Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

babu wani sau'ki ko ka'dan, dan ya fahimci babu ta inda abin yake da sassauci sam, nan da kwanaki goma Alhaji yqce yake nemen sa,  kenan akan auren ne...." Yah Allah ka taimake ni ka tarwatsa wannan auren".
Ya furta a fili yana maida idanu ya lumshe.

Kusan cikin kowacce sallar sa sai yayi wannan addu'ar, wanda ko yanzun ma hakan ya sake maimaitawa yana mi'kewa daga inda yake zaune.

Bayi ya shiga domin ya watso ruwa, yau yana jin shiga school ne haka kawai, bayan jin muryar Ammin sa sai yaji wata 'yar natsuwa ta shige shi duk da ma ba albishir 'din anfasa auren tayi masa ba, amma haka kawai sai yaji damuwar sa ta ragu sosai.

Yanzu da ya san cewa babu mai iya sawa afasa auren ne sai ya barwa Allah kawai sai dai yana wankan ma har murmushin mugunta yake yi dan irin shegen shirin muguntar da zai shiryawa duk yarinyar da ta kuskura ta yadda aka 'daura auren sa da ita.


Da fitowar sa sai ya koma wurin wayar tasa yana murmushin ya sa hannu ya 'dago wayar sai da ya shiga wajen text yaga abinda ta rubuta masa ro'ko ne kawai akan ya daure ya 'dauki 'kiran ta...a fili ya saki 'dan 'karamin tsaki afili ya furta" Kanki ake ji ai"  Fita yayi daga wurin text 'din ya koma ya dannawa layin Husnah 'kira yana furzar da huci daga bakin sa.


Tana cikin kuka sai taji 'karan wayar ta, bata yi tunanin shi bane cuz ta san da wuya yayi 'kiran ta dan haka share wayar tayi ta cigaba da kuka abin ta, sai taji kuma ta kasa daurewa, daf da wayar zai yanke tayi saurin kai hannun ta ta 'dago, da wuri ta gyara zama da rawar jiki taja recieve dan ganin sunan da ke yawo kan fuskar wayar tata.


Tana kukan ta 'kara wayar a kunnan ta batare da tayi magana ba, jikin ta har rawa yake yi haka ma bakin ta.

Hannu ta kai ta rufe bakin da shi yayin da 'dayan hannun ke ri'ke da wayar manne da kunnen ta sai ta kasa magana illah kuwa da ta cigaba da yi mai ha'de da sheshshe'ka, da ka ganta zaka san zuciyar ta ta wahala, tausayin ta ne sosai zai kama ka.

Mu'een na jin ta tana kukan amma ya share tamkar bai ji ta ba, sai ma ta6e baki da yayi ya'ki furta komai.


Ya bata a 'kalla kimanin mintina biyu da rabi yana tsaye yana jin ta tana ta sheshshe'kan kuka, bai ce da ita komai ba tsawon wasu mintina suna a hakan.

Yah Deen dai-dai da 'kwayar zarra daga cikin 'digon tausayin Husnah bai ji a zuciyar sa ba, yayin da Husnah kuwa ke  son tayi magana amma kukan sai sake taso mata yake yi, abubuwa ne duk suka yiwa rayuwar ta yawa suka mata rumfa...sunan sa  kawai take iya 'kira sai kuma ta cigaba da kukan ta idan tace.."..Mu...'een" kamar zata sake magana amma sai kuka ya 'kwace mata...tausayin rayuwar ta take yi ganin cewa daga mahaifiyar ta babu wanda ya damu da farin cikin ta, ko shi Mu'een 'din ma zuwa yanzun ta lura da kwai abu a 'kasan ransa.


Gajiya yayi da kukan nata at same time kuma ya gaji da ri'ke waya a saman kunnan sa, yayi tunanin sanya wayar a speaker ya ajiye amma kuma sai yaga kamar in yayi hakan ma tamkar ya bata wani dama ne na musamman da zata ji a zuciyar ta cewar he cares, hakan ya sanya a nutse cikin sanyin hali yace da ita" Quite please Husnah kunne na".


Fa'dar hakan da yayi ne ya sa kukan nata ya 'dan tsagaita a hankali bayan wasu sekanni, ji yake kamar ya yanke 'kiran ma kwata-kwata ganin kamar bazata natsu da kyau ta saurare shi ba, sai dai baya jin daga yau 'din akwai wata ala'ka ta daban da zata sake ha'da su, abu mai muhimmanci yake son sanar da ita da zai taimaki rayuwar ta da farin cikin ta, wanda idan ta yadda tayi na'am da shi to tamkar ta ceci zuciyar ta ne, ta wani 6angaren kuwa harda shi, fatan sa daga yanzu ala'kar su yanke koma ba haka b shi baya jin akwai wani abin da zai sa ya sake sauraran ta har ayi auren shiyasa kawai ya saka dauriya cikin ransa har ta rage sautin kukan da take yi.

Jin ta fara sau'ke numafashi ne ya sashi fa'din" Ki nutsu da kyau ki saurare ni... kina jina?"

Da " Umm" ta amsa shi tana goge hawayen dake fitowa ta 'kasan idanun  ta.
Sai ya sake fa'din" Magana nake so muyi dake na 'karshe kina ji?"

Yanzun kam bata amsa shi ba illah bada hankali da tayi sosai tana sauraron sa...yayin da ya cigaba da fa'din" Wani labari kika tarar a gida bayan komawar ki? ki gaya min inji..".
Yayi mata tambaya irin wacce ya ta6a yi mata abaya.

Da muryar kuka ta bashi amsa da fa'din" Ance wai an bada aure na ga wani a garin ku mai suna Muhammad..."

Idanu ya lumshe yana shafo suman kansa da 'dayan hannun sa yace da ita" Ya kika ji batun to?"

Tace" Hankali na ya kasa kwanciya".
Murmushin mugunta yayi yana fa'din" Really? Ni fa aka bawa auren ki Husnah?"

Shiru Husnah tayi tana jin yanda zuciyar ta dokawa, wani sashi na damuwar ta taji ya na silalewa nan take, sosai taji da'din jin cewa shine aka bawa auran ta, kenn shi zata aura su 'karasa rayuwar su da shi.


Take ta saki murmushi mara sauti na farin ciki da jin da'di wanda in ba kana gabanta ba baza ka ta6a sanin tayi shi ba.

Shima Yah Deen shiru yayi tun bayan abinda ya fa'di, a 'ko'karin sa na son jin amsar da zai fito bakin ta shiyasa ya bata lokaci.


Ganin kamar shirun yayi yawa ne ya sashi sake fa'din..." Tell me to kina son auren da ni ko baki so na?"

Yanda yayi maganar bazaka ta6a zaton he is up to something ba, muryar sa wasai yayi maganar bazaka ta6a fahimtar yanayin sa ba.


Husnah kam cikin jin da'di ta tana share hawayen farin cikin dake zubo mata ta bashi amsa da fa'din" Mu'een kaima ai kasan ina matu'kar son ka...me yasa zan'ki amincewa da auren ka? wallahi indai da kai ne inaso kuma na amince har zuciya ta....".
A 'dan fusace ya tare ta da fa'din
" To ni ban so!..Husnah ni ban amince da auren ki ba...kuma ki sani har abada tsakani na da ke Husnab
h babu wannan batun, rayuwar aure na ba rayuwa ce da zan yi shi batare da tsari ba, bada irin ki nake so in shimfi'da ta ba ma, ke kanki kinsan bamu dace da juna ba, bai kamata mu kasance ma'aurata ba Husnah ko kin ta6a ganin inda mutum mai hankali ya kwashi datti dake bola ya akai cikin gidan sa ya adana? Infact ma kin ta6a jin ni na furta cewa zan aure ki ne..ko da wasa?"
Ya 'karashe maganar yana huci da zararren idanu...da ace Husnah na kusa da shine na tabbata tsoron ganin yanayin da shiga a lokacin ma ka'dai ya isa yasa ta furta cewa ta fasa auran sa.


A 'dan gigice tana  'kan'kance idanun mamaki ta furta" Mu'een..."! Tana karkace wuya.

Saurin dakatar da ita yayi da fa'din" Just listen...ba amsar ki nake son ji ba." yayi maganar tare da 'dago yatsan shi 'daya kamar tana gaban sa sannan ya cigaba da fa'din" ...
Zan miki garga'di ne sau 'daya tak and that's na farko kuma na 'karshe..I won't ever repeat my self again..fatan kin fahimce ni?"

Bai damu da rashin amsar ta ba kawai ya cigaba da fa'din" Husnah idan kina son kanki da arzi'ki, farin ciki da walwala to is better ki rufawa kanki asiri ki nemi hanyar raba auren nan, dan ubanki zaki ci a hannu na matu'kar kika kuskura kika yadda igiyoyin aure na na farko masu matu'kar daraja suka fara dake, wallahi sai kin gane waye asalin Muhammad Tahir...abinda kawai zan iya gaya miki ayanzu kenan sauran kuma ki bari in kika yi kuskuran zuwa hannu na zaki fahimta da kanki..."

Daga haka ya cire wayar daga kunnan sa yana shirin yanke 'kiran sai kuma ya tuna da wani abu, saurin maida wayar yayi kunnan sa Husnah kam dama mutuwar zaune tayi bata ko motsa da hannun ta ba balle ta raba wayar da kunnan ta...wuri 'daya ta zubawa idanu ko hawayen ma yanzun bai fito ba banda aikin bugu da zuciyar take yi, gani take tamkar a mafarki ne Mu'een ke shirin nuna mata zallar tsana ta zahiri wacce babu ko kara aciki, fatan ta inma mafarkin rake yi to kar Allah yasa ya kasance gaskiya.

Tana cikin hakan taji yana sake fa'din"...uhumm kina jina ko? Wallahi kuma kika sake yin kuskuran da  'kiran ki ya ratso min cikin waya ko ki sani ni da ke ne, matu'kar ba cewa zakiyi na fasa auren ba kar ki sake ki 'kira layi na...don't tell me kin fasa but an fasa gaba 'daya as in harda 6angaren mahaifi na da hakan ne ka'dai na baki damar 'kiran wayata in ba haka ba...dont ever call my line ever again fatan kin fahimce ni?"

Bata iya ta bashi amsa
ba ko yanzun ma sai wani kuka da ya 'kwace mata mai matu'kar cin zuciya, haka ta ringa kuka babu mai lallashin ta, ita ka'dai ta san yanda take ji, ji take rayuwar na neman juya mata baya gaba 'daya.

Mu'een da ta sani ne wannan 'din ko kuwa wanin sa, Mu'een ne zai iya duban tsabar idanun ta ya fa'da mata wa'dannan maganganun  bacin ma ta san ba wani girman ta sosai yayi ba, in ba ma soyayya ba da ina ta ina shi? Da me ze ha'da shi da ita da har zai mata la'kabi da dattin bola...wannan abu da me yayi kama..wallahi Nu'een ka cuce ni ka gama da rayuwa ta"

Ta fa'di cike da takaici tana dukan katifa da duk hannuwan ta biyu...yau ne rana na farko a rayuwar ta da ta ta6a yin Allah wadarai da soyayya gaba 'daya, musamman ma irin soyayyar da ta masa irin wacce ke cutar da 6angare 'daya 'dinnan, Mu'een da ke haukace wa ya zauce a jikin ta wurin morar halittar da Allah yayi mata shine yau yake mata garga'di akan aure tsakanin su, bata ta6a zaton jin haka daga gare shi ba ko da wasa.

Ta tsinewa ranar da ta mallaka masa budurcin ta yafi sau hamsin, ko san tunawa bata yi, yanzu ne take da
na sanin sanin sa a rayuwa..kuma ra tabbatar da cewa kalaman da tayi matan babu wasa cikin su sam, atanda ta sanshi ra san cewa daga cikin zuciyar sa maganar ke fitowa kuma iya gaskiyar sa kenan, da gaske dama haka maza suke?...ba su da amana bayan sun gama da rayuwar ka da yan cinka...'karshe gudun ka suke cike da alfaharin sun fi 'karfin zaman aure tare da ke?
Yah ilahi...
Inannalillahi wa inna ilaiahi raji'un" Haka kawai ta ringa nanatawa tana kuka.


Ta 'dauki tsawon lokaci tana a haka kafin ta samu ta bawa kanta ha'kuri ta tashi ta je ta watsa ruwa, ko cikin bathroom 'din ma ta da'de kafin ta fito tunanin ta yadda zata tunkari mahaifiyar ta da wannan maganar take yi, me zata ce da ita da bazai tashi hankalin ta ba, tana son mahaifiyar tana kuma son farin cikin ta ta yadda take jin koda zata 'kuntatawa zuciyar ta ne tana son ganin mummyn ta na walwala, domin ita ka'daice ta fi kowa damuwa da damuwar ta in akwai na biyun ta to Yayan ta Hisham ne.


Haka ta fito ta sake shiri jikin ta sanyi 'kalau, kallo 'daya zaka yi mata ka tabbatar ba dai-dai take ba, gaban mirror taje ta tsaya tana 'karewa fuskar ta kallo sam bata so mahaifiyar ta ta fahimci halin da take ciki, dole zata 6oye mata komai dan kar ta shiga damuwa tunda tasan yadda Alhaji Mamman ke treating Mummyn ta ba lallai ne ya saurare ta kan batun ba, ta kuma san da mahaifiyar ta taji asalin meke tafiya dole ne tace zata same shi tayi mai bayani, ko da kuwa cewa akayi bata son auren sa6anin yanda ya yadda akan cewa sun daidata kansu tun farko 'din ma idan yayi niyya sai anyi to ina amfanin ta bar mahaifiyar ta da tunanin an aura mata wanda zai muzguna mata ya kusantata da lahirar ta.

Abin ma zai fi cimata rai a duk lokacin da ta tuna cewa Mu'een na azabtar da ita ne saboda already ya san ta matsayin 'ya mace shiyasa ya tsane ta yake azabtar da ita tasan ba komai bane ya kawo hakan face sakamakon yaudarar mahaifiyar ta da tayi take mata fuska biyu bacin a gefe tana holewar ta agaban ta kuma ta zama saliha, shiyasa ma tayi na'am ta kar6i hukuncin ita ka'dai bazata yadda zuciyar mahaifiyar ta ya 6aci sanadin hakan ba tunda babu s
hannun ta aciki...( _Mata fa naku...karfa kiyi zaton ko kinje kin yi kalar rayuwar da kika ga dama Allah ba zai kamaki ba...ba wai maza ne ka'dai Allah ke hukuntawa bisa aikata Zina ba a a harma da matan wallahi...gara ma mu nutsu dan babu yadda za'a yi iyayen ki su baki tarbiya su 6ata lokacin su wurin jan ki ajiki su saki farin ciki su wadata ki da komai na rayuwa 'karshe suje suna alfahari dake cewa sun haifi natsatstsa, amma 'karshe ki watsa musu 'kasa a idanu sanadin soyayyar wani banzan mayaudari sai ki zama mai fuska biyu bayan kin biyewa saurayin kun gama aikata son ranku... gaban iyayen ki kuma kina acting as babu yake fannin hankali da natsuwa dan munfurci, kuma a hakan sai kiyi zaton Allah ba zai kamaki ba? wallahi matu'kar baki tuba ba dole ne Allah ya hukunta ki....kar kiji ance in kayi da 'yar wani za'ayi da taka, haka in kayi da matar wani ma za'a yi da taka ki zaci hukuncin kan maza kawai ya sau'ka...to ki sani kema da kika biye masa akwai naki hukuncin gagarumi kuwa yana jiran ki, wasu mazan ma zasu yi ta aikata Zinan son ran su, su kuma yi dacen samun nitsatstsiyar mace su aura, 'karshe ma kika ga 'ya'yan su sun rayu cikin kariyar ubangiji...sai kiga sun yi tunanin ai sunci bulus....duk babu yadda Allah baiyi da bayin sa, kuma yana 'kaddara abu ne a duk kan wanda ya ga dama, yana jarbtar bayin sa ne da kala-kalar 'kaddara, idan ya so ka da Rahama nema zai hukunta ka tun anan duniya ba sai anje can ba....Sannan akwai Zina ta tilastawa misali kamar rape da sauransu, shine wanda hukuncin sa ke sau'ka kan namiji ma'ana shi wanda yayi niyyar yi 'din har ya tilastaki, amma in kin san ke da kanki kam kika je da niyyar ki da kuma yardar ki to fa ke ma kinsan naki hukuncin na jiran ki wurin mahalicci...'YAN UWA NA MU DAURE MU TUBA MU DAINA, ZINA FA DATTIN ZUCIYA TAKE SAWA ZATA NESANTAKA DA RAHAMAR ALLAH TA KUMA KUSANTA KA DA SHAI'DAN DA AIYUKAN SA 'KARSHE YA BARKA DA AZABAR WUTAR ALLAH MAJI RO'KO .... Yah Allah ubangiji muna ro'kon ka kayi mana tsari da kusantar Zina_ ).


Ba'kin kwalli ta nema ta ranba'da a idanun ta take ta 'dan sauya kamanni,  harda powder ta shafa ta saka lipstick a bakin ta sannan ta kama hanyar fita tana addu'ar Allah ya rufa mata asiri, fita tayi taje gefen mummyn ta dake zaune a palour tana kan lissafe-lissafe ta isa ta zauna daga gefen ta cikin sanyin murya tace " Mummy barka da hutawa".

" Yauwa Husnah...an fito ne?"

" Erh mummy...".

Kafin Mummyn ta sake magana sai ta riga ta da fa'din " 'Dazun nan munyi magana da shi ina zaune kawai naga ya 'kira ni".
Tayi maganar bayan ta 'ka'kalo murmushin 'karya.

Ba bu'katar sake tambaya cuz already abin ke ran kowannane daga cikin su, tsawon kusan sati biyu suka 'dauka suna jiran ji daga gare shi, hakan yasa mummyn Husnah cikin farin ciki ta furta " Alhamdulillah...ya kuma kuka yi da shi?"
Tayi maganar tana yi mata duba irin na jin da'di.
Husnah sai ta sunkuyar da kanta sannab tace
" Mummyn ce min yayj wai iyayen sa ne suka zo, kwana kin nan 'din ma an sace wayar sa ne shiyasa ya 'dauki lokaci bai 'kira ni ba...amma yanzun ya sai wata".
Cikin sanyi da dukkan dauriyar ta take magana, sosai tayi 'ko'kari wajen 6oye dukkan damuwar ta saboda son ganin farin cikin masoyiyar mahaifiyar ta.


Mummyn Husnah kam banda _Alhamdulillah_ babu abinda take ta nanatawa, dama damuwar ta shine kar a aura wa Husnah wanda bata san shi ba ko kuma ace bata son shi..yanzu kuwa da taji cewa wanda ta sanin ne ya sata 'dan ji sanyi cikin ranta.

Cikin kwantar da hankali ta yi mata nasiha akan kar ta 'daga hankalin ta dan ta ganta ta koma wata iri komai zai dai-dai ta da iznin Allah..ina ta 'karashe da fa'din" Ko akwai wara matsalar ne daban?"

Husnah na jin haka rayh saurjn girgiza kanta tare da fa'din" Babu komai Mummy kawai dai naga kamar lokacin yayi kusa ne sosai".

Murmushi Mummyn tare sannan tace" Shiyasa ai nace ki kwantar da hankalin ki, shi aure ai lokaci ne, idan Allah ya riga ya rubuta mutun bai isa ya canza shi ba, da shiri ko babu shiri idan lokaci ya tsaya to fa sai anyi, misalin sa tamkar mutuwa ne...karma wannan batun ya dame ki...ki saki ranki ki runguni 'kaddarar ki kinji Uwata".

Kai ta jinjina cike da gamsuwa still idanun ta na kan hannun ta bata iya ta ha'da idanu da Mummyn nata ba.


Kawar da wancen maganar Mummyn Husnah tayi inda tana gyara zamanta zuwa kishingi'da tace
"..Tambayar da nake so in miki tuntuni da nace sai kun yi waya da shi 'dinnan kin tuna ko?"

Husnah cewa tayi
" Erh mummy ban manta ba".

" Dama ina so idan ya kasance shi 'din ne in tamabaye ki shin Husnah daman can kuna soyayya da shine ne, ma'ana kina son shi yana son ki?"

Fuskar ta tayi saurin rufewa da hannuwan ta biyu kamar gaske sai kuma ta ta shi da hanzari ta bar wurin tama fice daga palourn gaba 'daya, ga duk wanda tayi hakan agaban sa zai yi zaton ko kunya ce ta sata tashi, sai dai sam ba haka bane kuka ne yaso 'kwace Husnah gudun kar tayi gaban mahaifiyar ta yasa tayi saurin ta shi ta bar wurin, dan tasan dole in Mummyn ta taga tana kuka sai ta tambayi dalili ita kuwa bata san amsar me ya kamata ta bata.

Yayin da Mummyn Husnah tayi tunanin ko tsabar kunyar ne ya sanya ta yin hakan, dan haka da murmushi kawai ta bi bayan ta tana jin farin ciki na ratsa ta ta ko'ina, yanzu kam tasan ba auren dole ake son yiwa Husnah ba dan haka bata da sauran damuwa.

Tun daga ranar ta fara sanar da 'yan uwa da abokan arziki tana fa'din date 'din bikin cikin farin ciki marar misaltuwa.

Haka ta fara shiri gadan-gadan wanda ya dace tayi ta 6angren ta na uwa, tayi 'ko'kari waje. gyare Husnah tsab cikin 'yan kwanakin duk kuwa da bata san ma cewa ita 'din already ta biyewa son zuciya ta lalata rayuwar ta ba, hatta da kayan fitan biki duk ta bada sa'kon su za'a kawo mata daga lagos bayan an 'din ke su.


Ko ha'duwa da Husnah ba sa yi sosai saboda yanda ta saka hidima agaban ta, bata san cewa Husnah na kashe kanta da damuwa akowace rana ba, kallo 'daya zakayi mata kasan cewa ta rame sosai.

Tsimin da Mummyn ta ke bata kuwa bata wasa da shan su, cuz tayi tunanin cewa babu mamaki idan yaji ta canza zai iya sakkowa su raya auren su kamar kowa cikin farin ciki, hakan yasa bata yi wasa da gyaran jikin ta ba...wani abin ma ta hannun friends 'din ta ake sayo mata su a 6oye batare da sanin Mummyn ba.



*****
    'Bangaren Ammi ma shirye-shirye ya kankama sosai...Anty Zainab tuni tazo suka wuce Kano da wata 'kawar Ammi suka yi siyayyar kayan lefe wanda Alhaji Baba da kansa ya bada ku'din masu nawin gaske, Anty Zainab kam sakin ranta tayi tayi siyayya tsakanin ta da Allah na ganj a yaba, duk kuwa da cewa bason auren take yi ba amma ance abinda ka sowa kanka ka sowa 'dan uwanka daga cikin ingantattun hadisan manzo, hakan yasa ta zage ta za6i latest kaya na gani a bada labari masu kyau da tsarin gani ga kuma daraja a jikin wanda ya sanya su.


Tun tana can ma ta 'kira Mu'een tana dariya tayi masa albishir 'din yawan ku'din da Alhaji ya bayar na siyan lefen auren sa, Yah Deen kam sai cewa yayi  " Ni ina ruwa na kuma Anty?".

Dariya tayi masa sosai  sannan tace" To kai me zan siya maka..?"

Tun ma kan ta rufe baki tace" Babu komai ". Inda ya bata amsa a takaice yana kashe wayar sa.

Anty Zainab kam Murmushi tayi ganin yau abinda yayi, rasan duk cikin fushin auren ne.." Ban da abinka ai Alkhairin sa zaka nema".
Ta fa'di hakan ne cikin zuciyar ta.

 
Wani shegen yadi ta za6a masa mai kyau da tsada, dan tasan wannan sarkin tempern da wuya idan zai natsu har ya 'dinka kayayyakin da ya dace a sanya su wurin biki.

Sai da ta gama za5a masa duk abubuwan da ta ga cewa sun dace da shi sannan ta dawo kaina a fili ta furta" Ba za'a bar yarinyar Ammi a baya ba".
Ta 'kaeashe da murmushi.

Siya min nima tayi tsadaddun lace kala biyu ta bada 'dinki tun acan aka 'din ka min dan ita Anty Zainab haka kawai take jina har cikin ranta, Ammi ma am mata nata kala uku masu masifar 'daukan hankali abin sai wanda ya gani, gaskiya Anty Zee tayi 'ko'kari sosai dan kayan da ta siyawa Yah Deen ma sun kusan kaiwa akwati guda.

Haka Anty Zainab suka dawo gida da kaya kaca-kaca, lokacin da ta nunawa Ammi kayan da ta 'din ko min sai duk farin cikin Ammi ya ninku akan nada, ko nata kayan bai sata farin ciki kamar yadda taga nawa ba, dama already ta bayar da kayan Yah Deen da ya ta6a siyawa Nanne tace a 'dinka min riga da skirt inda ta ha'da da wata super atampa tace duk a'dinkamin na fitan bikin Yah Deen, ta kuma siya min takalma na da mayafai, sai nake jina tamkar wata sarauniya tsabar da'di musamman da naga wanda Anty Zee ta kawo min suma da mayafan su da takalma sai nakasa 6oye farin ciki na...wanda Alhaji Baba ya siya mana kuwa ban san guda nawa ba amma dai daga ni sai Ammi ya siyawa...su Saif yace sai sun dawo.


Ma'u itace mutun ta biyu dana gaya wa cewa an 'dinko min kaya da yawa na bikin Yah Deen wanda tuni na kaiwa Ummah ta labarin...ina murna ta na fa'da mata lokacin an taso daga islamiya muna hanyar mu ta zuwa gida, gani nayi Ma'u ta tsura min idanu kawai tana kallo na, ban damu d kallon ba ni kam kawai na cigaba da bata labarin yawan kayan da kuma kyan su cikin jin da'di.


Muna kan hanya wani mai suna Ahmad dake matu'kar son Ma'u ya tari gaban mu yana yi mata magana, har a lokqcin kuwa bata ce da ni komai ba ni ke ta zuba abina, kawai tashin farko kamar dama jira take tga ya bayyana gaban ta sai gani nayi ta fara zazzaga masa masifa tamkar wani 'dan cikin ta, ni kuwa da ban iya yiwa wanda ya fini rashin kunya ba sai na zaro idanu na ina kallon ta, ina 'kiyasta shekarun tsakanin su kamar wacce aka gaya min, na dan yafi ta tsayi da girma amma bansan shekarun sa ba, Ma'u ce dai nasan sha shida ne shekarun ta cuz asali bata kai Nannen mu shekaru ba kawai dai Allah ya ha'da jinin su ne balle kuma da yake ita Nanne na da matsalar rashin lafiya shiyasa ma bata da saurin girma sai duk mu ka zama 'daya harda ni.

Ma'u na gama masifar tayi gaba abinta nima dake faman tunanin sai na bita abaya, har nayi gaba sai kuma na waigo na kalle shi" Yah Ahmad dan Allah kayi ha'kuri". nace da

Please Login or Register in order to submit comment