Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba".


Tana maganar ne tare da lalu6an abin shafa daga cikin jakar da suka zo da ita.

" Shine kuma kika dawo haka dan har yanzu bai 'karasa gidan ba? Miye abin damuwa a ciki? Mu'inuddeen ai ba ba'ko ko kuma yaro, 'dan gari ne fa .....kuma kin san shi da sabgogi...... ni fa har kin firgita ni wallahi da na ganki"
Ummah ta 'karasa maganar tata da 'dan sakin fuska.


Tunowa da tayi cewar man sha fan baya cikin jakar ne ya sanya ta sakin 'dan 'karamin tsaki a hankali.

Zipping jakar tayi sannan ta mi'ka hannu ta 'dauko mai 'din kuma sai a lokacin ne ta bawa Ummah amsar ta da fa'din " sabgogin mene da shi Ummah yanzu bacin duk abokan hul'dar tasa basa nan".

" kede ki bi a hankali uwata, ki daina sanya damuwa a ranki bisa wasu dalilai na daban marasa amfani da ma'ana, idan kince haka zaki cigaba da yi wallahi zaki sha wahala arayuwar nan.... hmm Allah kiyaye dai".
Ummah ta 'karasa da fa'din hakan tare da komawa ta kishingi'da abinta kamar 'dazun.


Noor kuwa har ta kammala da shafa mai 'din ta 'dauko kayan baccin ta sanya bata furta komai ga Ummah ba.


Mi'kewa tayi a gadon batare da ta 'kara fa'din komai ba cuz abinda Ummah take tunani daban yake da abinda ke tsakanin ta da Deen, ita kuwa tana ganin ba abin sanar wa haka ga kowa bane shiyasa kawai tayi shiru duk da kuwa ta fahimci Ummah kamar na ganin kishi take yi, duk da kuwa a yanda tasan halin sa ko da ace kishin ne a ranta to ba laifi ne amma ma bata sanyawa ranta faruwar wani abu daban ba a wannan lokacin, sam babu hakan cikin ranta a, dana sanin rashin 'kin amince masa ma takeyi duk da kuwa har a lokacin tana nan a kan bakan ta na farko, amma yanayin da taji yake magana ka'dai ma ya fi sanyata damuwa dan tasan babu mamaki fama yake da kansa akan 'kin amince masa da tayi.


Shiru ne ya 'dan biyo baya na wasu 'yan lokuta kowa da abinda yake sa'kwa cikin ransa, Ummah ce ta sake fa'din " ni kuwa ya jikin mijin naki fatan dai yanzu ciwon yayi sau'ki ?"

Sai da ta 'dan mi'kar da hannayan ta ta kuma lumshe idanu kafin tace " da sau'ki sosai sai godiya gaskiya, dan har ma na manta rabon da ya tashi masa....ina jin dai an dace ciwon ya tafi".

Ummah cewa tayi
" masha Allah, Allah ya 'kara lafiya da nisan kwana".


Da "Ameen Ameen " Noor ta amsa mata daga nan bata 'kara magana ba har bacci yayi gaba da ita.


*****
'Bangaren Deen kuwa da 'kyar ya samu zafin 'kirjin ya ragu masa inda ya lalla6a a 'dan ran'kwafe ya samu ya fita daga motar yaje ya bu'de gate 'din tare da jan motar ya shigar ciki.


Yanayin yanda yake tafiya idan ka ganshi har zakayi zaton cikin halin maye yake tsaban yanda yake tafiyar cikin rangaji shi ciwon da cikin sa keyi ne kawai ya dame sa.


Koda ya isa 'kofar parlourn ma sai da yayi 'ko'kari ya seta komai nasa, tafiyar sa da muryar sa ya daidaita ta yanda iyayen nasa ba zasu fahimci yanayin da yake ciki da wuri ba, amma a zahiri kallo 'daya zaka yi masa ka fahimci ba dai-dai yake ba musamman idan kayi duba da cikin idanun sa yanda suka riki'de zuwa ja suka kuma 'kan'kance, shi kansa ya san hakan amma bai damu ba saboda dare ne yasan gane hakan zai matu'kar yi musu wahalan gaske


Ciki-ciki yayi sallama yana daga wajen, jin an amsa shi ne yasa shi 'dago 'kafar sa ya shigo.

"Ka dawo ?"
Alhaji Baba ya tambaye sa sai ya amsa da " umm na dawo Alhaji"
A takaice.

Hanyar 'dakin sa ya nufa tare da furta "sai da safe Alhaji...."bai jira yaji nashi amsar ba ya 'kara fa'din" Ammee mu kwana lafiya".


"Zonan Deeni meke damun ka ne wai?"
Alhaji ne yayi wannan tambayar dan tun a muryar da yayi sallama Alhaji Baba ya gane ba lafiya ba.

Cak Deen ya tsaya da jin muryar Alhajin tare da 'dan juya idanu ya lumshe su ya kuma bu'dewa ba tare da yayi niyyan fa'din komai ba.


Alhaji ne ya sake fa'din" da kai nake magana ko?"


" Baba 'kirji na ke min zafi amma ba wata matsala bace, zan sha magani yanzu idan na shiga".
Ya bashi amsa da fa'din hakan dan hakan ka'dai zai iya furtawa ya kare kanshi batare da sun 'dago damuwar sa ba.

"Subhanallah"
Ammee ta ce cikin damuwa tare da tasowa ta nufo inda yake" me yaja hakan ?
Me yafaru bayan fitan naka ko dama haka yake yima kullum?"
Ammee ce ke jero masa wa'dan nan tambayoyin cikin tashin hankali.


Girgiza mata kai yayi a hankali tare da fa'din" Kar ki 'daga hankalin ki please Ammee, ba abin damuwa bane zai daina ne, bari inje insha magani yanzu".

"Wani irin kar in damu Mu'een ka ga idanun ka kuwa....?"


Bata gama kai aya ba ya tare ta da fa'din" idanu na bacci nake ji sosai ne shiyasa.......let me go nd take mu drugs.....okay".
Yayi maganar tare da 'ko'karin wucewa 'dakin sa.

" To Allah ya sawwa'ka" Alhaji ya fa'di yana daga inda yake zaunen cuz shi bai taso ba daman, batare da ya sake yun'kurin jefa masa wata tambayar ba ya barshi ya wuce 'din kamar yanda ya bu'kata.


Deen 'dakin sa na da dake gidan ya wuce, sai da ya shiga bathroom ya watso ruwa inda ya ya 'dauki tsawon lokaci kafin ya fito sai yayi kwanciyar sa a kan gado daya ke yanzu ma ya 'dan rage jin abinda yake ji 'din sai 'dan abinda ba'a rasa ba..... ba dai kamar 'dazun ba, amma duk da haka zuciyar shi bata hana shi lalu6o wayar sa yayi dialling wata number ba tare da lafewa sosai kan gadon.
(Kuyi ha'kuri fa dan nima banga sunan ba ballantana in fa'da muku).


Ammee sosai ta so 'daga hankalin ta da jin cewar 'kirjin Deen na ciwo, tsoro take yi kar ciwon zuciyar sa ne ke shirin motsawa.
Haka ta zauna ta dafe kanta, gaba 'daya ta nemi natsuwar ranta ta rasa shi.


Alhaji Baba ke kwantar mata da hankali akan kar ta damu ba abu mai tsanani bane tunda ma gashi ai da kansa ya shigo gidan.
Taso ta je ta sake duba shi bayan shigar tasa amma sai Alhaji ya hana ta da cewar " koma meke damun sa ai a yanzu ba zai so a dame sa ba ta bar shi kawai zuwa safiya in da rai komai zai dai-dai ta".


Haka Ammee ta ta ha'kura ba dan taso ba ta tafi ta kwanta.

Alhaji Baba kam anan ta bar shi yana zaune tsawon lokaci yana tunani, shi kansa fa abin ya dame sa kawai ya danne ne a zuciyar sa.
Sai daya kusan raba dare a nan palourn sannan ya tashi ya 'karasa 'dakin Deen 'din, a hankali ya tura 'kofar inda ya same shi kwance jikin sa ba ko riga sai dai dogon wando kawai na bacci da ya sanya.
Hannun sa duka biyu dafe da cikin sa yana kwance rigingine.
Duk kuwa da cewa bacci yake yi amma zaka ga goshin sa a tattare, kallo 'daya zaka masa ka fahimci cewa ba'a yanayi mai da'di yayi baccin ba.


Alhaji Baba kai ya jijjiga ganin yanayin Deen 'din, domin a fili yanayin sa ya fallasa asirin zuciyar sa, Alhaji Baba bai sha wani wahalar gane 'karyar da Deen ya sharara ba na cewa 'kirjin sa ne ke ciwo, amma dubi yanda ya dafe cikin sa.
Godiya ya jerowa mahallici Alhamdulillah har sau uku, da kuma fatan Allah yasa ba zuciyar bace da gaske, idan ya kasance hakan kuwa zai matu'kar jin da'di.


Jijjiga kai Alhaji Baba yayi tare da fa'din " Allah ya shirya min kai Mu'een Allah ya yafe mana kura-kuran mu gaba 'daya".(AMEEEN).


*****
" Daddy ina Mummy na?"

Jasmine dake tsaye daga bakin gadon da yake kwance ta tambaye sa hannun ta kan sa tana wasa da suman kansa, fuskar sa na 'daya gefen daya ke yana cikin baccin yaji hannun nata a kansa wanda sanadin hakan ne ma yasa shi farkawa.


A hankali ya juyo ya tsura mata idanu yana kallon ta cikin kyakkyawan shirin ta da yasan aikin Ammee ne a yau 'din, sosai yake son 'yar tasa da dukkan zuciyar sa, ba'kin cikin ta sam baya fatan gani har 'karshen rayuwar sa, buri, 'kauna da soyayyar sa kaf a kanta suka 'kare, zaka ga walwalar sa koda kuwa waye kai matu'kar ka sanya Jasmine cikin farin ciki.
Juyi yayi tare da 'dan yin mi'ka ka'dan, hannun sa ya kai yaja hancin ta yana murmushi yace " baki gaida ni ba kike tambayar mummyn ki ko?"

Kafin ma ya rufe bakin sa tayi gaggawan fa'din
"Ina kwana Daddy...." batare da ta jira amsa ba ta 'kara da fa'din" ai na gaida Baba Alhaji ma da Ammee, Baba Alhaji ya bani dabino da zam-zam".


"Iyeh Baby na ta dawo 'yar gatan su Alhaji kenan.....wato dan haka ne yasa har kika manta ki gaida ni ko?"

Jas jijjiga kanta tayi tare da fa'din " ah ah ai jan gaishe ka har da Mummy na ma".


" Mummyn naki ai bata nan itama taje wajen maman ta".
Cewar Deen yana kallon ta.

" To Daddy ka kaini wurin ta ".
Jas ta fa'di cike da shagwa6a kamar ba itace me surutu yanzun ba.


Shiru Deen yayi kawai ya kauda idanun sa a kanta ya mayar gefe yana tunanin yanda zaiyi da ita.
D'ayan wayar sa da ya kalla ne a gefen gadon yasa shi mi'ka hannu ya 'dauko ta, dialling numbern Noor yayi tare da 'kurawa wayar idanu, sai yanzu ma ya tuno abinda ya faru jiya, sam bai ga laifin ta ba domin ya san laifin sa ne gaba d'aya, amma me yasa itan bazata iya yi masa uzuri na rana 'daya ba?"

Noor kuwa fitowan ta kenan daga wanka daya ke tasan yau zasu koma kuma da wuri zasu tafi cuz idan sun koma Deen ma zai wuce Abuja duk a yau 'din, so shiyasa take 'ko'karin shiryawa da wuri dan kar su rigata shiri.


'Karan wayar ta da taji ne yasa hankalin ta ya koma can, tana ganin sunan Deen sai tayi saurin danna receive don dama tun jiya ta kwana da shi a cikin ranta.


Sassanyan muryar ta da yaji tana sallama cikin wayar ne yasa shi lumshe idanu " Barka da safiya Yah Deen".
Ta 'kara fa'di bayan sallamar daga 'dayan 6angaren.


Bai amsa mata ba sai yayi saurin mi'kawa Jas wayar shi kuma ya tashi ya shige bayi kamar an tsikare shi.


" Mummy".
Jas tace tana turo baki.

Ajiyan zuciya Noor ta sau'ke tare da fa'din
" Na'am Mamana ke ce?"

" Umm "
Jas ma tace a takaice.
Sai Noor ta sake fa'din " Ya a kayi baby kina lafiya ko? ina Daddy?"


"Yana bathroom".
Jas ta bata amsar 'daya daga cikin tambayoyin nata wanda taga zata iya badawa.

Noor murmushi ta saki a 'dayan 6angaren, tasan ba mamaki Deen fushi yake yi da ita, shiyasa ya shige bayi bayan ya ha'da Jasmine da wayar tunda ai tasan Jas ba iya 'kira zatayi da kanta ba dole sai an mata.


" Mummy ni zan zo gurin ki.....".
Da taji Jasmine na fa'di ne ya sanya ta yanke tunanin da take yi da kulawa tace da ita.
" me kika ce Baby ban jiki da kyau ba".

" Ni gurin ki nake so Mummy".
Jas ta sake maimaitawa a sakalce.

Murmushi Noor tayi tace
" Ai baki ko gaishe ni ba dan haka babu gurina da zaki zo nima ba ruwana".

" sorry Mummy, good morning".

" Yauwa my princess....ko ke fa, hope kowa na lafiya?"

"Ehh har da nima Mummy, Ammee ta min wanka ta samin turare a jikina".

"Ahh masha Allah ashe yarinya ta tayi kyau sosai ko?"

Jas washe 'yan ha'kwaran ta tayi na jin da'din maganar.

Noor sai tace " kin zama 'yar gatan Ammee kenan".

" Harda Baba Alhaji ma ai shima ya bani zuma da zam-zam da dabino na ci".

" iyeh....duka ke ka'dai mamana, gaskiya Alhaji ya kyauta, me kika ce masa to".
Noor ta 'karashe da tambaya sai Jas tayi saurin fa'din" nace masa nagode".


"Yauwa Babyn Mummy, May Allah's blessing be with you....hum".


Deen da fitowar sa kenan daga bathroom 'din kunnuwan sa suka jiyo addu'ar Noor, a saman la66an sa ya amsa da " Ameen summah Ameen".


Noor kuwa sai tace da Jas 'din" bari nima in shirya ko sai ki jirani zan zo kinji.... sai mu koma gidan mu ko ba kya so?"

A hankali Jas ta amsa da " inaso".

" Yauwa Baby bye"
Daga haka ta yanke 'kiran tare da cigaba da shirin ta.




*****
Lokacin da yaje 'dauko Noor a gida tare da Jasmine suka tafi, kuma ga mamakin Noor sai taga fuskar sa wasai a sake ba kamar yadda ta tsammaci ganin sa ba, cuz tayi tunanin zai yi fushi da ita ne tunda har ya kashe wayar sa jiya suna cikin magana.


Sosai taji da'din hakan da yayin har take jinjinawa wannan ranar mai tattare da sa'a a gareta, da har tayi masa laifi amma bai 6ata ransa ba.


Sallama yayi wa Ummah suka fito a tare dukkan su da Jas bayan Ummah ta cika su da tsaraba irin nasu, da tulin dabino, Ummie ce ta fito musu da shi aka sanya bayan mota.


Haka suka rabu da Ummah cikin farin ciki tana tsokanar Jasmine wai tsohuwa mai sunan flower, Jas kuwa tace ita ba mai sunan flower ba ce ita mai sunan maman Daddy ce".


Dariya suka 'dan yi kafin Ummah ta bisu da Addu'ahn sau'ka lafiya.


Ko cikin motan ma Noor shiru tayi fuskar ta cike da annuri, har kwantar da kanta tayi jikin kujera tana murmushi ita ka'dai.


Haka har suka isa gidan Alhaji Baba basuyi wani dogon magana ba tsakanin su, nan ma dukkan su suka shiga cikin gidan, Noor ta gaida in-laws 'din nata tare da yi musu sallamar tafiya.


Alhaji Baba bai bar su sun tafi ba har sai da ya 'kara jan hankalin su sosai a kan rayuwar duniya da kuma ha'kuri da juna cikin zamantakewar su.


Ammee ma sai da ta 'kara da nata kamar wasu sabbin aure su Alhaji basa gajiya da sake tunatar musu da muhimmancin kasancewar su a tare da junan su.


Daga 'karshe Ammee tace da Deen dan Allah ya daina wasa da shan maganin sa dan jiyan nan sosai ya so 'daga mata hankali dan ma Allah yasa ciwon bai yi tsanani ba.


Murmushi Deen yayi yace da ita " kar ki damu Ammee na insha Allahu ina nan araye har sai kingan ni cikin jikokina nima".


Murmushi sukayi dukkan su Ammee kuwa tace " ja'iri kakar ka ka mai dani ko?".


Basu 'kara 6ata wani dogon lokaci ba suka 'dauki hanyar Bauchi, Noor kam da'di take ji har cikin ranta, lokaci-lokaci ta kan tsura masa idanu sai kuma ta 'dauke, ba'a 'daukan lokaci kuma sai ta sake.
Sosai yake bata mamaki musamman da taji bai tado maganar jiya ba ya share tamkar babu abinda ya faru.

Deen kam kasa ha'kuri yayi da kallon har sai da ya tambayi dalili shima 'din fuskar sa a sake wasai yayi tambayar .


Tana jin ya tambayi dalilin kallon tamkar dama jira take yi sai ta juyo da kyau ta fuskance shi sannan tace " wai jiyan nan me ya sami wayar ka ne Yah Deen muna cikin magana naji ta yanke ko dana sake 'kira kuma bai shiga ba.....miye dalili".


Shi kam ma sai a lokacin ya tuna da batun wayar tasa dake jefe cikin motar, bai ce da ita komai ba sai da ya 'dauko wayar kafin yace " kin ganta ma ni ai sam na manta da ita, tun jiyan tana mota ina jin ba caji ne shiyasa".


Shiru tayi bata sake yin wata magana ba, tasan dai ba rashin caji bane ya sanya hakan, in ma rashin cajin ne ai kuma ba zai kasance ya bar wayar jefe a mota ba.
Sai dai bata tsawaita tunanin a ranta ba, duk kuwa da cewa tana da ya'kinin akwai wani dalili 6oye bayan wannan amma tunda kam shima 'din be nuna mata 6acin ransa ba ai shikenan.


Batayi mamaki ba lokacin da ya jona wayar a caji sai taga yana da kimanin 50% na caji a ciki, kauda kanta tayi tamkar bata gani ba ta koma kallon gefen hanya.


Kafin su isa kuwa aka ringa 'kiran Deen kan wani emergency aikin da ya taso dole tasa suna sau'ka ko hutawa bai yi ba sallahr azahar ka'dai yayi sai ya fito da shirin tafiya da jakar sa ka'dai a kafa'dan sa da yake motar kasuwa zai bi bai taho da mota ba san da zai zo.
_sai fatan Allah ya sau'ki Mu'een lafiya......Ameeen_




*****
Jikin mahaifin Sani yayi tsanani sosai, cuz a lokacin da aka kai shi asbitin ma ko gane ahalin sa bai yi illah sunan Sani da yake iya furtawa a hankali.


Gashi dama yana da hawan jini tun a baya sai kuma wannan ciwon da ya 'kara sako shi a gaba.
Da farko duk sun raina ciwon domin ganin kamar abin bana kirki bane sai babu wanda ya damu, amma tashin farko da ya gigita shi da azaba 'kafar sai take 'kara 'kumburi ga shi baya iya bacci koda dare ne.
Dole tasa suka kaishi wani asbiti dake cikin garin Jos.
Ko a asbitin ma ansha fama dashi kusan wata guda amma abin ba sau'ki sai an 'daga shi an kuma kwantar, daga 'karshe sai suka tattara shi zuwa gida domin a gwada yi masa na gargajiya.


Alhamdulillah kuwa ba laifi,sai aka dace domin kumburin 'kafar tasa ya ragu sosai ba kamar da da yake girma kullum ba.
Sai dai bakin da ciwon ya sanya ne yake sake bu'duwa amma shima suna 'ko'karin sanya masa maganin da aka basu a kullum.


Ganin kamar an 'dauko hanyar warkewa ne ya sanya Sani fara haramar komawa Bauchi bakin aikin sa, amma sai mahaifiyar sa ta taka masa birki.
Domin kuwa shi ka'dai ne 'dansu namiji da Allah ya basu a gidan gaba 'daya, 'yan uwan sa kaf mata ne, kuma duk suna gidan mazajen su, mahaifin nasa kuwa komai sai an taimaka masa kama daga wanka, bawali, alwala sallar ma kanta da sauran su.
Abinci ne ka'dai yake iya kaiwa baki da kansa yaci ya sha ruwa baya ga haka kuwa ba iya yin komai.

Sani dole ba dan ya soba ya sake wani zaman dan kulawa da mahaifin nasa.



*****
'Bangaren makarantar Jasmine kuwa Noor ce taci gaba da kaita makaranta tana kuma 'dauko ta har sukayi exams suka kar6i hutu, daga nan ne sai take barin ta a gida suna zama da Hauwa ita ta tafi nata makarantar ta dawo, dan su ma 'din jarabawar suke yi a halin yanzun so bata wani jimawa take dawowa gida.


Rayuwar su a kullum dai-dai take tafiya musu basu da matsalar komai, sai 'dan abinda ba'a rasa ba saboda halin rayuwa.


Lokacin da hutun Jasmine ya 'kare a lokacin kuma Noor ta fara nata hutun dan haka sai taci gaba da kaita makarantar da kanta kamar baya.


Bata ta6a gajiya ko 'kosawa da hakan ba, bata san me yasa ba amma haka kawai sai tafi jin da'din hakan, tafi jin natsuwa da kai Jasmine tana kuma 'dauko abinta.


Deen ma na 'ko'karin zuwa yana duba su duk bayan 2-3weeks baya ta6a wuce hakan batare da yazo Bauchi ba.
Idan yazo yayi weekend 'din sa sai ya koma Abuja.


Sha'kuwar sa da 'yar sa kuwa babu abinda ya ragu sai ma gaba domin kuwa koda baya gida ma toh kullum sai sunyi waya dashi kusan sau hu'du ko uku a rana.


Zaku yi mamakin irin masifaffen son da yake yiwa Jasmine 'din tamkar wanda akace masa ita ce 'daya k'wal 'kwansa a duniya gaba 'daya, yanzun ko bacci Jas bata yi sai taji muryar Deen, shima d'in da yake yasan abinsa to baya ta6a tsallake lokaci in dai bada wani 'kwa'k'kwaran dalili ba.
8:o clock bata gotawa batare da 'kiran sa ya shigo wayar Noor ba, haka zasu yi ta hira abinsu har sai bacci ya 'dauke ta kafin nan, wani sa'in ma shine yake karanto mata addu'o'in bacci awayar idan ya fa'da itama ta maimaita har su kammala gaba 'daya, a kullum 'karshen maganar sa da Jas shine " I love you Diamond 'din Daddy"

Itama sai tace " i love you Daddy".


Noor kuwa sai dai ta zama 'yar kallo da sauraren su, sau tari tagumi take yi ta zubawa Jas idanu tana kallon ta idan suna wayar, gani take yi da ace Deen ne yayi jigilar rainon cikin Jasmine tare da haihuwar ta da bata san abinda kuma zai aikata ba a rayuwar Jas tsabar so.
Zuwa yanzun baya bata mamaki sai dai kawai tana matu'kar jinjina masa afili da zuciyar ta.

A kullum sai bayan ya gama da Jasmine kafin nata turn 'din yake yi, wanda itan ma ba laifi Deen yana matu'kar 'ko'kari wajen ganin ya bata isassan lokacin sa a wayar, sosai yake nuna mata zallan son da yake mata tare da kewar ta a kusa da shi.


Haka rayuwar su taci gaba da tafiya da da'di ba da'di har aka kafe result 'din su Noor inda cikin rashin sa'a tafita da carryover har guda uku.


Ita da kanta batayi mamaki ba, dan tasan dama da yaya ma take iya karatun, bata kasance cikin 'dalibai masu haza'ka sosai ba.... ba kuma za'a ce da ita doluwa ba, tana nan ne a tsakiya tana lalla6awa and ta 'kara ha'dawa da rashin attending wasu lectures 'din, hatta test tayi missing har guda biyu ta dalilin 'dauko Jasmine daga makaranta, cuz bata tsayawa ta saurari komai matu'kar lokacin tashin Jas yayi to kuwa barin komai take yi tayi tafiyar ta.

Hakan bai ta6a damun ta ba, dan kuwa sama taka kawai ta tsinci kanta da son kaiwa da 'dauko y'ar ta ta da kanta batare da tunanin makomar nata karatun ba.


Hatta da Carryover 'din ma bai wani 'daga mata hankali sosai ba duk kuwa da cewa tana masifar son karatun amma farin cikin 'yar ta da walwalar ta yafiye mata komai.


Deen ne ma ya 'dan yi mamaki da yaji labarin dan kuwa last semester result 'din ta ba haka yake ba, batayi carrying ko wani course ba, tashi 'daya kuma wannan karan sai gata da 'yan rakiya har guda uku...... yaso yaji dalilin hakan amma sai ta nuna masa cewa ita kawai bata gane karatun ne yanzu sosai shiyasa.
Da kansa ya zurfafa tunani ya gano inda matsalar take, sai ya bari akan da hutun ta ya 'kare zai nemo wani driver 'din ya fara tafiya da Jas kafin Sani ya dawo, idan kuma ma ya dawo shikenan Alhamdulillah.




*****
Wasa-wasa har sai da Sani yayi wata uku cif bai dawo ba, sau 'daya Deen yaje duba mahaifin nasa daganan kuwa bai sake zuwa ba dan garin yayi lungu sosai gashi hanyar ba kyau ba gyara, akwai 'kura sosai hakan ya sanya bai 'kara sha'awar komawa ba.
Ya kan yawai ta 'kiran sa a waya su gaisa tare da jin ya jikin mahaifin nasa musamman ma saboda zaman tare, wani sa'in har ku'di yake aika masa tare da 'kara kwantar masa da hankali akan ya nutsu ya kula da mahaifin sa da kyau.
Ya kance da shi kar ya damu kansa a duk lokacin da ya samu daman dawowa Bauchi aikin sa na nan yana jiran sa.







Comment
Vote
Share





*Salmerh ce*๐Ÿ˜
[11/17/2019, 9:35 PM] ๐ŸŒธSalmerh๐ŸŒธ: ๐Ÿ’• *NOORUL* ๐Ÿ’•
(Haske nah)



By
*Salmerh MD*



*Wattpad @*
*Serlmerh-md*



๐Ÿ’ซ

Please Login or Register in order to submit comment