Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa* na can.


Bai dawo ba sai da ya tabbatar su Aliyu zasu dawo hutu kafin nan shima ya dawo, su kam ma ba haka suka so ba domin can suka so zuwa su same shi amma yace kawai su ha'du agida domin shima akwai abinda zai kawo sa.


Ranar da suka dawo Taheer, Mu'een da mahaifiyar sa duk a gidan suka yini sai yamma kafin suka koma gidan su....inda anan Umar ya ce abar musu shi mana su 'dan kara gaisuwa, take Aishatu tace a'a sai dai ya dawo gobe domin basu zo da kayan sa ba, kuma ma kar ya dame su daga sau'kan su gara idan sun 'dan huta sai akawo shi.
Da haka suka yi sallama suka koma gidan su.


Kwatsam tashin farko Taheer ya tsinci kansa a matsayin Assistant Manager na gidan man Oando dake nan cikin garin na Kano.


Wannan abin shi yafi komai yi musu da'di a rayuwar su baya ga haihuwar Mu'een, domin kuwa hakan shine ya kasance silar bun'kasuwan arzi'kin su suma suka zama abin kwatance.

Kunsan abu idan Allah ya dafa maka toh shikenan baka da matsalar komai domin babu wanda ya isa ya sha gaban ka face Allah ya kautar maka da shi.


Mahaifin Aishatu ne yayi masa hanyar hakan batare da sun sani ba dukkan su.....da yake mahaifin nata babban mutun ne mai fada aji....sai dai kuma bayan hakan bai yi wani tsawon rai ba ya koma ga mahallicin sa da dukkan sauran yaran sa biyu da suka zo hutu wato Aliyu da Umar.


Hatsarin mota suka yi akan hanyar su ta zuwa duba wani plot da ya siya zai kaisu ya nuna musu sai hakan bai faru ba, domin kuwa basu kaiga zuwa wurin filin ba ma motar su ta kife da su inda nan take biyu suka rasu, Umar kuwa a asbiti ya 'karasa da kalmar shahada abakin sa.


Wannan mutuwar itace ta kasance babban tashin hankalin su domin Aishatu gaba 'daya kasa nutsuwa tayi.... banda suma babu abinda take yi....shi kansa Taheer yaji mutuwar sosai wanda sai bayan mutuwar ne ma ya samu labarin halaccin da dattijo sirikin nasa yayi masa na canza masa wurin aiki tare da sawa a 'kara masa babban matsayi batare da ya sani ba.


Banda addu'ah babu abinda yake bin sa da shi domin dattijon iyamurin mutum ne mai mutu'kar dattako da halin girma sai fatan Allah yayi wa Alhaji Muhammad Ugoh Chukwu da iyalan sa rahama Ameen .


Hatta Mu'een da yake 'dan shekaru shida ma a lokacin sai da ya fahimci gidan nasu ba dai-dai yake ba, domin shima sosai ya rasa kulawar uwar sa, duk wani kulawar da ta dace ya samu daga gareta to baya samun sa.

Mahaifin sa ne ke 'ko'karin yi masa wa'dan su hidimomin da kansa, ga kuma aikin sa da yake yi, ganin hakan bazai fishshe su bane ya sanya shi nemo wata da zata ringa kulawa da yaron da kuma yi musu abinci.


Hutu ya bawa Aishatu sosai cuz ya san ko shine irin wannan mutuwar ta riske shi dole sai yaji babu da'di balle ita da take matsayin mace mai rauni.



*****
Haka rayuwar su ta cigaba da tafiya ba yabo ba fallasa, har akayi kwana arba'in da rasuwar, kafin hakan kuwa idan kun ga yanda Aishatu ta rame ta lalace abin har zai bawa mutun tsoro, sosai ta zabge ta fita hayyacin ta...ga uban low BP da ya sako ta agaba tun da 'kuruciyar ta...tana nan yau lafiya gobe babu.


Bayan arba'in ne lawyern mahaifin ta yazo da niyyar ya dan'ka mata dukkanin takaddun k'adarorin mahaifin ta harda ma wa'danda bata sani ba....bai wani dame ta ba balle ya d'aga mata hankali domin kyakkyawan nutsuwan ta ma lawyern bai samu ba, Taheer ne ya jagoranci lamarin inda ya kar6a mata wasu yayin da ya dan'ka wasu a hannun lawyern akan ya cigaba da kula mata dasu.

Abubuwa da yawa na mahaifin ta da basu san da shi ba, anan Kano harda ma can South Africa cikin su kuwa babu wanda ya bibiyi lamarin duk kuwa da cewa sun san yana da cibiyar kasuwanci acan, abinda yake gaban su ma ka'dai ya ishe su, domin shi Taheer a yanzu bashi da wani burin da ya wuce yaga matarsa ta warware amma abin ya faskara, tsawon wata uku da rasuwar amma ta kasa ha'kuri da rashin su.

Hatta Mu'een sai da ta koya masa tagumi da rashin son magana, cuz idan yaga tayi shiru tana tunani shima sai yaje gefen ta ya zauna yayi tagumi yana kallon ta, koda taga hakan bata tanka shi, idan kuwa yaga tana hawaye shima kukan yake yi....idan ta ga hakane sai ta rungumo shi zuwa jikin ta su cigaba da kukan tare.


Abin sosai yake ta6a masa zuciya domin ba 'karamin damun sa arai yake yi ba, amma ya rasa yadda zai yi, kullum yana ko'karin ganin ya nuna mata muhimmancin yadda da kaddara matsayin ta na musulma amma a banza kamar bada ita yake ba, ganin kamar yanayin yaron sa na son canza salo irin nata ne ya sanya shi dogon nazari, domin kuwa Mu'een surutaccen yaro ne amma tunda ya fara ganin mahaifiyar sa na yawan kuka shima ya zama shiru-shirun 'karfi da yaji, domin kuwa wani lokacin har mantawa zakayi cewa cikin gidan akwai yaro 'karami...tun farkon rasuwar yayi nacin tambayar su Granny, Uncle Umar da Uncle Aliyu yayi ta rigimar akai sa wurin su kullum amma rashin samun gamsasshiyar amsa daga bakin iyayen nasa ne ya sanya shi yau da gobe ya ha'kura shima duk kuwa da cewar ba wai ya manta dasu bane....tafiyar da ake ce masa sunyi ne ya sanya shi koma cewa " yaushe zasu dawo?".

Hakan ma ba amsa mai kyau yake samu ba amma dai duk da haka baya gajiya da yin tambayar.

Ita Aishatu idan ya tambaye ta sai dai tayi ta masa kuka, a wurin mahaifin sa ka'dai yake samun amsar " baza su dawo ba Mu'een mune zamuje mu tarar da su"
Take sai yace
" To Alhaji Baba mu 'din yaushe zamuje da Ammee na?"

Idan yaron ya fa'di haka sai kawai Taheer yayi murmushi ya shafa kansa yace koda wani lokaci Babana, tafiyar ba'a mata shiri kaji".

Sai ya 'dage kansa da nufin yaji.
Sosai jikin Taheer yake yin sanyi aduk lokacin da sukayi irin haka da Mu'een.


A hankali ma sai Allah ya taimake shi yaron ya rage tambayar sa sai dai kuma shiru-shirun nasa sam baya jin da'din sa.


Hutu ya shirya musu zuwa a Dubai... wai ko zasu d'an nutsu idan sun kauce duk kuwa da cewa ya kasa rabata da zubda hawaye da tunani amma sosai yake iya matu'kar 'ko'karin sa akan hakan.


Zuwan su Dubai ne ya sanya ta 'dan warware domin kuwa sam baya bari su zauna wuri guda kullum fita suke yi suna yawo suna zaga gari har na tsawon sati biyu, daga nan ne suka wuce Umrah....inda anan Taheer ya dinga kaiwa kukan sa wurin mahallici kan lamarin matar tasa, bai gushe ba yana addu'ah cikin kowacce sallahr sa har suka gama Umrah suka dawo gida.


Alhamdulillah babu laifi, domin kuwa yanzun abubuwan nata da sau'ki ta 'dan rage yawan tunanin..sai dai Mu'een 'din sa ne har yanzu bai dawo dai-dai ba, zama shiru ya riga ya zama halayyar sa.







*Kai ni 'din nan kamar azane ni ko* πŸ₯΄ *Gaskiya bana kyautawa, amma a 'kara ha'kuri dai plz na kasa settling ne wallahi*






_Comment_
_Vote_
_Share_





~Taku mai 'kaunar ku har kullum~ πŸ‘‡πŸΌ



*Salmerh ce*😍
[12/20/2019, 1:13 PM] 🌸Salmerh🌸: πŸ’• *NOORUL* πŸ’•
(Haske nah)



By
*Salmerh MD*



*Wattpad @*
*Serlmerh-md*



πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
πŸ’«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*



πŸ‘πŸ»~JUMMA'AT MUBARAKH TO ALL MUSLIM UMMAH~ πŸ‘πŸ»


*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*



πŸ…Ώ *17*



Amma duk da haka sosai yake yiwa mahallici godiya domin sai yanzu ya gama fahimtar cewa farin cikin mace cikin gida shine farin cikin kowa a gidan...cuz lokacin da Ammee ke cikin wancan yanayin kwata-kwata shi kansa baya samun matsuwar kansa akoda wani lokaci balle kuma 'dan yaro Mu'een.


Yanzun kuwa da abubuwa suka fara dai-daita banda godewa Allah babu abinda yakeyi....6angaren Mu'een 'din bai dame shi sosai ba domin kuwa yasan shi yaro ne har yanzun akwai yiyuwar canzawan sa idan yana 'kara girma in kuma Allah yayi nufin hakan shiyasa kawai ya 'kyale sa.




*****
Bayan sati uku da dawowar su daga Dubai...... a ranar wata Monday lokacin Mu'een na makaranta shi kuma Alhaji ya fita, kwance take kan kujera tana nazari kan rayuwa, sosai tayi nisa cikin tunanin marigayan dangin ta mahaifin ta, har anata danna bell na 'kofa amma sam bataji ba, sai da 'karan ya yawaita ne kafin tayi firgigi ta tashi zaune.
Sam sai taji bata son mi'kewan ma balle bu'de 'kofar amma haka ta daure ta tashi ta isa gurin 'kofan ta bu'de a hankali.


Baya ta 'dan matsa ganin wanda ke tsaye daga wajen, cikin murmushin ya'ke tace dashi" welcome Barrister ".


Bai furta mata amsar komai ba sai ya mayar mata da martanin murmushi madadin amsar maganar ta.


Hanya ta bashi domin ya shigo gami da yi masa iso .


Ta'aziya ya 'kara yi mata harda 'dan guntuwar nasihar sa a 'dan 'kagauce ganin 'yar ramar dake tare da ita, wanda har yasa 'dan guntun hawayen da suka ma'kale mata suka gangaro.


Amma sai tayi saurin sharesu saboda ba taso a kullum ta kasance cikin kuka....takaddu sun kai guda tara Barrister ya mi'ko mata gami da fa'din ta saka hannu akai akwai abinda za'a yi da shi ne kuma urgent ake bu'katar hakan.


Yanda yayi mata maganar sai ya sanya ta ba tare da tayi tunanin komai ba ta 'kar6i takaddun da biron da ya bata ta bisu 'daya bayan 'daya duk tayi signing a 'kasan su.
Yayin da Barrister ya tsura mata idanun sa wanda suke 'kulu-'kulu kamar zai cinye hannun ta yana gani da tabbatar wa idanun sa abinda ke shirin faruwa, be ta6a zaton abin zai yi masa sau'ki har haka ba.


'Kayataccen murmuhin da ya bayyana kan fuskar sa bayan 'dage hannun ta daga kan takaddar har ya 'danso ya 'daure mata kai amma sai bata sa a kaba saboda tunowa da tayi cewa yace ana da bu'kata ne urgent, bata damu ba duk da kuwa bai sanar da ita abinda ke faruwa ba, sai kawai tace dashi..." idan abin damuwa ne ko in 'kira Taheer yazo 'kila ya taimaka shima ko".

Da sauri Barrister yace " ah no karki damu ba sai yazo ba, zamuyi waya da shi kawai ba komai...".
Yana maganar ne yana tattara kan takaddun waje guda bayan hakan bai ko 'kara second biyar ba ya zuba su cikin jakar da yazo da ita yayi mata sallama ya 'kara gaba abinsa.


Koda Taheer ya dawo sai ta sanar dashi yanda sukayi da Barrister 'din da safe shi kam yaso yaji ko menene amma sai itama tace bata san me ya faru ba, sa hannun ta ka'dai ya bu'kata.



Bata tashi sanin babban kuskuren da ta aikata ba har se da aka shafe kusan watanni uku wayar Barrister bata tafiya, domin tun a ranar da Taheer ya dawo tayi masa bayani sai ya dinga gwada 'kiran sa da zummar yaji abinda ke faruwa amma wayar sa tun ranar ta daina shiga.


Wasa suka 'dauki abin dan haka suka cigaba da bibiyan layin nasa batare da sun tuntu6i office 'dinsa ko mazaunin sa ba, amma gaba 'daya abin yaci tura har aka shafe 3month da 'doriya basu sake ji daga garesa ba.
Abin haushin ma shine ko cikakken ainahin sunan sa basu sani ba balle akaiga zancen binciken gidan sa.....duk da haka Taheer yaso yabibiyi lamarin bayan ya fahimci abinda ya faru ko dan 'kwato hakkin matar sa ma amma Ammee ta hanasa domin tasan yin hakan dai-dai yake da sanya rayuwar sa cikin garari, irin wannan badakalar shiri babba take bu'kata domin in kayi wasa ma har sai rai yabi, ita kuwa shi ka'dai gareta a yanzun, shine ka'dai ya rage mata sai Allahn ta da 'dan ta kuma bata son ta rasa shi....dan haka sai tace dashi " ka barshi yaje kawai idan da niyya yayi hakan ai Allah yana sane kuma yana ganin komai....shi kansa yasan wani bai cin hakkin wani ya zauna lafiya dole sai yaga iyakar sa, balle shi da ya ha'da har da cin amana, ba'karamin yadda Daddy yayi dashi ba amma kalli halin 'dan Adam...... dan haka ka 'kyale shi yaje kawai Tahir idan da gangan yayi Allah zai mana maganin sa.....idan kuwa ba da gangan bane ni na yafe masa duniya lahira kuma har cikin zuciya ta, bashi da haufi akan hakan, da'din abin ma shine idan babu nan to akwai can...inda bawa bai isa ya 6oyewa kowa ba kamar yadda bai isa ya 6oye laifukan sa ba...to me yasa zamu 'daga hankalin mu?
wanda suka rage a hannuna ma Allah yasa musu albarka...let him be ai duniya ce girma gareta......"!


Sosai ya gamsu da bayanin ta kuma yayi na'am da shi amma hakan bai hana shi bincike kan Barristern ba, har sai da ya gano dukkan bayanan dake tattare da shi har inda ya koma a halin yanzun.
Tsananin mamaki yayi sosai da jin hakan domin a zahiri zaka fahimci manufar sa ta guduwa ya bar garin Kano adai-dai wannan lokacin.


Bai yi 'kasa a gwiwa ba gurin burin son zaman sirri da Barristern dan yana so ya nuna masa muhimmancin gujewa haramun da kuma illar cin dukiyar maraya cin amana da kuma illar biyewa zuciya......shi ka'dai ya shirya hakan cikin ransa batare da kowa ya sani ba, amma sai ya bari a kan cewa sai ya samu lokaci tukunna zaije masa da kansa su tattauna.


Kwatsam kafin faruwar hakan sai yaci karo da wani mummunan tashin hankalin da ya kusan zautar dashi.
Wai shi ake tuhuma da satan fuel na kusan 80million....meze yi dashi?
Abinda ya tambayi kansa kenan da yaji batun.


Sosai abin ya ta6a ransa bai ta6a tunanin irin wannan zargin zai hau kansa ba kuma shi ka'dai ake tuhuma batare da kowa ba, abin ya 'daure masa kai sosai.


Ita kanta Aishatu sai da ta kusan sumewa dan tashin hankali, kuka take yi har tana 'ko'karin kauce hanya cikin maganganun ta dan ganin kamar iftila'in na neman sufi 'karfin su ma, basu gama da wancan ba ga wannan kuma, gaba 'daya tashin hankalin ta sai ya ninka na 6acewan Barrister ta rasa yadda zatayi da ranta.


Duk ya fita shiga damuwa amma hakan bai hana shi kwantar mata da hankali gami da nasiha akan hakan ba.

Rana tsaka tana ji tana gani aka zo har cikin gidan sa gaban iyalan sa aka sanya masa Handcuff sannan aka tusa 'keyar sa zuwa ofishin 'yan sanda duk da kuka magiya da ro'kon da take yi musu bai hanasu tafiya da shi ba.


Mafita ko guda 'daya be iya yazo kanta ba banda aikin kuka da takeyi babu komai, domin ko sau 'daya basu ta6a bari ta gana da shi ba tsaro sosai akayi masa wanda hakan ya sanya ta shiga cikin mummunan yanayi.


Kullum yanda taje haka take dawowa gaba 'daya ta fita hayyacin ta, sarai tasan Taheer bai ci ku'din kowa ba domin baya yin abu batare da shawarar iyalan sa ba kuma ma ita bataga a inda yaci ku'di har Naira Million tamanin a gidan ba....taya za'ace shi ya 'dauka.


Har akaci sati guda Taheer na kulle ko bailing 'din sa bata iya tayi ba sun ma hana ta bailing nasa gaba 'daya.


Ran kwana na tara ne Ja'afar ya 'kirata domin baiji daga 'dan uwan nasa a kaf 'din satin ba, sanadin hakane ya 'kira ta inda anan cikin kuka ta samu tayi masa bayanin abinda ke faruwa.


A rikice shima yake mata tambayar " kina nufin sati gudan Taheer na kulle amma ban sani ba?...haba dan Allah me yasa baki 'kira ni tuntuni kin sanar dani ba?"


Kuka taci gaba da yi batare da ta bashi amsar tambayar sa ba dan haka sai ya kashe wayar.


Aranar ko kwana beyi ba ya dira garin kano rana tsaka dayake Allah ya taimake shi tun safiya ya 'kira ta bai 'kira a 'kurarren lokaci ba.


Sau'kar sa keda wuya kuwa ya dira gidan a hargitse...inda yana shiga parlourn ya samu Mu'een zaune cikin damuwa, ga ta ita kuma zaune ta kwantar da kant jikin kujera a hakan bacci ya 'dauke ta wanda tashin farko zaka fahimci cewa shima baccin ba'a nutse take yinsa ba, ba itan ba ba yaron ba hatta gidan gaba 'daya idan ka kalla zaka san cewa masu shi na cikin tashin hankali kowa yayi jugum har zaka rasa gane waye cikin su yafi shiga damuwa...domin shi ma yaron ya damu da rashin mahaifin nasa cuz ba haka suka saba ba ya saba ganin sa kullun agida amma yanzu babu shi kuma basa waya dashi ko Landline yaji tana 'kara ya kanje da sauri ya jira zuwan Amminsa a wurin da tunanin ko mahaifin sa ne, in kuwa tazo ta 'dauki 'kiran sai ya bita da idanu gami da zuba kunnuwa ko zaiji muryar mahaifin sa amma baya jin hakan.


Ga yawan kukan Ammin sa dake 'kara 'daga masa hankali shima sau da dama tayata yake yi suyi ta kukan tare shiyasa duk suka fita hayyacin su.


Makaranta kuwa itama babu labarin ta, domin tun ranar da aka kama Baban sa bai sake zuwa ba.


Shiyasa duk suka zama wasu iri dasu gwanin tausayi, kallo 'daya zakayi musu ka fahimci yanayin da suke ciki.

Mu'een na ganin Ja'afar a tsaye ya taso da sanyin jiki ya iso gaban shi, Ja'afar sai ya 'dago shi sama kafin yace wani abu ma Mu'een ya riga shi da fa'din " Uncle kaga Ammina kullum kuka takeyi kuma Alhaji Baba baya nan kullum bana ganin sa agida bansan inda yaje ba inaso in ganshi Uncle".


Kwantar da kan Mu'een yayi kan kafa'dar sa gami da sau'ke ajiyan zuciya, sosai zuciyar sa ta karye da jin furucin yaron.


Da kansa ya shiga ya watsa masa ruwa a extra room dake gidan dan ganin yana bu'katar hakan sannan ya fito da shi yace yaje ya 'dauko kayan sa ya sanya masa sai suje gurin Alhaji Baban.

Mu'een najin haka ya tafi da gudu da yake yana da wayo, da idanu kawai Ammin sa ta raka shi batare da tayi yun'kurin motsawa ba, har yaje ya 'dauko kayan wandon jeans da riga ya sake koma 'dakin " Uncle gashi ka samin da sauri muje wurin Alhaji Baba"
Yayi maganar fuskar sa cike da annurin zaiga Alhaji Baba.

Palour suka dawo bayan ya shirya shi wanda tana ganin su tare sai ta mi'ke tsaye tare da fa'din " Ja'afar please help me....Allah sharri suke yi masa kuma sun'ki saurarata wallahi Taheer bai saci ku'din kowa ba".

Sai yace
" Kunyi magana da shi ne?"
Tace
" ah ah sun hanamu ganin sa ma"

Tambayar Division 'din da yake yayi ta gaya masa sai yace to ta nutsu ta 'dauko masa key su je yanzu ko za'a dace su ganshi"


Da sauri ta wuce ciki ta duba key 'din da rawar jiki domin ita rabon ta da hawa mota tafi 3weeks tun ma kafin faruwar lamarin kuma koda abin ya faru ma idan zasuje Division 'din da aka kulle shin da taxi suke zuwa bata ko sauraran motar gida.


Shine ya jasu har Division 'din, inda aka kai ruwa rana kafin ya samu suka ganshi da dokar mintina biyar cif.


Ganin Tahir sai da ya kusan sanya shi kuka amma wannan dauriyar da ya ara ya yafawa zuciya da fuskar sa tun a gida gaban Mu'een yake so ta 'kara rufa masa asiri, yaso kar ya zubda hawaye amma ganin yanayin da 'dan uwan nasa yake ciki ka'dai ma abin ya ta6ashi sosai domin ba kyan gani, gaba 'daya ya rame yayi ba'ki ya fita a hayyacin sa, rashin 'kibar daya ke da ita ita ta 'kara taimakawa wajen bawa tsufa shiga yanayin halittar sa, gaba 'daya ya zama tamkar wani dattijon mutun ga wani uban handcuff da aka maka mai a hannu.


Mu'een na ganin sa ya fara murna yana fa'din " Alhaji Baba....Alhaji Baba kazo mu tafi gida kullum Ammi kuka take yi bata bacci..."


Kafin ya kai aya sai Taheer ya juya baya dan baya son yaron yaga hawayen da ya sau'ko masa...shi kuwa Mu'een sam ya'ki zama jikin Uncle Ja'afar 'din sai da ya 'kwaci jikin sa yaje ya rungume Alhaji Baban yace " Kaima kana kuka ko Alhaji Baba...Uncle kace yayi shiru mu tafi gida, Alhaji Baba waye ya saka maka wannan abin?"

Yayi tambayar gami da shafo handcuff 'din dake hannun sa......jikin sa Alhaji Baba ya jawo shi sosai ya rungume shi yana 'kara sau'kar da wasu hawayen masu zafi.


Ammi ma dake gefe kukan takeyi yayin da Taheer yayi 'karfin halin ri'ke nasa hawayen bai bari sun sau'ko ba amma kallo 'daya zakayi masa ka fahimci cewa baya cikin mood mai da'di musamman idan kayi duba da yanda idanun wansa suka yi jajir......a hankali Taheer yace " Ja'afar ban san me zance kan lamarin nan ba dan bansan meke shirin faruwa dani ba kwata-kwata, amma dai inada tabbacin kai da Aishatu kunsan cewa ni bazan ta6a iya aikata irin wannan aikin ba har abada ko?"

Kai Ja'afar ya 'dage gami da dafa kafa'dar sa yana shirin magana sai Taheer ya riga da sake fa'din " inaso koda mutuwa nayi sanadin hakan dan Allah kuyi 'ko'karin fahimtar da Muhammad cewa mahaifin sa bashi da laifi kan hakan, ni ban ta6a cin haramun ba, ban saci ku'din kowa ba... 'kaddara ce kawai ta hau kaina kuma na kar6e ta da hannun bibbiyu matsayina na bawan Allah...."


Taran shi Ja'afar yayi da fa'din " ka daina fa'din haka dan Allah Alhaji insha Allahu komai zaizo da sau'ki, mu miye amfanin mu? Zamu kai 'karar duk wanda ya zalince ka wurin mahallici da izinin sa kuma insha Allahu zamuyi nasara".


Bai ce dashi komai ba sai kawai ya 'dago kansa ya kalli Ammi da tun 'dazun take tsaye tana aikin kuka.....suna ha'da idanu sai ta 'daga kanta sama da niyyan tabbatar masa da kalaman Ja'afar 'din wani kukan na sake 'kwace mata.


Saurin cire Mu'een yayi daga jikin sa ganin mai kula dashi dake tsaye gefe dasu na shirin tunkaro su, baya son ayi abinda zaisa Mu'een 'din kuka ko kuma yaji ba da'di tunda bai san meke faruwa ba, dan haka sai yayi saurin mi'kewa tare da fa'din " Mu'inuddeen kuje gida da Uncle ko..nima soon insha Allahu zanzo gidan kaji Babana".


Kafin yaron yayi magana har ya juya 'dan sandan ya rufa masa baya suka yi ciki.

Kuka Mu'een ya sanya yana 'kiran sunan shi sai Ja'afar yayi saurin 'daga shi sama yayi waje dashi, Ammi ma cikin sakakkiyar gwiwa tabiyo su abaya har wajen motar su, da 'kyar Ja'afar ya samu ya lallashe sa yayi shiru da al'kawarin zai kawo shi wurin Alhaji Baban gobe sannan yayi shiru.


Zugum sukayi cikin motar ko'ina shiru babu mai ko motsin kirki illah hannun Ja'afar dake tu'ki har suka je gida. Yana sau'ke su ya sake fita da motar dan neman mafita, domin baya jin zai iya barin 'dan uwan sa ya sake ko kwana 'daya ne cikin wannan halin balle nan da 3weeks da aka ce kafin aje kotu.


Wahala sosai yasha kafin ya samu ganin mutumin da yake tunanin zai taimaka musu shima 'din kuma sai ya so ya nuna akwai wani uzurin a gaban sa amma haka ya nace bai bar inda yake ba da 'kyar ya samu Commisionern ya saurare shi da 'kyar ya amince abada bailing sa bayan ya 'kira wani da bai san ko wanene ba amma yana kyautata zaton ma'aikatar da Taheer 'din ke aiki ya 'kira amma da shara'din daga yau 'din har ranar da za'a shiga kotu kullum zai je ya sa hannu domin a tabbatar da cewa yana kusa, dai-dai da rana 'daya idan ya sa6a lokaci ko rana zasu yi abinda suke ganin dai-dai me agare su.







_Comment_
_Vote_
_Share_







*Salmerh ce* 😍,


[12/22/2019, 3:18

Please Login or Register in order to submit comment