Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Noor...nagode! Nagode!!..Allah ya biyaki da Alkhairi..a yau 'din na zan sanar da Uncle Ja'afar a maida muku auren ku domin babu wani abinda za'a jira tunda kin riga kin amince...sai dai fa kiyi ha'kuri da kalan auren naki 'kilan haka Allah ya 'kaddaro miki dukkan taron 'daurin auren ki na zuwa ne cikin rashin shiri".


" Zan koma gida Anty dama nazo ne batun komawa ta school inji yaushe ya kamata mu sa rana..." Karki damu ki bari zamu yi magana daga baya duk abinda ake ciki zan sanar dake...yanzun muje ki yiwa Ammi sallama kafin ki wuce".




Comment
Vote
Share




*Salmerh ce*😍💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)



By
*Salmerh MD*


*Wattpad @*
*Serlmerh-md*



💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*



_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_


*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*



🅿 *92*


Fita suka sake yi dukkan su zuwa wajen Ammi sun same t ne idanun ta kan waya tana faman dubawa, ko da tayi mata sallamn ma kai kawai Ammi ta jinjina mata cike da jinda'di, ita kam fuskar ta ba yabo ba fallasa ta fita.


Sai bayan fitar ta sannan Ammi ta kalli Anty Zainab tace" Zainab kinga fa ni nama rasa wanda zan 'kira in sanar mawa saboda farin ciki kaina ya kulle kuma".
Murmushi Anty Zainab tayi idan ka gansu bazaka yi zaton sune ke shar6an kuka lokaci 'kalilan da suka gabata ba.
" Bari zan gayawa Baffan su".
Shine abinda Anty Zainab ta fa'di tana mi'kewa tsaye.

Wayar ta taje ta 'dauka ta 'kira shi sai dai cikin rashin sa'a ko 'kira guda daga cikin missed call uku da tayi masa bai 'daga ba.

Text ta tura masa kamar haka.." _Mun yi magana da Noor kuma ta amince da auren ka sanar da Alhaji please_ ".
Tana gama rubutawa sai ta tura masa sannan ta 'kira Saif ta tambaye shi ya jikin Mu'een 'din yace " Anty da sau'ki dai za'a ce amma har yanzu akwai damuwa..ance sai an tare shi da labarin da aka san zai kwantar masa da hankali ya sa shi farin ciki kuma duk mun rasa yadda zamu yi tsoron kar ya farka ma muke yi a halin yanzu...."

Murmushi Anty Zainab tayi gami da fa'din" ka kwantar da hankalin ka be jima ba muka rabu da Noor kuma ta amince da batun maida auren su..ina jin kawai ku jarraba wannan labarin 'kila ze yi amfani".
Cike da farin ciki Saif yace" Alhamdulillah...ai kamar anyi an gama ne ma Anty...bari in sanar da Alhaji Yanzu".
Ko jiran jin ta bakin ta ba yi ba ya yanke wayar.


Alhaji Baba be wani bayyana farin cikin sa a fili ba ko bayan da ya ji labarin dan ciwon Mu'een 'din ya riga ya 'daure masa kai ya zarta tunanin sa gaba 'daya, gani yake kamar ba rayuwa zai sake yi ba kawai likitocin na yaudaran su ne, yau kusan kwanan su biyu kenan da zuwa Zaria amma ko motsi da yatsun sa be yi ba..yau ne ma ake saka ran farfa'dowar sa amma shiru har yanzu gashi har la'asar ta shige maghrib ta gabato.


Gani yake ma kamar wannan auren banda tauye hakkin Noor babu abinda za'a yi, mutun kullum yana kwance ba lafiya ina za'a yadda da aura masa mace irin Noor kuma...yaushe ma ake da tabbacin zai tashi, shi ya fara tunanin ma kawai gara su amince a ayi masa dashen indai har akan zai fi kawo masa sassauci sai dai dashen ance babban risky ne likitocin da kansu suka fa'da...Innalillahi wa inna ilaihi raji'un...a zuci yake tunanin amma be san lokacin da wannan kalmar ta kubce daga bakin sa ba, goshin sa ya dafe da shima yake jin yana sara masa.

Ganin hakan ya sanya Uncle Ja'afar kallon.sa, cikin 'yan da'kiku ya karanci yanayin da yake ciki, fara kwantar masa da hankali yayi domin duk yasan akan ciwon Mu'een ne yace masa su gwada batun auren dai tukunna su gani, yace shi inda hali ma tunda ta amince me zai hana kawai a 'daura auren ayau 'din aganin sa hakan zai fi kawo musu sau'ki fiye sanar da shi labarin amincewar tan kawai.

Alhaji Baba yaso ya nuna 'kin amincewar sa amma Uncle Ja'afar ya kafe dole sai da ya amince.


Saif ya tura ya ciro masa ku'di a bank sannan ya tura shi nemo dabino domin ya tura anemo masa goro ba'a samu ba.

Ai kuwa bayan sallar Isha'i aka gabatar da 'daurin auren Deen da Noor bisa sadaki 50k da Uncle Ja'afar ya bayar.


Alhaji Baba me ya bada auren kamar yadda ya ta6a bayar wa abaya dan haka a hannun sa aka bada sadakin nata karo na biyu...shi dai fuskar sa ba yabo ba fallasa haka yayi ta binsu da idanu har aka 'kare komai.


A daren Ja'afar ya ke6e da saif ya tsara masa duk yadda yake so ayi, Alhaji Baba kam bai ma san sunayi ba, kuma ma ko ya sani 'din ba baki zai sanya musu ba.


Saif ne ke kwana tare da shi su Alhaji Baba da Uncle Ja'afar Hotel suke kwana inda suka yi masau'ki tun farkon zuwan su.


Dama ya gama tsara masa cewar a duk lokacin da yaga alamun zai farka sai yayi kamar waya yake yi bayan ya gama shirya masa abinda zai fa'da.



Daren ranar kaf haka Saif ya gama gadin Mu'een amma bai farka ba, har washe gari shiru har sun fara cire rai ma da ganin farkawar tasa domin magashiyan yake kwance sai uban na'urori da aka jona mai..tunda suka kawo shi bai motsa ba yau kwana hu'du kenan..abin ya fara 'daure musu kai sosai gashi Uncle na so ya koma bakin aikin sa amma ya kasa dauriyar yin hakan sam ba ze iya tafiya ya bar Mu'een cikin wannan mawuyacin halin ba, gani yake kamar da ya tafi za'a sanar da shi mutuwar sa shi yasa yafi so yaga anyi komai a gama kan idanun sa.


Noor kuwa tun lokaci da ta tabbatarwa da Ammi amincewar ta bata 'kara kunna wayar ta ba, ko 'daura auren ma da akayi sai Ummah aka 'kira aka sanar mawa wanda itama abakin Ummhan taji.

Kuka kuwa kamar wacce aka ce an sai da ita ga wani ma'kiyin ta ne haka take ji..duk ta hana kanta sukuni da kuka..Ummah na 'ko'kari sosai wajen kwantar da mata da hankali amma a banza.


Haka Saif suka rabu da yammacin ranar ma duk jikin su sanyi 'kalau suka koma masu'kin su..Saif kansa har 'yar rama yayi, yana matu'kar tausayawa yayan nasa, bai san wace iriyar taimako ya kamata yayi masa ba...


Likitoci na zuwa akai-akai suna duba shi kuma kullum abin numfashi da bugun zuciyar sa na reading yadda ya kamata amma har yau farfa'dowa ta gagare shi.

Ko yau in ma Saif duk jikin sa da sanyi, gaba 'daya ya tsinke da lamarin Yayan nasa 'karfe tara likita ya bar 'dakin wanda hakan ya bawa Saif damar shiga wajen sa da yake tare suke kwana.


Baccin ma yanzu ko damun sa baya yi da yayi da bai yi ba duk baya jin komai ba, har ya saba da zama yana 'karewa Yah Deen kallo...sosai ya fahimci rayuwa ba'a bakin komai take ba..yana zaune sai dai ya duba wayar sa ko kuma idan uzurin shiga bayi ya kama shi ya tashi ya shiga ya fito, tunani kala-kala babu irin wanda bai zo ransa ba...

Kwana yayi idanun sa biyu amma babu wani canji da yagani tattare da shi.


Har gari yayi haske ma'aikata suka zosuka gama aikin su suka tafi amma shiru, haka likitocin ma suka shigo suka duba shi suka sake fita, su Alhaji Baba ma duk sun zo inda Saif ke ro'kon su akan suje su huta abinsu tunda shi yana nan duk abinda ake ciki yayi al'kawarin sanar da su, Saif yayi hakan ne saboda tausayin mahaifan nasa, tun zuwan su Zaria ba su huta ba kullum suna cikin zirga-zirga, aganin sa gara shi domin da 'karfin.sa inda sabo ma ya riga ya saba da hada-hada...sosai suka ji da'din furucin Saif in dan 'karara ya nuna tausayawar sa gare su....kafin su koma sai da suka sake ganawa da likitan anan Alhaji Baba ya fa'di nashi ra'ayin amma likitan yace har yanzun dai da saura su 'kara basu lokaci.

Haka suka fita suna baza babbar riga kowa jikin sa yayi laushi.
Fita suka yi suka koma masau'kin su suka bar shi da Saif 'din kamar yadda ya bu'kata.



'karfe tara da 'yan mintina na safiya lokacin Saif yaje yin breakfast ma, ko da ya dawo kuwa kamar ba zai shiga duba shi ba kuma sai wata zuciyar tace ka duba dai.



Tura 'kofan yayi da niyyan le'kawa sai cak idanun sa suka sau'ka kan yatsar 'kafan sa guda dake motsi.
Saurin 'karasowa yayi ciki yazo kusa da shi...saman idanun sa yaga yana motsi ka'dan-ka'dan yana jujjuyawa amma bai bu'de idanun ba.

Da farko tsaban farin ciki Saif rikicewa yayi har ma sai ya rasa mi ya kamata yayi tuno abinda Uncle Ja'afar ya sashi yi ne ya sanya shi saurin ciro wayar sa daga aljihu idanun sa kan fuskar Mu'een.

'Kira ya dannawa Uncle 'din wanda daga 'dagawa ya furta" Hello..Hello Uncle"
" Erh gani nan tare da shi"
" Ohh har kun dawo daga wajen 'daurin auren ne?"
" Kai..masha Allah..Ubangiji Allah ya sanya Alkhairi ya bada zaman lafiya...nayi matu'kar farin ciki sosai".


Shi ka'dai yayi ta maganar sa amma bazaka ta6a gane hakan ba.

Shima Uncle Ja'afar hakan da yaji Saif na fa'di ne ya sanya shi saurin fahimtar halin da ake ciki, yana da tabbacin Mu'een ya farka ne shiyasa Saif ya 'kira shi domin shine da kansa ya tsara masa komai da zai ce.

Albishir 'din da yayiwa Alhaji Baba kenan nan suka shirya a hanzarce suka fito.

Saif cikin farin ciki yayi wayar tamkar babu wata damuwa tattare da shi...yana sau'ke wayar daga kunnan sa sai ya suka ha'da idanu da Mu'een domin tuni ya bu'de nasan lumsassun idanun ya zubawa Saif tunda yaji muryar sa kusa da shi.


Cike da murmushi yace" Yaya albishirin ka..! yanzun Uncle ke ce min an maida muku auren ku da Noor...gaskiya ka bani tukuici na..."


Idanu ya zubawa Saif na tsawon lokaci sannan a hankali ya maida idanun sa ya lumshe gami da juya kansa...hawaye Saif yaga yana tsiyaya daga gefe da gefen idanun sa..take kuma na'urar dake irga bugun zuciyar sa ta fara 'kara yana 'dan sau'ka a hankali...fisga jikin sa ya fara ka'dan-ka'dan...kana iya ganin hawa da sau'kan da 'kirjin sa ke yi.


Rikicewa Saif yayi da ganin hakan take ya fara 'kiran sunan sa, hannu ya sa aka yana ji tamkar ya 'kwala ihu saboda tausayin Yayan nasa, a rikice ya fara ja da baya da niyyan fita 'kiran likita, sai dai kafin ya kai ga isa jikin 'kofan ma sai suka riga shi turowa.


Da sauri suka yi kansa bayan sun bawa SAIF
umarnin fita sai suka datse 'kofan ko ta glass in window Saif ba ya iya hango shi haka duk sai yaji hankalin sa ya tashi sosai.


Bei iya ya ko 'kira su Alhaji ba tsaye yake yana safa da marwa da ka gansa zaka san cewa hankalin sa duk a tashe yake, wanda ba'a 'dauki tsawon lokaci ba sai ga su Alhaji ma sun iso nan yayi musu bayani a takaice yana nuna damuwar sa a fili 'karara.


Innalillahi kawai suke ta maimaitawa yayin da Alhaji ya samu wuri kawai ya zauna ya dafe kansa.


Kimanin awa guda da rabi kafin likitocin suka fito su kansu ba'a nutse suke ba..domin da 'kyar Allah ya taimake su suka ceto rayuwar sa cuz bugun zuciyar san 'kasa sosai ya sau'ka.


Albishiri suka musu akan cewa ba wani matsala su kwantar da hankalin su nan da wani lokaci komai zai daidaita da iznin Allah...nan Alhaji Baba ya saki wani ajiyan zuciya Uncle Ja'afar kam godiya ya ringa zubawa mahalicci.


Cike da farin ciki suka samu wuri suka zauna gaba 'daya...tsabar sauri ma duk wayoyin su basu taho da shi ba, a masau'kin sun suka baro shi.


Allah cikin ikon sa kuwa kafin sati guda har yana iya shiga bayi da kansa...sai dai har yanzun baya magana da kowa...sai da ido kawai.


Uncle Ja'afar ma jiya ya koma ganin jikin nasa da sau'ki kuma likita yace ba sai anyi masa dashen ba ma insha Allahu komai zai wuce.
Fatan su dai Allah ya 'kara lafiya ne ingantacciya.



Sai da Alhaji Baba ya dawo ne kafin su Ammi ma da Anty Zainab suka shirya zuwa can Zarian, sai dai Alhaji yace bai yadda su kwana ba a ranar zasu dawo dan haka sassafe suka shirya tafiya.


Tun dare Anty Zainab tace da Noor ta shirya zata raka ta wani wuri gobe kuma da sassafe zasu zo su 'dauke ta, da yake da motar gida ne so basu da matsalar komai.


Noor kam toh kawai tace da ita ba wai dan ranta na so ba..sai da ma suka fito kafin take sanar da Ammi cewa tafiyar fa wai harda Noor ne tun jiya na gayyace ta amma ban sanar da ita Zaria zamu ba.
" Ammi jim tayi kafin tace kar kuma taga kamar an takura ta fa?"
Anty cewa tayi
" A a ita da mijinta wani takura kuma yanzu, idan kika biye ta Noor fa har abada baza'a yi abinda ya dace ba".


Haka driver ya jasu zuwa 'kofar gidan Ummahn Saudah..shiga suka yi suka gaggaisa kafin suka fito dukkan su, Noor kam tun da taga harda Ammi sai taji hankalin ta bai kwanta da tafiyar ba, ai kuwa kamar wasa sai taga sun 'dauki hanyar Zaria ta kuma san can Mu'een ke kwance...shiru kawai tayi tana jin faragabar ganin sa a zuciyan ta.


Sosai su Ammi suka yi farin ciki da ganin sa zaune, magana ce ka'dai baya yin ta sai ya ga dama, haka ya dinga bin Noor da kallo bai iya yace da ita ko uffan ba, ko gaisuwa akayi masa baya amsawa sai dai ya lumshe idanu kawai.


Banda murmushin farin cikin ganin su Ammi babu abinda zaka gani kan fuskar sa.

Haka har suka baro Zaria magana bata ha'da su da ita ba..ita kam ko a hanyar komawar su ma jikin mota ta kwantar da kanta tana share hawaye a 6oye.


Tana jin yanda su Ammi ke bayyana tsananin farin cikin su a fili da ganin yanayin jikin nasa, amma ita bata iya sanya musu baki ba.


Tunanin ta ma tafiyar da ke gaban ta ne, dama tun lastweek ya kamata ta koma amma Anty Zainab ta dakatar da ita, yanzun wai zuwa jibi zasu koma har da ita Antyn.


Koda aka sau'ke su ita kam bata fita daga motar ba tace a wuce can gida da ita tana so zata 'karasa shirin ta ne...


Bayan kwana biyu da zuwan su Zaria suka bar Shuwarin ita da Anty Zainab amma sai da suka kwana kusan uku a Zaria kafin suka wuce dama ashe haka Anty ta tsara tafiyar shiyasa ta dakatar da ita.


Tunda suka koma kuwa sam ta kasa barin ta ta ci abinda ranta ke so, ci wannan sha wannan duk ta ishe ta da su, a 'yan kwanaki biyu zuwa uku da suka yi a Azare 'din ba 'karamin ha'da abubuwa Anty Zee tayi ba shiyasa a kullum bata zama a gida har sai ranar da suka taho.


Wani sa'in har mamakin ta Noor ke yi domin sarai tasan dan me Antyn ke sa ta gaba da shashayen abubuwan ita kuwa ranta ba so yake yi ba, a ganin ta duk 6ata lokaci suke yi abanza da wannan auren nasu bashi da darajar da har za'a yi masa shiri irin haka.


Bata manta lokacin da ta kunna wayar ta ta 'kira AbdulHakeem ba..lokacin da kanta tasan ta sanyawa Zuciyar ta dauriya, amma duk da haka sai da tayi kuka daga 'karshe kasa ma magana tayi sai text ta tura masa akan cewa an riga an 'daura mata aure.


Da farko 'kin amincewa yayi sai daga baya ya yadda dan yasan Noor bata yi masa 'karya.
Ya ji haushi sosai kam amma hakan bai hana shi yi mata fatan Alkhairi a auran ta ba...Abin mamaki sai ga shi harda kyautar ku'di yayi mata masu 'dan nawi a fa'darsa wai tashi gudummuwar kenan, sam be nuna alamun yaji 6acin rai ko wani abu ba duk da tasan dole abin sai ya dame shi amma yanda yayin sosai taji ya 'kara birge ta.


Sai take jin dama shine ta aura da babu abinda zai hana ta shan duk wani abinda ake sha da ku'din ta ma zata siya amma Mu'een kam wannan ba damuwar ta bane shi domin ko duniya zata ha'da ta shanye saboda shi tasan ba kwarjini zata yi a idanun sa ba, tunda hakan ba zai hana shi ya tsallake ta ya tafi wurin wasu matan ba.




*****
_Wai ya labarin Husnah ne?_
Husnah na can yanzu duniya tayi mata da'di domin babu mai takurawa rayuwar ta, tun rabuwan ta da Mu'een bata 'kara sashi a idanun ta ba, da yake ma ha'kura tazo tayi da makarantar ta koma Abuja wurin mijin ta ta cigaba da bautawa auren ta.


Duk yanda Hisham yaso yaji dalilin barin makarantar Husnah 'kin sanar da shi tayi, ta kuma canza layi ta daina amfani da tsohon layin ta abin duk sai yake bashi mamaki matu'ka.


Da farko abin damunta yake sosai a zuci, haushin yanda ta ringa biye masa tana yadda da bacin da auren wani namijin akanta.
Sam ta rasa me ya toshe mata 'kwa'kwalne ma da bata 'dauki mataki akansa ba, tasan hadda sakacin ta ma baya ga haka da be isa ya 'keta mata haddin auren ta ba.


Haushin sa sosai yanzun take ji ko tunawa da shi bata so tayi, Allah ma ya taimake ta tun ranar da Noor da gansu bata sake sanya shi a idanun ta ba.


Wani sa'in idan abin ya ishe ta sai taji kamar ta sanar da Hisham gaskiyar abinda ya faru amma wani 6angare na zuciyar ta sai yake yawan garga'din ta akan kar ta fa'di ma kowa domin idan kasan farkon fitina baka san 'karshen ta ba.
Sai daga baya duk ta watsar da komai ta cigaba da rayuwar ta kamar kowa sai dai har yau 'din nan bata daina istighfari da neman gafarar mahalicci ba.


Hisham mutun ne mai tsananin ha'kuri da kawar da kai, ga sanin ya kamata ga shi sam baya 'dagawa kansa hankali a kan komai.

Zaman su lafiya suke da ita yana kuma kulawa da duk wani abu da yake hakkin ta ne.


Alhaji Maman mahaifin sa kuwa tun lokacin da wani hatsari ya rufta da shi jinya ya kasa 'karewa sai amaryar sa ta wawashi iya abinda taga zata iya sannan ta je har asbitin da yake jinya ta tsaya akansa wai ya sai ya bata sakin ta.
Ai kuwa sai da ya sake tan kafin tayi gaba tana ta6e baki gami da taunar chewingum tace bazata iya zama da miskini ba domin daga 'kugun sa zuwa 'kafafun sa duk sun yi damage basa amfani.

Haka tana yatsina fuska tayi gaba kowa dake wurin sai da yayi mamakin ta domin kaf cikin matan Alhaji Mamman ita yafi fifitawa sai gashi itace ta fara guje masa a lokacin da yake tsananin bu'katan kulawa.


Tun lokacin ya fara danasanin abubuwan da ya ta aikatawa dama kuma duk abinda ba'a shirya shi ta hanyar da ta dace ba 'karshen sa ba kyau yake yi ba.


Taimakon da Allah yayi masa ma shine be kai ga wula'kanta ba Allah ya kar6i ransa...domin dududu bai fi 3months da jinyar ba ya koma ga mahalicci.

Yanzu Mummyn Husnah da Hajiya Kareemah mahaifiyar Hisham suna rayuwa ne tamkar 'yan uwa babu ruwan su da wani batun dukiya ko kishi da junan su, sun ha'de kansu suna kasuwan cin su a tare balle ma da yake Hajiya Kareema ma'aikaciyar gwamnati ce shikenan sai Mummyn Husnah ke yi musu jagoranci haka komai yake tafiya musu dai-dai.


Babban damuwan Husnah a yanzu bakomai bane face rashin haihuwa..daga ita har Hisham 'din duk sun damu, banda ma iyayen su da kullum ke taya su addu'a ko za'a dace.


Ita kam Husnah wasu lokutan sai dai ta zauna tayi ta shar6an kuka, domin tasan musabbabin da yakawo mata hakan bakomai bane illah alluran da ta tayi lokacin da take tare da Mu'een shiyasa har yau bata yadda taje asbiti tare da Hisham ba gudun kar asirin ta ya tonu a idanun sa...sau da dama shike sake bata baki akan tayi tawakkali, haihuwa da rashi duk na Allah ne, kuma idan bai nufe su da samu ba ko ma me zasu aikata haka zasu ta wahalar da kansu bazai basu ba, idan kuwa ya nufe su da samu haka nan ma zasu tsinci kansu sun zama iyaye batare da sun wahalar da rayuwar su ko dukiyar su ba.


Sosai take jin da'din halayyar Hisham tana kuma godewa Allah daya ha'da ta da mutun irin sa..taje Umrah taje Hajji kusan sau uku tana ro'kon Allah akan haihuwa amma har yanzu shiru babu labarin komai.


Da kanta ta fara bawa Hisham shawaran yayi aure amma ya'ki, itan ma ba wai tana so yayi auren bane amma a ganin ta rashin adalci ne tayi idan tace da shi bazai yi aure ba tun da tasan matsalar daga gare ta ne.


Hisham 'kin amincewa yayi yace ai a wurin Allah suke nema ba mutun ba, idan kuma ya 6ata lokacin sa yayi auren kuma itama matar bata zo ta haihu ba fa me akayi kenan.

Cike da marairaita Husnah tace
" Duk da hakan dai ka gwada dan Allah, Familyn mu ya yi shiru da yawa Hisham ya kamata kayi wani abin kaima.".

Sai ce mata yayi" Ai ban isa inyi abinda Allah be nufa ba dan haka kima daina 6ata lokacin ki, ni babu wani aure da zanyi".

Da ta ga dagaske yake bazai amince ba sai ta kai 'karar sa wajen iyayen su.

Mummyn tace tafi 'karfafa zancen dan haka dole ta tilastawa Hisham fara neman aure...cikin kwanciyar hankali kuwa ya samu wata yarinya anan Azare ya aura, yarinya ce 'karama dan sacondary school kawai ta kammala aka bashi ita.

Sai a lokacin da kusanci yarinyar sannan ya fahimci akwai bambam mai tarin yawa tsakanin Husnah da yarinyar sai dai hakan bai yasa ya canzawa Husnah fuska ko kuma cin zarafin ta ba, balle ma shi ba gwanin dawo da abinda ya riga ya wuce bane.

Ya dai yi 'ko'kari wajen ganin ya daidaita tsakanin Husnah dayarinyar be yadda ya tauyewa kowa hakki ba kasancewar kowaccen su nada nata kalan muhimmancin a zuciyar sa.


Allah cikin ikon sa kuwa shekarar farko da auren su ta cika shi ne da 'dan ta namiji da Allah ya azurta ta da samun sa, yaro mai kama da ita...murna a wurin wannan familyn ba'a cewa komai...Husnah sam bata yi ba'kin ciki da haihuwar ba amma haka take shiga 'daki ta risgi kuka son ranta dan tasan itace ta cuci kanta abaya, da ace bata biyewa Mu'een ba da duk hakan bai faru ba...kusan kullum sai ta tuna lokacin da ya zubar mata da ciki ashe da rabon bazata sake ganin 'kwanta a duniya ba.


Hakan ka'dai idan ta tuna shi yafi komai 'kona mata zuciya haka ya dinga sawa ana 'dirka mata allurai ba bisa 'ka'ida ba.

Ta kanyi dana sani fin a irga a kullum gashi Allah ya ha'da ta zama da yarinya fitsararriya, duk ta raina ta bata kuma san dalili ba, takan yawaita yi mata habaicin marar haihuwa ko kuma komai a gida sai ta nuna tamkar mallakin 'dan ta ne shi ka'dai, Husnah bata ta6a biye mata ba amma Hisham kansa ya gaji da halin yarinyar.

Duk yadda yaso ta bawa Husnah girman ta abin ya faskara..gani take kamar dan ita ta haihu to bazai ta6a iya yi mata abinda ba shine ba.

Abin ma ya 'kara nin kuwa ne lokacin da aka sake yi mata gwajin ciki akaro na biyu, 'dan ta na da wata takwas ta 'kara samun wani cikin, iskanci, fi'ili da rainin hankali kuwa sai abinda yayi gaba..shab ta manta da cewa Allah ne ke bada haihuwa ba dabara ko kuma isar mutum ba.


Shekaran sa 'daya da wata biyar ta haifi wata

Please Login or Register in order to submit comment