Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsaye jikin mota daga gefe ka'dan da ita ba kawai ta shiga ta tada motar ta fizga da gudu tayi gaba bayan ta ha'da uban 'kura a wajen.

Zuciyar sa tamkar zata faso saboda takaicin halin da mafi soyuwa acikin zuciyar sa yake aikatawa, in bama shi ba ina shi ina wannan matar, ai da gani ba sa'ar rayuwar sa ba ce in ba biyewa zuciya ba.

Ya kai tsawon mintina uku bayan tafiyar tata kafin Alhaji ya shiga motar sa bai koma gidan gona ba sai ya wuce gida zuciyar sa na ta azalzalar sa dan 6acin rai.

Parlour yaje ya zauna shiru Ammi na ciki bata san da zuwan sa ba....ya kai mintina talatin da zuwa gidan sannan Ammi ta fito ta ganshi...da mamaki ta iso inda yake tana tambayar sa " Alhaji Lafiya kuwa?".

" Ba komai "
ya bata amsa a ta'kaice.
Ammi kam jan bakin ta tayi tai shiru cuz ta san tunda yace bakomai ga dukkan alamu ba hurumin sa ba ne.

Ruwa taje ta kawo masa ta ajiye gefen sa sannan ta zauna, tana shirin zata sake magana yayi saurin 'daga mata hannu.

Tsaye ya mi'ke yana safa da marwa cikin parlourn ransa ya kai 'kololuwa wurin 6aci...bai san me ze ce game da wannan lamari ba.

Yana cikin hakan Yah Deen yayi sallama, Ammi ce ka'dai ta amsa shi.
Shi kansa sai da yaji wani iri ganin Ammi ta buga tagumi ga kuma Alhaji tsaye cikin yanayi na damuwa....tunanin sa ko tun fa'dan shekaran jiyan ne bai 'kare ba hakan sai ya sashi tsarguwa.

A 'darare ya 'karaso gaban Alhajin yana niyyan durkusawa dan gaida shi sai kawai yaji sau'kan mari saman kuncin sa....daga Alhaji Baba.

Cikin ka'duwa ya dafe fuskar sa yana kallon Alhajin da cikin idanun sa ka'dai zaka kalla kasan cewa yana cikin yanayi na tsananin 6acin rai, yanayi ne da ya jima bai shige shi ba.

"....Waye ubanta?..Muhammad ka gaya min 'yar waye?"

Cikin rashin fahimta ya 'dago idanun sa da suka koma jaja ya zubawa Alhajin da alamar tambaya sannan ya juya ya kalli Ammi ma da ta mi'ke tsaye tun sanda Alhaji ya mare sa.

"...Irin rayuwar da kaga ta dace ka za6ar wa kanka kenan ko Muhammad?...mutunci na kake son zubar min agarin nan shiyasa ka nuna min ban isa da kaiba, inace da kaina na garga'de ka akan ban son in 'kara ji ko ganin tazo ko ba ji da kai muka yi maganar ba?"

Hawaye ya fara yayin da ya sunkuyar da kansa 'kasa gwanin tausayi, yayin da Alhajin ya cigaba da fa'din...." Nawa ma kwata-kwata kake da har zaka lalata rayuwar ka da biyewa matan banza..ko dan kaga na barka kayi rayuwa dai-dai da mura'din ranka shiyasa kake ganin yes kana da 'yan cin kanka yanzu?....laifi ne Muhammad dan nayi maka abinda ranka kake so?, ko laifi ne dan na barka ka zauna a gida kai ka'dai kamar yadda ka bu'kata...wato gani mutumin banza shine ka shirga min 'karyar abu take zuwa amsa to ko kaina malamin dake karantar da ita ai iyaka kenan..."

'Kasa ya zube yana kuka yake fa'din " Alhaji dan Allah kayi ha'kuri ka yafe min...wallahi ba nufi na kenan ba..."

" Shut-up da Allah munfukin banza...hala ka manta ni ne na haife ka...ni zaka yaudara da kalaman ka Mu'een...?"

Ammi ce tayi saurin isowa gaban sa tana tambayar" wai me ke faruwa ne Alhaji?.
Bai amsa ta ba sai ya koma kan kujera ya zauna Ammi sai ta bishi da idanu..ita kam mamaki duk yabi ya cika ta, a bai-bai take fahimtar maganar ta su.

Ajiyan zuciya Alhaji ya sau'ke bayan ya zauna 'din.

Kallon Yah Deen ya sake yi da har yanzu yake tsiyayar da hawaye, wannan karan cikin natsuwa ya ce dashi " Waye mahaifin ta kuma a ina yake ka sanar da ni?"

Baya so ya sake wasa da hankalin Alhajin dan haka sai yace " Mahaifin ta ya rasu".
Ammi kam kallon ta take ta rarrabawa tsakanin su sun 'daure mata kai gaba 'daya.

Alhaji kam cewa ya sake yi " Sunan sa na tambaya".
Kansa 'kasa ya amsa da
" Alhaji Hamza Ar'kilah".

Alhaji na jin haka ya tashi tsaye tare da 'daukan hular sa ya yi waje...Ammi kam da idanu ta raka shi har ya 'karasa barin parlourn sannan ta samu damar zama bisa kujera itama cikin tashin hankali.

Yah Deen tasowa yayi ya tsugunna gaban ta tare da kwantar da kansa bisa cinyar ta yaci gaba da kuka kamar wani 'karamin yaro.

Bata iya tace da shi komai ba har sai da ta dai-dai ta natsuwar ta kafin ta 'dau hannu ta 'dora bisa kan nasa dake jikin ta..." wai me yake faruwa ne Muhammad kaina ya kulle na kasa fahimtar komai...me maganganun Alhaji suke nufi?"

'Dago kansa yayi da raunin murya yace " Ammi dan Allah ki bawa Alhaji ha'kuri, Allah ba laifi na bane...ita ce take zuwa wuri na, sau tari na kan mata magana amma bata ji haka duk lokacin da ta ga dama zata 'dauki hanya tazo batare da ta sanar dani ba sai dai in ganta....to ya zan yi Ammi?... kuma babu komai tsakani na da ita kawai fa makarantar mu ce 'daya....shi kuma Alhaji yana zargin wata ala'ka ce daban a tsakani na da ita".

Hannun Ammi yayi saurin kamowa yace" Ammi please ki bawa Alhaji ha'kuri ya fahimce ni, abinda yake zargin bashi bane...kuma nayi al'kawarin daga yau insha Allahu bazata sake zuwa ba".



Comment
Vote
Share





*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

🤞🏻 ~MASOYA NA INA GODIYA SOSAI~ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *41*

Ammi 'dayan hannun ta ta 'dago ta shafa sumar dake kwance a kansa, cikin sanyin murya da kulawa tace da shi" ka kwantar da hankalin ka in dai ka tabbatar iya abin kenan kar ka damu, babu abinda zai faru, shima Alhajin ransa ne ya 6aci shiyasa amma zan masa magana insha Allahu zai sau'ko".
Kai ya jinjina mata alamar gamsuwa da maganar ta sannan a hankali Ammi ta kamo hannun sa ta mi'kar da shi tsaye, idanun sa jajazur kamar wanda ya yinin kuka.
Ammi ce tace da shi" je ka huta maza ka daina 'daga hankalin ka".
Bai 'kara furta komai ba kawai ya kama hanyar fita daga parlourn yayin da Ammi tayi zugum tana tunanin ma'kasudin zancen, ita a ganin ta ai laifin duk na yarinyar ne tunda ita ke zuwa wajen sa ba shi ke binta ba, toh me yasa laifin zai zama nasa shi ka'dai kuma?
Cikin ranta ta gama kudurta cewa zata fahimtar da Alhajin gaskiyar lamari kamar yadda Yah Deen ya bayyana mata, kar yaje yayi fushi da 'dansa a banza bacin ba shi ke da laifin ba...( a ganin Ammi kenan).


*****
      Bangaren Alhaji Baba ba kuwa da fitar sa bai zame ko'ina ba sai gidan gona, ransa a matukar 6ace yake, duk komai ya jagule amma haka ya danne kawai ya shiga tunanin mafitar da ta dace da matakin da ya kamata ya 'dauka tun kafin abin yazo yafi 'karfin sa.

Har cikin ransa baya zargin Mu'een da aikata mummunan aiki makamancin alfasha, amma bai san meyasa ba sam zuciyar sa ta kasa amincewa da abinda Mu'een ya sanar dashi, ya kasa amincewa da ala'kar sa da wannan yarinyar, dole yasan akwai wani sirri a 6oye dake tsakanin su wanda bakowane ya sani ba, rashin cikakkiyar shaidar zahiri ne ya sanya  shi ya yadda ba komai 'din kamar yadda Ma'een ya fa'di, sai dai hakan bashi zai hana shi cigaba da bincike akansu ba, matsayin sa na baligi kuma cikakken namiji baya so ace ya saba da ke6ancewa da mata tun yanzu, koma dan gudun abinda ka iya zuwa ya dawo, ita Zina kusantar ta ma Allah ya hane mu da yi balle aikata ta gaba 'daya, sannan matu'kar kana so imanin ka ya cika dole ne sai ka gujewa alfasha tun kafin faruwar ta ba, ba wai sai ya faru kazo kana dana sani ba bacin idan an aikata ba'a iya goge shi sam shiyasa gara ya yiwa tukfar hanci ya kare daraja da mutuncin ahalin sa tun lokaci bai 'kure mai ba.

Tunanin hakan ne yasa shi yanke shawarar nemawa Mu'een auren ta, cuz in dai har zata iya barin garin da iyayen ta suke matsayin ta na 'ya mace ta taho gurin sa to dole akwai wani 6oyayyen abin...hujjar haka kawai ya ri'ke, kuma ta gamsar da shi, babu mamaki cikin su zuciyar 'daya na son wani ko kuma ma duk ya kasance suna son junan su Yah Deen kawai ke 6oye masa da fa'din course mate 'din sa ce ita.

Bai sake bi ta takan Yah Deen ba, kuma ko da Ammi ta fara mai magana ma bai wani jira ya gama sauraren ta ba kawai ya dakatar da ita da fa'din...." Ta yi addu'ahn tabbatuwan Alkhairi kawai, idan ya gama shirya abinda zaiyi insha Allahu zai sanar da ita komai".
Abinda yace da ita kenan wanda hakan yasa dolen Ammi taja baki tayi shiru amma abin na nan cikin ranta...da ta tuno yanda Mu'een ya bar gidan kuwa sai ta sake shiga tashin hankali, hakan ne ya sanya ta saurin sake fuskantar Alhajin kana tace " Amma Alhaji please kar kayi fushi da shi,  kasan fushin iyaye ba alkhairi bane ga 'ya'ya, musamman ma shi Mu'inuddeen 'din karka ga yanda ya 'daga hankalin sa".

Takaitaccen murmushin takaici Alhaji Baba yayi yana duba agogon dake 'daure a tsintsiyar hannun sa yace da ita " Ni banyi fushi da shi ba, garga'di ne kawai nayi masa saboda gaba".

Ammi bata sake magana ba cikin ranta ta furta" Allah ya kyauta" daga haka bata 'kara fa'din komai ba.

*****
      Husnah ma wannan karan ranta ya 6aci sosai da abinda Tah Deen yayi mata hakan ya sanya ta shareshi, kwata-kwata bata neme shi ba, da kuma ta tuna kwanaki 'kalilan ne suka rage musu su koma school hakan sai ya sanyaya ranta, tasan koma menene da sun koma school za'a wuce wurin shikenan.

    Wannan tunanin ne ya sanya ta sakin ranta ta cire damuwar dake zuciyar ta ta cigaba da rayuwa.

Yayin da Yah Deen kuwa koda wani lokaci zuciyar sa cike take da tsoro da kuma fargabar irin matakin da Alhaji Baba zai 'dauka a kansa, zaton sa ma ko zai hana shi zama a gidan ne kwata-kwata ko kuma ya hana shi komawa school, amma ga mamakin sa ko ta kan sa Alhaji Baba bai sake bi ba...balle yace ya rufe gidan ya kai keys 'din gida.

Shikuwa fargabar tunkarar sa yake yi a wannan halin, sannan har a lokacin ya'ki kunna wayar sa saboda kar Uncle 'din sa ya 'kira shi yaji yanayin da yake ciki yai masa titsiye, cuz ya san halin Uncle Ja'afar muddin ya san abinda yake aikata bazata yi masa da'di ba.

Rashin jin komai daga aalhaji game da batun barin gidan ne ya sanya shi tunanin 'kila makaranta ce Alhaji zai hana shi zuwa kuma hakan ya barwa ransa.

'Bangaren Ammi kuwa da taga shiru bai le'ko su a gida ba har kwana uku sai hankalin ta ya fara tashi gashi bata samun wayar sa, and su Saif ba sannan balle tasa su dubo mata shi, babu kuma wani 'kwakkwaran aboki nasa 'daya da tasani agarin balle tai 'kiran sa ta tambaye shi abin sosai yai mata karan tsaye a ma'koshi.

Ni ce ka'dai a gaban ta wadda take tunanin zata iya turawa can amma kuma ranta bai kwanta da hakan ba sam.

     Ran cikar kwana na ukun ne ta 'kudira cikin ranta cewar koma menene zai faru ayau 'din nan sai ta ga 'danta da iznin Allah, ko ita da kanta zataje ta dubo ya yake tunda wayar sa ma har a lokacin bata tafiya.

Ni da nake tare da Ammi mafi yawan lokuta nice zan iya bada labarin sauyin da ya same ta a wancan lokacin, ban ta6a sanin 'kaunar da take yiwa Yah Deen ya kai irin wannan matakin ba ai da lamarin nan ya faru, yanda ta shiga damuwa, yawan gwada layin sa, yawan sakin tsaki, yawaita yi min hirar cewa bata san a wani hali yake ciki ba hatta Addu'ah bata ware ba nima sai da ta sani yin addu'a  akan in ringa tayata adda'ar "Allah ya dai-dai ta tsakanin Yah Deen da mahaifin sa"
Ina kuma yi cikin ko wacce sallah ta, hatta Alhaji Baba bai kaini fahimtar 'kololuwar damuwar da Ammi take ciki ba cuz shi idan ta fara complaint baya bari ta 'karasa zai tare ta da fa'din " Karta damu lafiyar sa 'kalau kawai ta barshi ai ya girma ya san abinda ya dace ya aikata ba sai an tuna masa ba".
Ya kan yi mata maganar ne ta sigar gatse amma bata fahimtar inda ya dosa.
Cike da damuwa zata sake fa'din
" Ko abinci fa  bai zuwa yaci".
Alhaji Baba murmushi kawai yake yi yace mata " Rabu da shi zaizo".

Yayin da ni kuma nake zama in nutsu in saurari damuwar ta kaf, tun bansan asalin me ya faru har yasa shi 'kauracewa zuwa gidan ba har nazo na fara fahimta a hankali cikin maganganun Ammi  cewa sa6ani suka samu da Alhaji Baba akan wai wata budurwa na zuwa gidan shi, ni kaina da naji zancen ban girgiza ba haka kuma ban 'karya zancen Alhaji ba, zan iya kasancewa shaida akan cewa dagaske tana zuwa 'din cuz da idanu na nasha ganin ta amma bazan iya kallon cikin idanun Ammi in sanar da ita cewa hakan gaskiya ne ba sam, banjin zan iya hakan har abada tsoro ma ba zai barni ba in furta ba dan haka kawai sai na bi Ammi da idanu.

Yawan damuwar Ammi akan sa yasa ni fahimtar 6oyayyen sirrin 'kauna dake 'kunshe a zuciyar Ammi game da shi, ashe tun asali farin ciki ta yana wanzuwa ne da tabbacin 'danta Muhammad na nan cikin walwala, ban ta6a sanin haka ba sai a wancan lokacin da lamarin ya faru.

Ni kaina ina so inga Ammi ta saki ranta ta dawo kamar da cikin sakin fuska da walwala, wanda hakan ya sanya ni niyyar zuwa can gidan dubo sa in kuma ce da shi Ammi na 'kiran sa, na shirya hakan cikin raina ne batare da na sanar da Ammi ba.



'Karfe 7:37 na safiya ina 'ko'karin fita daga parlour da tunanin ya zanje in tarar da shi, yanayin da na same shi da waccen yarinyar a wanacen ranar shine ya sake dawowa 'kwa'kwalwa ta, kenan idan tazo kullum abinda yake yi mata kenan, bana so in yawaita tuna yadda naga hannun sa na yawo saman 'kirjin ta dake bayyane a fili, bana so in tuna balle har in bada labari, amma na kasa mantawa, har yau 'din nan hoton yanda naga Yah Deen na shan boobs 'din Husnah ya kasa barin kaina, na kanji kaina wani iri aduk lokacin da tunanin hakan yazo raina....(Addu'ar Deeni bata samu shiga ba kenan tunda Noor bata manta abinda taga yana aikatawa ba).

Ko yanzun ma da nake shirin fita ina 'dagawa Ammi hannu tunanin da ya fa'do raina kenan, tsoron yau kuma a wani hali zan tadda shi, ba dan Ammi ba da babu abinda zai kaini wannan gidan, amma soyayyar Ammi cikakkiya ce cikin zuciya ta saboda ita da da kuma son dawowar walwalar ta dole na bawa kaina 'kwarin gwiwar zuwa gidan.

Addu'ah Ammi tai min kamar yadda ta saba idan zani makaranta" Allah ya tsare ya da sa'a autar Ammi".
Haka take yimin kullum, sa6anin yau da kawai cewa tayi " Allah ya bada sa'a sai kin dawo".
Abinda kawai na samu daga gareta kenan kuma ma cikin sanyin murya ta furta hakan babu wannan fara'ar nan balle ta iya yimin kirarin "......Autar Ammi" shiyasa naji cikin raina ko dan in samu cikakkiyar Addu'ar da take yawan yi min ma dole in tayata farautan Yah Deen yazo gare ta ta ganshi, wala Allah ko zata dawo dai-dai.

A hankali nake rakawa na tunkari  mafitar parlour ina gyara zaman babbar jakar dake rataye akafa'da ta wacce take cike tab da tulin takaddu na rubutu da kima textbook wanda Alhaji Baba da kansa ya aika aka siyo min su bai bari na yi rashin koda al'kalamin rubutu ba ne tunda na fara karatu a gidan sa, shiga na Jss one kuwa sai komai ya 'karu, uniform ma kala uku aka 'dinka min, safa na kusan kala biyar, canvas, sandal, tombs da kito mai kyau da tsada duk an tanadar min sai wanda naga daman anfani dashi nake sawa.

Sake gyara zaman jakar nayi karo na biyu dai-dai lokacin da na isa tsakiyar harabar gidan ina sake tunowa da Yah Deen, cikin raina nake ayyana " to meyasa zai yi purnishing Ammi akan laifin da ya san dagaske ya aikata ba sharri akayi masa ba?"
Da wannan tunanin na isa bakin gate ina shirin sa hannu in bu'de 'kofan sai naga an riga ni turowa wanda hakan ya sani 'dan matsawa baya ka'dan domin bawa mai shigowar damar shiga.

Lumshe idanu na nayi da jin yanda 'kamshin jikin sa ya buwayi hanci na take sai naji wata iriyar fargaba bansan ta menene ba, fuskar sa a hautsine ba ko alamun fara'a wanda a fizge na iya kallon yanayin fuskar ta shi take nayi 'kasa da idanu na ina fa'din " Ina kwana Yayah?"
Ko kula ni bai yi ba illah wuce ni da yayi  kawai yayi shigewar sa cikin gida.
Cikin raina na furta " Bazaka ta6a canzawa ba farin cikin Ammi".
Baki na na ta6e musamnan da na tuna yanayin da naga fuskar sa, a hankali na ri'ke 'kofan hannu na ban fita ba haka kuma ban rufe 'kofar ba, bayan sa nake kallo yanda yake ajiye takun tafiyar sa" Salon ka daban ne 'dan Ammi"
Na sake fa'di cikin raina, tafiyar Yah adeen ka'dai aji ne da ita, balle idan ransa a 6ace yakan 'karawa tafiyar sa wani salo na sanyi da natsuwa da shi kansa inajin bai san hakan na da matu'kar 'daukan hankali ba...sanye yake cikin riga ba'ka da godon wandon jeans shima ba'ki, suman kansa yasha gyara sai shai'ki yake yi musamman da hasken rana ya 'dan haske shi walwalin sa gwanin birgewa, 'kafar sa ma wata ba'kar takalmi ce mai tudu da igiyoyi da dama sosai ya amshi 'kafar sa, hannun sa babu komai sai Key holder na makullin gidan da yake zama sosai yaui kyau hasken sa ya kara bayyana cikin ba'kar dressing 'din nasa bakace yana tare da damuwar komai ba.

" Hmm"
Na saki ajiyar zuciyar tare da juyawa na sa 'kafa na fita daga gidan ina ayyana  " Allah yana sona sosai da bai barni naje wannan gidan ba ya ta'kaita min niyya ta".
A hankali na tunkari hanyar makaranta cikin tafiya ta ta masu natsuwa.

Ammi ka'dai ya tarar tsaye a palourn da yake yanzu ta gama sallama ta bata riga ta bar parlourn ba kuma dan yanzu Ammi komai cikin sanyin jiki take yin sa.

Tsaye take amma da ganin sa ya shigo sai ta saki ajiyan zuciya fara'a ta bayyana kan fuskar ta, komawa tayi ta zauna tana sakin ajiyar numfashi, cikin ranta take godewa mahallici da ya ta'kaita mata niyyar ta ya kawo mata shi har gida.

   Gefen ta ya 'karasa ya zauna kan kujera yana shafo sumar kansa da hannun sa na dama, yayin da Ammi ke binsa kawai da idanu ita ka'dai ta san me take ji cikin ranta game da shi.

Sai da ya daidaita natsuwar sa kafin ya gaida ta ganin irin kallon da Ammi take binsa da shi da bai san na menene ba.
A hankali da muryar masu hankali ya gaida ta yayin da Ammi ta amsa shi cikin sakin fuska da fara'ar ganin sa cikin 'koshin lafiya batare da ya illatu ta wani 6angare na jikin sa ba.

Fuskar ta wasai bayan ta amsa gaisuwar tace da shi " Me yasa ka 'dauki tsawon kwanakin nan baka le'ko mu ba Mu'een? Ko fushi kake nufin zakayi da mahaifin ka dan ya gaya maka gaskiya?"
'Dago kansa yayi sosai ya kalli fuskar ta yana 'kan'kance idanu yace" Haba Ammi...ya zaki ce haka please? Ni waye da zanyi fushi da shi? ni da nake 'dan gata, har na samu mai gaya min gaskiya wani ma fa nema yake ya samu irin hakan amma bai samu ba...so dan me zan yi fushi da mahaifi na?"
Yayi maganar cikin sanyin murya da natsuwa.

Ammi ma cikin natsuwan tana duban fuskar sa tace " To me ya hana ka zuwa bacin kasan dole ne mu damu da rashin ganin ka da sanin halin da kake ciki?"
" Kiyi ha'kuri Ammi,  amma ni kawai banson in 'kara 6ata ran Alhaji ne kar idan ya ganni ya sake harzu'ka shiyasa banzo ba".

Murmushi Ammi tayi da ya ratsa mata har zuciya sannan tace " Amma baka kyauta min ba".
" I'm so sorry Ammi na...kin san ai haka kawai bazan guji inda kuke ba".
" Ka kwantar da hankalin ka Alhaji bai yi fushi da kai ba...ya dai ce kawai muyi fatan Alkhairi".
Sakin numfashi yayi na jin da'di tare da fa'din " Alhamdulillah"
A fili tare da komawa ya kishingi'da da jikin kujera.

Ammi kuwa cigaba tayi da fa'din " Kwanaki uku kacal Mu'een amma ji bi ramar da kayi anya ma tun tafiyar ka ka 'kara cin abinci kuwa?"
Shima murmushin yayi tare da fa'din " Haba Ammi na, da bana ci ai da ban kawo wannan lokacin ba..."
" Banga alamaba ni".
Ta tare shi da fa'din hakan.
Sai yace " Hmm..Ammi agaban idanun ki fa Alhaji Baba ya sau'ke min yatsun hannun sa saman fuska ta alhali tunda nake da shi bai ta6a mari na ba tun haihuwa ta har sai yanzu da na girma na zama cikakken 'dan jami'ah mai shekaru ashirin har da biyar akai kinga kuwa dole in damu dan nasan abin ya ta6a ransa sosai".

Ido Ammi ta lumshe cike da jin da'din yanda yake bayyana gudun 6acin ran mahaifin sa a zahiri.
Fuskar ta cike da Annuree tace " ka kwantar da hankalin ka komai ya wuce har a wurin sa ma".
" I wish..."
Kai Ammi ta jinjina masa cike da tabbatarwa.
" Ni dai fata na Alhaji kar ya zarge ni da mummunan abu, Ammi kema ai  kinsan bazan aikata irin waccen abin ba sam".
Ya 'karasa maganar cikin marairaita ya wani yi kalar tausayi.

Tausayn kuwa ya bawa Ammi dan ta kwantar mai da hankali sai tace " Na sani kuma na yadda da kai, Alhaji ma na fahimtar shi kuma ya gamsu ka daina damun kanka...amma ka kiyaye karka bari ya sake kama ka da laifi makamancin wannan cuz a lokacin ko ni da kaina Mu'een bazan 'daga maka 'kafa ba".

" Insha Allahu ba abinda zai sake faruwa Ammi na".

Murmushin jin da'di tayi masa sannan tace " Allah ya albarkaci rayuwar mai sunan Baba na".
Yah Deen lumshe idanu na yayi yana jin wani sanyin da'di na ratsa shi har brain 'din sa, 'kaunar iyayen sa na sake ratsa shi zuciya da gangar jikin sa, baya fatan har abada ya kasance shine silan 6acin ransu.
    Shiyasa ko da wasa baya so ace sunji ainahin irin rayuwar da yake aikatawa balle su san cewa first kyautan da Allah ya bashi na haihuwa ta hanyar alfasha ya same shi sannan da kansa da kuma ku'din sa ya sayo maganin da ya narkar da shi ya zubar da shi a rariya...." *Astaghfirullah ya Rabb* "
Ya fa'di cikin zuciyar sa har launin idanun sa na sauyawa sakamakon tuno babban nawin zunubin dake kansa...zai iya aikata komai dan akan wannan sirrin cuz ya san bayyanar wannan maganar dai-dai yake da rugujewar farin cikin sa da na iyayen sa gaba 'daya...dan yasan baza su ta6a jin da'din faruwar hakan ba.

" Auntyn ka ta 'kira ni jiya da dare tace bata samun layin ka, idan ka samu lokaci please ka ta6o ta dan naji ta damu da rashin jin kan da batayi ba".

Ammi ce ta katse masa tunanin da yake yi da fa'din hakan.
Yana gyara zaman sa yace da ita " Insha Allahu zan 'kira ta....Alhaji fa?"
Ya 'karashe da tambayar ta mahaifin sa.

Sai da ta juya ta kalli mashigar 6angaren Alhajin kafin tace " Yana ciki yau be fito da wuri ba kam..".
Tsaye yayi saurin mi'kewa shima yana fa'din" Bari inje mu gaisa kafin ya riga ni fitowa".
Itama Ammi tashi tayi tsayen tana

Please Login or Register in order to submit comment