Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inda ya ha'da har da hancin ta ya rufe gam.



Jasmine kam nan take numfashin ta ya tsaya cak a wurin, duk da haka Sani bai fasa abinda yake yi ba, bai ma san da faruwar hakan ba sam.


Sani ya fahimci bata numfashi ne lokacin da ya ga alamar bata motsi, wanda hakan ne ya sanya shi 'daga hannun sa saman bakin ta.


Ko 'dar baiji ba balle yaga rashin dacewar abinda ya aikata, hannun sa dake jikin ta ya cire duk jini ya bata hannun, amm bai damu ba sai yayi saurin gogewa a jikin sa ya fara 'ko'karin cire belt 'din sa 'kato dashi ko kunya baya ji balle tsoron Allah, bansani ba ko ya manta cewar Baby Jas ne ba wata daban ba.



Duk kuwa abinda ke faruwa babu wanda ya lura da shi, domin hanyar ba wani cika binta akayi ba, by-pass ne da 'dai-'dai kun motoci ne ke bin ta, kuma ma yaushe kai da ke da naka uzurin yaushe zaka tsaya karantar faruwar wani abin da bai shafeka ba, abin ma cikin mota.


Shiyasa ko motocin dake wulgawan ma da gudunsu suke zuwa su wuce kamar yanda suka taho, gashi ha'di da ba'kin glashin da motar ke da shi wanda ya 'kara bada babbar gudummawa wajen rashin ganin haukar da sani ke aikatawa cikin motar.


Yana 'ko'karin 6alle belt 'din nasa ne sai yaji 'kara daga bayan sa, sai hakan ya matu'kar gigita shi sosai abinku da marar gaskiya.


A tsorace ya sa hannu kan key 'din motar ya tada da niyyan barin wurin duk da bai fahimci takamamman abinda ke faruwa ba, amma hakan bai hana shi zaburar da motar cikin gaggawa ba.



Wata mota dake 'ko'karin tsaya wa daga gaban sa ganin abinda ya farun shi kuma Sani a gigice ya tafi da 'karfi sai suka gwabza uban karo mai firgitarwa.


Take motar Sani ta gangara gefen hanya gaba 'daya sai ya kasa controlling 'din ta, kafin ma ya nutsu ya dakatar da motar har ta isa ta bugi wani bangon sabon ginin manyan shaguna da a keyi ya rubzo kan motar......nan take labari yasha bam-bam.


Domin kuwa tun daga lokacin Sani bai 'kara sanin abinda ke faruwa dashi ba.



Salati kawai tsirarun jama'ar dake wurin ke yi, yayin da wasu harda 'dora hannu sukayi aka, domin abin babu kyan gani.

Motar da su Sani ke ciki bazaka ta6a tunanin za'a rayu a cikin ta ba tsabar yanda yayi.



Take an gwabza accident har kala biyu wanda na farko an yishi ne sanadin mai tura baro mota ta ka'de shi, shi kam ma nan take bai ko shura ba ya amsa 'kiran Allah, dan kuwa duk yawancin masu bin by-pass 'din basa shigan ta a hankali, da gudun su suke tafiya saboda samun sarari yayin da wasu daga cikin su uzururruka ke sasu yin gudun.


Hatsari na biyun shine ya faru ta sanadin rikicewar Sani sakamakon rashin gaskiya da kuma jin 'karar hatsari na farkon sai gashi mota tayi kaca-kaca 'kar'kashin gini bazaka ta6a zaton an rayu cikin motar ba, shi kansa mai ginin ba 'karamin tafka asara yayi ba.

Wanda suka gwabza da Sani ne ka'dai nashi da 'dan sau'ki domin kuwa gaban motar ne ka'dai ya lalace da yake shi cikin hayyacin sa yake so sai yayi saurin yin baya lokacin da suka yi karon, shi kuma Sani garin kaucewa ne ya karkace yayi gefen hanya, wancan bawan Allah kuwa da ya ka'de mai baro motar sa bata samu ko 'kwarzane ba amma azumi sittin da ya hau kansa matsayin sa na musulmi ma ka'dai ya ishe shi fargaba.


Dr. Safwan abokin Deen ne ke wucewa shima da shirin sa na zuwa aiki cuz aikin rana yake yi a lokacin, sai shima yaja ya tsaya ganin faruwar lamarin, wanda ganin mutane an taru da 'dan yawane ya sashi shima yayi parking domin ganewa idanun sa.


Har ya iso 'din kuwa babu wanda ya kai ko da farcen sa kan wanda aka ka'de 'din, tsayawa sukayi suna kallon yanda jinin sa ke malala a 'kasa kamar ba mutun ba.

Dr. Safwan na isowa ya kutsa tsakankanin mutanen wanda shine ya duba wanda aka ka'de 'din yaga tuni rai yayi halin sa sai ya jijjiga kansa tare da fa'di wa wa'danda suke wurin.


Kafin wasu 'yan mintina guri ya sake cika ma'kil da jama'ah na ban mamaki, inda wasu suka maida hankali kan motar da gini ya zubzowa.


Dr. Safwan kam shirin komawa mota yake yi cuz bai lura da 'dayan motar ba, jin hayaniyar mutane agurin ne ya sashi waigowa yaga mai suke wa hayaniyar.

Caraf sai idanun sa suka yi arba da motar Deen abokin sa wanda matu'kar yana gari to da ita yake zuwa ko'ina idan zashi.


Tsinkewa zuciyar Dr.Safwan tayi sai yayi hanzarin tafiya da gudu izuwa wurin motar ya tarar da mutanen dake wurin suna hayaniyar ta inda zasu fara taimakon mai motar.


Sanin da Dr. Safwan yayi cewa Deen baya gari ne ya sanya shi tunanin cewa Noor ce cikin motar sai da ya isa daf kafin ya ganewa idanun sa kasancewar tuni glashin ya tarwatse.


" Innalillahi Jasmine". ya furta a fili tare da 'ko'karin taimaka musu.



Da taimakon Dr. Safwan aka fitar da su duk daga cikin motar inda ya sanar da jama'ar gurin cewa 'yar sa ce tare da nuna musu I.D card 'din sa na aiki da addreshin asbitin da yake aikin saboda kada su zarge shi.


Cikin motar sa aka sanya Sani, yayin da shi da kansa ya rungumo Jasmine ya isa motar da ita, wani dake gurin ya ro'ka akan ya taimake ya ja su zuwa asbiti sai yace bai iya mota ba.

Wani aka nemo ya jasu zuwa asbitin cuz Dr. Safwan baya jin zai iya tu'ki a dai-dai wannan lokacin.



Dukkan su Emergency ward akayi da su inda aka rufu akansu ana basu taimakon gaggawa.


Har alokacin kuwa cikin su babu wanda ya farfa'do balle su san halin da ake ciki.


Dr. Safwan da kansa ya duba Jas yayin da wani likitan ya duba Sani.


Sosai suka yi 'ko'kari wajen ganin sun shawo kan lamarin, cikin sa'a kuwa komai ya dai-dai ta wanda sai a lokacin hankalin Dr. Safwan ya kwanta ganin cewa dukkan su suna da sauran numfashi.


Sani ne dai sai aka sanya masa oxygen, ga kuma mummunan raunin da hannun sa yayi harma suna tunanin sai an yanke hannun gaba 'daya.


Ajiyan zuciya Dr.Safwan yayi jin abinda ya faru da Sani sai yace " Allah ya bashi lafiya"
Nan yayi musu bayanin cewa ai 'yar Dr Mu'een ne da drivern gidan sa, yace ga dukkan alamu daga makaranta ya 'dakko ta sai hakan ya faru"


Likitoci uku dake tare da shi 'din sosai suka tausaya tare da 'kara bada himma sosai wajen kula da su.






*****

Noor dake can gida kuwa zuwa yanzun har ta fara gajiya da duba agogo, har ta gama shirin ta tayi sallah amma har yanzu shiru, lokacin da ta 'daya ta gota har da rabi ne sai ta ji wani tu'ku'kin ba'kin ciki ya 'karu mata akan na baya.


Yanzun kam tana ganin cewa rainin hankalin Sanin da gangan ya keyi, in ba haka me ya tsaida su har wannan lokacin basu dawo ba.


Tayi tunanin 'kiran sa amma kuma bata 'kaunar sake ganin wayar tama a idanun ta, tsakin da ta ringa ja yafi cikin container daga 'karshe sai ta fito parlour, amma instead ta 'dauki wayar tata ta 'kirashi " ah ah.....sai ta kauda kai daga kallon wayar ma gaba 'daya ta zarce waje.


Wurin Mai gadi ta nufa tace da shi " har yanzu Sani basu dawo bane wai?"


"Ehh Hajiya, gaskiya basu dawo ba nima ina mamaki yau 'din"
Yayi maganar cikin bata girma matsayin ta na matar ubangidan sa.


" k'ira min shi mana please Bala kaji ina suka tsaya"
Tace dashi cikin dakewa tare da 6oye damuwar ta.


Batare da 6ata lokaci ba mai gadi ya 'kira layin Sani amma switch off aka ce dashi " Hajiya wayar a kashe".
Ya fa'da tare da raba wayar da kunnan sa.

Noor sai tace
" Sake gwadawa mana dan Allah ba mamaki matsalar network ne"

Koda ya gwada 'din kuwa still baya tafiya wanda wannan karon kam ba sai ya bu'di baki yayi mata 'karin bayani ba, kasancewar a speaker ya sa wayar.


'Dan 'karamin tsaki Noor ta ja tare da yarfe hannu sannan ta juya ta koma ciki tana mita cikin ranta.


Tana shigan ta sake jiyo rurin wayar ta karo na abinda bazata iya tunawa ba.


Zaton ta ko Sani ne ya 'kira dan haka sai taje inda take jiyo rurin wayar ta kalla, ganin sunan wanda ke 'kira ne ya sanya ta ta6e baki tare da wucewa abinta ciki.



Deen kam tun safiyar yau daya gaisa da Jas bai sake jin natsuwa ba wanda hakan ya sanya shi yake zaune a office ko mutun 'daya bai iya ya duba ba.


Bai san dalilin da ya sanya ta 'kin 'daga wayar sa ba wanda da farko ya zaci ko bata kusa ne, amma daga baya da ya 'kara 'kira bayan kusan hour guda still yaga batayi picking ba, daga nan ne ya fahimci cewa da gangan ta'ki 'dagawa.


Dan haka sai ya cigaba da 'kira tare da tura mata text har guda uku amma shiru ba replay sannan 'kiran sa har alokacin bai samu response ba.


Ganin haka ne yayi tunanin ko de ba lafiya ba, dan haka sai ya 'kira mai gadi ya tambaye shi matar sa tatafi makaranta ne sai maigadi yace "a ah tana ciki"


Ro'kon sa yayi akan ya duba masa ko ba lafiya ba dan yata 'kiran layin ta amma ba'a 'dagawa.


Wannan abin ya faru ne bayan fitar Sani izuwa 'dauko Jasmine daga makaranta.......koda mai gadi yaje mata da batun ma 'kin amsan wayar tayi tace dashi ita lafiyar ta 'kalau wayar tata ce bata san inda ta jefa ba.


Mai gadi na 'ko'karin juyawa ya fita ilsai ga 'karan wayar tata daga kan kujera, kallon ta yayi ya kuma kalli inda wayar take......Noor kuwa kauda kai tayi tamkar bata san meke faruwa ba kawai ta koma bedroom abinta.


Fita mai gadi yayi wanda tun ma kafin ya gama barin cikin parlourn wayar sa ta sake ruri.


'Dauka yayi yace " yalla6ai tana nan lafiya...wai wayar tata ce bata gani ba amma yanzu ta ganta".
Ya fa'di hakan ne da tunanin babu mamaki yanzu ta 'dauki 'kiran.


Godiya Deen yayi masa tare da kashe wayar sa, bai sake 'kiran maigadi ba kawai yaci gaba da 'kiran nata wayar amma har yanzun dai bata canza zani ba.


Barin office 'din yayi kawai ya koma gida ya fara shirin tahowa Bauchi, abokin sa da ke aiki a airport ya sanya yayi masa booking cikin sa'a ma sai ya samu 'karfe 'daya da rabi jirgin zai tashi, sosai yayi murna da hakan kuwa wanda kafin kace kwabo har ya isa filin jirgin.



'Karfe 'daya da ashirin yana cikin jirgin har ma ya fara haramar kashe wayar sa, sai ga 'kiran Dr. Safwan ya danno.


Kamar ba zai 'daga ba sai kuma dai ya 'daga dan sun 'dan kwana biyu basu gaisa ba.


Jin abinda ya sami 'yar sa daga bakin Dr. Safwan ne ya sanya gumi karyo masa nan take ha'di da bugun zuciya.......a fili ya furta salati tare da tambayar yanayin jikin.


Dr yace masa da sau'ki sai godiyan Allah domin nata abin bai yi tsanani ba kamar na Sani"


Cikin ransa yayi hamdala tare da tambayar " Noor ko tana wajen ne?"


Sai Safwan yace " ah ah, bama ya tunanin tasan abinda ke faruwa"


Deen bai bi ta kan hakan ba sai ya tabbatar masa da cewa ai shima yanzu haka yana cikin jirgi zai sau'ka nan bada da'dewa ba, ha'di da yimasa godiyan kulawa da yayi da su.


"Haba bakomai kar kadamu da wannan please"
Safwan ya fa'di tare da tsinke wayar shi.



Tun lokacin hankalin Deen ya kasu gida biyu har ji yake tamkar jirgin ma ba ya sauri, duk kuwa da cewa shi da kansa ya san da bambamci in da ace mota ce.
Amma yanda ya 'kagu ya gansa gaban iyalin nasa ya sanya har yake raina tafiya irin ta jirgi.



Daga 'karshe rintse idanu yayi ya kwantar da kansa yana addu'an Allah ya takaita masa Allah ya bawa Babyn sa lafiya mai 'dorewa.







*Sani ya aikoni yace a sanar da ku cewa kunnuwan sa a toshe suke* 🎧 *haka ma idanun sa😎, dan haka* *ba zaiji komai ba kamar yadda ba zai gani da idanun sa* *ba.*







_Comment_
_Vote_
_Share_








*Salmerhn ku ce*
[11/24/2019, 1:09 PM] 🌸Salmerh🌸: πŸ’• *NOORUL* πŸ’•
(Haske nah)



By
*Salmerh MD*



*Wattpad @*
*Serlmerh-md*



πŸ’« *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
πŸ’«
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*



_Godiya mara iyaka gareku 'yan uwa na, sosai naji da'din addu'o'in ku gare ni....Allahu ya saka muku da mafificin alkhairi, baiwa_ _da rahamar sa._ 😍
*_Fatan alkhairi masoyana Allahu ya bar 'kauna_ 🀝*



*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*



πŸ…Ώ *10*



Iya k'ololuwar tashin hankali babu inda na Noorul bai kai ba a ranar, amma taurin kanta da kuma haushin abinda ta gani ya sanya ta ta tsani sake 'daga wayar ta ma balle har ta 'kira Deen kan batun Jasmine 'din.


Haka ta daure ta sake 'kara mintina kusan talatin akai batare da ta kira Deen 'din.
Ga mamakin ta kuwa har a lokacin shiru babu labarin su.
Wnda zuwa lokacin kuwa duk wani dauriyar ta 'karfin su ya tafi, wani sabon kuka take jin yake taso mata, ita kanta tausayin kanta ta keji, da wanne zataji?
Da damuwar miji ko kuwa damuwar Sani?.


'Dan guntun hawayen da ya zubo mata tasa hannu ta goge shi da bayan hannun ta sannan ta mi'ke cikin hanzari ta zari mayafin ta, cikin jakar ta laluba ta zaro 2k sannan ta fita bayan ta rufe jikin ta da mayafin.


Ko da ta isa parlourn ma ko kallon inda wayar tata take bata yi ba, kawar da kanta tayi gefe ta fice abinta cikin sauri.


Kafin ta fita sai da ta saka mai gadi ya sake 'kiran Sani, amma har yanzun dai wayar sa bata tafiya, sai tace ya 'kira mata Deen tana so tayi magana da shi.


Ko daya gwada layin Deen ma a lokacin bata shiga, dan already jirgin su ya lula sararin samaniya zuwa Bauchi.


Noor da bata san da batun zuwan nashi ba sai taji wani sabon takaici ya kama ta, idan zata biye abinda 'kirjin ta ke mata da ko tafiya taku biyar mai kyau bazata iya ba.


Amma rashin sanin halin da 'yar ta Jasmine take ciki a lokacin shi yafi komai 'daga mata hankali......fiye da komai.


Cikin 'karfin hali ta ringa karanto maso sauran layukan Deen 'din yana gwadawa amma ko 'daya babu wanda ya shiga.

Rintse idanu da karfi ji take kamar iska zai yi sama da ita tsaban yanda take jin kanta, bata bari mai gadi yaga hawayen daya sauko mata ba....sai da ta juya ta fuskanci gate kafin ta furta " nagode Bala".

Bai ma ji da kyua ba amma kuma kuma bata kuma maimaitawa ba ta cigaba da 'daga kafafun ta a hankali ta fara tafiya izuwa bakin gate 'din.

Tunanin 'kiran Saif take yi amma bata rike numbern ki ba kuma baya san komawa ciki a yanzun balle ta dubo cikin wayar ta.

Wani tunani ne ya sake zuwa ranta cak sai ta tsaya sai kuma ta juya ta kalli Bala tare da fa'din " Bala....dan Allah Sani bai ce.....da kai zai biya wani.... wuri ba kafin ya fita?"
Muryar ta na cracking tayi maganar kana ji ba sai an sanar da kai ba zaka fahimci cewa tana tare da matsanciyar damuwa.


Mai gadi jijjiga kansa yayi, shima 'din duk jikin sa yayi sanyi domin irin hakan bai ta6a faruwa ba iya zaman sa a gidan, ace har 'karfe biyu na shirin haurawa amma babu labarin mai tashi 'karfe sha biyu daga makaranta.....abin gaskiya bai yi ba kuma dole hankalin ta ya tashi matsayin ta na uwa.



Yana jijjiga kai 'din ya ke wannan tunanin.
Sai kuma ya 'kara da fadin ....." Babu inda yace min zashi Hajiya, ni Sani ma tunda nake da shi a gidan nan bai ta6a sanar dani inda zashi ba...."
Ya 'karashe maganar a hankali domin tuno wani abu da yayi cikin ransa
Sai yace "...sai dai kwanaki ya ta6a ce min daga nan in ya bar aiki Lagos zai wuce amma ban san yaushe yayi niyyan tafiyar ba gaskiya".


Take lumsassun idanun Noor suka bayyana 6aro- 6aro, bakin ta har na 6ari tace da Bala " Lagos dai?
Shine ya gaya ma hakan kuma?"


" Ehh 'kwarai kuwa Hajiya...shine da bakin sa ya sanar dani, sai dai bai har ga Allah bai gaya min ranar da zai yi tafiyar ba".
Ya bata amsa cikin tabbatar wa.


Noor ji tayi tamkar ta sa hannu aka tayi ihu...bata sake waiwayan Bala maigadi ba balle maganganun sa, tasa kai kawai tayi waje da sassarfa tana share hawaye.....a fili kamar zautacciya take fa'din " Allah ka sa hasashena ba gaskiya bane, Yah Allah ka dawo min da yarinya ta....ina son 'yata Yah ka taimake ni ka sada ni da ita".



Tafiya take tana zubda hawaye har ta 'karasa bakin titi ta tari 'dan adaidaita, shigewa kaia tayi bata ma ko tuna ta gaya masa inda zai kaita ba dan tsananin tashin hankalin da take ciki, sai da yayi tafiya mai 'dan tsayi kafin yace da ita " Hajiya ina muka dosa ne?".


Firgigi tayi cikin damuwa ta sanar da shi sunan makarantar.


Ciki-ciki yayi tsaki dan kuwa shi ba hanyar ya 'dauka ba sai da ya 'dan 'kara tafiya ka'dan kafin suka yi U- turn zuwa hanyan makarantar su Jasmine 'din.



Bata yi mamaki ba lokacin da ta isa bakin gate 'din makarantar ganin tamkar mutane basu ta6a rayuwa a wurin ba domin kuwa shiru arean gurin babu kowa, ita kanta tasan babu mamaki koda ta ga hakan, cuz almost 2hrs kenan da tashin 'daliban makarantar to kuwa wa zata samu?


Kafin ta shiga sai da ta juya ta kakkali gefe da gefen hanya wai ko zata hango motar dasu Sanin ke ciki amma ina, bata ga komai ba.


A hankali ta tura gate 'din ta shiga hango mai securites biyu da tayi zaune kan table ne ya sanya ta nufan inda suke, 'daya sai faman zuba surutu yake yayin da dayan kokuwa da da asuwaki cikin bakin sa.


Kafin ma ta 'karasa mai asuwakin ya taso ya iso gare ta yana fa'din barka da zuwa Hajiya....wani matsala ne?"
Yana gama fa'din hakan sai ya karkata kai gefe ya tufar da yawu.


Noor kai ta 'dage masa tare da fa'din " ehh Baba yarinya ta ce har yanzu bata koma gida ba....bansan meke faruwa ba wallahi kuma tunda 'karfe sha 'daya na turo driver 'daukan ta".


Batare da wani dogon tunani ba securityn yace " ya sunan ta?"

Noor da sauri ta bashi amsa da fa'din " Jasmine ake 'kiran ta amma sunan Aisha Muhammad Tahir, nursery 2 take Baba shekarun ta kuma biyar ne!"
Inda ta bashi amsar tambayar tasa hadda ma wanda bai tambaya ba.


Sai yanzun ne ya 'dan kai hannu bakin sa alamar nazari, sannan yace " ehh toh a gaskiya dai ban gane ta ba......amma kuma yara yau duk babu wanda ya zarce 'ka'ida anan....kusan kowa ya watse tun ma kafin mu shiga Sallah, dama manyan sun ne ma ke 'dan 6ata lokaci amma yaran kam gaskiya duk basu da'de anan ba, sai dai ko ki tuntu6i drivern 'kila wani uzuri ya ri'ke su....."


Tun ma kafin ya rufe bakin sa tace " Na shiga uku ni kam, Allah ka rufa min asiri?"
Tayi maganar ha'di da dafe 'kirji.


Kallon da security 'din yayi mata ne ya sanya ta sau'ke hannun data 'dora a kanta dama na 'kirjin gaba 'daya.


" Me ke faruwa ne wai?"
Ya sake tambayar ta da kulawa, sai tace " Numbern drivern baya tafiya tun 'dazu wallahi an ta gwadawa".


Da sauri ya furta " subhanallahi......ashsha, Allah dai yasa lafiya....."

Bata amsa ba sai kawai ta juya ta fita tana share hawaye yayin da Baba security ya cigaba da fa'din rayuwar yanzu sai a hankali komai ya lalace gaba 'daya, zu'katan mutane ya gur6ace da son abin duniya....Allah dai yasa ba salwantar musu da rayuwar yarinya wannan mutumin yayi ba".


Daga inda take cigaba da tafiya tana iya jiyo duk abinda security 'din ke fa'di, daf da zata bu'de gate 'din ta amsa da " Amin".
Sannan ta fice tana tunanin ashe ba ita ka'dai ke zargin hakan ba.....ita dai ro'kon ta Allah ya ku6utar mata da 'yar ta ya kuma bata kariya a duk inda take.

Maganar da Securityn yayi sai ya 'kara birkita mata lissafi.........what if sayar min da yarinya yayi!.
Da sauri ta jijjiga kanta ha'di da fa'din no no it can't be....Sani ba zai yi hakan ba.
Wani zuciyar yace da ita idan kuma Lagos 'din ya tafi da ita fa........innalillahi Allah ka rufa min asiri......Allah kar ka tabbatar min da duk wadan nan abubuwan, Allah ka dawo min da baby lafiya.

Ita ka'dai take tafiya tana sa'ka da warwar ta a zuci sam bata cikin natsuwar ta wani mota da ya auno ta da ka'dan yayi wulgi da ita sai yayi saurin jan birki, ita kam ma duk bata kulaba.
Masifa ya so balbale ta da shi amma ganin tana kuka ya sanya shi jan bakin sa yayi shiru....haka taui wucewar ta ta gaban motar batare da ta kula da yanayin kallon da yakeyi mata ba.

Mace har mace amma duk ta zama wata tamkar mahaukaciya.......jijjiga kansa yayi sannan yaja motar sa yayi gaba.


'Kin taran abin hawa tayi taci gaba da tafiya tana yi tana 'dan dube-dube wai ko zata hangi motar a wani wuri, lokaci-lokaci ta kan share hawayen dake gangaro mata, gaba 'daya ta fita hayyacin ta, wuni guda amma idan ka ganta sai kayi mamakin yanda duk ta birkice.


Bata ta6a tunanin akwai ranar da zata tsinci kanta cikin tagwayen damuwa irin wannan ba, bata ta6a tunanin haka ba, ashe farin cikin mu da ba'kin cikin mu duk suna faruwa ne daga yanayin rayuwar mu.


Yunwa take ji sosai domin tun safe bata saka komai cikin bakin ta ba, amma sam bama ta jin cin komai a wannan yanayin, damuwar ta Jasmine ne, burin ta ta ganta tasan halin da take ciki.


Har yanzun kuwa hawaye na cigaba da sa'k'ko mata wanda yake tilasta ta yawan goge shi, domin da saurin sa yake sau'kowa hakan yasa bata jinkirin 'daga hannun ta takai saman fuskar ta ha'di da ro'kon Allah ya ji'kan ta ya ta'kaita mata wannan abin, Allah ya bayyana mata 'yar ta gudan jinin ta.


Mafi yawan lokuta wasu dake wucewa na binta da kallon mamaki wanda wasun ma sam bata san suna yi ba, yayin da wa'dan su masu 'karfin gwiwar har na tsaya wa da nufin jin damuwar ta amma sai ta rasa mai zata ce dasu, kusan mutane uku suka yi mata magana amma mutun biyu daga ciki bata tanka su ba wucewa kawai take yi ta barsu tsaye a wurin, me zasu yi mata take tambayar kanta, idan har mai gadin makarantar ma bai san inda Jasmine tayi ba to waue zai iya sani banda Sani, hakan data sanya cikin ranta ne ya sanya ko kula su bata yi ba kuma bata damu da halin da zata shiga ba in dai saboda yar ta ne.

Mutum na farko cewa yayi " Allah ya kyauta yayin da na biyun ya bita da kallon tausayi kawai gami da jijjiga kansa inda cikin ransa ya furta " Allah ya rufa asiri".

Mata ta uku da tayi mata magana kuwa itace ta 'danyi sa'an samin amsa daga bakin ta inda tayi mata bayanin rashin ganin Jasmine 'din a takaice.

Cike da tausaya wa kuwa matar tace Allah sarki, Allah ya bayyana ta....amma kiyi ha'kuri ki koma gida kinji, ki sanar da mahaifin ta sai ku kai report wurin 'yan sanda, in akayi sa'a za'a dace tun da kinsan aikin su ne, amma ai hakan kam wahalar da kanki kawai zakiyi"


" Idan batada mahaifi fa".
Ta tambayi matar tana kallon cikin idanun ta wanda tsintar kanta kawai tayi da fadin hakan.


Sosai fuskar matar ya nuna alamun tsananin tausayawa tace " Allah sarki....idan na fahimce ki dai-dai kenan kina nufin marainiya ce ko....Allah ya bayyana miki ita, duk da haka

Please Login or Register in order to submit comment