Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

murmushi tace da shi sai ka fito" Me zan tanadar maka?"
" Karki wahalar da kanki Ammi yau azumi nake yi".

Kai ta girgiza batare da ta 'kara fa'din komai ba ta shigewar ta kitchen.

Da shigar sa sai ya samu Alhaji Baba na 'karasa shiryawa zaune a bakin gado...links 'din hannun rigar sa yake 'ko'karin sawa sai Yah Deen ya yi sallama daga bakin 'kofar.

Alhaji 'dagowa yayi ya kalle shi tare da amsa sallamar da yayi, sai dai kallo 'daya kawai Alhaji Baba yayi masa take ya maida kansa ya cigaba da abinda yake yi.

Da sauri Yah Deen ya 'karasa kusa dashi kan gwiwoyin sa ya dur'kusa 'kasa gaban Alhajin tare da kaiwan hannun sa ya kar6i links 'din Alhaji Baba ma bai hana shi ba ya sake mai batare da ya kalli idanun sa ba illah tunanin " yau kaga damar zuwa kenan" da yake yi cikin ransa, wanda shirun san yabawa Yah Deen damar 'daura masa links 'din duka biyu sannan ya koma ya zauna da6as kamar 'dan yaro yace" Alhaji Baba fatan an tashi lafiya".
" Alhamdulillah"
Alhaji ya bashi amsa a takaice.

Daga haka yayi shiru bai iya sake furta komai ba...yana so yayi magana amma fargaba ta hana shi, tsoron yanda Alhaji Baba zai yanke hukunci akan makarantar sa yake yi, gashi dai fuskar Alhaji wasai take baka ce ga yanayin da yake ciki ba, amma kamala da kwarjinin sa sosai yayi tasiri a zuciyar Mu'een musamman da yake shi 'din babban mai laifi ne a gare shi.

Alhaji Baba kuwa tsaye ya mi'ke ya 'dauki babbar rigar sa dake gefen sa yana warwarewa da niyyan sawa batare da ya sake bi ta takan Yah Deen ba.

Ganin hakan ya sanya Yah Deen sake dai-dai ta nutsuwar sa bayan ya gama harha'da kalmar da zai fa'da cikin kwantar da murya da in ina yace " Alhaji 5days ya rage hutun mu ya 'kare gaba 'daya".
" Abinda da dama ya kawo ka gidan dan kazo ka tuna min kenan ko?"
Alhaji ya fa'di yana mai sanya babbar rigar sa still bai kalle shi ba.

Da sauri Yah Deen ya girgiza kansa tare da fa'din " A a ba haka bane fa Alhaji, yanzu ne na tuno shine nace bari kawai in sanar da kai tunda ina gaban ka".
Murmushin da ko akan fuska bazaka ga bayyanar ta ba Alhaji yayi illah sautin sau'kar numfashi da zaka ji, bai kalli inda yake ba yace " Allah ya kaimu ranar to...ka sanar da Ja'afar ne?"

Yah Deen sai yace " a a sai anjima zan sanar masa".

Shiru Alhaji yayi bai kuma magana ba, Yah Deen ne yayi 'karfin halin tattaro dukkan natsuwar sa tare da dun'kule abinda ya tsaye masa a zuci, tattara kalaman sa yayi wuri guda sai da ya saki ajiyar numfashi kafin cikin muryar masu neman alfarma ya furta " Alhaji dan Allah kayi ha'kuri ka yafe min......".
Alhaji Baba bai barshi ya kai 'karshen maganar tasa bama dan ya riga ya san kwanan zancen, dan haka sai yayi saurin taran sa da fa'din " Kar ka damu kanka da ni, na yafe maka tuntuni, sai dai ka sani duk abinda na riga nayi niyya sam bazan ta6a fasawa ba".
Alhaji Baba yana 'dora hular sa akai ya fa'di hakan cike da tabbatarwa.

Yah Deen cikin muryar Alhajin ya tabbatar da furucin nasan har zuciyar sa ne, sannan baya saurin yanke hukunci akan abu balle fushi amma idan ransa ya 6aci abin ba da'di.

Kwata-kwata sai ya rasa yanayin da ya shiga a lokacin,  shin na da'di ne ko kuma akasin haka?
shi kansa ya kasa ganewa, a zahiri yaji da'din kalmar yafiya da Alhaji ya furta masa duk dama tun kan ya iso ga Alhajin Ammi ta riga ta tabbatar masa da cewa Alhaji bai yi fushi da shi ba, amma ji daga bakin Alhajin yafi komai yi mai da'di har zuciya, gashi dai ya yafe masa kuma bai ga alamun zai hana shi komawa makaranta ba, amma abinda ya ringa yawo a 'kwa'kwalwar sa ya kuma rasa sukuni shine 'karshen furucin Alhajin da bai san manufar ta ba _....."....sai dai ka sani...abinda na riga nayi niyya sam bazan ta6a fasawa ba"._
Tuno maganar Alhajin ya sake yi a hankali ya 'dago ya kalle shi yayin da yaga fuskar Alhajin wasai ga dukkan alamu bashi tare da damuwa...Key 'din motar sa ya 'dauka ya nufi hanyar fita daga 'dakin yana fa'din " Na wuce yau na makara sosai".
Cikin 'karfin hali Yah Deen ya iya furta " Allah ya tsare".
Wa Alhajin sannan ya cigaba da tunanin ma'anar maganganun Alhajin amma ya rasa me suke nufi sam, cikin haka ya tuno abinda Ammi tace da shi " _yace muyi fatan faruwar Alkhairi_" .....tuno haka ne ya sanya shi furta " Allah ya tabbatar da Alkhairi akan komai".
A fili ya furta hakan tare da mi'kewa cikin sanyin jiki ya kama hanyar fita.

Koda ya isa parlour Ammi ka'dai ya tarar da itan ma fitowan ta kenan da Alhaji ya 'kira ta sa'ilin da zai fita, ga dukkan alamu Alhajin har ya fita dan babu shi a palourn.

Shima Yah Deen bai zauna ba kawai ya nufi hanyar fita yana fa'din " Bari inje in fara shirin tafiya Ammi hutun mu ya 'kare".

" Wai dagaske azumin kake yi ne?" Ammi ta tambaye shi da mamaki.
Sai ya amsa da fa'din " Erh Ammi dagaske ne mana".
Yayi maganar yana murmushin 'karyar da ya manta cewa ya shirga mata...banda girman kunyar ya zauna gaban su ya ci abinci ba mai zai sa shi wannan 'karyar.
Girgiza kansa yayi yana mai cigaba da tafiya izuwa ga barin palourn.

Har ya 'karasa fita Ammi bata ce da shi komai ba illah idanu da ta raka shi da shi tana tunanin " Ashe komai na iya canza mutum matu'kar abin n da muhimmanci ga rayuwar wanda abin ya same shi, yau ga shi Mu'een na Azumin nafila ta litinin da Alhamis abinda bata ta6a ji yayi ba tunda take da shi...Allah kenan mai juya Al'amura yanda ya ga dama ".
Har cikin ranta taji da'din faruwar hakan ta kuma godewa mahalicci.
_('Dan Ammi sarkin 'karya, sai dai kuma fa yayi sa'a karyar tasa tazo a dai-dai)._



~Comment Vote and share please.~ 👌🏻



*Salmerhn ku ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)


By
*Salmerh MD*

 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

🤞🏻
~KE TA DABANCE NUSEE TA, ALLAH YA 'KARA DAN'KON 'KAUNA...SOSAI NAKE JI DAKE HAR CIKIN JINI NA....~
🤞🏻
~MASOYIYA NANAH INA GODIYA SOSAI,  'KAUNAR KI A KULLUM SAKE YA'DUWA  YAKE YI CIKIN ZUCIYA TA~ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*


🅿 *42*

  Yana isa gida ya sanya wayar sa a caji tare da kunna ta, nan take kuwa sa'konni suka dinga shigowa amma ko bi ta kansu bai ba balle ya karanta abinda suke 'kunshe da shi.

Cajin awa 'daya wayar tayi sai ya cire ta, number Unlce Ja'afar ya fara dialling inda ringing 'daya ya 'daga kamar dama can zaman jiran 'kiran yake yi.

Ko amsa sallamar da Yah Deen ke yi masa ma bai yi ba kawai ya fara zazzaga masa masifar kashe waya da yayi tsawon kwanaki.

Yah Deen kam ha'kuri ya dinga bashi cikin kwantar da murya tare da shirga masa 'karyar baida lafiya ne shiyasa, burin sa kawai yaji ko Uncle Ja'afar na da masaniya akan abinda ya farun tare da son sanin ko yasan 6oyayyen shirin Alhaji akan sa....yayin da a masifance Uncle Ja'afar yace da shi " Da baka da lafiyan kuma ka sanar da ni ne?"
" So sorry bazan sake ba Uncle".
'Karamin tsaki yaja tare da fa'din ya jikin to?"
" Ai ina jin muryar ka na warke kamar ba ni ba".
Cewar Yah Deen yana 'dan smilling da bai wuce kan fuskar sa ba.
" 'Karyar banza sai kace ban san halin ka ba Mu'een".
Yah Deen 'yar dariya kawai yayi batare da ya 'kara fa'din komai ba.
Uncle Ja'afar ne ya sake fa'din"...ya batun school kuma, hutu ya 'kare ko?"

" Erh mun kusa komawa Insha Allahu 'karshen week 'din nan ma...ina Aunty na?"
Ya 'karashe da tambayar sa Anty Zainab.
Ja'afar kam yana shirin yanke 'kiran yace" Hala manta sunan da kayi saving number 'din ta a wayar kayi".
Bai sake sauraran jin komai daga gareshi ba kawai ya yanke 'kiran yayin da Mu'een ya bi wayar da kallo da mamakin rashin jin wani abu daga bakin sa da ya danganci damuwar da ke damun sa.

Ga dukkan alamu Uncle J bai san komai kan lamarin ba tunda baiga alamun hakan ko cikin kalaman sa ba.

Murmushi ya saki na jin da'din rashin sanar da Uncle J da Alhaji bai yi ba, nan take yana murmushin ya 'kira layin Antyn sa Zainab inda suka gaisa cikin sakin fuska da walwala itama tana mai mitan rashin samun wayar sa cikin kwanakin.

      'Karyar da yayiwa Uncle Ja'afar itama shi yai mata sai dai ita kam cewa tayi" Ya Ammi bata sanar da ni batun rashin lafiyar ba kuma?"
Ai da sauri ya bata amsa da fa'din" May be mantawa tayi Anty".
" Ammin ce zata manta da batun jinyar ka Mu'een?"
Anty Zainab ta tambaya mamaki bayyane cikin kalaman ta haka ma kan fuskar ta.
Sai yace
" Gashi kuwa, Anty ai babu mamaki...kinsan Ammi tunda ta samu wannan yarinyar ta daina so na, kullum masifa take min ban isa ko aikan yarinyar nayi ba sai ta tsigale ni".

Dariya Anty Zainab tayi tace" k'ilan kana muzguna mata ne shiyasa Ammi take yima haka amma ai yarinyar bata da matsala a yadda na fahimce ta".
Yace
" Ke de Anty kiyi shiru kawai amma ni da nake tare da su ni zan bada labari...".
Taran sa tayi da fa'din
"....Ai gaskiya ne Mu'een...ni dama nake cewa zan ro'ki Ammi ta bamu aron yarinyar danni fa tayi min gaskiya ina son ta sai mu zauna tare dukkan mu idan mun dawo Bauchi".
'Dan 6ata rai yayi yace " Anty ni kuma fa?"
" Har da kai ai sai kazama yayanta inda rabo kuma watarana da iznin Allah sai ka zamo mijin ta na har abada".
Da wuri ya furta " God forbid...Allah ya sawwa'ka Anty ina zan kai ta ni kuma?"
Zaro idanu Anty Zainab tayi tace masa" Inda ya dace da ita mana, jimin yaro da shiririta, har haka zaka ce Mu'een an gaya ma ana gayawa Allah yadda zaiyi ne?"
" Ni dai please Anty ki bar zancen nan...shima Allah zai kiyaye bazai bar hakan ya faru ba".
Anty cewa tayi " Ni dai da za'a ban za6i Allah ita zan za6a ka maka dan nasan ba 'karamin sa'a zakayi ba da samun ta".
" Hasara dai".
Ya fa'di 'kasan ma'koshi amma Anty sai da ta jiyo shi.
"...Hmm...Fatana ni dai a kullum inga ranar da za'a ce wannan yaron nawa na fama da zuciyar sa akanta..."

Lumshe idanu yayi yana tuno Nannen sa, masoyiyar sa, sahibar zuciyar sa, baya jin zai 'kara yiwa wata 'ya mace kwatankwacin son da ya yiwa Nanne har abada balle har tasa ciwon sa tashi, ko ita Nannen ma bata tada masa ciwon ba balle wata daban can da ya san bazata kai Nanne daraja a wurin sa ba.

Idanun sa a rufen cikin sanyin murya yace
" Babu ita Anty...ba ma za'a haifeta har abada".

'Yar dariya Anty tayi daga can 6angaren tace"...Zamu gani ai...in da rai kamar yau ne, ko angaya maka abin ana gudun sa cikin sau'ki ne tamkar yadda kake gudun abokai?"

Shiru yayi bai amsata ta ba sai ta cigaba da fa'din" Gara ka bari in mana kamun 'kafa wurin Ammi tun kafin wani ya riga mu".

'Kit!.. yayi saurin datse 'kiran cike da jin haushin maganar ta...cikin ransa yake ayyana" ina zan kai wannan abin da jiki ko'ina flat sam babu mamora, da'din me zata jiyar dani banda aikin kuka da ta iya da kayan takaici, yana ji cewa irin Noor ko a 'kafa aka 'daura masa Allah sai ya kunce ta ya tafi ya barta da gudu ma kuwa...har gara 'dayan yarinyar ma wato Ma'u, babu laifi ita tana da abin kallo ajikin ta...."

Take salo da tsarin tunanin sa ya canza, wuri guda ya 'kurawa idanu yana tariyo ranar da ya ha'da jiki da ita (Ma'u) yanda ya jima yana jin tudun 'yan matasan boobs 'din ta a jikin sa, tun ranar yake so ya samu damar ganin su da idanu amma sam ya rasa ta yadda hakan zai faru.

Tsaki ya saki a fili yana lumshe idanu tare da kishingi'da, a hankali tunanin sa ya koma kan Husnah, tuno yanayin surar jikin ta take sai ya saki ajiyar numfashi mai 'dumi, gani yake yi kamar ni har abada har in 'kare kaf 'din rayuwa ta bazan ta6a kamo Husnah 6angaren halitta ba, a fa'dar sa bai ma ga alama ba da har Anty ke yi masa fatan kasancewa da ni.


Wannan 'dan tuno Husnah da yayi sai yasa take yaji shi on, wani irin shau'kin son kasancewa da ita ne ya kama shi.

Aikin kenan dama indai tsakanin Yah Deen da Husnah ne ta 6angaren sa babu komai cikin zuciyar sa daya danganci so ko 'kauna illah son kasancewa da ita da yake yi koda wani lokaci, ya kuma rataya hakan akanta ya maida ta abar jin da'din sa kawai a mori rayuwa.

Yayin da Husnah ke yi masa so, so irin na asali mai ninkuwa a duk lokacin da take tare da shi, soyayya take masa wanda babu gauraye ko algus acikin sa, da tunanin yiyuwar aure tsakanin su watarana.

Akwai wani cousin 'din ta mai suna Hisham dake tsananin 'kaunar ta da aure amma ta'ki sake mai fuska ta 'kwallafa ranta akan Yah Deen bata san shi a 6angaren sa abin ba haka yake ba sam....(ni kuwa nace stop deceiving ur self am mata).

Imrana baya nan ya tafi Kano yanzu shiyasa gidan ya kasance shi ka'dai ke rayuwar sa babu mai takurasa....wa'dannan shai'danun tunanin da yayi ta biyewa zuciyar sa akai ne ya sanya shi jin muguwar sha'awa na taso masa.

Sai yanzun yaji babu dadi da rashin Imrana a kusa, ya so da yana nan da sun kammala maganar waccan yarinyar da ya'ki bashi ha'din kai akanta kwanaki, amma sai akayi rashin sa'a baya gari a ranar....fatan shi dai kawai shine Allah yasa dagaske Imrana yake yi cewa da yayi yarinyar itace waccan me zuwa gidan shi da 'yar gidan Ammin nan...cuz waccen tafi tsaye masa a ransa, ita yake so ya mora yanda take da 'danyen 'kuruciyar nan yasan zai kwashi gara.
(Hmm....Allah ya shiryi wannan 'dan gidan Ammin gaskiya).

Yanda abin ya gama ratsa shi ya kashe mai jiki nan take ya sanya shi mantawa da 6acin ran da Alhaji Baba yayi da shi kwata-kwata, neman hanyar da zai kawar da abinda ke damun sa kawai yake yi.

Bashi da mafita game da abinda yake ji wanda tasa dole ba dan yaso ba ya dannawa Husnah 'kira tare da sake yin luf kan kujerar da yake kwance..idanun sa duk sun 'kan'kance sun yi wani iri da su...yasan Husnah ka'dai yake da shi da zata taimake shi cikin wannan yanayin batare da yasha wahala ba.

Yanajin wayar tafara ringing sai ya lumshe idanu ya kifa wayar kan kunnen sa na dama yayin da hannun sa 'daya ke yawo saman cikin sa zuwa marar sa a hankali.

Har sai da wayar ta kusan tsinkewa kafin Husnah ta 'dauka tana yatsina fuska cike da jin haushin korar da yayi mata, bayan haka kuma bai ko 'kira ta ba tun ranar, haka ma sa'k'konin ban ha'kuri da tai ta tura masa ko reply 'din guda bata gani ba, da wannan tunanin ta daure a yatsine ta furta" Hello!"

Shiru yayi yana murmushin mugunta, tuno irin cin mutuncin da yayi mata rannan da tazo.
" Helloo!!
Ta sake fa'di kamar dole aka sanya ta.

Yah Deen bai amsa ba illah numfashi da ya furzar mai 'dumi wanda hatta Husnah sai da ta jiyo shi take kuwa jikin ta ya amshi sa'kon kamar wawuya, cikin sanyin murya da dauriya ta sake fa'din" Hello!!!... wai waye ne?"

Sai yanzun ya bu'di baki yace
" Husnah!"
Cikin mayaudariyar muryar sa mai narkar da zuciya.

Husnah na jin yanda 'kira sunan ta ta wani lumshe idanu saboda jin wani irin abu da ya tsarga mata tun daga kanta ya ratsa mata har 'kafafu, wani sanyin da'di  da farin ciki taji ta ciki marar misaltuwa wanda ya sanya ta kasa amsa sunan tan daya 'kira.

Yayin da Yah Deen ya cigaba da fa'din ".....Husnah har kin manta da ni da wuri haka ko?..kenan goge layi na kika yi cikin wayar ki?"

'Kasan ma'koshi tayi dauriyar amsawa da " um-um".
" To me yasa kika share ni? Baki damu kiji halin da nake ciki ba dan baki sona ko?"
Muryar ta na 'dan rawa tace" Ka manta abinda kayi min ne Mu'een?"

Murmushi yayi daga inda yake cikin son kawar mata da wancen zancen yace" Ba 'karamin kewar ki nayi ba fa Husnah na damu sosai...yaushe zaki koma school please? "
" Sunday".
Ta bashi amsa a takaice.
Sai yace
" Fatan kin shirya ha'duwar mu dan ni gaskiya na matsu...dan Allah ki taho da wuri karki sani jiran ki kinji?"

Shiru tayi masa kawai tana jin duk wasu damuwar ta na sulalewa suna barin ta, 'kuncin dake 'kunshe cikin zuciyar ta tun ranar rabuwar su kwanaki ka'dan da suka shu'de duk babu su,  irin soyayyar da take yi masa ita kanta bata san adadin yawan ta ba...irin makauniyar soyayyar nan dake ribatar 6angare 'daya cuz sam bata iya yin dogon fushi da shi koda kuwa mai ze mata, ko yanzun ma bai ko furta mata kalmar ha'kuri ko 'daya ba amma tana jin har ta sau'ko daga fushin, sannan bata iya 'kaurace wa bu'katun sa koda wani lokaci, ba kuma ta ganin ai bun alfashar da suke aikatawa...bai ta6a furta mata kalmar so ba amma ita sai take ganin kamar shima yana son ta musamnan idan taga yanda yake lalla6ata wajen sau'ke bu'katar sa sai taji kamar ta gama mallakar sa ne kawai ita ka'dai.

Maganar sa ne ya katse mata tunanin da take yi, inda yace" Yanzu me zan samu to?"
..."...ba komai".
Ta bashi amsa tana komawa ta kwanta rigingine tana kallon fan 'din dake sama.
Bai damu ba sai ma ya sake fa'din" Turo min abin nan in gani".
" Wani abu kuma?"
Ta tambaya haka kawai bawai dan bata gane abinda yake nufi ba.
Muryar sa kamar ta marasa lafiya yace" Kin fini sani ai ko wula'kanci zakiyi min yau 'din?"
"....a a naga kana da shi kala-kala a wayar ka ne ai..."
Bata ma kai 'karshen maganar tata ba ya tareta da fa'din" ai na san dasu na zo gare ki ko"!
Cikin rashin damuwa tace dashi
"Ni dai a a banda lafiya yanzu".

" Please Husnah karki min haka mana".
Ya 'kara fa'di a 'dan tsawace.
Yayin da Husnah tayi dauriyar sake fa'din" Allah bazaka gani ba".
Ta bashi amsa tana 'ka'kalo murmushin mugunta ta sanyawa fuskar ta na dole duk dama har cikin ranta taji da'din 'kiran nata da yayi, amma ta ganin wannan ka'dai shine iya jayayyar da zata iya yi masa a yanzu kafin ha'duwar su,  wanda take ganin da shine zata rama cin mutuncin da yayi mata rannan a Shuwarin.

Yayin da tana furta hakan Mu'een ya yanke 'kiran 'kat batare da ya 'kara koda kalma ba.

Ita kam husnah da ganin hakan sai ta 'kara fa'da'da murmushin ta dan for sure tasan haushi yaji kuma har cikin ranta taji da'din hakan a fili ta furta cewa" ur turn dear..kaima kaji inda da'di, 'kila daga yanzu zaka san muhimmanci na".

Sai dai me...tun ma kafin ta yi wani motsin kirki a wurin taji wani 'kiran ya kuma shigowa cikin wayar ta, tana dubawa sai taga video call ne ya 'kira.

Bayyananniyar murmushi ta saki tare da girgiza kanta gefe da gefe, receiving call 'din tayi tare da mi'kar da hannayen ta sama ta yadda zasu ga juna da kyau.

Wayar na gama connecting sai ya bayyana kan fuskar wayar ta..." i knew it dama ai" Ta ayyana cikin ranta sanadiyan ganin yanayin da yake ciki, tun cikin voice 'din sa ta fahimci ainahin halin da yake ciki yanzu kuwa da idanun ta suka gane mata shi sai ta gama tabbatar da zargin ta domin ba 'karamin sani tayi masa ta wannan 6angaren ba.

" I thought fushi kayi ai".
Ta fa'di tana kallon cikin idanun sa.
'Dan ha'de gira yayi kamar bashi ba yace" me yasa zan yi..ko dama burin ki kenan nayi fushi?"
Ya 'karasa maganar yana 'dage gira 'daya sama.

Tana shirin yin magana ya dakatar da ita da fa'din" Nuna min"...inda yayi maganar bayan ya sake yin luf da tunanin bazata yi masa gardama ba sai kawai ya 'kura mata idanu.

Husnah kafa'da ta no'ke sannan tace" An'ki".
A 'dan hasale yace
" Haba Husnah kashe ni kike so kiyi ne?"
" Nima ai kashe nin ka kusan yi da 6acin ranka".
Ta bashi amsa cikin salon son tuna masa kuskuren sa.
" Bazan sake ba i promise u, but please mana Husnah kinji".
Ya fa'di da kwantar da murya alamar rarrashi.

Husnah sai ta 'kara no'ke kafa'da wannan karan bata amsa masa da baki ba.
"...Husnah be serious mana u know i missed u kin 'dauka da wasa nake yi ne?"
" Sai kaima ka nuna min nagani tukunna".
Shiru yayi kawai ya tsura mata idanu tsawon da'ki'kai yana kallon ta irin kallon nan mai matu'kar 'dauke hankali da ma'anoni da dama, wanda irinta da ta san shi ta fuskar bu'katuwa ita ka'dai ce zata iya fassara ma'anar kallon...amma Husnah sai ta basar kawai ta tallafi fuskar ta da hannun ta itama tana kallon sa.

Haka suka cigaba da aikawa junan su kallo Husnah kam ji tayi so da 'kaunar sa na 'kara ninkuwa mata a zuciya yana ratsa mata har cikin jini, yayin da ta 6angaren sa banda tarin jarabar dake cin sa babu komai.

Cikin wata iriyar murya mai tafiya da hankali yace mata" Husnah ni kike wa wa haka ko?"
Ido ta rausayar tana gimtse dariya tace" Ni dai kayi ha'kuri".

" Naji to...kin yadda da dare zaki tura min?" Gira ta 'dage masa sama alamun ta yadda....sai yace " To karki manta ki 'kira ni".

Bata furta komai ba sai kawai ta 'dago masa yatsun ta ta karka'da alamun " bye".
Tana murmushi.
Shima 'din murmushin yayi mata tare da yanke 'kiran yayi gefe da hannun sa dake ri'ke da wayar ya mi'kar da shi yana sakin numfashi a hankali...ya jima a hakan kafin bacci 6arawo yayi gaba da shi.

Ai kuwa da dare misalin 'karfe tara Husnah ta 'kira shi kamar yadda ya fa'da harma yayi shirin bacci dan haka suna gama tambayar lafiyar junan su bai bari maganar tayi tsayi ba ya tuna mata al'kawarin da tayi masa....taso ta sake ja masa aji amma da yake yasan salon da yake bi da ita haka kafin ya kwanta sai da ya tabbatar ta tura masa photunan jikin ta da dama harda chat suka yi...kafin su rabu ma sai da ya tabbatar ta manta da batun koranta da yayi sun koma sha'kuwar su kamar babu abinda ya ta6a faruwa.



*****
            Ana gobe zai koma makaranta yana zaune yana faman harha'da kayayyakin amfanin sa cikin jaka duk ya hautsine ko'ina, lokacin 'karfe hu'du da 'yan mintina ne na yamma dawowar sa kenan daga masallaci sallahr la'asar sai ya fara ha'de kayan, so yake idan ya kammala ya tafi can gida gurin Ammi dan yau duk bai je can gidan ba.

Yana tsaka da ha'de kayan kawai yaji sallama a tsakar kansa kamar daga sama, tun zuwan sa gidan bai ta6a zuwa ba sai yau tamkar  mafarki.

Fara'a ya saki da ganin sa, cikin sakin fuska ya furta" Alhaji da kanka?"

Murmushi Alhaji Baba yayi yana bin 'dakin da duba cikin hikima ta yadda ba zai fahimce shi ba daga 'karshe ya dire idanun sa kan Yah Deen inda ya bi ilahirin jikin sa da kallo daga sama zuwa 'kasa.

Wando three-quater ne ajikin sa wanda bai ma sau'ka ko kan gwiwar sa ba ko singlete babu ballantana riga.
Wanda tun dawowar sa daga masjid ya raba jikin sa da kayan...sam matu'kar yana gida bai fiya zama da kaya wadatattu ba ya riga ya saba da haka, wanda hakan sai ya tafi da tunanin Alhaji kan cewa kenan babu mamaki a hakan kullum yarinyar take zuwa ta tarar da shi, ga ta mace har mace me ze hana shai'dan yin nasara akan su bayan ke6ewar su tare?
Ba yaso ya yawaita zargin Deen kan irin hakan musamman da yake babu wata 'kwak'kwaran shaida da ta bayyana hakan, amma

Please Login or Register in order to submit comment