Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

PM] ๐ŸŒธSalmerh๐ŸŒธ: ๐Ÿ’• *NOORUL* ๐Ÿ’•
(Haske nah)



By
*Salmerh MD*



*Wattpad @*
*Serlmerh-md*



๐Ÿ’ซ *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
๐Ÿ’ซ
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*



*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*



๐Ÿ…ฟ *18*


Batare da tunanin komai ba Ja'afar ya amince dan kuwa sosai yake da ya'kinin cewa Allah yana tare da su kuma shi zai taimake su, farin cikin sa 'daya kawai shine yau 'dan uwan sa zai kwana cikin gidan sa da iyalan sa .


Kamar yadda suka fa'da 'din kuwa hakan ne ya faru domin kullun yakan je yayi signing kamar yadda suka bu'kata har tsawon sati biyu batare da yayi fashi ba.


Ammi kuwa s
duk iya 'ko'karin da zatayi na ganin cewa ya amince an saida abubuwan data gada daga gurin mahaifin ta tanayi domin a biya bashin sharrin da aka tiwa mai gidan naga amma sam Taheer ya 'ki amincewa bai kuma sanar da ita da dalilin 'Kin amincewar yasa ba.

'Bangaren shi Tahir 'din kuwa har cikin ransa yake jin tamkar idan yayi hakan bai kyauta mata ba duba da yanda wancen Lawyern ya damfare ta ya tafi da dayawa daga cikin dukiyar ta sannan 'dan abinda suka rage kuma yace zai yi haka dasu ai bai kyauta ba....shi aganin sa.


Ammi kuwa rashin amincewar tasa sosai ya bata haushi har ma take jin tamkar da'ace takaddun dukiyar na wajen ta da tuni tayi abinda zatayi sai da ya 'dau duk matakin daya ga daman 'dauka daga baya amma baby abinda zai hanata aiwatar da nufin ta.


Abin na damun ta sosai a duk lokacin da ta tuna cewa mijin ta matsayin mai laifi yake dan har fargaban dare yayi gari ya waye take yi sai take ganin kamar lokacin rabuwan ta da mijin ta ne yake 'kara kusanto ta, dan haka ranar wata talata ta fara bincike sosai cikin 'dakin sa da niyyan duba takaddun dake wurin sa.....domin sunyi magana dashi ko yana da wasu ku'dade cikin account 'dinsa sai yace mata bad
baza su haura 10million ba ku'din ita kuwa bata son rasa shi ta ko wani 6angare.

Gaba 'daya tayi kaca-kaca da 'dakin amma bata ga komai ba kuma tana da tabbacin a 'dakin suke bai kai su ko'ina ba dan haka sai ta cigaba da dubawa da fatan Allah ya taimake ta can su....kamar daga sama kawai ta ganshi tsaye a bakin 'kofa dan ko motsin shigowar sa ma bataji ba tsaban yanda hankalin ta ya tafi.


Suna ha'da idanu da shi sai ta diririce abinda ke hannun ta ya fa'di 'kasa, batayi zaton zai dawo yanzu ba dan kuwa division yaje yin signing shiyasa ma ta saki ranta take binciken cikin kwanciyar hankali ko zata gansu tunda ya hanata ta da'din rai gara ta 'dauka tayi abinda ya dace dasu...ina amfanin ba'di ba rai" acewar ta kenan......

Da rawar murya tace dashi " har...ka....da wo?".
Sai yace
" Ke ma 'din na miki satan ne?"
ya tambaya a tsare batare da yabata amsar tambayar ta ba wanda daga jin yanayin muryar sa ma zaka san cewa ransa a 6ace yake.


Sai ta jijjiga kanta a hankali alamar " ah ah"
"So...?" Yace da ita da 'dagaggen gira 'daya.

Kwa6a fuska tayi kamar zatayi kuka gani da watsa hannayen ta tace dashi " please Taheer give me the documents i want use them...me yasa kake hakane wai?"


Cikin 'dakin ya 'karaso a hankali cike da 6acin rai ya nuna mata hanyar waje gami da fa'din " leave this room please"!


Tsayuwa taci gaba dayi cikin karya wuya da niyyan sake ro'kon sa amma kafin tayi magana sai ya daka mata tsawan " i said leave from here now"!

Fita tayi a hankali tana matse 'kwallan takaici.....yayin da Taheer ya rakata da jajayen idanun sa har ta fita.


Tana fita ya koma ya zauna bakin gado tare da dafe kansa, tunanin inda ya kamata ya 6oye takaddun kawai yake yi amma ya rasa, kuma baya so ya bawa kowa ajiya saboda gudun kar labari ya sake maimaita kansa...kar asake yi musu irin na Lawyer.


Sosai ya zurfafa tunanin har ya gano abinda ya kamata yayi....dan haka washe gari ya faki idanun ta tana kitchen yaje cikin 'dakin ta ya 6oye su inda yasan tunanin ta bazai ta6a zuwa wurin kwana kusa ba.


Ko bayan hakan ma tasha zuwa a 6oye tana bincikawa amma bata ta6a sa'ar ganin koda 'daya daga cikin documents 'din ba, har sai da ya kasance cikin 'dakin babu abinda bata 'daga shi ta canza masa mazauni ba saboda neman takaddun amma tarasa bata gansu ba.


Rashin sani ya sa bata ta6a ko kawowa cikin ranta cewa kullum tare take rayuwa dasu cikin 'dakin ta ba, shima dan yasan tunanin ta ba zai zo nan 'din bane shiyasa ya kawo su kusa da ita duk da hakan amma yakan saci jiki kullum ya je ya duba lafiyar su batare da ta kula da hakan ba.



*****
Kwanakin shiga kotu na 'kara 'karatowa yayin da abubuwa ke 'Kara shan kansu gaba 'daya, Addu'ah sukeyi ba dare ba rana... Hatta Ja'afar ba'a barshi abaya ba kamar yadda ya 'dau
al'kawari ga kuma tunanin inda zasu iya kammala ku'di mash uban yawa har haka sosai abun ke adamun sa.


'Bangaren Ammi kuwa sai take ganin kamar shi har yanzun bai wani damu da lamarin ba dan ko lawyern da Ja'afar ya nema musu ma 'kin bashi ha'din kai yayi acewar sa koma me zasuyi ba nasara zasuyi ba tunda bashi da proof ko 'daya da zai kare kansa dashi, dan haka su bari kawai ayanke masa duk hukuncin da suke ganin yayi musu he ll definitely accept it"


Cike da 6acin rai Ja'afar yace " haba Alhaji dan Allah...wai kai baka tunanin future 'din iyalan ka ne?"
Sai ya bashi amsa da fa'din...
" Duk wanda yake da 'dan uwa irin ka Ja'afar ai bashi da damuwar komai, na tabbata Mu'een bazai ta6a yin maraicin uba ba har abada matu'kar kana raye a duniya".


" ita kuma matar ka fa ya zakayi da ita... baka tausayin halin da zata shiga dalilin hakan ne?.... Me yasa ba zaka tausayawa maraicin ta ba?"
Ja'afar ya sake tambayar sa.

Kafin ya bu'di baki yayi magana sai Ammi ta taho da gudu ta rungume shi tana kuka gami da bugun 'kirjin sa tana fa'din " kawai ka kashe ni Taheer ka kashe ni ka huta dan Allah...wai ya kake so inyi ne fisabilillahi...baka son gani na ina farin ciki ko Taheer....?


'Kasa ta sulale tana kuka mai cin zuciya, haushin abubuwan nan da yake yi take ji, bata san manufar sa akan hakan ba, sam ta rasa wani irin zuciya ce da shi da har zai yi saurin yanke 'kauna da farin ciki so soon haka, me yasa ba zai bari su yi abinda ya dace ba, ko dama ya gaji da rayuwa da su ne shiyasa ko tausayin su baya ji zai bawa ma'kiyan sa daman cin galaba akan sa?"


Jikin Ja'afar sanyi yayi sosai dan haka sai yasa kai ya fice a 'dakin ya barsu su biyu.


'Kasan shima ya dur'kusa akan gwiwoin sa a hankali ya furta " Aisha.."

'Dago jajayen idanun ta tayi ta kalle sa da su sannan ta kawar da kanta gefe yana mai cigaba da zubar da hawaye.


Kai ya girgiza gami da fa'din " ke kina ganin tamkar duk abinda nake yi dan kaina nake yin sa ko Aisha? Idan kowa bai fahimce ni ba ai ke ya kamata ki fahimce ni, me yasa zan tauye miki hakkin ki in salwantar miki da dukiyar ki bacin bani da tabbacin cewa zan samu hanyar da zan biyaki abinki koda na rayu? Ke kina ganin hakan dai-dai ne idan na amince da batun ki?"


A fusace tace " ni nace maka zaka biyani ne?"

Murmushi ta'kaitacce yayi gami da mi'kewa tsaye tare da fa'din" bazaki gane bane Aisha, banfa saci abin kowa ba kuma sai in yadda naki dukiyar ya salwan ta saboda wasu can marasa tsoron Allah? kin sanni kin san hali na Aisha kinsan cewa bana saka kaina cikin abinda bai shafeni ba... ban nawa kaina magana tun farko, duk abinda kika ga ya faru dani to daga Allah ne, bance kince zan biyaki ba yanzu ba amma bazan 6oye miki ba wallahi har abada bazan ta6a iya cin dukiyar ki wai dan ni na rayu cikin farin ciki ba......"
Juyowa tayi ta kalleshi bai damu ba sai yaci gaba da fa'din ".....karki damu kinji...baki na yimin addu'ah kullum ba, nima kuma kinga inayi, kijira kiga ikon Allah tunda sharri ne ba gaskiya bane na tabbata Allah na tare da mu, in kinga ban tsallake wannan lamarin ba to 'kaddara wannan babban 'kaddara ce daga cikin babin rayuwa ta kuma dukkan mu ya kamata mu kar6e shi....duk abinda aka riga aka fawwalawa Allah shi to sanya wa ranki salama domin zai isar miki koma menene ".
Ammi sai tace
" What about the court...."
'Kyale su ni ba wani Lawyer da zamu 'dauka su suka sani...domin babu wani taimako da Lawyern zai mana sai dai ma cuta abanza".


Ammi bata 'kara magana ba illa binsa da idanu da take yi, sosai take jinjinawa taurin kai da kafiya irin nasa, yau ne ta yadda cewa lallai mijin ta mai tsantsan taurin kai ne, bata ta6a fahimtar hakan ba sai yanzu da wannan abin ya faru.


Haka ta ha'kura ta zubawa sarautar Allah idanu ba Wai dan task jakan ba... bata dai fasa addu'ah ba haka kuma zancen case 'din babu abinda ya canza.


Ana jibi za'a shiga kotun ne Manager da kansa ya 'kirashi ya sanar dashi cewa an janye maganar saboda an samo inda ku'din fuel 'din sukayi dan haka yayi ha'kuri.


Bai ce dashi komai ba illah lumshe idanu da yayi gami da fa'din Alhamdulillah cikin zuciyar sa tare da yanke 'kiran gaba 'daya.


Hawaye kawai yaji ya gangaro masa masu sanyi, tun fitar sa daga station bai 'kara zubda hawayen sa ba sai yau 'din da yake yiwa Allah godiya bisa ga babban taimakon da ya yiwa rayuwar sa.


Batare da ya sanar da Ammi ba ya shirya ya tafi Division 'din inda suka sake yi masa bayani gami da neman saka hannun sa na 'karshe tare da ban ha'kurin tuhuma inda suka 'karashe da fa'din " haka aikin mu ya gada ka gafarce mu visa abubuwan da suka faru.


Bai damu da wannan ba shi dai kawai fatan sa ya isa gidan sa ya sanar wa da Ammi wannan babban abin farin cikin da ya same su a yau.


Tunowa da yayi cewa jiya-jiya Ja'afar ya wuce Azare da niyyar gobe zai dawo a shiga court 'din dashi sai taji matu'kar tausayin 'kanin NASA..... dan sau'ka'ka masa tafiya sai yana fita daga ofishin 'yan sandan ya doka masa 'kira gami da fa'din " albishirin ka lil bro".

"Goro fari 'kal Alhaji...amma duk girmana mana 'kiranka Lil ai sai Mu'een ya min dariya..... nd kuma irin wannan albishir da kake min Allah yasa dai ku'dine suka bayyana"!


" Kusan hakane 'dan uwa domin kuwa an kori wannan case 'din i'm free now ba sai kazo goben ba".


Washe baki Ja'afar yayi gami da hamdala daga 'dayan 6angaren sannan ya 'kara da fa'din " ai zuwa dole ne Yayah, dole inzo muyi murnar tare...insha Allahu gobe ina hanya...kai masha Allah..... Allah ka 'kara rufa mana asiri".
Amin yace tare da yanke 'kiran.


Yana shiga palour da Mu'een ya fara cin karo sai yayi saurin 'daga shi da murnar sa yana dariya.


Shima Mu'een dariyar yake yi ganin mahaifin sa da ya jima baiga dariyar sa ba yau yanayi dan haka shima da 'karfin gwiwar sa yake darawa.


Hayaniyar sune ya fito da Ammi daga 'daki inda ta 'karaso da bu'd'den bakin mamaki tana kallon sa, fara'ar da take gani yau 'din direct take hango shi har cikin zuciyar sa domin kwata-kwata bai yi kala da na ya'ke ba.


Ganin kallon da take yi musu ne ya sanya ya shi sau'ke Mu'een gami da fa'din je kawo min ruwa insha kaji".


Da gudu yaron ya tafi yayin da Taheer yayi saurin tunkarar Ammi ya ha'de musu fuska gami da fa'din " ur husby is free now an kori shari'ar mu gaba 'daya".

Tsalle ta buga tare da rungume shi cike da farin ciki shima 'din sai ya rungume ta ka'dan dan hankalin sa na kan yaron da ya aika.


Yana sakin ta kuwa Mu'een ya dawo da goran ruwan Swan mai sanyi a hannun sa, shi Taheer bai sake bi ta kan farin cikin da Aishatu keyi ba yayin da itan kuwa take jin tamkar ta zuba ruwa a 'kasa tasha, ruwan ya kar6a ya bu'de gami da 'daga kai bai sau'ke ba sai da ya kwankwa'de gaba 'daya.

_Alhamdulillah_ ya sake maimaitawa gami da kallon ta yace " kinga ikon Allah ko? ai dama na gaya miki, ba'a dogaro da Allah aga failure, yanzu ya kika gani?".


Murmushi tayi tare da sake tahowa ta rungume shi cikin tsananin farin ciki, cuz she is totally speechless, Mu'een ya janyo ya ha'de su duka ya rungume su shima 'din yana farin cikin sosai.


A kunne ya ra'da mata" bakya jiko...didn't i tell u not to hug me in front of him?"

" Sorry...." tace a hankali itama.


Sannan sai tayi saurin samin shi gani da fa'din "amma Alhaji ya kukayi da Manager gurin warware case 'din? Baiji kunyar ka Ba da ya ganka? "


" Ai ban ma ganshi ba ni.... Sa'ko ne ya iso ni kawai"

"Hmm" tace gani da sakin tsaki.

Kallon ta yayi gami da tambayar abinda ya faru sai tace " ya kamata ya ji Mari Allah ko sau ' daya ne".

Sai yace " Ba damuwa ba kenan Aisha.... ai da naso yin hakan da har office zan same shi amma bani da wannan lokacin ni.....





*****
Washe gari kamar yanda ya fa'da Ja'afar suka zo harda matar sa Zainab, gaba 'daya suka ha'du suka yi farin cikin tare inda anan Taheer yayi musu bayanin yanda akayi gaba 'daya, dukkan su basuyi mamaki ba domin sunsan wannan ka'dan ce daga cikin buwayar mahallici balle bayyanar da gaskiya da take ta zahiri.... Wannan a gurin sa shi yafi komai sau'ki.


Anan Ja'afar ma yake sanar musu cewa ai shi har ya fara cuku-cukun kar6an loan sai kuma ta Allah ta kasance.....Ammi ma tace " ai ka bari Ja'afar ni da document sukayi min 6atan laya a gidan nan....gaba 'daya na rasa ina aka sanya su har na fara tunanin ko an sace ne".
Kallon sa tayi gami da ri'ke baki tace " wai dan Allah ina ka 6oye su ne... Yanzu kam ai zaka sanar dani tunda komai ya wuce?"
Sai yace
" D'akin ki na 6oye su saboda nasan hankalin ki bazai je gurin ba"


Salati ta sanya yayin da su Zainab suka tuntsire da dariya don ko su ma a lokacin confused sosai suka shiga da tace ta rasa document 'din dan yana yawan tiwa Zainab complaint a duk lokacin da ta gaji da bincikawa..... Abun na bash mamaki duk da take ma suma 'din basu goyi bayan a salwantar mata da dukiya ba yayin da 'dayan 6angaren kuma basa so rayuwar sa ta salwanta...abin sai ya 'daure kansu gaba 'daya shiyasa ma daga baya Ja'afar yayi tunanin kar6ar loan sai su cika sauran da abinda Allah ya hore musu.


" Ni dai Allah baka kyauta min ba kuma kar kaga kamar banji haushin abin nan da kayi ba wallahi har abada bazan daina jin haushin hakan ba, ace ina da abu amma mijina ya kasa anfana da ita to miye anfanin ta?"

Shi kan Taheer shiru yayi mata illa murmushi da yake yi a cikin ran sa ya furta "sai kiyi kuma ai"!
yayin da su Zainab suka cigaba da bata ha'kuri da ban baki har ta ha'kura.


Duk kansu babu wanda ya sake bi takan office 'din nashi balle har su nemi jin babban dalilin da ya sanya akayi masa sharrin, sude kawai fatan su Allah ya kare na gaba ya raba su da ma'kiyan su Amin.


Kwanan su 'daya suka koma Azare domin shima Ja'afar yawan zirga-zirgan da yayi a kwanakin ya so ya ta6a masa wurin aikin sa, kunsan aikin banki ba'a wasa dashi...dan haka yake so ya dai-dai ta komai..... Shiyasa suna komawa ya fuskanci aikin sa bada wasa ba.





*****
Rayuwar su ta dawo sabuwa 'kal, yanzun kam basu da matsalar komai illa Taheer da ya dawo da lamarin Barrister cikin ransa, so yake a matsayin sa na mijin ta ya kare mata maraicin ta, martabar ta da hakkin ta da ya kamata... dan haka yake so yaje ya ziyarce shi kamar yanda yayi planning run farko dan su magantu da shi wala Alla ka zai fahimce shi, amma da kansa yasan cewa abinda zai yi 'din riski ne babba kamar yadda Aishatu ta ta6a gaya masa tun farko, dan haka ya kamata wani nasa yasan da lamarin wanda zai ri'ke sirrin sa batare da ya taka masa birki ba.



Kansa ya dafe yana tunanin yanda Ja'afar zai 'dauki lamarin yasan da 'kyar ya fahimce shi amma kaf duniyan nan yanzu shi ka'dai yake da shi kuma shi kad'ai ya yadda dashi dan haka batare da 6ata lokaci ba ya danna masa 'kira ta landline 'din gidan sa dayake lokacin yasan already yana gida.


Bayani yayi masa cikin natsuwa akan duk yadda akayi, da kuma abinda yake son aikatawa, anan Ja'afar ya 'danso ya hana shi amma ya fahimtar dashi a fahimce ya kuma fahimta.


Yana sau'ke wayar daga kunnen sa Ammi ta fa'do 'dakin cike da 6acin tana kallon sa, sai yayi saurin mi'kewa tsaye.


Yaso yayi mata magana amma sai yayi tunanin kar dai taji shi ne...taji shirin nasa.

Dan haka sai ya juya inda ya fara rage kayan jikin sa tamkar bai kula da yanayin fuskar ta ba cikin 'karfin hali yace " yauwa ma tunda kinzo...ha'da min ruwan wanka please mai 'dan 'dumi".

"...bazan ha'da ba"!
Tace dashi a fusace.


Da mamaki ya juyo yana kallon ta gami da 'kan'kance idanu batare da ya furta komai ba.


'Kafa ta 'dago ta taho da gudu tana bugun sa a 'kirji tana kuka... Taheer bai hanata ba sai da ta gaji dan kanta ta bari cikin kukan ta nuna shi da yatsa tace " bazaka daina saka rayuwar cikin masifa ba ko? bazaka daina nemawa kanka rashin kwanciyar hankali ba ko...wai anya ma Taheer kana son farin cikin mu, kana son kallon mu cikin farin ciki kuwa kode nice baka so ka gaya min Taheer?"
Ta 'karasa maganar cikin kuka.

Bai furta komai ba kawai ya rungumo ta jikin sa tsawon mintina har tayi shiru, duk da yana kyautata zaton taji wayar sa ne amma still yana son ji daga bakin ta domin ya tabbatar.

" me ya faru ne wai haka?"
Ya tambaye ta as if bai san me ya farun ba dagaske.

Raba jikin ta tayi da nashi ta matsa baya ka'dan sannan cikin dakiya tace masa " nima ban sani ba...amma ka sani wallahi akan wannan abun ko ciwon farce kayi bazan ta6a yafe maka ba tunda mun gama magana da akai tun ba yau ba".

Juyowa tayi ta fuskance shi sannan tace " ina ruwan ka dashi, bashi ke son dukiyar ba ai sai ka bar masa, ni ko ka kar6o ma banso matu'kar zakasa rayuwar ka cikin halaka to wallahi banso Taheer, miye ma anfanin ta tunda ko akwai 'din ma ba abinda ya dace ake yi da ita ba, me zan yi dashi Taheer, kai kace bakaso to ni me zan yi dashi?amfanin me zata min? "
Cewa yayi
" Hakkin ki kine Aisha ni kuma nawi ne akai na in kare miki hakkin ki ko wani iri ne....."

" to hell with it...." ta fa'di a fusace, sannan ta 'dago yatsa ta nuna saitin fuskar sa tace " wallahi idan ka kaje da kanka ka kar6o ban yafe maka ba kuma daga ranar zamana da kai ya 'kare, lokacin da zai kar6a ya wahal da kai ne, me yasa lokacin da ake so kuma kai zaka wahal da kanka?
Kai kake cin dukiyar ne....? Zunubin ka ne ko kuma menene?.... I told u ka 'kyale shi ni na barshi da Allah matu'kar da gangan yayi ban kuma ce abi bayan sa ba har abada"...
Tana kaiwa nan ta fice a fusace ta bar 'dakin.


" Aisha! ..... Aisha!!....yake ta anbata amma ko waigowa bata yi ta k'yaleshi.



Comment
Vote
Share





*Salmerh ce*๐Ÿ˜
[12/25/2019, 12:27 PM] ๐ŸŒธSalmerh๐ŸŒธ: ๐Ÿ’• *NOORUL* ๐Ÿ’•
(Haske nah)



By
*Salmerh MD*



*Wattpad @*
*Serlmerh-md*



๐Ÿ’ซ *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
๐Ÿ’ซ
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*



*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*



๐Ÿ…ฟ *19*



Zama yayi bakin gadon gami da dafe kansa da har sara yake jin yana yi masa.

Daga nan bai 'kara ha'duwa da ita ba, bai je ba haka itama bata sake dawowa inda yake ba.

Mu'een kuwa Ja'afar sun tafi dashi da yake anyi hutun makaranta.....so kowa sai yake jin babu da'di.


Washe gari da safe Ja'afar ya 'kira shi dan yaji ko ya shirya tafiyar anan Tahir yake sanar da shi cewa ai ya fasa tafiyar gaba 'daya maganar ma ta wuce.


Baiyi masa dogon bayani ba ya yanke 'kiran shima Ja'afar 'din bai damu ba cuz dama can baso yake yi ba, ya ha'kura ne dai kawai dan babu yadda zaiyi, amma ai abun a zahiri yake, duk wanda kaga ya aikata irin wannan abun to kuwa shi ka'dai yasan me ya taka, shi ka'dai yasan shirin sa akan hakan, Tahir 'din ne dai kawai yake da taurin kai shiyasa ya kasa fahimtar su... Amma yanzun da yaji cewa ya fasa sai yaji hankalin sa ya kwanta sosai.




ใ€ฐใ€ฐใ€ฐ
...... Basu sani bama ashe ko wancan case 'din da ya faru da Tahir.... Lawyern ne ya assaso shi tunda ya samu labarin binciken da Tahir yayi akan sa sai ya rasa yadda zai yi ya 'kas'kantar da shi da rayuwar sa, ya so yasa akashe shi amma sai ya fasa ganin cewa managern Oando babban aminin sa ne, dalilin haka ya sanya suka shirya deal akan hakan da zummar idan an tuhume shi kan satan fuel dole zai biya ku'din komin yawan su, wanda dalilin hakan zaisa ragowar dukiyar dake hannun sa zata sami gi6i na gaske shikenan daga ranan koda zasu nemi karawa dashi they ll not win against him dan basu da komai, rayuwar yanzu kuwa sai kana da shi ake yi da kai.

Ku'din da zasu biya 'din kuma shi manager zai ri'ke sai lawyer ya cika masa ya zama 100million shi kenan deal 'din su ya 'kare daga nan.... amma 'karfin addu'ah da kuma rashin sabo da cin amana ya sanya manager rashin natsuwa bayan sun gama shirya komai, sai gashi kafin deal 'din nasu ya kammala da kansa ya bayyana cewa an samu ku'da'den...sai dai bai sanar da kowa cewa su suka shirya hakan ba.


'Bangaren Lawyer kuwa ganin ha'kar sa bata cimma ruwa ba a karon farko ganin hakan ne ya sanya shi canza tunani zuwa plan B.





*****
Bayan wasu kwanaki sai Oando suka rin'ka damun Tahir akan ya dawo bakin aikin sa, shi kuwa gaba 'daya aiki dasu ya fice masa arai harma ya fara 'ko'karin neman wani aikin a wani wajen daban.


Itama Aishatu bata goyi bayan ya koma can 'din ba haka ma Ja'afar, sai ma tace suje Kaduna su 'dan kwana biyu daga nan su duba gidajen mahaifin ta dake can 'din daga baya sai su dawo kafin nan ko zasu rage damun sa.


bai 'ki shawarar ta ba dan ko shima 'din yana so ya 'dan kauce ko ma dan ya huta, cuz tun bayan faruwar lamarin Kano ta bar ransa kwata-kwata.


Dalilin haka ne yasa washe gari suka wuce Kaduna su biyun su batare da kowa ya sani ba da yake ma har yanzu Mu'een na Azare gun Ja'afar shiyasa ya kasance su biyu ne sukayi tafiyar.


Sunje sunyi duk abubuwan da ya dace sun kuma huta 'din

Please Login or Register in order to submit comment