Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

koma, kuma ko wannan 'din ma zallar 'kauna ce da kuma yadda aka nuna, tunda dukiyar sa ya 'dauka ya dam'ka a hannun  Baban mu, amma sai gashi tun ba'aje da nisa ba abin ya koma kanta, tun zaman su da Baban mu bai ta6a ko tunanin yi mata kishiya ba balle aje ga yin ta, yanzu kuwa tashin farko sanadin Alhaji Baba gashi an mata kishiya, duk da cewa ita ta kawo shawarar amma dole da ciwo hakan nan kamar jira ake ba'a 'dau wani dogon lokaci ba komai ya kammala.

Sosai abin yake cin zuciyar Ummahn mu, wani sa'in sai taji tamkar dan ita su Alhaji Baba suka dawo garin mu, tunda gashi dumu-dumu an sar'ke ta ta 6angori biyu masu girma, an wargaza mata gidan ta ta yanda sake dun'kula shi zai yi mata wahalar gaske.

Duk kuwa yanda abin ya dami Ummah bata ta6a hirar da wani ko wata ba ciki kuwa hatta yaran ta, ta ri'ke ne daga ita sai zuciyar ta da fatan Allah yayi jagora kawai...idan hakan Alkhairi yake nufi ubangiji Allah ya tabbatar da shi.



*****
   'Bangare na kuwa bani da matsalar komai cuz duk abinda nake so shi ake yimin, hatta da gashin kaina sai da ya san da banbamci dan kuwa ba 'karamin kula yake samu daga wurin Ammi ba, har yanzu kuwa na kanje gidan mu, ni ka'dai wataran kuma da Ammi muke zuwa, lokacin da su Saif suka dawo hutu ma sai da muka je dasu Ammi ne tace muje mu gaida Ummah ta.

Ummah bata ta6a nuna min komai ba dake cikin ranta, haka zamuje mu gama iya zaman mu tana nan nan damu da nuna farin cikin zuwan mu a fili...bazaka ta6a fahimtar alhinin dake 'kunshe cikin ranta ba.

A hankali ma abin ya bar ranta da tayi tunanin kowani bawa kafin a halicce shi sai da littafin 'kaddarar sa ta zanu, komai yana tafiya ne bisa tsarin ubangiji to ita waye da zatace ba haka ba...tun da Ummah tayi wannan tunanin sai ta watsar da komai ta cigaba da harkokin ta, Addah ta ma yanzu ta samu sau'ki tunda ta fa'dawa mijin ta halin da take ciki a gidan shi kuma ganin gidan harda matan yayyen sa so ba dama shi yayi magana hakan yasa yaje ya dur'kusa ya zayyanawa mahaifin sa komai...da kansa ya tara su ya musu 'kira da babban murya akan baya son fitina kuma basu bawa mai tada ta goyon baya ba dan haka kowa ta kiyaye bakin ta, idan abin magana ne da wuya ka rasa ko wani mutun da shi me yasa za'a ringa takurawa Saudah a hana ta sakat bacin ba ita ce da alhakin komai ba...daga 'karshe yace kowa taja girman ta kowa ta kama mutuncin kanta baya son ya 'kara jin wani abu makamancin hakan ya taso in kuma ba haka ba to shikenan..yace da kansa zai 'dauki mataki akan koma waye".
Wannan jawabin ne ya 'dan samawa Addah ta sassauci a gidan har yasa ta koma ta cigaba da rayuwar ta kamar da can.

Baban mu ya kanzo duk lokacin da ya samu dama sai dai baya yin ko sati yake komawa 'kar'karin sa yayi kwana biyu ko uku shikenan ya koma.


*****
    'Bangaren Yah Deen ma sun sake samun hutu kuma yazo da yake idan ya tafi baya ko le'ko gida har sai semester ta 'kare, hakan ya sa har mantawa nake yi da shi, dan ko awaya ban ta6a gaisawa da shi ba...and kuma still a wancen gidan nasa ya zauna ni kam hakan yafi komai yi min da'di.....sai dai wannan karan Ammi ce masa tayi bazata tura kowa dan yi masa aiki ba, ai gida yanzu babu kowa tunda su Saif basu nan illah ni ka'daice me ze hana shi dawowa ya zauna tunda ba 'yan hayaniyar...da 'kyar Ammi ta amince ta yadda masa bayan uban ro'kon da yayi mata ranar farko ma a gida ya kwana amma washe gari muka je da shi na taya shi gyara gidan inata tura baki na gashi mai aikin Ammi bata zo ranar ba.
  Ranar nasha wahala sosai dan ma bai zauna ba shima tare muka yi aikin da yake yana so ya zauna a
gidan sai ya zage damtse ya manta da batun fi'ili, nima kuma gudun kar inje inyi abinda zaisa ya ta6a lafiya ta ya sa na saki jiki muka yi aikin tsaf.

Ko bayan da muka 'kare na riga shi komawa gida, sai kuma na sa Ammi a gaba na rin'ka yi mata kukan ciwon kai da gajiya, ita kuwa ta ringa masifan wai ya wahalar dani, haka yazo ya sami Ammi na ta sababi ita ka'dai ni kuma ina kuka.

Tsaki yayi zai shige ciki cike da 6acin rai dan yasan iskanci ne kawai ke damuna.

" Dan uban ka zo nan Muhammad".
Ammi tace da shi a fusace cikin harshen su na Igbo.

Sai ya dawo yana tattare goshi da 6acin rai yace..." Allah Ammi iskanci  kawai ke damun yarinyar nan...ki tambaye ta mana ita 'daya tayi aikin ne?"

Gira Ammi ta 'dage sama tana duban sa da mamaki tace " Ashe ma ka san abinda ka aitaka kenan?"
Sai ya kauda kansa gefe ji yake tamkar ya rarumo ni ya jibge ni.
" Wato dan ka samu na barta taje shine zaka min iskanci anan ko Mu'een? Ba ma zakace sannu ba sai ka hau yi mata masifa kaima ko? ba lafin ka bane ai na san isar ka ce ta sa hakan, shikenan je ka abinka....gobe ma ai rana ce zanga wa zai sake yi ma sharar ai".

A fusace ya shige 'dakin sa batare da ya 'kara furta komai ba.
Wanka yayi sannan ya fito ya sake fita abin sa bai ko sake kallon in da muke ga dukkan alamu fishi yayi da masifar Ammin.

Ni kuwa Ammi rarrashi na ta dinga yi tana lalla6ani, da kanta ta rakani 'daki tace in je in watsa ruwa bayan na fito ta bani magani nasha na kwanta sai bacci.

Ban 'kara ganin Yah Deen ba har sai dare lokacin sallahr isha'i suna shirin fita masallaci yake ce da Ammi wai sai da safe
" Saida safe zaka ce ko, ka wahal min da yarinya sannan ko ya take ko ya gajiya bazaka yi mata ba zaka wani ce sai da safe?"

Juya idanu yayi gami da rintsewa ya kuma bu'de su nan take cike da 'kosawa yace " Allah Ammi kina 6ata yarinyar nan da yawa ita ba mace bace...dan tayi aikin shara shikenan ya zama wani abin sakalci?"

Zata sake magana yace " Zanje masallaci please Ammi sai da safe zanzo in duba ta".
" Hmm"
Kawai Ammi tace da shi daga haka bata 'kara fa'din komai ba.

  Washe garin kuwa da yazo ko bi ta kaina bai yi ba ni ma dama kuma banso, haka ma Ammi bata 'kara tada maganar ba da yake dama da gangan take yi masa saboda gaba dan ya ji shakkan sake bani aiki mai wahala.


*****
   Bai nemi a sake yi mai aikin ba dan gudun masifar Ammi har kusan kwana uku, kuma sosai ya rage zuwa gidan yanzu, sau 'daya tak yake zuwa wanda ni kam ma wani lokacin bana sanin yazo balle in san lokacin tafiyar sa.

Har akaci sati guda yana lalla6a rayuwar sa acan, da kansa yake yin sharar sa, yana so ai masa mopping amma fargabar abinda Ammi zata ce ya hana shi furtawa gashi kuma shi bai iya ba.

Kwance yake yana tunani a wani dare da bacci ya gagare shi gaba daya feelings ya takura shi haka ya dinga taso masa kamar abin masifa, ba ranar ya fara ji ba amma sai na yau 'din ya bambanta da sauran ranakun da yake ji.

Cuz ya kasa jurewa har cikin sa sai da ya ri'ke shi, bai san me ze yi ba hakan yasa ya ri'ke cikin kawai ya mi'ka rayuwar sa ga Allah mahalicci.....kafin cikar awa biyu kuwa zazza6i mai zafi ya rufe shi jikin sa na kakkarwa.

Haka ya kwana yana fama da rayuwar sa, ranar hatta sallar asubah ma a makare yayi ta dan bai samu bacci ya 'dauke shi da wuri ba shiyasa ya makara.

Duk jikin sa bai jin da'din sa sosai dan haka sai ya 'kira Ammi a waya ya sanar da ita cewa bai jin da'di ta aiko masa tea kawai.

Bai ambaci sunan kowa da ai kawo ba dan gudun masifar Ammi kawai ya yanke 'kiran.

Ai kuwa Ammi sai tabi wayar da kallo a fili ta furta kalmar  " munafuki".
Sake dialling number tasa tayi kafin yayi magana tace " saura kuma idan na aiko ta ka sa ta aiki a gidan ka gani"
Ya riga ya san wa Ammi take nufi dan haka sai yace " Ammi ni na nace sai ita ne...ni ma ba san zuwan nata nake yi ba ai"
ya 'karasa maganar  'kasa-'kasa...dan har lokacin bai gane kan jikin sa ba.

A masifance Ammi tace " Sai ka fa'di wanda ka ajiye da zai ringa yima aika  agidan ai, idan ba itan ba wa kaga nake dashi yanzu?"
" Kuma dai"
Ya furta a hankali yadda Ammi ba zata jiyo shi ba ha'di da sakin murmushin takaici...sannan a hankali cikin natsuwa yace
" Ammi wai dan Allah yaushe kika daina so na ne? Fisabilillahi cewa fa nayi banjin da'di amma kike ta min irin wannan masifar Ammi, idan babu mai kawo wa kawai abar shi shikenan na fasa ma".
Daga haka ya yanke 'kiran harda kashe wayar shi gaba 'daya.




~Ina gaida masoyanah Allah ubangiji yayi ta faranta muku cikin kowani irin yanayi...Salmerh na 'kaunar ku irin sosai 'din nan~ 🥰😘



_Comment_
_Vote_
_Share_






*Salmerhn ku ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)


By
*Salmerh MD*

 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

🤞🏻

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*


🅿 *37*

Bansan yanda suka yi dashi ba ni dai kawai tace dani in shirya in kaiwa Yah Deen tea a gidan can wai baya jin da'di.

Ban damu ba da na ji tace baya jin da'di dan haka raina fari tas na kar6a na kama hanyar gidan da yake.

Koda naje 'kofan a rufe take sai dana ta bubbugawa kafin yazo ya bu'de bayan na shafe a'kalla kusan mintina goma sha uku ina tsaye.

Ina jin an bu'de 'kofar sai na nutsu kamar wawuya daga bu'dewa nace " Ina kwana". Nayi maganar ina sunkuyar da kaina, bai amsa ba haka kuma bai ce da ni komai ba  maimakon ma ya kar6i abin hannu na a a sai kawai ya bani hanya ya koma ciki abinsa batare da ya sake kallon inda nake ba.

A hankali nabi bayan sa bayan sa na shigo sannan na maida 'kofar na rufe ina 'kuk'kuni cikin zuciya ta.

Har parlour na shiga na same shi zaune yayi 'da'd'daya bisa kujera take na kauda kaina gefe bayan kallo 'daya da na mishi a hakan ma banko yi gigin kallan fuskar sa ba...ina shirin ajiyewa naji kakkausar muryar sa dake cike da 6acin rai yace" wai ke dan uwar ki miye ala'kar ki da Ammi?"

   Jikina rawa ya fara take idanu na ya cika da hawaye jin tsawan da ya daka min.

Sai na fara in ina ina fa'din " Ni...ni"
Yace " a a uban ki"!
Take kuka sai hawayen tsoro suka taru cikin idanu na.

Ganin nayi masa shiru ne ya sanya shi tashi ya dai-dai ta zaman sa yayin da ni kuma motsin da yayin ya sake firgita ni zato na ko hi zai yi ya dake ni hakan ya sa na saki sheshsh'ka ina jan baya ka'dan.
A tsawace yace.
" ki min shiru da Allah ni..."
Tsit nayi na maida kukan gami da toshe baki na da hannu na duk biyu illah hawayen dake zuba min kaina 'kasa.

" Munafuka kawai, ba kina jin Ammi ke zagi na ba lokacin bakiyi kuka ba sai yanzu?"
Daga jin yanda yayi maganar zaki fahimci cewa cikin 'karfin hali yake yinta amma dan masifa da sabo da yayiwa zuciyar sa da shi ya sanya shi tilastawa kansa yin sa.

Ina so ince masa " Allah ni banji ba". amma tsoron yin magana nake yi.

   "...Kuma ranar nan da kika je kina yi mata kuka 'din yankan jikin ki nayi?"
Naji ya 'kara fa'di.
Sai na jijjiga kaina alamar a a still ina hawaye.

" Na dake ki ne..ko kuma ke ka'dai na bari kika yi aikin?"
Nan ma da sauri na girgiza kaina.
"...oww wato munafurci dan ki ha'da ni da Ammi na ko?"

Da 'kyar nayi dauriyan furta
" Dan Allah kayi ha'kuri wallahi bazan sake ba...." Nayi maganar murya ta na cracking.
"...kima sake"
Ya tare ni da fa'din haka.
"Ai kin isa".
Ya sake fa'di.
Sai nayi shiru ina kallon sa hawaye na na zuba ji nake tamkar in zura da gudu inyi waje.

"..Ba kin sami 'daurin gindi daga wurin Ammi ba?
" a a kayi ha'kuri"
Nace dashi da muryar kuka.

Bai ce dani 'kala ba kawai sai naga ya koma baya ya kishingi'da, da hannun sa ya nuna 'kasan 'dakin sannan yace " Zo nan"!

Sheshsheka na saki cike da tausayin kaina a hankali na matsa kusa neasa ka'dan da shi na tsugunna kan gwiwoyi na cuz wannan karan ba 'karamin tsorata nayi da shi ba.

Tashi yayi ya dan rankwafo Kano dan gami da kama kunnan sa ya wani  'kan'kance idanu tare da nuno ni da yatsa yace
" Daga yau...me nace...?"
Namaimaita " Daga yau" kamar yanda ya fa'di.
" Idan kika kuskura kwana uku ta cika ban ganki cikin gidan nan kin zo sharewa ba wallahi take wuyan ki zanyi in karairaya ki...kinji abinda nace ko?"
Da sauri na 'dage kaina sama wani hawayen na sake gangaro min.

"..Useless kawai..."
Ya fa'di tare da komawa baya ya jingina da kujera sannan ya 'kara fact 'din " 6ace ki bani wuri".

Da sauri har ina 'ko'karin fa'duwa na tashi na nufi 'kofar fita sai kuma naji yana sake fa'din " Saura inji abakin Ammi....kashe ki zanyi da wu'ka babu ruwa na".

Da sassarfa na fice daga gidan ina share hawaye na...ko nayi niyyan yin shiru sai in kasa saboda takaici da kuma girman tsorata da nayi gashi ya hana ni sanar da Ammi.

Gudun kar in je gida ina kuka ne ya sanya ni zama jikin wani gida na sha kuka na son raina sannan na share hawayen tas na tashi na 'karasa gida ina sakin ajiyan zuciya.

   Ko da naje a parlour na tarar Ammi inda tana gani na kuwa ta tsura min idanu, sai nayi 'kasa da kaina ina 'ko'karin wucewa ciki sai tace da ni " zo nan Hudah..me ya same ki?".
Ta 'karasa da tambayata cike da kulawa.

Kaina 'kasa amma sai na kasa cewa da ita komai..ban sani ba aseh shirun nawa ya sa Ammi tabbatar da cewa akwai abinda ke damu na.
'Dan 6ata rai tayi tace " Shine ko?"
Jin haka yasa nayi hanzarin girgiza mata kai alamar a a.
" To menene?"
Ta sake tambayata tana kallo na.
Kaina kasa nace" ba komai fa Ammi".
Yanda nayi maganar yasa ta tsaya 'kare min kallo sosai tana karantar yanayi na.

Ganin har a lokacin ban 'dago na kalle ta ba ya sanya ta 6ata rai sosai a fili tace " Wato Mu'een bai jin magana ta ko?"
'Dagowa nayi da sauri jin ta ambaci sunan sa baki na har na rawa nace da ita " Ni..fa Ammi ba shi..bane...na ha'du da shanu da yawa a hanya ne irin na rannan... shine suka bani tsoro nayi ta kuka".
Ido ta tsura min sosai tana kallo na yayin da wasu hawayen ke sake sau'ko min ban kuma 6atawa kaina lokaci na share su ba dan nasan ko na share ma ba tsayawa zasu yi ba.

Can sai Ammi saki ajiyan zuciya ta janyo ni jikin ta cikin kwantar da murya tace" Ya isa haka nan to daina kukan kinji...bama zaki sake zuwa can 'din ba balle ki ha'du da su".

Jikin ta na kwantar da kaina ina ta sakin ajiyan zuciya, sam Ammi kam bata yadda da magana ta ba amma ta bari cikin ranta...musamman ma data ga yanda na yini sukuku a gidan babu walwala abin sai ya dame ta sosai dan tasan ba ganin shanu ka'dai ne zai sani hakan ba.

   Da yamma kuwa sai gashi yazo gidan cuz ranar basu da buga 'kwallo.

Gaida Ammi yayi ta amsa babu yabo babu fallasa fuskar ta wasai, d next thing abinda ya fito bakin ta shine..." Me ka yiwa Hudah ta da na aika ta da safe?"
'Dan 6ata rai yayi cike da basarwa yace " Ammi wa ce kuma Hudah?"
" Bansan iskanci Muhammad kai kace in sa akai ma abu kuma sai ka je ka samin yarinya kuka?"

" ohh....wai waccen yarinyar ?"
" a a uwar ka nake nufi".
Ta bashi amsa ada'kile.
Ganin haka sai ya sashi zuwa gefen ta ya zauna yana fa'din " Allah Ammi ni duk bangane abinda kike min ba kwanan nan, gaba 'daya kin daina 'kauna ta saboda yarinyar can, komai nayi masifa kike min....ki tambaye ta mana in akwai abinda nayi mata ai da zata sanar dake na sani tunda ba abakin ta nake zaune ba".
Ya 'karashe maganar da sanyin murya.
Kauda kai Ammi tayi tare da fa'din " kai de ka sani, gaba ai tafi baya yawa.."

" Ni dai yunwa nake ji Ammi..abar zancen please".
Yayi maganar yana shafa cikin sa.
Dinning ta nuna masa tace " Ga can abinci je ka 'diba kaci mana".
" Da kaina kuma Ammi?"
Wani kallo da tayi masa ne ya sashi sakin murmushi ya mi'ke yana girgiza kansa..cikin ransa yake fa'din " ai dole ma in ringa cin uban yarinyar nan ko dan huce takaici na".

   Ban gayawa Ammi cewa yace in dinga zuwa yi masa shara ba gudun kar tayi masa masifa ni kuma ya kashe ni, dan haka duk ranar da ya kamata inje sharar bana magana sai dai kawai inna shirya zuwa makaranta sai in bi ta gidan inje inyi masa kamar yadda ya fa'da, sau tari sai a lokacin break nake samun zuwa idan har nabi yi masa sharan dan wani lokaci harda wankin kayan ball da socks 'din sa yake bani, dan mugunta kuwa yana gani na sanye da Uniform amma bai ta6a cewa in bari in yi tafiya ta makarantar ba...sai dai abu 'daya bai ta6a duka na ba.

Idan kuma ranar babu makaranta to sai lokacin islamiya nake zuwa nayi masa aikin, wanda zuwa yanzun na fara fahimtar bashi ka'dai ke zama cikin gidan ba harda wani abokin sa mai suna Imrana dan ina yawan ganin ya shigo ko kuma wani sa'in su fita tare ...'dan iska ne na na 'karshe sam tarbiyya bata wadace shi ba,  kusan kowa kuma ya san halin sa a garin...shima Yah Deen 'din gurin ball suka ha'du dashi har suka 'kulla abota.

     Ni dai magana bata ta6a ha'da ni da shi ba illah gaisuwa idan na gaida shi ya amsa min da muryar sa da take abu'de, shima 'din kuma baya shiga harka ta musamman da yake idan nazo komai a tsarge nake yin sa bana sakin jiki na, kuma ma shi ya zaci ko 'kanwa nake ga Yah Deen shiyasa bai ta6a nuna min halin sa ba sam..shima sai yake min kallon 'kanwar sa..gashi kuma ma yana gudun zuciyar Yah Deen sosai shiyasa ya tsaya iya matsayin sa.



*****
     Ma'u itace mutun na farko da ta fara fahimtar halin da nake ciki na rashin zuwa makaranta akan lokaci, da kuma zuwa gidan Yah Deen da nake yawan yi yanzu, dan ma mun 'dan jima bamu ha'du da ita ba nasan da tuni ta jima da fahimta, amma da yake  mahaifin ta ya hanata yawan fitan nan da take yi shiyasa bata san da faruwar hakan ba.

        Akwai wani 'dan wan mahaifin ta da yake son ta da aure, mahaifin ta yaso ya ha'da auren su idan shekarun ta sun kai amma sai Ma'u ta nuna sam bata ra'ayi, hakan yasa ya barta batare da ya takura ta akan hakan ba, sai dai ya taka mata burki akan yawan fitan da take yi illah zuwa makaranta shima 'dib jifa-jifa ne...shiyasa ma muka kwan biyu bamu ha'du da ita a unguwar Yah Deen ba.

Wata ranar laraba ne da aka tashi a makaranta muna hanyar komawa gida hanya ta ha'da mu da ita sai take ce min" Yauwa dama ina so in ganki in tambaye ki"
Da " To gani ai " na amsa ta sai tace..." wai me yasa yanzu nake yawan yin lattin Islamiya da makaranta tace kinga fa yau Allah da kin sha duka sosai badan na bada ha'kuri ba?"

Take na 6ata raina kamar dama jira nake yi kamar zanyi kuka nace da ita " Ba wannan Yayan bane yake sani aiki kullum, kuma yace kar in fa'dawa Ammi shiyasa idan zani makaranta sai in bi inyi masa aikin".
Ido ta zaro tana fa'din wai dama har yanzu yana nan ne?"
Kai na 'daga mata alamar " Erh"
Ma'u kam sai tace kar in damu duk ranar da zanje aikin inbi ta gidan su zata na raka ni sai mu gama da wuri mu tafi.
Da murna ta na amsa da to har muka rabu kuwa ina jin farin ciki har cikin raina.

Tun daga lokacin muke zuwa gidan ni da Ma'u duk kuma jikin mu da kayan makaranta muke zuwa, cikin sa'a kuwa muna yin aikin kaf mu gama mu kuma wuce makaranta batare da mun yi latti ba, haka kuma wani lokacin har mu tafi bama ha'duwa da shi da yake ni dama in ba ganin sa nayi ya fito ba ban 'kwa'kulo shi dan wai in gaida shi.

Sau uku kacal  muka je da Ma'u Allah sai ya taimake ni ya tattara ya koma makaranta, ranar da ya tafin kuwa nafi kowa farin ciki tamkar in zuba ruwa a 'kasa insha haka nakeji.



*****
     Level 2 ya koma yanzu, sai dai ya fara ta ne da wata sabuwar rayuwa, rayuwa ce mai cike da 'kazanta, domin kuwa Husnah ba Campus ta zauna ba wannan karan gidan sa ta koma da zama...wanda da 'kyar ma ya amince sai da tayi masa al'kawarin bazata na shiga shirgin rayuwar sa ba.

Husnah bata damu da wani dokar sa ba cuz ita damuwar ta kawai ta same shi, yawan shariyar da yake yi mata cikin makaranta sosai ya ishe ta, gashi kuma dalilin sa ta rabu da ko wani saurayi bata kula kowa a lokacin.

Sai kuma cikin rashin sa'a sai ya kasance wanda take yi domin san bai san tanayi ba, sam bai damu da ita ba, baya neman ta matu'kar ba ita ta bu'kaci ganin sa ba.

Zaman su 'kar'kashin muhalli daya ne take ganin tamkar zai kawo mata sau'ki a zuciyar ta, dan tasan dole a kowace rana ta ganshi wanda take saka ran yawan kusancin su zai kawo mata sau'ki wurin saurin dasa soyayyar ta a zuciyar sa.

Ko da ta dawo 'din kuwa ba wani yawan shiga harkar ta yake yi ba, baya zama da ita dan wai suyi hira, haka ya tattari rayuwar sa gaba 'daya ya mayar cikin 'dakin sa bata fiye jin 'duriyar sa ba.

Sai dai duk wannan bai damu Husnah sosai ba tunda atleast ita ke yi musu girki kuma yana zama yaci...tasan duk tsiya dole watarana sai saki jiki da ita.

  Gidan dama 2bedroom ne dan haka sai ta shiga 'dayan ta tsara shi dai-dai da mura'din ta ya zama nata yayin da Yah Deen yake cikin 'dayan.

Daga baya abin yaso ya dame ta ganin cewa baya wani shiga harkokin ta, gashi babu wani abokin hira sa6anin da da take Campus da ba ya rabo da jama'ah, harma sai ta fara ganin tamkar an gudu ne baa tsira ba..tunda gashi akusa da ita kamar yanda ranta ke so amma sai dai kuma bata samun sakin fuskar sa sosai...sai daga baya ne ta basar kawai ta cigaba da harkokin ta ta daina damuwa.

'Bangaren Yah Deen kuwa ada yana lalla6a rayuwar sa ne da da'di babu da'di, yakan juri duk ciwo da damuwar da ta taso masa amma wannan karan da ya kasance da mace cikin gidan sai yake yawan sako ta cikin shirgin damuwar sa.

Husnah kuwa babu ruwan ta itama rayuwar ta takeyi irin wanda take so,  bansani ba ko mantawa takeyi da cewa shi'din ba muharramin ta ba ne oho...duk irin shigar data ga dama yi take yi, ita zatayi musu abinci ta gyara gidan tsaf tamkar matar sa, gata da tsafta ba laifi.

Babu abinda ya dame ta zaman ta

Please Login or Register in order to submit comment