Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

'daya ri'ke da remote yayin da gaba 'daya ya bada hankalin sa kan T.V 'din yana kallo.

Ko sallamar da nayi ma da 'kyar in yaji ta ni dai ban damu ba saboda sanin halin sa da nayi.

A hankali na 'karaso nesa ka'dan da shi na zauna na takuru cikin hijabi na...da rawar murya nace " Ina kwana Yayah".

Cikin sa'a kuwawannan karon ya jini duk da yake ma ba da 'karfi sosai nayi maganar ba, amma hakan nai hana shi jin abinda na fa'di ba, na fahimci yajin ne ta dalilin waigowa da naga yayi ya kallo ni, sai dai bai amsa ba gani kawai nayi ya sau'ko da 'kafafun sa ya dire su a 'kasa still kuma suna sar'ke da juna, sai a lokacin ma na lura ashe rigar Jumpan sa na jiya ce a jikin sa har yanzun, sai dai bai saka dogon wandon kayan ba...'dauke idanuna nayi da sauri na mayar da shi 'kasa ina kallon tiles dake 'kasan 'dakin zuciya ta na dokawa, a hankali na sake maimaita gaisuwar da nayi...
Yayin da ya amsa ni da fa'din" Lafiya lau".
Inda ayi maganar ne batare da ya 'dago ya dube ni ba.

Muryar T.V naji ya rage sannan ya dube ni a lokacin yana wani cin magani yace" Ya ma sunan ki?"

" Hudah"
Na bashi amsa a ta'kaice kaina a 'kasa...a 6oye nake ta6e baki cikin raina nake ayyana wannan shi baya ri'ke sunan mutane ne?" Cuz ni dai nasan tuntuni yasan sunana.
Ko da yake ma ai ban ta6a ji ya 'kira ni da sunan ba 'kilan ya manta ne"
Ni ka'dai nayi magana ta kuma na warware ta, har a lokacin kuwa zuciya ta bai bar bugu ba.

" Wani irin suna ne kuma Hudah?"
Shima naji ya tambaya da alamun rainin hankali cikin maganar tasa, idan ka gansa a lokacin zaka yi zaton ko wani abin da bai so aka ambata masa ko kuma irin bai ta6a jin ko da kalar sunan ba.

Baki na na 6ari na amsa shi da fa'din cikakken sunana wato" *NOORUL HUDAH* ..."

" What ever.." ya fa'di yana wani kawar da kansa...." Ni dai ki  saurare ni da kyau kiji..kin san waye ni ai ko baki sanni ba?"

" Na sani"
Na bashi amsa a ta'kaice
Yace
" Gud...kar kiga an ha'da ni zama gida 'daya dake kiga kamar kin samu hanyar raina ni ko wani abu, sanin kanki me bazan ta6a 'daukan wannan ba kinsanni... wallahi 6a66ala ki zanyi matu'kar kika ce zaki tsiro min da wani hali, ko kuma kika yi saken da har na ci karo da wani abinda bai game ni ba kin san sauran ba sai na miki bayani ba...Ina nan da hali na da kika sanni da shi wannan Deenin ne har yanzu ban canza ba, dan haka be careful...kar inji kuma kar in gani cewa kin 'dauki magana daga gidan nan kin kai wani wuri dan nasan irin ku 'din nan ba 'kananun munafukai bane...so ki kiyaye ni...ban ce ki samin idanu cikin rayuwa ta ba balle har kiyi tunanin shiga gona ta..bana ma tunanin ba saboda sa idanu aka ha'dani zama da ke ba dan banga abin da zai sa ayimin aure da ke ba in ba haka ba...wallahi kika kuskura naji sunana ya fita daga gidan nan ta 6angaren ki ki kuka da kanki...sannan bansan 'kazanta kina jina ko?..zaman ki anan ma na 'dan lokaci ne da an gama gyaran gidan gaba 'daya zaki koma wani 6angaren daban amma kafin hakan ban son takura sam...dan haka ki kiyaye..kinji ko baki ji ba?"

Da sauri na 'dage kaina sama tare da bu'dan baki nace" Naji.."
" Gud".
Kawai yace tare da sake maida hankalin sa kan kallon da yake yi bai sake bi ta kaina ba.

A hankali na tashi na fita zuwa harabar gidan ganin cewa gari ya riga yayi haske.

Tausayin kaina nake ji sosai yanzu...wai yau gani ga Yah Deen matsayin ma'aurata...sauran sahashin gidan da ba'a kammala 'din ba na tsaya ina kallo..ji nake da ma ayi a kammala gyaran ayau-ayau dan kawai in bar zama tare da shi.

Ban koma ciki ba nayi zama na a waje har lokacin da naji an turo 'kofar gida...da sauri na 'daga kaina sai naga Zaidu kamar daga sama.

Bana shiri da shi amma har ga Allah da na ganshi sai da naji wani sanyin farin ciki ya lullu6e ni...take na washe ha'kora na nufe shi ina fa'din" Zaid".

Fuskar sa ba yabo ba fallasa ya amsa ni ban damu ba na taho da sauri na kar6i bakset 'din dake hannun sa ina fa'din" Ya su Ammi..?"
" Lafiyan su"
Ya bani amsa ata'kaice sai na sake fa'din" Yah Saif bai zo ba to sai kai ka'dai".
Yace
" Nima 'din Ammi ce ta tilastani wai sai na kawo muku abinci".

Daga haka naga ya fara alamun juyawa sai nayi saurin fa'din " Yayah fa na ciki Zaidu...bazaka gaida shi bane.."
Na fa'di hakan ne kawai dan bani son ya tafi tun yanzu.

Waigo yayi ya 'dan ha'de goshi sannan naga ya dawo da baya ya nufi hanyar parlourn, abaya na bishi hannu na duka biyu ri'ke da basket 'din saboda akwai 'dan nawi..kallo 'daya zaka min ka fahimci fara'ar da nake 'kunshe da shi.

Sallama yayi bakin parlourn yayin da Yah Deen ya amsa masa 'kasa-'kasa kamar yadda ya saba.

'Karasawa yayi ya zauna saman kujera sannan ya gaida shi tare da yi masa bayanin abinda ya kawo shi.

Yah Deen jinjina kai yayi kawai...mintina biyu masu kyau Zaidu bai 'kara ba ya mi'ke da niyar komawa.

Yah Deen na daga inda yake yace da shi" Zaid da mota ka zo ne?"

" Erh" Zaidu ya bashi amsa yana kallon fuskar sa...Yah Deen sai yace da shi" idan kaje ka tambayi Ammi key 'din 'daki na akwai kayana aciki ka kawo min su gaba 'daya..."

" To" Zaidu yace sannan ya juya har ya kusa barin 'dakin sannan Yah Deen ya sake fa'din" Zaid kar ka da'de fa ina jiran ka yanzu please".

Jin cewa zai je ya dawo ne ya sani saurin dakatar da shi da fa'din" Zaid in zo in raka ka?"

Bai tanka ni ba sai ya waigo ya dube ni sannan ya dubi Yah Deen yayin da shi kuma yayi kamar bai san me muke tattaunawa ba.

Fita Zaidu yayi daga 'dakin yana 'ko'karin saka takalman sa nima na bishi abaya kaina har yanzu da Hijabi na...tsakani na da Allah nake so in bishi ni kam...so nake na koma gida...inga Ammi na da Ummah ta.

Ina gab da barin 'dakin najiyo muryar sa yana fa'din" Bani san rawar kai da hauka fa".

Cak na tsaya amma ban waigo ba...sarai nasan da ni yake yi wanda hakan ya sa na fara jin hawaye na taruwa cikin idanu na.

Daga hakan kuma bai sake furta komai ba ina ji ina gani daga inda nake ina hango Zaidu ta cikin labile har ya fice a gidan batare da na bishi ba, abu na 'karshe da naji shine dirin motar sa daga haka na lumshe idanu na take sai hawaye na ya gangaro a hankali..." _Kar ki yadda magana ta iso kunnena cewa kina fita ba da izinin mijin ki ba...koma ni ban ji ba kar ki manta Allah yana kallon ki..kuma baya son mace ballagaza marar kamun kai...duk macen da bata yin abu bisa tsari da koyarwar Annabin mu to azahiri za'a iya 'kiranta da suna ballagaza...kuma banda girman kai Hudah ki riga gaida shi kina yi masa biyayya kar ki yadda ki tsiri mugun hali da rashin kunya cikin zamantakewar ku, idan ma kika yi kece da asara domin darajar martabar ki kike ragewa_ ....."
Kalaman Ummah ta na tuna da tayi min irin su kusan sau uku a 'dan sati biyu da na zauna dasu kafin akawo ni gidan Yah Deen.


Hawaye na naji ya 'kara gudu ban iya na 'daga ko hannu na ba kuwa domin sharewa ba...kuma har a lokacin ban juya na kalle shi ba...kenan wannan shine auren?
Na gaida shi da safe shima garga'di kawaicya sake yi min, haka zan 'kare kullum cikin garga'di...badan kalaman Ummah ta da na tunobba da babu abinda zai hana ni fita da gudu in bar gidan nan.

Bai damu da yanayin da nake ciki ba sai naji yana fa'din" 'Dauko plates a kitchen ki kawo min".

Tamkar dama jiran maganr tasa nake yi sai kawai na yi waje da sauri na da yake nasan kitchen 'din a varanda yake...sai a lokacin ma na tuna da shi cuz ko 'dazu da na fito ban tuna na le'ka ba.

Tura 'kofar nayi na shiga ciki..ban yi abinda ya kawo ni ba kawai na tsaya na shar6i kuka na son raina sannan na tari ruwa a tap 'din saman sink na wanke fuska ta.

Plates 'din na 'dauko da spoon na 'dauraye sannan kawo masa..da fitowa ta sai na tarar da shi ya sauko saman carpet 'din tsakiyar 'dakin da kulolin abincin agaban sa, nima gaban sa nazo na zo na ajiye plates 'din tare da mi'kewa, idanun sa na hannu na har ajiye bai kalle ni ba naji yace" Je ki
'karo wani".

Kitchen 'din na koma na 'dauko wani plates 'din na dawo..zan ajiye yace" Zauna".

Dole na zauna..ina sake share hawaye na.

Da kansa ya zuba abincin cikin duka plates 'din..abinda ban ta6a gani yayi da kansa ba kenan shine serving abinci.

Gaba na ya tura min batare da yayi magana ba.

Ban kula ba har sai da yayi kusan spoon uku a nashi sannan ganin ban da niyya ne kafin ya kalle ni umarni ya min da fa'din maza in daina wannan kukan in cire hijabin kaina inci abinci...da nutsatstsiyar murya yaci gaba da fa'din" ke baki da wayo ne? Kin ta6a ganin inda mace ta fita washegarin auren ta ne ko kuwa so kike ke ki bar abin fa'di a gari?"

Shiru nayi kawai nayi 'kasa da kaina batare da na cire hijabin ba a hankali na kai hannu na 'dauki spoon na fara wasa da abincin kamar zanci nan kuwa ni koka'dan banji zan iya cin abinci a gaban sa ba.


Shima 'din kuwa bai sake kulani ba har ya kammala ya tashi ya shige bathroom...shirun da naji ne ya sani tunanin cewa bazai kuma fitowa ba.

Tattare kayan nayi kaf na mayar kitchen wanda zuwa lokacin na daina kukan tuntuni musamman ma da naji ya min magana cikin natsuwa sai na 'dan ji damuwata ta ragu.

A lokacin ne kuma na tsaya ina kallon 'kauye a kitchen 'din da ya amsa suna nawa...ni Noorul Hudah wai matar Yah Deen abin fa na matu'kar bani mamaki sosai, wannan 'dan 'kwalisan nan shine wai yau mijina...murmushi nayi mai sanyi har cikin zuciya ta naji da'di ganin komai da nasan ana amfani da shi a cikin kitchen to akwai shi a wannan kitchen 'din Ammi bata rage komai ba..yayin da aka sanya kalolin komai iri 'daya wato kalar lemon green da fari, 'dazu da nazo sam ban kula da kyau ba.

Sosai kitchen 'din ya haska yayi wani kyau da shi duk wani abin da ya kasance cikin kalolin sa babu lemon green to sai aka sanya fari...sosai komai ya 'dauki hankali na na rin'ka jin da'di...nasan ko bama ni ba duk wanda zai ga kitchen 'din dole zai birge shi... _harda su hajiya Nusee ma_.

Farin cikin da na shiga har ya kasa 6oyuwa a saman fuska ta...
Hijabin dake kaina na cire na ajiye shi saman counter na cigaba da sha'ani na....sai bu'de-bu'de nake yi ina sake kallon kayan dake kitchen 'din...duk babu wanda zai ban wahala wurin amfani da shi saboda duk nasan kaf kayan elctronics a gidan Ammi.

Duk yadda akayi 'ko'kari wajen tsara parlourn gidan amma sam banji ya birge ni kamar yadda kitchen ya shiga raina ba.

Ina nan ban sani ba na shagala a kitchen ashe har Zaidu ya kawo aikan da aka yi masa ya sake komawa.

Sai da na gama iya shirme na na fito da hijab 'dina a hannu na kafin muka ci karo da Yah Deen da jikin sa ke faman tashin 'kamshi.

Yasha kwalliya cikin manyan kaya da hula...hanya na bashi ya wuce abinsa cuz naga alamar fita zaiyi.

Ciki na shiga nan na tadda jakunkunan kayan sa a cikin bedroom wanda na tabbatar sune wanda yace Zaidu ya kawo masa.

Sosai naji haushi da har Zaidu ya iya zuwa gidan har ya tafi bai min sallama ba, na tabbata da Saif ne bazai ta6a yi min hakan ba cike da jin haushi nace" Banza mai ba'kin hali". 


Ranar rasa abinda zanyi nayi wallahi gidan duk babu da'di, gashi Yah Deen ma bai dawo ba har sai bayan la'asar sannan ya dawo wannan 'din ma yana zuwa yayi shirin fita ball ya sake ficewa daga ruwa babu abinda ya sha agidan.

Haka na yi ta zama ni ka'dai kewar su Ammi sosai ya dame ni, na kanji sanyi idan naga Ammi ta aiko mana da abinci hakan na tabbatar min da cewa bata manta da ni ba, abin haushin kawai shine da ake aiko wannan 'dan ra'ayin wato Zaidu, maganar arzi'ki ma bata shiga tsakani na da shi kuma da yazo yake komawa...ban san me yake hana Saif zuwa ba..in shi 'din ne kuwa nasan zama zai yi musha hirar mu da shi.


Ummah ta ma sosai nayi kewar ta sai da nasan in ba wani ikon Allah ba zan jima ban ganta ba cuz a tun zama na da ita ban ta6a ganin ta fita zuwa gidn 'ya'yan ta ba sai dai in da wani dalili 'kwa'k'kwara..so na kuwa san a kaina bazata fara ba, gashi nima banga alamun fita ta kwana kusa ba.

Tsakani na da Yah Deen gaisuwa ce kawai dan yanzu ko abinci bamu ci tare, tunda ya fahimci ban sakewa a gaban sa sai ya daina takura ni, a kullum sai ya gama nasa cin abincin sannan nake zuwa inci nawa, sau da dama kuwa cikin kitchen nake cin nawa kamar wata munafuka.


Ni ke yin aikin gidan kaf babu mai tayani, gashi shi sam bai san ganin koda 'dis 'din stain ne a muhallin sa...kullum kazo zaka samu ko'ina tsaf sai 'kamshi da ke tashi a koda yaushe.


Haka kuma bamu ta6a ha'da wurin bacci da shi ba, kullun kan kujera nake kwana shi kuwa yana cikin bedroom abinsa...sallah wannan bai ta6a janmu tare ba kuma gida yake yin har sallahr asubah amma bai ta6a tunanin tashi na in bishi sallah ba, nashi yake yi inyi nawa daban.


Duk da banjin da'din gidan amma rashin kyara da yake min ya sanya hankali na kwantawa...balle yanzu ni da kaina nake yi mana abinci...da farko ma idan nayi baya ko kulawa amma tun ranar da muka yi brekafast tare shikenan daga baya da kansa ma yake zama yace in zuba masa yaci.


Inaso in je gida wurin su Ummah ta da Ammi amma tsoron fa'di nake yi gashi banda waya balle in tambayi Ammi.

Zamana shirun ne yasa na fara jin matsanancin son ri'ke waya ya a hannu na ya kamani..sai dai dole na ha'kura saboda bansan ya zanyi in samu ba ban manta ba da Ammi tace min idan na kwantar da hankali na da kanta zata sa ya siya min waya...to gashi na kwantar da hankalin nawa amma bansan ta yadda zan yi in sanar da Ammi ba.

Abin haushi har su Saif suka koma makaranta ban sani ba...ranar wata laraba lokacin satina biyu agidan sa muka je da shi wai zan kwaso kayan makaranta ta anan na samu labarin tafiyar su Saif makaranta.

Ai kuwa na ringa yiwa Ammi kuka harda shahshe'ka...sosai naji haushin tafiyar tasu batare da mun sake ha'duwa da Saif ba.

Cikin lallashi Ammi ke bani bakin cewa ai Saif kam 'kin zuwa yayi amma ko ita tace da shi suje suyi min sallama kafin tafiyar su amma ya 'ki Zaidu kam dama shi ba damuwar sa bane...Saif kuwa cewa yayi ba yanzu zai je ba bata kuma san dalilin sa na yanke wannan hukuncin ba.


Haka muka 'debo kayan makarantar tawa muka kamo hanyar gida still ina share hawaye na...tun a hanya kuwa na daina kukan da Yah Deen ya banka min wata uwar  harara.


Abinda ya 'kara kwantar min da hankali na shine komawa ta makaranta, tunda na samu ina fita school shikenan na 'dan samu natsuwa...walwala ta ta 'dan dawo.

Sai dai komawa ta makarantar sai batun Ma'u ya dawo sabo, kullum sai anyi gulmar ta musamman ma ni da ake tunanin agidan su Yahvm Deen nake maganrctake zuwa akai-akai, sai wasu na tambaya ta wai dagaske ne 'dan gidan mu ne yayiwa Ma'u ciki?.

Wannan tambayar na matu'kar 'kona min raina amma haka nake daurewa na bada amsa da fa'din" nima ban sani ba.."

Tausayin Ma'u nake ji sosai musamman idan kana jin labarin irin halin da take ciki.

Nasan koma menene ita kanta cikin 'kunci take a yanzu, gashi ina so inje in ganta amma babu dama.

Abakin mutane nake jin labarin wai cikin yazo mata ne da matsala kullum bata da lafiya ta rame sai haske da tayi.

Ji nayi kamar in zubda hawaye na...jikina sanyi 'kalau ranar na koma gida inda na tadda shi a palour yana bacci...da shiga ta ya farka sai na gida shi.

Idanun sa ya sake rufewa bayan ya amsa, ban wuce ba sai nace " Yayah".

Hannun san ya 'dage ya kalle ni sai nayi 'kasa da idanu na a hankali nace " 'kawata ce bata da lafiya dan Allah inaso in je in gaida ta".

" Wacece 'kawar ta ki?"
" Ma'u"
Na bashi amsa"..me yasa meta?"
Ya sake tambaya ta yana sake ruef fuskar sa da hannun sa.

Shiru nayi na rasa abinda zan ce da shi...sai naga ya juya zai gyara kwanciyar sa ganin da yayi bani da niyyar magana, ai da sauri na furta" 'kawata fa Ma'u na gidan Malam Barau".

Fasa juyawan yayi ya tsaya kallon idanu na yana wani tattare goshin sa.

" Bazaki ba".
Haka kawai ya fa'di atakaice sannan ya juya ya gyara kwanciyar sa ya juya min baya.

Ni kam jiki na sanyi 'kalau na shige ciki, da uniform 'din na fa'da kan gado ina hawaye..bana so ya ji 'karan kukan nawa ballantana ya daka min tsawa...danbhaka sai.kawai ma ringa hawaye ina sjare abina.

Sam zama cikin gidan nan ya ishe ni sosai, ban kuma san yaushe zan gama ba, ban san amfanin kawo ni nan da akayi ba aka hanani zuwa ko ina, bansan laifin da nayi da yasa hukuncin takunkumi irin wannan ya hau kaina ba....gani nake yanzu kowa ya daina so na ne ma shiyasa suka share ni.

Hatta Baban mu inaso inyi magana da shi amma duk babu dama.
Bacci ne ya yi agaba dani a hakan cike da 'kuncin zuciya.



*****
     *Bayan wasu kwanaki*
Tun da muke da Yah Deen bai ta6a ko kwatanta nema na da wani abu ba balle yaga 'kwazo na ko kuma lalaci na ba...amma abin takaici ina cikin barci ranar wata Lahadi tsakanin sallar azahar da la'asar kamar ance da ni in farka sai ji nayi yana fa'din"....No karki damu gidan ai akwai mace yanzu, babu wanda zai zarge ki".

Ban san me akace dashi daga 'daya 6angaren ba haka kuma bansan farkon maganar tasu ba sai ji nayi kawai ya ajiye wayar.

Ban wani sa maganar tasa aka ba balle inyi tunani akai, ina nan ina kwancen kafin nayi wani yun'kuri sai naji motsin sa har ya shigo bedroom 'din.

Maida idanu na nayi na lumshe kamar mai bacci...ban bu'de ba kuwa har ya gama abinda zaiyi ya fita.
Sai da na tabbatar ya fita sannan na tashi nima na cire kaya na na fa'da bayi dan 'dauro alwala.

Sai da na sallaci La'asar da naji ana 'kira kafin na nufi kitchen dan neman abinda zan sawa ciki na cuz na fara jin yunwa a lokacin... maganar da naji yana yi 'din bai kuma zuwa kaina ba.




*****
    Yah Deen sai yamma ya dawo gidan lokacin ina 'ko'karin ha'da mana abincin dare...daga sannu babu abinda ya sake ha'da ni da shi ya wuce ciki.


Daf Maghrib sai muka ji sallama daga 'kofar gida.

Jin muryar kamar ta manya ne ya sani saurin fitowa ina amsawa yayin da Yah Deen dake parlour ma ya fito da sauri jin muryar abokin sa Imrana dan sam bai sanar da shi cewa zai zo ayau 'din ba.


Da ganin Yah Deen Imrana sai ya saki dariya sannan ya waiga ya kallo wa'danda ke tsaye gefe da gefen sa...sannan ya kalle ni...kan YahcDeen ya maida idanun sa daga 'karshe.

Ni dai bance da su komai ba ganin ba ni da ala'ka da su ya sani kowa cikin kitchen na cigaba da aikin dake gaba na.

Yah Deen na shirin 'karasawa gaban su dan su gaisa sai Imrana da rikitacciyar muryar sa irin ta 'yan wiwi yace" Bahba ashe fa sa'a ce da mu...ya akayivhakan ta faru banda labari?...kasan da jimawa labari ya iske ni cewa an kawo gara gidan ka..shab sai na manta da batun, ko munyi waya da kai ban tunawa, haka kaima baka yi min zancen ba, yau da dawowa ta su shadow ke sake tunamin maganar al'kawarin da muka yi da kai kasan harda su na yiwa magana a lokacin da kace in gayyato abokaina, ashe su sun saka rai sosai shine fa suka saka ni gaba wai sai munzo yau ashe kuwa gaskiya ne da zuwan mu sai gata...."
Ya 'karashe maganar yana 'yar dariya.

Turus Yah Deen yaja ya tsaya yana wani 6ata ransa...ji yayi tamkar ya hau Imrana da duka saboda takaici, take yaji ransa ya 6aci har canza launi idanun sa suka yi.

Cike da takaici yace" Ban son hauka ni Imran, hala ka manta ne ko? ba ni da kai muka samu labarin an fasa auren bane...ko tsabar ka raina min hankali ne ya sanya ka 'debo min wannan shirgin kuka zo min gida dan ka tabbatar min da cewa baka da hankali ko?..idan auren zanyi zan 6oye maka ne...dallah ku fice ku bar min gida...".


Zaiyi magana Yah Deen yayi saurin 'daga hannu ya dakatar da shi" Wannan 'din ce baka gane ta ba ko me? yarinyar Ammi ce fa kuma amanar ta Alhaji ya bani"..

" Kenan kai 'din darasi kake 'daura mata ko?"
'Daya daga cikin su ya fa'di wanda ganin sa ka'dai ya isa ya tabbatar ma da cewa a bige yake 'dif bada wasa ba.
" Ban sani ba mahaukatan banza kawai".
Wannan karan a fusace ya bada amsa.
Imran ma zai sake magana yana nuna kitchen 'din da nake ciki kafin fitowar maganar tasa Yah Deen sai ya cusa hannun sa 'daya cikin aljihu tare da dakatar da shi cikin tsarewa da fa'din" Ku bar min gida".

" Gaskiya Deeni ka iya yawa...wallahi wannan yawane".
Fa'din shadow da tunda suka zo bai furta komai ba sai yanzun.

Juya wa sukayi duk suka fice suna tanga'di tare da buga 'kofar gidan da 'karfin gaske.

Yah Deen ya 'dauki a 'kalla kusan mintina goma yana tsaye idanun sa tun 'dazun na kan 'kofar da suka fita, ko a kwatance baya so ya 'kiyasta Hudah da wa'dannan 'yan iskan...dama Husnah ce ya tabbata ko kwana zasuyi zai iya bar musu ita amma wannan yasan da ya ta6a ta iyayen sa zasu ci uban sa...shi duk a kan haka ya bar maganar wai dan saboda gudun 6acin ran iyayen sa shiyasa bai basu ni ba, nan kuwa ba haka bane dan da 'kyar ya samu nastuwar zuciya, kusan sati guda abinvna cin sa arai, da ya tuna sai dai kiji ya saki tsaki, sai dai shi kansa bai san dalilin da ke sashi yin hakan ba, haushi yake ji sosai kawai amma ya rasa takamamman dalilin shin zuwan su Imarana yake jiwa haushin ko kuwa dalilin zuwan su?"




🌷 ~Happy Ramadan in advance~ 🌷





Comment
Vote
Share









*Salmerh ce* 😍


💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)


By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

🕌🌙 ~RAMADAN MUBARAKH~ 🌙🕌


_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_


*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *61*


Nima ina kitchen duk ina jin tattaunawar tasu amma sam ban fahimci inda maganar tasu ta dosa ba, hakan yasa ban wani sa zancen aka ba.


'Kiran sallahr Maghrib da akayi ne ya sa Yah Deen lumshe idanu ya kuma bu'de su nan take...da 'kyar ya iya motsi daga inda yake tsayen ya juya ya koma ciki, zuciyar sa ba'ki'kirin haka yake jin ta, alwala ya 'dauro duk na zaci zai tafi masallaci ne ma amma ga mamaki na sai banga fitowar sa ba.

Shiga nayi nima dan inyi tawa sallar nan na tarar da kan dadduma

Please Login or Register in order to submit comment