Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankali fiye da tunanin ta..."

Mummy kam bata iya tace mata komai ba ganin kukan da take yi, hannun ta kawai ta sake ri'kewa ga gam tana jin so da 'kaunar 'yar ta na sake ratsa ta, dama tasan Husnah me biyayya ce bazata ta6a cewa bata so ba...da yake bata wani fahimci maganar da Husnahn ta 'dauko da farko ba dan haka bata yi ko tunani akai ba.

Bata da damuwa ta 6angaren Hisham dan tasan bashi da matsala shi, kuma dama asalima yana matu'kar 'kaunar Husnah tasan ko yanzun ma ba zai 'ki auren ta ba.

Tana cikin tunanin nan likita ta iso inda take bayan gaisuwa sai kawai tafara aikin da ya kawo ta.

Ba'a 'dauki dogon lokaci ba Husnah ta samu bacci sannan likitar ta tafi bayan ta basu shawarwarin da suka dace wanda hakan yasa suka fita suka bar ta dan ta huta illah mummyn ta suka bari dake zaune gaban ta ta zuba uban tagumi tana kallon ta tana kuma juya maganganun da ta gama furtawa, tausayin Husnah take ji sosai, da kuma tausayin maraicin ta, ba 'karamin da'di taji ba da taji cewa Husnah ta kar6i 'kaddarar ta hannu bibbiyu, ta amince da auren Hisham, ita kanta Mummy zata fison hakan saboda Hisham nagartacce ne, abu 'daya ya rage mata a yanzu shine..kare daraja da martabar 'yar ta, dole ne ta tashi tsaye ta sake shiri tunda Allah ya riga ya ha'da auren.


Can gidan Alhaji Mamman kuwa zaune yake kan kujera shi da amaryar sa bayan sallar maghrib...dawowar sa kenan daga masjid sai ya tarar da ita zaune tana jiran dawowar sa, hirar su suke yi cike da raha tana 'kara ziga shi akan auren da tasa ya ha'da shi batare da shiri ba wanda har alokacin labarin auren bai isa kunnen shi wanda akayiwa auren ba.

Hajiya Kareema ma tunda taji batun auren hankalin ta ya tashi sosai, tayi mamakin dalilin faruwar hakan, tunda la'asar ta baro gidan bikin ta dawo gida batayi zancen da kowa duk da kuwa abin ya dame ta sosai, musamman da taga yanda Husnah ke faman rusa kuka duk saboda jin cewa da Hisham aka 'daura mata aure, duk itama sai ta ji ta kasa natsuwa sai dai bata tattauna zancen da kowa ba, burin ta kawai Alhaji Mamman ne, so take taji daga gare shi menene dalilin wannan sauyin bazata da yayin.

Sanin da tayi cewa duk inda yake da zarar maghrib tayi zaka same shi a gida matu'kar yana garin, hakan yasa da idar da sallah bayan tayi addu'o'i kawai ta kamo hanyar 6angaren sa....sai dai me..abinda taji Amaryar ta ke fa'di ne yasa ta fahimtar da bakin ta kan maganar auren kuma bisa ga wata manufa....cak ta tsaya daga bakin parlourn bawai tazo da niyyar tayi musu la6e ba ne a a, sai dai ta tsaya ne kawai dan ta fahimci maganar ta su da kyau...
"...kaga ai hakan yafi..kai da kanka idan kayi duba da kyau zaka fahimci me nake nufi...har a yanzu fa da sauran dukiyar yarinyar nan masu nawi  wanda ina kyautata zaton da zarar ri'ko da kula da ragamar rayuwar ta ya bar hannun ka ma'ana idan ta zama mallakin wani daban haka kana ji kana gani dukiyar ma zata bar wajen ka dan nasan ba bari zasu sake yi a hannun ka ba, 'kila ma mijin nata da kansa zai zuga ta su kar6e a wurin ka, amma idan ta zama matar 'danka na cikin ka kuma ai kaga still dai tana hannun ka sai yadda kaga damar yi da ita da dukiyar gaba 'daya, sai ma fa kaso ka bar ta ta cigaba da rayuwa wallahi..kana iya..."

Saurin taran maganar tata yayi da fa'din
" A'a zatayi rayuwar ta ba ruwa na da ita, dukiyar ne dai kawai 'kwalelen ta, musamman ma wancen gidan mai 'din wallahi nafi jarabtuwa da shi dan ba 'karamin riba ake kwasa ba, in kuwa ya bar hannu na ai shikenan kashin mu ya bushe...."

" Sai ka tashi tsaye da kyau idan baka san tonon asiri..in ma zata cigaba da rayuwa dole ne sai ka tsaya da 'kafafun ka dan kasan uwar ta ma akwai kinibibi...".

" Ke de ki barni da su kawai...ai kin fargar dani, ba 'karamin da'din shawaran nan ta ki naji ba, ni fa ban ta6a kawo hakan cikin raina ba balle nayi tunanin zai anfane ni..da yanzu na bayar da ita ga wani can da zai kayar dani.... gaskiya kanki naja sosai..."
Ya 'karshe da 'yar dariya.
Itama murmushi tayi tana gyara zaman ta..take fa'din" Saura Hisham shima..."

" Wannan ma barni da shi duk dama nasan bazai min gardama ba amma dai zan bishi a hankali dan ya fahimce ni da kyau..kar ya wargaza min shiri na so ma nake duk sunayen kan dukiyar su canzu daga nata zuwa mallaki na kuma kinsan hakan ba zai yiwu ba sai da amincewar sa matsayin sa na miji agare ta...".

Hajiya Kareema da ta kasa cigaba da sauraran su shigowa tayi batare da ko sallama ba kawai sai jin muryar ta suka yi tana fa'din
" Haba Alhaji..da girman kake shirin yin wannan ta'asar ga yarinyar da kake matsayin uba agare ta?...kaine fa babban wan mahaifin ta amma Alhaji ka kasa bata wannan darajar a zuviyar ka? Marainiya ce fa kai ka'dai take dashi amma fi sabilillahi saboda tsananin son abin duniya kake shirin sadaukar da farin cikin 'ya'yan ka? Wallahi tallahi wannan sam ba halin girma bane...ka ringa tunawa da ranar 'karshe..miye ribar ka kan aikata hakan dan Allah..idan fa kace shai'danun mutane zaka dinga biyewa wallahi har abada kwa6ar ka bazata ta6a yin kyau ba...".

Juyowa tayi kan Amaryar Alhaji tace da ita" Ke kuma ki sani ita rayuwar duniya 'yar 'kalilan ce, masu aikata alkhairi ma suna kokwanto bisa ga ayyukan su, a kullum tunanin su shin an kar6a ne ko kuwa an barsu da shi ballantana dumu-dumu ka dulmiyar da kanka cikin sharri ai da kanka kasan makomar sakamakon ka, kin sashi ya aurar da Husnah ga Hisham saboda son zuviyar ku... sai dai ku sani Allah yafi ku kuma nasan zai bata kariya, sannan nima ko ka'dan ban yi ba'kin ciki da hakan ba, kuma na yi al'kawarin kar6ar Husnah matsayin 'ya agare ni bazan ta6a bari ta sami gi6i cikin rayuwar ta ba, idan dukiya ce kuje can gata nan ai duniya ce..ku ci ta son ranku ku gina farin cikin ku da shi...shawara ta agare ku kawai shine ku ringa tunawa cewa Husnah marainiya ce kuma sannan haramun kuke ci wanda Allah zai tsaida mu akansa ya tambaye mu bisa hakkin ta da aka tauye ta...."


Tana gama fa'din hakan tayi gaba abinta, yayin da amaryar Alhaji ta ta6e baki gefe tare da hararan bayan Hajiya Kareema, Alhaji Mamman kam kai kawai ya sunkuyar yana jujjuya maganganun nata cikin ransa...amma koda wasa bai ji nadama ba.


Tana komawa sashin ta sai ta 'daga wayar ta ta 'kira Hisham...bayan sun gaisa sai tace da shi.." Hisham kasan yau ne 'daurin auren 'kanwar ka ko?"
" Na sani Mummy".
" Me yasa baka zo ba to..?"
Cikin natsuwa yace da ita
"..Afuwan Mummy...wallahi abubuwa ne suka sha kaina amma idan nadawo har gidan ta zanje in duba ta insha Allahu".

" Hisham!"
Yace " Na'am Mummy".
Inda yayi maganar yana me sake nutsar da kansa sakamakon irin yadda yaji ta 'kira sunan san yasan da akwai magana.

Cikin sanyin murya tace da shi" Har yanzu kana son Husnah ko?"

Idanu ya rintse tare da 'dora hannu bisa 'kirjin sa yana shafawa a hankali yana jin yadda sunan 'kanwar tashi ke ratsa masa gangan jiki...a hankali ya furta" haba mummy..me yasa zaki tambaye ni hakan bacin kinsan yanzu ita mallakin wani ce?..duk abinda zan fa'da yanzu zai iya zamowa laifi wurin ubangiji mummy...fatana kawai shine Allah ubangiji ya basu zaman lafiya ya albarkaci auren su ya ha'da kan ta da mijin ta".

Da" Ameen" ta amsa shi sannan ta 'kara da fa'din" Hisham gobe nake so kazo gida please we need to talk...."
Yace
" Kuma har sai nazo gida Mummy?"
Sai itama tace
" Hakan nafi bu'kata in da hali".
" Insha Allah zanzo goben Mummy idan Allah ya kaimu".

" Allah yasa".
Ta fa'di cike da jinda'din sau'kin halin da 'dan nata ke da shi..lokuta da dama takan gode wa mahalicci da ya azurta ta  da samun nagartaccen yaro irin Hisham sam bai gaji halin mahaifin sa ba.

'Yar hira ka'dan suka yi wanda tayi saurin yi masa sallama da jin ya fara tambayar ta abinda ke damunta, cuz a muryar ta ya fahimci tana tare da damuwa amma bata sanar da shi ba sai ma sallamar da tayi masa...hakan ne ma ya 'kara masa kaimi wajen ganin ya taho goben duk da kuwa bai shiryawa hakan ba, amma sam baya son yji ko ganin mahaifiyar sa cikin damuwa.


Hajiya Kareema kuwa tun daga lokacin ta yiwa kanta al'kawarin yiwa kanta komai da dukiyar ta tunda tasan babu haramun a ciki, bazata 'kara bari Alhaji Mamman yayi mata komai da kansa ba sanin da tayi cikin dukiyar sa akwai son zuciya.



*****
   'Bangaren Yah Deen kuwa bai sake tada maganar auren ba, har yamma da suka je can gidan gaisuwa sai anan ya fahimci fuskar Alhaji Baba da ke 'kunshe da annahuwa wanda kallo 'daya zaka yi masa ka fahimci tun daga zuciyar sa ne.

Bai yi mamaki ba cuz tashin farko ya ayyana cewa ai shima dama ba wani son auren yake ba kawai 'karfin hali ne, ga shi yanzu da aka fasa ai shima yaji da'di...har ya kasa 6oye farin cikin sa.


Ya ayyana hakan ne kawai kuma saboda hakan aka sanar da shi, amma sam a zahiri bai ga wani alamar fasa aure tattare da yanayin gidan na su ba, dan akwai wani abokin Alhaji da ke can Jos yana so ya koma ma a lokacin amma harda tsayawa ya yi masa nasiha kamar gaske.

Shi dai Yah Deen yaji shi ne kawai bawai dan nasihar ta shiga kansa ba...gani yake kamar rashin abinyi ya sanya mutumin yi mai nasiha baya ga haka menene ze sa hakan tunda ba auren ne akayi masa ba.


Ko cikin gida da suka shiga bai ga alamun sauyi ba, hidindimun su kawai suke yi hankali kwance...Yah Deen kam sai ya ta6e baki gefe bai damu ba cikin ransa ya ayyana" Kwayi ku ha'kura ai".

Basu da'de ba suka koma gida shi da su Ishaq wanda suke shirin komawa Jigawa washe gari, shima Yah Deen 'din ya riga ya tsara cikin ransa cewa tare zasu koma a goben tunda babu batun auren gara yaje yaci gaba da karatun sa yafi masa.


Sai dai hakan bai yiyu ba, dan Uncle Ja'far ne da kansa ya hana shi tafiya yace ya bari sai next week sannan zai koma...yaji haushin hana shi tafiya da akayi hakan yasa ya ro'ki Ishaq da fa'din dan Allah su bari to ranar Sunday sai su tafi,  basu yi masa musu ba kuwa suka amince.


Ranar Asabar da safe nayi shiri na da wuri nace da Ammi zanje in gaida Baban mu da yake tunda  yazo 'daurin auren bmu ha'du ba..to tunda bai koma ba gara inje mu gana da shi...hakan yasa nake ta 'dokin zuwa in ganshi dan na kwan biyu ban gan shi ba.

Atamfa ta sabuwa fil na sanya a jikina Ammi ta bani mayafi sabo dal shima na rufa a jiki na...kayan biki dangin flour ta cika min a leda tace in kai wa Ummah ta tare da fa'din in gaida su kuma banda yawo tace min inda ya dace kawai zanje banda shige-shige nace to Ammi.




_Comment_
_Vote_
_Share_





*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)


By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *54*

Daga nan nayi musu sallama Anty Zee na ko'da ni ina murmushi na fita.

A harabar gida na ci karo da su Alhaji Baba da yaran sa, wato Yah Deen da abokan sa...ban san me suke tattaunawa ba sai dai ga dukkan alamu shigowar su kenan... na tabbatar da hakan ne lokacin da na kusan isa inda suke naji suna faman mi'ka masa gaisuwa inda yake amsa musu da fara'ar sa hannayen sa duk na cikin babbar rigar sa amma kallo 'daya zaka yi masa ka tabbatar ba shi tare da damuwa...fara'a fal a fuksar sa har kana iya hango hasken ha'koran sa afili.

Da gani na sai ya maida hankalinsa wuri na ina gaida shi ya amsa tare da 'karawa da fa'din" Uwata ina zuwa da sssafe haka?"

" Murmushi nayi sannan na 'daga kai na dubi harabar gidan inda duk rana ta mamaye ko'ina..." Ba sassafe bane fa Alhaji Babba kalli fa yanda rana ma tayi".
Na fa'di ina murmushi tare da nuno wurin.. shima Alhaji sai yayi murmushin..sannan ya sake fa'din unguwa zaki ne?"
Nace" Nace a a zanje in gaida Baban mu ne ".

Sai yace
" Ya kamata kam..dan inajin gobe ma zai koma...amma ki bari ba yanzu ba kinji maza ki koma cikin gida".

" To" kawai nace da shi tare da 'daga kaina na kalli su Yah Deen da ke tsatstsatye wanda da shi na fara ha'da idanu sai naga ya ta6e baki tare da kawar da kansa gefe, bansan me nayi masa ba dan haka sai nima 'dauke kaina daga kallon sa zuwa na gefen sa (Anas) shi kuma sai naga yana min murmushi ban damu ba kawai a jimlance nace da su " Ina kwanan ku?"
Mutun biyu zuwa uku ne daga cikin su suka amsa min wanda cikin sun kuwa ina da tabbacin babu Yah Deen a ciki.

Juyawa nayi na fara tafiya zuwa cikin gida yayin da Alhaji Baba ya nufi hanyar fita tare da 'kiran sunan Ishaq da alamun yana so su ke6e da shi, Ishaq sai ya bi bayan sa su Yah Deen kuwa cikin gidan suma suka 'karaso dan gaida su Ammi...in tafe suna bina abaya amma tsakani na da su akwai 'yar tazara ka'dan...ledan hannu na na gyara dan ya fara min nawi hakan yasa na 'dago shi zuwa saman 'kirji na na rungume dalilin hakan yasa mayafin da ke rufe da jiki na ya kame min jiki sosai...bansan da faruwar hakan ba sam illah tsinkayar muryar Yah Deen da naji a tsawace yace" Ke...wani irin hauka ne wannan kuma?"

" Ke" da naji ya furta cikin maganar tasa ne ya sani tsayawa cak sannan na waigo dan ganin shin da wa yake.

Kicin-kicin naga yayi da idanu hakan yasa nayi gefe da nawa idanun ina jiran jin irin haukar da yace nayi...." Gyara mayafin ki".

Ya sake furtawa still suna tunkaro ni...sai a lokacin ma na 'dan fahimci abinda ya faru take sai kuma naji tsananin kunya ta lullu6e ni, tfiya na cigaba da yi ina me gyara mayafin nawa...shi kam haushi sosai ne ya cika shi da be san dalili ba...tunda ya tsinkayi irin kallon da su Imam ke bin baya na da shi yaji tsananin 6acin rai ya shige shi..sai da kuma yayi mata masifar sannan yaga wautar sa, to shishshigin miye kuma nayi?"
Ya tambayi kansa...'yar 'karamar tsaki ya saki a fili da yasa duk 'yan tafaiyar tasa suka kalle shi...dariya m ya bawa Anas sosai dan abinda yayin da yanda yayin tashin farko zaka fassara hakan da tsananin kishi ga wanda yasan asalin tushen kafuwar 'kauna.


Ina shiga parlour sai Anty Zee ta kalle ni da mamaki baki bu'de take min kallon ya haka?
Bance da ita 'kala ba har sai da na iso gefen ta na zauna sannan ta furta" Kin fasa zuwan ne kuma?"

Kai na girgiza mata tare da fa'din" Alhaji Baba ne yace ba yanzu ba".

" Ow woh...sai ki huta abin ki kafin lokacin da ya tsara 'din tayi..."

Bata gama rufe baki ba sai ga sallamar su Yah Deen da tawagar sa...tun ma kafin su 'karasa shigowa na mi'ke tsaye na nufi hanyar 'dakin Ammi da sauri na, ba naso in ha'da idanu da kowa daga cikin su bayan sun gama kalle min baya.


Zazzaunawa suka yi suna gaida Anty Zainab inda take amsawa da fara'ar ta...tana duban Yah Deen tace" Tunda yanzu kayi auren ka sai ka daina firgita mana yarinya kuma ko..kana gani fa yanzu da jin sallamar ku ta tashi ta gudu ciki..."

" Ni ina cin mutane ne Anty da zata guji inda nake?"
" Ni na sani maka ne..ga dai zahiri yanzu...kuma wallahi kabi a hankali in ba haka ba in kayi wasa ita zamu aura maka a ta biyu".
" Ai kuwa da kun kyauta masa Anty".
Cewar Anas yana 'yar dariya.
Anty ma murmushi tayi tana duban sa tace" 'yale shi mana ana masa gata yana min yanga".
Shi kam Yah Deen " Hmm"
kawai yace sannan ya 'kara da fa'din " Ina Ammi take?".
Anty ce ta bashi amsa da fa'din
" Tana ciki yanzu zata fito ma ai".

Nima acan 'daki na sami Ammi inda itama tace dani" ya kika dawo kuma me ya faru?"
Tayi maganar tanacduba na da kulawa da son jin ko wani abin ne ya hana ni tafiya
Sai nace da ita" Inji Alhaji Baba ne wai in bari ba yanzu zani ba".

" Saboda me yasa to?"
Nace
" Nima ban sani ba".
Inda nayi maganar ina cire mayafin da ke kaina.
" Ikon Allah".
Ammi ta fa'di da mamaki harda kama baki.

Ni kam ban damu ba nayi kwanciya ta tare da 'daukan abin da muke buga game ni da su Saif na fara bugawa batare da damuwr komai ba, dan nasan hakan bai ta6a faruwa ba, 'kila akwai dalilin da yasa Alhajin ya fa'di haka a yau 'din.

'Yar hira suke yi sama-sama da su har Ammi ta 'karaso nan duk suka gaida ta sannan suka cigaba da hira.

A can waje kuwa Alhaji Baba duban Ishaq yayi yace" Ya maganar mu?"

" Tana nan Alhaji..babu wanda ya sanar da shi har yanzu".

Murmushi kawai Alhaji Baba ya saki...sannan yace baka gane wancen yarinyar ba ko?"

" Erh gaskiya ban gane ta ba amma ina dai ganin ta agidan nan jifa-jifa".

" Itace Amaryar taku ai, kaga itama har yanzu bata san da maganar auren ba shiyasa na ce ta koma gida kar ra fita."

Take fara'a ta bayyana kan fuskar Ishaq yana murmushi yace" Masha Allah...Ubangiji Allah yayi albarka Alhaji..godiya muke da wannan za6i Allah ya 'kara girma".

" Ameen..Ameen..zan sanar da su da kaina idan naga dacewar lokaci insha Allahu..."
" To Alhaji hakan ma yayi..Allah ya
'kara girma"
Cewar Ishaq..Alhaji Baba kuwa cewa yayi
" Goben zaku koma ko?"
" Erh hakan da muka ce idan Allah yaso".
" Bakomai Ubangiji Allah ya kaimu goben...ka shiga ku gaisa da matan gidan tukunna ".
" To Alhaji".
Ya furta cikin girmamawa tare da juyawa ya koma ciki.

Da isar sa kuwa ya tarar da su kan maganar Fitan da Alhaji ya hanani wanda Ammi ce da kanta ta fara kawo maganar saboda tsananin mamakin da ya cikiu

Sallamar Ishaq ne ya dakatar da maganar da Ammi ke yi cuz ita kam sosai tayi mamaki, batun yau nake fita unguwa ba amma bai ta6a magana ba bai ta6a hanani zuwa ko'ina ba sai yau ka'dai, sannan kuma duk iya tunanin ta takasa hasko musababbabin faruwar hakan.

Ishaq kam da ya san dalilin kawai sai yake ta sakin murmushi, yanzu ne ya fahimci cewa dagaske babu wanda yasan auren dake tsakanin Deeni da yarinyar can, illah su Alhaji Baba...shi dai farin ciki kawai yake taya abokin sa da dacen da yayi...yasan ko shi da kansa aka bawa za6i a irin wancen lokacin ba zai iya za6o irin yarinyar ba, tashin farko ya fahimci natsuwar dake tattare da ita...ha'ki'ka Mu'een yayi dacen samun mace a duniuar nan.

Basu da'de tare da su Ammjn ba suka koma can gidan Yah Deen.



*****
'Bangaren Ma'u kam abin tausayi bata bari taje gida tana kuka ba, kuma sai tayi sa'a lokacin da ta isa gidan matar Baban ta ta shiga ma'kwabta, tana shiga sai ta wuce 'dakin ta ta kwanta tana faman bibiyar lamarin cikin ranta, bata da'de ba bacci yayi gaba da ita saboda maganin da ya bata mai 'karfi ne...ba ita ta shi ba sai kusan maghrib...Allah da ikon sa kuwa duk sai taji ciwon ya ragu...wanka ta sake yi tana ta 'ko'karin daidaita kanta gudun kar a fahimci yanayin da take ciki...matar baban ta sai mita take yi wai tun 'dazu ta tsaya baccin asara bata yi musu ko wanke-wanke ba.


Bata damu ba ita dai burin ta kawai kar a fahimci abinda ya faru tsakanin ta da Deeni kafin ya dawo neman auren ta kamar yadda yayi al'kawari.

Tana yin sallahr la'sar ta dawo ta tattara wanken-wanken ta wanke musu tas ta sake komawa 'dakin ta..tunanin ta kawai shine zuwa yaushe Yah Deen zai zo neman auren ta.

Bata sani ba ashe shi kam ma har ya manta da ita, balle tunanin auren ta...abinda ke gaban sa ma yawa ne da su.


Ammi kuwa rashin ganin an kawo amaryar Yah Deen gida ne ya matu'kar sa ta mamaki, ko da ta tambaye shi dalili sai cewa yayi shima fa bai sani ba..ya dai ji ance ba'a 'daura auren ba an fasa.

Abin sai ya sake 'daure mata kai, ga shi Alhaji bai zauna ba balle ta samu dama ta tambaye shi yana can yana fama da ba'kin sa.

Si taji ta kasa natsuwa da Anty Zainab suka tattauna maganar inda tace abin ya 'daure mata kai sosai itama kuma duk babu wanda yayi musu bayani, da farko ta zaci can Jigawa aka kai amaryar sai daga baya kuma tayi tuananin ba'a kaita can ba tunda ga shi maj auren anan ita zaman me zatayi acana ita ka'dai, amma tunda har anje an 'dauro auren kuma me yasa baza'a kawo amaryar gida ba.

Da daran ranar da yake ba'kin Alhajin duk sun watse anan Ammi ta sami daman ganawa da shi, tambayar sa tayi kan batun amaryar sai taga Alhaji Baba na murmushi yace mata ai tuntuni amaryar na gida.

" Kamar yaya?"
Ammi ta sake tambaya cike da mamaki tana duban sa
Sai yace " Kamar yadda kika sani".
" Nifa na kasa ganewa Mu'een ce min yayi wai an fasa auren yanzu kuma ga ka kana cemin wai amaryar na gida".

" Yana saka jallabiya yace mata" To be frank Aisha..auren Muhammad bai yiyu da wancen yarinyar ba dan wan mahaifinta yaci amanar mu..muna zaune a wurin ya 'daure auren 'yar sa da wani daban bacin ya san shi muke zaman jira...sai daga baya ne ma Ja'afar ke sanar dani ashe wai shi wanda ya 'daurawa auren 'dan sa ne na cikin sa..kinga an nuna mana bambanci a zahiri.
...ran kowa da muke tare sai da ya 6aci a wurin hakan yasa Mahaifin Hudah yace tunda muka zo har Azare da niyyar aure to baza'a fasa ba...yace s 'daura auren kawai da Hudah ya bashi ita...na so in nuna 'kin amincewa amma yace matu'kar na nuna bana do to azahiri na nuna masa 'kyama matsayin sa na talaka...dole naja baki na nayi shiru na wakilci amarya Ja'afar kuma ya kar6awa Mu'een gudun maganar da zai biyo baya, yanzu dai Hudah 'yar ki da kike tsananin so marsayin mata take a wurin 'dan ki Muhammad..."
Ya 'karashe yana 'yar dariya.

Ammi kam rasa abinda zata ce da shi tayi saboda farin ciki..ita kanta ta fahimci jin da'din Alhaji Baba kan wannan auren...to inaga ita da ta jima da son ganin faruwar hakan duk da bata furta ba amma ya da'de cikin zuciyar ta.

Maganar Alhaji Baba ne ya katse mata tunanin ta inda yace" Sai dai bazan bashi Hudah ba har sai na tabbatar da cewa halin sa mai kyau ne , zargin da nake yi masa abaya idan ya kasance ba gaskiya ba ne sannan zan bashi Hudah matsayin mata dan bana so ya lalatawa yarin farin cikin ta da gur6ataccen tunani..matu'kar na tabbatar da zargi na akan sa wallahi da kaina zan sa ya rabu da ita in aura mata wani daban..dan haka a yanzu ko sanin cewa itace matar sa bana so yayi harda itama...ke de kawai ki 'kara kulawa da rayuwar ta ki tabbatar babu wanda ke shiga rayuwar ta tunda yanzu da aure akanta, batun zuwa gida kuma gobe da safe zan sa akaita ta gaida mahaifin nata 'kila ma a goben...zai koma".


Ammi kam ji tayi kamar ta taka rawa saboda tsananin farin ciki...ba ta iya ri'ke maganar ba sai da ta sanar da Anty Zee a daren ranar..ga mamakin ta kuwa sai taga farin cikin da Anty Zainab

Please Login or Register in order to submit comment