Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta shiga har yaso ya zarta nata ma.

Sam hakan bai sa Ammi mamaki ba cuz tasan irin 'kaunar da Anty Zainab ke wa Mu'een, in sha'kuwa ce kuwa ko ita da ta haife shi baza ta ce tafi ta sha'kuwa da shi ba saboda a gaban ta ya tashi..so fiye da haka ma idan ta gani daga Anty Zainab bazai sa ta mamaki ba.

Itama Anty Zainab Uncle Ja'afar ta 'kira a waya tace dashi gaskiya bai kyauta mata ba da har ya 6oye mata wannan maganar.
Sai yace" Tunda yanzu kinji ai shikenan".

Ita ka'dai tasan me take ji cikin ranta...Alhamdulillah kawai take ta maimaitawa, cuz tafi kowa 'kaunar ganin Mu'een 'din ya samu mata irin Hudah sai gashi Allah ya cika mara burin ta cikin sau'ki, badan Ammi ta gaya mata abinda Alhaji Baba yace game da batun ba da gobe sai ta ha'da sabuwar gagarumar walima na farin ciki dan ta nuna godiyar ta ga mahalicci.

Washe gari sunday..kamar yadda Alhaji yayi al'kawari kuwa hakan ne ya faru..cuz wani yaron sa ya sa ya kaini gidan mu dan gaida mahaifi na, anan na tarar da shi ma yana kan shirin tafiya, ban fahimci komai ba duk kuwa da cewa naga anata nan nan dani sannan Baban mu yayi min doguwar nasiha cikin natsuwa kan ha'kuri tamkar wanda ganawar mu da shi kenan ta 'karshe har yasa jiki na yayi sanyi.

Ko da wasa babu wanda yace min an 'daura min aure duk kuwa da cewa duk sun sani, ban sani ba ashe duk Alhaji Baba ya ro'ki da kar a fa'di min har sai yaga abinda hali yayi.

Abu 'daya na fahimta kawai canji daga wurin ahali na, yanda ake bani wani daraja da kaffa-kaffa dani abin ya 'daure min kai sosai, sai dai ban kawo batun aure ba sam ko a tunani na, na dai yi tunanin girman da na 'kara ne ya sa ake min hakan dan haka naji Anty Zainab ta fa'di lokacin da zan taho.

Turare wannan hanani amfani tayi da asalin nawa ta bani wasu marasa 'kamshi sosai wai ai na girma yanzu so in dinga kula da komai na rayuwa ta.

ko da nace zanje gidan su Binta ma Ummah ta hanani tayi, ko gidan Anty saudahn mu banje ba Ummah ta ta ri'ke ni a gida tace wai in bari sai wani lokacin kawai.

Ban fi 3hrs ba a gidan aka dawo 'dauka ta...haka na shiga mota ina tuttura baki na gaba da mitar ni banganewa wannan sabuwar tsarin ba duk an bi an takura ni.

Da isata gida kuwa na tari Ammi da mitan Ummah ta bata barni naje ko'ina ba, ko gidan Addah ta banje ba da gidan su Binta...kafin in kai 'karshen magana ta kuwa sai ga hawaye ya gangaro min.

Ammi rasa abinda zata ce da ni tayi kawai sai ta jawo jikin ta ta hau lallashi na, cikin hakan dmtake ce dani kar in da mu wataran ai zanje...nace" Ammi kinga ma fa Ma'u tace min zata zo bikin Yah Deen kuma bata zo ba bansan me yasa ba kuma ban je na duba ta ba duk Ummah ta ta hana ni".

" Rabu da ita ai zata zo may be bata samu daman zuwa bane kawai".

Anty Zee na ganin yanda nake yiwa Ammi kuka sai ta janyo ni ta ringa bani misalai tana jan hankali na da da'da'dan kalamai take fa'din duk mace mai aji ai bata yawan yawo komin ta bisa tsari take yin sa ba wai ta ringa shige-shige ko'ina kamar akuyar da babu 'dauri ba.

Ni dai kawai jin ta nayi ba wai dan na fahimci me take nufi ba.

Ranar kuwa gida ya watse kaf kowa ya koma inda ya fito, ko abokan Yah Deen ma ranar duk suka koma dan daga gida da suka gaida su Alhaji sai suka wuce bayan ya sallame su, aka bar shi shi ka'dai sai Imrana kamar da can.

Yah Deen ranar bai je ko'ina ba dan haushin an hana shi tafiya bacin ba komai yake yi a gidan ba, haka ya yini a wuri 'daya illah Imrana da ke faman shiga yana fita...cikin kwanciyar hankali abin sa.

Uncle J ma da sassafen ranar ya koma Taraba Anty Zee kuwa ba yanzu ba sai daga baya zata koma dan sai ta 'dan kwana biyu a Azare ma tukunna kafin ta tafi, gida ya zama shiru babu da'di..lalle jama'ah rahama.

Haka inaji ina gani aka takurani da zaman gida, illah makaranta da nake zuwa...kuma ko makarantar ma ban ganin Ma'u, gashi su Ammi sun hanani yawo balle inje gidan su in dubo ta...

Sai da aka yi kwana biyar da bikin Yah Deem kafin Ma'u tafara fitowa makaranta...nan na isheta da tambayar me yasa bata zo bikin Yah Deen ba?"
Tace min" bikin da aka ce an fasa 'din?"

Nace" Erh amma ai de mutane sun taru kowa yazo nayi ta duba ki bangan ki ba...".
Tace" Banda lafiya ne shiyasa banzo ba".
Sai nace
" To waye yace miki an fasa kuma ?"
" Imrana".
Ta bani amsa a takaice.
Sai nace
" Ayyah ai naso in zo gidan na ku amma an hanani yawo yanzu shiyasa banzo ba".

Shiru tayi bata sake kulani ba.

One thing da na fahimta game da Ma'u yanzu sam bata son yawan surutu sosai sai dai ban san dalili ba dan haka nima sai nayi shiru ko mun ha'du a makaranta ko Islamiya hirar mu ka'dan ce da ita da yake ma ba kullum take zuwa ba sai jifa-jifa...amma duk ta natsu ta daina rawar kai yanzu (ban sani ba ashe Yah Deen ne ya koya mata hankali).







_Comment_
_Vote_
_Share_








*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)


By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

_Nagode sosai masoya Allah ya bar min ku..._


*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *55*


Hisham yazo gida kamar yadda mahaifiyar sa ta bu'kata sunyi magana kuma ya fahimce ta, musamman ma da yaji cewar an riga da an aura masa Husnah, jin hakan ya matu'kar faranta ransa har ma ya kasa 6oye farin cikin sa, bakomai bane kuma yasa hakan face tsananin soyayyar da yake yi mata, shiyasa ma ko guda daga cikin sharu'd'dan da mahaifiyar sa ta gindaya masa akan Husnahn bai yi jayayya da shi ba.

Zuciyar sa 'daya ya 'daukan mata al'kawarin kulawa da Husnah da kuma sau'ke duk wani hakkin ta da ya rataya akan sa, ya kuma yi al'kawarin bata kariya iya iyawar sa, duk da Hajiya Kareema bata fito fili ta bayyana masa asalin meke tafiya ba amma tayi 'ko'karin ganin ta nuna masa daraja da muhimmancin da Husnan ke da shi a wurin sa...wanda bayaga aure akwai kyakykyawar dangantaka tsakani wanda shi kansa ya sani.

Ko da ya isa ga mahaifin sa ma ba wani ba'kon al'amari yaji daga bakin sa ba wanda zai rikita shi, bambancin kawai shine shi bai yi masa maganar ta fuskar fahimta ba, ya dai ce da shi yayi masa aure da Husnah and kuma yana fatan zai masa biyayya bisa hakan.

Hisham bai wani damu ba dan ya riga ya san wace Husnah, kuma sun riga sun gama magana da mahaifiyar sa kafin nan so hankalin sa kwance ya bar gaban mahaifin sa da 6oyayyen farin cikin sa a zuci.


Bai samu damar zuwa ganin Husnah ba har sai washegari...kuma Alhamdulillah 95% ya samu ha'din kanta kan auren dan bata nuna masa tsana ko nuna bata 'kaunar zaman aure da shi ba.
Batun tarewar ta kuma yace shi da kansa zai shirya komai kafin ya koma.

Wurin mahaifiyar sa yaje  suka sake magana akai inda ya nuna mata cewar ba abin damuwa bane tunda ma tana makaranta, so zata cigaba da karatun ta a Jigawa har sai ta kammala kafin.


Ai kuwa muhalli kawai aka canza mata daga campus zuwa wani madaidaicin gida zubin zamani, wanda Hisham ya cire ma'ku'dan ku'dade aka biya haya da shi.


Gidan ta aka tsara mata tamkar acan zata 'kare rayuwar ta dan sosai gidan yaci ku'di abin ba'a cewa komai, yayin da shi Hisham 'din zai cigaba da zaman sa a Abuja bakin aikin sa, sai dai ziyara kawai zai ringa kawo mata aduk lokacin da ya samu dama.

~Sai fatan Allah ya basu zaman lafiya mai 'dorewa.~



*****
          Cikin shirin makaranta ta na fito da yake nayi latti so sai nake ta hanzari inga na fita dan kar in makara sosai, Ammi da Anty Zee na zaune a parlour na fito ina sanya Hijab akaina ko duban su da kyau ma banyi ba na nufi 'kofa ina fa'din" Ammi na tafi yau na makara sosai".
" Adawo lafiya".
Ammi tace da ni gami da mi'kewa tayi ciki kamar dama jiran fitowa ta take yi...ko juyawa banyi ba na cigaba da tafiya ta ina gyara zaman jakata da tunanin saurin da zanyi kafin in isa, daf da zan bar parlourn naji muryar Anty Zainab na fa'din" Hudah baki ko gaida Yayan ki ba zaki tafi?"
Saurin waigowa nayi jin ta ambaci Yaya na..nan naci karo da Yah Deen zaune daga gefen ta ya wani kishingi'da yana danna wayar sa.

Sam ban lura da shi ba lokacin da na fito sai yanzun na ganshi.

'Dauke idanu na nayi daga kallon sa na mayar kan Anty sai naga ta min murmushi tana min nuni da in gaida shi...cikin sanyin murya na furta" Ina kwana Yaya"...kamar ba zai amsa ba can 'kasa-'kasa cike da izza ya amsa da" Lafiya" ata'kaice.

Sai da na juya na kalli Anty Zainab dan ganin yanayin ta da son tabbatar mata da cewa na gaida shin sannan na
juya na sa kai nayi gaba da tunanin halin sa cikin raina.

" Wai me yasa kake haka ne Mu'een...?" Anty ta tambaye shi tana kallon fuskar sa bayan fitata.

" Me nayi Anty?"
Shima ya mayar mata da tambaya madadin amsar maganar ta yana mai 'daga idanu ya kalle ta.
" Aww kana nufin kai baka san me ka aikata yanzun ba? Yadda kake wa yarinyar nan ai kai da kanka kasan bai dace ba...kai baka tunanin gaba ko Mu'een?...kar fa...".

Bata 'karasa fa'dar abinda tayi niyya ba ya tare ta da fa'din"...Insha Allahu babu abinda zai faru Anty...dan nasan abinda zaki fa'di bai wuci wanda kika saba fa'da ba".

" Hmm..amma dai ya kamata ka daina haka nan tunda babu wanda ya san me gaba zata haifar..'kila sai ka gama mata fi'ili yanzu wataran kuma mugan ka kana ro'konta.. kasan ita rayuwa babu abinda bata tafiya da shi..."

Gira ya ha'de tare da gyara zaman sa da kyau yana duban Anty yace" A wani dalili zan yi hakan kenan Anty?"

" Dalilin aure mana".
Ta bashi amsa tana murmushi...take ya sake ha'de ransa tare da kauda kai gefe yana fa'din" Allah ya sawwa'ka wallahi..wannan 6eran kike fatan aure tsakanina da ita Anty ni me zan yi da ita?"
" Ko ma menene dai kai kasani..ko da ita kiyashi ce kuwa idan Allah ya tsara kaine mijin ta baka isa kayi jayayya ba..."

Da serious tune cike da 6acin rai yace
" Please Anty ki daina min wannan fatan dan Allah..ban so".

Bata 'kara cewa komai ba kuwa illah bayyananniyar murmushi dake haskawa saman fuskar ta...tana tunanin ranar da Mu'een zai ji da kunnen sa cewa Hudah matar sa ce ta sunnah da aka 'daura musu aure batare da sanin sa ba... ayanda ta sanshi take kuma ganin take-taken sa tasan ranar kuka ne kawai ba zai yi ba saboda ba'kin ciki...ni kuwa nace ( ~time ll tell~ ).


Tunda suka yi wannan maganar bai sake doguwar hira da Antyn ba, bai ma jima a gidan ba ba ya tashi yayi musu sallama ya koma gidan can sa ransa a matu'kar 6ace.


Daga ranar kuwa naga ya sake canza min, ni ban san abinda ya faru ba sai gani nayi idan mun ha'du ko kallon arzi'ki bai min, duk da ma ko da can baya ma haka ne amma dai ba kamar yanzu ba, ada, haka ma gaisuwa ta sai ya ga dama yake amsawa, ni kam ban wani damu da hakan ba da yake nasan wannan ka'danne daga cikin halin sa da ni na sanshi da shi.

Sati guda bayan bikin Yah Deen sai ya tattara ya koma Jigawa ranar wata Sunday...Anty ma washegarin tafiyar sa ta koma Azare wurin dangin ta...gida ya dawo shiru babu kowa sai mu ka'dai.


Duk wani abu da ya faru a bikin bai sa na kawo faruwar wani lamari cikin zuciya ta ba, da yake ma har a lokacin ban gama mallakar hankali na ba shiyasa sam ban ta6a wani dogon tunani kan maganganu ko abubuwan da naga suke faruwa a gidan ba.

Sai daga baya ne ma bayan kowa ya watse nake tambayar Ammi ashe wai an fasa auren Yah Deen 'din.

Ammi sai tace da ni a ina naji..ban 6oye mata ba nace Ma'u ce ta gaya min nima.

Ammi sai tace 'karya ne ba'a fasa ba, an 'daura auren tun a ranar babu wani fasawa da akayi.
A 'kagauce na sake tambayar ta ta da fa'din
" Ammi to ya banga amaryar ba har yanzu?"
Sai tace" Tana gidan su tukunna ba yanzu za'a kawo ta ba".

Jin haka yasa na yadda cewa amaryar Yah Deen 'din tana gidan su har kuwa na fa'dawa Ma'u yanda muka yi da Ammin kaf da muka ha'du da ita...jim naga tayi bata ce dani komai ba, ashe abin ya dame ta sosai sai dai ta ri'ke cikin ranta kawai...tunani take yi akan 'karyar da suka shirga mata shi da abokin sa Imrana akan wai ya fasa auren kuma  gun mahaifinta zasu zo neman auren ta ashe 'karya ce ba'a fasa auren nasa ba...shiyasa ma ya yi tafiyar sa bai ko sake bi ta kanta ba ashe..bayan uwr azabar da ya bata suka kuma hanata sanar da kowa.


Bayan wasu kwanaki...
Yanda abin yake cinta arai har yasa ta fara 'dan ramewa sai dai babu wanda yasan takamamman me ke damun ta, ko makaranta ma yanzu ba zuwa take yi sosai ba sai lokaci zuwa lokaci.

Yah Deen ya riga Husnah komawa makaranta so hankalin sa kwance ya cigaba da karatun sa.

Ya kusan yin a'kallah kwanaki tara da komawa amma bai ta6a ganin ko gilmawr Husnah ba..shi kam ma ko tunawa da ita bai yi ba, sai dai acikin 'yan kwanakin ranar wata laraba labari ya iso masa cewa anga Husnah cikin makaranta.

Basarwa yayi bai nuna wata alamar damuwa ba,  dan harga Allah shi yanzu ba ta gaban sa..sai da ma aka same shi da maganar ta kafin ya tuno da ita.

Sai dai me ?
komawar sa gida sai tunanin Husnah ya bi ya cika shi, a lokacin ya fara missing presence nata, 'kewar ta ya'ki barin sa ya sarara har ya kasa ribatar zuciyar sa shai'dan yayi galaba a kansa ya mantar da shi cewa tana da auren wani daban  akanta wanda bashi ba.


Kamar wasa ya 'daga wayar sa...batare da wani tunani ba kawai ya danna mata 'kira da wani layin sa da ya tabbatar bata shi.

Daf da 'kiran zai yanke sannan ta 'daga tare da fa'din " Hello".
Cikin sanyi..cuz duk yanzu Husnah tayi sanyi kamar ba ita ba.


Yah Deen kuwa shiru yayi bai ce komai ba illah murmushin mugunta da yake saki daga 'dayan 6angaren.." Hello"!!
Ta sake fa'di akaro na biyu tana yatsina fuska amma still shiru bai amsa ba.

'Dan 'karamin tsaki taja da niyyar yanke 'kiran dan ganin kamar ba'a da alamun furta komai  wanda jin zata yanke wayar yasa Yah Deen saurin ambatan sunan ta cikin muryar da ya san zai sanyatar mata da zuciya.

Ai kuwa cak ta fasa abinda tayi niyyar yi zuciyar ta take ya fara dokawa abinku da zafin 'kauna...sai dai bata iya ta ce da shi ko 'kala ba.

Cikin wata mayaudariyar muryar ya sake fa'din" Husnah ashe kin dawo shine kika 'ki neme ni ko?..Husnah har haka na zama a wurin ki ban sani ba?"

" Meyasa sai ka sani to?"
Tayi 'karfin halin furta hakan.
Sai yace" Haba Husna..."
Saurin tarar sa tayi da fa'din" Malam matsayin matar aure nake yanzu...."

" Na sani Husnah bacsai kin tuna min ba.."

" So ka fita hanya ta please ka daina damuna.."

" Husnah ni ne fa? ko kin manta badan wani 'dan dalili ba da nine mijin naki a yanzu.."

Cike da takaici ta cire wayar a kunnan ta tana jan tsaki.

Yah Deen kam da murmushi yabi wayar sa dake ri'ke a hannun sa jin yanda ta yanke masa 'kirara a zafafe...shi kansa yasan ya cancanci fiye da haka daga gareta saboda sam bai mata adalci ba a rayuwar ta.

Sam maganar auren dake kantan bai dame shi ba dan yasan shi ka'dai take so, shiyasa ma shai'dan ke 'kara ingiza shi akanta yana sake tunzura zuciyar sa akan sake mallakar jikinta cikin ko wani irin hali.

Text ya rubuta ya tura mata
_"..Ina fatan baki manta abinda yafaru a Azare ba.."_

Yayi zaman kusan mintina ashirin da uku yana jiran reply amma har a lokacin shiru baiga komai ba.

Yanzu kam yasan Husnah gagarumin fushi tayi da shi tunda har ta iya masa wannan wulan'kncin.

Cikin ransa ya ayyana zai share ta tukunna na kwana biyu yagani..sai dai me?
Kafin cikar mintina talatin sai ga text 'din Husnah ya ratso cikin wayar sa, wanda da ganin hakan ya saki murmushi a fili ya furta" ai nasan hali..yarinya indai zaki kulani ko yayane ai shikenan..".

Text 'din ya bu'de ya karanta abinda ta turo
_" Me yasa zan manta abinda ya faru ai ba ma su da dalilin mantuwa, 'kyamar da ka nuna min zan manta ko kuwa yaudara da muguntar da ka shirya min?"_
Take shima ya rubuta amsa kamar haka.." _Please pick my call Husnah_ ".
Ya tura mata haka ya sake dialling numbern ta.

Kamar bazata 'dauka ba amma sai gashi ta 'dauki 'kiran daf da zai yanke.

Shiru tayi yayin da Yah Deen ya cigaba da fa'din
" Kina jina ko...Husnah wannan duk sun faru a can baya ne, amma daga baya da kaina naga rashin kyautawa ta,  lokacin da na gama saka saka rai na sakankance zan mallake ki kuma a dai-dai lokacin mahaifan ki suka yi betraying iyaye na...nasan kin san komai so ba sai sake gaya miki ba....Husnah hankali na ya tashi sosai da naji labarin auren ki da wani daban ba ni ba ban san cewa kece zuciya ta ba sai a lokacin da naga alamun rasa ki zanyi,  amma is too late dole na 'dau dangana tunda an riga an aura masa ke, nayi tunanin zaki 'kira ni kimin bayani da kanki amma ke ma sai naji ki shiru..bazan iya misalta miki halin da na shiga sanadin hakan ba..all I can say is nayi takaicin rasa ki..please ki sassauta min Husnah.. "

" Ni babu wani sassauci da ya rage tsakani na da kai cuz matar aure nake yanzu so ka fita hanya ta, ko ka manta cewa da bakin ka ka sanar dani baka 'kaunar aure tsakanina da kai, ka 'kira ni da dattin bola Mu'een da bakin ka, cikin hankalin ka ka nuna min tsana ta zahiri to dan Allah ya musanya min kai da wani kuma me yasa zan damu har ince zan 'kira ka in ma bayani...?"

" Husnah..!"
" Ni dai please ka fita hanya ta..kar ka sake 'kira na"

Tanacgama fa'din hakan ta yanke 'kiran tana tsiyayar da hawaye...ta san har abada bazata ta6a daina son Mu'een ba, amma yaza tayi dole ta 'dauki hakan matsayin kaddarar rayuwar ta.

Ta so ace da kanta cire shi a ranta musamman saboda ba'kin halin da ya nuna mata, amma ga dukkan alamu hakan ba me yiyuwa bane still zuciyar ta na nan tarecda shi...fatan ta kawai shine Allah ubangiji ya bata ha'kurin zama da mijinta.


'Bangaren Yah Deen kuwa sam bai wani damu ba...ya riga ya 'kudura cikin ransa cewa zai dawo da Husnah cikin rayuwar sa kuma sai hakan ya faru.







Comment
Vote
Share






*Salmerh ce* 😍
💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)


By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *56*

'Bangaren Yah Deen kuwa sam bai wani damu ba...ya riga ya 'kudura cikin ransa cewa zai dawo da Husnah cikin rayuwar sa kuma sai hakan ya faru no matter what.


Haka suka cigaba da rayuwa bai sake 'kiran layin ta ba kuma ko cikin school ma ba kullum suke ha'duwa ba saboda 6angare daban-daban suke..duk kuwa ranar da ha'duwar su ta kasance yakan bi tane da idanu kawai fuskar sa 'dauke da yalwataccen murmushi, musamman idan yaga irin shigar da tayi...cuz yanzu Husnah babban mayafi take sawa harda safa a'kafafun ta, wanda duk hakan ya kasance ne cikin dokar da Hisham ya gindaya mata, sai kuma akayi sa'a itama shigar ta kwanta mata sosai take jin da'din sa dan haka kuwa ba tare da damuwar komai take 'ko'karin bin umarnin sa duk da basa tare.


Bata ta6a tunanin komawa rayuwa da Mu'een ba tunda tayi aure...har wasu lokutan ma da kanta take ganin tsabar wautar da ta tafka abaya na biye masa suka ta aikata son ransu.

A kullum soyayyar sa na ma'kale da zuciyar ta amma tayi 'ko'kari sosai wajen ganin ta danne hakan, shiyasa ma ko sun ha'du cikin school bata yi masa kallo sau biyu, sau tari ma ta kan ga kamar ha'duwar tasu shiryayya ce kawai dan ya ringa bayyanar da kansa gare ta a lokutan da bata zato saboda kawai ya ringa tunatar da ita wanzuwar sa cewa still yana nan karta manta.

Ko 6angaren shi Mu'een 'din ma kuwa bai ta6a gigin sanar da su Ishaq cewa yana so ya dawo da Husnah cikin  rayuwar sa ba, ya bar hakan ne kawai cikin ransa dan gudun mitar Ishaq kuma yasan matu'kar Ishaq yasan hakan birki zai taka masa...ba zai barshi ba.


A kullum tunanin sa bai wuce taya zai sake mallakar ta ba..duk wani hanya da yayi tunanin zai 6ulle masa sai kuma yaga abin ba haka ba saboda Husnah duk ta canza yanzu kamar ba ita ba...kwata-kwata ta 'dauke masa wuta, bai ta6a tunanin Husnah zata iya yi guje masa cikin lokaci 'kan'kani haka ba...shiyasa sau da dama ya kan tsinci kansa dumu-dumu da jin haushin mijin da ke auren ta a yanzu dan yasan shine sanadin rabuwar su....(ni kwa nace ka manta Addu'ahr da ka ringa yi abaya kenan?)

Kwatsam ranar yana gida dawowar sa kenan daga lecture sai yaji 'karan wayar sa, ko da ya 'daga sai yaga sunan Ishaq na yawo kan fuskar wayar, batare da damuwar komai ba ya 'daga nan Ishaq ke tambayar sa wai ko yana gida ya bashi amsa da" erh yana nan".
A takaice.

" Gamu nan zuwa to yanzu".
Fa'din Ishaq daga 'daya 6angaren.
Mu'een sai yace
" Kun fasa fitan ne kuma?"
" Ah no bamu fasa ba... ai ba zama zanyi ba yanzu zan koma".
" Ok sai kazo to".

Da haka suka yi sallama kowa ya ajiye wayar sannan ya ci gaba da abinda yake yi ba tare ya ko yi tunanin me ze kawo Ishaq wurin sa a dai-dai wannan lokacin ba tunda yasan basu da'de da rabuwa ba kuma kafin rabuwar su bai sanar da shi cewa zai zo ba.


Yana zaune a wurin yaji sallamar Ishaq daga bakin parlourn sa sai ya amsa a hankali tamkar bai son yin magana kamar yadda ya saba yin komin sa cikin ra'ayi.

Ishaq ne ya fara shigowa kamar daga sama sai ga Husnah a bayan sa ta sha Hijabin ta ash colour wanda yake babba har 'kasa ya kuwa yi mata kyau ta fito shar abinta gwanin birgewa.

Kallo 'daya tayi masa ta 'dauke idanun ta daga kansa...kishingi'de yake har yanzun bai motsa ba sai ma yayi kamar ganin su taren bai sa yaji wani abu makamancin mamaki ba.

Ishaq ne ya zauna daga gefen sa tare da bashi hannu sannan a takaice yayi mai bayanin abinda ya kawo su cewar Husnah ce ta same shi da batun ya rako ta zata 'dauki wasu kayayyaki agidan shiyasa ya rakota amma shi yanzu haka ma ana jiran sa zai koma...bai kai ga rufe bakin sa bama wayar sa ta fara ringing sai ya mi'ke tsaye yana ciro wayar daga aljihun sa yake fa'din ai basu san nan na taho ba.
Saurin 'kara wayar yayi a kunnan sa yana fa'din" Gani nan tahowa yanzu Anas..".

Hanyar fita daga parlourn ya tunkara yana sake fa'din"

Please Login or Register in order to submit comment