Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tattara da Anty Zainab suka tafi bayan sunje har makarantar sukayi masa sallama bayan haka sannan sukaje suka yiwa su Alhaji Baba ma.

     Mu'een bai damu sosai ba da yake baya gida a lokocin dan haka ya cigaba da karatun sa batare da wata damuwa ba har 'karshen semester.

    Sai lokacin da ya dawo hutu ne kafin yaji babu da'di, kewar su ta dame shi sosai....gashi Uncle Ja'afar ma ya 'kira shi yace da shi ya wuce gida kawai kar yace zai zauna shi ka'dai a gida daya ke yasan kadan ga aiki sane yace a gidan zaiyi hutun.

Kwanan sa uku sannan haka badan ya so ba ya tattara ya wuce garin iyayen na sa.

  Sai dai Yah Deen 'kin zama yayi agidan wai mu bama ji zamu dame shi da hayaniya.

Wani gida da Alhaji Baba ya ta6a ginawa acan wajen hanyar  makarantar mu yace zai koma inda Alhaji Baba yaso nuna 'kin amincewar sa amma Ammi ta ro'ki ya 'kyale shi kawai tunda hakan yayi ra'ayi.

Ita kanta tasan ba dai-dai bane hakan amma dan kawai kar su 6ata ran sa ko kuma yaga kamar an 'ki yi masa abinda yake so ya sanya ta amince....amma Alhaji Baba kam sam hankalin sa  bai kwanta da hakan ba, ta ya shi da yake matashin saurayi zai koma zama shi ka'dai acan bacin ga gidan mahaifin sa, ai rayuwar makaranta daban take da na gida...abin ma sam bai masa tsari ba.

Amma yadda Yah Deen ya dage da kuma yadda Ammi ta goya masa baya yasa shi amincewa kawai ya 'kyale shi.

Hakan kuwa akayi da yake gidan babu kowa wa'dan da ke haya a gidan basu jima da tashi ba dan sun gina nasu, so bayan 'dan gyare-gyare da akayi wa gidan sai aka shishshirya komai...yayi sa'a ma ba'a jima da canza kayan gidan Alhaji baba ba so tsofin nan aka zo aka zuba su, Ammi ce ta aika aka gyara komai sai T.v data sa aka siya masa da curtain, gida yayi kyau tamkar na amarya...sai dai babu da'di saboda shiru babu ko neighbours illah kangon gidaje da'd'daya.

A hakan shi kam  ransa yafi jin da'di ya fi farin ciki.

Rayuwar Yah Deen kullum akarkace take shi, kusan ko wani lokaci yafi so yaji shi zaune shi ka'dai yayi tunanin da ransa ke so, shi ka'dai batare da an yanke mai ba, yayi rayuwar sa shi ka'dai, ba tare da yaji motsin kowa ba.

Mutane na gudun ka'daici amma shi hakan ne mura'din sa koda wani lokaci...a fa'dar sa wai damuwa ce kawai bai so...sannan wai mu mun cika hayaniya.(Ohh ni Salmerh...naga de banda abin Mu'een dama wake son damuwa a rayuwar nan kawai dai ha'kuri ake ana lalla6awa kawai).

Kuma fa 'karya ce kawai yake yi amma babu wata hayaniya da mukeyi gara ma idan musu ya ha'da mu da Zaidu mukan 'dan ta6a hayaniyar amma itan ma ba kullum ba, bayaga haka kuwa ba komai, sai ko idan muna kallon movie musamman American Movie mu kan 'dan yi hayaniya saboda kowa na za6an star 'din shi ne tun kafin film yayi nisa so aduk lokacin da star 'din wani cikin mu yayi abin da ba dai-dai ba mukan 'dan yi mai ihun mugunta sai kuma idan film yazo 'karshe duk wanda star ya fito daga 6angaren sa ya kanyi murna sosai...shine kawai hayaniyar da muke yi agidan, wannan kam nasan ko Ammi ma tana mana fa'dan ihun, to a daren ranar da ya zo mun kalli Fast 3 da Terminator 2....kuma munsha shagalin mu aranar shine fa ya fake da shi...har da 'kin zama a gida.(ALLAH YA RAKA TAKI GONA....inji Maman Muhammad fa amma).

      Washe garin tafiyar sa da muka zauna ni da Saif lokacin zai koya min karatu kuma sai ya kasance ranar a harabar gida muka zauna, tashin farko tunani na sai ya tafi can wurin sa ban san dalili ba amma har da ta6e baki na.
Ban iya nayi shiru ba kuma sai nace da Saif " Amma wannan Yah Deen 'din gaskiya yana da mugun hali".

Ido Saif ya zaro yana kallo na...sai na ha'de goshi na ganin yanda yake kallon nawa...A hankali yace
" Ni dai ba ruwa na idan yaji ki".
Saif ya fa'di yana mai bu'de text book 'din da ke hannun sa.
Cewa nayi
" A ina zai jini shida ya koma can jejin..."
Tun ma kan in rufe baki na Saif ya tare blni da fa'din" To wai ke ina ruwanki...haka ya ga dama, kuma ra'ayin sa ne ba tilasta shi akayi ba kuma ya koma 'din bashi kenan ba".
Baki na ta6e ina jin araina cewa da ni Aljana ce da sai na ringa bashi tsoro da dare tunda ya koma can shi ka'dai.
Daga haka muka ci gaba da karatun mu bamu sake bi ta kan zancen sa ba.

Yakan zo gidan kullum da safe da rana da kuma yamma, bamu fiye ha'duwa da shi da safe ba da yake sai bayan mun tafi makaranta yake zuwa yayi breakfast wurin Ammi, da rana ma sai kusan 'karfe uku yake zuwa a lokacin kuwa har mun tsufa a Islamiya ma, da yamma ka'dai ne muke haduwa da shi sai dai kuma ba kullum ne yake zuwa gidan da yamma ba sai ranar da yaga dama...saboda bai wani damu da cin abincin dare ba shi.

Sai ko a weekend mukan ha'du dan muna gida ko wani weekend da safe.

Ni kam haushi sosai yake bani yanzu, balle da naga ya 'karawa kansa mugun hali, ko kallan arzi'ki bai mana a gidan, idan kuwa mutun ya kuskure yayi mai wani abu ranar zai kwashi yatsun sa biyar a fuska.

Yah Deen sam baya shayin sau'kewa mutun mari akan kowani irin laifi ne, sa'ar da ni nayi kawai shine ban ta6a ha'duwa da marin sa ba tun zuwan sa, amma ranar da ya mari Saif a gaba na ji nayi tamkar in rama masa dan haushi.

Wai dan ya bashi wankin singletes da safunan sa kala kusan biyar, Saif kuma hannun sa na ciwo shine fa na kar6a yana zaune ina wankewa da ya fito zai tafi sai yaga ba Saif ke wankin ba batare da yayi magana ba kawai muka ganshi tsaye agaban mu..." Ban isa ni in saka abu kayi min ba ko ?"
Yace da Saif da damammiyar fuska.

Saif na shirin magana kawai sai ya 'dago hannu ya wanki fuskar Saif da mari....ba zata kawai naji 'karan mari, ina 'daga kaina sai naga Saif ya dafe kuncin sa da hannu...
" Dan ka raina ni Saifu in baka ka wanke min shine zaka bawa wannan yarinyar salon ta 6ata min kaya ko me?"

Ko da Saif ya bu'di baki zai mai bayani sai ya sake kai masa wani mari gami da fa'din " Shut up da Allah bana son maganar banza...kuma ka tabbatar ka wanke min kaya na da kyau...stupid kawai ".

Yana gama fa'din hakan yayi gaba abin sa cikin ta'kun sa na 'kasaitattu.

Yanda tsoron sa ya shige ni sai naji ko kallan banza ba zan iya yiwa bayan sa ba ballantana inyi magana, badan haka ba da sai na yi masa bayanin abinda ya sanya nake taya Saif wankin da har ya mare shi akan hakan.

Ha'kuri kawai kawai na dinga bawa Saif kamar zanyi kuka sai da naga ya fice daga gidan kafin a hankali nace " ai sai na gaya shi da Ammi....take Saif ya hana ni yace min a a kar in fa'dawa kowa.

Tun daga ranar nake jin haushin sa ga kuma tsoron sa da ya dasa min a zuci....ganin akan 'dan wannan abin shine Saif yasha mari har haka to ina ga kayi wani babban laifin ai sai ya tattaka ka abanza....wannan dalilin ne ma ya sa ko ya zo gidan ban fiya fito wa ba koda ina nan, zama na nake a 'daki har yazo ya tafi ban fitowa ko gaida shi dan gani nake kamar idan mun ha'du zan iya masa abinda zai mare ni batare da nasan na aikata laifi ba, tunda shi komai ma laifi ne a wurin sa...ga kuma wani uban 'daure fuska da ya koya ba zaka ta6a ganin fuskar sa asake ba sam sai dai ko in yana tare da su Ammi su 'din ma wataran ba fara'ar yake yi musu ba.

   Da yake kusan kullum muka ha'du da Ma'u sai ta tunadar dani cewa kar in manta idan ya dawo in sanar da ita...tun wancan tafiyar tasa take kan tunatar da ni, da yake yanzu mun saba sosai tunda nace da ita ai Ammi tace idan an 'kara fa'da min irin waccan maganar inzo in sanar da ita, Ma'u sosai ta kiyaye bakin ta bata ta6a 'kara gigin sanar da ni ba, dama itama ji tayi ana fadi, to ko mutanen ma sun tayin gulmar a tsakanin su sika yi shiru ganin babu hanyar ya'dawa, Ammi ba shiga cikin shirgin matan garib takeyi ba balle taji, sai dai bansan ko Ummah ta ba...'kilan taji amma dai bata ta6a ce da ni komai ba.

Rashin sake maimaita maganar da Ma'u batayi ba yasa nima na saki raina itama mukayi sabo da ita, daga 'kawata Bintu ban kula kowa sai Ma'u.

Ai kuwa kwana shida da dawowar sa muka ha'du da Ma'u, da ta tambaye ni kamar yadda ta saba bama ta6a ha'duwa bata kawo maganar sa ba...sai nace mata " ai ya dawo ma amma ya koma wancan gidan na hanyan makaranta..." na 'karashe da yi mata kwatancen gidan.

Tun daga lokacin Ma'u bata 'kara tambaya ta shi ba ban kuma san meke faruwa ta 6angaren ta ba.

Ni dai ban ta6a zuwa gidan ba dan ko ya 'kira su Zaidu bana binsu, sau tari kayan wankin sa yake ha'da su da shi idan sun wanke sun goge sai su 'kara kai masa can.

Har akaci sati biyu da dawowar sa.
   Akwai watarana da Zaidu ke 'dan jin zazza6i Saif ne shi ka'dai yayi wanki da gugan kayan Yah Deen 'din da ya bayar, dan mugunta kuma wai shi bai son asanya masa kayan a machine dole Saif yayi wankin da hannun sa ko shanya ban taya shi ba saboda tsoro.

Da zai kai masa kayan ne yace in raka shi na'ki, yayi-yayi dani na'ki amincewa, sai da Ammi tasa baki da fa'din " ki raka shi Hudah kinga ma yace yau bazai shigo ba wai atafi masa da Tea kuma ai kinga kayan sun yiwa Saif yawa ko...daure ki raka shi kinji uwata".

Kafa'da na no'ke nace da Ammi" Nifa Ammi tsoro nake ji kar ya mareni".
Na 'karashe maganar da shagwa6a ta.
Ammi sai tace
" Ai idan ya kuskura ya mareki rama miki zanyi kinji Hudah...yi ha'kuri ki raka shi ai ma ba zama zakuyi ba...yana ta6a ki let me know.. i ll deal with him insha Allahu".
Tayi maganar tana mi'ka min 'dan madaidaicin Teaflask da ke hannun ta.

Kar6a nayi ina share hawaye na nudi 'daki na 'dauko 'dan hijab 'dina fari na sanya har na 'kara fitowa hawaye na bai daina zuba ba.....ganin hakan ne ya sanya Ammi fa'din "...To Saif idan kunje sai ta jiraka a waje in ka mi'ka kayan sai kazo ka anshi flask 'din ma ka kai  tunda ita tsoron sa takeji...."
Ta 'karshe da gungunin " Ya maida kan sa dodon 'karfi da yaji kam ba dole yara suji tsoron sa ba".
Da " To". Saif ya amsa ta sannan muka wuce.

A hankali muke tafiyar cuz ni bana sauri yau 'din da yake raina ba son tafiyar yake ba.

Har kuwa muka isa layin gidan babu wanda yace da 'dan uwan sa uffan......akan layin gidan muka ha'du da Ma'u bansan me take yi a wurin ba,  tana ganin mu kuwa sai naga ta washe ha'kora ta iso gaban mu..." Hudah ina zakuje haka naga kina ta fushi?...da alama ma kiyi kuka".
Tayi maganar tana kallon cikin idanu na.
Kafin nayi magana Saif sai yayi murmushi yana gyara zaman kayan dake hannun sa yace" Rabu da ita matsoraciya, gidan nan zamu fa shine take kuka".
Da murmushi Ma'u tace" Kuka kuma saboda me?"
" Wai tana tsoro"
Washe baki ta sake yi tace " haba da Allah tsoro kuma...muje in rakaku to nima kawai dama gida zan koma yanzu".
Tayi maganar tana kar6an abinda ke hannu na, ni kuwa da wuri na sake mata kamar dama jira nake yi ta kar6a.

   Tunani na ko dan bata san waye a gidan bane shiyasa take wani azar6a6i....ashe Ma'u kam ta sani, mantawa ma nayi da cewa ni na gaya mata a gidan yake,  dama kullum hanyar da zata 'kara ganin sa take nema shiyasa take yawan shawagi a arean gidan tamkar wata mai gadi, duk da haka kuwa sau d'aya tak ta gansa ranar ma zashi filin ball ne dayake ya fara fita ball.

    Tun daga ranar bata 'kara ganin sa ba kusan kwana biyar kenan yanzu, sai yau da in ka lura zaka ga har jikin ta rawa yake yi saboda zata shiga wurin sa.

Ni har Saif duk bamu lura da yanayin ta ba, illah surutun ta da ta cika mu da shi sai ya 'dauke hankalin mu gaba d'aya.

Muna isa 'kofar gidan sai na ja tsaya na basu hanya, duk suka wuce ni, sai na 'kara jan baya ka'dan, Saif ne ya fara shiga da sallamar sa, sai Ma'u a bayan sa, ni kam 'kin shiga nayi nayi tsayuwa ta daga waje...Saif ma bai kulani ba da yake an riga an gama magana tun a gida, Ma'u kuwa hankalin ta ma bai kaina burin ta kawai ta shiga cikin gidan ta ganshi shiyasa bata ko bi ta kaina ba.

Da shigar su sai suka tarar shiru tamkar baya gidan, parlourn ma shiru.

Tsayuwa suka yi suna jiran sa duk da ko sallamar ta su bai amsa ba amma Saif bai damu ba cuz ya san wannan 'daya daga cikin halayyar sa ne, rashin amsa sallama musamman idan ba babba ne yayi ba, ko yanzun ma kuwa yana da ya'kinin yaji su sarai amsawar ce dai kawai ba zai yi ba.

...Ai kuwa hakan akayi, dan batare da ya amsa sallamar ba kawai ya fito daga bedroom 'din jikin sa ko riga babu illah wandon 3quarter a fili zaka ga dukkan baiwar halittar da Allah ya tsara masa na daga cikin sa har zuwa kansa gaba 'daya, Deen ba 'karamin kyakkyawa bane na 'karshe, sosai yayi sa'an fitowa cikin mutanen da ako ina za'a kirashi da kyakkyawa batare da haufi ba, yanda kansa ke cike da yalwattaccen gashi haka ma 'kirjin sa yake..... a hakan kuma ya 'karasa fitowa fuskar sa ba yabo ba fallasa ya 'karaso ya zauna kan kujera.

Ma'u kam tunda idanun ta yayi tozali dashi ai sai ta manta kanta gaba 'daya, ido ta tsura masa tana kallon fuskar sa ji take tamkar tayi ihu saboda farin ciki, haka kawai Allah ya jarabce ta da sonshi, so kuma mai tsanani irib masifaffen nan wanda bai san fulaku ba, tun Nanne na raye suke fama gashi yanzu Nanne ta tafi ta barta kamar wasa abin ya girma cikin zuciyar ta, kullum kwana take tana tashi da lodin soyayyar wanda bai ma san da zamanta cikin garin ba balle ya san matsayin sa a zuciyar ta.

" Yayah na yini?"
Saif yace da shi yana mai ko'karin ajiye kayan hannun sa.

"A'a shigar ciki mana".
Yayi maganar batare da ya amsa gaisuwar Saif ba illah gyarawa da yayi ya kishingi'da kan kujerar.

Saif sai ya kama hanyar shiga ciki kamar yanda aka umarce shi wanda sai lokacin Ma'u da rawar murya tace da shi " Ina..yi...ni?"

Bai amsa ba sai a lokacin kuma ya 'dago tare da kankance idanu yana kallan ta jin sabuwar murya kamar daga sama a tsakar kansa.

Suna ha'da idanu sai ya ha'de gira yayin da Ma'u ta fara rarraba idanu a 'kasa cike da bugun zuciya handle 'din flask 'din dake hannun ta ta kama da duka hannuwan ta biyu.

" Daga ina ke kuma?"
Yace da ita cike da mamaki yana kallon ta.
" Ni....?"
Tace a tsorace still muryan ta na rawa.

Bai amsa ba sai yace " Me kike yi anan nace?"
Yayi maganar a'dan tsawace har Saif dake ciki ma sai da ya jiyo shi.

"..Na..na rako su ne ".
Ta fa'di kamar zata zura da gudu.
Dai-dai fitowar Saif daga cikin bedroom 'din Yah Deen sai ya maida hankalin sa wurin sa...
" Saif nace ka ringa kwaso min mutane anan gidan ne? ko kuma tsabar rainin hankali ne?"

"A'a fa Yayah..Ammi ce ta aiko mu da Hudah ita kuma wai tana tsoro shine Ma'un ta kar6a tace zata rako mu".
Ba sai ya sake tambaya ba cuz ba yau yasan sunan ta hakan ba...a zafafe yace da Saif " Tsoron uban me take ji?"

Shiru sukayi dukkan su...a 'darare Ma'u ta ajiye flask 'din hannun ta ta kama hanyar fita, sai ya dakatar da ita da fa'din " My friend...come back here!"
Tana jin haka jikin ta na rawa ta dawo ta tsaya.
Abin shara ya nuna mata tare da mi'kewa sannan yace" Ki share parlourn ki goge shi and don't waste my time...zan fita ne yanzun".
Yana maganar ne yana tafiya zuwa cikin bedroom 'din nasa.

Ma'u da idanu ta rakashi har ya 'karasa shigewa ciki.
Sam bata zaci haka yake da masifa ba, idan ta ganshi awaje shiru-shirun nan sai ta zaci ko sau'kin hali gare shi har zuciya, baza manta ba da jimawa Huda na 'dan bata labarin sa amma sam bata sawa aka, musamman in 6angaren mugunta ce, gani take tamkar duk rashin jin su Hudah ne ya sanya yake yi musu hakan, bata san cewa haka asalin halin sa yake ba sai yau da ta fara gani...duk da haka Ma'u ko ka'dan bata ji haushi ba sai ma gani da tayi kamar ai dama ta samu tunda har ya sakata aiki a gidan sa kuma da kansa... farin cikin ta sai ya rinjayi raunin ta har hakan ya sanya zuciyar ta cika fal da farin ciki..a hakan tafara aikin tana 'dan murmushi.
( Ni kuwa nace, Babbar Cuta ta kama Ma'u gaskiya).

Shi kam Yah Deen bayi ya shige abinsa ransa ba'ki'kirin, duk zaton sa nice, shiyasa ko lokacin da ya fito bai damu da ya ga inda take tsaye ba saboda yasan dole zan gaida shi ko bai dubi inda nake ba.

Murya ta kawai yake son ji tana masa da'di...bambancin murya ta da ta Nanne kawai shirme ne da nake yi ada amma yanzu ma da sau'ki tunda 'kara girma nake yi ina 'kara wayo ina barin shirmen abaya, yayin da sautin murya ta ke 'kara riki'dewa zuwa na ta sak, Yah Deen ya gama saka rai da yaga Saif tare da wata shiyasa ma bai ko tsaya ya lura da yanayin bambancin halittar mu ba.

Sai a lokacin ma yaga wautar sa da tun farkon shigan sa 'dakin ya kasa gane bani bace tun awajen suturar mu, cuz yasan ji Ammi bata ta6a bari na in saka kayan da suka canza launi ko suka 'dan yage ko kuma kayan da ba'a goge ba, hakan yasa kullum zaka ganni fes dani bana ta6a zama da datti..tun daga 'kafafu idan ka duba zakaga bambanci dan ni 'kafata kullum fes take da haske yayin da 'kafar Ma'u tayi futu-futu da ita da yake ta zama wuri guda ita.
     Tsayin mu zai kusan zuwa 'daya da Ma'u duk da kuwa tafini shekaru amma mu 'yan gidan mu muna da tsayi cikin halittar mu shiyasa muka zo kusan 'daya da Ma'u, amma tafini kaurin jiki dan ni haka nake tamkar muciya banda jiki sam sa6anin Ma'u da har ta fara ajiye halittar Allah a 'kirjin ta, ban sani ba ko dan kanta da hijab ne ya sanya bai gane bambamcin halittar mu ba...kuma ma daya ke ni ya saba gani a gidan su, kuma yasan ni jinin Nannen sa ce....sannan kuma ba zai ce ya tsane ni ba saboda wannan ala'kar, amma sau tari idan ya ganni na kan tuna masa da ita har hakan yake sawa yake 'dan yawaita kallo na koda asace ne.

     Babban abinda yafi tsaya masa arai game dani kuma shine yanda muryar mu tazo iri 'daya da Nannen sa.

Shiyasa ma wani sa'in bai amsa gaisuwa ta saboda bugun da zuciyar sa keyi na sakamakon jin murya ta da yayi, amma ni sam bansan haka ba zato na ko kuma zallar tsana ce kawai da yake min da mugun halin sa.

   Ranar da 'yan Jahilcin suka zo kuma yakanyi abinsa da gangan ne, idan yayi tunanin dama ni mutuwa ta d'auka ta bar masa sahibar sa, hakan sai yasa shi jin haushi na har ma ya'ki amsa gaisuwa ta...ha'ki'ka soyayyar Nanne ta zame masa ne tamkar ciwo a zuciyar sa wanda batada magani, ta kan motsa a duk lokacin da ta ga dama....da kanshi ya san cewa erh lallai Amina ta rasu ba kuma zata dawo ba har abada, da kansa ma yake yi mata adduah kusan kowace sallar sa, amma wannan dun'kulalliyar soyayyar tata ta kasa bajewa cikin zuciyar sa a lokacin, shi kansa bai san me ke 'kara ha66aka masa ita ba balle wani daban.

Saif fita yayi can waje domin ya dubo ni dan kar naji shiru inda ya same ni tsugunne daga waje na buga uban tagumi tamkar wata almajira da ta rasa madafa, ina jin an bu'de 'kofa na zabura na mike a razane.

Saif sai yayi murmushi.." Miye kuma?"
Ya tambaya yana kallo na da murmushi.

Narai-narai da idanu na nace " Ai tsoro ka bani".

" Yi ha'kuri to".
Ya fa'di tare da matsowa kusa da ni sannan ya sake fa'din" Allah ya taimake ki yarinya".
Yayi maganar yana kallo idanu na.
   Ban amsa shi ba sai kawai nace da shi" ina Ma'u?"
" An saka ta shara".
Ya bani amsa yana 'dan dariya.

" Maganin ta ai".
Nima na fa'da harda mugunta ta.
Au haka ma zakice ke da ta tazo taimakon ki...ai badan ita ba da ke za'a saka sharar".
Sai nace" Ba wani nan ai dama Ammi tace kar in shiga ciki".
"  Naji to, muje ki taya ta"
Cewar Saif yana bani hanya.
Kafa'da na no'ke tare da 'kara matsawa baya.
Dariya ma bashi, sai da yayi dariyar kafin yace " Allaj kin fiya tsoro, nima fa an min masifar nan amma kin gani a jikina ne...mazgewa akeyi in ba haka ba bazaki daina tsoron nan ba".

" Ni dai ba ruwa na, ka 'kirata mu tafi ko kuma muyi tafiyar mu idan ta gama sai ta wuce itama".

" Rufa min asiri ni kam in ba so kike ya 6a66alani ba...bari in dubo ta".
Yana gama fa'din hakan ya juya ya shige ciki.

Lokacin da ya shiga sai ya samu ma har ta gama sharan tana kwashewa.

Sannu yayi mata sannan ya wuce ya ha'do abubuwan da za'ayi mopping 'din dasu.
      Ga mamakin  Saif fuskar Ma'u cike take da murmushi, sa6anin yanda ya zaci zata ji haushin ta rako su kuma an saka ta aiki.

Bai damu ba ya wuce ya fara goge 'dakin, sai tayi saurin tasowa ganin abinda yake shirin yi tace.." Me zakayi?"
" Wai da zan tayaki ne"
" Banso..nace ka taya ni ne?" tayi maganar tana kar6a daga hannun sa.
Saif baki ya ta6e yaja gefe ya tsaya yana binta da kallon mamaki.






Comment
Vote
Share





*Salmerh ce*😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)


By
*Salmerh MD*

 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Dedicated to Hassan ATk & 80k...Allah ya bar Zumunci ya biya bu'katu...( Amin thumma Amin)* 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*


🅿 *35*

Haka tayi abinta ita ka'dai har ta kammala goge tiles 'din tas,.

" Sannu".
Saif yayi mata sannan ya shiga ciki dan sanar da shi zasu wuce sai kuma ya tarar yana bayi ne a lokacin.

Saif kam hakan ma yafi masa, dan bai son wata sabuwar mitar kuma da yake baya rasa na yi shi. { a fa'dar Saif kenan}… 
  Dalilin ma kenan da ya sanya batare da 6ata wani lokaci ba ya fito yace da Ma'u wai yace ya gode za su iya tafiya.

Ma'u kam ba haka taso ba dan taso ta 'kara ganin fuskar sa ma ko da kuwa ace wata masifar zai kuma yi mata… amma ganin bata samu hakan ba sai kawai ta basar suka fito daga gidan inda suka suka same ni tsaye tsuru-tsuru duk na gaji da jiran su, sosai na 'kosa su fito muyi gaba.

     Ai kuwa ina ganin sun fito sai na saki hamdala a zuciya

Please Login or Register in order to submit comment