Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ganin 'kiran Ammi a wayar sa, zaton sa ko itan ta sau'ko ne dan Alhaji Baba ko sauraran sa be yi ba kafin ya tafi da suka je da Ishaq bashi ha'kuri.

Da farin cikin sa yayi sallama bayanvya 'daga 'kiran Ammi ko amsa shi bata yi ba kawai ta tsuke fuska tace" Meet me..".
Wani ras zuciyan sa ya tsinke tun daga kansa har tafin.'kafan sa yaji wani yir saboda gudun da jinin sa yayi a lokacin, ko daga jin yanayin muryar Ammi ka'dai ya san da akwai matsala babba.

Shi ka'dai ne kwance a 'dakin sa, cuz duk ba'kin sa da suka zo sun koma garuruwan su, dama kwance yake yana tunanin ta inda zai fara shawo kan iyayen sa su yafe masa, a ganin sa 6angaren Noor da sau'ki baya jin ta ita kamqr yanda yaga su Alhaji sun 'dau zafi kan maganar, shi ka'dai ya san me yake ji a zuciyar sa dan har a lokacin babu abinda ya canza daga ciwon dake damun sa a 'kirji gashi kuma ya'ki komawa asbiti balle ya samu kulawa, magungunan sa kawai ya cigaba da sha batare da ya koma an sake duba matsayar lafiyar tasa ba.

Tafiya ma ba ya iya mi'kewa idan zai yi ta kawai wani sa'in daurewa yake yi yana yi tamkar bai jin komai.
'Kiran da Ammin tayi masa sai ya sa shi jin wani ras a zuciyar sa da ya haddasa sabon yanayi, har jiri yake ji na kwasan sa dan yasan dole there must be something da shi bai sani ba.

A hankali ya mi'ke amma ganin idanun sa na barazanar daina gani ne ya sashi komawa da sauri ya zauna yana dafe kansa dake barazanar tarwatsewa, sara yake yi masa tamkar wanda ake buga abu akai idanun sa duk sunyi laushi ga jiri dake kwasan sa idan ya mi'ke.

Ya 'dauki tsawon sakanni a hakan kafin ya sake yun'kurawa ya tashi yana waro idanun sa da 'kyar, da dubara da bin bango ya samu ya isa parlour yana tanga'di tamkar 'dan maye.

Antyn sa Zainab na ganin sa tayi saurin mi'kewa cike da kulawa take tambayar sa me kuma ya same shi.

Batare da ya dubi fuskar ta ba yace" Kar ki damu Anty Bakomai, Ammi ce tayi 'kira na..."
Tun ma kafin ya rufe baki ta nuna masa 'dakin da Ammin ke ciki.

A hankali ya taka ya shiga 'dakin da sallamar sa, yayain da Anty Zee ta bishi da kallon tausayi, a 'dakin babu wanda ya amsa shi illah Ammi da ta amsa sallamar ciki-ciki ko sautin muryar ta ma bai ji sosai ba.

Idanun sa da su gani sosai in ya tsurawa Noor ganin yanda duk ta rame cikin sati guda kacal, koma me ya same ta yasan laifin sa ne, da idanu yake nuna alamun tausaya agare ta har da karkata wuyan sa gefe yana duban ta, amma Noor bata jira ganin hakan ba tayi saurin kawar da kanta gefe tana share siraran 'kwalla dake bin kuncin ta.

Mu'een be wani damu da hakan da tayin ba cuz yasan itama fushi take yi da shi, fatan sa Allah yasa Ammi sulhu zatai musu tunda yaga Noor zaune tana kuka 'kila ba'a son rqnta bane.
A hankali ya 'karasa gaban Ammi ya dur'kusa ya gaida ta muryar sa na sar'kewa, haka Ammi amsa shi a ta'kaice a fili zaka fahimci ba har zuciyqr ta take yi masa maganan ba saboda yanayin da take nunawa.

Hannu ta 'kai ta dauko memo da biro 'din da ta ajiye ta mi'ka masa batare da ta furta masa komai ba.

Deen da bai san manufar hakan ba sai bai yi musu ba yasa hannu ya kar6a yana mai duban fuskar ta da alamun neman 'karin bayani sam bai kawo faruwar wani abu mummuna cikin ransa ba.

Idanu Ammi ta lumshe cike da 'dacin zuciya, sosai take son Mu'een take ji da shi, take kuma 'kaunar ganin farin cikin sa akoda yaushe har a zuciyan ta take jin da'di a duk lokacin da ta fahimci yana tare da walwala, amma babu yadda zata yi halayyar sa yasa dole ne tayi abinda ya dace da shi ko da hakan na nufin tashin hankalin sa ne, ko  tilasta shi ne dole tayi ko dan gudun 'daukan alhaki ma.

Fes ta bu'de idanun ta akansa suka ha'da idanu a hankali cikin muryar natsuwa tace da shi"...Ina fatan da kanka ka shiryawa wannan ranar Mu'een? hope ka riga kasan mai zai biyo bayan cin amanar da ka jima kana yi mana...?"
Kallon Ammi yayi kawai yana mai jin nauyin abubuwan da suka ta yaudaran sa wurin mata har ya kasa tsaida hankalin sa wuri guda, ya kasa tsaida zuciyar sa da gangan jikin sa wurin matar da Allah da kansa ya za6a masa isa batare da wayo ko dabarar sa ba, sai dai har yanzu bai fahimci me Ammi take nufi da dam'ka masa littafi da al'kalami ba, bai san me zai yi da su ba sam.
       Sannan shi bai shiryawa faruwar komai ba hasali ma shi bai ta6a kawo faruwar wani abu makamancin hakan da ya riga ya faru cikin ahalin sa ba...sai dai maganganun Ammi sun masa karan tsaye, sosai hankalin sa ya kasu kashi-kashi ya shiga nemo ma'anar su, kuma har lokacin batun saki sam bai zo kansa ba...illah zuciyar sa dake faman lugude na tashin hankali.
Yanzu kam bai ga wani alamar sulhu da yake tunanin Ammi zata yi tsakanin sa da Noor ba...

A hankali ya sau'ke idanun sa kan littafin dake ri'ke a hannun sa yayin da Ammi ta cigaba da fa'din"...'Kauna da mutuntaka yasa aka 'dauki auren Hudah aka baka kasani Mu'een ba wai dan ka isa ba, amma kayi watsi da komai, ka bi son zuciyar ka baka damu da halin da na kusa da kai zai iya tsintan kansa ciki saboda damuwar ka ba, musamman ma iyalin ka, bansani ba ko dan kana ganin baka sha wahala kafin ka same ta bane shiyasa oho..cuz na tabbata da da kanka ka nemi auren ta bazaka dinga yi mata hakan ba, if zan tuna lokacin da ka fara jin.soyayyar Amina a zuciayr ka a lokacin kusan zaucewa kayi, ba mamaki da itama Noor in ka wahala wajen neman auren ta da bazaka yi mata irin wannan cin zarafin ba...sai dai ka sani idan baka son ta ni ina son kaya na, Mahaifiyar ta da dangin ta duk na son ta ba zai yiwu mu zuba maka idanu kana azabtar mana da zuciyar ta ba while tana da gatan ta, dubi yanda duk ta lalace kuma na tabbata duk damuwar ka ce ba komai ba, ni kaina nasan yarinyar nan tayi ha'kuri da kai matu'ka, tunda kuwa har aka zo wannan gandun nasani mai iya zama da kai sai yayi ha'kurin ya kai a buga misali da shi, a kulumm idan na tambayi yarinyar nuna min take babu matsalar komqi duk wai dan ta rufa maka asiri, ba'kin halin ka da rashin wayo bai sa ka fahimci rashin walwala da yarinyar nan ke ciki ba saboda ka 'dauki hankalin ka gaba 'daya ka dam'ka a hannun matan banza, da aure ka ce zaka yi Mu'een wallahi ko ni bazan hana ka ba, amma madadin.hakan bige da biye-biyen mata sai kace wani.bunsuru, kai ko.kunyar Allah ma baka ji? yarinyar nan koda wasa bata ta6a kawo min 'karar ka ba bata ta6a nuna min ko alama cewa bata jin da'din zama da kai ba, ta rufa maka asiri Mu'een wanda ko mu iyayen ka da muka haife ka iya ka rufin asirin da zamu iya yi maka kenan a wannan duniyan,  amma duk ka san hakan ka kuma yi watsi da shi ka cigaba da cutar da ita saboda son zuciyar ka.
Bazan hanaka ba, rayuwar ka ce, iya ka ta da kai a kullum in nuna maka cewa sa6on Allah kake yi ba bakomai ba, sai dai ko yanzun nasan ka fahimci cewa ba'a aikata Zina ya kuma tafi abanza, kayi ne kaina ka jira ranar faruwan naka..ai kaga misali 'daya, idan kuwa kace ba zaka bar 6ata yaran mutane ba haka kaina.zaka yi ta haifa ana  lalatawa...".
Da sauri ya 'dago ya dubi Ammi zuciyar sa cike da rauni...a ganin sa bai kamata Ammi ta fa'di hakan ba saboda ita Uwa ce agare shi...me yasa bazata banbance tuban sa na da da na yanzu ba, ji yake da ana iya bu'de zuciya da ya bu'de mysu yanda yake game da rayuwar sa na baya, sosai yayi nadama ta gaskiya baya jin akwai ranar da zai sake komawa wancan rayuwar har abada..yana cikin tunanin ya fara jin hawaye na tauruwa masa kuma still bai daina kallon Ammi..gani yake kamar zata iya karantar zuciyar sa a fuskar sa.

Idanun su sar'ke da juna Ammi ta cigaba da fa'din" Yes..i mean it..fa'dar Allah ce ba ni ba, kuma ko yanzun sai dai ince Alhamdulillah cuz i know zuwa yanzun da kanka kasani ba sai an sake maimaita maka ba, in da akwai dattako ma kai ne ya kamata ka zaunar da mutane kana yi musu nasiha akan irin hakan amma tunda ka za6i rayuwar jind'adi fiye da tsoron Allahn ka shikenan, kaje kayi tayi, ni nasan akwai ranar nadama tana tafe, domin ina da ya'kinin cewa har yanzun baka 'dauki darasi cikin abubuwan da suka faru ba, yau gashi kana ji kana gani babu Baby ta koma ga Ubangijin ta inda ta tafi da mummunan tabon da halayyar ka ya ja mata...akan hakan ka'dai ma bana jin har abada zan iya yafe maka Mu'een sam naji ka fice min arai na...nd bazan iya barin yarinya ta ta mutu da ciwon zuciya ta sanadin ka ba...ha'kurin ta ya riga ya kai ma'kura ta yanda ko ita da kanta ta nemi sake zama da kai ma bazan amince ba bazan barta tana gida zaman bautar aure kaje can gantalin ka ka kwaso mata wata cutar ba....i just want u to open this book now ka rubuta min sakin 'ya ta...".
Wani ras yaji a dukkan ilahirin jikin sa ya amsa, lumshe idanu yayi da 'karfi hawayen sa suka gangaro a fili ya furta Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'un... tunda Ammi ta fara magana sai yanzun hawayen sa ya gangaro.

Idanun sa ya bu'de ya zuba akan fuskar Ammi suka ha'da idanu...wanda ganin hawayen nasan bai sa ta fasa niyyar ta ba sai ma cigaba da tayi da fa'din" Ka sakar min.'yata sai ka je kayi ta jin da'din.rayuwar ka kai ka'dai, duk ranar ka tabbatar nadama ta shige ta gaskiya sai ka zo ka tabbatar min in gani.may be a lokacin zan iya yafe maka...but for now banda case da kai da kai bama na jin ka matsayin 'dan da ni na haifa..."
Zaro idanun sa yayi da kayu yana duban Ammi, harshen sa yaji yayi masa nauyi sosai, wai shi Ammi ke wa irirn wa'dannan mugun kalaman?

Ga Noor ya maida kallon sa sai yaga kanta ma kife yake kan cinyoyin ta  kuka take yi sosai har da sheshshe'ka....
Yun'kuri yayi da niyyan tashi ya isa gare ta sai Ammi ta dakatar da shi a tsawace.

Kallon fuskar ta yayi yana girgiza kansa wasu siraran hawaye na bin kuncin sa yayin da hannun sa 'daya ke dafe kan 'kirjin sa da yake jin tamkar zuciyar san fa'dowa zata yi bisa hannun sa.

Bai san me ze ce da Ammi ta yadda da shi ba, Noir ce ka'dai yake da tabbacin zata fahimce shi but yaga itama tana kuka.

Kallon Ammi ya sake yi 'kwalla na zubo masa masu zafi sosai...a hankali ya fara takawa ya  'karasa wurin ta wannan karon Ammi bata hana shi ba.

Kafa'dar ta yayi niyyan kamawa da niyyan ro'kon ta ta taya shi yiwa Ammi bayani ko zata fahimce shi da kyau fatan sa Allah yasa itama ta yafe masa su sake shimfi'da sabuwar rayuwa..." Cikin zuciyar sa yake wannan tunanin but bakin sa ya kasa furta komai..ji yake tamkar an tokare shine daga 'kirjin sa numfashin sa ma da 'kyar yake fita.

Ga mamakin sa sai yaga yana ta6a jikin Noor ta firgita tamkar an tsikare ta ta mike tsaye tana banka masa hararan ta6a mata jiki da yayi.

Murmushi Ammi tayi domin ba'karamin birge ta Noor tayi ba dama tasan hakan na iyq faruwa tunda ita ce da kanta ta nemi rabuwa da shi, shiyasa ma Ammi ta barshi ya isa garetan dan ya tabbatar wa kansa da kansa.

Shi kam cikin zuciyar sa yake furta" Ki yadda dani Nuree wallahi ni mai 'kaunar ki ne, bazan ta6a ha'da ki da wata cuta ba, soyayyar ki daban take a zuciya ta, ban ta kwatanta 'kaunar da nake yi miki da wata macen daban ba kuma har abada bana jin zan iya ha'da ki da wata, Deen 'din ki ne Yayan ki dan Allah ki bu'di ki wakilce ni wurin Ammi ki fahimtar da ita cewa nadamar gaskiya nayi, tayi ha'kuri kar ta raba ni dake na rasa Baby bana so.kema in rasa ki Nuree, ki ce min ta yafe min laifuka na Insha Allahu bazan sake 6ata mata rai ba har 'karshen rayuwa ta..."
He wish a fili ya iya furat hakan amma harshen ya kasa yi mai motsi duban ta kawai yake da idanu zafin zuciyar sa na 'karuwa.

..Gaban sa Ammi ta tako ta tsay nesa ka'dan da shi, hannun Noor ta ru'ko cikin nata ganin kallon da yake yiwa Noir ne ya sa Ammi nuna shi da 'dayan hannun tan sannan ta nuna inda littafin ke ajiye tace" Kai nake sauraro...".

Bisa gwiwoyin sa ya sulale yana hawaye ya dafe kansa da dukkan hannuwan sa biyu kuka yake yi mai matu'kar tsuma zuciya da 'kyar ya samu bakin sa ya bu'du ya furta" Haba Ammi!...ke xe fa kika haife ni, me yasa bazaki tausaya min ba, 'yata fa na rasa Ammi.kuma sannan.ki sake raba ni Noor ina zan sa kaina?".
" Inda ka saba sawa mana...".
Ta bashi amsa a hassale.
Bai damu ba ya cigaba da fa'din" Please! please ba dan ni ba, dan Ubangijin mu Ammi ki ji 'kaina ki bani wani chance, i promise u bazan sake yin wannan kuskiren ba, zan canza wallahi zan zame mata d best husband ever morethan u can imaging, nasan ban kyauta ba nasan nayi kuskure amma dan Allah ku yafe min Ammi i promise u bazan sake maimaita irin wancan rayuwar ba...Ammi ki tausaya min ki yadda da tuba na, believe me bazan miki 'karya ba.. wallahi ina son Matata, i luv Noor with all my heart that rabamu zai iya zame mana matsala Ammi, ki tambaye ta kiji ita kanta nasan..."
Hannu Ammi tayi saurin 'daga masa alamun ya isheta haka nan sannan tace" Kalaman kan nan 'kona ni suke yi Mu'een sam basu da amfani yanzu lokacin da ya kamata ka basu muhimmanci.watsi kayi da su, i don't care weather son mutuwa kake yi mata is alla useless tun da kayi wasa da damamma kin ka abaya...now komai ya wuce buri na kawai inga babu wata ala'ka tsakanin ka da 'yata, buri na inga bata tare da mutun irin ka, ka rubuta min abinda na bu'kata kawai yanzun nan..."
" Ammi ta ya kike tunanin zan iya rubuta wa Nuree saki da hannu na, matar da nasan idan na rasa ta tamkar rasa farin cikin rayuwa ta ne, Ammi Noor itace rufin asiri na, itace Hasken rayuwa ta, ada da kaina nayi al'kawarin zan bar rayuwan su saboda ta bu'kaci in daina zuwa inda take, nd nayi i promise zan bar su saboda su sami farin cikin rayuwa ita da Baby, but Ammi yanzu babu Baby, ta tafi...ina jin tausayin Noor sosai, sam bazan iya rabuwa da ita ba a wannan halin bacin nasan cikin 'kunci take ayanzu, Ammi ki fahimce ni ki bani daman gyara kuskire na, ta ya Noor zata samu wani  farin ciki bacin babu kowa tare da ita...?"
" Dan ubanka kuma sai akace maka kaine ka'dai farin cikin ta?..
Ammi ta jefa masa tambaya a hassale cike da 'kosawa da maganganun sa.
'Kasa yayi da idanun sa yana mai share hawayen fuskar sa da hannun sa 'daya tamkar yaro 'karami.
Ammi kam bata damu ba ta cigaba da fa'din" Ai koka'dan banga alamun tausayi tattare da kai ba, shekaru nawa kake tare da ita? kwanaki nawa ka 'dauka kana cutar min da ita? ko angaya ma bana damuwa da rashin ganin walwala a fuskar ta da banayi ne...ko dan kaga ban ta6a tuhumar ka akai ba ko?
Idan soyayyar da kake ikirarin kana yi mata na gaskiya ne to ka sakar min ita domin na tabbata rayuwa babu kai shine farin cikin Hudah na har abada...."
Zai yi magana tayi saurin taran sa da fa'din" Matu'kar kana so ka cigaba da rayuwa matsayin haifaffen 'dan halak to ka je ka 'dauki pen ka rubuta min sakin 'yata..."

Noor na jin Ammi ta fa'di hakan tayi saurin.matse hannun ta dake cikin.na Ammi, hawaye ne sosai yake zubo mata kan kuncin ta, bata so irin hakan ya dinga shiga tsakanin sa da iyayen sa amma ya zatayi? harga Allah bata jin zata sake jin da'din rayuwa tare da shi...burin ta ayanzu kawai shine taga bata 'karkashin inuwar auren sa.

A hankali Deen ya mi'ke  ya isa inda pen in yake ya dur'kusa hannun sa na rawa yana share hawaye yayi rubutu layi 'daya tak daga hakan ya mi'ke ya fice yana share hawaye bai ko sake kallon inda Ammi take ba balle Noor in.






Comment
Vote
Share





*Salmerh ce*😍

💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)


By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*


_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*


🅿 *81*

Bin bayan sa da idanu Ammi tayi har ya 6acewa ganin ta, sannan ta dawo da hankalin ta ga rubutun da yayi, a hankali ta 'dago takaddan ta sada shi da idanun ta...

Wani tu'kukin bakin ciki taji ya mamaye mata zuciya...sakamakon ganin rubutun da yayi.
Saman la66a ta furta" Mu'een ya raina ni da yawa".

Abinda ya rubuta 'din yawo ya dinga yi mata aka, sake 'dago wa tayi ta karanta karo na biyu tana mai cize le6en ta na 'kasa.

Noor da bata san abinda ya rubuta ba a hankali ta 'karaso gaban Ammi ta dur'kusa tana kuka take ro'kan Ammi akan ta yafe masa kar tayi fushi da shi, tace ita ba nufin ta tsakanin su ya 6aci ba da shi bane, rayuwa da shine ka'dai bata so ayanzu...
Amma bata ce da ita 'kala ba kawai ta saki takkadan ya fa'do 'kasa dai-dai 'kafafun Noor, a hankali Ammi ta 'daga kafar ta tayi waje tana mai jin wani abu na taso mata, tausayin Noor gami da Danasanin bawa Mu'een auren ta da suka yi, ba kowa ce mace ba zata iya irin hakan, ace duk irin abinda yayi mata amma still burinta taga bai samu sa6ani da mahaifan saba, sa6anin matan yanzu da wasun su da kansu ma suke raba tsakanin mijin su da iyayen sa saboda son zuciyar su.

Kuka sosai Noor ta sha har kanta nayi mata ciwo mai tsanani, tana hawaye ta 'dago takkadan da Ammi ta jefar da niyyan ganin yawan sakin da yayi mata amma abinda idanun suka gani sosai ya bata mamaki take kakan ta ya tsaya cak, 'kurawa rubutun idanu tayi tana karamtawa tana 'karawa" _Kiyi ha'kuri.. bazan iya sakin ta ba Ammi_ ".
Abinda kawai ya rubuta kenan...cikin zuciyar ta ta furta _Allahumma ajirni fi musibati_ ...yayin da a fili ta furta" Wallahi ko babu saki tafiya ta zanyi bazan sake zama da kai ba".
Haka ta 'karashi kukan ta tayi shiru...zuciyar ta cike da haushin Yah Deen ji take tamkar ta sha'kesa.


Deen kuwa tunda da barin sa wurun Ammi direct 'dakin sa ya wuce ya 'dauki key kawai yayi waje.

Can wani gida can wani gidan sa da yake ginawa bai 'karasa aikin ba ya tafi da yake babu wani nisa sosai da gidan nasa na asali.

Babu komai a gidan na amfani, amma haka yake tahowa yayi zaman a duk lokacin da yaji abubuwa sun sha mai kai.

Safwan ka'dai ne kuma yasan da cewa yana ke6e kansa a wannan gidan.
Kuka ya dinga rizga kamar yaro 'karami gashi babu mai lallashi, tausayin Noor yake ji sosai, mai yasa Ammi bazata fahimce shi ba? tayaya zai iya rabuwa da Noor cikin wannan halin bacin yasan cewa komai da ya faru sanadin sa ne, meyasa bazasu bashi dama ya cika al'kawarin da ya 'dauka ba?...yasan sakin Noor a wannan ga6ar na iya haddasa mata wani matsananciyar damuwa ne saboda yasan dole tunanin Baby zai dame ta sosai ga kuma ace shima ya sake ta da wanne da zataji?

" Ammi ki yafe min amma bazan iya rabutawa Noor saki ba sam, nasan ni mai laifi ne sosai na sani, kuma ban cancanci afuwar Noor ba, bama ni da idanun.da zan iya duban ta in nemi afuwar ta.
Amma ya zanyi Ammi? Rabuwar mu da Noor bazai gyara komai ba, al'kawari nayi yanzu Ammi zan bar dukakkn abubuwan da nake aikatawa, wallahi ko garin Bauchi Noor tace mu bari zan bari saboda ita ina son sake ganin farin cikin ta..ina son matata ina 'kaunar zama da ita, iyace farin ciki na hasken raina...".
Haka yayi ta sumbatu kamar mahaukaci, duk ya fita hayyacin sa gaba 'daya, gashi yana jin ciwo amma ya basar saboda tsananin damuwar da ke cinsa...a hakan har bacci ya yi gaba da shi.

Sai cikin dare ya tashi ya alwala ya 'dauro sai da ya koma motar sa ya 'dauko dadduma sannan yazo ya sallaci sallar da bai yi ba.

Sai da ya 'kara da nafilfili haka ya dinga istighfari yana ro'kon yafiyar ubangijin sa da fatan ya daidaita masa rayuwar gidan sa yasa mahaifan sa su yafe masa fusgin da suka yi da shi.

Akan daddumar ya koma ya kwanta wani baccin ya sake 'daukan sa.



*****
Washegari su Ammi suka firfito da kayan su gaba 'daya har da na Noor dake ta faman share hawaye lokaci zuwa lokaci, Ammi sam bata damu da 'kin sakin Noor da Mu'een yayi ba ta riga tasa cikin ranta cewar ko bai sake ta ba bazata barta tare da shi ba.

Tun jiya Safwan ke ta 'kiran layin sa amma baya 'dagawa, abin ya 'daure masa kai sosai dan ko da safiyar yau ma sai da ya 'kira amma still bai 'daga ba, sanin da yayi cewa lafiya bata ishe shi bane yasa shi kamo hanyar gidan nasa da sassafe da zummar jin ko lafiya.

Yana zuwa sai ya tarar da kayan su Ammi a harabar gida, shiga yayi suka gaisa da su ganin su cikin shirin kuwa bai sashi mamaki ba cuz yasan da batun tafiyar, fahimtar da yayi harda Noor a tafiyan ne yaso sashi mamaki har ma ya kasa yin shiru sai da ya tambayi Ammi cewa tafiyar harda Noor ne?"
Kallon sa Ammi tayi tana 'dan ha'de rai tace da shi" Umm da ita zan tafi Safwan..ko so kake in barta ku 'karasa min ita a banza?"

Kai ya 'dab sosa sannan yace" kiyi ha'kuri Ammi naga ai mijin nata ba lafiya sosai gare shi ba..."
" Ya mutu mana shi ya sani ai...ita ma lafiyar bata ishe ta ba jinyar ta zanje inyi bazan iya barin ta ku 'karasar min da ita ba...".
" Ammi kiyi ha'kuri dan Allah kar ki yanke wannan hukuncin wallahi Mu'een na bu'katan kulawa yanzu kuma na tabbata zai canza tunda ga abubuwan da suka yi ta faruwa nasan sazu zame masa izna, ga dukkan alamu ma already yayi nadama ai Ammi..."
Baki Ammi ta ta6e cikin nuna halin ko'in kula ta kawar da kanta.
Ga Noor ya dawo da kallon sa yace" Please Noor ki yafewa mijin ki kuma ki taya ni bawa Ammi ha'kuri...."
Noor tun bata kai ga jin 'karshen furucin nasa bama kuka ya 'kwace mata.
Ganin hakan yasa Ammi saurin fa'din" Baruwan ka da ita Safwan, ku bar min yarinya ta yi numfashi mai kyau dan Allah, ba ita ta aiki mutun aikata abinda yaso ba so bata da alhakin jinyar sa, sam bashi da alamar gyaruwa, ba yau ya fara irin munafurcin nan ba daga baya kuma sai kaga ya koma ruwa dan haka ka barshi...yaje shiya sani nasan akwai ranar da duniya zata juya mai baya, idan ta'kamar shi kyau da Allah yayi masa ne ai mai gushewa ne, kuma kansa yake yiwa mummunan tabo

Please Login or Register in order to submit comment