Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

palourn ya sanya ta direct ta nufi hanyar bedroom 'din sa sai dai bata 'karasa ba lokacin da ta iso daf da 'kofan sitting room 'din sa sai tayi tunanin ko yana ciki, hakan yasa ta 'dage labilen kawai da yake dama da nufin dubawa kawai da le'ka so lokaci guda ta 'daga labilen gami da sallama a bakin ta.

A dai-dai lokacin Alhaji Mamman na shirin cire babbar rigar da ke jikin sa saboda yanda yaji tamkar ta takurashi tana sha'kesa, yayin da mahaifin Husnah ke kwance a 'kasa baya numfashi.

A rikice ta 'karaso ciki tana binshi da idanu bakin ta cike da tambayar abinda ya faru amma ta kasa furtawa.

Da 'kyar ta iya harha'do kalmar " Lafiya...Alhaji me ya faru?"

Ko 'kala bai iya yace da ita ba tsabar yanda ya ru'de, fuskar sa ka'dai zaka kalla ka fahimci ba a dai-dai yake ba.

Bayan fahimtar cewa suma Alhaji 'karami yayi yasa Hajiya Kareema da 'dan gudu-gudu ta nufi fridge ta 'dauko ruwa mai sanyi tazo ta yayyafa saman fuskar sa, yayin da Alhaji Mamman ke tsaye yana faman firfita da hular sa dake ri'ke a hannun sa, ji yayi komai ya kwance masa.

A hankali mahaifin Husnah ya bu'de lumsassun idanun sa ya sau'ke su akan fuskar Hajiya Kareema then kan Yayan sa da suke uwa 'daya uba 'daya wato Alhaji Mamman.

Rintse idanu yayi a hankali hawaye ya gangaro ta gefe da gefen idanun sa saboda takaici...".... _Zai zo wurin ku ya kammala ha'do ku'da'den, yanzun nan ma ya bar wuri na bayan ya sanar da ni..so ku kula da komai bisa tsari saboda 'dan uwa na ne shi ban son ku bar kafa ko ka'dan da za'a iya fahimtar cewa da hannu na cikin lamarin..... sannan ina fatan baku illata yarinyar ko ka'dan ba ko?"_
Bai ji abinda aka fa'di daga 'daya 6angaren ba sai ji yayi Alhaji Yayan nasa yace" _To shikenan ku dai ku tabbatar bai zo da kowa ba kafin a sake ta dan bana son hukuma ta shiga cikin maganar kasan tonuwar asirin ku tamkar tonan nawa asirin ne and i hate that..."_

Abinda kawai zai iya tunawa kenan da yaji wan sa ke fa'di...wanda tashin farko kalaman yayan nasa suka bayyana masa cewa yana da hannu dumu-dumu kan sace Husnah da akayi.

Yana kwancen yake tambayar zuciyar sa" miye dalilin hakan? Ashe 'dan uwa bazai ta6a sakin ransa ya rayu da 'dan uwan sa cikin amana da gaskiya ba?
Kuma wai duk akan dukiya da Allah ne ke bada ita..."
Zuciyar sa nawi yake jinta ga numfashin sa take ya sar'ke sa yake fita da 'kyar, banda hawaye babu abinda yake iya yi a wannan halin.

Cikin ransa sa yake jin kamar ya tashi yayi ta jibgan yayan nasa har sai ya illata shi saboda cin amanar da yayi masa, ya nuna masa dukiya tafi masa komai a rayuwar nan ciki kuwa harda zumuncin da Allah ne ya ha'da tsakanin su yayo su daga tsatso 'daya, to laifi ne dan Allah ya fifita 'dan uwanka akan ka? Laifi ne dan Allah ya bawa 'dan uwanka dukiya kai bai baka ka? Shin kasan naka kyautar da ya ajiye maka?
'Kilan duk zafin neman ka ba zai ta6a baka dukiyar ba saboda babu ita cikin 'kaddarorin rayuwar ka ta duniya to meyasa zaka takurawa kanka?
Idan kayi ha'kuri ma kabi Allah kabi manzon sa kayi tawakkali babu mamaki ka dace da samun taka dukiyar acan matabbata tana jiran ka, inda ko wani abu zakayi da shi ba zai ta6a 'karewa ba sannan Allah ba zai ta6a gajiya da baka ba, haka nan kuma ba zai ta6a raba ka da aljannar sa ba..to menene yafi wannan fisabilillahi..?"
( ALLAH KASA MU DACE DA NI'IMAR KA DUNIYA DA LAHIRA)
" Amma wannan wace iriyar rayuwa ce, ashe mutun ba zai iya ri'ke 'kaddarar da Allah ya 'dora masa ba sai ya nuna nasa ikon ta hanyar da be dace da karantarwar musulunci ba, me yasa muke zalunci muke dagewa da cewa sai mun yi arzi'ki ko ta halin 'ka'ka bacin a littafin 'kaddarar mu Allah bai tsara hakan ba?.

Hawaye yake ta zubowa amma bai iya ya furta komai ba yana jin muryar Hajiya Kareema nata 'kiran sunan sa" Alhaji 'karami!..Alhaji 'karami!!.." amma sam ba zai iya amsa mata ba kamar yadda ya kasa motsa koda 'dan yatsan sa ne dake jikin sa.

Har a lokacin kuma bai ji muryar Alhaji Mamman yace komai ba yayin da shi kuma ta 6angaren sa ido kawai yake iya rolling amma haushin ganin wan sa tsaye akan sa sai ya hanashi sake bu'de idanun illah hawaye da yake fitarwa.

Ganin haka ya sanya Hajiya Kareema a rikice ta mi'ke tana fa'din " Alhaji akai shi asbiti mana ga dukkan alamu fa yana jin jiki..."

Shiru bai kulata ba saboda damuwar dake cikin ransa ta isheshi, imaging yanda zakaji idan an kama ka da hannu dumu-dumu bisa cin amana, amanar ma ta jinin ka, 'kanin ka, mabiyin ka da kuka fito ciki 'daya, bayan ko Allah ya san irin 'dawainiyar da yake yi maka amma duk da haka ka ci amanar sa kuma ya kama ka...ya zaka ji please?...kun san ba sau'ki.."

Wannan dalilin ne ya sanya shi komai ya tsaya masa cak ya kasa aiwatar da komai a 'adakin hatta maganar da Hajiya Kareema tayi ma bai ji ta ba hakan yasa bata samu amsa daga gare shi ba.

Ganin hakan ya sanya ta jijjiga shi da 'karfi tana sake maimaita abinda ta fa'di domin tunanin ta ko duk ya ru'de ne saboda ganin 'kanin sa kwance babu lafiya.

Jijjiga shin ke da wuya kuwa take sai ya dawo hayyacin sa, kallo 'daya yai mata sai ya 'dauke idanun sa daga kanta, kowa ma yanzu kunyar sa yake ji gani yake tamkar itama ta san abinda ya aikata.

Baya yayi ya zauna bisa kujera yana sakin numfashi mai mugun numi...batare da ya furta komai agare ta ba.

Da fahimci kamar baya hayyacin sa sai tayi hanzarin barin 'dakin da gudu Hajiya Kareema tayi waje ta 'kira driver mai gadi da masu aikin ta suka cicci6e shi suka kai mota, sannan ta tafi ta zaro mayafin ta suka wuce asbiti da shi while Alhaji Mamman na nan inda yake bai ko motsa ba, kallo 'daya zaka yi masa ka fahimci ba'a hayyacin sa yake ba wanda in baka sani ba dagaske zakayi zaton ko tashin jikin 'kanin nasa ne ya sanya shi hakan...sai dai shi ka'dai ya san girman kunya da takaicin da yake ciki a wancan lokacin.

Sai da ya tabbatar sun bar gidan gaba 'daya kafin ya samu ya sawa ransa 'kwarin gwiwa ya sake 'dauko wayar sa a inda ta fa'di, harha'dawa yayi wannan karan sai da ya 'dan le'ka gudun kar wani ya sake jin sa, duk da kuwa yasan cewa kishiyar Hajiya Kareema bata gari a lokacin amma hakan bai hana shi tunanin itama kar tazo ta jishi ba abinku da marar gaskiya.

'Kira yayi ya bada umarnin akai Husnah 'kofar gidan mahaifin ta a sau'ke ta nan kawai suyi tafiyar su yace daga baya zamu ha'du mu kammala deal 'din.

Hakan kuwa akayi, domin mahaifiyar Husnah na nan zaune tayi tagumi tana jiran isowar 'yar ta da yake tasan mahaifin ta ya fita da ku'din amsar tata(ransom), tare suke zaune da wasu 'yan taya ta jaje 'kalilan daga dangi sai da wasu makwabtan ta mafi kusa.

Kamar daga sama ta fara jiyo tashin kukan Husnah yana tunkaro ta ai kuwa da gudu ta tashi ta fita itama tana kukan ta rungume ta.

Sun 'dauki tsawon lokaci suna a haka tana ta godewa mahallici a fili da zuci...sai da ta 'karashi murnar ta saura na tayata kafin ta tambayi Husnah ina mahaifin nata kuma ya tsaya ganin har a lokacin bai shigo ba kuma bata ga motar sa ba a harabar gidan.

Husnah ce tace itama bata ganshi ba...tace mutanen sune suka kawo ta har gida.

Sauran dake tare da Mummyn Husnah wasu salati suka sanya da mamaki suke fa'din" Har gida suka kawo ki da kasu..tashin hankali?"

Mummyn Husnah kam batayi mamaki ba da jin cewa sun san har gidan su damuwar ta mai gidanta ne kawai.

Amma menene abin da zai sa ta dami kanta dan sun har gidan su, tunda kam har suka iya sace ta a makaranta ai zuwa har gidan mahaifin ta ma ba zai gagare su ba...duk kuwa da tasan cewa yanda suka yi abin ba abu ne mai 'daure kai ba.

Drivern da yake 'dauko Husnah aka tsare da bindiga ya jawo su zuwa makarantar cikin motar da yake kaiwa da 'dauko ta daga scool 'din, bayan an tashi su Husnah tazo ta shiga sai suka 'kara sashi ya ja motar suka yi gaba, Husnah har na gaida su ganin ba'ki har mutun biyu cikin motar duk kuwa da cewa fuskokin su sanye suke da ba'ka'ken face mask, basu amsa gaisuwar tata ba ma dan hakan sai ta kalli drivern ta tambaye shi su wanene...shima 'din bai kulata ba cuz shi ka'dai ya san halin da yake ciki.

Dan haka itama ganin babu mai niyyarf magana cikin su ya sanya ta ja bakin ta tayi shiru, yayin da driver yayi tsuru yana cigaba da driving ji yake kamar yayi ta tsala ihu har aka musu 'dauki amma ina no way...cuz gefen cikin sa bindiga ne hakan yasa ya cigaba da jan motar suka yi nisa suka zo inda babu mutane sosai sannan yaga wata ba'kar mota mai ba'kin tinted glass ta sha gaban su, dole tasa yaja yayi parking.

Yana tsaya yaga sun bu'de sun fita tare da dakawa Husnah tsawar ta fito a firgice ta fita 'dayan ya tisa 'keyar ta zuwa 'dayan motar yayin da 'dayan ya tsaya ya bugawa driver gindin bindiga akan sa dan kar ma yayi tunanin binsu abaya, take kuwa ya kifa kanshi bisa sitiyari ya suma.

Tun daga lokacin da suka sa ta shiga motar Husnah bata 'kara sanin kanta ba bata 'kara sanin komai ba sai tsintan kanta tayi a wani gida da bata san ina ne ba..amma basu ta6a lafiyar ko 'dan yatsan ta ba.

Sai bayan wasu mintina sannan drivet ya dawo hayyacin sa bayan har dan taru akansa ganin kansa da 'dan jini-jini.

A gigice yayi musu takaitaccen bayani sannan ya ja motar yana zubda hawaye ya koma gida ya sanar da iyayen Husnah abinda ya faru...Alhaji Mamman ne ya fara 'dora zargin sa kan Nasiru driver har yaza aka kama shi aka kulle da fa'din wai duk munafurci ne, tun ranar ake gana masa azaba wai adole sai ya amsa cewa shi ya sace Husnah amma ya kasa amsawa saboda yasan ba shi bane...'yan sandan da kansu sai da ya fara basu tausayi suka zuba masa idanu kawai duk ya fita hayyacin sa yayi zuru-zuru da shi amma babu wanda zai iya fahimtar sa sai Allahn sa.

Tun daga ranar da aka sace Husnah iyayen ta basu sake natsuwa ba har yau da Husnah ta dawo gida hannun su, ko jiya ma sai da mahaifin ta yaje station wurin Nasiru driver yana kuka yana ro'kon sa kan cewa idan shine ya taimake shi ya sanar dashi inda Husnah take, yace shi ko duk dukiyar sa suke so duk zai basu amma dan Allah kar su ta6a masa lafiyar 'yar sa, kar su lalata mata rayuwa matsauin ta na ya mace matashiya su rufa masa asiri...amma Nasiru kuka kawai ya ringa yi bai iya ya furta komai ga mahaifin Husnah ba ya riga ya mi'ka ma Allah kansa bashi da wata mafita...dan shi yawan ku'din da yaji mahaifin Husnah yace anne ma a wurin sa ma ka'dai sun 'daga hankalin sa duk dama dai yasan Alhajin zai iya bafawa amma sosai hakan zai na'kasa tattalin arzi'kin sa...yana kukan yake ro'kon Allah ya tsare al'ummar musulmi daga dukkan azzalumai da masu sharri...to shi me zai sashi yincwannan 'danyen aikin da banda 'diban alhaki babu komai cikin sa, duk mummunan yanayin da yake ciki hakan bai sa ya kasa tausaya wa yanayin da Alhaji Hamza ya koma saboda 6acewar 'yar sa ba duk ya zama wani iri da shi ya fita hayyacin sa, hakan ma shine da yake matsayin namiji to inga mahaifiyar ta?
Tausayin ahalin ne ya sake ratsa shi...hakan yasa cikin ransa yake addu'ar" ALLAH ya bayyana ki Asma'u, Allah ya tona asirin duk wanda ya zalunce ki ya raba ki da iyayen ki, yarinya mai hankali da natsuwa abin alfaharin ko wani irin mutun, Allah ya tsare miki mutuncin ki kamar yanda mahaifin ki yake fata".

Haka har Alhajin ya bar inda yake bai furta komai agare shi ba...da ikon Allah kuma yau sai ga Husnah cikin gidan mahaifin ta cikin 'koshin lafiya.

Mummyn Husnah kam banda hamdala babu abinda take yi, godewa Allah kawai ta ringa yi da dawowar 'yar tata duk da kuwa zuwa lokacin hankalin ta ya kasu gida biyu ne amma a hakan ta basar farin cikin ya rinjayi tunanin inda mahaifin Husnah ya tsaya...ta bari akan cewa duk inda yake ai soon zai dawo ta sani.

Sai da suka gama koke-koken su kafin ta Husnah ta shiga wanka yayin da take jin tamkar ta shiga bayin ta yi mata wankan da kanta saboda so, wani zazzafan 'kaunar 'yar tata ne ya ninku mata cikin zuciya da yasa bata so ko nan da can ace Husnah ta matsa batare da ita ba, tun shigar Husnah wankan Mummyn ta bata zauna ba, ta gyara nan, ta kimtsa can duk sai ta rasa takamamman abinda ya kamata tayi ma gaba 'daya.

Sai dai duk da haka tunanin ta bai kauce kan binciken ingancin lafiyar Husnah ba, farin cikin da shiga bai sa ta mance hakan ba, tsoro take ji kar sunyi mata wani abin, sai dai ta bari cikin ranta da niyyar sai Husnah ta huta kafin su tattauna.

Tuni ta fitar mata wata doguwar riga mai kyan gaske da duk abubuwan da tasan zata bu'kata wurin shirya kanta.

Koda Husnah ta fito daga bayin Mummyn ta da kanta tai mata drying na gashin ta da hand dryer sannan ta bata dama ta shirya cikin doguwar rigar da ta ciro mata, kafin hakan sai ta wuce kitchen dan samar mata abinda za ta ci.

Mintina 'kasa da talatin ne suka 'dauke ta shirya abincin ta kawo mata.

Wannan karan a palour suka zauna dukkan su da sauran mutanen da ke cikin gidan tare da su.

Kowa yayi matu'kar farin ciki da bayyanar Husnahn, haka aka zauna ana maida zance ana kuma tuno ire-iren abinda ya fari da Husnahn ana bada misalai da su, yayin da Husnah ke cin abincin ta cikin natsuwa tana sauraren su...tana kuma sake tunanin irin rayuwar da tayi acan da mutanen da bata sani ba.

Ko mutun 'daya bazata ce ga kalar fuskar sa cuz basu ta6a gangancin zuwa inda take babu face mask ba wanda hakan ya kasance umarnin Alhaji Mamman ne, basu ta6a cutar da ita ko da wasa ba, dan ko bakin farcen ta babu wanda ya ta6a mata sam cikin su babu wanda yayi gigin kusanta kansa gareta, sun bata damar yin sallah sannan basu 'daure ta ba kawai 'dakin da take ciki ne kullum ba'a barin sa a bu'de, daga an kawo mata abinci da ruwa sai a sake datsewa ta waje...sau 'daya magana ya ta6a ha'da ta da wani shine ranar da aka ha'da ta da mahaifin ta cikin waya ranar ne ta san dalilin kama ta da suka yi, domin a lokacin taji mahaifin ta na fa'din ko nawane zai bayar shi dai su taimaka su sakar masa ita ta dawo gida...ranar kusan kwana tayi tana kuka da tausayin iyayen ta, shiyasa ma ta ringa addu'ar Allah ya kawo sanadin da zata bar hannun si cikin sau'ki...sai gashi kuwa da kansu sun 'dauko ta sun dawo da ita gida batare da sun yi mata komai ba.

Wannan tunanin da tayin ne ya sanya ta tunowa da mahaifin ta lokaci guda dan haka sai ta dubi mahaifiyar ta tace" Mummy ki 'kira Daddy na awaya mana kice masa na dawo ya daina nema na".

Take sai Mummyn Husnah ta 'dago wayar ta bayan ta jinjinawa Husnahn kai alamar gamsuwa da maganar ta.

'Kiran sa tayi da niyyar taji inda ya tsaya duk da ma dai tasan inda aka tura shi kaiwan ku'din da nisa sosai cuz can wajen gari ne amma ai tunda Husnah har ta dawo gida shima 'din kama ta yayi ace ya iso.

Sai dai ko tayi 'kiran sa sai bai 'daga wayar ba, missedcall uku ta jera masa ganin bai 'daga ba ya san ya ta tura masa text 'din albishir cewa Husnah ta dawo...ashe ma wayar tasa bata jikin sa tana cikin motar sa dake gidan Alhaji Mamman.

A fili tace da Husnah" Na 'kira bai 'daga ba, amma na tura masa text".

Shiru Husnah tayi yayin da sauran suka cigaba da hira bayan sun bata 'kwarin gwiwar cewa" Hakan ma yayi idan ya ga text din ma zai 'kira ko kuma yayi hanzarin dawowa ma gaba 'daya...".

Duk abincin taji tafi ce kanta shiru kawai tayi komai ya kwance mata.

Mahaifiyar ta ne ta lura da daina cin abincin da tayi sai tace" Eat mana Husnah..ki kwantar da hankalin ki kinji very soon zaki ganshi ya dawo da yardar rabbi".

"..To Mummy..Allah ya kawo shi lafiya, amma ni na 'koshi da abincin ne".

Kafin Mummyn Husnah ta sake fa'sldin wani abu sai wayar ta ta 'dauki 'kara, lokaci mintina takwas ne da 'kiran da tayi masa, da sauri ta 'dago wayar da tunanin ko shine ya 'kira amma sai ta ga sunan Hajiya Kareema ke yawo kan fuskar wayar.

Nan take kowa dake palourn suka yi tsit kamar 'daukewan ruwan sama suka baza kunnawa suna kallon Mummy da son jin abinda ke tafe da 'kiran wayar da akayin.

Afili Mummyn Husnah ta furta" Hajiya Kareema ce ta 'kira, ta fa'di hakan ne dan su san cewa ba wanda ake tsammanin bane.

Nan Hajiya Kareema take gaya mata cewa ai Alhaji 'Karami is unconscious yana asbiti ma yanzu haka....ta 'karashe maganar da sanar mata sunan asbitin da suke.

A rikice mummyn Husnah ta sa hannu aka tana sakin salati at same time tana kuka da hawaye wanda ya janyo hankalin Husnah da sauran izuwa gare ta...
Tsaye Husnah ta mi'ke a rikice tana fa'din" Mummy lafiya me ya faru kuma?"
Tayi maganar tana mai tahowa inda mahaifiyar tan take 'karara fuskar ta ta nuna alamun damuwa...Sauran ma tambayar da suka jefa mata kenan irin ta Husnah.

Tana cikin kukan tace da su" Wai bashi da lafiya yana asbiti".
Take palourn ya ru'de da salallamin jajantawa.

Mummyn Husnah kam cewa tayi" Wanda zashi ya shirya da sauri mu tafi...waiyo Allah na sun illata min shi".
Ta 'karashe da fa'din hakan tana nufar 'kofan fita.

Su hu'du suka tafi asbitin ciki harda Husnah, isar su asbitin ke da wuya sai ta sake 'kiran Hajiya Kareema ta kwatanta musu inda suke take suka nufi wurin sai dai likita ya hana su shiga saboda gudun hayaniya kuma wai zasu yi yawa a 'adakin.

A rikice Mummy tace" Doctor iyalan sa ne mu fa dan Allah karka yi mana haka...ki bar mu mu ganshi please bazamu yi hayaniya ba".

Tana hawaye tayi maganar, Husnah kam kuka harda sheshshe'ka take yi bata iya fa'din komai ba, sauran matan ma sai suka shiga ro'kon likitan amma ya kafe shi sam a a.

Hajiya Kareema na jin dramar tasu tana daga ciki ta fito da yake itan babbar likita ce a hospital 'din sai tace da likitan ya bar su su shiga 'kilan ganin 'yar san zai sanyaya masa rai duk dama tun zuwan su bai bu'de idanun sa ba, amma halin da yake cikin ya tsananta sosai...ga mutuwar gangar jiki saboda hawan jini sannan ga heart attack abin ba sau'ki gaskiya dole atausaya mai...bata iya ta bayyana farin cikin ta afili da ganin Husnah ba illah kawai ta janyo ta ta rungume ta tale kuma sai ta sake ta ta bata damar zuwa ta gana da mahaifin ta...daga haka ta wuce ta nufi office 'din ta.

Duk da Hajiya Kareemah tayi magana amma sai yace baza su shiga dukkan su ba dole sai dai da bibbiyu tunda su hu'du ne.

Nan sauran suka ce to Husnah ta shiga tare da mahaifiyar ta in yaso su 'din sa shiga daga baya.

Ana barin su shiga kuwa Husnah da gudu ta isa ta fa'da jikin mahaifin ta tana kuka, yayin da mahaifiyar ta ma ta dur'kushe nan 'kasan tiles 'din 'dakin tana kukan itama ganin sa kwance shame-shame kamar ba shi ba, duk da tayi zaton ganin sa jina-jina ne saboda tunanin ko 'yan kidnappers 'din ne suka illata shi da tayi, musamman da ta tuna yanayin da Nasiru driver ya dawo musu gida rannan, amma ga mamakin ta sai ta gansa haka babu wani alamun ciwo tattare da shi..duk da haka bata fasa yin kukan ba cikin ranta take ayyana Allah yasa ba na'kasa ta ciki aka yi masa ba..domin sau 'daya idan ka dibe shi zaka fahimci cewa yana jin jiki sosai.

Jin muryar Husnah cikin kunnuwan sa ne ya sanya shi bu'de idanu ya sau'ke su akanta yana 'dan murmushi da daga gani kasan na 'karfin hali ne..." Daddy please ka tashi gani na dawo,l..ka ganni ko Allah Daddy bazan sake tafiya in barka ba.. wake up Daddu please".

Haka kawai take ta maimatawa cikin kuka, yayin da mahaifinta ke binta da takaitaccen murmushi da shi ka'dai ya san ma'anar sa.

A hankali ya kai idanun sa kan mummyn Husnah dake 'dan nesa ka'dan da shi sai ya tsura mata idanu kamar me shirin bata sa'ko ko kuma wanda yake so ta karanci wani abu cikin 'kwayar idanun sa.

Lokacin da yake kallon nata sai idanun sa suka cicciko da 'kwalla, ganin hakan yasa take sai ta matso kusa da shi ta kama hannun sa tana yi mai sannu Alhaji.

Tari ya fara a hankali amma akai-akai wanda da kaga yanayin yanda yake tarin zaka fahimci cewa cikin azaban ciwo da ra'da'di yake yin ta.

A rikice Mummyn Husnah ta umarci Husnah da taje ta 'kira likita suzo a sake duba shi in bazai yiwu ba sai su wuce Zaria kawai dan bazata iya juran ganin Alhaji cikin wannan yanayin ba.

Da gudu Husnah ta fita yayin da mahaifin ta ya cigaba da tarin da yake yi amma a hakan ma sai da ya bi bayan ta da idanu...da 'kyar cikin tarin ya iya furta sunan..." Fa..tee..ma" bayan ganin fitar Husnah wanda tun kwanciyar sa bai iya furta komai ba sai yanzun Allah ya bashi ikon yin magana karo na farko.

Ita da bata san asalin abinda ya faru ba kawai sai tace" Na'am Alhaji ka kwantar da hankalin ka ga Husnahn ka ta dawo ai ka ganta da idanun ka ko?"

Bai bi takan maganar da tayi masa ba, burin sa kawai ya fidsa abinda ke cikin ransa, dan haka cikin dauriya yace
"...Fateema ki kula min da rayuwar Asma'u...dan Allah, kar ki bawa kowa ri'kon ta ki ri'ke min ita da kanki ki bata tarbiya mai kyau kinji?"
Mummyn Husanh take tace
" Insha Allahu Alhaji ka kwantar da hankalin ka kai ne zaka kula da rayuwar 'yar ka daina fa'din hakan".
Idanu ya lumshe sannan yace
"...Ki yafe min Fateemah...ki ce da Husnah ma ta yafe min kinji..da...da"
Sai kuma ya kasa 'karasawa saboda tsananin ciwo.

Shiru yayi na 'yan sekanni kafin ya sake furta" Fateemah!"

Wannan karan itama cikin sanyin murya ta amsa shi cuz jikin ta duk yayi sanyi sosai".

"....Duk yanda zaki yi Fateema ki 'ko'kar ta kiga kinsa an saki Nasiru kinji, Nasiru bashi da hannu akan wannan abin...ya gafarce ni nayi komai ne cikin rashin sani...gida na dake...ya fa'di sunan unguwar yace na bashi halak malak ki mallaka masa dan Allah...".

Baki bu'de take dubam sa tambaoyi ne fal cike a bakin ta amma sai dai kafin ta yi magana likita ya shigo da Husnah a bayan sa, nan ya nemi su basu wuri zai yi aikin sa, hakan yasa duk sukayi waje badan ransu na son hakan ba.

Wannan shine 'karshen ganawar mahaifin Husnah da iyalan sa, awa guda bai 'kara a duniya ba bayan fitar sun Allah ya kar6i ransa...batare da ya sanar da kowa abinda wansa ya aikata masa ba...haka ya tafi ya bar Mummyn Husnah da tarin tambayoyin da shi ka'dai ya kamata ya amsa mata su, amma ina ba dama..domin wanda ya fi ta son shi ya 'dauke abin sa.

Husnah tasha kuka da jin rasuwar

Please Login or Register in order to submit comment