Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baya jin zai iya samun natsuwa matu'kar ya bar sa haka kawao batare da ya idasa nufin sa akan su ba.

      Domin shi 6arna tun kafin ta faru ya kamata ka tareta ka kuma  gyara ta in ba haka ba matu'kar kayi kuskuren da ka bari 6arna ta faru to fa gyaruwan ta sai dai in Allah yaso...shiyasa yake ji is better yayi wa abin tufkar hanci in yaso suje can makarantar su cigaba da rayuwar su zuwa kammalawar su kafin aga yanda hali yayi.


Kujera ya samu ya zauna still murmushin kan fuskar sa bai gushe ba.

Gaishe shi Mu'een yayi ya amsa yana mai daidaita zaman sa da sakin fuska yace" Kawai cewa nayi bari in shigo in duba ka...kuma inaso za in gayama za'ayi gyara agidan amma kuma yau 'din bamu ha'du ba shiyasa nazo da kaina".
Yah Deen kai ya sosa cikin tsananin jin kunyar rashin zuwa gaishe su a ranar yace" Afuwan Alhaji wallahi ina kan hanya gaba 'daya ban nutsu bane shiyasa".
" No kar ka damu, ba gashi ni nazo ba".
Alhaji ya fa'di yana kallon yawan kayayyakin dake wajen a goge tas komai tsaf-tsaf.
Cikin ransa ya san ba wai haka kawai dan shiryawa ne yasa bai je can gidan ba, yana lura dashi tun faruwar lamarin sai ya 'danye 'kafafu, sau 'daya tak yake zuwa kuma shima 'din ba kallum ba, lambu kamma yafi 1week bai je ba.
   Duk da tuna hakan da Alhaji yayi amma bai damu ba cikin kulawa yace" Duka wa'dannan kayan tafiyar ne?"
" A a ba duk ba Alhaji, ai mafi yawan suna can Jigawa kawai ina so in kintsa su da kyau ne saboda 'kura".

Alhaji Baba kai ya jinjina cike da gamsuwa yace" Babu mamaki kafin ka dawo ma a kammala komai...ka ha'de sauran duk abin da kake bu'kata kar suzo su 6ace cikin shirgi".

" To Alhaji insha Allahu..zanyi kamar yadda kace".
Ya fa'di yana shafa kansa.

Mi'kewa Alhajin yayi ya nufi 'kofa yana fa'din" na wuce ni kam dama abinda ya kawo ni kenan".
Yah Deen sai yace
" To Allah ya tsare ya 'kara girma da arzi'ki".
Yayi maganar yana bin bayan Alhaji, har ya raka Alhajin ya tafi Yah Deen bai ko tunanin suturta jikin sa ba koda wasa ma hakan bai zo ransa ba abinka da sabo.

Har 'kofa ya raka shi amma bai fita ba daga nan ya juya ya koma ciki fuskar sa wasai na jin da'din ganin yanda Alhaji Baba ya sake dashi, ko ka'dan bai yi tunanin Alhaji Baba CID ya zo yi da kansa cikin gidan ba.

'Bangaren Alhaji Baba kuwa koda ya shiga motar sai da ya tsaya yayi 'dan tunani, shi dai ya san 'dan sa ba mazinaci bane kuma ya yarda dashi, ya san halin sa bai tara shirgin abokai kuma musamman marasa dalili shiyasa ma bai yi shayin barin sa ya zauna shika'dai ba, sai gashi koda yazo 'din ma bai tarar da kowa tare da shi ba..( u know Imrana ya tafi Kano shiyasa basu ha'du ba)...amma da yake ya san mutum mutum ne shiyasa ba zai ce ga ainahin halin sa ba, ba zai ce ga abinda yake aikatawa ba musamman ma da ya san ba'a shaidan mutun a duniyar mu ta yanzu.

Sannan zargi da sharri sunyi yawa ga hassada da 'kyashi, wani hakan kan same shi ne batare da ya aikata komai ba sai dai idan bincike yayi tsanani a tarar da shi bashi da laifin komai, yayin da wani zargin anayin sa da 'kamshi gaskiya domin idan an bincika wani lokacin akan tarar da gaskiya abin hakan yake faruwa ba sharri bane.

Zaiso Mu'een ya kasance cikin sahun mutane na farkon ba wa'danda zargin da ake yi musu yake kasancewa gaskiya ba, hakan yasa ya shirya kawo masa wannan ziyarar ta bazatan da kansa a kuma cikin lokacin da bai tsammaci ganin sa ba da tunanin ko zai ga wani abu da zai tabbatar masa da zargin sa amma baiga komai tare da shi ba.

Sosai ya samu nutsuwar zuciya sai dai duk da haka hankalin sa ya kasa kwanciya da batun  zuwan wata mace wurin yaron sa ba.

Wanda ya samu 'kwarin gwiwa daga wani 6angare na zuciyar sa cewa indai har shi da yake matsayin  mahaifi a gareshi zai zo wurin sa amma bai yi tunanin suturta jikin sa ba to inaga wata daban kuma?...sannan akwai possibilityn da za'a iya fassara ala'kar su zuwa wani abu daban musamman idan kayi la'akari da yadda duk da darajar da Allah yayi mata matsayin ta 'ya mace amma tayi watsi da shi ta iya tsefe idanu tun daga cikin garin Azare ta biyo shi har Shuwarin to me ze hana ta binsa can gidan sa a Dutse tunda yace makarantar su 'daya da ita.

Sannan ba sau 'daya aka ta6a ganin zuwan ta garin ba shima da idanun sa yaga zuwanta har sau biyu to meyasa take zuwa? me yake kawota wurin sa? Wace iriyar ala'ka ce da zai sa bazata ha'kura ta kama mutuncin kanta ba sai ta zo inda yake bacin ba hadda take kar6a wurin sa ba, wannan dalilin ka'dai ya sanya Alhaji Baba yake ji ba zai iya janye 'kudurin sa ba ba zai ta6a bari rayuwar 'dan sa ta lalace hakanan ba.


Key yayi wa motar ya tada ya nufi hanyar gida wanda yana isa ko fita daga motar ma bai yi ba ya 'dago wayar sa saboda a ganin sa yin haka ne ka'dai zai sama masa natsuwar zuciya.


Layin Uncle ja'afar ya 'kira inda bayan sun gama gaisuwa yace da shi" Fatan kasan Late Alhaji Hamza Ar'kila?"

" Nasan shi, amma ya rasu shekaru bakwai kenan da suka wuce..wani abu ne ya faru?".
Uncle J ya 'karashe maganar da jefawa Alhaji Baba tambayar haka.






Comment
Vote
Share





*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)


By
*Salmerh MD*

 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*


🅿 *43*

" Babu komai, amma inda hali ina so mu ha'du da kai nan da 1week.."

Take hankalin Uncle Ja'afar ya tashi sosai da jin hakan dan ya san dole akwai abinda ke faruwa da har ya sanya Alhaji fa'dar hakan, ta shin farko tunanin sa gun Kiddo ya tafi, cikin yanayin tashin hankali ya jefawa Alhaji tambayar " Akwai matsala ne? In akwai wani abin ka sanar da ni please hankali na ya tashi sosai".

Cikin salon son kwantar masa da hankali Alhaji Baba yayi murmushi sannan yace" Ka kwantar da hankalin ka Ja'afar ba komai bane ya faru face abin alkhairi..."
" Alkhairi kamar wani iri kenan Alhaji?"
Ya sake tambayar sa cikin rashin fahimta...yayin da Alhaji ya bashi amsa da fa'din" 'Dan ka ke neman auren 'yar Alhaji Hamzan shine na ga ya dace mu sanya baki a maganar, kuma bana so a 'dauki dogon lokaci...".

Bai kai ga rufe bakin sa ba ma, Uncle J cike da mamaki yace" 'Da na Alhaji..ban gane wa kake nufi ba".

" Kana da wani babban 'dan da kaga ya kai ya nemi aure ne banda Muhammad?"

Ido ya zaro da mamaki yace" Mu'een kuma..aure Alhaji? Karatun fa?"

Hannu Alhaji Baba ya 'daga tamkar Uncle J na gaban sa yake maganar cikin sanyin magana yace" Bar wannan batun tukunna idan mun ha'du ma tattauna, abu mai muhimmanci yanzu shine zuwan ka, ka samu kazo nan da 1week ina jiran ka".

Daga haka Alhaji Baba ya yanke 'kiran tare da jinginar da bayan kansa da jikin kujeran motar yana sakin numfashi, cikin ransa yace" Allah ka rufa mana asiri".

Ya 'dauki a 'kalla tsawon mintina uku a haka yana tunani, shi kansa baya son auren Mu'een tun yanzu amma yanajin sam ba zai iya biyewa son zuciyar sa akan hakan ba, cuz babu wanda ya san mai gaba zai haifar..dan gara yayi masa auren hankalin sa zai fi kwanciya, sai da ya gama tunanin nasa kafin a hankali ya ja motar yayi gaba.

Uncle Ja'afar kam hankalin sa tashi yayi sosai, jin batun yayi wani banbara 'kwai wai Mu'een ke neman aure, yaushe har ya kai wannan matsayin, shi a ganin sa sam shekarun Yah Deen
basu kai wannan matsayin ba, ya zai yi da karatun nasa to, ko kuwa tsabar ya raina masa hankali ne yasa yake nuna masa a kullum cewa karatun sa ya sa agaba nan kuwa ba haka ba ne, wa ma ya bashi wannan damar da har zai jajibo musu maganar aure tun yanzu?"

Kasa ha'kuri yayi sai da yayi dialling number Mu'een domin ya tabbatar daga bakin sa...sai dai har wayar tayi ringing ta katse ba'a 'daga ba.

Cike da jin haushi ya sake 'kira....Yah Deen kam bai ma san ana 'kiran wayar sa ba da yake bata 'kara sosai kuma can cikin bedroom take shi yana palour.

'Kira uku Uncle J yayi masa amma duk ba'a 'daga ba, hakan yasa shi zama bisa couch 'din dake kusa da shi yana mai dafe kansa dake barazanar tarwatsewa...abubuwa duk sun kulle mai kansa ya rasa mai ke masa da'di, yaron da ya kwallafawa Burin ganin ya zama wani abu a rayuwa shine kuma tun yanzu zai watsar da karatun da batun aure..how dare he.

Mu'een kuwa bai bi ta kan wayar sa ba har sai da ya kammala komai da yake yi ya watsa ruwa yayi shirin sa cikin jumpa riga da wando kalar mint green yayi fes abinsa.

Lokacin daf maghrib ne, so niyyar sa sai ya biya masjid idan ya idar da sallah sannan ya wuce wurin iyayen sa ya gaida su.

Sai da ya gama fesa turaruka ya 'dauki key 'din gidan kafin ya kai hannu ya 'dauki wayar sa dake jone a caji gefen gado.

Yana 'dagawa ya danna ta kawo haske da niyyan duba agogo nan yaci karo da missedcall a wayar take ya shiga ya bu'de su.

Ganin har sau uku Uncle J ya 'kira shi ya sanya shi 'dan firfito da idanu waje...hanyar barin 'dakin ya nufa yana kan dialling numbern, sai dai shima 'din koda ya 'kira ba'a 'daga ba.

Da wani ne daban da ko da wasa ba zai kuma 'kira ba amma da yake Uncle J ne ya sa shi sake 'kira a karo na biyu.

Yana 'ko'karin danna locked a 'kofar palour Uncle J ya 'dauki wayar wanda zuwa lokacin zuciyar Uncle J ya 'dan sau'ko daga fushin da yayi ba kamar 'dazun ba, hakanne ma ya sa har ya iya amsa sallamar da Mu'een yayi masa har ma ya amsa gaisuwar sa babu yabo babu fallasa.

Yana danna padlock 'din 'kofar waje yace" Na ga missedcall 'din ka har uku Uncle wallahi banji ba wayar bata kusa dani...".

Bai bi ta kan maganar tasa ba kawai sai ya 'kira sunan shi "...Mu'een"!
Yace" Na'am Uncle".

" Wai me nake ji daga bakin Alhaji 'dazun?"

Yah Deen dake kan tafiya a hankali sai ji yayi zuciyar sa ta tsinke da 'karfin gaske, nan take zuciyar sa ta fara bugawa da sauri...firgici ne ya shige shi marar misaltuwa.

Tsoron sa 'daya kar Alhaji ya sanar da shi komai ne, in kuwa haka ne da bai san yadda zai yi da Uncle Ja'afar ba.

In ina ya fara cikin rashin abin cewa kawai sai ya yanke 'kiran yana sakin numfashi harda dafe kansa da yake jin ya fara sara masa.

Yana shirin kashe wayar gaba 'daya ne 'kiran Uncle J ya sake shigowa cikin wayar.

Kamar ba zai 'daga ba sai kuma ya basar ya ja recieve button, cuz ya san in ya'ki 'dauka Uncle J zaiyi saurin gano cewa bashi da gaskiya kuma zai san da gan-gan ya'ki 'dagawa tunda  yanzun nan suke kan waya da shi.

Daf da wayar zata tsinke ya 'daga tare da sada ta da kunnan sa.

"...Ba ka da hankali ko Deen?"
Abinda Uncle J ya fa'di kenan daga 'daya 6angaren...bai kuma jira jin abinda Yah Deen zai ce ba kawai ya cigaba da fa'din" Tsabar ka raina ni shine ina tambayar ka abu zaka wani kashe min waya ko?"

Dauriyar yin magana yayi wanda cikin dakiya ya furta" Afuwan Uncle ba da gangan na kashe ba...".
"..My friend please  hold ur sorry i just need my answer now...ko kuwa 6acin raina kake son gani?"

'Dan 6ata rai yayi ka'dan jin tsawan da Uncle J ya daka masa, dan yaja hankalin sa ya sanya cike da shagwa6a yace" Uncle nima fa ban sani ba".
Kwafa yayi tare da fa'din
" Baka san me ba?"
Sai yace
"Abinda kake magana akai 'din".
Ya bashi amsa da sauri ganin kamar ya dan sauko.
Sai dai Uncle Ja'afar a tsawace ya sake fa'din
"...Dan ubanka ba kai ke neman auren bane da zaka ce min baka san komai akai ba?"

Manyan idanun sa ya zaro waje da jin cewa wai shi yana neman aure....bai iya 6oye mamakin sa ba a fili ya ce" Ni kuma neman aure Uncle..a ina?"
"...Raina min hankali kaji ai dama ka saba...hala yanzun ma cewa zakayi Alhaji sharri yayi maka ko?"

Wani tashin hankali ne ya ziyarce shi marar misaltuwa...maganar da Uncle J ya fa'di 'din sosai ya tayar masa da hankali, kuma wai Alhaji ne ya fa'di masa, to shi yaushe sukayi haka da shi dan Allah, yaushe yace yana neman aure?, babban abinda ya guda kenan wato sanya bakin Uncle Ja'afar cikin maganar cuz ya san 'kaniyar sa zaici bada wasa ba shi ba ai masa wargi, to ma ta ya zai iya 'karyata maganar Alhaji Baba gun 'kanin sa kan wannan batun fisabillahi....
" Tambayar ka nake yi fa Mu'een kayi min shiru".
Maganar Uncle J ce ta dawo da shi daga tunanin da ya tafi.

Cike da da damuwa da jin haushi Yah Deen yace" Ni dai dan Allah Uncle help me, wallahi bansan da maganar nan ba ni kam sai yanzu, 'kilan ba mamaki auren dole Alhaji yake shirin yi min".
Uncle cewa yayi
" Banson munafurci ni..."
Yah Deen ma sai yayi saurin taran bakin da fa'din" Please Uncle ni dai kazo ka ro'ka min Alhaji ya bar wannan batun nifa ban ce ina son aure ba, hasalima ni ban nemi auren 'yar kowa ba...Allah in kazo zan ma ka bayanin komai da ke faruwa...ni dai help me".
Ya 'karashe maganar kamar zai yi kuka.

Uncle J kam tunanin sa gida biyu ya kasu, sai ya rasa wani 6angare ne yafi rinjaye, jin yanda Yah Deen yayi maganar ya sanya shi ta shin farko ya yadda da batun sa sannan ga Alhaji Baba ma ba zai iya 'karya ta shi ba.

Ji yayi dama a kusa yake da a yau 'dinnnan ba sai an kwana ba zai je a warware wannan maganar tun kafin tayi 'karfi.

Duk da haka bai yi 'kasa a gwiwa ba, take ya shirya cikin ransa cewa kafin 1week 'din da Alhaji Baba ya fa'di dole zai je su ha'du.

" Zanzo nextweek insha Allahu".
Haka kawai ya iy furtawa a fili ga Yah Deen 'din dake ma'kale da waya a kunnan sa yana sauraro... sannan ya yanke wayar kowa zuciyar sa cike da tunani.

   Haka Yah Deen ya 'karasa masallaci ya gabatar da sallar maghrib cikin jam'i bai taso ba sai da ya tsaya yayi addu'o'i masu tsayi akan auren da yaji wai ana shiryawa akan sa, tsoron sa kar Alhaji Baba yace Husnah zai aura masa..yace in kuwa haka ne da ya shiga bakwai ba ma uku ba, wannan dalilin ka'dai ya sanya shi kai kukan sa wurin mahallici akan cewa kar Allah ya sa auren sa da Husnah ya yiwu in dai da ita ne Allah ubangiji  ya tarwatsa auren.

Inma ya zama dole sai Alhaji yayi masa auren ne to ubangiji Allah ya musanya masa da wata mafi alkhairi.

Zai iya zaman aure da kowa koma wacocdb amma banda Husnah, sam ita kam bai jin zai iya rayuwa da ita matsayin matar sa....(ni kuwa nace kaji ja'iri kamar ba shi ne ya 6ata mata tarbiyya ba).

Bai iya ya bar masallacin ba har sai da ya idar da sallar Isha'i, nan suka ha'du da Alhaji Baba a masallaci suka yo gida tare kamar yadda suka saba.

Sai dai yanzu babu wannan rahar da Alhaji Baba ke yi musu duk sanda suke tare da shi, to ada 'din ma ko shi Alhaji bai yi musu hira ba Yah Deen kan ja shi da hirar yana 'dan takalo shi tamkar kakan sa, amma yanzu kam shiru kana ganin su zaka san da bambamci cuz tafiya kawai suke yi kowa da abinda ke cikin ransa, har gara ma Alhajin ya kan 'dan tambaye shi abu jifa-jifa har suka isa gida.

A palour duk suka zauna nan Ammi ma tazo ta same su.
Gaida Ammi yayi sai dai tana jin muryar sa ta fahimci ba dai-dai yake ba, take sai tace" Me ke damun ka?"
Tayi maganar tana kallon sa.
" Headache"!
Ya bata amsa a takaice yana me sakin 'dan 'karamin tsaki.

" Allah ya sawwa'ka..kasha magani ne to?"
Tace tana duban sa da kulawa.
" Zan sha idan na koma".
Kai ta jinjina tare da mi'kewa ta gabatar musu da dinner ta kuma 'kwalla 'kiran suna na.

Kafin in fito ma har sun isa ga dinning 'din sun zauna, da fitowa ta kuwa ganin su uku ne ya sanya na isa na zaune raku6e gefen Ammi kamar wata ba'kuwa...Ammi kam bata kulani ba da yake tasan abinda ke sani yin hakan ba ya rasa nasaba da wanzuwar Yah Deen a wurin.

Alhaji Baba ne yace dani" Ba zaki dai na wannan ra6e-ra6en bako Uwata, maza saki jikin ki ki ci abinci".

" Hmm".
Kawai Ammi tace tare da karkatawa ta kalle ni sai na sake du'kar da kaina.

Sai da ta gama zuba min abincin kafin tace dani"  bismillah"
A hankali na kai hannu na na wanke kafin na janyo abincin gaba na, har a lokacin Yah Deen bai ko kalli inda nake ba balle in san cewa ya san da zama na, a hankali na 'daga kaina na kalle shi ganin bai ma san da ni wurin ba ne ya sanya ni fara cin abincin a hankali.

Shi kam bai fi hannu uku yayi ba ya kawar daga gaban sa tare da 'dauraye hannun sa yaja baya.

Babu wanda ya kula shi cikin Ammi da Alhaji nima kuwa kaina 'kasa ban kuma kallon inda yake ba, sai dai har lokacin na kasa sakin jiki na, Ammi ne ta waigo ta kalle ni tana shirin yin magana na riga ta da fa'din " Ni na 'koshi Ammi".
" kin tabbatar?"
Alhaji Baba ya tambaye ni sai na 'dage masa kaina alamar " Erh".
" Yau abincin Ammi yayi ba'kin jini kenan".
Alhaji ya fa'di yana 'yar dariya tare da maida idanun sa kan abincin.

Ammi sai tayi murmushi kawai.
A hankali na tashi na bar table 'din cikin raina nake tunanin wannan shi kullum bai canzawa.

Yah Deen ma da yake zuciyar sa cike take da damuwa hakan ya sanya bai 'kara mintina sha biyar cikin gidan ba yai musu sallama Ammi na tuna masa shan magani yace zai sha... daga haka ya wuce can gidan da yake.

Yana kwance yana aikin tunani yaji 'karan shigowar sa'ko cikin wayar sa, da yake wayar na hannun sa hakan yasa bai 'dauki dogon lokaci wurin duba text 'din ba.

Nan ya ci karo da bank transfern ku'di daga Uncle J kimanin 40K ya tura mai.

Take ya 'kira sa yai masa godiya, anan ne Uncle J ya ji yanayin yanda muryar sa take a 'dan dusashe sai yace" Me ke damunka kuma Mu'een?"

Kamar zai yi kuka yace" Ni dai Uncle please help me out of this issue...tsoro nake ji kar Alhaji Baba ya 'daure ni".

" Ka kwantar da hankalin ka nextweek insha Allahu zanzo mu gana da shi...ina dai ka tabbatar ba kai ka nemi auren ba?"
Sai yace
" Haba Uncle ina ni ina neman aure tun yanzu?"

'Yar dariya Uncle J yayi yace " Rabu da Alhaji 'kila dan ya koma 'kauye ne shiyasa zai maka irin na su".

" Ni dai banso...Uncle please kazo da wuri".
Ya fa'di kamar zai yi kuka.
Uncle Ja'afar kuwa
" Insha Allah" kawai yace da shi wanda daga haka suka yi sallama da shi yana 'danjin dama-dama, sai dai wani 6angaren hankalin sa ya kasa kwanciya da 'karya ta mahaifin sa da yayi, tsoron kar idan Uncle J ya tunkare shi da maganar shi mai ze ce? kar dai ya bayyana masa komai cewa mata ke zuwa wajen sa shiyasa zai yi masa auren...hankalin sa duk ya kasa kwanciya ji yake tamkar ya fasa tafiyar ma gaba 'daya..amma ya san hakan ma ba wata mafita ba ce mai amfani tunda koda yana nan 'din ma bai isa ya hana Alhaji abinda yayi niyya ba.

A wannan daren sam bai iya yayi baccin kirki ba, yaso ya 'kira Husnah ya tambaye ta ko taji  wani labari amma sai ya bawa zuciyar sa ha'kuri akan kar yayi gaggawa tunda bai ji daga bakin Alhaji ba.

Washe gari da sassafe misalin 'karfe takwas ya fito, da yake weekend ne so a wajen gidan ya samu Alhaji Baba zaune yana hutawa,  anan suka gaisa ya sanar da shi batun tafiyar tasa...fuskar Alhaji babu yabo ba fallasa yayi masa fatan Alkhairi..daga nan ya shiga wurin Ammi da tunanin ko zai samu jin wani sirri game da batun auren da daga bakin ta...ni kam a lokacin ina can ina bacci na a 'dakin Ammi.

Ga mamakin sa koka'dan Ammi bata kusanta maganar ta da batun aure ba, ga dukkan alamu itama bata san shirin Alhaji akan sa ba...cikin ransa ya ayyana wannan karan kenan Alhaji Baba shi ka'dai ya ya yanke shawarar sa cikin ransa.

Yah Deen ji yayi tamkar ya sa hannu aka ya tsala ihu, shi sam bai son wani batun aure yanzu, ga shi abin haushin bai ma san wace ake magana akanta ba.
Ammi kam bata bar shi haka nan ba, duba da abinda ya faru tsakanin sa da mahaifin sa kwanaki ya sanya ta ringa yi mai nasiha akan ya kiyaye duk abinda zai aikata ya guji wanda zai yi leading 'din sa da kaucewa mahalicci...sannan ta 'kara garga'din sa akan Husnah, tace tunda yace course mate ce ita to ta tsaya iya matsayin ta ya daina bawa mutane damar da zasu iya shiga tsakanin sa da iyayen sa tunda yasan babu wanda zai so ganin hakan daga 'dan sa, shima ya kiyaye, tace in dama 'dan uwan ka namiji ne ai kaga babu wanda zai damu matu'kar tarbiyar sa tana da kyau amma ita a matsayin mace be kamata ace tana zuwa har muhallin ka ba da sunan course mate...kayi mata magana ta daina please babu kyau, kamata yayi ta ri'ke darajar ta 'ya mace.

Yace " Insha Allahu Ammi zan mata magana bazata 'kara ba".
Zuciyar sa duk acunkushe yake jinta, bai san me ke shirin faruwa da shi ba.

Ga shi kalaman Ammi sun 'kara bayyana masa cewa itama a duhu Alhaji Baba ya barta bai sanar da ita komai ba.

10k Ammi ta 'dauko ta bashi tace ya hau mota da shi, yayi mata godiya sosai sannan ya fita, cikin ransa yake jin wani iri tamkar yayi mantuwa cikin gidan amma ko za'a yanka shi ba zai ce ga abin ba, haka ya daure ya fito ya sake tarar da Alhaji Baba a wurin.

Da ada ne kafin su sami sa6ani irin wannan tafiyar ta kamashi da yasan tare zasu koma cikin gidan da shi amma yanzu kam Alhaji ko ajikin sa kamar ma bai san da batun tafiyar ba, nan ya sake yi mai sallama ya wuce amma ga mamakin sa Alhaji ko sisi bai ciro ya bashi ba abin ya bashi mamaki sosai cuz ba hakan suka saba ba.




Comment
Vote
Share




*Salmerh ce* 😍
💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*


*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

Masoya na godiya nake sosai Ubangiji Allah ya cika muku burikan ku na Alkhairi😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *44*

Hakan da yafarun ne ya 'kara fahimtar da shi irin 'kuncin da ya sanya Alhaji Baba ciki, gashi dai zai amsa sallamar sa da gaisuwar sa har ma wani sa'in zai 'dan ja shi da hira amma wannan fara'a da sakin fuskan sam babu su.

Tafiya yake yana tunanin abinda zai biyo baya...ya riga ya san zancen auren nan babu fashi tunda har Alhaji ya iya furtawa ga Uncle J, ya san babu mai iya dakatar da shi, cuz tun sanin da ya yiwa mahaifin nasa ya san shine akan magana 'daya tak, duk da'din da kuke da shi kuwa baka isa ka sanya shi canza ra'ayin sa ba, he is the

Please Login or Register in order to submit comment