Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zanso inji ni dai...... babu mamaki kece kike ganin sa matsayin abin haushi da takaicin, 'kila ni bazan ga hakan ba".

Murmushi tayi mai ciwo a zuci..but sosai ya 'kawata mata fuskar ta duk da kuwa kallo 'daya zakayi mata kasan cewa na 'karfin hali ne...a hankali cikin sanyin murya ta sau'ke ajiyan zuciya tare da fa'din.
" hmm...karki damu Hafsat zakiji labarina insha Allahu.....
'Dan yamutsa fuska ta sakeyi sannan ta cigaba da fa'din " amma inajin cikina na min zafi yanzun ban san....."

Tun ma kafin ta kai 'karshen maganar Hafsat tayi saurin mi'kewa taje ga flask 'din da Nurse ta shigo dashi 'dazu ta ha'da mata tea mai kyau ta kawo mata.

Duk abinda takeyi Noor bata ko bi ta kanta ba illah tsurawa inda Jas ke kwance kawai da tayi idanu, tana matu'kar tausayin Baby sosai..a inda take 'din sai ya kasance tana fuskantar fuskar Jasmine 'din ne, gani tayi yarinyar tayi fayau sosai, hasken ta ya 'karu fiye dana asali.


Kuka take jinyi a duk lokacin da ta kalli Jasmine ta tuno mummunan 'kaddarar da ya hau kanta, sosai abin yake ta6a mata zuciya.....amma sai take daurewa take bawa kanta 'karfin gwiwa da ya'kinin Allah zai yi mata jagora wajen kulawa da ragowar rayuwar Jas 'din har 'karshen rayuwar su.


Dawowa Hafsat tayi inda take zaune gami da dafa 'kafa'dun ta...Noor sai ta rintse idanu a hankali, 'dan guntun hawayen da ya cika cikin idanun ta suka gangaro sai tayi saurin share su.


'Dagowa tayi ta kalli Hafsat 'din yayin da ta 'dago Cup 'din tea 'din ta mi'ka mata ba tare da ta furta komai ba illah yanayin fuskar ta da juya zuwa yanayi na tsantsan tausayi.


Kar6a Noor tayi ba tare da 6ata lokaci ba ta kur6a, tana jin yanda 'dumin Tea 'din ke ratsa mata ciki kasancewar babu komai acikin nata tun safe...cigaba tayi da kur6an tea 'din yayin da zafin da cikin keyi yake 'kara yawaita mata, duk da haka kuwa bata fasa sha ba dan tasan ba komai ya jawo hakan ba face tsantsan yunwa.... ka'dan-ka'dan take sha har ta shanye rabin sa sannan ta ajiye cup 'din a gefen ta.


Babu wanda ya sake magana acikin su, shiru wurin ya 'dauka kusan na tsawon mintina goma, kowa da abinda yake sa'kawa cikin ransa, wanda cikin 'yan mintinan Noor ta danne zafin da take jin cikin nata na mata duk da kuwa yaso yafi 'karfin dauriyar tata amma sam bata nuna haian ba, kafin cikan mintina goman kuwa har ya 'dan sarara.


Ganin yanda Hafsat ta tsura mata idanu take kallon tane ya sanya ta tunowa da abinda Hafsat ke zaman jira daga gareta...wato labarin rayuwar ta.


Noor sama ta 'daga kanta gami da rintse idanun ta a hankali wasu siraran hawaye masu sanyi suka sake sau'ko mata.

Bata sharesu ba wannan karon sai ta barsu suka cigaba da sau'ka a hankali.


Hafsat kuwa ita kawai ta zubawa idanu take kallo gami da sauraron jin labarin Hudah daga bakin ta....amma ganin kukan da take yi sai itama taji wani iri jiki da zuciyar ta, gani take yi kamar Noor bata son tunowa da rayuwar ta na baya ne, sai take ganin tamkar takura mata tayi akan hakan.

Ajiyan numfashi Noor ta sau'ke sannan ta sau'kar da kanta gami da goge hawayen da ya gangaro mata....wanda tana cikin hakan ta tsinkayi muryar Hafsat na fa'din " idan da takura Huda ki bari sai wani lokacin babu damuwa ai muna tare....".


Murmushin gefen baki na 'karfin hali Noor tayi mata batare da ta bata amsar wancen tambayar ba taci gaba da fa'din.........




*****
Asalin suna na Nurul Hudah, iyayenmu mu biyar suka haifa, Yah Usman shine babba sai Addah Maryam, sauda, Amina (Nanne) sai ni autar mu da mahaifina ya sanya min suna *Nurul Hudah* .


Na taso cikin gatan Ummah na da Babana dan su ka'dai na bu'di idanu na ganni tare da su, cuz tun kafin nayi wayo aka aurar da yayuna mata biyu, Yah Usman kuwa ba zama yake yi sosai damu ba, shi ya kan ziyarce mu ne lokaci zuwa lokaci saboda yanayin sana'ar sa, daga ni sai yayata Amina da nake bi mata, haka muka taso gaban iyayen mu cikin so da 'kaunar juna.


Mahaifina asalin manomi ne tun a wancen zamanin, bashi da wata sana'ar da ta wuce noma, kuma Alhamdulillah ba laifi dan a hakan muke lalla6a rayuwar mu cikin rufin asirin Allah, bamu fiye neman abu mun rasa ba.


Da yawan mutane kan 'kira shi da Malam Mamman Jaji...mun kasance asalin fulani ne na garin bauchi, mahaifiyata 'yar asalin 'karamar hukumar Darazo ne yayin da mahaifina ya kasance haifaffen garin Shuwarin.....rabon aure ne kawai ya ha'da mahaifana lokacin da wata tafiya ta kai shi garin Darazo har Allah ya 'kaddara auren su.


Sana'ar Ummah ta shine kunu da suyan waina kullum safiya a 'kofar gidan mu....wanda ya kasance nice ke taimaka mata koda wani lokaci idan mun gama komai sannan sai inje inyi shirin makaranta ta shiyasa mafi yawan lokuta na kasance cikin lattin zuwa makaranta kusan mafi yawa daga cikin 'dalibai na riga ni isa makarantar.


Sam Ummah bata saka Amina Nanne cikin sabgar sana'ar ta harda ma ayyukan gida gaba 'daya, kasancewar bata da isashshen lafiya kamar ni.

Shiyasa Ummah bata fiya matsa mata akan komai ba sai dai ni duk da kuwa baya nake da ita.

Duk wani abinda ya kamata ace Nanne ce ke yi matsayin ta na wacce take sama dani to ni ke yinsa.

Hatta da wankin kayan mu Ummah da kanta ke mana da kanta, wani lokaci kuma ina taya ta da 'dauraya har mu kammala....tun tasowata ban tashi da 'kiyuya ko son jiki ba.


Na kan birge Baban mu a duk lokacin lokacin da yaga na bada himma ina ayyukan gida tun kafin shekaruna su suyi 'kwari...wanda har hakan ke sanya shi yawaita sa min albarka cikin matu'kar jinda'di.


Wainar Ummah ta yayi farin jini ba laifi domin da yawan mutane kanzo wurin ta dan ha'da abin karin su yayin da wasu ke ci a wurin batare da sun yi dakon sa zuwa wani wurin ba.
Akwai wa'danda har booking suke yi tun kafin ayi.....yayin da wasu ke zuwa su jjira har layi ya iso kansu.

Gurbin wainar Ummah ta baya ta6a rabo da masu siya har sai in ta kammala gaba 'daya.


Alhaji Baba ya kasance 'daya daga cikin masu siyan wainara Ummah ta, kuma babban abokin Baban mu ne, mafi yawan lokuta tare zaka gansu indai har babu wani uzuri dake gaban 'dayan su.

Ya kan siyi wainar Ummah ta da da 'dan yawa dan kullum yakan sawa ayi masa sadaka dashi sannan akai masa wani gida.
Tun ban da wayo nike zuwa gidan Alhaji Baba har na fara wayo kaina, domin kusan kullun sai ya siya an kuma kai masa gar gida.


Mutum ne shi mai matu'kar kamala da sakin fuska gami halin girma, ga faram-faram da jama'ah bashi da mugun hali sam.


Shi na fara sabawa da shi kafin kowa cikin gidan sa, domin duk ranar da muka ha'du na kan zauna da shi muyi ta hira abin mu shima baya gajiya da biyewa yarinta ta.

Abu 'daya dake kulle min kai game da shi shine yanayin rayuwar su...sam ba kamar yanda mu muke rayuwa bane, sosai tsarin rayuwar mu ta bambanta da su.

Yanayin sa shi kansa da yaran sa, yanayin gidan sa, tun daga harabar gidan, ciki da kuma abubuwan more rayuwa dake cikin gidan sosai suke bani mamaki, domin ni in ba agidan nasa ba ban ta6a ganin dayawa daga cikin su ba.


Komai na gidan Alhaji Baba na musamman ne...idan kana cikin gidan sa har manta cikin garin da kake zakayi in ba ka fito ba, domin zakayi tsammani cewa cikin babban gari kake.

Yanayin yanda yake dressing 'din sa ma daban ne ba irin na su Baban mu ba, domin shi Alhaji Baba kusan kullum zakaga kayan jikin sa sababbi ne masu kuma matu'kar birgewa.


Na rasa dalilin da ya sanya su 'din komin daban domin hatta da wankin kayan su da engine suke yin sa, kasa ha'kuri nayi da hakan har naje na tambayi Ummah ta.

Abakin naji naji ta'kaitaccen tarihin Alhaji Baba kamar haka.........







*~One Luv masoya na~* πŸ₯°β€πŸ˜ *......yau dai ga NOORUL ta dawo fatan ha'kurin naku bai kammala* *'karewa ba* πŸ˜‰


*Daga yau insha Allahu zaku cigaba da samun update akai-akai koda read more 'daya ne ma* πŸ₯΄ *....agafarce ni pls.*
*Kuyi manage da wannan kafin ku sake jina.* πŸ‘ŒπŸ»

😎😎😎
Deen 'dina na gaisuwa fa πŸ™‹πŸ€ 









*Salmerh ce* 😍
[12/17/2019, 10:50 AM] 🌸Salmerh🌸: πŸ’• *NOORUL* πŸ’•
(Haske nah)



By
*Salmerh MD*



*Wattpad @*
*Serlmerh-md*



πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
πŸ’«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*



*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*



πŸ…Ώ *16*


Kafin Ummah ta fara magana sai ga Nanne ma ta zo inda muke zaunen ni da Ummah, zama tayi a gefena tayi shiru itama kamar yadda taga nayin muka cigaba da sauraran Ummah a tare....domin zuwan Nanne bai sa Ummah ta taka birki daga fa'dar labarin da tayi niyyan bani ba........


*****
Alhaji Taheer Manga.....haifaffen cikin garin Azare ne na jihar Bauchi....wanda yanayin aiki ya kawo mahaifin sa mai suna Mukhtar garin mu inda anan yayi katari da samun matar aure Fatima wacee itama ta kasance matashiyar malama ce a makarantar da yake aiki bata ko yi rabin shekara da fara aikin ba......batare a wani 6ata lokaci ba suka dai-dai ta kansu, iyaye suka shiga maganar akayi bikin Mukhtar da Fatima cikin farin ciki da 'kaunar juna.

Sunyi zama na tsawon shekaru wanda har ya kasance sun zama tamkar 'yan asalin garin ne, shima bai hanata fita aikin ta ba suka cigaba da fita abinsu atare har Allah ya azurta su da samun 'Ya'ya.

....Mahaifin Alhaji Baba bai ta6a samun matsala da kowa agarin ba, har yazo yayi dacen samun matsayin Headmaster na makarantar......ga shi kuma yana da kyakkyawar ala'ka da manyan cikin garin sosai suke girmama junan su.

Wanda har wa'adin Allah ya kasance akansa bai sake samun wata haihuwar ba duk kuwa da yana son samun 'ya mace amma Allah bai nufe sa da samu ba..... ya rasu ya bar yaran sa maza guda biyu wato Taheer (Alhaji Baba) sai mai bi masa Ja'afar da yanzu haka yake zaune can garin Kaduna da iyalan sa.

Lokacin da ua rasun shekarun Taheer goma shabiyu yayin da Ja'afar yake da shekara tara fa haihuwa.


Tun bayan rasuwar sa Fatima taci gaba da kulawa da yaran da karatun su da tarbiyyar su bisa jagorancin mahallici.

Bata sake tunanin sake yin wani auren ba duk da kuwa alokacin tana da 'yan 'karancin shekaru wanda hakan yasa mutane da da dama ne suka bu'kaci auren ta amma sam bata bawa kowa dama ba dole tasa kowa ya janye nasa 'kudurin

Haka har yaran ta suka girma suka zama mutane, bata kuma koma can garin iyayen ta ba saboda tana ganin tamkar yaran nata da nan suka bu'di idanu so bata so ta canja musu salon rayuwa, kuma ko dan saboda nata aikin da take yi shiyasa ma kawai suka cigaba da zaman su nan.

Suma yaran nata ba laifi suna 'ko'karin yin 'kananun sana'o'i basu zama haka nan....cikin rayuwar su babu abinda ya canza face kewar mahaifin su, karatun su ma sun cigaba da yi atare domin tsakanin su babu wani rata sosai shekaru uku ne zuwa hu'du kawai hakan yasa karatun su yake tafiya lokaci guda.

Suna kammala secondary ta basu zauna ba suka zarce da karatu Taheer BUK yatafi yayin da Ja'afar yayi karatun sa a nan cikin garin Bauchi inda ya karanci Accounting, basu samu matsala da komai ba har suka kammala kasancewarsu yara masu bada himma haza'ka da kuma 'ko'karin karatu.


Cikin sa'a kuwa suna kammala makarantar kowanen su yayi dace da samun aiki dai-dai da abinda ya karanta....inda Ja'afar yayi dacen samun aiki a banki cikin garin Bauchi, yayin da Taheer kuma ya samua gidan mai a Kano a matsayin 'kananun ma'aikata.


Duk da hakan sam ba raina ko kuma yin girma kai ba, hannu bibbiyu ya rungumi aiki gami da godewa mahallicin sa.

Samun aikin nasu ya matu'kar yi musu da'di domin kuwa suna gani cewa lokaci yayi da ya kamata mahaifiyar su ta huta.....ai kuwa gata sosai take samu daga dukkan 6angarorin biyu sai godiyan Allah ita kanta sai da tasan cewa ehh lallai haihuwa na da rana.
Sai dai kawai tayi ta binsu da addu'ar samun sa'a da kuma dacewa.

Taheer ne yaso ya 'dauke ta ma kwata-kwata daga wannan garin amma ta nuna masa ba komai ya barta a nan 'din kawai, kuma ma me yasa zata bishi bacin ba iyali ne dashi ba sai ta 'karasa da fa'din ka bari idan ka ajiye iyali sai ij bika ko kuwa?"

Shiru kawai yayi mata dan sam shi ba haka yaso ba amma dolen sa ya ha' kura tunda ta nuna bata ra'ayi ai shikenan.



Ba su shekara da fara aikin ba Zmz sai Allah ya kar6i ran mahaifiyar ta su bayan jinya (Allahu Akbar) mutum mai rai kenan.....sunci kuka sunyi takaici domin sunso mahaifiyar su ta fara cin moriyar su kafin kafin kowa yaci, amma hakan bai yiyuba Allah ya nuna ikonsa dole suka ha'kura suka yi tawakkali, domin *hukuncin Allah* ba a ja da shi...mutuwa kuma dolen kowa ce..


Bayan sun gama kar6ar gaisuwa sai duk suka koma bakin aikin su zuciyoyin su cike da alhaini.

Cikin sa'a kuwa Taheer bai wani jima da fara aikin ba ya samu 'karin girma...sun yi matu'kar farin ciki sosai, bayan hakan ne Ja'afar ya shawarce shi da cewa gara ya ajiye iyali saboda halin rayuwa kuma ma ko don cika sunnar ma'aiki (SAW).....Ya 'karashe da fa'din " kaga ni tuntuni fa kai nake jira in ba dan haka ba da tuni anyi nawa".


Washe baki Taheer yayi yana kallon sa yace" haba malam.... kace kenan dama hanya kake so in baka"!

"Ashe ka gane manufata".
Cewar Ja'afar yana dariyar shima.
Sai Taheer yace masa " kar ka damu to....ba sai ka jirani ba.....inaga ai za'a iya ha'dawa duka rana 'daya ko?"

" Gud idea...."! Ja'afar ya furta yana murmushi sannan ya 'karasa da fa'din " gaskiya shawarar ka tayi 'dan uwa, aini da banyi tunanin hakan ba sam".

" Hmm " kawai Taheer yace dan shi sam ba mai son yawan hayaniya bane, ta inda bambancin su yake kenan da 'kanin nasa.


Taheer bai yi 'kasa a gwiwa ba yaje ya tuntu6i wacce suke 'dan soyayya da ita..har yake tunanin inda hali ita zai aura.....wata matashiyar yarinya ce 'yar 'kabilar Igbo da bazata gaza 23yrs ba, mazauna garin Kano ne su....ama Kano aka haife su....duba da karamci da mutunci gami da ha'ku'ri irin na mabiya addinin muslunci da kuma mazauna garin Kanon ya sanya mahaifin su kar6an muslunci tun kafin yaran sa suyi wayo...anan matar sa ta nuna 'kin amincewar ta da wannan batun inda batare da 6ata wani lokaci ba ta tattara ta koma mahaifar ta wato Imo State.

Shi kuwa ya hanata tafiya da kowa cikin sa, dolen ta ta tafi ta tafi ta barshi da yaran nata guda uku, biyu maza da mace 'daya wacce mahaifin ta ya za6a mata suna Aishatu yayin da 'kannan ta maza biyun suka ci suna Aliyu da Umar, shikuma uban ya za6i sunan fiyayyen halitta annabi Muhammad (SAW) yace wannan ne yayi masa.


Haka suka cigaba da rayuwar su cikin haske da alfarmar addinin muslunci har yaran sa suka yi wayo, babu wanda ya 'kara ziyar tan su daga 6angaren dangin uwa har ma da na mahaifin nasu, hatta ita kanta mahaifiyar tasu ma bata sake waiwayan su ba haka shima mahaifin su bai yi gigin taka 'kafar sa zuwa can garin nasu ba domin yasan bazata 'kare musu da da'di ba.


Tunda ya kar6i addinin muslunci ya ri'ke sa da hannu bibbiyu domin koda wasa baya sakaci da islamiyar yaran sa sosai yake bada muhimmanci ga wannan 6angaren shi kansa ma neman ilimin yake bai zauna haka nan ba......shiyasa yaran nasa suka taso cikin tarbiya dai-dai gwargwado, amma bai yadda ya sake yin aure duk kuwa da malamai na nuna masa muhimmancin hakan amma sam ba bada himma ga hakan ba har girma ya kama shi.


Aishatu tayi matu'kar farin ciki da jin cewa Taheer na so iyaye su shiga maganar su... dan kuwa ba 'karamin so take yi masa dama, shi 'din ne dai yake 'dan taka mata birki da irin salon sa na shariya da basarwa.


Bata wani 6ata lokaci ba taje ta samu mahaifin ta da maganar take kuwa ya basu dama domin shima baya da burin da ya wuce yaga ya aurar da ita a lokacin.......cikin 'kan'kanin lokaci aka tsaida maganar auren su harda na Ja'afar ma.
Bayan wata uku akayi bikin su kowa ya tare da matar sa.
Tun daga nan kowa ya dasa gidan sa cikin so da kulawa da iyalin sa...kuma ba laifi suna zumuncin su dai-dai gwargwado duk da ma ba gari 'daya suke ba amma suna 'ko'karin kulawa da zumuncin dake tsakanin su.


Taheer Kano yake da zama yayin da Ja'afar yake zama Azare da matar sa dan shi anan ya samu aikin nasa tun farko.


Shekara na zagayowa Aishatu ta haifi 'dan ta namiji kyakkyawa da shi, yaro mai kyau da haiba sak Baban sa sai dai farin sa gaba 'daya na uwar sa ya kwaso har ma ya 'dan so ya zartata.


Murna gurin wannan familyn ba'a cewa komai sai wanda ya gani...domin kuwa babu wanda bai yi farin cikin da samun wannan 'karuwar ba.


Tun washe garin haihuwar Zainab matar Ja'afar ta zo shima 'din ba a barshi abaya ba domin kuwa ana gobe suna shima ya dira garin Kano dan asha shagalin suna dashi.


Ranar suna yaro yaci sunan kakan sa wato mahaifin Aishatu.... *Muhammad Taheer*, matar 'kanin baban sa Ja'afar ne ta fara ambatan sa da suna *Mu'inuddeen* ( the helper of d religion).......tace da sunan zaa 'kira shi....sosai akayi shagalin suna cikin bawa Naira kashi...kowa ya nuna bajintar sa sosai abin ba'a cewa komai.

Shi kansa mahaifin Aishatu da yaro yaci sunan sa ma ba'a barshi a baya ba wajen bada nasa manyan gudummuwan domin shima wani irin so yaji yake wa yaron na ban mamaki hakama Umar da Aliyu da suke ji tamkar su dawo zama tare da babyn.


Yaro ya taso cikin so da 'kaunar duka dangin sa musamman ma Baban sa Ja'afar da har yanzu Allah bai ba shi haihuwa ba, matar sa ko 6atan wata bata ta6a yi ba, amma bai wani 'daga hankalin sa da hakan ba domin ya san Allah shike bada haihuwa a duk lokacin da yaso haka kuma saiga wanda yaso.


Matar san ce dai take 'dan damun sa wasu lokutan amma ba laifi ya kan kwantar mata da hankali da nuna mata cewar hakan ya faru ne saboda buwayar mahallici kuma bawai dan bai san su ba a a sai dan kawai ya jarrabe su, ya kance da ita kuma ma dududu shekar su nawa da yin auren da har zata damu kanta ai komai yana da lokaci kuma hanzari ko rashin ha'kurin mu baya ta6a sawa mu samu abu face Allah ya so, mu ci gaba da addu'ah insha Allahu watarana ke ma zaki haihu".
Idan ya fa'di mata hakan kuma Alhamdulillah tana fahimtar sa.



*****
Allah cikin ikon sa haihuwar *Mu'inuddeen* sai ya zowa mahaifin sa da *wani haske*...domin sai ya ringa samun 'karin girma a hankali wurin aiki ga kuma hanyoyi da suka 'kara bu'de masa na ban mamaki, inda cikin natsuwa tattalin arzi'kin sa ya ringa bun'kasa yana 'kara girma.


Kafin shekaru uku kuwa har ya zama wani abu da shi kansa ya san cewa ya shiga sahun wasu daban masu fa'da aji ko wani bai fa'da shi 'din ya san hakan.


Manyan store ya bu'de kusan guda uku ya zuba kaya inda ya wakilta masu kula masa da shi cikin ri'kon amana da gaskiya.


Bashi da matsalar komai a yanzun illah ya kula da tarbiyar iyalan sa da hakkokin su.


A gidan Alhaji Muhammad Ugoh Chukwu (mahaifin matar sa) ya bar Mu'een lokacin da zasu tafi aikin hajji da matar sa...wanda hakan ya 'kara sanya 'ka'k'karfar so da sha'kuwa tsakanin Mu'een da kawunan nasa.


Kafin su dawo kuwa Alhaji Muhammad U.C ya bada kyautar wani babban plot 'din sa dake can Zaria road har ma ya musanya sunan an 'daura na Mu'een.


Koda suka dawo kuwa sunyi matu'kar farin ciki da jin hakan baran ma Aishatu da take 'kara jin da'din yanda mahaifin ta ke so da kula da jinin ta.


Taheer ne dai ya 'dan so yayi 'korafi amma Alhajin ya dakatar da shi da fa'din " Kyautar sa ga mai sunan sa ne shi bai ce ya sa baki ba".
Yayi maganar ne cikin karkatacciyar hausar sa da har yau bata 'dauki hanya ba da kuma murmushi kan fuskar sa.


Taheer baya so yaja da maganar Alhajin amma sai yake ganin kamar ai kyautar tayi yawa sosai Mu'een 'din ma nawa yake da har zaa yi masa irin wannan kyautar amma dole haka ya ha'kura da maganar ganin 'korafin sa bai samu shiga ba, domin Alhajin ba sauraran sa zai yi ba ga dukkan alamu.


Shi haka tsarin sa baya son ayi masa godiya sam koda yayima kyauta baya son yawan godiya shiyasa wa'danda suka san halin sa idan hakan ya faru kawai sai su bishi da addu'o'i cikin ransu.

Shima 'din yafi gane hakan....dan haka shima Taheer sai ya ja bakin sa yayi shiru gami da jinjinawa karamci irin na mutumin tamkar ba 'kabila ba haka yake rayuwar sa.



*****
Alhaji da Mu'een yaji 'kannan mahaifiyar sa na kiran Baban sa da shi ne ya sanya shima ya 'kara Alhaji kan sunan da yake kiran sa da shi wato daga Baba zuwa Alhaji Baba.


Babu kuwa wanda ya hana sa har hakan ya zauna bakin sa abu kadan sai yace Alhaji Baba...Alhaji Baba.


Kwanci tashi rayuwa babu wuya.... har Mu'een ya shekara biyar da haihuwa, yaro kakkykyawa da shi abin so da birgewa.. yayin da yana 'kara girma kywaun sa na 'kara yawai ta.....sai dai kuma har a lokacin ba'a sanya shi makaranta ba haka rayuwar sa ta kasance yau yana gun iyayen sa gobe yana gidan kakan sa, sosai yake samun *gatan kowa* daga cikin su, har da ma Uncle 'din sa dake Azare shima ba'a barshi abaya ba.


Wani zuwa da Ja'afar yayi ne ya kai musu ziyara sai ya dinga masifar me yasa ba'a sanya shi makaranta ba, yanda yake yi 'din idan kun ganshi har zaku zaci cewa ko shine babba, sosai ya nuna musu rashin dacewar hakan, su kansu ma sunsan ba dai-dai suka yi ba kuma bama su da dalilin 'kin sashi a makarantar amma kawai hakan bai zo kansu bane shiyasa, zuwan Ja'afar 'din ne sai ya fargar dasu, musamman da yace idan ba su so shi zai 'dauke sa ya tafi dashi.

Kowa bai so yayi missing yaron dan haka cikin satin suka 'dauri aniyar kaishi makaranta.


Ashe ma basu sani ba Kakan sa ya gama masa komai, shima daya gaji da jiran ganin sun sanya shi yaga shiru shine kawai ya nema masa makarantar da ta dace da kansa batare da ya shawarci kowa daga cikin su ba.


Monday da suke tunanin zasu fara yi masa cuku-cukun makarantar, aranar da sassafe Alhaji ya aiko driver aka 'dauke shi
sai dawo musu yayi da uniform a jikin sa yazama d'an makaranta.


Tun daga ranar Mu'een yaci gaba da zuwa makarantar, wata tsadaddiya da kakan sa ya sanya shi.


Sosai suka ji da'din hakan a lokacin.....Aishatu ce da kanta ta 'kira mahaifin nata tayi masa godiya amma bai ma tankata ba kawai ya kashe wayar.


Bayan ya gama da layin Mu' een sai hankalin sa ya dawo kan processing wa yaran sa tasu makarantar domin suk sun gama secondary school yana so su cigaba.


A Canada ya samar musu dukkan su Umar da Aliyu.. inda suka tafi cikin matu'kar farin ciki suka bar mahaifin nasu da kewa sosai domin gida yayi shiru babu kowa, shima 'din kawai sai ya wuce South Africa inda ya tafi domin gudanar da harkokin *Kasuwancin

Please Login or Register in order to submit comment