Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanar da iyayen sa..amsar da ya bata shine wanda Hudah taji ranar da ta farka a bacci...idan ya tuna wannan abin ya kan sake jin haushin kansa da kansa akoda yaushe.

Ba zai gaya wa Noor a zahiri ba amma insha Allahu saboda ita zai yi 'ko'karin ganin ya kame kansa daga aikata abinda yake yi.

Cuz idan har wannan yarinyar ta iya ganin abu makamanci wannan kuma ta iya 6oye wa yasan shima barin zina abu ne mai sau'ki a wurin sa...wannan abin ka'dai da ta aikata ya ja mata wani babban matsayi cikin zuciyar sa da shi kansa bazai iya misaltawa ba.


Bakin sa na son furta _kiyafe min_ amma harshen sa sai yayi masa nauyi wurin furta shi, sai ma yake jin gaba 'daya Noor 'din tayi masa kwarjini a idanun sa.

Tsaye ya mi'ke da niyyar tafiya...bai kuma niyyan sake furta komai ba, nima ban ko yi motsin kirki daga inda nake ba har ya isa bakin 'kofa zai bu'de sai a sannan nace da shi" Ammi tace in tambaye ka kayi min izni inje gida".
Take ya waigo yana fa'din
" Wani gida kuma?"
Inda yayi tambayar yana kallon bayana dan ko juyowa banyi ba, shi kansa yana mamakin wai 6eran yarinyar nan ce ke yi masa irin wannan abin...hmmm Allah mai sanadi...sai yayi 'dan ta'kaitaccen murmushi.

Amsa na bashi da fa'din" Gidan mu zani da wurin dangi na".

Wannan karan murmushin mai sauti yayi jin yanayin maganar tawa kamar da gaba....
Sai da ya juya yana bu'de 'kofan kafin yace" Toh ki je mana sai kin tamabaye ni ne?"


Shiru nayi ban ce masa komai ba...har ya sa kai zai fita kuma sai dakata sannan yace" Amma fa family kawai na miki izni ki ziyarta ban yarda da shiga ko'ina ba".

Ko yanzun ma shiru nayi sai dai bai damu ba cuz yasan sarai na jishi.. daga haka kuma ya fita daga 'dakin yana fa'din"  Sai da safe"...cuz daga masallaci wai bazai dawo gidan ba saboda yau 'din bai jin cin dinner shiyasa.







Comment
Vote
Share




*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)


By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

🕌🌙 ~RAMADAN MUBARAKH~ 🕌🌙


_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *62*


Washe gari kuwa da safe ya koma Jigawa, wanda kafin tafiyar tasa sai da yazo gidan Ammi ya musu sallama ni kuma ya ciro ku'di ya ban masan nawa bane ya ajiye min yayi tafiyar sa, daga" na tafi" babu abinda ya sake ha'da ni da shi, kuma ko da yace ya min hakn ma baki n ta6e ban furta masa komai ba illah harara da na bi ku'din nasa da shi.


Ban ko saka 'dan yatsana na ta6a ku'din.ba na bar su nan inda ya ajiye su na cigaba da harkoki na.

Sai bayan tafiyar sane ne ma da 'dan jimawa kafin Ammi tazo ta ga ku'din da kanta sannan tactambaye ni sai nace mata" Yayah ne ya ajiye".
Ammi da ku'din a hannun ta tace
" Shine kuma kika bar su nan?" Inda tayi maganar tana kallo na.
'Dan marairaicecfuska nayi nace
" Ammi to ni ina zan kaisu? shine fa da kansa ya ajiye a wurin".

"Da ya ajiye 'din ce miki yayi ki ta kallon su ko kuma ki barshi a nan, i thought ke ya ajiye ko?"
A hankali nace" Ammi to ki ri'ke a gunki".

Kai ta girgiza kawai ta tafi ta bar ni a wurin.

  Nima ban jima ba bayan hakan na gama shiri na dan zuwa gidan mu wurin Ummah ta...lokacin da zan tafi Ammi sai ta ce in tafi da ku'din zan yi magana ta hanani...dole ta 'dauko tasamin cikin jakata tare da ha'da ni da tsaraba tace in kai wa Ummah ta.

Ranar Allah ka'dai ya san irin farin cikin da nake ciki musamman da naga Ummah ta...'kin zuwa ko'ina nayi saboda so nake na 'dan kwana biyu agidan Ummah ban san komawa can gidan a yau 'din.

Sosai naji da'din zuwa gidan kuwa inda nan take na sake cikin gidan mu walwalata duk tacdawo sabuwa har ma 'dan manta damuwar da ke ci na arai.

Ammi data ga dare yayi sai ta 'kira Umman mu awaya bayan sun gaisa tace ta ha'da mu...nan nayi mata bayanin ba yau zan dawo ba...Ammi bata damu ba haka bata ce dani komai ba illa sai da safe kawai da tai min.

Nan na sake sakan jiki na a gidan ganin Ammi bata hana ni ba.

Ko Ummah ta ma da na bata ku'din 'kin kar6a tayi abin sai ya bani haushi sosai, sai da ta ga na fara hawaye kafin ta kar6i 5k ta bar min 15k wai in ajiye a wuri na...nace mata Ammi ce fa tace in zo da shi..ni me ma zanyi da ku'din to?"

Ummah ta yi tayi tamkar bata jini ba, kukan da taga na dage da yi ne ma yasa ta ciran 5k 'din wanda ni kuwa kukan nawa har da tunowa da sirrin da na 6oyewa zuciya ta wanda ganin ku'din da ya bani da kansa a hannu na ne ya sani tunowa da shi da halayyar sa..ha'kika wani lokacin furta abu ma yakan sa ya yi ma sau'ki a zuciya yayin da ri'ke abu sam baida wani amfani inba yazama dole ba, nasan da ace na samu wanda zamu tattauna batun da shi na fahimta da zanji sau'ki cikin raina amma bazan ta6a iya yin hirar ga kowa ba, ciki kuwa harda mahaifiya ta...yanzu kam na fahimci akwai sirrin da 6oye shi ya fiye wa kowa alkhairi fiye da furta shi, balle ma ni da ya kasance sirrin mijina ne, ban manta garga'din da akayi min kan ri'ke sirri ba...nasan zan iya ri'ke shi har abada duk da na san bazan iya manta shi cikin raina ba.

Na bari dai akan sanin da nayi cewa rufin asiri ga wani tamkar ka rufa naka asirin ne...al'kawari 'daya da na 'daukan ma kaina game da Yah Deen shine zan nayi masa addu'ah ubangiji Allah ya shiryar da shi Allah yasa ya gane hakan da yake aikatawa babban laifi ne a wurin Ubangiji.


Sai washegeri muka je gidan su Addah ta saudah ni da Ummie, har  gidan Yaya Usman da sauran 'yan uwan mu dake kusa duk munje yayin da wasu daga cikin su ke min zolayar wai har na canza amarcin ya kar6e ni, ni dai kawai sai dai inyi murmushi cuz' ni ka 'dai na san damuwa zuciya ta.

Kamar yadda ya umarceni kuwa banje gidan kowa da yakansace ba ahali na ba, duk iya ziyarar da nayi ban 'ketare maganar sa ba, daga nan kuwa na dawo gidan Umma ta.

Kowa ya ganni sukan ce kyauna ya 'karu haka shiru-shiru na ma, hatta ma'kwabtan gidan mu sai da suka yabi tsari na...ni kam murmushi kawai nake yi ban bada amsar komai.

A duk lokaciin da na ke6e na a mafiya yawan lokauta na kan tsinci kaina ian mai zubda hawaye wanda duk baya rasa nasaba da Yah Deen, sam ban san dalilin damuwa ta akan rayuwar da na ga yake yi ba, kuma nayi-nayi in manta da lamarin amma na kasa a kullum yana nan sabo cikin zuciya ta.

Ban ta6a bari kuma Ummahn mu ta fahimci halin da nake ciki ba, sosai nayi 'ko'kari wajen 6oye mata, ni da kaina nasan nayi wannan 'ko'karin ko da wani bai fa'da ba.

Kwana na biyu sannan na koma gidan Ammi na cigaba da zama na,  hankali na a 'dan kwance saboda ko waya bama yi da shi, ina dai gaisawa da su Saif akai akai amma shi kam ban da shi, sai dai inji suna waya da Ammi lokuta da dama ina gefen ta amma ban ta6a ji ya ko gwada ambatan sunana ba balle yace a bani wayar.

'Bangarena nima hakn yafi min da'di dan idan akec zan yi magana da shi nasan kuka ne kawai zai rinjaye ni bazan iya maganar ba...in kuwa hakan yacfaru nasan zuciyar Ammi zai cika ne da tarin tambayoyi.

Ashe Ammi ma da kanta hakan da yake yi 'din na bata haushi, kawai ta 'kyale shi ne dan tana so taga iya gudun ruwan sa akaina.

Haka take amsa masa gaisauwa faram-faram su kuma sha hirar su amma ko da wasa bata ta6a sako sunana a cikin zancen su.

Zancen waya ma nake so in tunawa Ammi zancen  da tace zata sa a siya min amma ina tsoron kar tace ai ban kwantar da hanakalin nawa ba tunda nace ni gida zan dawo, ita kuwa ina ganin kamar ta manta ma da batun, hakan yasa nima 'din dole nayi shiru na barwa lokaci kawai inda rabo na nasan wataran da kanta ma zata sai min in dai Ammi ce ba ma sai na tambaya ba.



*****
     Bayan tafiyar Yah Deen da Sati uku wani tashin hankalin ya sake faruwa, domin kawai wayan gari akayi Ma'u bata raye Allah ubangij ya amshi abin sa bayan tasha uwar rashin lafiya, tunda ta samu cikin nan bata samu nutsuwar kanta ba...ranar nasha da naji labarin mutuwar nasha kuka sosai,  kuka kamar raina zai fita, bazan manta ba yanda nayi ta damuwa da son zuwa dubata amma aka hana ni, bacin ina jin labarin wahalar jinyar da take sha a bakin mutane 'yan makarantar mu.

A kullum tausayin ta 'kara kamani yake yi, bayan uban gorin da ake binta da shi agida cewa ta bi ku'di ta lalata rayuwar ta, haka ma duk ranar da Alhaji Baba ya aika mata da kayan marmari da kaji ko 'yan ku'di ta kan yini cikin bakin ciki na gori akan ta,  gashi ko iya cin abincin ma bata yi bata iya cin komai da ta ci zata harar...maltina ka'dai ne ke iya zama acikin ta shima 'din babu wanda yake siya mata cuz ko Alhaji ya aiko ku'di bata ganin idanun su, babu wanda ya damu da lafiyar ta balle yunwar cikin ta, ga tsananin wahalar laulayi ga zazza6in typhoid da ya sako ta a gaba...a kullum kuka ne aikin ta, yau gashi ta bar mana duniyar ta koma ga mahallicin ta.

Alhaji Baba yayi namijin 'ko'kari wajen ganin ya kula da lafiyar Ma'u, saboda yasan koma menene ya same ta 'dan sa ne sanadi.

Akwai ranar da ya kawo mota ma da kansa yace akai ta asbiti dan lokacin bata da lafiya amma daga ranar ba'a 'kara sanar da shi rashin lafiyar ta ba.

Shi 'din kuma yanzu baya zuwa gidan nasu sai dai kawai yayi aike koda, ya Deen yazo ma bai damu ya sashi zuwa wajen ta ba dan ya bari ne akan idan ta haihu dole maganar auren su ta taso.

Allah cikin ikon sa sai
lokaci 'daya kawai ya amshi ran baiwar sa.






Comment
Vote
Share






*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_🎑🎆🌙Barka da sallah to d all Ummah...Taqaballahu minna min kum...ubangiji Allah ya maimaita mana shi da Alkhairi_ 🙏

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *63*

Tsanar da naji ta Yah Deen cikin zuciya ta a lokacin ni kaina ban san iya adadin ta ba...ban ta6a jin na tsani mutun sama da yanda nake jin haushin sa a lokacin ba.

Ji nake tamkar duk duniya baza'a ta6a samun mai mugun hali irin nasa ba, saboda duk lokacin da tunanin sa zaizo raina baya ta6a zuwa min da Alkhairi,  shiyasa nake gani kamar nasa halin na musamman ne.

Yau gashi sanadin sa Ma'u ta ta rasa ranta, ta tafi tafiya irin ta har abada, ta tafi ta bar duniyar cikin 'kuncin zuciya..ni da kaina a lokacin na yi fatan Allah ya saka mata zaluncin da aka yi mata sau babu adadi...ban sani ba ashe sakayyar har da ni ma da nake tare  da shi zata shafa...Hafsat dubi abinda aka yiwa yarinya ta dalilin mugun halin sa, Jasmine 'di na....bata iya ta 'karasa maganar ba kawai ta sunkuyar da kanta ta sanya kuka mai matu'kar tsuma zuciya.

Hafsat kanta sai da ta share hawaye amma gudun kar a rasa mai lallashin wani a cikin su ya sanya itan ta daure ta shanye nata kukan ta bawa Noor ha'kuri cikin nuna mata ai komai dake faruwa da bawa 'kaddara ne, duk abinda ya samu bawa to rubutacce ne tun kafin ya zo duniya 'kaddarar sa ta zanu..shiyasa ake so bawa yai imani da ko wace irin 'kaddara idan ta same shi mai kyau ce ko kuma akasin haka, wannan shine cikar imani da Allah da kuma Manzo.

" Hakane...".
Noor tace tana me share hawayen ta da suka kasa tsaya mata, tana goge wa amma wani na sake gangarowa...amma a hakan ta daure ta furta..." Allah ubangiji ya ji'kan Ma'u, Allah yasa ta ta huta, Allah ya ji'kan duk wa'danda suka mutu ya kyautata makwancin su, muma da muke raye Ubangiji Allah ya sa namu 'karshn yayi kyau,  Allah yasa mu mutu muna masu aikata Alkhairi ba sharri ba.."

" Ameen Thumma Ameen" Hafsat tace cikin sanyin murya, yayin da Noor ta cigaba da labarin ta kamar haka" Babban abin tausayi ma shine  Malam Barau, dattijon kuka ya ringa yi da hawaye yana sharewa, Alhaji Baba kam komai tsaya masa yayi cak, musamman da yake yana ganin cewa 'dan sa ne sanadin komai, abin ya tsaya masa arai sosai har ya hana shi sukuni.

Da shi akayi komai har aka sada Ma'u da makwancin ta na gaskiya, hatta abincin da za'a bu'kata gidan rasuwar Alhaji Baba duk shi ya 'dauki nawin komai har aka 'kare kar6an gaisuwa, bayan bakwai jama'ah kowa ya koma harkokin gaban sa amma banda Alhaji Baba.

A kullum zaka same shi ne cikin tunani, yana so ya sanar da Yah Deen batun rasuwar amma idan ya tuno shi sai yaji takaici ya kama shi haka ya sa ya kasa sanar da shi da kuma nuna masa muhimmancin sa a wurin.

Alhaji baya ta6a yin kwanaki biyu batare da ya ziyarci mahaifin Ma'un ba saboda zuciyar sa ta kasa nutsuwa wuri guda.

Ko gidan gonar sa badan mutane masu amana ne akai ba da komai lalace masa zaiyi dan baya tuna zuwa can kwata-kwata illah waya da suke yi, hakan ma sai dai yace da su suyi duk abinda ya dace kawai kar su damu.

Ammi ce ta sanar da  Yah Deen batun rasuwar inda yaji abin har zuciyar sa saboda mutuwar ta masa bazata, sosai jikin sa yayi sanyi...amma ko da Ammi ta nuna masa dacewar zuwan sa dan gaida mahaifin ta take ya kawo wani excuse cuz baya son zuwa cikin irin wannan taron musamman ma da yasan cewa sai an ta nuna shi idan yazo wurin, shi kuwa ba ha'kuri ne da shi rayuka sai su 6aci a banza.

Da gama wayar su da Ammi take sai ya 'kira Imrana da tun baya zuwan su gidan sa basu sake wata gaisuwar kirki ba, ko rasuwar Ma'u Imran bai 'kira shi akai ba, nan suka nunawa juna alhini cuz shi Imrana bai ma san da batun ba ashe tuni yana Kano sai da Yah Deen 'din ya sanar da shi kafin nan daga nan kuwa suka yi sallama kowa ya ajiye wayar.

Cikin sati na biyu da rasuwar Ma'u sannan Yah Deen yazo gida bisa umarnin Alhaji Baba da yake ma a lokacin duk an watse babu kowa sai mutanen gari.

Lokacin da Alhaji ya umarce shi da zuwan ma sosai hankalin sa ya tashi, zaton sa ko magana ce akaina ko kuma abinda ya faru abaya kafin tafiyar sa, hakan ya sa natsuwar sa tayi masa 'kaura dan Alhaji bai kawo batun Ma'u cikin maganar tasa ba.

Da niyyar sa yace su taho da Ishaq amma sai yayi tunanin kar Ishaq yaji wannan uban abin kunyar da ya tafka wanda basu da masaniya sam akanta, hakan yasa ya shirya kawai ya taho dan ba zai iya yiwa Alhaji musu bane ma baya ga haka da babu abinda zai sashi tahowa.

Sai da ya iso ne ma kafin ya 'dan ji natsuwa da yaji dalilin zuwan nasa ashe ba abinda yake zato bane gaisuwar gidan Malam Barau ne kawai.

Bai wani damu ba cuz can cikin zuciyar sa ma wani kwantaccen farin ciki yake ji wanda daga baya bayan jin labarin rasuwar Ma'un yayi tunani, a ganin sa Allah ya so shine ma shiyasa ya kar6i ranta bayaga haka da ina zaije da ita da abinda zata haifa a duniyan nan...ba'a farin ciki da mutuwa saboda kowa mutuwar zaiyi amma shi kam sai dai yace Alhamdulillah...duk da haka zuciyar sa na 'dan jin abin a sirrance saboda shi kansa yasan ya zalunce ta ya ci mutuncin 'kuruciyar ta  da wayo.

A fili kuwa sosai yake nuna alhinin sa ga Alhaji Baba da duk wanda zancen ya ha'da su.

Washegari da sassafe Alhaji Baba ya sa shi gaba suka wuce gidan Malam Barau ya gaida shi ya kuma nemi gafarar sa bisa abubuwan da suka faru, inda Malam Barau ya nuna masa ba komai ai 'kaddara rubutacciya ce sai dai fatan a kiyaye gaba, Allah kuma ya shirya, yace karamcin da mahaifin sa yayi masa ma ka'dai ya ishe sa..Ma'u kuwa addu'ah ce kawai tsakanin su a yanzu, Ubangiji Allah yajiqan ta da Rahama ya kyuatata makwancin ta.
Nasiha ya yiwa Yah Deen sosai game da rayuwa sannan suka taho gida bayan sun yi masa goma ta arzi'ki.

Kwanan sa biyu ya sake komawa Jigawa wanda a kwanaki biyun nima sau uku ka'dai na ga fuskar sa, tsanar sa ce ta ke sake girma a zuciya ta yanzu, musamman da na san cewa shine sanadin mutuwar Ma'u...haka abin yake kuwa ko a bakin mutane 'yan kaiwa da kawowa ma abinda suke yawo da shi kenan...hatta Ammi a lokacin na lura abin ya dame ta sosai sai dai ban san takamamman dalilin damuwar tata ba dan bamu tattauna batun da ita ba.

Ina dai da tabbacin itama 'kilan taji ra'de-ra'den da jama'ah ke yi ne game da rasuwar, kawai sai naga ta 'kara jana a jiki ta jan yawaita bani ha'kuri da nasiha mai kwantar da hankali wanda a hankali na fahimci duk ta nayin hakan ne saboda ta rage min damuwa, cuz tasan dole yanda taji nima zanji koma fiye da hakan.

Ni kuwa da na fahimce ta sai na dinga 6oye damuwa ta agaban ta, sosai nake nuna mata babu komai ni cikin zuciya ta hakan kuwa ya matu'kar faranta ranta a yanda na lura.

A gidan Ammi Yah Deen yayi kwanaki biyun nasa har ya koma, sai bayan tafiyar tasa ne ma nake jin Ammi na labarin irin gyaran da za'a yiwa 6angaren sa na gidan saboda yace yanzu anan gida zai na zaman hutun sa har sai an kammala aikin wancen gidan gaba 'daya.

Nikam baki na ta6e cikin raina na furta damuwar sa ai ni me ruwa na..shi yasani da ba'kin halin nasa.

*****
       *Bayan watanni biyu*
Su saif suka dawo hutu, sosai zuciya ta ta cika da farin cikin dawowar su saboda sune dama abokan hira ta.

Har Ammi na min dariya lokacin da nake ta sauri da zumu'di wajen ganin na shirya musu lafiyayyen abinci.

Ammi ce ke gyara min ta na nuna min abinda ban yi dai-dai ba yayin da na zage na nuna mata 'ko'kari na sosai..ita kanta ta yaba min da 'ko'karin da nayi wajen saurin koyan kalolin girki sosai kuma ta bayyana min farin cikin ta kan haka matu'ka...tace tana so ranar da miji na ma zai dawo in yi masa fin na yau wanda zai manta inda kansa yake idan ya 'dan'dana..ta 'karashe maganar tana murmushi.

Ni kam da jin ta ambace shi sai na ta6e baki na a 6oye a fili kuwa shiru nayi, ganinbhakan yasa fa'din" Baki ce komai ba kuma".

Da sanyin murya nace" Ammi shi kam sai dai ke ki yi masa ni bazan iya ba kin san..."

Murmushin ta ta 'kara fa'da'dawa sannan tace" Ai tunda yayi aure nima na watsar da shi, ga matar sa na me zan sake dinga yi masa wahalar kuma ke de ki shirya kawai ranar da duk zai zo a kitchen zaki yini".

Ban kalle ta ba na shagwa6e murya nace" Ni dai Ammi a a".

" Toh shikenan naji".
Ta fa'di tana 'yar dariya.


*****
     Kamar de kullum Saif ne ka'dai me min fara'a acikin su banda Zaidu, shima Saif 'din yanzu sai naga duk ya canza min, duk da haka sai da nayi ta jera masa 'korafin share nin da yayi lokacin da nake wancen gidan da tafiyar da suka yi batare da sun min sallama ba.

Ha'kuri kawai ya bani yana fa'di kin san yanzu kin zama Miss Yaya sai a hankali, dole sai mun iya takun mu...yayi maganar yana 'yar murmushi daga haka kuwa bai sake fa'din komai ba har suka nufi wajen cin abinci.

Ko wajen cin abincin ma da suka fara yabawa take Ammi ta sanar da su ai duk nice nayi, bu'dan bakin Saif sai cewa yayi" Ashe yaya ya huta shi kam ya ji da'di".

Zaidu kam bai ce komai ba, Ammi kam murmushi kawai tayi yayin da ni kuma na kawar da kaina, na tsani wannan ha'din sam, ace komai nawa sai an dangana ni da shi.

Wani abu guda da na lura game da su yanzu shine kamun kai, ba kamar baya da muke zama muyi wasa da karatu cin abinci duk tare ba, yanzu kam hira ka'dai ke ha'da mu, hirar ma sai an ha'du a parlour lokaci zuwa lokaci.

Ammi ma taja kunne na game da zama da su ta garga'de ni da kame kaina matsayi na 'ya mace inda ta sake yi min tuni da igiyar Auren da ke kaina.

Nice na basu labarin mutuwar Ma'u inda duk suka nuna alhinin su sosai sai dai sam ban iya na fa'di musu asalin sanadin mutuwar tata ba na barwa zuciya ta..na kuma san ko Ammi ma da 'kyar ne ta sanar da su ainahin labarin.

Zuwan su Saif sosai ya 'debe kaso mafi girma daga cikin damuwa ta, yayin da farin ciki ya lullu6e ni gaba 'daya, sam na manta da batun Yah Deen na watsar da lamarin sa, sau tari sai dai idan cikin hira ake tuno min da shi ko kuma idan naje bacci wasu lokutan yake zuwa raina  har nayi bacci.

Satin su biyu da dawowa shima ya zo gida kuma gidan Ammi ya sau'ka dagaske...shiyasa naga an 'kara gyare 6angaren nasa an canza tsarin komai.

Sosai naga ya canza min ya sake zama babban mutum da shi ga kyau da ya 'kara komin sa tsaf, gashin kansa sai shai'ki yake yi sosai naji ya birge ni amma ban nuna a fili ba na cigaba da sha'a ni na.
Shima bai damu da ni ba duk da kuwa cikin ransa ba haka bane, amma ya basar...ko bayan isowar sa ban yi niyyan gaida shi ba amma da yake muna zaune ne da Ammi a lokacin dole na daure ba'kin hali na na gaida shi, sau 'daya ya kalle ni ya amsa da" Lafiya"
A ta'kaice.
Sanye nake da ba'kin Hijab akaina 'dan madaidaici cikin wa'danda nake zaman gida da su, hannaye na duk na daga ciki illah 'kafata, da yake ma ba'ki ne hijab 'din sai ya 'kara fito min da haske na sosai, da yake ma kwanaki biyu kenan da Ammi ta sa aka zo akayi min kitso har gida tace ayi min harda jan lalle ma mai zanen flower ya kuwa yi kyau sosai ni kaina ya birge ni...a lokacin ban san dalilin da yasa akayi min lallen ba, kawai dai ji nayi Ammi nata 'korafin wai na da'de banyi lalle ba sai kace ba mace ba, ni idan ba'a inyi ba da kaina bazan yi tunanin inyi ba...zato na ko haka kawai ne ta sa akayi min sai daga baya na fahimci ashe dan zuwan Yah Deen ne.

Tashin hankali na ya fara ne lokacin da Ammi ta zo da batun na daina kwana anan 'dakin daga yau lokacin ina shirin bacci na tace da ni in shirya in wuce wurin mijina ba anan zan kwana ba.

Take na marairaice fuska na fara yi mata kuka amma Ammi ko kula ni bata yi ba, sai ma zaman jiran in kammala shiryawar da tayi...tana fa'din ai Alhaji Baba ne yace ba ita ba idan kuma zanja da maganar sa ne to sai taje ta sanar da shi.

Jin sunan Alhaji cikin maganar

Please Login or Register in order to submit comment