Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ita aganin ta halin mahaifinta ne yayi mata katanga da samun farin cikin ta, shine ya hanata mallakar zuciyar masoyin ta na dindindin...sam bata ga laifin Mu'een ba.

Domin tasan koma waye aka mai irin wannan da 'kyar ne ya iya amincewa da batun aure kuma tsakani, sa'an sa 'daya da suka barshi ma dawo basu ha'da shi da hukuma ba.


Haka suka tattara suka bar masa gidan sa gaba 'daya sai shi sai halin sa.


Hankalin sa sake tashi yayi amma yafi bada kai wurin ganin ya tattara duk dukiyan Ammi daya mallake ya bata abinta shima ya raba kansa da haramun, kafin satin yake so ya harha'da komai ya sada su da abinsu in ma hukuma zasu ha'da shi da shi duk bai damu ba, da ace ya mutu yana cikin haramun gwamma ace ya mutu a hannun hukuma yafi masa.


Maganganun Mu'een ne a kullum ke ta mar yawo aka, kuma ya 'kara fargar da shi, ha'ki'ka gaskiyan sa ne da ya ce wanda ya tara dukiyar ma ya barta, kuma haka aka kaishi makwancin sa daga shi sai farin yadin da aka mai sutura da shi shi kansa shaida ne akan hakan, balle shi da 'karfi da yaji ya kwace ta ma amfanin me kuma zata yi masa, bacin yasan mutuwa na iya 'daukan sa a duk lokacin da ta ga dama...me ze je yace da ubangijin sa?


Tun da yake a rayuwa bai ta6a danasanin aikata abu irin wannan ba, yayi danasani fin yawan shekarun sa, yayi nadama fin laifukan da ya aikata gaba 'daya yayi nadamar komai.





*****
Basu sake zama sun tattauna batun ba har kusan kwana biyar da tafiyar Barrister, duk a kwanakin kuwa gidan wani iri ya dawo tamkar lokacin da aka ta6a kulle Alhaji a shekarun baya can.
Gidan sam babu mai walwalar kirki kowa tunanin da ke cinsa daban.


Noor ma a lokacin ta 'kira Ammi amma sai taji muryar ta wani iri ba kamar yadda suka saba ba, koda ta tambaya kuma Ammi sai tace da ita ba komai.


Hankalin ta sam ya kasa kwanciya sai take jin kamar wani abin ne daban ke faruwa.


Anty Zainab ta samu da maganar itama sai taji wani iri amma bata nuna mata ba kawai ta kwantar mata da hankali.
Sai daga baya kuma Uncle J ke fa'da mata wai zai yi tafiya zuwa Bauchi.


Tambayar sa tayi cikin natsuwa abinda ke faruwa dan ta fara zargin kamar jikin Mu'een ne ya motsa sai da yayi mata bayani ata'kaice kafin ta samu natsuwa.

Itace tayiwa Noor bayanin amma still Noor ta kasa hankalin ta dan tana da tarihin abinda ya faru abaya can, tsoron ta kar labari ya sake maimaita kansa ne.
Hakan yasa ta kasa kwantar da hankalin ta.




*****
Sati na cika Barrister ya dawo wanda kafin zuwan sa ma already Uncle Ja'afar ya iso shine ya 'kara tausan Ammi ya kuma yi magana da jam'ian tsaro in ma wani abin zai biyo baya ya zama na suna da masaniya akai.


Shima Barristern da yake ya riga yayi niyyan dam'ka musu dukiyar su ne da kansa ya taho da wasu Jam'ian tsaro wanda ganin hakan yasa Uncle Jafar 'kin amincewa da su, Ja'mian tsaron da yai magana da su tun farko ya 'kira aka zo duk suka 'dunguma da su can garin Bauchi Ammi kam sam bata so tafiyar ba tana kuka take fa'din ita bata son dukiyar...ya koma da abinsa bazata kar6a ba tace yaje har abada ta yafe masa ita dai ya barta da iyalan ta su zauna lafiya.


Lokacin da zasu tafi ma kuka ta ringa yi sosai ga shi daga Alhaji, Mu'een sai Uncle Ja'far suka tafi ta 6angaren su sai kuma Jami'an tsaro ita kam 'kin binsu tayi...

Saif da Zaid ne ka'dai suke tare da ita suke kuma bata baki akan ta kwantar da hankalin ta babu abinda zai sake faruwa da iznin Allah.


A kotu suka 'karashe maganar bayan ya 'dauke su kusan kwanaki uku, domin sun 6oye ainahin abinda ke faruwa kuma basu so a tona shi saboda Alhaji yace baya so ace za'a hukunta Barrister, Uncle Ja'afar ne ma da Mu'een suka 'dan so su nuna tirjiya amma daga bisani suka amince da hukuncin Alhajin inda daga 'karshe Mu'een ya sa hannu aka dawo wa da Ammi dukkan dukiyar ta hannun ta duk wani hannun jari da sanya a kampanoni duk ya dawo da shi harda ribar da yake samu ma, a adalcin sa sai yaga hakan ka'dai ne idan yayai zai sashi wanke kansa, sai ya zamana kamar juya mata dukiyar kawai yaje yi ya dawo mata da abinta.


Bai barwa kansa komai ba illah gidan da yake ciki da kuma 'yan ku'dade da basu haura 5ml ba..yayi hakanne kuma dan yasan komai da ya mallaka daga dukiyar Ammi ya same shi, cuz ya jima da ajiye aikin sa tun awancan shekarun kawai ya kama harkar kasuwanci.


Ganin cewa dukiyar ta sake ninkuwa ne ya sanya Alhaji Baba neman 'karin bayani nan Barrister ya sanar da shi be 6oye masa ba, sosai Alhaji ya yadda da gaskiyar sa nan take ya yi 'ko'karin ware wani abu daga ciki ya bashi da tunanin idan ya koma zai yiwa mai dukiyar bayani amma 'kememe Abban Jidda ya 'ki amsar komai yace wanda suka rayu a ciki ma yana neman afuwa akanta su yafe mai amma ba zai sake yadda yaci dukiyar su ba koda kuwa da amincewar su ne.
Hakan ma yasan sun mai halacci domin yasan da wasu daban ne da babu abinda zai hana shi cin prison baya ga haka ma gashi dokar aikin sa ya karya.

Amma duk suka rufa mai asiri kawai aka yi maganar akan cewa mahaifin Ammi ya rasu ne ya bar dukiyar sa a hannun Barristern sai yanzun ya dawo mata da shi bayan ya samu labarin inda suke...daga 'karshe Uncle Ja'afar ya sake yi masa babban kashedi kan cewa duk abinda ya samu 'daya daga cikin familyn sa to kuwa ya kuka da kansa yace ya amince indai ta 6angaren sa ne bashi da matsala.

Da haka suka rabu da Barrister yana ta zuba musu godiya.


Duk wannan hada-hadan da aka tayi babu abinda ya ha'da Uncle Ja'afar da Mu'een magana, duk yadda yaso ya ga ya shiga jikin sa Uncle Ja'afar kawar da kai ya ringa yi sam Mu'een bai ji da'di ba, ga shi ana gama case 'din ya koma Taraba abinsa.


Wannan dalilin ya tabbatarwa Mu'een da cewa sosai Uncle 'din nasa ke fushi dashi.
Abin tsaye masa arai yayi sosai.


Ga shi a kullum Ishaq na sake bashi shawaran komawa bakin aikin sa shima 'din zuwa yanzun yayi na'am da wannan shawaran..Sati biyu bayan case 'din su Jiddah ya tattara ya koma Abuja...kafin hakan kuwa sosai Alhaji ya zaunar da shi yayi masa nasiha cikin natsuwa ta yadda zai fi fahimtar sa, shi kam ma yana jin yanzu ai ko hauka yake bazai sake ra6ar 'yar wani ba..Burin sa kawai ya dawo da Noor 'din sa cikin rayuwar sa ne yanzu.


Noor ma yanzu hankalin ta ya 'dan kwanta cuz Ammi duk ta yi mata bayanin komai da ya faru sai alokacin ta 'dan ji natsuwa amma still kewar su Ammin na dumun ta.


Gefe guda shima Yah Deen a kullum baya gajiya da gwada 'kiran layin ta amma baya samun ta...haka ma Anty Zainab ya daina samun layin ta sam hakan dai ya daure ya cigaba da aikin sa yana lalla6awa, idan yace lafiyar sa 'kalau ma yayi 'karya ne, cuz tun rasuwar Jasmine har yau 'din nan bazai ce ga ranar da yaji shi garau ba, sai dai Alhamdulillah ba laifi gaskiya.


Da ciwon sa yake tafiya sai dai ramar da ke yi har yanzun sake bayyana take yi, yana kuma 'kiran sa mahaifan sa akai akai suna gaisawa inda a kullum nasiha ce ke 'kara ha'da su..basu gajiya da yi masa.





Comment
Vote
Share





*Salmerh ce* 😍💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)



By
*Salmerh MD*


*Wattpad @*
*Serlmerh-md*



💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*



_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_


*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*



🅿 *89*


Baya yin cikakken wata biyu bai zo gida ba..haka zai zo yayi weekend 'din sa ya koma lafiya lau, duk yanda zai ji ciwon sa na damun sa baya bari kowa ya fahimta sai dai in abin yafi 'karfin sa ne.


Sai dai ko a fahimta ta yanayin 'karfin jikin sa ko kuma rashin walwalar sa amma da kansa kam baya furtawa ga kowa cuz gani yake kamar shine ya jawa kansa da kansa...



'Bangaren Jiddah kuwa ta riga ta sanyawa ranta ha'kuri yanzu, tayi kuka, kuka sosai fiye da zaton mai karatu har sai da ta raaa mai lallashin ta ma, da 'kyar ta daure ta fara rage damuwar dake cikin zuciyar ta akan Mu'een.

'Ko'kari sosai tayi wajen ganin ta cire shi cikin zuciyar ta domin ta fahimci tana son wanda ba zai ta6a zama mallakin ta bane, 'kila 'kaddarar ta kenan shine 'dumbin 'kaunar sa da tayi tasan har abada bazata iya ta6a son wani kamar yadda ta so shi ba, amma ya zama ta ha'kura da shi, badan komai ba sai dan labarin da mahaifin ta ya bata, abu guda 'daya tak ne ya taka mata birki ya kuma yi mata katanga tsakanin ta da shi baya ga da babu abinda zai sa ta janyewa har sai inda 'karfin ta ya 'kare domin tana son shi sosai, amma kunyar abinda mahaifin ta ya aikata musu ka'dai ma ba zai barta ta sake kusantar inda Mu'een yake ba har abada.


Sam ta'ki mahaifin ta ta 'ki komawa inda yake kamar yadda mahaifiyar ta ma ta'ki...duk da cewa tana da masaniya akan irin 'kaunar da yake mata amma hakan bai hana ta jin haushin sa ba.


Mahaifin Jiddah lokuta da dama ya kan zauna ne yayi kuka da hawayen sa kamar yaro 'karami ganin cewa duk ahalin sa sun gushe shi ne saboda mugun halin da ya shuka tun abaya, ji yake dama lokacin ya dawo baya ya kasance bai aikata hakan ba, yasan da yanzu yana zaman sa cikin farin ciki da iyalan sa kamar kowa...tsananin tausayin Jiddah yake ji a koda wani lokaci, dan ya san abin ita zai fi ta6awa, gashi bata kusa da shi balle ya san halin da take ciki har ya samu daman tausan ta yana bata ha'kuri.



Cikin cousins 'din ta ta samu wani Bilal ke son ta..da farko 'kin bawa kowa fuska tayi wanda daga baya da kanta tayi tunani taga dacewar bawa wani dama ko dan ta rage ra'da'din damuwar da ke cin ta ma a kullum game da Mu'een hakan yasa ta amince da shi sai dai ba sosai take bashi fuska ba sai lokacin da ta ga dama...a hakan har manya suka sanya baki cikin maganar ta su.


Tambayar auren tane ya kai wasu daga cikin dangin mahaifiyar ta wajen Barrister nan suka tarar da shi ya koma abin tausayi, ciwon diabetes yake fama da shi gashi babu wani da ke kula da shi.

Koda suka tambayi auren batare da 6ata lokaci ba ya basu ya kuma ce da su duk lokacin da suka ga ya dace kawai su sanya ba sai sun sake dawowa wurin sa ba.



Shikam ma farin ciki yayi da jin batun auren Jiddah ya taso cikin 'kan'kanin lokaci haka kuma Allah ya nufe shi da bada auren da kansa.


Ko da suka koma gida hankalin su kasa kwanciya yayi haka suka dinga yiwa Mummyn Jiddah nasiha da yake manyan yayun tane da kuma kawunan ta bazata iya yi musu gardama ba dole haka ba dan taso ba ta dawo gidan mijin ta amma Jidda 'ki tayi tayi zaman ta can wurin dangin mahaifiyar ta.





*****
_Bayan wasu watanni_
Lokaci ya 'dan ja sosai dan 'yan biyun Ammi duk sun kammala makarantar su yanzu saura bautar 'kasa...sun girma sun zama manyan samari dasu.
Ishaq kuwa na nan har a lokacin bai kuma 'dago zancen aure ba tun da aka raba shi da wancan yarinyar shikenan ya fawwalawa Allah komai, da farko ma gani yake kamar zata dawo watarana amma da yaga har anci shekara guda shiru shikenan ya saki ransa ya manta da ita, ya kanzo Shuwarin ya gaida su Alhaji Baba duk lokacin da ya samu dama, kuma ba 'karamin da'di yake ji ba da yanda suka 'dauke shi kamar 'dan su na cikin su...abu da ke tsaya masa arai a kullum kan rashin matar Deen ne, gaba 'daya ya rasa har ina su Ammi ke son jan maganar dan har ga Allah shi ba 'kaunar rabuwar sun yake ba, gefe guda kuma da kansa ya 'daukan ma Alhaji Baba cewa idan yayi masa kyauta yayi al'kawarin baze mayar masa da kyautar sa ba, duk da be san miye ba amma ya amince masa yanzu kuma abin na damun sa bayan fahimtar da yayi cewa kyautan da Alhajin ke fa'di na aure ne bana komai ba nd be san wace ba.


Alhaji Baba da kansa ya bashi labarin dukiyar Ammi da aka dawo da ita sosai yayi murna 'kwarai da gaske ya kuma sanya albarkar sa a ciki...


Sani ma yazo Shuwarin kamar yadda yayi al'kawari, abin tausayi yanzu hannun sa 'daya sai hannun riga 'daga dake lilo amma babu hannu ciki, sosai ya sake neman afuwar su Ammi sun kuwa yafe masa, rashin sa'ar da yayi shine duk be tarar da Deen da Noor a gida ba balle ya 'kara basu ha'kuri, haka ya koma zuciyar sa babu da'di, kyautar 10k Alhaji Baba ya bashi yayin da su Zaidu ke ta banka masa uwar harara, ji suke kamar su sha'ko banza...haushin sa suke ji sosai.


Yah Deen kam jiki ya'ki yin da'di sai dai ace Alhamdulillah kawai, tun yana dannewa har ta kai shi ga kwanciya a asbiti, wanda zuwa lokacin hatta Saif yafi shi kaurin jiki, tausayin sa sosai Saif yake ji kamar ya 'dauke masa ciwon..shine ma ya tafi Abujan lokacin da labarin rashin lafiyar tasa ya iso kunnuwan su.


Hankalin sa 'kara tashi yake yi idan yaga Yayan nasa na aman jini, kuka yake yi yana share masa, duk sai ya galabaita ya fita a hayyacin sa gaba 'daya, Saif sai yake ganin tamkar kowa baya tausayin Yayan nasa ne...ya kan yawan ambatan sunan Uncle Ja'afar da Noor wanda da kanshi ya fahimci cewa sune ka'dai damuwar zuciyar sa a yanzu shiyasa baya iya 6oyewa.


Uncle Ja'afar ya 'kira ya sanarmawa yana kuka, hankalin sa sai yaji ya tashi nan take, duk da baya kula shi har yanzun amma sosai yake jin sa aransa, kuma shima yasan be kyauta ba da yaja tsawon wannan lokacin yana fushi da shi.

Lokacin ko maganar kirki Mu'een baya iyawa, da idanu kawai yake bin komai.
Bayan 'kiran da Saif yayiwa Uncle da kwana biyu sai ga shi ya dira Abuja dan hankalin sa ya kasa kwanciya, a zihiri lokacin da Saif 'din ya 'kira shi bai ce da shi uffan ba but daga baya abin sai ya dame shi sosai domin ya fahimci akwai abinda ke faruwa dole sai da ya yanke shawarar tahowa.


Lokacin da ya iso ma Mu'een bacci yake yi, ba'a barin kowa zuwa inda yake saboda ciwon san ba mai son hayaniya sosai bane hatta Saif 'din ma ba koda yaushe ake barin sa shiga inda yake ba, amma yanda Uncle Ja'far in ya matsa dole sai da suka barshi ya shiga wajen sa.


Gaba ya sashi ya na kallo, tausayin sa duk ya mamaye masa zuciya duk yayi ba'ki ya rame daga inda yake yana iya hango 'kasusuwan dake 'kirjin sa da wuyan sa in ma irgawa akace masa yayi tsaf zai uya irga su, uwar rama yayi fiye da zaton mai karatu, ji yayi tamkar ya zubda mai hawaye, gaba 'daya jikin sa sai yayi sanyi, wannan idan ba dan farin sani da yayiwa Mu'een ba idan akace masa shine sam ba zai yadda ba.
Ido kawai ya tsura masa yana sake 'kare masa kallo.

......Alhaji Baba ma sau biyu yana zuwa duba shi amma baya wani 'daga hankali da ciwon nasa sosai, gara ma wani lokaci da yayi wata doguwar suma Saif duk sai ya rirkice he thought mutuwa Yayan nasa zaiyi, sai da ya 'dauki sa'oi ashirin da bakwai kafin ya farfa'do wannan lokacin ne me Alhaji Baba ya nuna damuwa sosai cuz hadda Ammi suka zo suka duba shi, itama kuka ta ringa yi tana 'karawa, bata san ina zata sanya tausayin 'dan nata ba.


A hakan bata ta6a kuskuren sanar da Hudah abinda ke faruwa ba, ko waya zatayi da ita tana 'ko'kari sosai wajen ganin ta daidaita muryar ta...ko da Anty Zainab ma sai dai taji labarin ciwon.nasa a wani wuri amma Ammi bata ta6a sanar da su saboda tasan tare suke koda wanai lokaci dole idan 'daya yaji 'dayan zai ji.

Hikimar ta anan kuwa shine wai m kar Noor taga tamkar tana son dawo da ita cikin rayuwar Mu'een ne shiyasa bata yadda ko zancen sa ya ha'da su.


Shima Uncle Ja'afar in sai yanzu da yake zaune gaban sa sannan ya ke jin haushin kansa ma, ai kuskure ya kan zama kuskure ne idan mai aikata shi ya kasa canzawa, yanada ya'kinin yanzu Mu'een ya canza rayuwar sa gaba 'daya, ha'ki'ka bai ji da'din abinda Deen 'din ya aikata ba shiysa ransa ya 6aci sosai cuz ko a mafarki be ta6a tunanin har Mu'een na iya 6ata rayuwar sa ta hanyar biyewa matan banza ba, shiyasa ya kasa bashi fuskan da zasu fahimci juna...
Yanzun kuwa da yake jin 'kaunar yaron sa gami da tausayin sa na sake ratsa shi hannun sa ya kamo cikin nashi yana shafawa a hankali zuciyar sa duk tayi rauni ya karaya gaba 'daya.



A hankali Mu'een ya bu'de idanun sa, jin hannun sa cikin na mutun sam bai sashi mamaki ba dan yasan Saif na nan tare da shi...bai bu'de idanun sa ba dan ra'dadi suke yi masa sosai...sai da ya 'dauki tsawon lokaci kafin ya bu'de idanun a hankali.


Dishi-dishin da yake gani ne ya sashi sake maida idanun ya rufe amma a hankalin sa sai ya tafi kan wanda ya gani zaune kusa da shi, sam girman jikin sa ba irin na Saif bane.


Bayan wasu da'ki'ku ya sake bu'de idanun tare da 'dan motsa hannun sa dake cikin na mutumin...nan take ya 'dago kansa, ha'da ido yayi da Uncle 'din sa da ya jima bai ganshi kusa da shi kamar hakan ba, ido ya tsura masa tsawon lokaci yana duban sa, sai yake ganin tamkar a mafarki...kasa gaskata idanun sa yayi dan haka sai ya maida su ya kuma kullewa siraran hawaye suka gangaro masa ta gefe da gefen fuskar sa.


Uncle J goge masa hawayen ya fara da sauri yana yi masa magana cin murya mai kwantar da hankali.." Kayi ha'kuri Baba na insha Allahu bazan sake yin fushi da kai ba..ni da kaina nasan nayi kuskure may be ma fin wanda kayi...na dawo gare ka yanzu kaji ka kwantar da hankalin ka insha Allahu farin cikin ka zai dawo soon..."


Gefe yayi da kansa batare da ya sake kallon inda Uncle in yake ba yayin da hawayen sa ke cigaba da gangarawa...Uncle bai damu da hakan da Mu'een yayi masa ba dan yasan shima sam bai kyauta masa ba...wayar sa ya ciro ya 'kira Matar sa wanda tana 'dauka yayi saurin fa'din" Meet ur Mu'een.."
Bai jira jin komai daga gare ta ba ya sanya wayar a speaker ya kai kuda sa da shi.


Anty Zainab tsabar farin ciki bata san lokacin da ta zauna daga tsayen da take ba...'kirjin ta ta dafe ta wani sau'ke ajiyan zuciya tana murmushin jin da'di, bayan wani tsawon lokaci yau ga Mu'een da Uncle 'din sa zaune wuri guda ga dukkan alamu komai ya daidaita tsakanin su kenan abinda ta jima tana fatan faruwar sa sai yau Allah ya cika mata burin ta.

....a hankali take jin hucin numfashin sa na sau'ka ta cikin wayar amma bai ce da ita komai ba... Sunan sa ta 'kira da sanyin murya amma bai amsa ta ba...." Talk to me pls Mu'een kar kayi fushi da ni, kasan haka kawai bazan share ka tsawon wannan lokacin ba ko/ dan Allah kace min wani abu...".

Noor da ke cikin 'daki fitowar ta kenan sai taji Anty na ro'ko a waya ido ta 'dan zaro tace" Anty ke da waye haka?"
Tayi maganar tana nufo inda Anty Zainab take ganiana yanda ta tattara dukkan hankalin ta kan wayar harda hannu biyu ma ta ri'ke wayar tamkar wacce akace mata za'a 'kwace ne.


Anty Zainab kam ma hankalin ta sam bai je ga maganar Noor ba, dagsken duk ta bada hankalin ta wajen sa amma still ya'ki cewa komai.


Shi kam jin murya kamar ta Noor 'din sa cikin wayar ne ya sanya shi nutsar da zuciyar sa wuri guda, ido ya 'dan zaro ya kalli wayar sannan ya kalli Uncle Ja'afar da lumsassun idanun nasa.


Uncle Ja'afar da ya san abinda ya sashi hakan kawai sai yayi masa murmushi cuz wayar a speaker take kuma shima yana jin dukkan motsin da aka yi daga wancan 6angaren ballantana muryar Noor da ya fito tarwai.

Kunne ya sake kafewa amma bai ji muryar ta 'kara magana ba illah muryar Anty Zainab ka'dai.


Idon sa ya sake lumshewa yayi shiru yanayin fitar numfashin sa na 'kara hauhauwa yana canza salo.


Ganin hakan ya sa Uncle Ja'afar 'daukan wayar ya cire a speaker sannan ya kai kunnan sa domin ya fahimci Mu'een sam bai da niyyan cewa komai...." Ba shi da lafiya ne shiyasa bai yi miki magana ba but anjima zan 'kira ki".
Haka kawai yacecda Anty Zee wanda da gama fa'din hakan sai ya kashe wayar tasa ya sanya ta cikin aljihu.



Cigaba yayi da lalla6an Mu'een wanda har a lokacin ya'ki sake bu'de idanun sa ballantana ya bu'di bakin sa ya furta wani abu, cikin zuciyar sa yake ta ayyana" Uncle...kaima ka daina so na...ba ka tausayi na....ji nake kamar in mutu idan na tuna fushin da kake yi da ni Uncle..me yasa ka kasa fahimta ta? me yasa kuka 6oye Noor daga idanu na, me yasa kuka 'ki bayyanar min da ita bayan kunsan ina matu'kar son mata ta?..."


Haka har likatan sa ya dawo Uncle Jafar ya fita magana guda bata ha'da su ba.
Shi kam abin yawa suka yi masa, muryar Noor da yaji cikin wayar yafi komai 'daga masa hankali...ga kuma Uncle 'din sa da ya kama da laifin 6oye ta navtsawon lokaci, da wanne zai ji, da murnar dawowar Uncle rayuwar sa ko kuwa da ba'kin cikin rashin Noor zai ji.


Uncle Ja'afar na fita daga ward 'din sai yaci karo da Saif sai suka koma suka zaune tare.
Shiru na 'yan sakanni kowa na jimami cikin ransa, nan ma wayar Uncle Ja'afar ce ta fara ruri ko da ya ciro ya duba sai yaga sunan Anty Zainab ne...dama yasan sai ita, yasan tunda taji batun yaron ta ai babu sau'ki.


'Daukan wayar yayi ya kai kunnan sa..." Nextweek zan dawo".
Shine abinda ta fara furtawa cike da 'dauki wanda yake fita tun daga cikin zuciyar ta.
Goshin sa ya 'dan tattare sannan ya tambaye ta dalili.
Instead ta bashi amsa a a sai tace" Dan Allah kar ka hana ni...ina so in ga jikin Yaro vna.."

" Toh ita kuma Hudahn da wa zaki barta?"
" Tare zamu zo zan mata bayani ai".
" Toh shikenan Allah ya kaimu".
Da gama fa'din hakan sai ya cire wayar a kunnan sa daidai lokacin da Saif ya jefa masa tambayar" Unlce wace Hudah kake magana akai kuma? kar dai Noor 'in Yaya?"

Kallon sa kawai Uncle Ja'afar yayi yai shiru Saif kam haushi kamar yayi kuka, dama duk wannan abin baki suka ha'dewa Mu'een, dama sun san inda matar sa take shine suka bar shi yake faman kokuwa da rayuwar sa?".
" Hmm.."
kawai ya iya furtawa a fili gami da sunkuyar da kansa, ji yake badan kawun sa bane Uncle Ja'afar da sai ya tara masa mutane anan wurin, wannan ai rashin tausayi ne a ganin sa.

Zuwan Uncle Ja'afar sosai ya bada himma wajen ganin an tsananta kulawa da lafiyar Mu'een yadda ta dace, maku'dan ku'da'de ya dire kafin ya samu aka

Please Login or Register in order to submit comment