Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da shi alokacin dan yana ga har kisa zai iya yi in ba Allah ya tsare shi ba, amma yarinyar nan ta gansa da idanun ta kuma tayivshiru ta rufe masa wannan sirrin duk da 'karancin shekaratun amma sosai ya jinjinawa bajintar da tayi.

Bazai 'karya ta zuciyar sa ba ya sani faruwar hakan shine babban dalilin da yasa shi tsintan kansa cikin zazzafan soyayyar ta da yayi, sau da dama ko yana school idan ya tuna sai ya dafe kansa, ko da shika'dai ne zaune amma haka kawai sai yaji ya tsinci kansa cikin matsanancin jin kunya haka kawai karma ace ya tuno da Hudah wannan kam sosai tunota yake tsuma zuciyar sa.

Bance da shi 'kala ba kawai na kawar da kaina gefe...

Sai can naji ya sake fa'din" In tambaye ki?"
Kallon sa nayi sai na kawar da kaina tamkar abokan gaba, cigaba yayi da fa'din" Kin gayawa Ummah ne cewa wata ta tazo gidan mu kwanaki?".
Kaina na girgiza masa alamar a a, sai yace" Ammi fa?"
Nan ma kaina na sake girgizawa sai naga yayi murmushi harda lumshe idanun sa sannan ya bu'de bai kalle ni ba yace" In ma kin fa'da cewa zanyi mafarki kika yi ba gaskiya bane".
Tunani yake cikin zuciyar sa cewa ai dama yasan matu'kar ban bada labari a lokacin da abin ya faru ba da 'kyar in sake iya furta galibi 'dan adam nada wannan halayyar.

Baki na ta6e ni kam 'kasa-'kasa nace" Ai Allah ya gani".
Ko da na fa'di hakan ma sau 'daya kawai ya kalle ni daga haka kuma bai sake kallo na kamar yadda bai 'kara fa'din komai ba har muka isa gida.

Da shigan mu gida kuwa ina yin arba da Ammi sai ta kama bakin ta tace" Ikon Allah..haba Mama na yanzu zuwa kika yi kika yini kuka wa Ummahn naki ko? Dan Allah dubi yanda idanun ki duk suka 'kan'kance kuma nasan duk kuka ne ya kawo hakan".

Shiru nayi bance da ita komai ba sai ta jijjiga kanta kawai ta shige ciki.

Washegari Ammi ta tura ni yin kitso da lalle tamkar wata sabuwar amarya..ma'kudan ku'da'de ta kashe wajen ganin an tsara ni yanda ya kamata, nikam ma anayi ina tura baki na har raina bana so.

Tun ranar da muka rabu bayan ya sau'ke ni daya 'dauko gidan Ummah shikenan babu abinda ya sake shiga tsakanin mu, baya shiga sabgata haka nima ban kuma da shi ba sam...mu kan gaisa dai idan mun ha'du da safe ko rana ko yamma sai in gaishe shi.

Ranar da yashigo bayan sallar azahar ya tarar ina waya da su Saif tsayawa yayi ya 'kare min kallo yanda nake fama walwala da sakin fuska baki ya ta6e ya shige ciki ni ban ma kula da shi ba, sai bayan kamar mintina sha biyar sai naji wayata na ringing sunan sa ya bayyana kan fuskar wayar kamar yanda nayi saving" YAH DEEN".
Sosai zuciya ta ta tsinke da ganin 'kiran cuz na jima banga hakan cikin wayata ba.

'Dauak nayi na kai wayar kunne na sai naji yace min" Kawo min wayar ki zan duba abu".

Baki na tura sannan na yanke 'kiran.

Ko da na kai masa wayar kar6a yayi yace inje zai kawo min.

Haka na fita ina 'kukkuni cikin zuciya ta.

Kamar wasa ranar wata laraba Ni da Yah Deen muka bar Shuwarin zuwa cikin garin Bauchi, da kansa yayi driven motar cikin 'daya daga cikin motocin gidan Alhaji Baba...tunda kuwa ya fara tafiyar babu ko kalma da ta ha'da mu, lokaci zuwa lokaci na kan goge hawaye na a haka har bacci yayi awan gaba dani.

Da yake ma baya bin mota da wasa hakan yasa bamu wani da'de ba muka isa.
Kafin lokacin ma na jima da farkawa domin baccin nawa bai wani yi nisa ba, sai da muka shigo cikin garin kafin ya tambayi me nake so nace da shi bakomai, bai tsaya ko'ina ba direct gida muka wuce.








Comment
Vote
Share








*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)


By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*


_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *68*

Gida ne 'dan madaidaici mai kyau da kyan tsari, da shiga ta ma naji ya birge ni har 'kasan zuciya ta, gidan Yah Deen dake Jigawa aka siyar sai aka sayi wannan 'din da ku'din ashe wai.
Already ma an zuba funitures da komai na amfani a ciki wanda duk ragowar kayan cikin suka kasance sababbi ne a idanu na, kitchen ne ka'dai na riga na san da zaman kayan, sai dai yanayin tsarin kitchen 'din nan ya tsere na Shuwarin nesa ba kusa ba.

Da isowan mu Yah Deen  ya sake fita ya barni ni ka'dai a gidan, gajiya ce ta hana ni lalle'kawa amma na so in yi gulma  har bayan kamar 1hr sannan ya dawo da ordern abinci masu rai da lafiya.



*****
     Rayuwar aure na da Yah Deen ya fara ne tun washe garin komawar mu garin Bauchi, a lokacin ne Yah Deen ya fara 'dora ni kan asalin nufin kasancewar mu tare da shi, sai dai bai fito fili ya bayyana bu'katar sa gare ni ba yakan yawaita yi min wayo idan yana so ya ra6i jiki na da fa'din wai size 'din boobs 'dina kawai yake so gwada saboda ya sani wai ko na girma.

Shekaru na goma shida ne a lokacin amma ba laifi ni da kaina nasan inada albarkatun 'kirji dai-dai da yanayin jiki na masha Allah wanda ko marar idanu ya ta6ani sau 'daya amsar sa ta isar masa ba sai ya 'kara ba.

Sau da dama na kan yi mamakin irin auna size 'din da yace yake min cuz yakan 'dan shafe 'yan mintina bai cire hannun sa daga jiki na ba, wani sa'in har bacci na 'dauka ta da hannun sa ajiki na, wani lokacin ma har sai na nuna banso ko kafin yake bari na dan haushi sosai hakan ke bani banda ma tsananin kunyar sa dake kamani, ayanda na fahimta kuwa 6angagren sa ko ajikin sa bai damu ba sam.


Ya 'dauki a'kalla kusan kwanaki biyar yana min wannan gwajin da bansan ma'anar ta ba, tun ina jin nauyin sa har nazo na fara sabawa dan dole na, da yake ma duk Addah ta karantar dani cewa dole akwai faruwar irin hakan cikin zaman aure amma ban san cewa haka abin zai zo min cikin lokaci 'kan'kani ba, du da haka nayi 'ko'kari sosai wajen ganin na 'dan saki jiki na bisa la'akari da maganar Addar Maryam, wannan dalilin ne yasa ko lokacin da naji ya zarce da kissing baki na zuwa wuyana ma ban wani 'daga hankali na ba balle in yi yun'kurin hanashi, balle lokacin da na tsinci la66an sa saman boobs 'dina ranar da kaina sai da na shiga wani yanayi.

Wasa-wasa abubuwan da Yah Deen ke min suka fara zarce tunani na, a time 'din ne kuma na fara  'kin amince masa da gwajin da yake min, da yaga hakan kuwa sai ya  daina sassauta min zafafan romance ya fara yimin mai tsayawa a zuci, bansan yanayi da hakan ke shigar dani ba ni dai kawai sai in jini ina kuka sosai, da sannu naga yafara haukace min yana 'ko'karin raba ni da sittarar dake jiki na, ganin haka yasa nayi saurin ri'ke masa hannu ina girgiza kaina ina hawaye.

Hannun nawa ya ri'ke cikin nasa sannan ya rufe baki na da nashi...tsawon wasu da'ki'kai yana kissing baki na sannan ya barni, kansa ya kwantar gefen fuska ta hannaun sa na yawo min a baki idanun sa rufe naji yace min" A gida ba'a ce miki ki kula da hakki na ba?"
Shiru nayi hawaye na gangaro min ta gefe da gefen fuska ta, cikin raina nake tunanin abinda Addah ta da Ummah ta suka gaya min, Ammi ce ka'dai wannan kalmar bata shiga tsakanin mu ba.

Jin hucin numfashin sa gefen kunne na ya sani dawowa daga tuanin da na tafi, take na matsara da kaina, ai kuwa sai ya sake dawo dani kusa da shi hakan ne ya sani sakin wani kukan amma ko bi ta kai na bai yi ba sai da yaga dagaske nake kukan kafin ya 'kyale ni badan ransa ya so ba, bai kuma iya yace dani komai ba kawai ya shigar dani cikin jikin sa ya rungume, hakan bai dame ni ba cuz a yanda ya saba caku'da min jiki na a ganina runguma is normal dan haka bacci 'dauka ta yayi cikin kwanciyar hankali.

Ban san halin da yake ciki ba balle hakan ya dame ni, ban sani ba ashe shi kam daban yake,  sassaucin sa ka'dan ne ta wannan fannin.

Cikin bacci na ji ana sake bin jiki na, lokacin da na farka ma ya riga da ya yi nisa, duk wasu 'kananun koke-koke ne bai bi ta kansu ba, wani azaban zafi da naji ya ratsa ni ne ya sani sakin ihu mai 'dan 'kara tare da dam'kan hannun sa da 'karfin gaske tamkar zan cire mishi naman wurin, shi kam ma bai wani damu ba illah saurin toshe min baki dayayi da nasa dole kuka na ya tsaya illah hawaye ban kuma saki hannun san ba har a lokacin saboda koka'dan ban ta6a sanin akwai irin zafin nan a duniya ba tamkar ana yankan naman jiki na haka naji.

Ranar Ammi na ta sha 'kiran neman ceto, duk da hakan bai barni ba har sai da ya cimma burin sa kafin nan.

Duk kuwa da cewa cikin tsananin tashin hankali nake amma hakan bai hana ni jin albarkar da ya dinga sanya min ba dan da naji ya fa'da nima zance" Ni bana so ka 'kyale ni".


Sai yayi murmushi kawai, ranar kam na ga sauyi sosai domin da kansa ya rakani bayi nayi wanka inayi ina banka masa masa harara, in zai kamani kuma ince bana so sai ma na saki wani kukan dan ni harga Allah tsoro yake bani yanzu.

Da yaga haka sai yace" Ai ramawa nayi, nima kusan cire min fata kika yi ashe ba da'di"

Ban kula shi ba na kawar da kaina gefe, sai ya kamo hannun nawa a 'ko'karin sa na ganin faratana, saurin fisge hannu nayi na cusa su 'kar'kashi na ina tura baki.
Ganin hakan ya sa shi sakin murmushi kawai ya dawo baya na ya kwanta, saurin jan jiki na zan matsa sai yace min" Kul...dan kinga ban rama yakushi na ba ko? kina matsawa sai na rama kuma irin na 'dazu zanyi ni...".
Luf nayi da jin abinda ya fa'di ban kuma yin wani yun'kuri ba illa hawaye dake gangaro min zuciya ta cike fal da tsoro.

A kunne na ya ra'da min" Matsoraciya kawai... kiyi baccin ki bazan sake ba kinji?".
Shiru nayi masa kawai na rintse idanu na yayin da ya cigaba da bin fuskata da kallo a hankali ciki-ciki ya furta" Kin sani farin ciki sosai, ubangiji Allah ya biya ki da aljannah"
Yana 'dan shafa kaina yay i maganar ni kam sai na ta6e baki na na ma manta da abinda ya fa'da da farko take na matsa gefe na karkata kaina hannun sa ya bar jiki na...haushin sa nake ji ni kam, dama halin sa duk basu yi min ba, gashi yazo ya 'kara min da mugunta irin ta marasa imani na raya hakan a zuciya ta.

'Bangaren sa kuwa kasa sakewa yayi da na bar jikin san sai ya tsaya bin bayana da kallo, a hankali ya sake matsawa kusa da ni 'kafafaun sa ya 'daga ya 'dora saman nawa wai dan kar in sake zamewa sannan ya ran'kwafo da kansa saman nawa.
Inajin sa nayi shiru dan ni ka'dai nasan kalar azabar da nasha, nake kuma jin gurbin sa har yanzu shiyasa ma hawayena suka kasa tsayawa.

" Me kike so?" naji ya tambaye ni cikin murya mai sanyi kamar ba Yah Deen ba, shiru nayi ban kula shi ba sai da ya sake maimaitawa kafin nace" Ni bakomai".
Da muryar kuka nayi maganar.
Sai yace" Owk in shikenan..so kike in sake ko?" Da jin haka sai nayi saurin girgiza kaina gami da fa'din" a a".
" Fa'da min to me kike so?"
" Ni bacci nake so in yi".
' Yar dariya yayi wanda da ji kasan daga cikin zuciyar sa ta fito" Kiyi baccin ki to...shikenan?"
Na 'dage kaina.
" Akwai ciwo ne?"
Kai na sake 'dagawa alamar ehh sai yace" Very sorry dear Ki yafe min Kinji?"
Shiru nayi na 'ki kulasa.

Shima bai sake ce da ni komai ba har bacci yayi gaba dani.

Ko da asubah dana farka ban gansa cikin 'dakin ba, sai nayi zaton ko masjid ya tafi, shaf na mance da abinda ya faru, 'ko'karin mi'kewa tsaye na fara nan naji 'kafafuna sun ri'ke ni, komawa nayi na zauna da sauri hawaye na kuwa tamkar an 6alle su sai na dafe kaina a hankali na fara tariyo abinda ya faru, cikin hakan tunani na ya gangara can Shuwarin ganin da nayi masa da Husnah a can...sai na rasa ma dalilin da yasa nake jin haushin lamarin, ashe irin azaban da itama take sha a wurin sa kenan, Allah sarki shiyasa ranar naga tana zubda hawaye, gaskiya Yah Deen mugu ne shi na gaske.
Na fa'da cikin raina, zuciya ta cike da fal da tausayin mu gaba 'daya.

A daddafe na taka na 'karasa bakin bayin ina 'ko'karin saka silifas sai na gansa ya shigo jikin sa da farar jallabiya..da gani na tsaye awurin sai yayi saurin jefa min tambayar" zaki iya ne?"
Cike da kulawa.
Kawar da kaina nayi sannan na bashi amsa da fa'din umm hannu na dafe da bango.
Sai yace" Kiyi amfani to da ruwan 'dumi kinji?"
" Uhum"  nace tare da 'karasa shigewa na rufo bayin.

Yinin ranar kam ba laifi na yi tane cikin kulawar sa da yake ma bai fara fita aiki ba tukunna, hakan yasa muka yini a gida tare da shi, sau 'daya kawai ya fita ya mana odern abinci sai kuma masallaci da yaje.

Lokacin da ya sanya 'karamar riga ne naga inda na yakushe shi ashe  wurin har ciwo yayi kau da kaina nayi sai kuma naji ba da'di har cikin raina.

'Kilan hakan ne yasa idan zai fita sai ya canza riga zuwa mai dogon mai hannu dan ya rufe wurin.

Yah Deen kam da ya fahimci.bana sakewa da shi sai ya ke barin idan nake dan kar ya takura ni, suna dai yana gida ne amma ba inda nake ba, ya kan shigo dai akai kai duba ni dan ko abincin ma da kansa ya zo ya 'diba min duk da ina cikin ciwo amma bai hana ni mamakin sa ba, ni dai sai naga bai canza min daga Yah Deen dana sani tun farko ba, fuskar sa dai wasai ba yabo ba fallasa amma bazaki ta6a iya fassara yanayin sa ba, tunani na kuma bai bani cewar a yau 'din ina matu'kar bu'katan kulawar sa ba, dan ni ko shigowa da yake yi ma takurani yake yi, saboda har a lokacin tsananin kunyar sa da haushin sa ne suka yi min ca.

Hankali na ya 'kara tashi ne da lokacin bacci na yayi, fargaba yabi ya cika min zuciya, duk yanda naso in kawar da tunanin abinda ya faru tsakani na da shi jiya kasawa nayi saboda yanda tsoro ya mamaye ni.

Haka na kwanta luf amma motsin kirki idan naji sai zuciya ta ta harba take sai in shiga firgici.

Lokacin da naji ya janyo jikin sa kuwa kusan sumewa nayi jiki na ya fara kakkarwa sosai..yi nayi tamkar ina bacci da tunanin 'kila hakan zai sa ya 'kyale ni duk dama nasan jiya ina cikin baccin amma ya tada ni bai kuma sassauta min ba.

Cikin sa'a ma sai bai yi min komai ba ashe shi da kansa ya fahimci halin da nake ciki na tsorata da nayi da shi, da kansa ma kuma bai yi niyyan yi min komai ba,  ina rungume cikin jikin sa naji yana sau'ke numfashi da alamu bacci ne yayi gaba da shi.

A fili na sau'ke ajiyan zuciya sannan na bu'de idanu na, hannun san da ya rungumo ni da shi nabi da kallo a hankali na 'daga nawa hannun na 'dora kan nasa kamar ance dani inyi hakan.
Ban san lokacin da bacci ya tafi da ni ba, yayin da nayi bacci na cikin kwanciyar hankali.

Kwanan mu biyu da shi amma bai sake yi min komai ba, haka kuma har a lokacin shike siyo mana abinci rana da da na dare, haka kuma ako da wani lokaci ya kan tabbatar da cewa nayi amfani da ruwan 'dumi, nima kuma da yake na fahimci idan nayi amfani da shi 'din ina jin da'di shikenan da kaina ma ko bai tuna min ba na kanyi anfani na da shi.

Sosai na fara sakan jiki na ganin irin waccan abin bai sake faruwa ba, gashi ba laifi yanzu na 'dan samu samu lafiya da yake da kansa ya duba ni,  bana so amma bazan iya yi masa gardama ba dole inaji ina gani ya gane min jiki na da sunan wai duba lafiya ta...ranar haka na yini ina tura baki na, ga shi kunya sosai ya kama ni fiye da na ranan can...ko lokacin da ya gama duba nin ma kifa kaina na yi na kasa 'dagowa in kalle shi..ga haushi ga kunya haka suka taru suka hanani sakat...shi kam sai naga ko ajikin sa bai damu ba...cikin zuciya ta na raya ai dama Yah Deen ba shi da kunya sam.

Ranar kwana na uku da jinyan nawa ne na sake raina kaina, domin Yah Deen mantar da zuciyar sa yayi wace ni, ya manta da batun tsorona ya kuma kawar da kai ga 'kan'kantar shekaru na, tun kafin yayi nisa na raina kaina, domin ji nayi ko na farkon ma ba komai bane  akan yau, azabar na danaci ranar sam bazan iya misaltawa ba.

Nayi kuka kamar raina zai fita ko tausayi na bai ji ba yau kam bai min sassauci ko na 'kwayar zarra ba, ba 'karamar wuya nasha a hannun sa ba.

Tun daga ranar ya maida ni abincin ruhin sa, duk lokacin da yaga dama baya ko bi takan hawaye na...watarana da abin ya isheni ne ina kuka nake ce da shi ya 'kyale ni ya tafi wurin 'yam matan sa, ni banaso yaje inda ya saba wurin Husnah ya 'kyale ni.

Da jin na ambaci sunan Husnah sai ya bige min baki na take kuwa nayi shiru ina hawaye cike da takaici.

Sam ni banason abin nan da yake yimin, sa'a ta ma 'daya yanzu yakan fita asbiti bakin aikin sa baya yini a gida, hakan yasa nake 'dan samun sararin da zan zauna ni ka'dai, a haukana gani nake zama tare da shi 'din takura ne babba.

Abu 'daya da yake tilastawa kansa shine lalla6a ni a duk lokacin da yaso ra6a ta, amma idan zaki gan mu da shi haka bazaki ta6a zaton muna zaman kirki a gidan ba, saboda babu wata sha'kuwa ta zahiri a tsakanin mu rayuwar sa yake yi nima nake yin tawa, musamman ma da ya fahimci ba nason zama da shi shikenan ya sawa zuciyar sa gudun takurani, tunda ya fahimci bana samun walwala a inda yake sai yake taka tsantsan da duk abinda zai takurani balle ya shiga rayuwa ta,  lokacin baccin ne kawai rayuwar mu take zama wuri guda wanda hakan ma dan yasan ba zai iya bane.

He was da so kind to me that koka'dan ban ta6a zata ba, ban ta6a tunanin zai saki ransa mu zauna har haka da shi ba hantara ba, cuz a zato na zan fuskanci abu fiye da hakan a zama tare da shi.

Ni sam  hakan sai ta6a damu na ba dan banga aibun sa ba ballantana in hango illar sa, abu 'daya da na sani shine kawai Yah Deen mijina ne na aure wanda idan nayi masa biyayya wata'kil Allah ya ha'da ni da rahamar sa, ko shawarwarin da akayi ta 'dura min cikin kaina har yanzu suna nan a brain 'dina ban manta ba, sai dai har yanzu ban ta6a tunanin akwai ranar da zan iya amfani da wasun su ba, saboda a gani na a gun Yah Deen ba aiki zasu yi ba da ma ace wani daban ne, ban kuma ta6a yin tunanin zamantakewar mu da sha'kuwar mu zai iya saurin dai-daita ba idan nayi amfani da damar da nake da shi musamman da nasan cewa yakan sau'kar min da kansa aduk lokacin da yake son ra6ata ba.

Na bar hakan ne matsayin dole akai na ne kawai matsayi na na matar sa shiyasa a kullum yanayin zama na da shi bai ta6a damuna ba.

Da kaina na fahimci 6oyayyen halin sa na sanyin hali, kyautatawa da kuma sanin hakkin wanda ke tare da shi, sai dai idan baki zauna da shi sosai ba bazaki ta6a gane hakan ba, 6angare na kuwa duk da na fahimci duk wannan amma sam nakasa yin wani yun'kuri dan yin amfani da damammakin da na samu.

Ko dogon hira ban ta6a zama nayi da shi ba, gani nake kamar komai da Addah ta ta koyar dani idan nace zan yi a wannan gidan tamkar wahal da raina ne kawai,  shiyasa na share na watsar da komai hakan ma da muke rayuwa ni anawa ganin ya ishe mu.

Na kan yi waya da duk makusanta na, Ammi na, Ummah ta, Anty Zainab, Addah na Maryam Saif da sauran su, Yah Usman ma sau 'daya na ta6a 'kiran sa muka gaisa ya tambaye ni akwai matsala ne nace da shi bakomai yace to shikenan idan da wani abin in sanar da shi nace to, tun ranar ban sake 'kiran sa ba haka kuma shima bai 'kira ni ba, Addah Saudah kam ba waya a hannun ta shiyasa ban ta6a samun daman magana da ita ba tunda na zo garin Bauchi.

Addah Maryam ma kan yawaita tambaya ta yanayin zaman mu sai ince da ita ai bakomai yanzu lafiya lau muke zaune, a kullum ta kanyi 'ko'karin ganin ta 'dora ni a kan hanya amma ni kam a wautata sai dai inji ta inyi murmushi kawai a 6oye..ko da wasa ban ajiye akwai ranar faruwan irin zaman da Addah Maryam take tunanin muna yi ba.

Anty Zainab ma yanzu bana gaya mata komai dake tsakani na da shi, kullum idan ta tambaye ni sai ince da ita ai ya canza yanzu ba kamar da ba...duk da haka Anty idan tayi waya da shi akullum sai ta yi masa fa'dan cewa dan Allah kar ya yawan yi min masifar sannan sai yayi dariya yace" Itace ta ta gaya miki ina mata masifa ko Anty?"
" a a haba dai, ai nasan  halin kane Mu'een shiyasa".
Yace
" To ki kwantar da hankalin ki Anty, ni da ma ba zama nake yi agidan sosai ba yaushe zan ganta ma har nayi mata masifa.."
" Bangane baka zama ba, ba ka ganin ta? Kamar yaya? wai kana nufin a haka kuke zaman auren Mu'een?"
" Kai Anty ba yanda kika 'dauka nake nufi ba".
Tace
" To yaya ne?"
Yana sosa kansa ya bata amsa da fa'din
" Ina ganin ta mana Anty,  amma ai kinsan abubuwa sun min yawa yanzu sai ahankali bana  samun zama ne sosai".
Anty kawai sai tace
"  Hmm.. Allah dai ya shirya min kai".
" Ameen Anty na".
Ya 'karasa maganar da 'yar dariya
Duk da hakan a kullum Anty bata gajiya da tunasar da shi yaji tsoron Allah ya gujewa sharrin duniya, ta kan kuma ce da shi dan Allah ya ringa sassauta min da yake tasan ni da masifar tsoron sa.

Ko Ammi ma ta kan yawaita tambaya ta abinda ke damu na acewar ta wai sanyi na yayi yawa, sai dai inyi murmushi ince da ita bakomai, dan ni yanzu nawin Ammi nake ji sosai...yanzu nasan asalin matsayin ta waje na.

Ko bayan gama wayar ta mu da ita ma murmushi  kasa barin fuska ta yayi saboda jin da'din yanda suke bani kulawa, ni kaina yanzu bazan iya ce ga matsala ta ba, cuz ban san ta ba, na kan samu kaina cikin matsananciyar nisha'di idan ina game da waya ta, in 'dauki pics in yi duk yanda nake so da ita, zan yi wanka na in sanya duk irin sittirar da nake so babu mai takura ni, ko shi Yah Deen 'din ba shiga sabgata yake yi ba, ko da kwalliya nayi baya yabamin a

Please Login or Register in order to submit comment