Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sai mun dawo...Husnah feel free ki yi abinda ya kawo ki kinji?".

" Ok Nagode Ishaq".
Ta fa'di a hankali da sanyin murya.

Ba haka ta so ba sam, ta so ne ace da ya rako tan ya tsaya idan ta 'dauki abinda zata 'dauka sai su koma tare saboda sam bata 'kaunar ta ke6ance da Mu'een koda wasa.


Bai ko kalli inda take ba har yanzun sai ya 'dauke jansa yayi kamar bai san da tsayuwar ta a wurin ba, wanda hakan yasa itama bata kalle shi ba ta nufi hanyar 'dakin ta dake gidan nasa tana fa'din" Barka da gida Mu'een...ya studies?"

Ko 'kala bai ce da ita ba illah 'daga kai da yayi ya kalle ta ka'dan take ya sake maida idanun sa ya cigaba da abinda yake yi.

Duk da bai amsa mata gaisuwar da tayi masa ba amma bata damu ba fatan ma shine ya kasance shirun a wurin  har ta kammala kwasan kayan ta ta koma inda ta fito.

Taso ta 'dauko wata 'kawar ta su taho tare amma sai tayi tunanin yin hakan tamkar ta tona sirrin ta ne na baya wanda take tunanin ba kowa yasan shi, ba kowa yasan cewa gidan sa take zama ba...shiyasa ta nemi Ishaq tunda shi yasan komai, kuma sarai tasan halin sa bashi da tashin hankali ko neman magana.

Ba dan ya zama dole bama da babu abinda zai sake kawota gidan sa balle su ha'du sai dai hakan bai yiyuba saboda waccen tafiyan da tayin cikin rashin shiri tayi sa, duk wasu muhimman abubuwan ta na nan gidan nasa, taso ta bar su ma amma hakan ba zai yiyu ba...dan hatta system 'dinta agidan yake da sauran tarin littatafan karatun ta,  ayanzu kuwa matu'kar bu'kace take da su cuz semester ta ja sosai.


Cikin sa'a kuwa a bu'de ta tarar da 'kofan ba'a saka key ba tana mur'dawa sai ya bu'du, 'kasan zuciyar ta ta saki hamdala dan dama bata 'kaunar zuwa kansa ta tambaye shi wani abin sam.


Tana shiga ta sake maida 'kofar ta rufe sannan ta cire hijab 'din kanta ta ajiye shi, cikin sauri-sauri ta fara ha'da kayayyakin da tasan zasu mata amfani, bata tsaya shirmen komai ba tayi abinda ya kawo ta dan kar ta 'dauki lokaci, daf da zata kammala ha'da kayan wayar ta ta 'dauki 'kara wanda tana dubawa taga sunan Hisham na yawo kan fuskar wayar.

'Dauka tayi tare da sallama ya amsa sannan ta gaishe shi, tambayar ta yayi ko har ta fito daga lectures 'din tace " Erh ta fito har ta dawo gida tana aiki ma".

" Aikin me?"
Ya tambaye ta
Sai tace " A kitchen ne".

Yace" Abinci kenan?"
'Kasan ma'koshi ta amsa da " Umm".
Sai yace" To ayi aiki lafiya 'yan mata anjima zan 'kira ki kinji?"

Da" Toh".
Ta amsa cikin sanyi.

Tana cire wayar daga kunnanta sai suka yi ido hu'du da Yah Deen dake tsaye ri'ke da 'kofa amma bai 'karasa shigowa ba.


Take sai taji wani iri fargaba mai tsanani ya shige ta, sarai tasan halin Mu'een bashi da da'di ta kuma san salon muguntar sa shiyasa take matu'kar tsoron ha'duwa da shi balle har su ke6ance, tun bayan auren ta ta yiwa kanta al'kawarin tsare mutuncin ta.

Ai kuwa suna ha'da idanu da shi sai ya bar bakin 'kofar a hankali ya 'karaso ciki tare da maida 'kofar ya rufe fuskar sa 'dauke da murmushi.

Nesa ka'dan da ita ya tsaya tare da cusa hannun sa 'daya cikin aljihun wandon jeans dake jikin sa yana kallon fuskar ta yace" Me yasa ki kai masa 'karya?"

Bata tanka shi ba kawai ta tafi ga mayafin ta ta 'dauka da niyyar sanyawa amma sai taji ya fisge daga hannun ta ya rataya shi saman shouldern sa sannan cike da gadara ya sake fa'din" Tambayar ki nake yi baki bani amsa ba".

Husnah kam hankalin ta sosai ya fara tashi, dan haka tuni jikin ta yayi sanyi...a hankali ta bashi amsa da fa'din" Waya ta bata da ala'ka da kai Mu'een so please respect ur self".

Murmushi ya saki yana mai sake binta da idanu " Hus...nah".
Ya ja sunan ta tare da 'dan matsawa kusa da ita...da sauri ta matsa baya...tana ha'de gira cike da 6acin rai.

" Husnah kin raina ni...yanzu dan zaki zo inda nake shine sai kin nemo wani ya rako ki? cinye ki zanyi ne ko me?...Husnah gaskiya kin 6ata raina...ni ne fa ba wani ba me yasa 'karara zaki nuna min irin wannan 'kyamar?"

Tace" Darajar aure na nake karewa".
" I see...yanzu ina auren to?..tunanin ki zan iya ha'kura dake ne?"

" Ni dai Please kayi ha'kuri badan hali na ba".
Tayi maganar da muryar kuka...ita harga Allah yanzun tsoro yake bata ma, mutun tamkar ba'a ta6a 'diga masa ruwan imani a zuci ba.

Baya ta sake yi ta koma gefe tana mai tsiyayar da hawayen takaici.

Bai damu ba ya cigaba da binta har takai bango wanda ya sanya dole ta tsaya cak da 'dan 'karfi tace" Wai meke damun ka ne Mu'een da aure fa akaina".

" Nasani ai, amma ai kin lura ba ni ne na biki ba kece kika biyo ni gida na so miye laifi na dan na more ki? Wannan abinda ya saki tahowa har muhalli na shi ka'dai zan cire miki and nothing else".

Kuka ta sanya mai zuciya ji take da ace akwai wani abin kusa da ita da babu abinda zai hana ta maka mai aka ko dan ta samu ta tsira da mutuncin ta...amma yanzu da ya kasance babu komai so itama bata da coice than ta ro'ke shi ya bar ta, tasan duk abinda ya fa'di gaskiyar sa ne, itace ta zo koma me yafaru kuma laifin ta za'a gani ba nasa ba...hannun ta 'daga duka biyu ta ha'de su wuri guda idanun ta cike da hawaye ta fara ro'kon sa akan dan Allah yayi ha'kuri ya bar ta ta tafi tayi masa al'kawarin bazata sake zuwa masa gida ba, ya taimake yaji 'kan igiyar auren dake kanta".

Shiru yayi bai ce da ita 'kala ba idan ka gansa a lokacin zaka yi tunanin ko maganar da tayin ta shiga kansa ne, hakan yasa itama bata sake magana ba kawai ta cigaba da rera kukan ta gwanin tausayi.

Tsawon mintina shida suna a haka har ta daina kukan tayi shiru duk ta sake rai cewa ya ha'kura zai barta ta tafi ganin yanda ya tsaya shiru sai dai me tmkar wani 'kanin fir'auna bu'dan bakin sa sai cewa yayi"..saboda kin samu wani banzan shine ni kike shirin guje min ko Husnah?"

Shiru tayi masa bata bashi amsa ba ganin yanda yayi mata katanga...tsoro duk ya bi ya sake cika mata zuciya.

Zai sake magana tayi saurin taran sa da fa'din
" Dan Allah Mu'een kayi ha'kuri kasan fa yanzu ala'kata da kai haramcin ta yafi muni fiye da baya".

" Me kike nufi kenan Husnah?"
Yayi maganar yana me 'ko'karin ha'da jikin sa da nata.

Surin gocewa tayi tana fa'din" Let me go please Mu'een kai wani irin mutun ne dan Allah?".

Murmushi yayi da jin abinda ta fa'di wai shi wani irin mutun ne..
" Husnah so kike kisan ni 'din wani iri ne?...ni mayen ki ne kawai..kuma da kike so in barki ki tafin ya kike so inyi da tarin 'kaunar ki da ke cike a zuciya ta Husnah?"

Da muryar kuka tace tace" 'Karya kake yi wallahi baka 'kauna ta ko ka'dan..."
Inda ta 'karashe maganar hawaye na gangaro mata.

Cikin nuna rashin damuwa da kukan da take yi yace" Ki bari in gwada miki zaki fahimta..."
Tunkan ma ya rufe bakin sa tace" Ban so..ni ka 'kyale ni..Allah yayi min tsari da kai mayaudari, azzalimi wallahi har abada bazan ta6a yafe maka ba...".

" Really?"
Ya fa'di yana zare idanu cuz sosai ransa ya 6aci da zagin da tai masa idanun sa har canza kala suka fara...bata kula shi ba ta cigaba da kukan ta duk da kuwa ta fahimci ransa ya 6aci sosai da ita...Hijabin ta dake hannun sa yayi jifa da shi gefe sannan ya sake tunkarar gaban ta, yatsa ya 'dago ya nuno ta da shi da jajayen idanun sa cike da 6acin rai ya furta" In dai har haka kika ce Husnah nima bazan ta6a fasa abinda nayi niyya ba tunda cewa kika yi har abada bazaki yafe min ba...kuma ki sani daga yau duk lokacin da na bu'kaci ganin ki u must come to me dolen ki, kuma bazan kar6i excuse ba, in bahaka ba kuwa zan baki mamaki..."

A firgice ta 'daga kai ta kalle shi da mamaki idanun ta na tsiyayar da hawaye tace" Mu'een da auren nawa kake fa'din haka?".

A tsawace ya bata amsa da
" To hell with ur auren...ko ma uban wa kike aure i don't bloody care ni dai na gaya miki.."

'Kasa tayi da gwiwar ta tare da sau'kar da murya take ro'kon sa hannayen ta biyu ta 'dago
" Kayi ha'kuri wallahi na yafe maka komai dan Allah kar ka tozarta min aure Mu'een".

" Ki ri'ke yafiyar ki ban so...kuma ki sani duk lokacin da kika yi kuskuren yi min taurin kai wallahi ki tabbatar labarin rayuwar ki na nan Jigawa zai isa ga mahaifan ki da mijin da kike tutiyan auren sa akakin duk cikin sa'o'i 'kalilan kin san zan iya ko?".

Hannu tasa aka ta rusa kuka tamkar ance da ita mahaifiyar ta ta rasu ne a dai-dai lokacin.

Tayi danasanin ha'da ala'ka da Mu'een yafi sau 'dari abaya lokacin da ya nuna mata 'kyama bayan tasowar maganar auren su but na yau 'din tana jin nadamar da take yi tamkar bazata sake yin irirn sa ba har abada....bata san Mu'een bashi da ko 'digon imani cikin zuciyar sa ba sai yau...kuka ta sha son ranta wanda sam shi hakan bai dame shi ba...duk yadda ta so ta hana shi aikata abinda ya yi niyya kasa wa tayi yayin da ya ringa yi mata komai cike da rashin imani da mugunta.

Husnah kam ita da kanta sai taji ta sani kanta ta tsani rayuwar ta, tayi Allah wadai da rayuwar ta gaba 'daya, bata san me zuwa Jigawa ya 'kare ta da shi ba face ba'kin ciki da takaici.


Bazata manta ranar da Hisham ya fara kusantar ta ba kafin tafiyar sa...duk da ba laifi ta 'dan yi amfani da wasu abubuwa na gyaran jiki amma duk da haka bai hana Hisham fahimtar cewa ba cikakkiya ya aura ba...Hisham mutum ne mai nagarta da sanin ya kamata, shiyasa bai wani nuna mata rashin jin da'din sa afili ba, duk wani abinda ya dace da yayi mata a lokacin sai da yayi har tana tunanin ko bai gane bane.

Amma daga baya cikin natsuwa sai yake tambayar ta abinda ya faru da ita da yasa ta rasa pride 'din ta.

Nan take tayi masa musu ta nuna masa ita ba abinda ya ta6a faruwa da ita...sannan in ba shi ba babu wanda ya ta6a kasantar ta, a zahiri ita kanta tasan ba gaskiya ta fa'da masa ba wanda tunanin ta wai kar idan yasan gaskiyar ya tozarta ta shiyasa ta 6oye masa.

Bawan Allah Hisham kam ganin yanda ta dage ne yasa take ya amince da batun ta kuma bai sake tada zancen ba.

Shiyasa tayi al'kawarin kame kanta ta ri'ki mijinta tayi masa biyayya sakamakon rufin asirin da yayi mata.

To yau idan akace labarin ala'kar ta da Mu'een ya isa kunnen sa da wani idanu zata dube shi? Sannan mummyn ta ma wani irin kallo zatayi mata?"

Tana hawaye ta koma gida da kayan ta cikin jaka, hatta 'dan sahun da ya 'dauko yakan waiga ya kallo ta lokaci zuwa lokaci ganin yanda take ta share hawaye.

Ko wanka ba ta tsaya tayi a gidan sa ba sai da ta koma gidan ta kafin tayi shi idan ka ganta duk ta fita hayyacin ta, da 'kyar ta samu hawayen ta tsaya amma haushi da ciwon abinda Mu'een yayi mata bai bar zuciyar ta da wuri ba.


Da dare da Hisham ya 'kira ta ya so ya fahimci yanayin da take ciki daga muryar ta saboda ya ji ta duk tayi sanyi sarai ya fahimci akwai abinda ke daminta, amma sai ta ce da shi ba komai...ita kawai garin ne ya isheta tace makarantar ma ta gaji da shi gida zata koma ita kam.

Lalla6an ta ya ringa yi akan ta daure ta 'karasar tunda watanni 'kalilan ne suka rage musu ai kamar yau ne...bata san me zata ce da shi da zai sa shi aminta da 'kudurin ta ba indai ba kanta zata tonawa asiri ba, hakan yasa dole ta ha'kuran kamar yadda ya bu'kata sai dai tasan rayuwar da zatayi a Jigawa yanzu zai kasance ne mafi muni daga cikin rayuwar ta na duniya, bata jin zata sake yin farin ciki kuma matu'kar ta kasance cikin garin Dutse tare da Mu'een.

Husnah har 'yar rama tayi saboda damuwa...sai dai cikin sa'a Mu'een bai sake tuntu6ar ta da batun ba kusan kwanaki goma sha 'daya da zuwan ta gidan sa, wanda cikin hakan har Hisham ya zo yayi weekend wurin ta ya koma Abuja.

Kaf Mu'een ya san da zuwan Hisham shiyasa ma ya share ta..cuz barazana kawai yai mata dan tana bashi ha'din kai idan ya bu'kaci ganin ta bawai dan yana da niyyar tona ta dagaske ba.


Ko zuwan Hisham daya ga halin da take ciki ma hankalin sa ta shi yayi sosai wanda yayi-yayi ta sanar da shi damuwar ta amma ta'kiya sai dai tace ita garin ne kawai ya ishe ta da kuma zaman ka'daici.

Al'kawari yai mata akan zai sa abincika mata  yarinya da zata na taya ta zama da kuma wasu ayyukan...bata 'ki ba ta amince cuz ita kanta zata so hakan ko babu komai zasu zauna suyi hira zata rage mata tunani.


Sati biyu cif da zuwan ta gidan sa amma basu sake ha'duwa da shi ba, har ta 'dan fara sakin ranta kwatsam ranar wata talata sai ta ga text 'din sa cikin wayar ta.
" _Ina jiran ki by 4pm_ ".

Innalillahi ta ringa maimaitawa sannan da rawar jiki ta tura masa " _Ina da lectures_ ".
Sai yacturo mata reply da " _'karya kike yi...ni dai ina jiran ki_ ".

Tun daga gidan tan ta fara share hawaye na ba'kin ciki, haka tana ji tana gani ta shirya ta fita, ni'kab ta sanya ta rufe fuskar ta dashi ita ka'dai tasan ciwon da wannan lamari take yi mata...ganin da auren ta amma Mu'een na so ya lalata mata shi ya na janta izuwa ga mummunar halakar da bazata 6ulle musu ba.

A parlourn sa ta same shi yana kishingi'de kamar ba shi ba...da ganin ta sai ya fara murmushin mugunta...kai ta kawar gefe sannan tace da shi" Kai baka tsoron Allah ko Mu'een?"
Yace " Idan koyawa mutun akeyi sai ki koya min tunda ke 'din na lura gwana ce ta wannan fannin".

Yanda yayi maganar da izza ya sanya ta dole ta sau'kar da muryar ta cuz ta fahimci shi 'din yayi nisa sosai.

Da sanyin murya tace" Nifa indai akan batun yafiya ne wallahi na yafe maka har abada dan Allah ka barni in zauna da mijina lafiya"

Ido ya tsura mata kawai yana kallon ta..wato auren bazata da akayi matan yafiye mata shi da suka da'de suna tare.

Baki ya ta6e yana shafa cikin sa yace" Ni dai yanzu yunwa nake ji..sama min wani abu please ".






Comment
Vote
Share








*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)


By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *57*


Bata ce da shi 'kala ba kamar zatayi kuka ta juya ta nufi kitchen 'din sa dake gidan, sharp-sharp tayi masa jallop na cous-cous da yaji attaruhu sai 'kamshi ke tashi...a hakan ma bata samu vegetables a fridge 'din sa ba shiyasa tayi masa a hakan.


Gaban sa ta kai abincin ta ajiye, har a lokacin kuwa sanye take da hijab 'din ta bata yi gigin cire shi ba.

Tana ajiyewa ya tashi ya mi'ke tsaye da kansa ya 'dauko ruwan gora da cup sannan ya dawo ya zauna ko inda take bai sake kalla ba.

Bata zauna ba haka shima bai ce da ita ta zauna ba, tana tsaye har ya 'kare cin abincin ya kora ruwa...'dayan plate 'din ya 'daga yana rufe guntun abincin da shi yace " Zaki iya tafiya".

Wani sanyin da'di da Husnah ta ji ya sau'ko mata har sai da yasa ta saki ajiyan numfashi a fili.

Da sauri ta nufi hanyar fita dan ma kar yace ya fasa shiyasa bata wani 6ata lokaci ba...sai hamdala take da abun ya tsaya iya girki duk da hakan 'din ma tasan ba dai-dai bane amma ya zatayi...abin is complicated to her bata san hanyar 6ullewa ba tako ina ba sau'ki.

Haka ta cigaba da rayuwa a kullun Allah take mi'kawa kukan ta akan ya yi mata katanga da sharrin Mu'een...duk da tana tsananin son shi har yanzun amma darajar auren ta yafiye mata komai.

Cikin sa'a bai kuma neman ta ba har aka 'kara cin wasu kwanaki, wanda zuwa lokacin har an kawo mata yarinya mai tayata zaman 'yar matashiya mai suna Dija, yarinyar nada nutsuwa kuma tana 'debe mata kewa sosai, ga ta da aiki bata san jiki, ga girmama ta da take yi tamkar 'kanwar ta..hakan ne yasa hankalin ta ya kwanta yanzu sosai.




*****
    A can Shuwarin kuwa Ammi sosai take bani kulawa, tana jana a jiki da maganganu inda har take shan cikina cikin dubara dan taji ko ina kula wasu samari awaje, ban ma san manufar ta ba amma da yake ba kowa 'din nake kulawa ba shiyasa ban 6oye mata ba.

Sosai yanzu ta ri'ke min wuta da shiga kitchen kula da tsafta ta duk da dama can ina da ita amma yanzu Ammi komai na sake yimin gyara take yi akan sa ni kam duk ban ta6a kawo komai cikin raina ba.


Ko jiya ma da nace zanje in dubo Ma'u dan bata lafiya Ammi hana ni zuwa tayi tace in bari ba yanzu ba bata son in cika yawo sosai...tace kawai inyi mata addu'ah.



*****
'Bangaren Ma'u kuwa tun cikar sati uku da ha'duwar su da Yah Deen abubuwa suka fara canza mata, ga damuwar yaudaran da yayi mata ga kuma wasu 'yan canze-canze da take jin jikin ta ciki.

Sai tana jin 'kananun zazza6i da ke tashi mata lokaci zuwa lokaci.
Babu wanda ya damu da zazza6in nata dayake ba kwantar da ita yayi ba amma kafin sati biyu sai abin ya 'karu ta fara jin bakin ta na tara yawu akai-akai ga kasala da ke yawan damun ta.

Matar Baban ta ce ta fara mitar hakan dan ko 'dan wanke-wanke da take yi mata ma yanzu da 'kyar take yin sa.
Ga wankin kayan ta nan ma duk ta tara su amma takasa wankewa.

Ko a school mun fara jarabawa amma banda Ma'u cuz ko taje makarantar bata iya yin komai shiyasa ma ta daina zuwa.

Wata biyu ba sati 'daya kenan yanzu da ha'duwar su da Yah Deen, abin nata kuwa sai abinda yayi gaba, mahaifin ta da jansa ya 'dauke ta ya kai ta Chemist dan aduba ta tunda jikin nata ya'ki da'di da tunanin typhoid ke damun ta da yake yaga sai 'karewa take yi wuri guda.

Mai Chemist kam ko daya ganta da yanayin ta kawai sai ya bata su paracetamol sannan ya 'debi jini da fitsarin ta yace za'a kai gwaji a cikin Azare.


Ku'din da duk za'a bu'kata ya gaya wa mahaifin ta take kuwa Malam Barau ya ciro ya biya sannan suka koma gida da sunan jibi zai dawo ya kar6i result 'din test 'din nata.


Ranar ne ya kasance ranar 'kunci da damuwar ga mahaifin Ma'u dan tashin farko likita ya fito fili ya bayyana wa MALAM BARAU cewa 'yar sa Asma'u na 'dauke da juna na tsawon wata biyu.


Kusan mutuwar tsaye Malam Barau yayi saboda tashin hankali, gashi ko da yaje gida da labarin ma step mothern Ma'u bata kwantar masa da hankali ba sai ma masifar da ta haushi da shi wai maganin su kenan ai tunda yace sai tayi makarantar boko ai  sakamakon su kenan.


Ma'u kuwa kamar ranta zai fita haka taji...wai ita ce ke 'dauke da ciki ajikin ta..tayi kuka fili da zuci.

Duk ta rame tayi fayau da ita..saboda ko abinci ma ba iya ci take yi ba da taci yake dawowa.

Duk abin nan dake faruwa Ammi bata bar ni naje dubo Ma'u ba...har ma zuwa yanzun na gaji da tambayar na ha'kura.

Mahaifin Ma'u bai iya yayi magana da Ma'u ba saboda takaici, matar sa ce ma cikin 'kananun maganganunta har ta tuna masa batun sanin mamallakin cikin wanda shima sai a lokacin hakan yazo ransa.

Tun ranar da ya shigo da result na test 'din abinda kawai ya iya ce da Ma'u shine" Baki kyauta min ba Ma'u".
Cikin tsananin rashin walwala ya fa'di mata hakan tare da wulla mata takardar gwajin har yau bai 'kara ce da ita komai ba, ita kam ma nawin ahalin gidan ya hanata sakat bata ko iya fitowa ta zauna tare da su..ga shi shirun da mahaifin ta yayi matan sai ya 'kara tada mata hankali, abubuwan duk sun taru sun yi mata yawa.


Sai yanzun ne Malan Barau ya iya tashi ya shiga har cikin 'dakin da Ma'u take inda ya same ta du'kun'kune cikin hijabi kamar mai bacci...jin motsin shigowar shi ne ya sa ta yun'kura ta tashi ta zauna amma sam ta kasa ha'da idanu da shi.. yana daga tsaye ta gaishe shi kanta 'kasa inda ya amsa mata babu yabo ba fallasa shima 'din ji yake kamar ya zubar da hawaye idan ya ganta, Ma'u banda hawaye babu abinda ke motsi a jikin ta su ka'dai ke gudu wani na bin wani.

" Ban ta6a tunanin zaki bani kunya ba Ma'u, nayi 'ko'kari sosai wurin ganin na bawa rayuwar ki kariya bansani ba ashe shirme na nake yi..."

Cikin kuka tayi saurin  taran sa da fa'din" Baba dan Allah kayi ha'kuri ka yafe min wallahi ba hali na bane..."

Yanda tayi maganar da yanda take kuka ya sashi juyawa kawai ya bar 'dakin saboda tausayin ta da ya sake tsarga masa a zuci, abin ma da ya kawo shi bai iya ya tambaye ta ba.


Yana fita Innar su ta tare shi da fa'din" Waye mamallakin cikin ta gaya maka?"
" Bansani ba nima".
Ya bata amsa atakaice.

Bata 'kara sauraron sa ba kawai ta fa'da 'dakin da Ma'u take kamar wata zararra, kan Ma'u na 'kasa tana faman share hawaye da sheshshe'ka kawai taji muryar innar tasu kamar daga sama tana fa'din" Munafurcin banza da wofi...da kika je kika yo cikin baki san cewa abin kunya kika yo bane sai yanzu da ya bayyana kansa?...kuma da kike ta faman nu'ku-nu'ku da cikin idan anbarki da shi zaki zama uwa da ubansa ne...in ba munafurci ba ai kinsan wanda ya 'dirka miki cikin da bazaki fa'da ba har sai kin sa zuciyar ubanki ta buga saboda ba'kin ciki ko?...to bari kiji tun wuri ki bu'di baki ki fa'di wanda yayi miki in ba haka ba wallahi su Salele zansa suyi miki dukan mutuwa agidan nan tun da baki da amfani...shashasha kawai wacce bata san ciwon kanta ba.."

'Dagowa tayi ta kalli Innar dan sanyin murya tace
" Inna dan Allah kiyi ha'kuri wallahi zan fa'di".

Kunne Innan ta juya mata tare da furta" Uhum ina jin ki".
Sai da ta share haware kafin ta furta
" Yah Deen ne".
Inna kam ha'de goshi tayi tana ta6e baki ta ce
" Waye kuma Ya Deen?"

Ma'u kam 'kara yin 'kasa da kanta tayi tace" Deeni 'dan gidan Alhaji Tahir mai gidan gona".

" Innalillahi wa inna ilaihi ra ji'un..."
Innah ta saki salallami da 'karfin ta tana tafa hannuwa....daga 'karshe ta dire hannun saman bakin ta sannan tace" Yanzu Ma'u har can kika kai kanki saboda tsananin kwa'dayi?"

Kuka Ma'u ta saki bata iya ta sake magana ba har Innar ta gama surutan ta ta fita.

Tasan dama kowa yaji labarin zai yi zaton kwa'dayi ya kaita wurin sa...nan kuwa ba haka bane tsabar iya salo da yaudara suka nuna mata shi da abokin sa Imrana da sunan aure...alhalin tun ranar har yau bata 'kara ganin ko Imaranan bane ma ballantana uban gayyar.

Take Inna taje ta samu Malam Barau ta sanar da shi mamallakin cikin kamqr yadda taji daga bakin Ma'u.

Jikin sa sanyi 'kalau yayi, shi kansa ya bari ne akan kwa'dayi yaja Ma'u, haka ya yini yana tunanin abin cikin ransa, da

Please Login or Register in order to submit comment