Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

'dau fansar abin nan da yayi masa, sai ya 'kuntata masa shima ta yadda zai san cewa bakomai bane Naira ke wakiltan sa, cuz ya san dagangan ne yasa mahaifin sa yazo ya ro'ka masa gurbin sa dan ya kawai ya nuna masa shi ba komai bane, sai dai ta ina....iya tunanin sa bai iya ya tuno abinda zai masa ba sai dai duk da haka bai ta6a cire abin aransa ba........tun faruwar lamarin kuma yake jin 'kirjin sa na yawan mai ciwo lokaci-lokaci...da yake bai san miye bane shiyasa bai damu ba.



Ba'a da'de da yin hakan ba sai ya samu labarin cewa anje anyi debate 'din acan Bauchi kuma makarantar su ce ta kasance ta 'daya wai sanadin Hayatuddeen abin mamaki, wanda har hakan ya sanya suka samu manyan kyaututtuka na ban mamaki daga manya-manyan mutane wanda basu ta6a samu ba, abin sosai zai baka mamaki musamman idan already kasan waye Hayat, mutumin da ko a class kusan kowani semester shike 'daukan second to d last position taya zai iya winning debate din jaha harma kuma ya samu lambar yabo?
amma kuma abin a fili yake domin sai wanda ya sani ne ka'dai zai fahimci cewa mafiya yawan kyaututtukan sun fito ne daga manyan abokan Mahaifin Hayatu.....wanda a fili zaka fahimci manufar hakan ga dukkan alamu yayi ne dan nemawa 'dan sa suna dan kuma ganin ya goge fuskar da'ki'kanci da aka sansa dashi.


Ranar da Mu'een yake da niyyan shigowa makarantar aranar yaci karo da 'kira cikin wayar sa...bai san ko numbern waye ba dan haka koda ya 'dauka shiru yayi........sai ji yayai ance " yane Man har yanzu banga kazo taya ni murna bafa ko ba'kin cikin bai barka ba har yanzu?"

Bai 'kara 6ata lokaci ya saurari komai ba kawai ya yanke 'kiran.

Har ji yayai dama ya fasa shiga makarantar amma kuma idan yayi hakan kamar ya nuna sarewar sa ne dan haka sai ya gama shiri ya ya tafi makarantar.


Amma ko iya zama bai yi ba dan haushi, duk inda ya wulga zancen akeyi, ana yaba 'ko'karin Hayatu bacin shi da suke class 'daya dashi ya san sirrin brain 'din Hayatuddeen tun ba yau ba....amma ya akayi hakan ya faru sam ya rasa.


Babu abinda akeyi cikin makarantar banda hayaniya dan haka sai ya yanke shawarar komawa aji kawai ya 'dan duba takaddun sa cuz gab suke da fara exams.


Dai-dai 'kofar class 'din su yaci karo da Hayat da wasu abokan sa guda uku, bai yi niyyan tanka su ba domin dama can ba magana ce ke hada su ba...take sai suka fara yi masa dariya suna nuna shi " bana an fa'do".
Abinda wani daga cikin su ya fara furtawa kenan yayin da Hayatu yace " an gamu da maza ai...wannan karon ansha kashi.....yaro yaci 'kasa sai ha'kuri".
"....na gaba ma duka za'a sha ai Bahbah".
Cewar wani daga cikin su.


Shiru Mu'een yayi yana kallon bakunan su harma sai ya daina fahimtar abinda suke fa'di...banda 'daci babu abinda yake ji cikin zuciyar sa...


Lumshe ido yayi sannan sannan kamar an ingiza shi yayi taku 'daya, na biyu sai gashi tsaye a gaban su, yana bu'de idanun sa nan take sai ya sau'ke su kan fuskar Hayatuddeen yana dariya har a lokacin, dun'kula hannun sa yayi cikin zafin rai ya bashi naushi a bakin nasa da yasa nan take sai ga jini....batare da 6ata lokaci ba sai ya ware hannun ya sau'ke mishi mari 6arin makauniya a duka gefe da gefen fuskar tasa wanda hakan ya faru ne tun kafin Hayat ya warware daga jin sau'kar naushin.


Sauran abokan tafiyar tasa duk sai suka yi turus gami da matsawa baya ka'dan, yayin da wasu suka kama baki, wani kuwa bakin ya bu'de cike da mamaki.


Yana gama yi mai marin kawai ya watsa hannun sa gami da goge guntun hawayen da suka zubo masa, tafiya yaso yayi batare da ya furta komai ba amma taku uku masu kyau bai yi ba kawai ya fa'di 'kasa warwas a wurin dafe da 'kirjin sa.


Mu'een ya kasance ba mai tara abokai bane haka kuma ba mafa'daci bane, rayuwar sa kawai yake yi cikin school 'din with respect tsakanin sa da kowa, bashi da shiga shirgin da ba nasa ba, abokin sa 'daya ne tun shigar sa makarantar wanda shima shigan su SS3 akayi mai transfer zuwa wata makarantar a can Maiduguri dan ya kammala acan....shiyasa yanzu bashi da aboki ko 'daya.


Amma da yake tun naushin da ya yiwa Hayat na farko hankalin sauran 'daliban da ke gurin ya dawo kansu shiyasa yana fa'duwan akayo kansa ana salati yayin da wasu ke furta" ikon Allah...ganin cewa shine da bugu kuma shine da kaiwa 'kasa.


'Bangaren Hayat kam haushi kamar ya kake shi, haka ya 'daga 'kafafu fuu yayi hanyar waje da fasheshen baki ya nufi offishin mahaifin sa.


Ba'a 'dauki dogon lokaci ba wurin isar da sa'kon abinda ya faru ga headboy 'din makarantar wato Mu'een.


Nan take aka zo daga school administration aka 'dauke shi zuwa asbiti da ambulance cikin hanzari.....suna zuwa aka fara bashi taimakon gaggawa musamnan da yake jikinsa da uniform na makaranta.


Principal da kansa ya nemi Uncle Ja'afar ya sanar dashi halin da ake ciki wanda nan take shima ya garzaya asbitin wurin Mu'een a rikice.


Lokacin da yaji abinda ke damun sa ba 'karamin tashin hankali ya shiga ba, wani 'dalibin ne da suke class 'daya dashi akazo asbitin dan shi sosai Mu'een ke birgesa duk da ba sa wata abota amma duk halin da yake ciki yanada labari.
Shine yake basu labarin duk abinda ke faruwa da Mu'een 'din, tun daga kan team 'din su na ball, da batun debate har abinda ya faru tsakanin sa da Hayat last kafin faruwar hakan.


Uncle Ja'afar ya damu sosai fiye da zaton mai karatu dan masifa ya fara yiwa malamai biyu dake tare da su a wurin su kuma suna bashi ha'kurin cewa basu san da wannan batun ba sam dan ba 6angaren su bane.
" munafukan banza munafukan wofi....an gaya muku shi 'din bashi da galihu ne ko ance muku ba'a son shi, wallahi da Mu'een na fa'da min halin da yake ciki da sai inda 'karfina ya 'kare wajen faranta masa.... da bazan ta6a bari a wula'kan ta min yaro ba, wato dan kunga 'dan mai arzi'ki shiyasa kuka fifita shi akan yaro na ko, to gani gaku wani abu ya same shi kuga mai zai faru tsakani na da ku...aikin banza aikin wofi".


Su kam ha'kuri sukayi ta bashi daga nan suka dan'ka shi hannun Uncle Ja'afar 'din sukayi gaba abin su.


Sam bai tuna ya 'kira Alhaji Baba bama har sai da dare yayi kusan 'karfe sha 'daya jin cewa numafshin Mu'een ya daidaita kafin ya sami hankalin tunawa da Alhaji Baba take kuwa ya 'kira yayi masa bayani.


Ammi taso binsa lokacin da zai taho dan sosai hankalin ta ya tashi da jin abinda ya farun amma Alhaji Baba ya hanata....koda yaje ma bai wani nuna damuwar sa a zahiri ba duk kuwa da cewa ya damun amma daga Allahn sa sai zuciyar sa ne suka san hakan.... ganin yanda Uncle Ja'far gaba 'daya ya fita hayyacin sa ne ya sanya Alhaji Baba 6oye tasa damuwar sa kawai ya dinga kwantar masa da hankali.


Allah cikin ikon sa kuwa kafin Azahar tayi Mu'een ya tashi wasai dashi kamar bashi ba sai 'dan abinda ba'a rasa ba.

Amma harda 'dan rama yayi a kwana 'dayan da yake kwancen, Alhaji Baba fa'da yayi masa sosai akan rashin ha'kuri da kuma biyewa zuciya da har zai je ya bugi 'dan mutane akan kishin ya maye gurbin sa.


Mu'een bai ce dashi komai ba, dan yasan ba Alhaji Baba ka'dai ba kowa ma babu mamaki a haka aka 'dauki abin.....idan ya fahimtar da Alhaji Baba to sauran mutane fa dole akan hakan zasu 'dauke shi......amma shi sam ba nufin sa kenan ba, me yasa zan dake shi dan kawai ya sha gabana akan wani abu?
Wannan ai ba komai bane face halin rayuwa, amma ya bar ni da haushi na da nake ji mana dan me yasa zai 'debo wasu banzayen abokan sa da ko kallo ma basu ishe ni ba suzo su tsaya agaba na suna gaya min magana son ransu.....zan iya 'daukan komai amma banda rainin hankali".
Cikin zuciyar sa yake wannan maganar yayin da a fili kuwa Uncle Ja'afar ya 'dago ya kalla gami da fa'din " ni gida zani Uncle..."

" Baka jin komai ne?"
Uncle 'din ya tambaye shi cike da kulawa.

Sai ya 'dauke kansa gami da kallon gefen gadon yace " ina jin nawi a 'kirjina da kuma zafi sannan numfashi na na sar'kewa".

Da sauri Uncle Ja'afar yace
" Bari toh sai Doctor ya sake dubaka tukunna".


Alhaji Baba shiru yayi yana kallon su har Uncle Ja'afar ya fita 'kiran Doctor....'dakin sai ya zama shiru gaba 'daya.

Mu'een ne ya yanke shirun da fa'din " Ya su Ammi?"
Inda yayi maganar a hankali batare da ya kalli fuskar Alhaji Baba ba kamar ba'a son ranshi ba.


Ajiyan zuciya Alhaji Baba ya sau'ke sannan batare da ya bashi amsar tambayar tasa ba ya 'kira sunan shi da fa'din " Muhammad!"
Cikin natsuwa.


'Dagowa yayi ya kalle shi gami da bashi hankalin sa gaba 'daya.

" Dan Allah ba dan ni ba Mu'een ka daina saka kanka cikin irin wannan rigimar kaji, mutane kala-kala ne Mu'een ni nan na ha'du da ire-iren mutane wasu zuciyar su babu Allah ciki dan Allah ka daina cusa kanka cikin ire-iren su, ba nason wani abu ya same ka ko ka'dan...."


Cikin 'karfin hali yace " Alhaji ka daina ha'da ni da Allah nifa ban shiga rayuwar kowa ba shine ya ke gaya min magana bayan sun 6ata raina shiyasa na maresa".

Alhaji Baba cewa yayi
" amma me yasa bakayi ha'kuri ba to a lokacin?"

" nima ban sani ba Alhaji".
Yace A hankali.

" shai'dan ne ya ingiza ka Muhammad shiyasa ka kasa ha'kuri har ka biye masa...."


Sallamar Zainab ne ya katse maganar Alhajin inda ya amsa mata sallamar tata gami da mi'kewa tsaye....barka da hanya tayi masa gami da gaishe sa wanda suna gama gaisuwar sai yayi waje.


Kallon ta ta dawo dashi kan Mu'een tace " ya jikin naka Mu'een?"

" Da sau'ki Anty sai godiya, please kice da Uncle mu koma gida ni banson asbitin nan".


Murmushi Zainab tayi gami da fa'din " ai kai da gida sai ka warke".


Dai-dai nan su Ja'afar da likita suka shigo bayan su kuma Alhaji Baba ne.


Bayan likita ya sake duba shi sai ya tabbatar musu da cewa ciwon sa bai kammala kwanciya ba tukunna sai an 'kara bashi kulawa.

Da jin haka sai ya lumshe ido gami da furta " ya salam" cikin zuciyar sa.


Haka aka cigaba da bashi kulawa har kwana uku daga nan Alhaji Baba ya koma gida.


Dan likita ya tabbatar musu da cewa zuwa jibi insha Allahu za'a sallame shi.


Washe garin tafiyar Alhaji Baba ne dismissal letter ya same shi har asbiti, abin takaicin ma wai shine Hayatuddeen ne ya kawo masa cike da izza da gadara,
wannan abin ba 'karamin 'kona ransa yayi ba har ciwon sa yaso dawowa sabo.

Uncle Ja'afar ne ya dinga kwantar masa da hankali dan ko shi Uncle Ja'afar 'din ma abin ya bashi haushi amma magangunun Alhaji Baba kafin ya wuce jiya su suka hana shi yin wani yun'kuri.


'Bangaren Mu'een kuwa sai ingizashi zuciyar sa take sake yi akan ya koyawa Hayatuddeen hankali....sam baiji zai iya barin sa haka kawai ba tunda har yayi sanadin da aka kore shi daga makaranta.....in ma akan yayi fa'da ne ai Hayat 'din shi ya tunzura shi, kuma in dole ne sai anyi hakan mai yasa sai Hayat....me yasa ba za'a 'kirashi ya kar6a da kansa ba.


The following day aka discharging nasu suka koma gida, Mu'een bai sake taka 'kafar sa a makarantar ba dan haushi, Uncle Ja'afar ne yaje da kansa ya kar6o mai transfer dan ya canza masa wata makarantar inda anan ya samu labarin cewa babu wanda ya kori Mu'een daga makaranta, Uncle Ja'afar ne ya ciro DL ya nuna musu sunyi mamaki sosai cuz stamp da komai na makarantar ne amma kuma ba su sukayi ba...su shirin bashi horo ma sukeyi na sati biyu kuma gashi nan suka nunawa Uncle Ja'afar.


Uncle Ja'afar ma sai ya sanar dasu wanda ya kai wa Mu'een lettern sai yaga basu nuna wata damuwar komai ba sai ma ha'kuri kawai da suke bashi.


Abin mamaki, da wata makarantar ce a yanda ya sani ya san yin hakan babban laifi ne ace 'dalibi ya aikata irin hakan sa6anin wannan da yake ganin kamar babu adalci cikin lamuran su.


Wannan dalilin ne ya sanya shi 'kin fasa kar6ar transfern acikin satin ya canzawa Mu'een makaranta dan baya son ya 6ata lokaci a gida dan zuwa nan da watanni biyar zasu fara zana waec.


Ba yabo ba fallasa ya fara zuwa makarantar babu laifi tayi masa sai dai bata shiga ransa sosai kamar waccen ba amma a hankali makarantar take shiga ransa musamman da ya fara karantar yana yin makarantar.


Mai tsada Uncle Ja'afar ya sanya shi dan har tafi wacce ya baro 'din tsada...shiyasa ya bada himma sosai ga abinda ke gaban sa baya wasa sam da karatun sa kuma har yanzun bai yi aboki ko 'daya ba.





*****
Akwai watarana yaje Library karatu sai ya tarar da wasu 'yan mata su uku na faman musu kan pronouncing wani word, kowa da abinda yake fa'da ga dukkan alamu kuma 'kawaye ne su dan haka sai ya 'dauke kansa da zummar wucewa bai yi niyyan tanka su ba.


'Daya daga cikin su ne yaji tace " yauwa Bross dan Allah tambaya".

Cak ya tsaya gami da waigowa dan baiga alamun cewa da wani agurin bayan shi ba.


Tasowa tayi da text book a hannun ta ta iso gaban shi ta nuna masa tace " ya ake pronouncing word 'din nan please?"

Bai san me yasa ba amma sai tsintan kansa yayi da fa'din " ke fa'da inji".
...kamar an batsi bakin ta sai ta fa'da.
Karo na farko da ya yiwa wani murmushi a makarantar a hankali sai yace
" ba haka bane".


Baki ta 'dan tura dan ita duk zaton ta nata ne dai-dai.

Sauran ma jin yace nata ba dai dai bane sai sukayi hanzarin tasowa dan suji da kunnuwan su.


Batare da 6ata lokaci ba ya sanar dasu yanda ake pronouncing word 'din, ai kuwa take sauran suka fara murna jin cewa nasu ne dai-dai.

Yatsa ya sanya kan bakin sa gami da fa'din " shiii kun manta ba'a hayaniya a Libry ko?"

Tsit sukayi kamar ruwa yaci su gami da komawa mazaunin su.


Shima har ya juya sai kuma ya saci kallon wacce ta fara yi masa tambayar ganin ita bata motsa ba har yanzun.


Waro idanu yayi ganin ta kafe a tsayen ga dukkan alamu ranta ne ya 6aci....kallon ta yayi da kyau gami da fa'din " wai fushi kika yi ?"


Girgiza kai kawai tayi tare da komawa gurin sauran 'kawayen nata ta zauna.


Shima sai ya girgiza kansa ya juya ya tafi can inda hayaniyar su bazata dame shi ba dan yayi karatun sa, amma haka kawai fuskar yarinyar sai yake masa kama da fuskar sani amma ya kasa fahimtar a ina ya san fuskar.









_Comment_
_Vote_
_Share_







*Salmerh ce* 😍
[12/29/2019, 9:36 AM] 🌸Salmerh🌸: πŸ’• *NOORUL* πŸ’•
(Haske nah)



By
*Salmerh MD*



*Wattpad @*
*Serlmerh-md*



πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
πŸ’«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*


~Dedicated toπŸ‘‡πŸΌ Hussaina B. Abubakar~
~Wannan kam naki ne Mrs Habou~ ~(Sa'eenah) wallah kina sani nisha'di sosai....~
~Allahu ya bar min ke~ πŸ˜˜πŸ‘ŒπŸ»



*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*



πŸ…Ώ *21*



Bai wani tsawaita tunanin ba balle har ya hana shi sukuni kawai yaci gaba da harkokin sa.

Bai kuma kara bi ta kan yaran ba haka bai sake ganin su ba, kamar yadda bai sake tunawa da su cikin sha'anin rayuwar sa ba dan basu ne a gaban sa ba a halin yanzun.

Karatun sa kawai ya sa agaba littattafan sa sune abokan sa baya shiga rayuwar kowa cikin makarantar.




*****
*Bayan sati 'daya*

Zaune yake daga gefen bakin Varandern 'kofar class 'din su yana duba wani handbook fuskar sa sanye da farin siririn glashi, yayin da uniform 'din dake jikin san suka matu'kar amsar fatan jikin sa yafito shar da shi.

Wajajen goma da rabi ne dan break akeyi a lokacin hankalin sa sosai ya 'dauku ga karatun littafin, batare da yayi zato ba kawai yaga an 'daura masa wani takadda kan nasa handbook 'din har ya kansance ma baya ganin nasa sai wannan 'din.


Mamaki ne ya cikashi na ganin hakan mamakin waye mai wannan uban 'ko'karin da har zai masa haka, dan shi ba saba yin hakan yayi da kowa ba, sai dai yana da ya'kinin duk yadda akayi an sa6a lamba ne shiyasa akai masa hakan, may be kama yayi da wani daban da har yasa aka ga kamar wancen 'din ne.


A hankali ya 'dago kansa dan ganin kowaye sai yaga ashe ma mace ce, macen ma kuma waccen yarinyar da suka ta6a hast duwa a Libry last week... ita ce tsaye kansa cikin sakalalliyar fuska take duban sa....da wata 'kawar ta su biyu suka zo.


Suan hada idanu da ita sai yaga ta tura baki gaba kamar yanda yaga tayi rannan a Libry, sarai ya gane ta amma sai ya ce da su " me ya faru?"


'Dayar yarinyar ne ta juya ta kalle ta sai ta wani yan'kwana fuska sannan cike da shagwa6a tace da shi " Ayyah Bross tun ranar fa nake ta neman ka ban ganka ba, am bamu assignment na mathematics da yawa ni kuma ban iya ba, kullum sai na ta duba ka amma ban samun ka na kaima Yayah Hayatu shi kuma yace wai bai iya ba ni bansan yanda zan yi ba sai yau na ganka anan".


Bai furta mata komai ba illa takaddar tata da ya 'daga da niyyar ganin set 'din da take sai idanun sa ya sau'ka kan sunan ta dake rubuce a bangon littafin da manyan haruffa RAHMA SALIS GIMBA......
yaga an rubuta...Dum yaji zuciyar sa ta tsinke haka kawai bai san dalili ba.


Tuno sunan Hayat yayi da ya baro a wancen makarantar wato HAYATUDDEEN SALIS GIMBA.....
Batare da ya 'dago ya kalle ta ba ya tuno kamannin su take ya fahimci dalilin da ya sanya yake ganin kamar ya san yanayin fuskar ta a wani guri.
Kenan itan blood sister 'din Hayat ne....me hakan ke nufi kenan?"
Ya tambayi zuciyar sa.


" Please kayi min anjima zanzo nan in kar6a wai gobe za'a yi submitting kaji".

Tana gama fa'din hakan ta kama hannun kawar ta suka bar wurin.


Bai iya yace da ita komai ba har ta 6acewa ganin sa, sai a sannan ya sake duba bayan littafin SS 2A yaga an rubuta.


Gaba 'daya sai yaji jikin sa yayi sanyi, Hayat da yafi tsana a duniya ne yau kuma Allah ya ha'da shi da sistern sa anan, me hakan ke nufi wai, na kasa ganewa ?"
Ya sake tambayar kansa...gami da cire gilashin dake manne a fuskar sa.


Har lokacin break ya wuce bai iya ya yanke shawarar da ta dace ba, tambayar kansa yake shin yayi mata ne ko kuma ah ah kar yayi....koda bai yi mata solving Assignment 'din ba taci Zero sanadin hakan sam ba zai wanke zuciyar sa daga takaicin da Hayat ya 'kunsa masa ba, dalilin sa aka tono masa ciwon da shi kansa bai san yana da shi ba, dalilin sa yasa ya bar school 'din da yafi 'kauna kaf fa'din jihar Bauchi..bar ma batun abubuwan da suka faru cikin makaranta...taya zan iya yafe masa...taya zan iya mantawa da abinda Hayat ya min cikin kwanaki 'kalilan, a duk lokacin da na kalli kaina cikin makarantar nan na ganni matsayin ba'ko abin na matu'kar sosa raina.

Bhu yarinyar sam bata da hali irin na yayan ta, ga dukkan alamu halin su ya banbanta dashi....

Ido ya lumshe cikin zuciyar sa ya furta " ohh Allah help me....ko dan hakan ma yana ganin zai iya yi mata Assignment 'din ba dan komai ba saboda Allah kuma saboda yaddan da tayi da shi.



Class ya tashi ya shiga inda batare da 6ata lokaci ba duk ya solving mata Assignment 'din, sannan yabi cikin littafin duk ya duba yaga anan ya fahimci matakin brain 'din ta 6angaren Maths, babu mamaki gajiya tayi da ganin Zero cikin takaddan ta shiyasa ta nemi agajin sa....murmushi yayi sannan ya rufe littafin ya ajiye.


Shai'dan ne ya dinga zuga shi game da fansar dake ransa na tsakanin sa da Hayatu, har ma yake ganin kamar Allah ne ya kawo yarinyar cikin rayuwar sa dan kawai ya koya wa Hayatu hankali...sam bai 'karyata wannan tunanin ba, take yayi na'am da hakan ya kuma saki murmushin mugunta na gefen baki....sai dai inda gizo ke sa'kar shine bai san wani irin fansa zai 'dauka ba tunda yarinyar ba sa'ar sa bace balle suyi takun sa'ka, ya dai barwa lokaci....da ya'kinin cewa watarana zai iya tuna kalar fansar da ya kamata ya d'auka wanda Hayatu zai ji ciwon abin sosai, zai kuma san ba komai ne ku'di ke siyan sa ba.


12:03pm ta bayyana bakin class 'din su tana neman izinin shiga, class representative ne ya dakatar da ita sai tace da shi wurin brother 'din ta tazo amsar abu.

Sai yace " ta bari ba yanzu ba".

Take tayi kalan tausayi gami da fa'din " please mana it's urgent Allah".


Sunan brother 'din nata class rep ya tambaya....anan sai tayi shiru tana rarraba idanu cikin ajin, bata san takamamme nan ne ajin ba ko ah ah balle har ta san sunan sa da ko za'a yanka ta bazata iya fa'da ba dan ba sani tayi ba, ita dai 'dazu ta ganshi zaune anan dan haka sai ta cigaba da binciko shi da idanun ta...ko Allah zai sa ta hango shi.


Mu'een kuwa yana zaune harda kishingi'da yana kallon duk dramar da suke yi....sam bashi da niyyan motsawa balle ya tanka su so yake yaga iya gudun ruwan ta.

" baki san sunan nashi ba kenan?"
Class rep ya sake tambayan ta.

Sai tace dashi " na manta ne fa".

Da mamaki sai yace " U ar not serious sunan brothern naki kika manta?"

Hannu ta ha'da kamar zatayi kuka...yayin da class rep ya cigaba da fa'din
" may be ma baki san class 'din ba shiyasa kika zo nan, ai da yana nan 'din da yanzu kin ganshi dan haka jeki neme shi ba anan yake ba".

Juyawa tayi zata fita da tunanin inda zata kuma zuwa neman sa, amma me yasa da nace masa zanzo nan bai ce min ah ah ba....
" _Rahmah_ ".
Tana cikin tunanin tajiyo muryar sa ya ambaci sunan ta.


Cak sai ta tsaya gami da waigowa caraf sai idanun su ya sarke cikin na juna take sai ta sau'ke ajiyan zuciya harma bata san lokacin da ta furta " haba Bross... kana jina shine ka 'kyale ni ko?"
Cike da shagwa6a tayi maganar gami da 'karasawa inda yake zaune.

Bai ce da ita komai ba kawai ya mi'ka mata takaddar ta.

Kar6a tayi gami da fa'din " Thanks" tare da hanzarin barin ajin yayin da ilahirin mazan ajin suka bi ta da idanu dan sosai kalar shagwa6ar ta ta birge su sa6anin Mu'een da ko akan sa ma bai sa hakan ba.

Wani dake seat 'din gaban Mu'een ne ya waigo yana murmushi yace dashi " Amma sister n kan nan da gani rigimammiya ce ko?"
" indeed".
Yace dashi a takaice shima 'din yana murmushi kamar gaske.


Tun daga lokacin sha'kuwa mai tsanani ya shiga tsakanin Mu'inuddeen da Rahma, tun Mu'een na kaucewa har yazo ya saki jikin sa da ita dan ita komai zatayi sai ta neme shi haka kuma duk abinda ya dameta gurin sa take zuwa, sosai take girmama shi matsayin yayan ta.


Tsananin sha'kuwar ta sun ne ya sanya shi fahimtar komai game da ita a haka ya fahimci cewa itan ba sosai suke zama gida 'daya da yayanta Hayat ba.


Ta kan zauna gidan kakar ta wani sa'in, yayin da wani lokaci take zama gidan Antyn ta wato babbar yar su dake aure da yaranta uku, lokuta 'kalilan nan take zama gidan mahaifin ta, bai sani ba ko wannan dalilin ne ya sanya halayyar su ta banbanta da Hayat....sam basu kama ta fuskar halayya ba bayaga jini da ya ha'da su.


Rahma sanyin

Please Login or Register in order to submit comment