Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baki tayi da jin hakan sai tace " ah ah lallai kun sha yawo, .....sai kuma.......".


Noor na shirin sake yin wata tambayar sai suka ji motsi.


Itace tayi saurin juyawa cike da firgici cuz' bata yi zaton ganin Deen a dai-dai wannan lokacin ba dayake idan yafita sallar maghrib baya dawowa gida har sai anyi isha'i tukunna, amma kawai yau 'din kwatsam bata san dalili ba sai gashi kuma ya dawo.


A hankali ya 'karaso cikin basarwa ya furta
"gyaran gashi kuke yi ne?"
Yayi maganar tare da kallon fuskar Jas hannun sa cikin aljihun wando.


Kai Jas ta 'daga masa alamar "ehh "
yayin da Noor ta amsa da " umm"
a 'kasan ma'koshi.


Deen bai sake magana ba kamar yanda bai sake kallon 6angaren da Noor take ba sai ya dan ja baya ya zauna daga kan side drawer yana duba cikin wayar sa.


Noor kuma ta cigaba da warware gashin Jas 'din, shiru wurin ya 'dauka na 'dan lokaci har ta kammala tsifan mata kan ta taje tare da yin parking wuri guda da 'dan 'karamin ribbom Deen na zaune yana kallon wayar sa kowa abinda ke cikin ransa daban.


Sai data gama mata komai kafin tace da ita ta je parlour ta jirata bari ta wanke hannun ta tana zuwa.


Har Jas tafara tafiya sai Deen ya 'kira ta zuwa inda yake, Noor bata damu ba illah shigewa bathroom da tayi dan tsaftace hannun ta.


Koda ta fito kuma bata samu Jas a 'dakin ba sai shi ka'dai a zaune kamar yanda ta barshi.


A hankali ta 'karasa inda yake ta zauna daga gefen sa sai take jin wani iri da shirun nasa sosai take jin guilty conscious na sar'ke mata ga6o6i game da tambayar da ta yiwa Jas 'dazun wanda take kyautata aton yaji ta dan bata san tsawon lokacin da ya 'dauka tsaye a wurin ba.


'Dan 'dago wa tayi ta saci kallon sa sai da kuma mai da kallon ta gefen sa bakin ta na sar'kewa tace " Yah Deen!"


Kallon ta yayi ba tare da yayi magana ko amsawa ba illah 'dage gira 'daya da yayi yana kallon ta a karkace.


Itama idanun ta sau'ke a 'kasa sam takasa 'daga idanu ta kalle shi balle har su ha'da idanu dashi balle irin kallon da yayi mata yanzun sam yasa ta jin ba da'di.


Kanta a 'kasan tace dashi
" d'azu daku ka fita ka manta 'dayan wayar ka a gida kuma an ta 'kiran ka".


Bai kalle ta ba yace " waye ya 'kirani ?"

Amsa ta bashi a takaice da fa'din
" _Jiddah_ !".








*Kuyi min afuwa plz......nasan ban kyauta ba amma insha Allahu zan na 'ko'kar tawa wajen ganin nayi muku typing ko ba yawa ma.*






Comment
Vote
Share







*Salmerhn ku ce* 😍
[11/17/2019, 9:34 PM] 🌸Salmerh🌸: πŸ’• *NOORUL* πŸ’•
(Haske nah)



By
*Salmerh MD*



*Wattpad @*
*Serlmerh-md*



πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
πŸ’«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*



*It's ur day dearies so enjoy it πŸŽ‚πŸ© *HAPPY BIRTHDAY 2 u* πŸ©πŸŽ‚
*Sis Faateemah and my besty Dr Khausar.......may Allah bless u with d very best of evrything in your life. πŸ₯°.*


*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*



πŸ…Ώ *4*


Ha'de rai Deen yayi ya wani tsare ta da idanu tare da fa'din " dalilin kenan da ya sanya kike neman sanin inda muka je ni da Jas?"

Kai ta jijjiga masa da sauri alamar "ah ah".

" to menene?"
ya sake tambayar ta.


Noor sharesa tayi ta 'kurawa gefen inda yake zaune idanun ta da suka cika taf da hawaye 'kiris suke jira su gangaro.

Daya ga bata da niyyan tankawa ne yasa shi fa'din
" am i not talking to u ?"
yayi maganar a 'dan tsawace.


Sai a lokacin Noor ta juyo da idanun ta kan fuskar sa ta kalleshi jin yanayin da yayi maganar sai suka ha'da idanu.

A hankali ta furta " Yah DEEN......."
daga haka bata 'kara fa'din komai ba illa saurin 'dago hannun ta 'daya da tayi ta toshe bakin ta da shi.


Kukan daya ma'kale mata tun 'dazu ne ya kubce mata inda ta ringa yin kukan mai sauti da ko Jas dake parlour zata iya jiyo ta amma daya ke akwai 'karan T.V kuma Ninja Turtles 'din da take kallo a MBC 3 ya matu'kar 'daukan hankalin ta shiyasa bata jiyo ta ba.


Deen kuwa kai ya kawar gefe tare da cizon la6en sa na 'kasa sam koka'dan baiji da'din abinda ta aikata yau 'din ba, amma babu yanda zai yi cuz ya tsani jin kukan ta sosai yake ta6a masa zuciya.


A hankali ya juyo ya kalle ta ba tare da wani 6ata lokaci ba ya sa hannu ya rungumo ta jikin sa batare da ya furta komai ba sosai yayi 'ko'kari wajen ganin ya danne 6acin ransa yana rumgume da ita har sai da yaga ta 'dan tsagaita da kukan yanayin ta ya 'dan daidaita ta fara sau'ke numfashi kafin ya fara 'ko'karin raba jikinsa da nata.


A hankali itama Noor ta furta sunan sa ganin yana 'ko'karin sakin ta
Sai tace
" Yah Deen dan Allah kayi ha'kuri ka yafe min......."

Bata gama rufe baki ba ya tare ta da fa'din
" amma kinsan koma miye ne ai bazan ta6a 'daukan 'yata ta cikina na kai inda be dace ba ko ?"
Cikin 6acin rai sosai yayi maganar sai ma ta gode Allah da ya furta mata hakan domin Deen sosai yake 'daure ta da shirun sa idan tayi masa laifi amma yau 'din ga dukkan alamu zata 'dan samu sassauci.


Da muryar kuka ta bashi amsa da fa'din
" na sani Yah Deen.... i'm sorry please ba nufi kenan ba....kawai fa na tambaya ne".
Ta 'karasa maganar tare da barin jikin sa ko dan taga yanayin fuskar sa a lokacin.


Deen kuwa bai ce da ita komai ba sai 'dan 'karamin tsaki da ya saki tare da mi'kewa tsaye yana gyara rigar jikin shi yace da ita
" na tafi masallaci".
Bai ko jira jin abinda za tace ba ya sa kai yayi gaba abinsa.


Noor da idanu ta raka shi har ya idasa barin 'dakin kafin ta dawo da hankalin ta gaban ta.


Tagumi ta rafka tare da rintse idanu tana tuno rayuwar su na baya da shi a hankali siraran hawaye ke bin kuncin ta masu 'dumi, wani abin idan ta tuno shi murmushi yake sata yayin da wani abin kuwa ji take tamkar tayi ta rafka ihu ko zata ji 'dan sami sassaucin abinda take ji a cikin zuciyar ta.


Ta 'dau tsawon lokaci a haka batare da ta sani ba, sau'kan hannun Jas da taji saman nata hannun ne ya sata yin firgigi ta dawo daga tunanin data fa'da.



Murmushi ta 'ka'kalo ta sanyawa fuskar ta na dole tare da dai-dai muryar ta kafin tace da Jas 'din
" Baby har kin gama kallon ne?"

SJas cewa tayi
" yunwa nake ji Mummy kuma Daddy yace zai kawo min ice cream amma har yanzu bai dawo ba ".


Ajiyan numfashi Noor ta sau'ke sannan tace
" ohh sorry Baby zai dawo kinji sallah yaje yi daya idar zai kawo miki...muma bari muyi sallahn kafin ya dawo ko?"


Kai Jas ta 'daga sama tana kallon Noor 'din.

Sai ta sake fa'din
" Mummy idon ki fa akwai hawaye me ya same ki?"

Noor saurin kaiwan hannu tayi ta goge fuskar tata sam tama manta da hawayen sai tace mata
" bakomai Jas abu ne ya shiga min idon kuma na cire shi".


Tana gama fa'din hakan sai ta mi'ke tare da kama hannun Jas suka nufi bathroom dan yin alwala.


Sallahn isha'i suka gabatar tare da jero addu'o'i kamar yanda ta saba yi kullum Jas na tayata da fa'din Ameen sannan suka shafa.


Ganin har a lokacin Deen bai dawo ba yasa ta tasa Jas agaba ta karanto mata suran da suka tsaya da karatu a islamiyar su dan ta gyara mata inda take 'dan kuskure wa.


Take kuwa Jas tayi bismillah cikin muryar ta ta yarinta ta karanto mata suratul *Fajr* daga farko har zuwa aya ta goma sha tara a duk cikin ayoyin kuwa bata yi mata gyaran komai ba dan kuskuren ta yawancin yana bin yanayin harshen ta ne dayake yarinyace har sai da ta kai inda suka tsaya kafin Noor ta yi mata gyara wajen _wata'a kulunat-turatha aklal-lammah_
Wannan ayar ne yayi mata wahalan fa'da sosai sai da tayi ta maimaita mata kafin ta ri'ke shi daga shi sai ...... _watu hibbunal mala hubban jammah_
wato aya na ashirin kuma anan suka tsaya da karatun a cikin satin.

Jas akwai 'ko'kari ba laifi dan Noor bata 'dauki wani tsawon lokaci ba wajen gyarawa Jas karatun sai gashi ya zauna abakin ta.


Ganin haka yasa Noor sai ta kama hannun ta suka koma parlour dan suyi zaman jiran Deen kafin ya dawo.


Ga mamakin su kuwa suna shiga parlourn sai suka ganshi zaune a ya sanya T.V a gaba yana kallon labarai.


Ko da yaji motsin fitowar tasu ma bai 'daga kai ya kalle su ba yi yayi tamkar bai san da fitowar sun ba.

Jas ce ma da ganinsa sai ta wuce gurin sa da gudu ta 'dane jikin sa tana tambayar ice cream 'din ta.


Murmushi yayi tare da kamo chicks 'din ta da hannun sa 'daya yace " y'an matan Daddy mai kwa'dayi to na manta ban siyo ba "


Kafa'da Jas ta no'ke tana cunno baki gaba tace dashi " ni kan ah ah".

Waro idanu Deen yayi yace " ya za'ayi kenan to ?"

Tace " Daddy tunda ka tuno yanzu ai sai kaje ka siya min".

Sai yace
" Smile then...in ba haka ba nima ba zani ba".


Murmushi Jas ta saki tare da fa'dawa jikin sa ta kwanta.


Shima Deen murmushin yayi sannan ya kai hannu gefen kujera inda ya ajiye ledan daya zo dashi ya 'dago shi.

Itan ma 'dago ta yayi zaune tare da 'dago ledan saitin fuskar ta yana murmushi.


Jas na ganin ledan bata yi wata-wata ba ta sa hannu ta kar6a ta rungume tare da fa'din
" thank u Daddy".


" yes Dear"
Yace tare da mi'kewa da ita tsaye suka nufi dinning ganin cewa tun 'dazu Noor take wajen tana jiran su.


Bai zauna ba sai da ya samawa Jas gurin zama a kujerar dake tsakanin su kafin shima yaja 'dayan kujerar ya zauna.


Already Noor tagama arranging dinner 'din ta rurrufe dan haka bu'dewa kawai suka yi ha'di da bismillah suka fara cin abincin.


Kuma ko a lokacin ma Deen ne da 'yar sa kawai sukayi ta shagalin su yayin da Noor ta sanya abincin a gaba tana kallo bai fi spoon uku ta kai bakin ta ba abubuwa duk sunyi mata yawa a zuci.


Deen kam da Jas kamar ma sun manta da ita a wurin dan baya ci sau biyu batare da ya kai wa Jas a bakin ta ba ita ma kuma Jas haka suna ci suna raha abinsu.


Noor ce shiru kamar bata wurin duk kuwa ashe Deen na lura da ita batare da ta sani ba.


Jas ma kamar tasan abinda ke cikin ransa sai da ya mi'ka mata ta kar6a tana murmushi tace da shi
" saura Mummy ma ".


Juyawa yayi ya kalle ta sai amma bata ma san yayi ba domin ga dukkan alamu tunani takeyi aranta.

Tana cikin tunanin kuwa taji an take mata 'kafa daga 'kasan table.


Firgigi tayi tare da kallon inda yake ganin yanda ya nufo bakin ta da spoon cike da abinci fuskar sa ba yabo ba fallasa amma ya'ki kallon fuskar ta.


Abincin ta kalla sannan ta sake maida kallon ta kan fuskar sa still ya'ki su ha'da idanu.

Da niyyar ta ta'ki kar6an abincin amma sai taji muryar Jas na fa'din " Mummy is ur turn now "

Dolem ta ta bu'de baki a hankali yasa mata abincin.

Shine yaci gaba da bata tana kar6a ana uku sai tace ya ishe ta ganin har a laokacin ya'ki kallon cikin idanun ta sai yake sake sata cikin ru'dani.
Parlour suka koma bayan sun 'kare cin abincin inda suka zauna jigum babu mai yiwa wani magana a tsakani Jas ma jikinsa take har tayi bacci.


'Karfe tara da 'yan mintina ya 'dauke ya kaita 'dakin Noor ya kwantar da ita, da kansa ya rage mata mata kayan jikinta amma rashin sanin inda kayan baccin ta suke yasa shi barin ta da 'yar rigar ciki ya fita ya koma nasa 'dakin.


A parlour ya wuce Noor da ta kwantar da kanta jikin kujera tana binsa kawai da kallo.

Ganin ya koma nasa 'dakin ne yasa ta tashi itama ta kashe dukkan switch 'din sannan ta shiga 'dakinta.

Sai da ta gama shirin baccin ta kafin ta 'dauko wa riga da wando marasa nauyi ta sanya mata da hula.

Zama tayi tai mata addu'o'in bacci ra shafe ta sannan ta rage 'karfin fan tare da kashe wuta ta fita bayan taja mata 'kofan.

D'akin Deen ta nufa inda ta same shi kwance luf tamkar mai bacci dan ko sallamar da tayi ma bai amsa ba, a hankali ta 'karasa shigowa ta tura 'kofar ta kamar yanda ta samu.







plz kar kuce yayi ka'dan fah.




Comment
Vote
Share








*Salmerhn ku ce*😍
[11/17/2019, 9:34 PM] 🌸Salmerh🌸: πŸ’• *NOORUL* πŸ’•
(Haske nah)



By
*Salmerh MD*



*Wattpad @*
*Serlmerh-md*



πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
πŸ’«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*


Dedicated to MeemarTJ


Nagode sosai da Addu'o'in ku masoyana ubangiji Allah saka da mafificin alkkhairi.


*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*



πŸ…Ώ *5*


'Dakin ba wani haske sosai dan haka kawai sai ta 'karasa bakin gadon ta tsaya 'dan takaitaccen kallo tayi masa cuz rashin hasken 'dakin bai hana ta kallon fuskar sa dake 'dauke da lumsassun idanu da kyau ba, sam sai taji bata yadda baccin yake yi dagaske ba, 'dan murmushi ta saki da ya tsaya mata iya kan fuskar ta sannan a hankali ta haura gadon tare da matsawa jikin sa ta kwantar da kanta bisa hannun sa tayi shiru tana 'dan tunani.
Ga dukkan alamu yau 'din _Mu'inuddeen_ 'din da ta sani tun baya ne ya motsa, musamman data ga yanda yake ta faman share ta ta fuskan magana, shi bai nuna 'karara cewa yana fushi da ita ba amma azahiri yanayin da yake yi matan sosai yake ta6ata.


Ajiyan zuciya ta sau'ke a hankali....shiru tayi na 'dan lokaci itama tana sau'ke ajiyan zuciya tare da 'dan lumshe idanu.
Tunanin irin matsayin da _Jiddah_ take dashi a wurin sa takeyi, wannan shine karo ba biyu da taga 'kiran Jiddah a wayar shi, sai dai kuma na yau 'din taga ko bi takan wayar be 'karayi ba har yanzu tana nan ajiye a parlour kan center table tunda ta kashe ta ajiye a wurin shima bai sake dubawa ba, sa6anin ranar farko da Jiddahn ta ta6a 'kiran sa, a lokacin kam taga 'kiran ya 'dan 'dauki hankalin sa ka'dan.
Bata san manufar sa a yau 'din ba da be duba wayar ba.
Baki ta ta6e tare da ayyana " ALLAH YASA IYAKAN ALA'KAR KENAN".


Ganin har a lokacin DEEN bai motsa ba sai ta fara 'kiran sunansa a hankali tare da yi masa yawo da hannun ta saman 'kirjin sa.


Deen kuwa bai amsa sunan shin da ta 'kira ba duk kuwa da cewa sarai yaji ta amma still sai yayi kamar bai ji ta ba a yanda ta samo shin ko motsin kirki bai yi ba, 'ko'kari yake yi kawai ya nuna mata kuskuren ta akan abinda ya faru 'dazun.... amma ba wai dan yaja maganar ko kuma dan ya 6ata ranta ba.
Duk da hakan kuma ma sai yaji ba zai iya yin fushi da ita na dogon lokaci ba cus he missed her alots, and kuma bama ya son ace daga zuwan sa har sun samu sa6ani akan abinda bai taka kara ya karya ba, abin doesn't make any sence at all.
( shi a ganin sa)

Sunan shin data 'kara ambata ne ya sanya shi bu'de idanu amma da yake tayi 'kasa da fuskar sa sai bata san hakan ba yayin da taci gaba da yi masa yawo da hannun ta saman jikin sa da har yake 'ko'karin canza masa yanayi ba tare da ta sani ba.

Deen sake lumshe idanu yayi tsawon da'ki'ku yana ji da sauraron abinda take yi masan har ya fara jin tana neman 'kure shi musamman data ke yi masa wasa da nipple 'din sa tana 'dan ja ka'dan-ka'dan, dama gashi gwanin son ayi masa hakan sai kuma yaji bazai iya jurewa ba.
Karo 'daya kawai ya birkito ta take ya maida ita 'kasan sa.


Kallon fuskar ta ya tsaya yi kamar mai karantar wani abu har zuwa cikin idanun ta.
Kallon-kallo suka tsaya yiwa juna na 'dan lokaci batare da sun furta komai ba.
Noor ce ta bu'di baki a hankali tace " i'm sorry plz Yah Deen.....kayi ha'kuri kaji?"

Deen bai tanka mata ba sai kawai ya lumshe idanu ya kuma bu'de su akan nata.


Tana shirin sake magana sai yayi saurin matsar da fuskar ta ya ha'de bakin su waje guda, kissing 'din ta ya fara azafafe tare da sarrafa dukkan ilahirin jikin ta zuwa wani yanayi na daban mai wuyar fassaruwa.




*****
Noor wutan da Deen ya 'dauke mata ne 'dazun ya 'dauki hankalin ta har ya sa kwata-kwata ta manta da batun Sani balle ma har tayi magana a kan sa kamar yadda ta tsara cikin ranta tun kafin isowar Deen 'din.
Har kuwa suka gama faranta wa juna rai suka yi bacci bata tuna da hakan ba... sam bai zo kanta ba.


Washegari da shirin tafiya suka tashi, kafin 'karfe takwas kuwa har sun kammala komai.
Noor ce ma take 'dan mitan wai ai da an bar tafiyan sai gobe saturday ko kuma kawai abari sai Jas tayi hutu sai suyi tafiyar mai ma'ana yafi amma Deen sai cewa yayi " ai wannan tafiyar ta Jas ce ba tasu ba ita ke son aje dan haka kuwa shi ba zai 'ki faranta mata ba dan kawai makarantar friday ba, dan haka idan ita bata son zuwa tayi zaman ta".


Shiru Noor tayi ta 'kyale shi kawai ta ta6e baki yayin da Jas ke ta murnar zata ga su granny da su uncle Saif da Zaid.


Noor kam tun lokacin da ta ga Sani da sunan shi zai ja motar sai taji haka kawai ranta ya 6aci sai lokacin kuma ta tuna da batun maganar da ta tsara a ranta game dashi wanda bata samu daman sanar da Deen ba har yanzu.
Tsanar Sani take ji cikin ranta haka kawai batare da tasan takamamman dalili ba.


Lokacin da zata shiga motan 'dan 'karamin tsaki taja wanda daga ita ka'dai babu wanda yaji shi musamman data ji yanda Sanin yake tsokanan Jas yana yi mata wasa.

Deen kuwa bashi da matsalar komai dan shi Sani baya gaban sa abinda kawai ya sani shine Sani amintaccen yaron gidan sa ne mai matu'kar raha da iya zama da mutane.
( ganin Deen kenan).


Sani driver 'din ne ya ja su inda Deen ya umarce shi daya tsaya a shopping mall zasu yi siyayya.


Da niyyar shi su biyu da Noor zasu shiga amma da Jas ta'ki zama a motar tace zata bisu sai kawai ya 'kyale ta suka shiga tare, siyayya suka yi mai 'dan yawa na tsaraba da wasu kayan amfani daga nan suka 'dauki hanyar garin Shuwaryn.


Gari ne mai matu'kar yalwa da ni'ima ga da'din rayuwa, ita kanta Noor na jin da'din ganin ta cikin garin nasu, daya ke ma ta 'dan kwana biyu bata zo ba, sau tari Deen da Jas kanzo suyi weekend su koma abinsu batare da ita ba.
Yau kuma Alhamdulillah gata a cikin mahaifar ta ta asali.


Lokacin da suka isa 'kofar gidan Alhaji Baba tuni Jas tayi nisa a baccin da take yi tun a hanya.

Koda a kayi parking 'ko'karin 'daukan ta Deen ya fara yi amma yana 'dago ta daga jikin sa kuwa sai ta bu'de idanun ta a hankali, da yanayin bacci ta fara rarraba idanu caraf tayi arba da 'kofar shiga gidan kakan ta Alhaji Baba wanda tana ganin haka tafara 'ko'karin barin jikin sa shima sai ya 'kyale ta kawai ya bita da murmushi.


Batare da wani 6ata lokaci ba Jas tayi cikin gidan da gudu tana fa'din Ammee na, Alhaji Baba, Uncle Saif.


Murmushi suka yi kusan dukkan su harda Sani ganin yanda Jas ta shige batare da sauraran kowa daga cikin su ba, 'dan 'karamin mayafin Jas 'din na ri'ke a hannun Noor yayin da 'dayan hannun nata kuma ta ri'ke handbag 'din ta da shi, itama tana murmushin tace " Jas ko shirme".


Deen ne ya jagorance su zuwa cikin gidan da sallamar su, suna shiga ma sai suka ci karo da Alhaji Baba a harabar gidan tare da Jas ya 'dago ta sama da hannun sa 'daya 'dayan hannun kuma daddumar sallah ce ri'ke da shi ga dukkan alamu cikin shirin zuwa masallaci yake, dan kuwa sanye yake da shaddah sabuwa mai tsada ruwan zuma d'inkin riga da wando da babbar riga, yasha hula mai kyakkyawan zubi da birgewa sai tashin kamshi yake yi, sosai kayan suka kar6i faran fatan jikinsa.

Idan ka kaga Alhaji Baba bazaka ta6a yin tunanin a 'dan wannan garin yake rayuwa ba.


Yana ganin shigowar su kuwa ya sake fa'da'da fara'ar sa fiye da na baya ganin iyalan nasa tare da fa'din
" ah ah ah..... yau har da 'ya ta kuka zo kenan.....bar kanku da zuwa 'yata"
Yace tare da juyawa zuwa ciki.

Suma murmushin suka yi tare da binsa a baya zuwa yalwataccen parlourn gidan suka zazzauna.

Deen ne yana shirin zama yace " Alhaji nifa baka yi min barka da zuwa ba sai 'yar ka ka'dai ko in koma abina".

" bani da damuwa ai ko ka koma tunda ga 'yata ga kuma amaryata tare da ni".
Alhaji Baban ya bashi amsa yana murmushi.
Sai suka maida masa da martanin murmushin gaba 'dayan su batare da wata kalma ba.


Suna zama Jas tayi cikin 'dakin Ammee da gudu tana 'kiran sunan yayin da sauran dake zaune suka hau gaggisawa Alhaji Baba na tayi musu maraba da zuwa cikin farin ciki sosai dake fita tun daga zuciyar sa.


Jas kuwa koda ta shiga 'dakin Ammee bata ganta ba sai de taji motsin ruwa a bayi dan haka sai ta fito ta dawo wurin Alhaji Baba da ke ta faman hira da yaran nasa cikin walwala da raha Jas sai tace dashi
" Baba Alhaji ina su Uncle Zaid suke ?"
Murmushi Alhaji Baba yayi sannan yace da ita " ai kya bari mu gaisa da kyau kafin ki tambaye sun ko amaryata".

Jas cewa tayi
" ah ah ai na gaishe ka kuma ina so in gansu ne".


"Ai kuwa baki zo da sa'a ba domin kuwa duk suna makaranta".

'Dan 6ata rai Jas tayi tace" ai zanje makarantar in gansu".

Juyowa tayi ta kalli Deen sannan tace da shi" Daddy ai zaka kaini ko?"

" insha Allahu zan kaiki Mamana amma ba yanzu ba kinji?"
Deen ya bata amsa da kulawa.

Kai ta 'dage sama tana murmushi tace da Alhaji Baba " ai Daddy na yace zai kaini"!

Shafa kan ta yayi yace " to 'yar Daddy Allah ya bada iko".
Daga nan sai ya tambayi Deen yanayin sabon wurin aikin sa da ya koma.
Deen yace " ba matsala komai na tafiya dai-dai".

" masha Allah...Allah ya taimaka ya bada sa'a ya kuma rufa asiri".
Baba Alhaji ya fa'di da kyakkyawar niyyar sa a zuci.


Fitowar Ammee ne ya katse su gaba 'daya inda Jas ta tashi da gudu ta nufi Ammee ta 'kan'kame ta tana dariya Ammee ma dariyar tayi tace ' 'yar tsohuwa an zo kenan".

" ni ba tsohuwa ba ce Ammee ai ni 'yan mata ce".
Jas ta bawa Ammee amsa tana 'dan turo baki.

" Iyeh lalle kuwa ai ban san kin zama 'yan mata ba sai yanzu".
Ammee ta fa'da tare da 'dago Jas 'din sama suka 'karasa shigowa.


Nan aka sake dasa wani sabon gaishe-gaishe daga nan Ammeee ta kawo musu ruwa daya ke ma dukkan su suka shigo har Sani

Please Login or Register in order to submit comment