Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fahimtar farin cikin dake fuskan Saif wanda ba na komai bane face na zuwa kawai da tayi ta duba Yah Deen...tana lura dashi sosai farin cikin nasa na fita tun daga cikin zuciyar sa ne.
Hakan ne ya 'kara fahimtar da ita 'dumbin 'kaunar da suke yiwa 'dan uwan su.


'Bangaren Yah Deen kuwa bakin sa nawi yayi masa sosai, banda ma haushin dayake ji yana cin sa arai, ganin ta ka'dai da yayi ya rage masa kaso dayawa na abinda yake ji yanzu, ba gaisuwar ta yake bu'kata ba burin sa kawai yaji an sake mallaka masa ita ne, burin sa ta sake kasancewa matar shi ta har abada...a lokacin ne yake da duk wasu kalmomi da zai iya fahimtar da ita yawan 'kaunar da yake yi mata.


Washe gari Alhaji Baba da ya fita lambu sai ya samu lokaci ya 'kira 'kanin sa Ja'afar nan yake yi masa bayanin 'kudurin dake cikin ransa na son bada auren Noor da yake da buri wa Ishaq.


Uncle Ja'afar kam take ya nuna 'kin amincewra sa da fa'din.." a a ai hakan zai zama ne tamkar an shiga hakkin su gaba 'daya musamman ma shi Ishaq 'din, tunda kam ba aure ne da shi ba, kuma ma Noor matar abokin sa ace za'a bashi ai sai ya ziya ama sanadin rabuwar abotan su kenan..dan yasan Mu'een bazai juri hakan ba, kuma ma Alhaji kai baka tunanin halin da shi Mu'een 'din zai sake shiga ne? zuwa yanzun fa ya kamata ace an watsar da komai...yana son matar shi kawai a maida auren su idan ta amince da hakan shine ka'dai mafita in yaso sai a sanya idanu sosai akansa shima Ishaq 'din ayi masa fatan Alkhairi Allah ya bashi wata ta gari".

Shiru Alhaji Baba yayi yana tunani.
Uncle Jafar jin shirun yasa shi fa'din" Baka ce komai ba Alhaji?"
" Ka bari zanyi tunani".
Cewar Alhaji Baba wanda daga hakan suka yi sallama kowa ya ajiye tasa wayar.


'Bangaren Noor kuwa ganin tana gida ya sanya Abdulhakeem matsawa akan yana so kafin ta koma manyan sa suzo ayi magana in yaso data 'kare karatun sai a 'daura auren su kawai ta tare a gidan sa.

Duk yanda ta so ta kauce masa abin gagarar ta yayi domin ya matsa sosai, shi har ya yi magana ma da mahaifiyar sa akanta ta dai nuna 'kin amincewar ta amma yasan da zaran mahaifin sa ya amince shikenan.


Yanda ya matsa 'din ya sanya dole ta yiwa Ummah maganar cewa iyayen wanda ke neman auren ta naso su zo daga Kano wai.

Ummah kam shiru tayi tana duban ta da mamaki tace" Kina nufin wani auren daban zaki yi ne wai?"
Tuni ta marairaice tace" Ummah toni ya zanyi? ya matsa min kullum na rasa yadda zanyi da shi..".

Ummah baki ta ta6e gami da kawar da kanta gefe sannan tace" Sai kije ki sanar da iyayen naki ai kinsan suke da zancen auren ki ni ba ruwa na".

Koda ta shiga 'daki kuka ta ringa yi sosai, haushin kan ta ma take ji da danasanin biyo Anty Zainab da tayi, tasan ba dan ta zo 'din ba da duk hakan bazai faru ba.

Saif yace da ita Yayan sa na rashin lafiya ne saboda ita toh taya zata iya tunkarar su Ammi da batun wani daban kuma, ai sai suga kamar bata da tausayi ne shiyasa, ita kuma har ga Allah bata jin zata sake iya zaman aure da shi, a yanzu banda tausayin sa babu komai a zuciyar ta game da shi.



_Wai ina labarin Husnah ne?_





Comment
Vote
Share






*Salmerh ce*😍💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)



By
*Salmerh MD*


*Wattpad @*
*Serlmerh-md*



💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*



_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_


*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*



🅿 *91*


Waya ta 'kira Anty Zainab da niyyan ta nemi shawarar ta amma sai ta kasa fa'din komai sai kuka, hankalin Anty Zainab tashi yayi sosai da jin hakan nan ta kwantar mata da hankali da al'kawarin gobe zata zo ta same ta, dama ta 'kira ne akan ga6a domin itama Anty Zainab in tana cikin tunanin ta ta 'kira, bata da'de da gama waya da Uncle Ja'afar ba tana cikin tunanin ta inda zata fuskanci abin sai gashi ta 'kira ta.


Washegari ta sa Saif ya sau'ke ta bayan tace da Ammi zataje gaida Ummahn Hudah ne.

Koda taje suka gaisa da Ummah suka 'dan ta6a hira ka'dan sai Ummah ta basu wuri kamar dama tasan da maganar da zasu yi sai ta tafi cikin gida gun ayyukan ta.


Nan Hudah ta samu sararin bayyanawa Anty abinda ke damunta...tace ita bata san ta ina zata fara tunkarar Alhaji Baba da batun auren Hakeem ba.


Anty Zainab shiru tayi tana nanata abin cikin ranta.
Wannan shine ana wata ga wata.
Ajiyan numfashi ta sau'ke sannan ta kalle ta tace" Ni har ma na rasa abinda zan ce da ke wallahi...kina nufin wai dagaske bakya tunanin sake zama da Mu'een ne yanzu?"
Shiru Noor tayi ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsun hannun ta...kowa irin tambayar da yake yi mata kenan, to ita me zata ce da su? amsar wannan tambayar tuntuni ta bayyanar musu da shi me yasa kuma suke son sake maida maganar baya?


Anty Zainab rage sautin muryar ta tayi sosai ta sake matsowa kusa da ita tace" Hudah kin san mun 'dauki tsawon lokaci tare da ke ko haka ne ko ba haka ba?"
Da sanyin murya ta amsa ta da fa'din" Hakane Anty".
" A iya zaman mu dake na ta6a tilasta ki yin abinda ranki bai so ne?"
Nan ma kai ta girgiza mata.
" Na ta6a cusa miki ra'ayin son Mu'een ko kuma na ta6a nuna miki rashin jin da'di na game da 'kiyayyar da kike yi masa?"
" A a Anty baki ta6a ba".
" Kin san dalili?"
" a a".
" Toh saboda naga ra'ayin ki ne hakan shiyasa na biye ki, kuma na fuskan ci ciwon da kike ji a lokacin cikin zuciyar ki shiyasa ban ta6a takuraki akan sa ba, nasan duk wacce irin hakan ya same ta dole ne taji babu da'di amma Noor bazan 6oye miki ba, dai-dai da rana guda ban ta6a farin ciki da rabuwar ki da Mu'een ba, idan kuwa naga irin 'kiyayyar da kike yi masa har cikin zuciya ta nake jin babu da'di kinsan dalili?"

Kai ta girgizawa Antyn.
Yayin da ta cigaba da fa'din" Saboda 'kaunar da nake yi masa ne matsayin sa na 'dana, Mu'een tun yana da shekaru shida a duniya ri'kon sa ya dawo hannu na bai kuma bar gaba na har sai lokacin da ya shiga Jami'ah a lokacin kuwa kinsan ya riga ya mallaki dukkan hankalin sa ya san me ya kamata yayi da rayuwar sa, Noor ki kwatanta yanda ni nake ji matsayi na na uwar ri'kon sa da yanda Ammin sa zata ji ita datake matsayin mahaifiya agare shi wacce ta haifi abinta da kanta, kinsan dole nata fin nawa ne ko?...wallahi ko ala'kar dake tsakanin ki da Hakeem ban son ta, amma babu yanda zanyi, inaso inga auren ku ya gyaru da shi amma na rasa ta ina zan fara, ina ganin ki agaba na amma ban isa nayi yanda nake so ba saboda gudun kar inci amanar da Ammin ki ta bani, domin an kawo ki wuri na ne da niyyar shiga tsakanin ki da Mu'een..kinga babu yadda zanyi in nuna miki muhimmancin dayake da shi agare ki tunda ga dalilin zuwan ki waje na, shiyasa kika ga ban ta6a furta komai agare ki ba, amma wallahi nasan hatta Ammi kawai dauriya take yi tana biye miki ne saboda farin cikin ki, ko lokacin da kuka ha'da baki da ita kika canza layi ma ba 'karamin takaici naji ba haushi sosai hakan ya bani har ya sani furta wasu 'yan maganganu idan baki manta ba... amma ba wai nayi ne saboda wani abu ba kawai dai raina ne ya 6aci da ganin 'kyamar da kuke nunawa duk wani abinda ya shafe shi...dukkan ku ina son ku Noor ina kuma son farin cikin ku, yanzu da kike gaban iyayen ki kika bar hannu na a yanzu ne nake da damar da zan iya bayyana miki komai da ke raina...Ke da kanki kinsan Mu'een na 'kaunar ki kuma nasan kema kina son shi Noor me yasa zaki da'kile muku farin cikin ku ta hanyar shigowa da wani cikin rayuwar ku? me yasa bazaki koma 'dkin mijin ki na asali ba? kar kiyi zaton auren wani da zakiyi mafita ce agare ku domin shima baki da tabbacin nagartar halayyar sa, may be idan kika bincika ki samu nashi halin ninkin na Mu'een ne ta iya yiwuwa kuma ki kasa fahimta har sai bayan auren ku a lokacin ya zakiyi da shi to?..ko shikenan kin ringa yin aure kina fitowa kenan saboda mazajen nada wasu halayya?, na tabbata bazaki yadda da hakan ba, me ze hana ki daure ranki ki koma ga mijin ki tunda shi kin riga kin san halayyar sa kuma gashi nan da kanki kinsan yayi nadama sai ku rungumi rayuwar ku ku rufa asirin junan ku, dan Allah zakiyi badan komai ba nd na tabbata Ammin ki kanta zata fi farin ciki da hakan, kar kiga wai su suka raba auren ku da shi, ina da tabbacin har gobe suna son sake ganin ku tare kawai farin cikin ki suke son gani da kuma gudun danne miki hakki shiyasa suka basar...yanzu ki zauna kiyi tunani da kanki ki ga me yafi dacewa da ke, koma bazaki tausaya wa halin da yake ciki ba dan Allah ki zauna kiyi nazari ki bi dacewa ba wai dan nayi miki maganar ba a a, kiyi abinki saboda Allah, ni ban miki magana dan ki takura kanki ko kuma dan in tilasta ki koma masa ba face dan ki fahimci gaskiyar da ta kasa bayyana miki.
Horo ko wani irin horo kun hora min yaro Hudah sauran kuma sai dai in bayan sa kuke son gani...".
Ta 'karasa tana murmushi sannan ta 'dora da fa'din" Kinga ko Uncle J ma jiya muka gama magana da shi kuma ban sanar da kowa ba wannan tsakanin ni dake ne, yace Alhaji Baba na shirin bada auren ki ne ga wani abokin Mu'een amma ya dakatar da shi saboda yafi so ki koma ga mijin ki ya ma ce idan ya samu amincewar ki zuwa nextweek yake so amaida auren kun kafin tafiyar ki in yaso sai ki 'karasa karatun da auren ki..ke ya kk gani jira kawai yake yaji daga gare ki yanzu dan ke ke da linzamin komai".


Kuka sosai Noor ta sanya ta kife kanta tsawon lokaci babu wanda ya sake furta komai tsakanin su Anty ma shiru tayi tana jimamin wannan lamari, tasan duk laifin sa ne koma menene da ace bai aikata abinda ya aikata ba da duk hakan bazai faru ba, da yanzu suna can zaune a gidan su cikin farin ciki da iyalan sa.


Ganin kamar kukan Noor 'din bashi da alamun tsagaitawa ne ya sanya Anty Zainab fara rarrashin ta tana neman afuwan magangun da tayi tace idan na 6ata miki raine kiyi ha'kuri Noor ko ka'dan ban fa'di abu guda da niyyan 6ata miki ko cin zarafin ki ba, abinda ke raina kawai na gaya miki saboda ganin kamar na isa in fa'da 'din ne, nasan dole zakiji babu da'di amma please kiyi ha'kuri on behalf of dukkan iyalan Taheer Manga nake baki ha'kuri, Noor kar kiga laifin mu kuma kar kiga kamar son zuciya muka nuna, dukkan wanda irin hakan ya faru da 'dansa dole ne yayi wani yun'kuri dole zai aikata abinda yaga yafi dacewa ne shiyasa kika ga mun dawo miki da maganar baya kuma ba wai dan kema bamu son ki bane a a kawai dai dacewa muka duba sai dai nasan a yanzu bazaki ta6a fahimtar hakan ba, inaso kiyi mana afuwa dan Allah idan kinji 'kudurin mu ya 6ata zuciyar ki..ni zan tafi amma ina so ki zauna ki nutsu kiyi nazari kafin wani lokaci ina so in san abinda kika yanke.."
Anty ta shi tayi tai mata sallama ta fita nan taje ta samu Ummah ma suka yi magana..a nan ta sake fahimtar Ummah ma ba da'din hakan take ji ba, tunda taji cewa akan ta lafiya tayi masa 'karanci duk sai take tausayin sa, Ummah tace su fita harkar ta kawai duk abinda suke ganin ya dace suje suyi.

Anty Zainab ne tace a a kam ba za'a yi haka ba, Umman Saudah ai hakkin ta ne yanzu dole sai an nemi amincewar ta kafin a zartar da wani hukunci".
" Hakane kam..to Allah ya za6ar mana mafi Alkhairi".
" Ameen Ameen" Anty Zainab ta amsa ta da shi sannan ta yiwa Ummah sallama ta fita daga gidan gaba 'daya.


Nasiha Ummah tayi wa sosai akan hakan ta kuma bata wasu addu'o'i tace ta ringa yi ta kuma ro'ki Allah akan yayi mata za6i mafi alkhairi...kar ta wani ru'dar da kanta domin dukkan mafita yana wurin Ubangiji ne..".



Anty Zainab da 'kafan ta ta koma gida kuma tun a hanya ta 'kira Uncle Ja'afar tayi masa bayanin abinda ke faruwa bai damu ba sai yace a barta ta samu lokaci tukunna.


Anty bata ko tattauna batun da Ammi ba dan tasan hanawa zatayi zata ga kamar za'a takurawa Hudah ne hakan yasa Anty Zainab taja bakin ta tayi shiru sai dai a kullum bata fasa Addu'a akan Allah ya daidaita lamarin ba.


A ko wani da'ki'ka rashin natsuwa ke sake ziyartar ta haka take yini ba ko walwala domin kuwa sosai Hakeem ya matsa mata a hakan ma bata fasa Addu'ahn da take yi kullum ba, wani sa'in yini take yi da wayar ta akashe saboda Hakeem ka'dai, gefe guda kuma maganganun Saif da Anty ke mata yawo aka, banda wanda Ummah ke shigar mata cikin brain 'din ta kusan kowace rana tana sake nuna mata ribar da mai ha'kuri ke da shi, ta kan ce ita kanta lokacin da labarin ainahin waye Muhammad ya iso gareta ba 'karamin ba'kin ciki taji da auren da ke tsakanin su ba dan a ganin ta bai cancanci a ha'da jini da shi ba, amma tunda taji cewa ya bada sakin Noor shikenan kuma sai jikin ta yayi sanyi, bata tsinke da lamarin ba sai da taga ya kasa samun cikakken lafiya tun rabuwar sa da matar sa tace da 'kafafun ta ma ta sha zuwa duba shi idan an dawo da shi gida da yake zuciyar tausayi ne da ita tuni ta zubar da makaman ta ta fara tausaya masa..." Bani da tabbacin ga dalilin ciwon sa amma ina ji ajikina kina da ala'ka da ita, kuma naji wasu ma na fa'de cikin gari...bazan yi son kai ba domin bamu san inda rana zata fa'di ba...haka nasan idan har ya kasance kece matar sa na san mu bamu isa mu hana ku rayuwa tare ba..kinga anan dole ne ke ki danne naki burin kibi za6in da Allah yayi miki..idan kika cigaba da ha'kuri sai kiga Allah ya dubi zuciyar ki sanadin biyayyar auren ki sai ya saki a aljannar sa ma'daukakiya kinga idan hakan ya faru ai bakiyi hasarar rayuwar duniyar ki ba ko?"
" Hakane Ummah".
" Toh ki yi ha'kuri ni dai a kullum shawarar da zan baki kenan shine ki sawa ranki ha'kuri ki rungumi 'kaddarar ki kinji?".
" Insha Allah Ummah..nagode sosai..".
" Yauwa Uwa ta..idan kin kunna wayar ki ma ki 'kira Addar ki, 'dazun take gaya min wai a kwanakin nan bata samun ki sai ki neme ta kinji..".
" Uhum" Tace gami da tashi ta bar inda Ummahn ke zaune.


Cikin 'daki ta koma ta rizgi kukan ta son ranta kafin daga bisani ta nemi layin Addar tata.

Ko Addah maryam ma shawarar da ta bata kenan duk kalan na Ummah ne wanda zuwa wannan lokacin ita kanta ta fara jin wani 6angare na zuciyar ta na yin na'am da batun amma mafi rinjaye na zuciyar tan yana garga'din ta ne yana kuma tuno mata da can abinda ya wuce abaya..ji take kamar ace an canza ta ba ita bace yafi mata, wani sa'in har ji take dama Allah ya 'dauke ranta 'kila hakan zai fi mata sau'ki..har ga Allah ita bata son komawa auren sa amma ya zatayi? abu ne mai mai matu'kara wahala agare ta ta iya duban idanun su Ammi tace da su wani daban zata aura ba 'dan su ba, aganin ta sam Ammi bata cancanci hakan daga gareta ba bayan duk 'kaunar da ta nuna mata arayuwa.


Tun ba yau ba ta za6i ta farantawa Ammi fiye da kanta wanda hakan ke nuni da cewa ta amince da sake zaman aure da Mu'een ne, amma inda matsalar take yanzu shine ita sam bata san ta ina zata fara furtawa ba, a zuciyar ta take jin ta amince saboda Allah da kuma Ammin ta amma bakin ta yayi mata nawi da furtawa.


Addar ta Saudah ka'dai ce bata yi na'am da batun ba cuz ita cikin gari take tana kuma yawan jin maganganu akansa musamman da yake rayuwar babban gidan take yi shiyasa a kullum aibun Mu'een baya ta6a barin kunnuwan ta.


Hatta Yah Usman ma bai nuna rashin amincewar sa ba lokacin da Ummah ke bashi labari sai yace Allah dai ya shige mana gaba.
Abinda kawai ya iya fa'di kenan da yake shi ba gwanin jan magana bane hakan yasa bai sake sanya bakin sa ba..dama ace Saudah ce ko Maryam da a matsayin sa na babban wan su dole ne zai yi wani yun'kuri amma Noor kam yasan ko ya fa'di wani abin ma aikin banza zai yi domin ita tun mahaifin su na raye aka bawa Alhaji Baba ri'kon ta so yanzu su ke da iko da ita ba shi ba...gashi sanadin su har waje ta samu daman fita dan yin karatu wanda ko cikin 'ya'yan Alhajin ma ya tabbata babu wanda ya fita karatu a waje ita ka'dai suka bawa wannan gatan...da ace kuwa suna da son kansu da nasu 'ya'yan ka'dai da ya tabbata Noor ko kusa da jikin 'dan su ma bata isa taje ba balle har batun aure ya ha'da su...talk more of fita malesia karatu.

Wannan tunanin yayi shi ne cikin zuciyar sa kawai amma a fili bai wani yi dogon magana ba.




*****
Cikin satin kuma jikin Yah Deen ya matsa sosai hatta Uncle Ja'afar sai da yazo Bauchi, idan yana tari har ta hancin sa jini ke fita duk ya galabaita baya iya ko yin numfashi mai kyau dole aka tafi da shi asbitin koyarwa dake garin Zaria.


Tuni Uncle Ja'afar ya fara shawarar fitar da shi waje ma amma sai likitocin suka nemi abar shi tukunna akwai possibilitin sabon dashe da zuciyar sa ke so ayi dan gab zuciyar tasa take da daina yi masa amfani kuma koda anje can 'din ma duk zancen 'daya ne..so idan ance za'a ja lokaci kuma yana iya rasa ransa ma gaba 'daya duk da ba lallai ne sai anyi dashen ba amma dai hakan na da matu'kar muhimman ci..sai dai kuma hakan zai iya zama tarihi idan zasu iya wani abu..likita yace su tanadi abinda suka tabbatar zai sanya shi farin ciki da farkawar sa idan anyi sa'a ma yin hakan zai iya sau'kar da kaso mafi girma daga cikin ciwon nasa.

Dole ba dan suna so ba suka ha'kura suka zubawa sarautar Allah idanu sai dai zu'katan su cike da yake tunanin abinda ya kamata su tanada kowa ya rasa mafita yayin da dukkan su suka zurfafa tunani wajen gano abinda ya dace suyi, kowa tunanin sa kan Noor ya fa'da dan sun san itace ka'dai matsalar sa a yanzu sai dai ta ya zasu iya sanya shi farin ciki da batun ta wannan me har yanzun sun kasa ganowa..Duk 'ko'karin da ya kamata ace likitocin sunyi sun yi shi akan sa kafin su samo kan matsalar tasa.


Kwanaki na sake 'karatowa lokacin tafiyar Noor na sake matsowa domin kwanaki hu'du ya rage mata ta tafi..sam bata san cewa ankai Mu'een Zaria ba saboda babu wanda ya sanar da ita, Saif kuwa da shi aka tafi balkanatan taji labarin daga wajen sa, Zaidu kuwa dama tuni ya tattara ya koma Taraba wurin Uncle Ja'afar so baya gida yanzu.


Kan batun tafiyar tata taje gidan Alhajin domin su tattauna da Anty hadda Ammi ma, nan ta tarar da su kowa jigum-jigum gashi dama tun ranar da suka yi magana da Antyn basu 'kara ha'duwa ba ko awaya basu gaisa ba yau kusan kwana shida kenan rabon su da juna shiyasa ma ta raso ta zo.


Hankalin ta tashi yayi da ganin yanayin su Ammin gashi da alamu hankalin su duk ba wuri guda yake ba.

A bakin Anty Zainab take jin labarin abinda ke faruwa..wanda nan take taji gaba 'daya tsigar jikin ta ya tashi.
Bata kai ga dai-dai ta natsuwar ta ba taji wayar Ammi na ringing nan duk suka maida hankalin su kai..Saif ne ke yiwa Ammi bayanin duk abinda likitocin suka ce..harda lokacin da suka nemi abasu dan shawo kan abin suga ko dashen ne ya dace ko kuma zasu dace su shawo kan matsalar tunda da saura zuciyar tasa bata daina amfani ba har yanzu.

Ammi kawai hawaye ne ya fara gangaro mata wayar ma sulalewa tayi ta fa'di kan cinyar ta batare da ta kula ba..." Allah ka jarabce ni, Yah Allah ka bani ikon cinye wannan jarrabawar..".
Haka ta fa'di cikin kuka wanda da sauri ni da Anty Zainab muka zo kusa da ita ni kam ban iya magana ba illah kukan da yaci 'karfi na ganin halin da Ammi ta shiga.


Anty Zainab ma hawaye take yi tana kuma bawa Ammi baki..Ammi sai girgiza kanta take yi tana jin zuciyar ta babu da'di...idanun ta lumshe tace" Zainab Mu'een na shan wahala sosai, ban san inda ya samo ciwon zuciyar nan ba gashi tana neman halaka min shi, wallahi ji nake da ina da damar da zan bashi farin cikin da yake so da na bashi Zainab bana so in rasa shi...'kalubale da yawa ya fuskan ta a rayuwar sa kuma ya jura wannan kam ina jin ba zai iya jurewa ba...".
Ban da shashshe'ka babu abinda ke tashi cikin parloun idan ka gammu sai kayi zaton ko labarin mutuwa ce ta riske mu a lokacin.

Ni da Anty Zainab ko magana ma bama iyawa Ammi ce ka'dai ta cigaba da fa'din"...yaro ne shi mai matu'kar 'kauna da tausayin iyayen sa, 6angare 'daya kawai ya samu mummunar shaida..."
Bu'de idanun tayi tace" Zo Noor zo kusa da ni..." Da sauri na matso jikin ta na kwantar da kaina a jikin ta na cigaba da kuka na..tana shafa kaina tace" Zainab ku yafe masa dan Allah duk abinda yayi muku ku yafe masa...Noor please ki yafewa yayan ki kinji..kar ki ri'ke shi a zuciyar ki kinga ma rayuwar sa gaba 'daya tana neman 'karewa...kar ya mutu da fushin ku akan sa..."
'Dago kai Noor tayi tana toshe bakin ta da hannun ta 'daya take duban Ammi, idanun ta cike taf da hawaye wasu na gangarowa yayin da idanun ke sake cikowa.

Girgiza kanta kanta take yi a hankali tace" Ni bana jin haushin sa Ammi...tuntuni na yafe masa..ban rayu da haushin sa cikin zuciya ta ba..kuma na riga na yanke shawaran sake auren sa kice masa kar ya tafi ya barni Ammi dan Allah kice masa ya yafe min...".

Kuka sosai ne ya ci 'karfin ta yayin da taji 'dumin hannayen Ammi ya sau'ka abayan ta.
Runguma Ammi tayi mata mai nuna tsantsar farin ciki da jinda'din ta a fili..." Allah yayi miki albarka Noor dama nasan ke 'yar halak ce..Ubangiji Allah ya faranta miki ya baki 'ya'yan da zasu ji 'kanki su faranta miki fiye da wanda kika yiwa manyan ki...".


Anty Zainab kanta murmushi take yi agefe tana kuma zubda hawaye na jin da'din furuci na.

Ammi na sake ni Anty Zainab ta kama hannu na muka bar 'dakin.
Itama rungume ni tayi cike da farin ciki tace" Baki ta6a sanya ni jin cewa Mu'een yayi dacen mace fiye da yau 'din ba

Please Login or Register in order to submit comment