Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da fa'din " ai nasan idan na barka bacin komai zakayi ba shiyasa"....
" Ai ko yanzun ma ba ci zanyin ba Ammi, banjin cin komai Allah, farin cikin da nake ciki ma ya ishe ni....bari sai zuwa anjima can babu mamaki zan nema".
Da mamaki Ammi ke kallon sa har ya dasa aya a maganar tasa sannan tace..." Farin ciki ne zai hana ka cin komai Mu'een? yau ne ka fara ganin mu? ko kuma yau ne ka fara zuwa garin nan?"
" Ai yau 'din na musamman ne Ammi".
Yayi maganar yana murmushi.

" Kai de kasani"
ta fa'da tana murmushin itama,  while a cikin zuciyar ta ita ka'dai ta san tausayin sa da take ji, tasan cikar farin cikin nasa ba na ganin su ka'dai ba ne, sam bata son wannan fara'ar tasa ta 6ace daga kan fuskar sa, sai dai tasan wannan dole ne, ko ba yanzu ba, ko anjima ko gobe, sati, watanni ko shekara matu'kar mummunan labarin ya isa kunnuwan sa dole farin cikin sa zai yi masa 'kaura.

Har ya sumbaci goshin ta ya wuce ciki bata lura ba sai bu'de idanun ta tayi taga baya nan.

Tagumi ta zabga nan kan dinning 'din kawai tausayin sa na 'kara shiga dukkanin ga6o6in jikin ta.

Alhaji Baba ma yau har sai da aka idar da sallar maghrib kafin suka dawo cikin gidan tare shi da yaran nasa da duk suka ha'du a can masallaci.

Suna ha'duwa Alhaji Baba ya saki fara'a ya bashi hannu tare da fa'din...
    " ....sau'kan yaushe?"
" Tun jiya da safe Alhaji"!
Mu'een ya bashi amsa da fa'din hakan.
Alhaji Baba sai yace
"Ashe har ka tsufa gidan ma ni ban sani ba?"

" Ni ai har na yi fishi Alhaji, awanni na kusan biyu a garin nan amma ka 'ki dawowa ai da niyyya ta ma yanzu in bika can gidan gonar inga ko lafiya".
" Shi kenan ai yanzu kam tunda gani nazo, ayyukane yau 'din suka 'dan taru mana sai a hankali".

" babu laifi Allah ya taimaka"
Cewar Yah Deen kenan.

Koda suka shiga cikin gidan ma a parlour suka zauna shi da Alhaji Baba suna sake gaisawa, su Saif kuwa 'dakin su suka wuce dan dama basu zama da shi suyi hira, dama Alhaji ka'dai ne amma da Deen kam a a.

Ni kuwa da Ammi muna 'dakin ta tana duba Hisnul muslim yayin da nayi kwanciya ta daga gefen ta har bacci-bacci nake ji yana shirin dauka ta.

Mu'een bai yadda ya zauna nesa da Alhaji ba saboda tambayar da yake son yi masa dan haka gefen sa ya dawo ya zauna a hankali cikin ra'da yace " Alhaji Baba amana ta"!
Ido Alhaji ya 'dan bu'de yana kallon sa a 'ko'karin sa na ganin ya 6oye damuwar dake cikin ransa....cikin 'karfin hali yace da shi " amana wace iri?"

" Haba Alhaji, ai amana guda 'daya tak na bari a hannun ka kuma ita nake tambaya fa?"
ya 'karashe da shagwa6a wa Alhaji Baban.

Kasa juran kallon sa cikin yanayin Alhaji Baba yayi sai kawai ya kauda kansa gefe, sannan a hankali cikin basarwa yace " ai ni har na manta da batun ma gaba d'aya".
Mu'een zai sake yin wata magana sai Alhaji Baba yayi saurin mi'kewa tsaye bai jira jin komai ba kawai ya nufi hanyar 6angaren sa yana fa'din " idan ka gama ka sameni ciki mu 'karasa maganar".

Ido Yah Deen ya lumshe gami da mi'kewa tsaye shima ya wuce 'dakin sa, wata arniyar shadda ya ciro mai kalar sararin samaniya sabuwa dal ya sanya ajikin sa, agogo, hula da takalmi ma duk ba'a barsu abaya ba...ya dauki a'kalla kusan rabin sa'a kafin ya kammala shiryawan cuz cikin sanyi yake yin komai, can 'kasan zuciyar sa yake jin babu da'di sai dai bai san dalili ba sam.

  Sai da ya gama 'daura links 'din hannun rigar sa kafin ya sake taje gashin kansa, turare ya sake fesawa ajikin sa mai sanyin 'kamshi...sannan yaje ya maida kayan da ya siyo matan cikin leda cuz tun 'dazun bai sake bi takan su ba...da gama sasu cikin ledan sai ya ajiye gefen gado da niyyar da ya dawo daga wurin Alhaji kawai sai ya 'dauka ya wuce.

   Agogo ya kalla sannan ya fito a hankali yana gyara hular kansa ya nufi 6angaren Alhaji Baba, sallama yayi aka bashi iznin shigowa inda yaje ya samu Alhaji zaune har ya fito daga wanka ya shirya cikin farar jallabiya yana 'ko'karin shafa man zafi kan gwiwan sa.

A hankali ya 'karasa ya kar6i man zafin yana fa'din " Alhaji har ka fara abin tsoffi tun kafin ma kayi jika ko 'daya ko?"
Murmushin ya'ke Alhaji Baba yayi sannan yace " in bazaka yi ba bani abina ni".
" a a gashi inayi ai Alhaji".
Mu'een ya fa'di yana shafa man gami da 'dan massaging gwiwar a hankali.

'Dan satan kallon sa Alhaji Baba yayi sai ya cigaba da kallon gwiwar tasa " sai ina haka na ganka cikin shiri kamar me shirn barin gari?"
" Unguwa zani"
Ya bashi amsa a takaice.
" To bani abu na na 'karasa kar na 6ata ma lokaci...maza yi tafiyar ka".
Mu'een 'kara yin 'kasa yayi da idanun sannan yace
" A ah ai sai naji dahir daga bakin ka kafin zanje, kar inje a koro ni dan bafa sani na akayi ba Alhaji".
" Har ina ne haka?"
Alhaji Baba ya sake tambaya as if bai gane inda zancen Mu'een 'din ya dosa ba.
Sai da ya saki murmushi kafin ya biyo bayan ta da fa'din " zance fa zani...shiyasa ma na shirya da wuri dan ban son dare yayi sosai".

Ido Alhaji Baba ya lumshe cikin zuciya ya furta" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..."
A hankali ya sake furta sunan _Muhammad_ .

'Dagowa yayi ya kalle shi batare da ya amsa ba jin cikin lokaci 'kalilan muryar Alhaji Baba ta canza...'dan matsakaicin hasken 'dakin bai hana shi hango kwantacciyar damuwar da ta bayyana kan fuskar Alhajin ba.

".....Muhammad kar de kace min shirin zuwa wurin Amina kayi yanzun?"
Shiru Mu'een yayi bai iya yace da Alhajin komai ba kamar yadda bai iya cigaba da sake massaging gwiwar Alhajin ba illah ri'ke man da yayi yana kallon gefe....cuz shima zuwa yanzun ya fara jin bugun zuciyar sa na 'karuwa, fatan sa dai Allah ya sa alkhairi ne ke tunkaro sa, fargabar sa 'daya kar ace da shi an bada auren ta ga wani wanda ba shi ba.....
" Muhammad ka zauna ka saurare ni da kyau kaji...."
Yah Deen da jin haka sai ya d'ago ya kalle shi take y'ar guntuwar fara'ar da ta rage kan fuskar sa ta kau, dan ya fahimci akwai wani 6oyayyen abin daban da Alhaji Baba ke son sanar dashi wanda shi bai sani ba.

Jin cigaban maganar Alhajin ne ya dawo masa da tunanin sa, abinda ya tsinkaya cikin kunnuwan sa kuwa shine " Amina...fa ta jima da komawa ga mahallicin ta...."
Kallon da Yah Deen ya cigaba da yi masa ne ya sanya shi 'karawa da fa'din " ...ma'ana Amina ta rasu Muhammad sanadiyyan tashin ciwon....."

  Bugun zuciya mai karfi gami da fargaba ne suka ziyar ce shi lokaci guda...har ma bai san lokacin da ya 'dago hannun daman sa ya toshe bakin Alhaji Baba da shi ba....abinda kenan ya hana Alhaji Baba 'karasa maganar da yayi niyyan fa'da.

    Cikin in ina yace " Dan Allah...Alhaji kar kayi....min irin wannan wasan, ba zan...iya jurewa ba....".
Ya 'karasa maganar da girgiza kansa.

Baya ka'dan Alhaji Baba yaja tare da cire hannun Mu'een daga kan bakin sa, Yah Deen sai yabi hannun sa da kallo sannan ya cigaba da kallon Alhajin wanda ya cigaba da fa'din.

" Duk da yake ina yi maka wasa Muhammad amma wannan bai kasance cikin abinda zan yaudare ka dashi ba, ai nine mahaifin ka, kai kanka kasan bazan so abinda zai ta6a rayuwar ka ba, miye ma ribar yin hakan idan nayi?....mutuwa sau 'daya tak ake yinta Muhammad kuma shi Amina tayi, and kai kanka kasan idan an mutu ba'a dawowa....kayi mata addu'ah kaji, na 6oye maka tuntuni ne saboda gudun irin halin da zaka shiga amma banyi hakan da wata manufa ko kuma dan 6ata maka ba....."

Ido kawai ya tsurawa Alhajin, bama ya fahimtar komai, tuntuni maganar Alhajin ta farko take faman amsa kuwa cikin kunnuwan sa...... _" Mutuwa 'daya tak akeyi Muhammad kuma shi Amina tayi_ "..... abinda ke nan yake ta yi masa yawo a tsakar kansa.

Bai iya ya sake motsa ko da 'dan yatsan sa ba ne, sakamakon jin kalaman Alhajin cikin tabbatar wa, take 'kirjin sa ya ri'ke shi ga bugu da zuciyar sa keyi tamkar zata fito fili, bai ankara ba sai jin sau'kan hawaye yayi saman fuskar sa.
Bai damu da hakan ba kawai ya cigaba da kallon Alhajin cikin rawar murya ya nuna kansa sannan ya bu'di baki da 'kyar yake fisgan maganar yace" Alhaji...kana nufin...Amina Amina....ta rasu... tuntuni kuma ban sani ba?"

  Kai Alhajin ya jinjina masa alamar tabbatar wa.....
Take sai ya kai hannayen sa ya dafe kansa da yake jin yana juya masa ha'di da barazanar tarwatsewa, ga 'kirjin sa da ya yi masa nawi sosai jikin sa na faman kakkarwa.....kafin Alhaji yayi wani yun'kuri sai ji yayi ya saki 'kara mai 'karfi sannan ya saki kan ya dafe 'kirjin sa da duka hannuwan sa biyu hawaye na cigaba da bin kuncin sa.




~Kwana biyu kun jini shiru nima na rama ne~ 🤪


_Comment_
_Share_
_Vote_



*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)


By
*Salmerh MD*

 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*


🅿 *31*

'Karan da yayin ne ya janyo hankalin mu gaba 'daya, Ammi da dama take kan hanyar zuwa gurin Alhajin sai tayi saurin 'karasawa ciki.

A rikice ta shigo tana tambayar Alhajin " me ke faruwa?"

Alhaji Baba ri'ke yake da hannun Deen yana 'ko'karin kwantar masa da hankali amma ina sam ya rasa nutsuwar sa.
    Jin muryar Ammi da yayi ne ma ya sanya shi 'karfin halin mi'kewa cikin idanun sa cike taf da ruwan hawaye ya tsaya gaban Ammi.

Hannun ta na dama ya kamo ya 'daura saman 'kirjin sa saitin zuciyar sa yace " Ammi...kiji bugun zuciya ta, kiji irin 'ka'k'karfan soyayyar da nake yi mata...Ammi dan girman ki tausaya min kar kice min dagaske ne Amina ta rasu...Nanne ta tafi ta barni Ammi dagaske ne...?"
Sai yanzun hawayen sa suka gangaro kan kuncin sa, yana jin hakan amma bai kula ba still hankalin sa na wurin Ammi yana sauraran jin amsar bakin ta...Ammi kam duk jikin ta yayi sanyi bata ma san me zata ce da shi ba, bata san abin nasa har haka ya girmama ba, Muhammad 'din ta ne yau yake kuka da hawayen sa, kuma kukan ma akan mace.
Tsura masa idanu tayi tana kallon sa, tausayin sa na sake ratsa ta ji take tamkar ta taya shi kukan itama, amma tasan yin hakan tamkar ta fallasa asirin zuciyar ta ne.
     Ganin kamar yana 'ko'karin sulalewa 'kasa ne ya sanya Alhaji saurin 'karasowa ya tallafo shi wanda sai a lokacin Ammi ma ta ankara da hakan a firgice ta ambaci sunan shi tana tallafan 'daya gefen nasa.

Kai Mu'een ya girgiza mata idanun sa lumshe batare da ya amsa sunan shin da ta 'kira ba kawai ya fara fa'din ..."..me ya..sa..zaki tafi..ki barni?...Ammi me yasa...bata jira na dawo na sanar da ita 'dumbin soyayyar da na ke yi mata ba..."

" Haba Muhammad kai fa musulmi ne, me yasa kake fa'din irin wa'dannan kalaman...bacin kasan Allah ne ke da mutuwa ba mu ba".
Alhaji Baba yayi 'karfin halin fa'din hakan yana gyara masa kansa dake jikin sa.

Wasu hawayen ne suka sake gangaro masa da gudun su...idanun sa ya bu'de ya tsayar cak akan fuskar Alhaji Baba bakin sa na rawa da alamar magana yake son yi amma ya kasa saboda azabar dam'kar da zuciyar sa tayi masa da 'kyar ya iya fuzgan " Alhaji...dagaske....ta barni...?"
Kafin Alhaji yayi wani yun'kuri sai gani yayi Mu'een ya mi'ke sumamme a jikin sa.

Ammi kam tuni ta fara kukan itama cikin ranta take fa'din " wannan wani irin masifa ne?"
Ganin yanda ya mi'ke ne ya sanya ta rikice tafara fa'din _innalillahi wa inna ilaihi raji'un_ ... _Alhaji me yafaru what's wrong with him..?"_

     Cikin sanyin murya Alhaji Baba yace " ki kwantar da hankalin ki please...ba wani abu bane he just fainted".

Yana shafa cikin hannun Yah Deen ya fa'di hakan batare da ya kalli Ammi ba...shi kansa ya kasa nutsuwa gaba 'daya hankalin sa ya tashi, dama irin abinda tuntuni yake gudu kenan shiyasa ma ya kasa sanar da shi tun farkon faruwar lamarin.

  Ammi na jin cewa suma yayi ta tashi da sauri ta 'debo ruwa tana 'ko'karin she'ka masa Alhaji Baba ya dakatar da ita.
Da mamaki tace " me yasa kuma Alhaji...idan ansa masa ruwan zai ta shi ai".
Kai Alhaji ya girgiza mata sannan ya bu'kaci ta bashi wayar sa.

Wayar ta 'dakko masa yayi 'kira inda ya bu'kaci ganin wani likita dake unguwar tasu ya kuma sanar dashi abubuwan da yake so ya zo dasu sannan ya cire wayar daga kunnan sa ya ajiye ta gefe.

    Daga nan ya dai-dai ta kwanciyar Mu'een 'din ya kasance straight bai ko saka masa pillow ba ya barshi a hakan illah cikin hannun sa da ya cigaba da shafawa...yana tuna abinda ya ta6a gaya masa ranar da ya bashi amanar ta....".... _dan Allah Alhaji kar ka bari a aurar da ita ma wani, ina kammala karatuna zan dawo ka nema min auran ta....please...please Alhaji!, in kuma ba haka ba to kawai ka tanadi likkafani ka ajiye tun yanzu_ ..."
     Allah sarki....sosai tausayin sa ya 'kara kamashi ga tsoron halin da zai iya shiga sanadin hakan, jikin Alhaji Baba har rawa yakeyi ga gumin da ke faman keto masa, shi ka'dai ya san halin da yake ciki dalilin wannan lamari.

    Ammi kam zama tayi daga bakin gadon Alhaji Baba ta rafka tagumi tana share hawaye  tana kallon sa....amma tunanin ya tafi wani wuri ne can daban, tunanin har yaushe Muhammad ya san soyayya, yaushe ma ya fara son Amina da har zai 'dagawa kansa hankali saboda rasuwar ta....ko cikin ahalin ta babu wanda taga ya suma saboda rashin ta, ko ni da nake ta haukan damuwa da ita ban ta6a suma saboda rashin nata ba...amma dube shi, yana matashin saurayi da shi amma ji yanda ya maida kanshi saboda macen da ba ma tasan yana son ta ba..."
Sosai abin yake damun Ammi a zuci.


Ina daga parlour ni da su Saif muna zaune munyi jigum dan tun 'dazu da mukaji 'karar Yah Deen muka rage volume na Tv muka yi shiru, babu kuma wanda ya motsa daga inda yake illah hankulan mu da duk suka zama a tashe.... sallama muka ji daga bakin 'kofar parlour.
Zaidu sai ya tashi yaje ya bu'de...gami da gaishe shi.
  Likitan da ke ri'ke da 'yar jakan aikin sa sai ya bu'kaci ganin Alhaji Baba.

Sai lokacin Zaidu ya bashi hanya ya shigo jin cewa Alhaji ne ya 'kira shi, yana maida 'kofar yana rufewa sai yake bani umarnin zuwa in yiwa Alhaji Baba magana.

Banyi musu ba na tashi da sauri na isa 6angaren Alhajin na tura 'kofa a hankali da sallama a bakina...babu wanda ya amsamin illah 'dagowa da sukayi suka kalle ni bansani ba ko sun amsa min a zuci...ni kuwa tunda idanu na ya sau'ka a kansa mi'ke sai hankali na ya tashi sosai, Nannen mu kawai na tuna ranar da ta rasu a hannu na wanda ya kasance shine rana na 'karshe da na ganta..tun daga lokacin akace Nannen mu wai rasuwa tayi, da gama wannan tunanin take sai hawaye ya fara bin kuncina, kuma still ina kallon sa ban kuma iya na furta komai ba.

  'Bangaren Alhaji kuwa ganin na tsaya shiru ne ya sanya shi tambaya ta da fa'din " uwa ta ya akayi ne?"
Sai da na goge hawaye na kafin na ce da shi " wani ne yazo"
Nayi maganar ina nuna hanyar da na shigo kamar wata sokuwa.
Alhaji sai yace " maza je ki ce masa ya shigo, kuma ki daina kukan nan babu abinda ya faru da shi kinji".
   Da sauri na juya na ifmsar da sa'kon Alhaji amma ban iya na sake zama da su Zaid ba sai bin bayan likitan nayi, Allah ya taimake ni ma da ya shiga bai tura 'kofar ya rufe ba hakan sai ya bani daman shiga batare da sun lura da ni ba dan lokacin hankulan su yana wajen Yah Deen ne.

  Direct wajen Ammi na wuce na jinginu da jikin ta na yi shiru, Ammi kam hankalin ta na ga 'ko'karin da likita ke yi ne na ganin farfa'dowar Mu'een amma duk da haka Ammi bata kasa bani kulawa ba, bata kalle ni ba kam amma da hannun ta 'daya tayi 'ko'karin tallafoni zuwa jikin ta.

    Tsawon mintina uku likita na fama da shi kafin ya farfa'do da sakin ajiyar zuciya mai 'karfi.

Ammi da Alhaji Baba duk a fili suka saki hamdala Ammi har tana murmushi inda ta sake tallafa ta....wanzuwar likita awurin ne kawai ya hanata isa ta rungumi 'dan ta cikin jikin ta amma Allah ne ka'dai yasan yanda ta ji da'din farkowar tasa.

    A hankali ya bu'de lumsassun idanun sa wanda suke saitin inda muke zaune ni da Ammi.

     'Kara waro idanun nasa yayi akan mu saman la66a ya furta _" Amina...."_
Take Alhaji Baba da likitan duk suka juya suka kallo mu.

Ammi kam da bata ji maganar tasa ba ganin sun kallo mu ne sai ta tsorata da sauri ta mi'ke gami da kama hannu na muka isa gaban su tana tambayar su abinda ya faru cikin  harshen turanci.

   Ni kuwa ido na tsura masa ganin yana dafe 'kirjin sa kuma yana kallo na, a hankali sai na cire hannu na daga na Ammi na tsuguna agaban sa...idona cikin nasa cikin sanyin murya nace " Yah deen baka da lafiya ne?"
Bai amsa ni ba dan haka sai na cigaba da fa'din....kar ka yadda ka mutu irin na Nannen mu kaji...su Saif da Ammi suna sonka kuma idan ka mutu kuka zasuyi baza su 'kara ganin ka ba".

Maganar da nayi ne ya sanya shi rintse idanu da 'karfi sai a lokacin ya fahimci cewa ni 'din ba Aminan sa bace, ya san Aminan sa bata shirmen magana kamar ni.


Idanun sa a rintsen likita ya gwada B.P 'din sa sai yaga bai hau ba...yana cire abin sai ya fara yunkurin mi'kewa da sauri likitan ya tallafo shi har suka mi'ke tsaye.
" Ina zaka ne wai Muhammad?"
Alhaji Baba ya tambaya yana mi'kewan shima... a hankali da rawar murya yace " 'daki... na".
Shiru suka yi masa dukkan su, inda Alhaji Baba ya iso ya kama shi da kyau yayin da likita ya tsaya ya tattari tarkacen sa sannan ya bisu abaya nima ganin Ammi ta bisu sai na bita da sauri.

Shigar su parlourn ne ya sanya su Saif saurin mi'kewa duk jikin su sai ya 'kara yin sanyi da ganin yanayin da 'dan uwan su yake ciki, tamkar ba 'dazun yazo garin da 'kafafun sa ba.
     
   Likita ne ya fara shiga sai ya ri'ke musu 'kofa suka shigo sannan Ammi ma ta shiga, ina 'ko'karin shiga sai Zaidu ya ri'ko hannu na a hankali yace " me zaki je yi ke kuma?"
Ban bashi amsa ba kawai na sanya kuka ina 'ko'karin 'kwatan hannu na ni dai burina ya barni in je..." let her go please Zaid".
Saif ya fa'di yana kallo na.
Take kuwa sai ya sake ni...na kuwa kama hanyar 'dakin na shiga.

    Lokacin da na shiga Alhaji Baba na cire mai rigar Jumps da ke jikin sa sai ya rage masa sauran farar singlet ne da dogon wandon kayan....a hankali ya komar da shi ya kwantar Ammi ta dai-dai ta masa pillow akan sa.

Numfashi yake fitarwa da 'karfi wanda duk sanda zaiyi sai kaji ya fitar da sauti har 'kirjin sa na hawa da sau'ka sosai...in kin ganshi a lokacin gwanin tausayi Hafsat tamkar ba shine Mu'eenuddeen 'din Uncle Ja'afar ba".
Nuree ta fa'di tana kallon fuskar Hafsat da murmushi kan fuskar ta.

Hafsat ma murmushin tayi sannan tace " Sharrin zuciya ne ba laifin sa bane ai, kinsan so mugun cuta ce sam bata da da'di".
"Hmm"
Kawai Noor ta ce sannan ta cigaba da bata labarin.

" Allurar bacci kawai Alhaji ya bu'kaci ayi masa kafin gobe dan haka batare da 6ata lokaci ba likitan yayi masa nan take.

Har a lokacin kuma ina tsaye ina share hawaye na, har ga Allah tausayin shi nake ji sosai duk da bansan meke damun sa ba amma yanayin sa ba 'karamin karya min zuciya yayi ba, ga kuma tunanin Nannen mu da ya tsaya min cak a zuci banaso ace shima ya mutu irin na ta a daina ganin sa...har cikin raina nake jin banason hakan sam.

Likita na cire Allurar sai nayi saurin 'karasawa gaban gadon na dur'kushe gwiwa na daga 'kasa tare da kamo hannun sa 'daya na ri'ke da duka hannuwa na.... na cigaba da kuka na.
Idanun sa dake lumshe ya bu'de a hankali, yana kallon fuska ta sai yayi murmushi mai kyau mai sanyi mai kuma tsaywa a zuciyar wanda ya san muhimmancin ta.....dishi-dishin da yake gani a lokacin ne ya sanya shi kasa tantantace kamanni na...a hankali ya bu'di bakin sa ya ce da ni ".....Amina ai baki mutu ba ko?....ai dama nasan bazaki tafi ki barni ba..."
Yayi maganar yana kallon fuskata.

Ban damu ba duk da sunan Amina da naji ya 'kira ni da shi ban kuma san manufar hakan ba, ni dai fatana kar shima ya mutu irin na Nannen mu, bansan me yasa na damu da hakan ba tun a wancen lokacin...nafi son rayuwar sa fiye da rashin sa duk kuwa da cewa ba wani 'kwa'k'karan ala'ka ce tsakani na da shi ba.

  Hannun sa naji kan fuska ta yana share min hawaye na batare da ya sake magana ba...su Ammi kam kallon mu suka tsaya yi da mamaki jin sunan da ya 'kira dashi, wanda sai a lokacin ma Ammi da ta 'kura min ido sannan ta fahimci kammanin dake tsakani na da Nanne, bata ta6a lura da hakan ba sai yanzu, sosai kuma muke kama da ita abinki da jini kinsan ko babu kamar ma dole sai an gani ta wani 6angaren, sai dai haske kawai da Nannen mu ta fini dashi da kuma karan hanci....
Yana gama share min hawayen ya sau'kar da hannun sa tare da sake lumshe idanun sa a hankali inba a kusa da shi kake bama baza ka ta6a jin abinda yace ba...ni dai dake tsugunne gaban sa naji yace "....do not ever leave me...plea...se?"
Daga haka bai sake magana ba.
Alhaji ne ya tambaye ni abinda yace dan yaga bakin sa yayi motsi,  ba ma iya fa'da zanyi ba dan ban fahimce shi ba a lokacin da yake ban gama koyon turanci ba ni, Saif ne ma yake 'ko'karin koya min kuma ya kan min magana da shi wani sa'in shiyasa nake 'dan ji ka'dan-ka'dan....so naji abinda yace kuma zan iya fa'da a baki amma bansan nufin sa kan hakan ba.
Ina shirin maimaitawa Alhaji Baba abinda naji ya fa'da ne sai Ammi ta riga ni fa'da masa...ashe itama taji.


   Kallon sa kawai Alhaji yayi sannan ya kalle ni, ni kuwa ban ma san yana yi ba.

     Suna ganin ya samu baccin Alhaji Baba yayi godiya wa likitan anan yake sanar da shi cewa babu mamaki ma ya tashi da 'dan 'karfin jiki koma babu ciwon tunda da farin ciki yayi baccin cuz har a lokacin idan ka dubi fuskar sa zaka hango kwantaccen murmushi akai.

  Godiya sosai Alhaji Baba ya sake yi masa sannan ya sallame shi, tare suka fita daga 'dakin ya raka shi, nima suna fita na mi'ke na fita ina goge fuskata.

Ammi ce dai bata fita ba sai da ta 'dan kintsa 'dakin tukunna, wanda ga rin hakan ne ta ci karo da jakar da ya saka kayan da siyawa Aminan sa.

Ammi zazzage su tayi da mamaki take 'dagawa take gani, sosai tausayin sa ya 'kara kamata dan a zahiri zaka fahimci zazzafan soyayyar da yake yiwa yarinyar.

Tun lokacin da na fito sai na isa gefen Saif na raku6u jikin sa nayi shiru...shima shirun yayi, Zaid kuwa da idanu kawai

Please Login or Register in order to submit comment