kaina, sau 'daya tak na kalle shi ban sake kallan inda yake ba, jikin sa rigar Jessy ce ja cikin wa'danda yake zuwa wasan ball da su sai ba'kin dogon wandon jeans da ya sanya, kansa sai tarin kwantacciyar suma da ya saba tarawa.

Gefen hanya na maida idanu na ina bi da kallo yayin da yake tu'kin cikin hankali tamkar ba shi da niyyan jan motar.
Kamar daga sama na tsinci muryar yana fa'din" Kinje kin ta yiwa Ummah kukan naki ko?"
Kallon sa nayi saurin yi batare da nayi niyyan bashi amsa ba, sai yace" Dubi yanda idanun ki suka yi ja dan Allah..baki son mu tafi taren ne?"

Jin tamabayar da yai min daga 'karshe yasa da sauri na 'dage kaina alamar" Erh" zato na ko zai ce to inyi zama na ne, ga mamaki na kuwa sai ji nayi yace" Toh ai sai ki kashe kanki kafin ranar tafiyar tunda ni cinye ki zanyi idan kin bini".

Shiru nayi ban ce da shi komai ba, cikin zuciya ta nake jinjina ba'kin hali irin na Yah Deen, shi dai a kullum bai canzawa halin sa na nan tare da shi sai mugun hali da ba'kar magana kawai ya iya tsarawa.

Kaina gefe nace" Ni dai kam bazan je ko'ina da kai ba".
" Wai saboda mene...ni in ba mutun bane da baza'a bini ba?"
Yayi maganar cike da murmushin mugunta.
Cikin shagwa6e murya nace dashi" Ai wasu mata kake kawowa gidan ka kullum kuma ance babu kyau".
Na fa'di hakan ne saboda abinda ke cikin raina yake cimin zuciya kenan.

Dariya ma maganar tawa ta bashi a yanayin da na yita tamkar yara 'yan goye, amma sai yayi murmushi madadin dariyar, bai kalle ni ba tunda na fa'di hakan, dama yasan dole har yanzu hakan na nan cikin raina bn manta ba, kallo na yayi sau 'daya sai kuma akayi sa'a nima 'din bashi nake kallo ba so ban ma san ya kalle nin ba, sai da ya maida idanun sa kan hanya sannan yace" Kar ki damu yanzu ke ka'dai ce bazan 'kara kawo kowa ba kinji". Fuskar sa ba yabo ba fallasa yayi maganar amma shi ka'dai yasan yanda yaji furucin nawa cikin zuciyar sa, abu ne wanda ya matu'kar girmi lissafin koma waye idan yaci karo da shi, wanda ko shi da kansa ma ba iya jura zai yi ba misali ace ya kama abokiyar zaman sa dumu-dumu cikin wancan halin, yasan Allah ne ka'dai yasan me ze faru

Please Login or Register in order to submit comment