Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Me kuma ya dawo da ita yanzun?"
Ya tambayi kansa..shaf ya manta da cewar dama 'karfe hu'du zata dawo..2-3 ne last lecturen ta na yau...tuni hankalin sa ya koma gare ta sai dai bai bari Uncle ya gano sa ba ya dake kawai suka cigaba da tafiya zuciyar sa cike da fargabar kar ta tona mai asiri, har suka kusan ha'duwa da ita bai daina satan kallon ta ba.

Yayin da itama Husnah tun da ta hango shi tafe da wani mutun ta tsura musu idanu da tunanin ko wanene mutumin oho...sai dai Husnah har cikin ranta bata yi niyyar tanka shi ba..cuz da gani mutumin ba sa'an shi bane in kuwa haka ne magana ga junan su agaban idanun sa sam bai dace ba ko dan su bashi girman sa matsayin babba agare su.

Shi kam Ya Deen ya kasa natsuwa sam duk sai ya raba hankalin sa gida biyu, ji yake da da wata hanyar agaban su kafin ha'duwar su da Husnah da yace su bita koda kuwa ba ita ta dace su bi ba amma a lokacin kaucewa Husnah shi zai fi komai yi masa da'di cuz gani yake kamar zata tona asirin sa.

Ganin sun kusan ha'duwa ne ya sanya shi jan hankalin Uncle J da labarin makaranta, yana fa'da masa ire-iren wahalar da yake sha, shi kuwa Uncle Ja'afar na bashi 'kwarin gwiwa da fa'din me ma ya rage kuma ai saura ka'dan, yace ha'kuri kawai zasu yi sun ma yi mai wuyar ai saura ka'dan ne cuz dudu semester biyu kacal ne ya rage masa....tun kan Husnah ta iso daf yake yi mata wani irin kallo, da ido yake nuna mata alamun kar ta kuskura ta kula shi, da suka kusan ha'duwa kuwa sai ya kauda kansa gefe tamkar bai ganta ba wanda hakan ya bayyanawa Husnah cewa shima 'din baya so tayi masa magana ne, hakan yasa itama ta 'dauke kai tayi wucewar ta kamar yadda ta yi niyyar yi da tunanin waye wannan mutumin to...sai dai ta fahimci koma wanene mutumin to mai matu'kar daraja ne a wurin Mu'een...kuma yana mutunta shi gami da girmama shi irin na musamman 'din nan.

Sam Uncle J bai fahimci komai tsakanin su ba, da yake sam baya kawo ko zargin Yah Deen akan irin wannan abin ko cikin ransa...ko abinda ya gaya masa 'dazun ma ba wai ya zarge shi haka kawai bane, illah tunanin da yayi kan cewa haka a banza Alhaji Baba bazai takura shi akan maganar aure ba dole ne akwai wani abin wanda baya fatan yaji abinda zai ta6a masa zuciya akan mafi soyuwa cikin zuciyar sa wato Mu'een.

Har ajiyan zuciya ya saki lokacin da yaga ta shin motar su Uncle J, cuz har cikin tasha ya raka shi.

Hamdala ya ringa saki ganin bayan motar tasu, musamman da Allah ya rufa mai asiri ba suje ga abokin Uncle da yace zasu je ba.. Lokacin suna wani eatry ne sunje cin abinci bayan barin gidan Yah Deen da suka yi, har sun gama cin abincin suna niyyar tafiya sai yace dashi wai zai raka shi wurin wani abokin sa har da yi masa kwatancen wurin.

Nan take hankalin sa ya tashi da jin sunan wanda Uncle J 'din ya ambata da kuma sana'ar sa...kuma already tun daga kwatancen da yake yi ya fahimci wurin.

Mamallakin babban medical center da ya ta6a zuwa sayo magani wa Husnah ne da yake tunanin yaje da nisa inda babu wanda ya sanshi ya sayo drugs 'din, sai gashi Uncle J na shirin banka'da asirin sa da fa'din wai zasu je ya gaisa da shi wai abokin sa ne..." to idan ya gane ni kuma fa?"
Ya tambayi kansa...Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..ya nanata cikin zuciyar sa kusan sau uku.." wai yau 'din nan me ke shirin faruwa da ni ne?"
Ya tambayi kansa, sannan ya sake fa'din" Idan kuma ya gayawa Uncle na ta6a zuwa wurin sa sayan magani kaza kuma fa... ya zanyi in 'karya ta shi ni Muhammad".
Fargabar sa 'karuwa tayi sosai akan nada duk kuwa da yasan cewa ba lallai ne mutumin ya gane shi ko tuno abinda ya kaishi wurin sa ba, amma kunsan abin ku da marar gaskiya..zuciyar su rangaji take bata tsayuwa wuri guda.

Kamar Uncle J ma yasan tunanin da yake yi sai yace" Bari dai in 'kirashi inji ko yana nan".

Sai yanzu ya iya samun damar fa'din" Gaskiya is better ka 'kira shi kam dan wurin akwai nisa ga kuma tafiya a gaban ka..."

Yana 'kira kuwa bayan sun gaisa sai yace da shi ai yana Dutse, mutumin sai yace shikuwa wallahi yana Kano amma wai gobe zai dawo why not ya jira shi...Uncle sai yace masa a a yana kan hanya ne dama sai dai wani lokacin kuma idan Allah yayi".

Da haka suka yi sallama yake yiwa Mu'een bayani...tsabar murna ma bai san lokacin da ya saki ajiyan numfashi ba har har da fa'din _Alhamdulillah_
Uncle J sai da ya dube shi yace" Ya dai".

" Bakomai Uncle banson kayi dare ne kasan kasar tamu sai a hankali".
Ya bashi amsa yana 'yar dariya...sai yace" Hakane".

Daga nan suka nufi tashar mota...ya tafi abinsa.

Ko yanzun ma ganin har Uncle J ya tafi bai fahimci komai game da rayuwar sa ya sanya shi a fili ya furta" Alhamdulillah".
Sai dai har cikin zuciyar sa ba zai iya bayyana a wani matsayi ya ajiye wannan ziyara ta Uncle Ja'afar ba, shin farin ciki zaiyi da shi ko akasin haka?"

Shi da kansa ya san ba dai-dai yake aikatawa ba amma yayi watsi da sanin sa, banda nasihar Ammi gare shi...sannan ga fushin mahaifin sa, duk hakan bai sa ya bar abinda yake yi ba.

Allah ma sai ya sake rufa masa asiri ya tsallake dukkan stage 'din da ya kamata Uncle J ya gano sirrin rayuwar sa...'dan baya gane cewa idan duk ka tsallake irin wannan kalubalen bayan kayi watsi da sanin ka, ka yi watsi da fushin manyan ka ka cigaba da aikata abinda ranka ke so to Allah yana so ya maka talala ne, ranar tonuwan asirin ka na nan yana jiran ka duk da'dewan shekaru kuwa dole ranar sai tazo, ranar da baka isa ka 6oye laifukan ka ga kowa ba...(ALLAH UBANGIJI KA SADA MU DA HASKEN KA, KA KUMA GYARA MANA ZUCIYOYIN MU KA SANYA MU CIKIN BAYIN KA SALIHAI AH'LUL JANNAH...(AMEEN YA RABBAL ALAMEEN).

Mashin ya hau ya koma gida, bai bi ko ta kan Husnah ba kawai yayi alwala ya wuce masallaci abinsa cuz la'asar ake 'kira a lokacin.

Ko da ya dawo daga masjid 'din ma direct 'dakin sa ya wuce, zuwa yanzun rayuwar da yake yi 'din tafara isan sa, shi kansa ya san cewa ba abin kirki yake aikatawa ba...sannan ba ya kyautawa iyayen sa musamman ma da ya tuno nasihar Ammin sa agare shi lokacin da zai taho, sai gashi cikin lokaci 'kan'kani yayi watsi da komai yana aikata abinda yasan Allah da kansa baya so...sosai yake so ya zama mutun nagartacce kamar kowa, so yake ya zama yaron da iyayen sa zasu yi alfahari da kasancewar sa da agare su, ba irin wanda ake Allah wadai da shi ba a duk lokacin da 6oyayyen halayyar su ta bayyana....sai dai tayaya zai iya hakan?"
Ya tambayi kansa..da farko dole ya san sai ya sallami Husnah ta bar gidan shi..in hakan ya faru to ina zan je da bu'katu na?"
Ya sake tambayar kansa..goshi ya dafe sannan ya furta" Iyaye na fa?..ya zanyi da su duk ranar da suka gano abinda nake aikatawa.." Ya Rabb please help me".

Yanzu da ace Uncle Ja'afar ya kama shi kan hakan fa.. da ya zaiyi?"

Juyi yayi kan gadon sa yana sake tunanin abin sosai ya dame shi, yana so ya zama nagari amma kuma yana gudun irin halin da zai shiga...not knowing that komai sawa arai ne musamman abu dangin zunubi.

Idan kasa aranka shai'dan sai ya 'kara ingizaka ya rura maka wutar 'kaunar abin cikin ranka...juyi ya ringayi yana tunanin mafita da ya gaji sai ya tashi ya fa'da bayi.


*****
     'Bangaren Uncle Ja'afar kuwa ranar da ya isa Shuwarin basu samu daman ganawa da Alhaji ba sai washegari...sai dai ko a lokacin da suka zauna kan zancen ma.. Alhaji bai fito fili ya bayyana masa asalin dalilin da yasa yake so ayiwa Yah Deen auren ba...kawai ce masa yayi ya fahimci yana da bu'katar auren ne dan haka ba za'a 'dauki dogon lokaci ba yace already ma ya gama binciken da ya dace ayi.

Da Uncle Ja'afar yaji Alhaji Baba ya ambaci Azare ne yasa ya tuno da maganar Mu'een da ya fa'da masa kan yarinyar da yace tazo wurin sa daga Azare.

Nan ya bu'di baki dan yiwa Alhaji bayani amma ya dakatar da shi yace baya son jin komai shi dai kawai burin sa ya fahimci inda ya dosa.

Uncle Ja'afar sai yace" Amma ai Alhaji kamata yayi a tuntu6e shi aji nasa ra'ayin tukun..."
" No need..ai mun gama magana da shi tuntuni sai dai kuma in zaku ha'de min baki ne ku juya min baya kai da shi".
Alhaji Baba ya tare shi da fa'din hakan.

Jin haka yasa Uncle J jan bakin sa yayi shiru...yana tunanin abinda Mu'een ya gaya masa.

Ko iya sanar da Yah Deen ma bai yi ba kawai ya dinga juya batun cikin ransa tare da jinjinawa irin zafin da ya fahimci Alhaji ya 'dauka kan lamarin.

Babu wani 6ata lokaci washegari suka wuce Azare gidan Alhaji Hamza da sunan nemawa Mu'een auren Husnah.

Sun yi sa'a kuwa basu yi tafiyar banza ba dan Alhaji Mamman na gari a lokacin, take yasa akayi musu jagora zuwa asalin gidan da sauran matan sa suke...kafin isowar su ne ya gayyato wani ma'kwabcin sa Alhaji Halliru suka yi jiran isowar su.

Tarba ta musamman akayi musu cikin girmamawa da karamci tamkar dama ansan da zuwan su...bai nuna musu alamun komai ba har suka bayyana masa kansu da kuma abinda ya kawo su...su kam ma tafe suke harda sadakin su a hannu...ga dukkan alamu Alhaji Baba dagaske yake yi bada wasa ba.

Ba'a 'ki kar6an batun su ba take Alhaji Mamman ya amince musamman da yaga yanayin shigar su da kuma motar da suka zo da shi yasan cewa ba 'kananun mutane bane, dan haka take yayi musu albishir 'din ya basu auren Husnah batare da yayi tunanin komai ba...har ma ya basu sati guda kacal da zasu dawo a tsaida ranar 'daurin aure.

Cikin farin ciki suka rabu, su Alhaji Baba nayi musu godiya sosai da yake tare yake da makwabcin sa.

Sai daga baya ne ma ya 'dan yi tunanin abin kamar bai yi dai-dai ba, amma bai tsawaita tunanin ba yaci gaba da harkokin gaban sa.

Washegari da girki ya dawo hannun Mummyn Husnah anan yake yi mata bayanin abinda ya faru da bada auren 'yar ta da yayi batare da yayi shawara da ita ba...  inda Mummyn Husnah ta matu'kar nuna ba'kin cikin ta da 'kin amincewar ta kan batun..hankalin ta ya tashi sosai..tace da shi" Alhaji a gaskiya bai kamata kayi hakan batare da kaji ra'ayin Husnah ba, ko da ni ban kai ayi shawara da ni kan lamarin ba amma ai ita da babu mai tayata zaman auren ya kamata a tuntu6e ta..."
Tayi maganar cikin nuna 6acin ranta.

Ganin Mummyn Husnah ta 'dau zafi ne ya sanya shi fa'din" To Fateemah sai ki gaya min abinda ya dace inyi tunda ni banda hankalin kaina kinji?"
Sai tace
" Ai ba batun haka bane Alhaji, amma ai ya kamata ka duba lamarin kai da kanka, ko binciken kirki fa ba ka yi ba kawai ka 'dauki auren yarinya ka bayar bacin bakasan ko su 'din wasu irin mutane ba ne haka akeyi ne saboda Allah...?"

Shareta kawai yayi yayi kwanciyar sa yayi baccin yayin da Mummyn Husnah kuwa saboda tashin hankali ma kasa rintsawa tayi, zugum ta rafka uban tagumi, daren ranar ka'dai sai da ta tuna mahaifin Husnah yafi sau 'dari, cuz tasan shi din da wuya yayi mata hakan, koda yayi hakan ma to zai bita da kalamai masu da'di da kwantar da zuciya ne.

Gari na wayewa ta 'dauki wayar ta ta 'kira Husnah tace mata ko me takeyi maza ta bari ta zo gida aranar ba sai an kwana ba.

Jin yanayin da  Mummyn ta tayi maganar sai ya sa hankalin ta ya tashi sosai, kuka ta fara tana tambayar ta abinda ya faru, sai tace" Sai dai kin zo kawai..Allah ya tsare hanya".
Tana fa'din haka ta yanke 'kiran tare da zabga uban tagumi, wannan wace iriyar rayuwa ce fisabilillahi?"
Ta fa'di cikin ranta.

Alhaji na bayi tayi wayar lokacin da ya fito ya ganta da tagumi sai ya kauda kansa ya cigaba da abinda yake yi, dan yasan silar hakan.

Batare da ya dube ta ba yace" Wai ke Fateema kina tunanin kin fini son Husnah ne ko me? Ko kuwa ke aganin ki dan bana son ta ne yasa na yanke wannan hukuncin?"

Ko 'kala bata ce dashi ba dan takaici, kawai sai ma ta tashi tayi ficewar ta ta barshi a 'dakin..tana mitar" Wannan wace iryar tambaya ce haka..sai ana shirin cutar da rayuwar ka sannan za'a wani fake maka da soyayyar 'karya, bayaga haka ta yaya ma zai iya ha'da soyayyar da takewa Husnah da wadda yake mata, 'kilan ya manta cewa ita ka'dai ta sha wahalar na'kudar ta ta haifi abinta da taimakon ubangiji, shikuwa ganin ta yayi tar idanun ta a bude batare da yasha wahalar komai ba". sai ya ta6e bakin sa gefe.

Har kuwa ya gama shirin sa ya bar gidan kulashi ba..da yake ma ba kullum yake yin breakfast a gida ba shiyasa shima bai ko nema ba yayi ficewar sa.

Haka Mummyn Husnah ta yini ranar zuciyar ta cike da damuwa da tunani..har Husnah ta iso wajajen 'karfe biyu na ranar Mummyn ta bata warware ta saki ranta ba, gani take an dauko hanyar lalata rayuwar Husnah...ai gwamma ma Hisham 'din tunda shi duk lalaci tushen su 'daya kuma zai ga darajar ta matsayin kanwar shi koda kuwa sadakar ta aka bashi, akan wani can da bata san lungun da ya fito ba balle tasan halayen sa...ta ji bata son tarayyar Husnah da Hisham ne kawai dan taga Husnah na nuna kin amincewar ta ba wai dan ta tsane shi ba, yaro mai hankali da sanin ya kamata sam bai 'dauko ko 'kwara 'daya daga cikin halayen mahaifin sa ba..yaro nagartacce bata ma san me yasa Husnah 'kin amince masa ba.

Hankalin Husnah  a tashe ta iso gidan burin ta kawai taga ya mahaifiyar ta take ta kuma ji abinda ya same ta, sai data yi ido hu'du da ita kafin taji hankalin ta ya 'dan kwanta ganin garau cikin 'koshin lafiya tsaye bisa 'kafafun ta.

Amma duk da haka sai da ta saki kuka ta tafi da gudu ta rungume ta kamar wacce cewa tayi zata tafi ta barta.

Da 'kyar ta lallashe ta tayi shiru har ta je ta watsa ruwa taci abinci ta huta...zuciyar ta cike fal da tunanin dalilin da yasa mahaifiyar tan tayi kiran ta.

*****
'Bangaren Yah Deen kuwa har lokacin bai gama yanke hukuncin da yaka ta ya yanke kan rayuwar sun ba, ya dai sanar da ita cewa 'kanin mahaifin sa ne ta gansu tare sannan yana shakkan ranar da akace ya sake dawowa dan kawo masa ziyara musamman ta bazata irin wannan.

Ita kanta Husnah sai taji ta damu sosai har ta fara tunanin komawa cikin Hostel cuz da wani tozarci da abin kunyan ya faru gareka gwamma tun farko ka 'kuntatawa zuciyar ka kayi abinda ya dace kawai koda kuwa hakan zai saka ka cikin damuwa ne to yafi maka indai tsakanin ka da zuciya da gangan jikin ka ne.

Sannan tasan da kunya a ganta ace ta bi saurayi ta tare gidan sa dan tsananin son da take yi masa..shiyasa tuntuni ta fara tunanin mafita da zauna ta kwashi kunya abanza bacin bata ga ribar rayuwar da suke yi shi ba cuz har yau bai ta6a furta mata kalmar so ba, hira da itama sai lokacin da yayi ra'ayi yake mata, haka zasu kwana tare su tashi amma babu wata kalma mai da'di da take samu daga gare shi sai ranar da yayi niyyar sake mata fuska, in kinji ya kwantar da murya to yazo mata da bu'katar sa ne ita kanta tasani...amma duk da haka 'digo daga cikin son da take yi masa bai agu ba.

Tana nan ne dai tana tare da shi da tsammanin wataran zatayi nasara ya so har ya aure ta.

Koda ta ta sanar da shi zata je gida mahaifiyar ta ta'ki ra ta ma bai wani damu ba da yake dama tun tafiyar Uncle J maganar kirki bata shiga tsakanin su ba..kowa nada tashi damuwar 'kunshe cikin ransa.

Duk da yaga hankalin ta a tashe amma bai wani damu ba sai yayi tunanin ko family issues ne da yake cewa tayi zata je gida mahaifiyar tayi 'kiran ta, dan haka bai nemi jin dalilin tafiyar tata ba illah 5k da ya 'dauko ya bata da sunan ku'din mota...bai san cewa an bashi auren ta ba sam nasan da ko sisin sa ba zai bata ba.


*****
  Sai bayan kwana biyu da dawowar su Alhaji daga Azare sannan Uncle J ya sanar da shi cewa sunje sun tambaya masa aure a Azare kuma an bashi...bai fa'di gidan da suka je 'din ba haka ma sunan yarinyar duk bai fa'da masa ba..duk da lokacin da suka je yaji Alhaji Baba ya fa'di sunan ta Asma'u wanda shima yaji ne abakin Yusha'u da ya tura yi masa bincike da sunan mahaifinta da yake ba 6oyayyen mutun bane, kuma ita ka'dai ya mallaka kafin ya bar duniya shiyasa ma Yusha'u bai sha wahalar binciken ba.

Hakan ma da Uncle J ya samu ya sanar dashi da 'kyar ya ro'ki Alhaji ya amince akan asanar masan, dan da farko cewa yayi ba za'a gaya ma kowa ba ciki kuwa harda Ammin sa, wai har sai bayan an tsaida ranar 'daurin auren kafin a sanar musu.

Ranar kam in akwai sahun tashin hankali na 'karshe to shi Mu'een ya shiga, musamman ma da yaji wai a Azare aka tambayo auren, bai nemi 'karin bayani ba cuz ya san ba Rahma bace, dan ita tuni tayi auren ta harda 'yar ta, shi kenan ta tabbata shine mijin Husnah.

Bazan iya misalta muku yanayin yanda ya shiga ba kudai ku misalta da kanku ku gwada girman 6acin ransa akan aure tsakanin sa da Husnah, nasan ku kanku kunsan abin sam bazai yi masa da'di ba.

Tun daga ranar da yayi jifa da wayar sa bayan jin bayanin Uncle J bai sake bi ta kan wayar ba...bai ko sake tunanin 'kiran kowa ba dan yasan duk babu wanda zai iya dakatar da auren tunda har takaiga anje anyi tambaya...to wama zai 'kira?
Dam Alhaji ne ko Ammi kuma suma 'din a yanzu rashin jin su yafiye masa.

Allah sarki Ammi kuwa Allah ne ka'dai ya san halin da shiga da ta daina samun wayar sa domin sam bata san abinda yake faruwa ba har tausayi take bani, kwata-kwata na rasa wani irin so take yiwa wannan gagaren 'dan nata.

*To ina labarin Husnah?*
       mahaifiyar ta bata sanar da ita komai ba har sai da ta tabbatar da natsuwar ta that's washegarin zuwan ta, shima 'din sai bayan da suka idar da sallar Zuhr kafin ta sanar da ita cewa wan mahaifinta ya bada auren ta ga wasu mutane da suka zo daga Shuwarin...sai ta kasa tantancewa, shin Mu'een ne ko kuwa wani daban, dan ita sam bai ta6a nuna mata alamun a shirye yake da auren ta ba...ya akayi haka kuma?...duk da haka sai take jin 6oyayyen farin ciki cikin zuciyar ta gefe guda kuwa fargabar kar yakasance ba shi bane.

Taso ta same shi awaya ko zata damu jin asalin labarin daga bakin sa, amma layin baya tafiya ta gaza samun sa, duk yadda taso su gana abin ya faskara.

Haka ta yini neman layin sa amma bata samun sa hankalin ta duk sai ya tashi cuz tasan ba'a fiye rasa shi a waya ba, his phone is always on baya ta6a kashe wayar sa" To yau din meke faruwa kuma?
Ta tambayi kanta while tana sake dialling numbern but still is switch off.

Damuwar Husnah bai wani yi tsayi kan batun auren ba fiye da rashin samun sa da bata yi ba, dan hankalin ta gida biyu ya kasu, idan Mu'een aka bawa auren ta tasan zata dawwama ne cikin farin ciki musamman ma saboda irin dumbin soyayyar da take yi masa shiyasa ma ba ta damun ba, gefe guda kuma tana tunanin inba shi 'din aka bawa auren kuma fa?"
Wannan duk bai dame ta sosai ba kamar yadda ta bawa neman layin sa muhimmanci cuz tasan da ta same shi zata ji komai in yaso daga baya sai ta san me ya dace tayi kan batun.

Duk abinda take yi  mahaifiyar ta na lura da ita musamman da taga bata wani damu sosai da jin labarin ba sai tayi matu'kar mamaki, bata san haka Husnah zata 'dauki abin da sanyi ba, she thought zata 'daga hankalin ta ne idan taji labarin amma ga mamakin ta sai taga akasin haka.

Ido ta zuba mata domin ganin iya gudun ruwan ta, daga ranar da ta gaya mata har zuwa daren washe gari..amma Husnah bata nuna mata komai ba sai dai ta lura tafi bawa wayar ta muhimmanci a cikin lokutan.

Zaune suke tare a parlour bayan Sallar maghrib, amma idanun Husnah na kan wayar ta tana dubawa, daga jiya zuwa yau 'din ta tura masa text kusan thirteen times, amma ga dukkan alamu ko guda 'daya bai gani ba, ko yanzun ma text 'din take rubutawa karo na goma sha hu'du inda bayan ta kira dukkan layukan sa basu shiga ba kamar yadda ta saba ji shine ta shiga rubuta" Please Mu'een ka 'kira ne idan ka kunna wayar ka, hankali na ya tashi sosai, gashi ina cikin damuwa we need to talk".
Ji take kamar ta fasa ihu dan ba'kin cikin da take ji tana dannan "send"
sai taji muryar Mummyn tana cewa da ita" Husnah ko dai dama wannan batun auren naki shine abinda kike tambaya ta kwanaki akan wai ko naji wani abu kuma kika 6oye baki bayyana min ba?"

" a a Mummy"
Ta bata amsa cikin sauri tare girgiza kan ta side by side.
Mummyn Husnah kam sam bata yadda ba dan yanayin Husnah ya nuna mata akwai wani abinda take 6oyewa, dan haka cike da 6acin rai ta cigaba da fa'din" Ashe Husnah dan bani da matsayi a wurin ki shine har zaki iya bawa namiji damar turowa gidan ku batare da kinyi shawara da ni ba?"

" Ba haka bane wallahi mummy, nima fa bansan da maganar ba Allah..wanda na sani a can Shuwarin 'din kuma na ta 'kira layin sa bai tafiya bansani ba ko shine ya turo ko ba shi bane...Mummy in har auren zanyi ai kisan kece mutum ta farko da zata fara sani tun ma kafin aje ga Abbah".
Jin haka yasa Mummyn ta 'dan sakko sai tace
" A ina dama kika sanshi?"

" Makarantar mu ne 'daya da shi".

" Amma bai ta6a sanar dake cewa zai turo gun mahaifin ki ba?"

"A a wallahi Mummy ni bai ta6a sanar da ni ba ko da wasa ma".

" Ikon Allah!"
Mummyn ta fa'di cike da mamaki sannan ta cigaba da fa'din..." To ki ta gwada layin nasa duk sanda kika same shi kukayi magana, zan miki wata tambaya".

" To Mummy".
Tace cikin sanyin murya tana mai sake maida fuskar ta kan wayar ta dake ri'ke a hannun ta.




*Hmmm....Allah Ubangiji ka raba mu da sharrin social media* 🙏



_Comment_
_Vote_
_Share_




*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)


By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *48*

Ita kanta ta matsu ta jishi su gana, musamman ma da ta tuno jiya da dare bayan dawowar Abbah da ta gaida shi yanda ya kar6i gaisuwar ta cikin nuna halin ko'in kula, yana gyara zaman sa zuwa kishingi'da yace da ita" Wato mahaifiyar ki ce ta gayyato ki musamman domin ki zo ki gaya min cewa baki amince da za6in da nayi miki ba ko?"
Da sauri ta 'daga kai

Please Login or Register in order to submit comment