Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta kalle shi tana girgiza kai tace" Ba haka bane  Abbah..Mummy fa bata ce da ni in ce ban yadda da za6in ka ba..."

Tun kan ta rufe baki yace" To ai shikenan..sai ki je ki jira ranar 'daurin auren dan ba dogon lokaci za'a saka ba,  mahaifan sa sunce min already kun daidaita kanku da yaron dan haka ba wani abinda zamu jira... daga Shuwarin suka zo wai sunan sa Muhammad...sai kije ki bincika cikin maneman ki babu mamaki kiyi saurin gano shi".

Sum-sum ta tashi tana juya sunan cikin ranta da matu'kar mamaki sai taji yace" Yauwa tunda kin riga kin dawo to babu kuma batun komawa sai bayan auren, idan mijin ki ya yarje miki komawa Falillahil hamd in kuwa yace a a shikenan sai ki fawwalawa Allah kinji?"

Kai ta 'daga masa alamar " Erh taji".
Sannan ta juya ta 'karasa fita daga 'dakin nasa wanda ada ya kasance 6angaren mahaifin ta ne.

Yanda 'karara wan mahaifin ta ya nuna rashin damuwa kan halin da zata shiga ya nuna rashin damuwar sa kan farin cikin ta ko akasin haka yasa a daren ranar sai da ta sha kuka amma babu wanda ya sani daga ita sai Allahn ta ne ka'dai da ta gaji ta lallashi kanta.

Shiyasa yanzun ta damu sosai wajen ganin ta same shi a waya, tafara gano kamar shi 'din ne amma bata da hujjar gaskatawa inba taji daga bakin sa ba....ko kashe wayar tasa ma sai take ganin kamar yana da nasaba da faruwar maganar auren amma duk tayaya zata gaskata hakan?..No way".

Ta riga ta san halin sa da kafiya da kuma bakin hali in ba dan haka ba da ko wata friend 'din zata 'kira tace a kai masa waya suyi magana amma tasan inba ra'ayi yayi ba Mu'een ba zai ta6a ansan wayar ba sai dai a idon 'kawartata yayi 'karyar ta bari zai 'kira ta kawai.

Ishaq ne ya fa'do mata cikin ranta, sai kuma ta tuna bata da contact 'din sa..haka ta zauna tayi tagumi tana tunani ta ringa sa'ma sa'ka abubuwa tana kuma warware su da kanta.


*****
      Shi kuwa Mu'een har lokacin ya 'ki 'daga wayar ta sa ma a inda ya wullata balle ya kunna ta, haka zai yi duk abubuwan da suka zame masa dole ya yi shirin sa ya wuce makaranta ko kallo wayar bata ishe sa ba, wani sa'in ma bai zuwa makarantar sai dai ya yini a gida yana tunani...Ishaq ne yafi damuwa da lamarin sa, cuz sosai ya fahimci akwai abinda ke damun sa da yake so ya hana shi sukuni yake kuma faman 6oye musu.

    Watarana da bai shiga school ba sai Ishaq da Imran da wani abokin su Anas jibo suka taho gidan sa dan duba shi dan sau tari idan basu gan sa ba suka sha gwada 'kiran wayar sa amma bata tafiya dole suke hakura su bar sa.

Yau kam Ishaq yace suje gidan su dubo shi, tun zaman su da shi kuwa ranar shine rana na farko da suka ziyar ce shi har gida, yau din ma bazata suka yi masa da yake already sun riga da sun san gidan, Mu'een bai ta6a basu daman zuwa inda yake ba ko da wasa.

Da sallama suka shiga gidan inda suka zarce har ciki.

A palour suka tarar da shi kwance fuskar na kallon ceilling, jikin sa kuwa ko singlate babu balle riga wandon jikin sa ne dai dogon ba'kin jeans ya sanya...hannun sa 'daya ya lan'kwaso ta ta ratsa ta saman fuskar sa yayin da 'dayan kuma ya dafe saman 'kirjin sa da shi.

Wanda Ishaq da yake yafi son shi da damuwa da shi yana ganin sa a haka yayi saurin zuwa gare shi inda ya taho yana fa'din" Me ke damun ka ne  gaye har haka please?"

Yana jin tun daga yin sallamar su har isowan su kanshi amma ya kasa 'daga idanu ya dube su duk kuwa da cewa ya gane su, amma haushin zuwa masa da suka yi yasa yayi luf kamar mai bacci... 'kofar gidan ma sa'a suka ci da ya dawo daga masjid 'dazu ya manta bai kulle ta ba, amma ba dan hakan ba inda ace bugawa zasu yi to da kuwa ko kwana zasu yi suna bugawa ba zai ta6a tashi yaje ya bu'de ba sai dai su ha'kura suyi tafiyar su.

Gefen sa Ishaq ya zauna ya dafa hannun sa dake kan fuskar tasa yana sake tambayar " wai lafiya kuwa?"

Hannun ya 'dauke a hankali sannan ya bude idanun sa ya kalli Ishaq dake gefen sa, Ishaq gani yayi idanun sa sun koma jajazur tamkar ba nashi ba" Subhanallah"!
Ishaq yace a fili yana tattare goshin sa sannan ya sake fa'din " Me ke damun ka dan Allah Mu'een?"

Bai kula shi ba sai ya 'dan juya idanu ka'dan a 'dan fizge ya kalli Imran da Anas dake tsaye sai ya sake maida hannun sa kan fuskar ta sa ya rufe idanun sa.

Cikin dauriyar magana yace da su" Ya studies?"
Anas ne ya amsa da " Alhamdulillah".
Yayin da Imran ya jinjina kansa kawai yana 'ko'karin zama kan kujera...Ishaq kam baki bu'de yake binsa da kallon mamakin yanda ya koma a 'yan kwanaki 'kalilan din nan.

Duk yadda Ishaq yayi 'ko'kari wajen gano abinda ke damun sa amma Mu'een ya'ki sake furta komai sai da ya ga kamar hankalin Ishaq kwata-kwata bai kwanta da ganin sa hakan ba shine yayi dauriyar fa'din" kar ka damu babu abinda ke damuna".

Ishaq bai yadda ba sam amma haka ya 'kyale shi, har yamma suna tare da shi, tare suke zuwa Masjid su dawo amma babu wata hirar kirki ta 6angaren sa, sai bayan Sallar Maghrib kafin suka yi masa sallama suka wuce cikin makaranta.

   Sam bai damu ba shi kam, dama dauriya kawai yayi  amma wanzuwar ta su ba 'karamin takura shi yayi ba a gidan, surutun su na damun sa sosai da ya samu suka tafi kuwa sai da ya sau'ke ajiyan zuciya na jin dafi, har girki Anas yai musu suka ci amma shi Yah Deen bai ra'ayin abinci sam-sam, hakan yasa bai ko yiwa abincin nasu kallon arzi'ki ba.

Sai bayan ya dawo daga sallar Isha'i kafin ya ha'da Tea ya sha yayi kwanciyar sa....har a lokacin bai yi tunanin le'ko inda ya yada wayar tasa ba.

A kwanciyar san nan nema Ammi ta fa'do ransa sai yaji yana so yayi magana da ita 'kilan ko akwai taimakon da zatayi masa wajen hana faruwar auren.

Amma yanda yasan Alhaji Baba yasan Ammi bazata iya dakatar da shi ba...hakan yasa shi gyara kwanciyar sa da kyau batare da ya tashi ya 'dauko wayar ba...cuz ya lura babu amfani yin 'kiran ma.

Haka ya cigaba da rayuwar sa cikin 'kunci da damuwa kan auren da ake shirin yi masa, ya kan shiga school amma ba kullum ba sai ranar da ya ga daman hakan, su Ishaq ma yanzu na yawan zuwa gidan duba shi musamman idan suka ga shiru bai shiga school 'din ba, cikin hakan har suka samu Mu'een ya bayyana musu damuwar dake damun sa wato auren da mahaifin sa ke shirin yi masa sai dai bai fa'da musu ko wacece ba dan shima bai gama tabbatar wa ba tukunna.

Ishaq sun matu'kar tausaya masa amma hakan bai hana su bashi 'kwarin gwiwa akan kar ya bijirewa mahaifan sa ba ya daure yayi musu biyayya 'kila sai yaga auren yayi albarka ya kuma zame masa abin alfahari.

Yah Deen kam jin su kawai yake yi wani lokacin kuwa sai yayi murumushin takaici da gefen bakin sa..." Wai auren sa da Husnah ne zai zame masa abin alfahari"
In ji shi yace" Banga alama ba".


Duk da ko da ace a giyar wake itace abincin sa a kullum dama bai isa yace zai ja da maganar Alhaji ba, zai nuna baya so cikin harkokin sa, zai iya sanar da Ammi bai so, haka ma Uncle J musamman da ya fahimci cewa har a lokacin bai san labarin asalin abinda ya faru ba...Amma ga Alhaji Baba kam...a a dole ne zai yi masa biyayya ko ma dan kar ya 'kara masa 'kunci kan wanda ya 'kunsa masa abaya.

Wani sa'in ha'kuri kawai yake yi amma baya son zuwan da su Ishaq ke yi gidan sa gani yake suna takura masa ne sosai.

A hakan ma wataran da gangan yake rufe 'kofar ta ciki yana jin su suyi ta bugawa amma motsin kirki bayayi balle asa ran zai tashi yaje ya bu'de musu....ya kai kusan sau biyu hakan na faruwa haka zasu zo su koma batare da sun ha'du dashi ba duk bugun da zasu yi wa 'kofar gidan kamar babu wani abin halitta mai rai dake rayuwa cikin gidan baza'a bu'de musu ba, haka zasu ha'kura su tafi suna masu trying layin sa amma har lokacin bata shiga bai ko tattare wayar a inda ta fa'di ba balle aje ga batun kunna ta..Ishaq kuwa har ransa dan su ringa rage mai yawan tunani ne yake sanyawa gayyato su Imran su taho.

Mu'een kam bai ko damu da yawan mutanen da ke neman layin sa basa samu ba, duk da yasan dole dama za'a neme shi, musamman Ammin sa da Uncle J, amma ya zam masa dole ya nuna musu 'karara shi ba ya son auren nan, wanda ganin sa hakan ma ka'dai ya isa ya bayyana meke cikin ransa.

To Husnah fa da sauran mutanen da zasu neme shi? Wa'dannan duk basu dame shi ba kwata-kwata, bai ma sasu cikin tunanin sa ba, in sun gaji da neman layin nasa kowa ya ha'kura kawai..acewar sa.




*****
   Kamar yadda aka tsara... sati na cika su Alhaji suka koma shi da Uncle J da yake har ranar bai koma ba inda suka tafi da duk wani da duk wani da suka san za'a bu'kata ranar...bayan ganawar su da Alhaji Mamman sai aka sanya lokacin biki sati uku masu zuwa kacal...Uncle Ja'afar ne ya biya sadaki dubu 'dari cif   sannan suka koma gida.


Uncle Ja'afar kam washe garin da aka basu auren yayi shirin sa tsaf domin ya tattara ya koma Jalingo a fa'dar sa wai sai lokacin biki ya 'karato sannan zasu dawo da iyalin sa cuz shi zai kar6i auren matsayin waliyin Mu'een.

Shi kansa ya damu da rashin samun Mu'een a waya duk da ma ya san iskanci ne ya sashi rufe wayar tasa amma duk da haka ya kasa daurewa da da hakan.

Da farko ya so ya share shi amma zuciyar sa ta kasa aminta hakan tausayin Mu'een ya fara kama shi, dan zuwa yanzun ya fara yadda cewa ba da yardar sa Alhaji Baba ya shirya wannan auren ba.

Wannan tunanin ne ya sa shi yanke shawarar sake komawa Jigawa ya ganshi kafin ya wuce amma Alhaji Baba bai bashi damar hakan ba yayi masa katsalandan da cewa zasu je Jos tare da shi su duba Gidan gonar Alhajin dake can in yaso daga Jos 'din sai ya wuce abinsa Taraba.

Hakan kuwa akayi dan tare suka yi tafiyar suka dira Jos wurin Baban mu, inda suka tarar abubuwa na tafiya normal babu matsalar komai, sosai Baban mu ke 'ko'kari wajen kulawa da amanar da aka dan'ka masa.

Da yaji labarin batun auren Yah Deen kuwa cikin farin ciki ya ringa sanya albarka yana fatan Allah ya nuna musu lokacin suna cikin rayayyu.

A ranar Uncle J ya wuce Taraba yana mai sake dialling number Mu'een amma baya samu zuwa lokacin kuwa abin nasa sosai ya fara bashi haushi,  dan haka sai ya yayi fushi ya share sa bai ko sake gwada 'kira ba har ya isa gida.

Alhaji Baba kam kwanan sa 'daya ya dawo gida cikin farin cikin yanda yaga dukiyar sa na 'kara habbaka wurin Baban mu...wanda kafin rabuwar su Baban mu sai da yayi alkawarin insha Allahu kafin ranar auren zai zo ayi komai da shi Alhaji Baba sosai yaji da'din jin hakan kuwa duk da cewa shima auren ba wai ya kwanta masa bane amma gani yake yiwa Yah Deen auren shine babbar mafita saboda gudun fitinar shai'dan da kuma abinda zai biyo baya.


Lamarin da ya matu'kar 'daga hankalin Husnah shine jin wai ansa ranar bikin ta kuma kwanaki 'kalilan, ba 'karamin tada hankalin ta hakan yayi ba gashi har a lokacin ta kasa samun sa a waya balle taji ta tabbatar da cewa shi 'din ne ko kuwa wani daban ba.

Abin ya dame ta sosai, gashi Abbah ya hana ta komawa Jigawa wai har sai bayan bikin, badan haka ba ai da taje sun magantu da shi, fitan kirki ma yanzu bata yi Alhaji Mamman ya hana ta zuwa ko'ina. 

Da farko kamar abin bazai dame ta ba amma daga baya har kuka take 6uya tayi cikin 'dakin ta bayan ta kulle gudun kar mahaifiyar ta ta ganta tana kuka damuwar ta ta ninku.

Wasa-wasa sai da aka share kwanaki goma da dawowar ta amma har ranar bata samun layin sa.



*****
       Yanda yaga Ammin sa cikin mafarkin sa na jiya da dare tana kuka da hawaye tana bin sa da idanu ne ya sanya duk jikin sa yayi sanyi 'kalau, har bayan ya idar da sallar asubah ma ya kasa warwarewa, photon scene 'din ya kasa barin kwanyar sa.

Yanzu ne ma yaga rashin kyautawar sa da yayi watsi da tunanin halin da mahaifan sa zasu shiga na rashin jin sa da basu yi ba...musamman Ammin sa da Anty Zainab ga kuma Uncle Ja'afar da yasan cewa sun fi kowa damuwa da shi, Alhaji Baba ne ka'dai bai sa ran zai neme shi ba saboda abinda ya faru kwanaki.

Jikin sa sanyi 'kalau ya isa ga wayar tasa inda ya watsar duk tayi 'kura kasancewar tun bayan tafiyar Husnah gidan bai sake samun gatan shara ba ko'ina in ka duba zaka gansa futu-futu illah bedroom 'din sa ne yake iya kintsawa shima 'din dan acan ya fiye zama ne shiyasa, ranaku 'da'dai ku ne zaka gansa kwance a palourn sa.

Ko da ya rufe wayar ya kunna ta sai yaga babu caji sannan fuskar wayar ya tsatstsage, mi'kewa yayi ya isa ya saka wayar a caji tare da zama gefen ta ya rafka uban tagumi yana bin wayar tasa da kallo zuciyar sa fal da tunanin Ammin sa.

Tsawon mintina 30 yana a haka sannan ya cire wayar yana 'ko'karin shiga dan 'kiran Ammin yaga duk bata 'daukan hannun sa saboda fashewar da tayi, da 'kyar ya samu da dabara ya yi dialling numbern nata tare da 'kara wayar akunnan sa yayi shiru yana jiran ta 'daga.


Ringing biyu ana uku sai aka 'daga tamkar dama zaman jiran shigowar 'kiran nasa akeyi...dan Ammi yanzu bata ta6a yin nisa ta bar wayar ta.

Shiru Ammi tayi duk da irin jin dadin da ya shige ta da ganin kiran sa yau a wayar ta, sai da yayi sallama sannan Ammi ta amsa masa ciki-ciki kamar dole aka sanya ta amsawa.

Gaida ta ya fara cikin kwantar da murya da tunanin 'karyar da zai shirga mata akan rashin samun sa da ba'a yi ba tsawon kwanaki...sai dai kafin ma ya 'karasa furta gaisuwar Ammi sai tayi saurin dakatar da shi da harshen su na Igbo tace" Sai yau ka ga daman tunawa da ni kenan ko Muhammad?"
Da sauri ya girgiza kansa tamkar a gaban ta yake tare da fa'din" Ba haka bane Allah Ammi...am sorry..wayar tawa ce ta lalace amma Ammi believe me kullum kuna cikin raina".
Inda ya bada amsa cikin harshen Hausa kamar yadda ya saba a duk lokacin da tayi masa yaren Igbo baya ta6a mayar mata amsa da yaren sai dai ya canza harshe zuwa wani yaren daban turanci ko kuma Hausa.

Tun lokacin da naji 'karar ring 'din wayar Ammi na farka daga baccin da nake yi har tazo gefen bakin gado ta zauna tana amsa wayar da hannun ta 'daya a 'kirji..ido kawai na tsura mata da son jin da wa take wayar domin babu mamaki 'daya daga cikin yaranta ne da yake duk basa gida a lokacin.

Sai dai jin da nayi ta ambaci suna Muhammad yasa na gane da wanda take wayar kasancewar mutun 'daya tak nasan take 'kira da wannan sunan baya ga shi kuwa sai dai wani daban can da ba 'dan gidan ba.

Ido na tsura mata ta baya ina sauraran maganar tasu cuz har abinda yake fa'di tar inajin sa dan wayar Ammi akwai lafiyar speaker mai 'karfi sosai...bansan me yasa yake son wahalar da Ammi ba shi Yah Deen sam, domin bazan manta ba ya ta6a yi mata irin hakan lokacin ma yana cikin garin Shuwarin Amma karkiga yanda Ammi ta damu sosai sai gashi wannan karan ma ya sake maimaitawa, yanda nasan Ammi ta damu da rashin sa wallahi nima sai da naji wani sanyin da'di a zuciyata bayan fahimtar cewa shi 'din ne yayi 'kiran ta, a hankali na ja jikina na kwantar da kaina bisa cinyar Ammi zuciya ta cike da farin cikin daga yau Ammi na zata dawo Ammi ta asali.

Hannun ta dake kan 'kirjin ta ta sau'ke shi a kaina tana shafa kitso na batare da mun yiwa juna magana ba.

Ammi bata wani iya dogon fushi da shi sam shiyasa ko yanzun ma tun daga kan amsar da yabata sai tace dashi " Amma me yasa ka 'dauki dogon lokaci baka gyara wayar ba bacin kasan mutane da yawa ne zasu damu da rashin jinkan...Antyn ka Zainab sosai ta 'daga hankalin ta tunda taji batun auren ka hankalin ta ya kasa kwanciya kusan kullum sai ta 'kira ni sai dai ince mata nima baka 'kira ni ba..me yasa kai sam kanka ka'dai ka sani ne baka damu da damuwar kowa ba ko?"
Tayi maganar hannun ta yawo a kan kitso na.

Sai yace
" Kiyi ha'kuri Ammi na.. insha Allahu bazan sake ba...ya su Alhaji Baba da su Zaidu".
A ta'kaice tace
" Zaidu suna school basu dawo ba"
Yace
" Owk...Alhaji fa?"
Sai tace dashi
" Ka 'kira shi mana".
Yace
" Toh zan 'kira shi Ammi na.."

Tun kafin ya rufe baki tace da shi" Hope kasan lokacin bikin ka ya 'karato ko?"
Take salon muryar sa ta canza zuwa wani iri yace da ita" Biki na kuma Ammi?"
A nutse tace da shi
" Erh mana ko kana nufin baka da labari?".

" a a Ammi Uncle Ja'afar ya sanar da ni cewa an tambayo aure amma bamu sake wata magana da shi bayan hakan ba".

" To sai ka 'kira shi mahaifin naka..may be zai yi maka bayani da kansa, amma ina jin 2weeks kacal ya rage a 'daura auren ma..".
Cewa yayi
" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un...Ammi wai wace yarinyar dan Allah?"
" Ni ta ya zan sani Mu'een, nima fa ba'a sanar dani ba har sai bayan da aka tsaida rana..amma an dai ce a Azare take 'kilan waccen yarinyar ce..ai kasan da batun tun kafin komawar ka...kuma kasan Alhaji baya canza maganar sa shi....".

Idanu na lumshe ina take kunnuwa na suka daina cigaba da sauraron maganar Ammi, jin wai zai yi aure...sam ban san yanayin da nake jin zuciya ta ba, na dai tsinci la66a na da furta" Barka"
'Kasan ma'koshi amma na kasa tantance manufata ta fa'dan hakan.

Ban ma san ya 'karshen wayar ta su ta kasance ba sai ji nayi Ammi na fa'din" Kitson ki ya tsufa sosai Hudah...anjima za'ayi miki ko manya ma kafin kuma lokacin bikin Yayan ku sai ai miki mai kyau ko?"

Sai lokacin tunani na ya tsaya inda na no'ke kafa'da tare da fa'din" Ni banaso Ammi".

Ammi sai tace
" To shikenan naji..amma zamu wurin Umman Saudah anjima sai tayi miki na bayan hannu ko ai nata babu zafi zan ma ce tayi miki manya kinji".

Jin haka sai nayi saurin 'dage kaina alamar to jin cewa Ummata ce zata min kitson.


Yah Deen kam suna gama waya da Ammi sai ya 'kira Alhaji Baba suka gaisa faran-faram...Alhaji bai nuna masa alamun komai na 6acin rai ba haka nan bai yi masa zancen auren ba kamar yadda shima Mu'een 'din bai iya ya tambaya ba...kafin suyi sallama sai Alhaji yace da shi nan da kwana ki goma yana bu'katar ganin sa a gida, wanda a lokacin zai yi dai-dai ne da sati guda kafin ranar 'daurin auren.

Bai yi musun komai ba kamar yadda bai nemi jin dalilin zuwan nasa ba illah " To Alhaji" da ya amsa shi da shi a takaice, har suka yanke 'kiran baii ya sake fa'din komai ba illah damuwar sa da ta 'karu.

Bin wayar yayi da kallo yana sake kallon sekannin da yin waya da mahaifin sa ta 'dauke su, dududu 43seconds ne, sa6anin baya da in suna waya sukan shafe a 'kalla mintina goma ko 'kasa da haka.

Tun suna waya da Alhajin yake kallon 'kiran Husnah amma bai 'daga ba ko yanzun ma kuwa da yake ri'ke da wayar yana tunanin yanda sha'kuwar sa da Alhaji Baba ta sami babban gi6in da ke nemen ta6a masa zuciya sai ga wani 'kiran Husnan ya shigo...ku ayyana yanda Husnah zataji bayan ta shafe kusan kwanaki goma tana neman layin sa bata samu sai a yau da ta samu ya kuke ganin zata ji...ai 'kira kam babu sassauci ta ringa yi tana 'karawa kenan.

Bai bi ta kan 'kiran da Husnah ke yi masa ba sai ya fara tunani tsakanin Antyn sa da Uncle Ja'afar wa ya kamata ya fara 'kira.

Layin Uncle Ja'afar ya 'kira shima da 'kyar dan wayar sosai ta tabu, sai dai ma Uncle Ja'afar bai 'dauki 'kiran ba, daman baya son masifar sa dan ya san dole sai yayi dama...shi yasa bai sake ba.

Daga 'kira 'dayan kuwa sai ya bar shi ya koma 'kiran Anty Zainab.

Wacce tana dauka ta fara fa'din
" Haba, haba Mu'een gaskiya baka kyauta mana ba, me yasa ka kashe wayar ka dan Allah bacin kasan za'a neme ka?"

" 'Dan murmushi yayi da bai kai masa zuciya ba kawai yadda Anty Zee ke bayani ne ya 'dan bashi dariya...
Sai yace" Anty ai kya tsaya mu gaisa tukunna ko?"
" a a bar wannan batun gaisuwar...baka san yadda hankali na ya tashi ba ne da jin wai an tsaida lokacin auren ka har ma ya kusa, ya akayi haka kuma Mu'een kai da kace min ba yanzu zakayi aure ba?"

Yana gyara zaman sa yake ce da ita
" Alhaji ne fa ya shirya wannan auren Uncle bai gaya miki bane?"
Tace" Ya min bayani amma gaskiya banji da'di ba, yace wai kai kace baka son auren Alhaji kuma yace masa kai ke bu'katar auren shiyasa zai yi maka me yasa hakanne to wai kaina duk ya kulle".

Idanu ya lumshe not knowing abinda zai ce mata, tsintan bakin sa kawai yayi da fa'din" Ni kaina bansani ba Anty..ni dai ki min addu'ah Allah yasa afasa dan Allah".

" Da gasken baka so kenan?"
" Har cikin zuciya ta Anty".
Sai tace
" Wallahi nima ji nayi auren bai kwanta min ba especially da bai kasance 'yar gidan Ammin nan ba gaskiya banji da'di ba ni kam...ita wannan 'din 'yar waye ce?"

" 'yar makarantar mu ce Anty".

" To Allah ya sanya Alkhairi.."

Bai ce da ita komai ba kawai ya yanke 'kiran tare da kife wayar tasa ya lumshe idanu.

Yana ganin 'kiran Husnah amma ya 'ki kulawa..tayi masa missedcall a 'kalla goma sha uku duk bai 'dauka ba, har hawaye take tsiyayarwa daga inda take tana jin tamkar tayi tsuntsuwa ta ganta gaban sa dan kawai taji me ze ce da ita.






Comment
Vote
Share





*Salmerh ce* 😍
💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)


By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *49*


Text ta tura mishi nan ma bata ga alamun ya kula ba, a hankali hawayen ta ya fara sau'ka saman kuncin ta tsabar haushin rashin samun response daga wajen sa, tunanin halin da yake shirin sanya rayuwar ta bayan ya gama da rayuwar tan ya sa itama a zuciye tayi jifa da wayar ta, sai na ta wayar ta tsaya ne iya kan tsakiyar gadon ta pillow ne ya tare ta bata 'karasa sau'ka ta ha'du da 'kasan tiles ba da anyi biyu.

Kwanciya tayi tana sake sakin wani kukan mai tsuma zuciya gwanin ban tausayi.

Ji take kamar zata yi hauka..sam ta rasa menene dalilin hakan, ina zata je ta samu sau'ki cikin ranta? ta rasa gaba 'daya, me zata ce da mahaifiyar ta wanda ba zai 'daga hankalin ta ba shima ta rasa kwata-kwata.


Mu'een ma 6angaren sa

Please Login or Register in order to submit comment