Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yamma da zai fita sallar maghrib ne ya 'kira ta ya sake tambayar ta dan tabbatarwa nan kuwa tayi shiru bata musa masa ba..kai Malam Barau ya jijjiga sannan yasa kai ya fita zuciyar sa cike da tausayin halin da Ma'u ta sanya rayuwar ta ciki.

Sai da ya idar da sallar maghrib kafin ya nufi unguwar mu gidan Alhaji Baba.

Lokacin shima dawowar sa kenan daga sallahr maghrib yana zaune cikin gida yana shan iska Malam Barau yayi sallama.


Duk da bai ta6a kawo masa ziyara ba amma Alhaji Baba yaso su shiga ciki sai dai Malam Barau ya 'kiya ya nuna ba komai nan 'din ma yayi, nan suka zauna cikin gidan dan aganin sa nan 'din zai fi sirri tunda suna ganin kowa.

Bayan gaisuwa cikin natsuwa yayiwa Alhaji Baba bayanin abinda ke faruwa agidan sa da kuma sunan 'dan sa da ya fito cikin lamarin.


Abu 'daya da Alhaji Baba bai ji da'din sa ba shine lalata musu yarinya da Yah Deen yayi, amma bayaga haka bai ji lamarin matsayin ba'ko agare shi ba cus ya jima da zargin Mu'een na aikata irin hakan tun ba yau ba.


Ba 'karamin 6aci ransa yayi ba, iya 'kolouwar 6acin rai ranar sai da yajita dan har kasa magana yayi ko ya fara sai ya carke zuciyar na 'kullewa, daga 'karshe dole Malam Barau 'din ne ya dinga bashi ha'kuri yana kwantar masa da hankali ganin halin da ya shiga sannan yayi masa sallama ya tafi.

Ya san in ba sharrin yara ba ai Alhaji Baba yafi 'karfin aje har gidan sa ayi masa titsiye akan irin wannan abin, mutun ne shi mai matu'kar mutunci sanin girma da kuma kwarjini.

Har akayi sallar Isha'i Alhaji Baba bai sani ba, sosai ya fa'da duniyar tunani, halayyar Mu'een tsoro take bashi ayanzu...har a yanzun ma nawa yake da har ya za6awa kansa irin wannan rayuwar...kuma ma ya rasa 'yar wa zai lalata sai yarinyar Malam Barau dake suke cikin gari 'daya, da wani irin idanu yake so adube shi ne sam bai sani ba.

Sai da 'karfe tara na dare  ta gota kafin ya iya tashi a wurin ya shiga ciki...alwala kawai ya iya 'daurawa ya gabatar da isha'i daga haka ya kishingi'da har gari ya waye yana istighfari ga mahalicci, bai san inda Mu'een ya samo wannan halayyar ba sam...bai kuma san ya zai yi da shi akan hakan ba da ya wuci Addu'ah...shiyasa ya mi'kawa Allah komai...da fatan ubangiji Allah ya shirye shi.

Hankalin sa bai 'kara tashi ba sai da yaje gidan Malan Barau yaga Ma'u, cuz washegari da sassafe ya isa gidan.

Ganin 'kan'kantar yarinyar sosai ya karya masa zuciya, ransa ya 'kara 6aci da Mu'een sosai....da yake ta 'dan rame kwana biyu idan ka ganta bazaka ta6a tunanin tafini shekaru ba. ..shiyasa ko Alhaji Baba ma tashin farko da ni ya 'kiyasta shekarun Ma'u.

Cikin ransa ya 'kuduri aniyar ko Mu'een zai mutu kuwa idan har Allah ya sau'ke ta lafiya dolen sa sai ya aureta tunda shi ya lalata mata rayuwa..in ba hauka bama yarinya 'karama irin wannan me ze kai tunanin mutun kanta.


A fili kuwa ha'kuri ya dinga bawa Malan Barau cuz jiya bai samu daman bashi ha'kuri ba...kafin ya tafi sai da ya ciro ku'di kimanin 20k ya dan'ka a hannun Ma'u da sunan ta kula da kanta dashi kafin aga yanda hali yayi.

Bakuma wai yayi hakan bane saboda ya goyi bayan Mu'een akan cikin ba a a, kawai ba yadda zai yi ne tunda abinda ya faru ya riga ya faru bai kamata kuma a 'kara 'daga mata hankali da tozarci ba shiysa ko Malam Barau 'din ha'kuri Alhaji Baba ya dinga bashi akan Ma'un kan cewar kar su 'daga mata hankali, yasan da wahala abinya zama laifin ta.

Shi kansa Alman Barau yayi wannan tunanin sai dai shi ya ajiye ne akan raina matsayin su da Yah Deeb yayi ne ya sashi lalata musu yarinya.

Idan baka sani zaka yi zaton duk abinda Alhaji Baban ke yi bakomai bane face goyawa 'dansa baya bisa abinda ya aikata...sai dai da zaka bincika zuciyar sa shi ka'dai yasan abinda ya 6oye, shi ka'dai yasan 'kuncin da yake ciki...shi ka'dai yasan yanda ransa ya kai 'kololuwar 6aci da Mu'een kan lamarin.

Malam Barau kamdamuwar ta 'dan ragu tunda Alhaji Baba bai goyi bayan 'dansa ba ya yi na'am da batun dama shi tsorin sa kenan kar ace basu kar6i cikin da be san inda zai sa ransa ba saboda ba'kin ciki.

Ko Ammi Alhaji bai sanar da ita abinda ke faruwa ba ya bari kawai cikin zuciyar sa, haka bai yi magana da Mu'een akan lamarin ba haka ma Uncle Ja'far.

Yah Deen na 'kiran sa suna gaisawa kusan kowacce safiya amma bai ta6a nuna masa alamun komai ba, gasiuwa kawai sukeyi kamar yanda suka saba a 'yan kwanakin, ba wannan zolaya da wasan tuni shiyasa ma ko da yaji yanayin Alhajin wani iri bai sa akan sa ba.

A makarantar mu naji ana gulmar wai ai Ma'u tayi cikin shege ne shiyasa bata zuwa makaranta har akayi jarabawa bada ita ba, lokacin kuwa ana gobe za'a bamu hutu ne.

Haka nazo na samu Ammi da maganar amma sai ta kwa6e ni da fa'din wai ita bata son gulma..in daina saka kaina cikin shirgin da bai shafe ni ba.

Baki na naja nayi shiru ban 'kara tada maganar ba.

Ranar hutu kuwa murna ni kaina murnar nake yi saboda ayau ba sai gobe ba su Saif zasu dawo gida...sosai nayi kewar su abin ba'a cewa komai.


Ana tashi ko tsayuwa na fahimci abinda ke faruwa ban yi ba saboda murna yau zanga abokai kuma 'yan uwana.

Ashe bayan tafiya ta akayi kwanba aka tafi gidan su Ma'u da sunan gaishe ta ashe tsabar gulma ce tsantsa ta kaisu.

Daga ranar kuwa kuwa labari ya watsu ko'ina cikin gari cewa Ma'u tayi cikin shege da 'dan Alhaji.

Maganar har kunnan Ummah ta sai da bata ce komai kan lamarin ba...ko ni banji a bakin ta ba...Addah ta Saudah ma da ta same ta maganar birki ta taka mata da fa'din ku dinga kyautata zato wa mutun".
Dole Addah Saudah taja baki tayi shiru tunda bata ga fuska wurin Ummahn mu ba, sai dai abin ya dame ta sosai cikin zuciya musamman da yake tasan cewa matsayin matar sa nake a lokacin nice kawai ban sani ba.








Comment
Vote
Share





*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)


By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *58*

Mu kam muna ta murna da farin cikin ganin juna ni da su Saif ko fita bamuyi ba, Saif sun girma sun 'kara tsayi da fa'di kamar basu ba...ganin yanda nake 'ko'karin sakan jiki da sune ya sanya Ammi ta 'kira ni ta ja min kunne sosai akan.hakan...tace tsakani na dasu maganar baki ce kawai bata so taga ko hannu mun ha'da dasu saboda Allah ya haramta hakan tsakanin mu a yanzu tunda mun girma.

Hakan kuwa akayi dan ko da wasa ban ta6a kuskuren tsallake maganar Ammi ba ina kulawa da komai tsakanina da su Saif...balle Zaid kam ma dama sama-sama muke da shi har yanzu.

Duk mu da muke cikin gidan bamu ji labarin komai ba, gara nima ranar naji ana gulma akan Ma'un amma da Ammi ta kwa6e ni kan zancen shikenan ban kuma tada maganar ba haka kuma ban sa aka ba.

Anty Zainab ma muna yawan gaisawa da ita, da yake ma already ta koma Taraba so sai a waya muke ha'duwa kawai.

Kwatsam ranar sai ga waya daga mahaifi na da wata safiya, inda yake ro'kon Alhaji Baba da ya bari akai Hudah (ni) 'dakin mijina, bai fito fili ya fa'di dalilin sa na yanke wannan hukuncin ba amma duk da haka Alhaji Baba ya fahimci dalilin da ya sa shi fa'dar hakan cuz dama yasan lamarin ba zai ta6a 6oyuwa ba.

Cikin kwantar da murya yace da Baban mu
" Wai da ni cewa nayi idan yazo kawai ya sakam min ita tunda dama can bai san da maganar auren ba kaga shikenan...."
Taran sa Baban mu yayi da fa'din" A a Alhaji kar ayi haka, abashi matar sa kawai rabuwar ai bata da wani amfani".

Alhaji Baba zai sake magana sai Baban mu yayi saurin fa'din" Dan Allah Alhaji kar kace komai...kawai ni dai na ce abashi matar sa".

Dole tasa Alhaji Baba yin shiru ganin cewa mutun dattijo irin Baban mu ke ro'kon sa akan 'dan wannan lamarin yasan abin ya girmama ne...duk da yasan kawai dauriya ce yayi har ya sa shi iya yanke hukuncin akai ni 'dakin mijina alhalin yasan 6oyayyar halayyar mijin nawa.

Sai da ya zauna yayi nazari sosai akan hakan kafin for the first time tun bayyanar cikin Ma'u sai yau ya sami Ammi da maganar inda yayi mata bayani filla-filla harda abinda mahaifina ya fa'di.

Ammi kam shiru tayi saboda tsabar mamaki, wai jin Mu'een 'din ta ke da wannan alhakin, sai dai bata jin zata iya barin 'yar ta zama tare da shi, tunda rayuwar da ya zabarwa kansa kenan sai yaje yayi tayi...ita bata san me zata ce da shi ba.

Da yake ita ba shiga cikin jama'a take sosai ba dama da Ummah ta suka fi zumunci a kaf 'din garin , Ummah ta kuwa nasan koma menene zai faru bazata ta6a bu'dan baki tayi mata bayani ba...musamman ma da yake abin ya shafi 'dan ta ne na cikin ta.


Ammi kam bata 6oyewa Alhaji Baba ba take ta bu'di bakivta bayyana masa cewa ita bazata ta6a yarinyar ta zama da shi ba tunda haka halin sa yake...wannan abin.kunya da me yayi kama, mutun haka kawai batare da an tambaya ko matsa shi bavya 'dau ki kyauyar yarinya sukutum ya basu auren ta amma sai gashi tun ba'aje ko'ina ba sakayyar da zai musu kenan...hawaye Ammi take tsiyayar wa tsabar takaicin halin Yah Deen...cikinvranta take tuno ranar da ya ta shirga mata 'karya akan case 'din sa da Alhaji Baba akan Husnah ashe ninke ta yayi abai-bai har ta yarda shi cewa ba komai ke tsakanin sa da ita ba...ga shicda Allah ya tashi kama shi sai yasa shi aikatawa a inda bai isa ya musanta ko 6oye abinda ya faru ba...tace wallahi yarinya ta tafi 'karfinvta zauna da mazinaci yake can ya nemi irin sa amma ba 'yata ba.

Da 'kyar Alhaji Baba yata bata baki gami da convincing nata ta sau'ko bisa umarnin mahaifina yace baya so yaga kamar ko bai ji maganar sa bane shiyasa amma ko shi ba so yake yi ba da niyyar sa araba auren kawai amma bakomai su cigaba da addu'a kamar yadda Baban mu ma ya fa'da....zai bashi Hudah amma bisa shara'di..Ammi hawauen ta kasa tsayuwa yayi, takaicin halin Yah Deen take sosai, tarasa meyasa ya za6arwa kansa irin wannan rayuwar...ace tun a yanzun sa ya san ya bibiyi mata to gaba idan ya fi haka shekaru kuma bata san me zai aikata ba...fatan ta kawai shine Allah ubangiji ya shirya mata shi. 

Babu wanda ya bi takan sa har a lokacin, Ammi.bata 'kira shi haka ma Alhaji Baba...Sai dai shi Mu'een ne kan 'kira Alhaji su gaisa dan Ammi kam ma yanzu ko 'daukan wayar sa bata yi...da farko abin na damun sa saboda be san dalilin hakan ba amma daga baya sai ya share da yake suna waya da Alhaji kuma bai ta6a sanar da shi cewa akwai matsala ba..hakan yasa a kullum sai dai ya bada sa'kon gaisuwa yace a gaida su...ga shi Imrana ma tuni yana Kano shiyasa ma bai san da labarin abinda ke faruwa cikin garin nasu ba.


*****
Cikin Ma'u nada wata uku sannan Yah Deen suka dawo hutu wanda yazo da tsananin son ganin mahaifiyar sa dan ba 'karamin kewar ta yayi ba...amma cikin rashin sa'a ko da yaje sam Ammi bata wani nuna alamun jin da'din ganin sa kamar yadda ta saba ba.

Ko gaisuwa ma da yayi mata bata amsa ba sai ma ta tashi ta bar shi a wurin zaune.

Baki bu'de ya bi hanyar da ta fice da kallo cike da mamakin dalilin da ya kawo hakan.
  Duk iya tsawon tunanin sa bai iya ya tuno laifin da yayi mata ba....ya kwashe a 'kalla kusan mintina ashirin bai ko yi motsin kirki ba saboda damuwa.

Wai yau Ammin sa ce ke share shi bayan tsawon watannin da suka 'dauka basu ga juna ko jin muryar juna ba? 

Bai iya ya bar gidan ba har Alhaji Baba ya dawo wanda bayan gaisuwa sai ya fara shigar da 'korafin sa kan Ammi kamar zai yi kuka...Alhaji Baba kuwa ce ma yayi" Abinda ya dace da kai kenan Muhammad..ko nima daka gani ina amsa gaisuwar ka ne saboda wasu dalilai amma abin kunyar da ka jawo mana cikin garin nan hukuncin da yafi haka ya dace ya hau kanka....nan Alhaji Baba yayi masa maganar cikin da yayi wa Ma'u inda yai masa ba da'di cike da 6acin rai ya nuna masa kuskuren sa...jikin Alhaji har na karkarwa saboda 6acin rai...shi kansa Yah Deen hawaye yake tsiyayarwa jin yanda mahaifin sa ke faman yin Allah wadai da halayyar sa..yasan ba 'karamin 6aci ran Alhaji Baba yayi ba.

Ammi kam ko kallo ma bai ishe ta ba, tsaf ta fice a harkar sa ta daina ko kallon inda yake, yayin da tashin hankalin jin abinda ya faru a bayan san ya matu'kar 'daga masa hankali, bai ta6a yin tunanin yarinyar zata iya 'daukan ciki ba dayake ya bata magani daga baya kafin ta tafi...wancan karon da Husnah ta samu cikin sa hankalin sa ya tashi sosai har yasa shi zubar da cikin saboda gudun kar iyayen sa su san abinda take aikatawa, to sai gashi da Allah ya tashi kama shi yanzu sai  labarin ya fito daga bakin mahaifin sa...'karshen tika tikin tik...'karya ta 'kare ya zaiyi kenan...ya zaiyi ya iya kallon mahaifin sa ya 'karyata wannan batu, ya zaiyi ya raba Ma'u da wannan cikin kafin ta haife sa...ina zai je da 'dan shege 'dan da ba ta hanyar aure ya same shi ba? _Uncle Ja'afar_ mutumin da ya fa'do ransa kenan a dai-dai lokacin take sai ya rintse idanu yana maimaita kalmar...innalillahi wa inna ilaihir raji'un.

Kwata-kwata ma ya manta da faruwar wani lamari tsakanin su kwatsam sai ga wannan mummunan labarin, ji yake tamkar ya bu'de 'kasa ya shige ciki...yanzu iyayen sa sun riga sun san 6oyayyiyar halayyar sa...yanzu kenan kowa kallon mazinaci zai ri'ka yi masa? Mai lalata 'ya'yan mutane.

Abubuwan duk sun taru sun yi masa yawa...ga fushin Alhaji, ga Ammin sa, ga tsoron kar Uncle Ja'afar yaji, ga shi 'karfi da yaji yana ji yana gani za'a haifa masa 'dan da ba na Sunnah ba kuma na shicda ikon hana faruwar hakan sam, ga tarin abin kunya ga kuma wai inji Alhaji Baba dole sai ya aure ta bayan ta haihu uwa uba ma kuma wai ya ha'da da matar sa su zama biyu...abin ya 'daure masa kai sosai, ina ya samu mata shi da har za'ace ya ha'da su su zama biyu...tunda yake a rayuwar sa bai ta6a jin kansa cikin tsananin damuwa da tashin hankali irin na yau ba, tafiya yake amma sam bai san inda yake saka 'kafafun sa ba...gaba 'daya hankalin sa baya jikin sa bai san inda ya dosa ba.


Tafiya ya ringa yi kawai cikin duhun daren yana tunani, wanda tashin farko kawai tsintar kansa yayi kan barandar makaranta...nan ya zauna ya du'kufar da kansa yana kallon 'kasa hannayen sa sar'ke cikin juna...nazari yake so yayi amma gaba 'daya ya rasa ta inda zai fara, duk abubuwan zuwa suke yi suyi masa karo a zuci.

Nawin da yaji 'kirjin sa nayi masa ne a lokacin ya sanya shi komawa ya kwanta da bayan sa hannun sa 'daya dafe da 'kirjin nasa yayin da ya dafe kansa da 'dayan hannun...bai ta6a tunanin akwai ranar da zai tsinci kansa cikin irin wannan halin ba sai yanzu da ya yaji shi aciki gashi ya rasa hanyar 6ullewa.

Bai san tsawon lokacin da ya 'dauka yana a hakan ba sai kawai jin 'kiraye-'kirayen sallah Asuba yayi.

Idanun sa nawi suka yi masa ga zogi lokacin da yake bu'de su ganin inda ya tsinci kansa ne ya sa shi saurin tashi zaune, mamaki ya so kama shi amma tuno abinda yake faruwa da shi ya wanki mamakin sa gaba 'daya.


Cikin hasken alfijir 'din dake haskawa ya tashi a hankali ya lalla6a ya isa gidan sa...sai da ya watsa ruwa ya saka jallabiya sannan ya tada sallar asubah wanda a lokacin har ma an idar a masallaci gari ya fara haske.

Da idar da sallar ko azkar bai tsaya yi ba kawai ya lalu6o wayar sa ya dannawa Imrana 'kira...wanda cikin sanyin murya yayi masa bayanin komai da ke faruwa harda zafin da iyayen sa suka 'dauka akansa da kuma hukuncin da Alhaji Baba ya yanke akan sa.

Imrana kam kwantar masa da hankali ya ringa yi da fa'din kar ya wani 'daga hankalin sa ba abinda zai faru...dama ai haka a rayuwa, balle wannan da ya kasance kuskure ne yasa har asirin abin ya tonu amma  Insha Allahu komai zai wuce in auren ne ma ba sai ya aure tan ba kawai indai hakan zai sa hankalin su Alhajin ya kwanta...rayuwar gidan sa kuma ai a hannun sa take sai yadda ya so yayi agidan sa.

Duk maganganun Imrana ko guda daga ciki bai ji ta sau'kar masa da natsuwa ba...hakan yasa ma daga 'karshe ya daina fahimtar sa...sallama kawai sukayi ya ajiye wayar yana tunanin 'kiran Antyn sa Zainab dan yasan zata bashi shawarar da ta dace...sai dai ko giyar wake yasha ba zai ta6a 'kiran ta cikin wannan halin ba...dan yasan idan taji labarin kamar Uncle Ja'far yaji ne.

Shi fa tun bayan tafiyar sa makaranta bai sake tunawa da batun wata Ma'u ba balle abinda ya shiga tsakanin su..bai sani ba ashe harda ajiya yayi ajikin ta...abinda yafi 'daga masa hankali ma shine jin labarin cikin...sai kuma maganar da Alhaji Baba yayi kan cewa ya shirya da zaran Allah ya sau'ki yarinyar lafiya dolen sa ya aure ta ya ha'da ta da matar sa su zama biyu...In yaso yaje can shi ya sani...kuma ko da wasa ya kuskura ya cutar da guda daga cikin su bazai ta6a yafe masa ba...." _Yah Allah ka yafe min_ "
Ya furta a fili.



*****
   Mamakin sa bai tashi 'karuwa ba sai da iyayen sa suka zaunar da shi bayan kusan 1 week da dawowar sa kan batun matar sa wai...karo na farko da magana ta ha'da shi da Ammin sa tun dawowar sa, inda tayi masa garga'di mai zafi kan 'yar ta ta kuma nuna masa cewa ba son ranta bane zaman sa da Hudah...kawai dai dan mahaifin ta ya matsa akan akai ta 'dakin mijinta ne bayaga haka da bata san mai zai sa ta ha'da jini da shi ba.

" _Da gaske auren ne da ni kenan?_ Ya tambayi zuciyar sa...kansa 'kasa lokacin da yji sunan Hudah ya fito cikin maganar iyayen nasa, ya so ya 'daga kansa saboda mamaki amma sam ya kasa bayyana mamakin sa a fili cuz har yanzu nawin mahaifan nasa yake ji...fatan sa Allah yasa ba wannan 6eran Hudahn da ke gidan su bane.


Kamar wasa abin shi dai kawai shiru yayi yana bin komai da idanu tare da sauraron kalaman nasu...duk da halin da yake ciki a lokacin amma hakan bai hana shi murmushin takaici ba da yaga zahiri cewa wai Hudahn Ammi ce matar sa...yaushe hakan ya faru sam bai sani ba.

Akan yarinyar nan ne shine Ammi ke cewa in ba dole ba bazata ha'da jini da ni ba?
Me Ammi ke nufi kenan?
Tana nufin yarinyar ce jinin ta ba ni ba?


Kansa 'kasa ya lumshe idanu take fuskar Nanne ya bayyana cikin brain 'din sa..." _Allah yayi miki Rahma ya sa hutun ki kenan_ "...Cikin zuciyar sa ya furta hakan yayin da a fili babu wani yanayi da zaka iya fassara shi saman fuskar sa.

Sam ya rasa dalilin da ya sa bai ji haushin komai ba koda labarin cewa Hudah matar sa ce isa kunnuwan sa...shi kansa ya kasa tantance ainahin halin da zuciyar sa take ciki kan hakan.


Harcya isa gidan sa yana tunanin yausgechakan ya faru? Yaushe aka 'daura auren sa da ita bai sani ba.

Tuno maganar da abokan sa suka yi masa ranar da suka dawo daga Azare wurin 'daurin auren sa ya sa ya zargi wani abu..." _Ai shi yasa nace maka mai abin mamaki domin har gobe ango kake mijin amarya kuma..."_
Maganar Anas ya tuno wanda ya fa'da masa ranar 'daurin auren saxda Husnah bayan suna da tabbacin cewa an riga an fasa auren sa da Husnah ...to mecyasa shi fa'din hakan kuma....?
Kenan duk 6oye minvsuka yi alhalin sun san gaskiya, sun san cewa da Hudah aka 'daura min aure kuma suka 6oye min.

Laifin Ishaq ka'dai yafi gani kan hakan saboda duk cikin su ya fi kusanci da shi....take ya 'kira shi a waya ya tambaye shi gaskiyar lamari.

Tunanin Ishaq ko a wai-wai yaji zancen shiyasa yaso 6oye masa but take Mu'een ya nuna masa cewa yasan komai amma miye dalilin su na 6oye masa iya tsawon lokacin nan..?"

" Kayi ha'kuri Mu'een..umarnin Alhaji Baba ne kuma kasan yafi 'karfin hakan a wurin mu shiyasa bamu sanar da kai ba.."

Tsaki yaja tare da yanke wayar ya ajiye gefen sa..kishingi'da ya koma yayi yana jin ba da'di...tun dawowar sa garin nan bai samu natsuwa ba...har 'yar rama yayi saboda ko abincin kirki baya samun lokacin ci ga damuwa da yayi masa yawa.


Ni kuwa gidan mu wurin Ummata aka maidani wai zanyi 2weeks acan kafin akaini gidan miji na...ban sa damuwar komai cikin raina ba...ni dai kawai abinda ba naso shine zama da shi, kuma ma tun kafin na baro wurin Ammi kullum sai ta kwantar min da hankali tana bani baki akan in daina tsoron sa kuma duk abinda ya min inzo in sanar da ita zatayi maganin sa.

Ban ta6a sanin cewa Yah Deen na da ala'ka da cikin jikin Ma'u ba har sai da na koma gidan Ummah ta...anan da muka ke6e da Addah ta Saudah take min gulmar wai ai su Ammi sun san cewa manemin mata ne shiyasa suka aura masa ni dan mugunta...yanzu kuwa da halin sa ya bayyana kowa ya sani cewa shine yayiwa Ma'un Malam Barau ciki shine kuma za'a wani ce za'a kaini gidan sa matsayin matar sa..."


Abin ya matu'kar kulle min kaina jin batun Addah Saudah...amma duk da hakan ban wani damu sosai ba...sai dai har yanzu cikin zuciya ta banjin cewa ina son zama da shi.

Nasan ma in ba dan Addah Saudan ba in dai dan Ummah ta ne bazata ta6a yimin zancen ba...banda ma nasihar zaman ha'kuri kullum babu abinda ke shiga tsakani na da ita.


Yayah Usman baya gari haka ma Baban mu...sai dai duk sun 'kira munyi waya da su kuma sun turo ku'din da za'a min siyayyar kayan 'daki na da shi...har Ammi taso hanawa wai ai wannan hakkin tane amma iyaye na suka 'kiya dole ta ha'kura amma tace ita zata min komai na kitchen ta ro'ki kar asayi komai.

Wannan 'din kuwa aka bar mata hakan ma da 'kyar Ummah ta ta amince..kusan kullum sai munyi waya da Baban mu inda da kansa cikin natsuwa batare da ya dubi 'karancin shekaru na ba ya bani kaf 'din labarin tun farkon dalilin kafuwar aure na da Yah Deen...saboda acewar sa abin ya shafe rayuwa ta ne kuma kar inga kamar ba'a yimin adalci ba.


Yace lokacin da Alhaji Mamman yaci amanar su ya bayar da auren 'yar sa ga wani sai dukkan su ransu ya 6aci gashi ba laifi sun gayyaci mutane da dama kuma kowa zaman sauraron jin 'daurin auren yake yi...yanayin da yaga Alhaji Baba abin sam bai masa da'di ba..yace to a lokacin sai yayi tunanin me ze hana a 'daura dani tunda duk matsayin 'ya'ya muke a wurin Alhaji Baban kuma ba haramcin auren tsakanin mu.

Yace Ja'afar 'kani ga Alhaji Baban ya ja gefe yayi masa bayani badan komai yayi hakan ba kuma sai dan rufin asirin juna...take kuwa Uncle Ja'afar ya amince kuma shine ya kai labarin kunnan Alhaji.

Take batare da 6ata lokaci ba aka 'daura mana aure kan sadaki dubu 'dari cif Alhaji

Please Login or Register in order to submit comment