Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta a fili kuwa ajiyan zuciya na sau'ke har ina lumshe idanu.
"...Kamo ta nan".
Naji muryar Saif ya fa'di da 'dan 'karfi.

A firgice nayi baya da niyyar kwasa da gudu kawai sai naji sun kwashe da dariya atare suna nuno ni, baki na tura ina 'dan kalle-kalle dan harga Allah ni tsorata nayi.
" Y'ar gidan Ammi matsoraciya".
Cewar Saif bayan ya gama dariyar tasa.

" Ni dai kam kuzo mu tafi".
Nayi maganar tare da juyawa na fara tafiya ina 'dan 'kun'kuni.

A hanya daf da zamu sha kwana muka ci karo da manyan shanukai masu yawa ga dukkan alamu kiwo suka nufa.

Wannan karan Ma'u tafi kowa tsorata musamman da yake itace agaba .

Ihu ta tsala cike da firgici tare da komawa da baya ta ranta ana kare....duk sai muka bita da idanu da mamaki, hakan yasa kafin mu ankare sun mana 'kawanya sai ganin mu kanmu muka yi a tsakanin su.

Ganin hakan ya sanya ni daskarewa wuri guda tare da rintse idanu na da karfin gaske.

Saif kam mai zai yi in ba dariya ba, Ma'u kuwa bata tsaya ko ina da gudun ba sai gidan Yah Deen....tana tura 'kofar sai suka ci karo da shi da yake 'ko'karin fita, bata lura da shi ba har sai da suka yi wata irin gwabzuwa gaba 'daya ta fa'da jikin sa har tana shirin kayar da shi.

Jinta jikin mutun ne ya sanya ta 'kara ru'kun'kume shi da karfin gaske.

Yah Deen kam mamaki, 6acin rai da takaici ne duk suka cika shi, sai hakan basu yi wani tasiri a zuciyar sa ba fiye da yanda yaji tudun boobs 'din ta ajikin sa nan hankalin sa yafi tafiya duk da kuwa bai gane ko wacece ba balle yasan manufar ta nayin hakan.

Da 'kyar yayi 'ko'karin raba jikin sa da nata bayan shu'dewan kusan mintina uku suna a hakan jin yanda wani abu ke shirin taso masa.

Bai iya yaui mata masifa ba balle wani abu kawai sai tsintan kansa yayi da tambayar ta abinda ya faru bayan fahimtar ko wacece, cuz kallo daya yayiwa fuskar ta ya gane cewa itace suka zo da Saif mintina 'kalilan da suka wuce.

" Shanu".
Da yaji ta fa'da ne ya sanya shi matsawa ya le'ka 'kofar sai yaga ma har sun wuce sauran basu fi uku ba.

   Dawo da kansa ciki yayi batare da ya kale ta ba yana duba jikin sa ya furta" sun wuce".
Itama Ma'u le'kawa tayi sannan ta sa kai ta fice tuni farin cikin ta ya kori tsoron kaf, ganin cewa da shi ta ha'du har ma yayi mata magana cikin natsuwa ba tare da tsangwama ba.

   Tafiya take a hankali tana sakin murmushi, ita ka'dai ta san da'din da taji ayau kuma take kanji har cikin zuciyar ta, a ranta take faman maimaita kalaman da yai mata ayau 'din...tambayar ta da yayi " Me yafaru" da kuma " sun wuce " 'din da ya fa'di...sosai suka tsaya mata arai suke kuma sata nisha'di....da haka har ta isa wurin mu ni da Saif da ke ta faman yi min dariya wai dan na tsorata...sai dai ganin dawowar Ma'u ya sanya dariyar tasa ta koma kanta wai ita kuma 6acewa tayi 6at da ganin shanayen sai aka rasa ta.

Ni kam baki na tura bance da shi komai ba haka ma Ma'u kamar ha'din baki...kawai muka cigaba da tafiyar mu.

'Bangaren Yah Deen kuwa fasa fitan yayi ya koma ciki kan kujera ya zauna tare da dafe kansa a 'ko'karin sa na saita yayanin sa, amma ya kasa  daina jin tudun 'kirjin ta a jikin sa...sai daga baya ma ya fara jin haushin kansa da har ya biyewa zuciyar sa bai saisaitawa yarinyar nan zama ba....(daga baya kenan). 


Har muka rabu da ita Saif nayi mana dariyar harda ta mugunta, sai da har muka rabu da Ma'u kowa ya kama hanyar gida kafin ya tuna da 'dagun murya yace " Na manta Ma'u matsoraciya...mun gode fa ".
Ma'u batace da shi komai ba kawai ta cigaba da tafiyar ta tana ji har cikin ranta cewa batayi komai dan a gode mata ba tayi ne kawai saboda sanyin ranta wato Yah Deen.

Koda muka je gida kuwa babu wanda ya sanar da Ammi abinda ya faru duk da kuwa har a lokacin idan muka ha'da ido da Saif sai in ga yana min murmushin mugunta, da abin ya ishe ni shine naje na sanar da Ammi tamkar zanyi kuka ita kuwa tace kar ya 'kara min dariya ai tsoro halak ne ba laifi bane dan na tsorata da ganin shanaye tace ko ita ma ai tsoron nasu take ji.
   Jin abinda Ammi ta fa'di ne yasa na saki raina har ma na fara murmushi nima na jin da'din an bi baya na.

   Sai yamma Yah Deen yazo gidan anan yake ce da Ammi ta dinga tura ko mai yi mata aiki ne tana gyara can gidan saboda 'kura na yin yawa.

Hararan sa Ammi tayi sannan tace " ni na tura ka can 'din nace ka zauna ne?"

" Haba Ammi na...".
Ya fa'di yana rausayar da kansa gefe.
Ammi sai tace
" Kaida ka guje mu saboda me zan dinga wahalar da mutane a kanka?"
" Allah Ammi ba haka bane yaran kin nan ne sun fiya surutu kuma kinga ina karatu ne shiyasa".
" Kaide ka sani".
Ammi tace gami da mi'kewa ta bar shi wurin.

  Murmushi kawai yayi ya koma ya kishingi'da har Ammi ta dawo da ha'da'd'iyar juice 'din Abarba da ta ha'da 'dazu da bama nan ta kawo masa.



*****
      Ammi bata tura kowa ba har sai da aka kwana uku da maganar wanda ganin shiru ya sanya shi sake tuna mata kafin nan ta turani ni da Nana mai aikin ta muka je.
 
Ni kam da muka shiga gidan a varanda na tsaya ita ka'dai tayi sallama, da yace a shigo sai ta shiga, bai san ma da ni akazo ba har sai da ya fito da niyyar fita ya bar gidan sannan ya ganni tsaye a wurin ina ta wasa da hannu na.

Turus yaja ya tsaya da mamaki yace.
" ke kuma fa?"
Inda yayi maganar yana kallo na.

Take sai tsoro ya kamani na kasa ce dashi komai tamkar wacce ta ga dodo a gaban ta.

_".....A a fa Yayah...Ammi ce ta aiko mu da Hudah ita kuma wai tsoro take ji....."_ Maganar Saif ta rannan ne da ya tuna ya sashi sakin tsaki kawai yayi gaba....dan ya gano dalilin tsayuwar tawa a wurin.

Ni kam ajiyar numfashi na sauke har ina dafe 'kirjina ganin ya wuce batare da ya 'kara tanka ni ba.

Har ya kusan fita sai kuma ya tsaya sannan ya waigo ya kalle ni yace " Idan kun gama ku rufe ko'ina ki wuce min da keys 'din can gida zanje na kar6a acan".

Kai kawai na 'daga sama alamar " to" sannan nayi 'kasa da kaina.
Shi kam juyawa yayi ya fita abinsa ba tare da ya 'kara fa'din komai ba.

Yana fita kuwa na bi bayan sa sa'daf-sa'daf ina le'ken sa, sai naga tafiya yayi dagaske amma zuwa bakin hanya ba hanyar gida yayi ba inda yana tafiyar ne ma yana amsa waya hankalin kwance ga dukkan alamu baya tare da damuwar komai.

Da'di naji har cikin raina da ganin ya tafin, gudun kar ya dawo ya tarar da ni da abinda nakeyi ya sanya ni dannawa 'kofar sakata sannan nayi ciki da gudu ina fizge hijab 'din kaina.

Raina fari tas mukayi aikin dan zagewa nayi na tayata amma ina yi ina 'kara jaddada mata cewa kar ma ta yadda tace da ni akayi aikin gudun kar laifi ya shafe ni.

Duk abinda naga be yi ba zan nuna mata a gyara wanda duk ina hakan ne dan kare kaina..." Allah ki tabbatar komai yayi dan in yazo yana masifa cewa zanyi ke ka'dai kika yi abinki dan ban isa da masifa ba ni kam"!
Haka nake ta maimaitawa Nana har muka kammala gyare komai tsaf muka fito bayan mun rufe ko'ina.

A hanyar mu ta komawa gida ne muka ha'du da Ma'u wanda tana ganin mu ta saki fara'a.

Tambaya ta tayi daga ina muke...na gaya mata harda abinda ya kaimu gidan ma duk na sanar da ita.

Bu'dan bakin Ma'u  sai tace " daga yau idan zaku nima zan na raka ku tunda Hudah ma ai tsoro kike ji ko?"
Ta 'karashe maganar tana idanun ta a kaina.

Da kai na bata amsa ina murmushin dan bata san asalin halin sa bane shiyasa take son zuwa inda yake.

Ko da muka 'karasa gida dan gudun magana ma wa Ammi na bawa makullin nasa nace inji shi wai a ajiye zai zo ya ansa.

Anan parlourn Ammi ta ajiye itama bata kai da nisa ba.

Yah Deen kuwa bai zo gidan ba har sai dare shi ko tsoro ma baya ji, arean gidan da yake 'din ba mutane sosai bama shi da makwabci na kusa...amma hakan kullum sai ya ringa yin dare wani lokacin ni har mamakin sa nakeyi ma.


*****
     'Karfe takwas da 'yan mintuna, suna zaune shi da Alhaji Baba da Ammi suna 'dan ta6a hira,
ni da su Saif kam duk muna 'dakunan mu, gara su ma su biyu ne sa6anin ni da nake ni daya sai dai inyi ta buga game ko kuma inta jagwalgwala wayar Ammi dan ba sanin kai nayi ba.

Alhaji Baba ne ya duba agogo sannan ya ce da shi " Tunda ka guje mu sai ka tashi ka wuce ai naga dare ya fara kawo kai".

Kishingi'da ya 'karayi tare da fa'din " Ina waccan yarinyar taki ne Ammi tazo ta bani Key na sai in tafi".

Kan center table Ammi ta nuna masa sannan tace " gasu nan ba ta kai da nisa ba ma".
Bai ce 'kala ba kawai ya tashi ya suri key 'din sa ya nufi hanyar fita". Nayi nan ni kam...Allah ya bamu alkahiri".
" Amin-Amin"
Cewar Alhaji Baba.


Tun daga ranar kuwa Ammi ke turamu ni da 'yar aikin ta Nana duk bayan kwana biyu ko uku da sunan muje muyi masa shara.

    Ma'u da ta gane kwanakin dake tsakanin zuwan namu sai ya kasance bama ko tunanin ina take ko kuma a ina zamu ganta, kawai tarar da ita muke yi tana jiran mu a gefe da gidan, da ta gan mu kuwa sai ta mi'ke mu 'karasa tare.

Ni kam zuwan Ma'u ai rana ya min...gani nake tamkar ceto na tayi, cuz har a lokacin tsoro nakeji dan haka ba kullum ne nake sakin raina in shiga hankali kwance ba, sai dai na kan shigo cikin harabar gidan ne yanzu in jira su har su kammala sannan mu tafi, da yake watarana bai fita har suyi su fito.

Ranar da na samu ya fita ya barmu mu ka'dai ne nakan saki raina in sha shagali na bayan na saka sakata wa mashigar gidan.

A lokacin bansan dalilin da ke sa Ma'u biyo mu ba kuma banta6a tunani akan hakan ba sam, ashe ita burin ta kawai ta ganshi ne...ta kuma kusanci inda yake, masifaffen son shi Allah ya jarabce ta da shi.....



*****
     Satin da hutun Yah Deen zai 'kare a week 'din su Saif suka fara zana JSCE wanda a lokacin Jss 2 ma suke amma da suka ce suna son zanawa sai Alhaji Baba ya shige musu gaba ya tsaya kai da fata har sai sunayen su ya shiga jerin 'yan Jss3 'din masu shirin fita.

        Kwanan su uku da farawa Yah Deen ya tattara ya tafi Jigawa Dutse.

Duk da ba gida 'daya muke da shi ba amma sosai naji da'din tafiyar sa da murnar zan huta ma da zirga zirgan zuwa yi masa shara.

Bayan tafiyar sa ne su Saif suka 'kare jarabawar suka fara hutu kuma.



*****
  Bayan wata uku da tafiyar sannan aka kai su Zaid makarantar boarding, ranar kam nasha kuka da 'kyar Ammi ta lallashe ni nayi shiru...tun daga lokacin gida ya zama shiru daga ni sai Ammi sai kuma Alhaji Baba idan ya dawo daga gidan gona.

Sam banjin da'din zaman gidan kwata-kwata dan ya zama babu da'di...i missed Saif alot dan shi abokina ne sosai ba kamar Zaidu ba.

    Da na kasa gane kan walwala ta sai na dinga tafiya wajen Ummah ta ina wuni acan daga nan mu wuce yawon mu da su Ummie muje gidan Addah da sauran 'yan uwa...inda duk da bana fahimtar hausar ta su sosai amma tun a lokacin na kanji suna cewa wai iyaye na sun bada ni saboda kwa'dayin abin duniya shiyasa suka ringa cusa ni tun ba'a so gashi yanzu har na zama 'yar gida kala ta ta bambanta da sauran 'yan uwa na, wannan maganar sai dai idan bamu je yawo ba sai an fadi min ko kuma idan an ganni ata6e baki sai kiji ance  Lalle fa gaskiya kwalliya ta biya ku'din sabulu". Ko kuma kiji ance " Umm su Hajiya Hudah 'yar gidan masu ku'di gaki nan kin dawo kamar 'kosai" ....Ni sam ba na sa maganganun aka a lokacin nalle in san cewa abin 6acin rai ake gaya min hakan yasa ban ta6a bawa maganar muhimmanci ba.

     Sai ma in an anga yanda na koyi iyayi na canza na dawo fes dani sai kiga ana sakin tsaki da juya kai gefe....ni kam ko ajiki na ban damu da abinda ke faruwa ba...inda har zaki ji wasu na fa'din " Da ayi rawa da bazar uban wani dai gwamma kayi da naka saboda ko babu komai nanne tushen ka kuma nan za'a koma daga karshe musamman idan kasuwa ta watse"..Wannan a gidan da Addah ta Sauda ke aure ne aka fa'di hakan wanda ya fito daga bakib kishiyoyin balbalin ta.

Addah Saudah shiru tayi bata tanka ba balle ni da bama fahimtar manufar su nayi ba sam.

Yawan zuwa gida da nake yi a lokacin ne ya sanya wasu ma'kwabtan mu suka fara gulmace-gulmacen wai ai an fara gajiya dani ne shiyasa aka fara koro ni gidan iyaye na, bansani ba ashe tun zama na agidan mutane da yawa na jin haushi, kuma Ummah ta ta sani amma bata ta6a nunawa ba, haka ma Addah ta ita kuma bata nuna damuwar ta bane saboda tasan abinda suke fa'da 'din ba gaskiya bane shiyasa take juran jin maganganun duk kuwa da cewa suna matu'kar yi mata ciwo har cikin ranta.

A hakan idan maganar tazo kunnan Ummah ta ta kanyi 'ko'karin fahimtar dasu cewa Ammin ke son zama dani ba wai cusa ni akayi ba amma sai aga kamar duk 'karya ne take yi.

Ummah ta shiru take yi musu tunda Allah ya san gaskiya ai shikenan, wannan dalilin ne ya sanya da wuya kaga 'kafar Ummahn mu a gidan Ammi sai indai da 'kwa'k'kwaran dalili kafin nan...sosai take 'ko'karin kare mutuncin ta dana 'ya'yan ta game da hakan.
  

Akwai ranar da nazo sai na 'ki komawa can wurin Ammi, 'karfe 8 har ta gota na dare na gama shirin bacci na har na kwanta, Ummah ta bata ce da ni komai ba, tun kafin Maghrib da tace min inyi in tafi kar dare ya same ni sai nace mata ai nan zan kwana Ammi ne tace min in kwana.
Na shirga wa Ummah ta 'karya nan kuwa bakomai ne ya sani hakan ba illah sabon 'kaunar ahali na da ya shige ni musamman saboda yawan zuwan da nake yi sai yasa sha'kuwar mu 'kara 'karfi.

Ummah kuwa tun lokacin da na fadi hakan sai ta shiga tunanin kardai dagaske zancen mutanen gaskiya ne cewa an fara turo ni gida da dabara...abin ya kulle mata kai sosai cuz tasan ada matu'kar zanzo gida kwana to da Ammi muke zuwa bata ta6a bari na in taho ni ka'dai...amma ga mamakin ta sai gashi yau 'din ni ka'dai ne na taho.

Ita kanta zata so in dawo gaban ta ta cigaba da ri'kon kayan ta amma tafi so inma hakan ne zai faru to ayi shi cikin mutunci kamar yadda aka 'dauke ni ana ganin darajar juna yafi.
Duk da haka Ummah bata 'kara damuna akan in koma ba kawai tayi shiru.

Har na kwanta ni da Ummie ina bata labari tamkar wata sa'a ta saboda shirme...kamar daga sama kawai sai naji tsayuwar mota wanda ya janyo hankulan mutane da dama harda wasu ma'kwabtan mu.

   Alhaji Baba da kansa ya janyo motar suka zo da Ammi ganin dare har tayi amma ban koma gida ba, shiyasa Ammi ta damu Alhaji Baba sai da suka zo tare dan ya tayata ro'ko a bar mata ni gaba 'daya ta cigaba da ri'ke ni.

Ai kuwa a 'kofar gida wurin Baban mu Alhaji Baba ya bayyana abinda ya kawo su inda ya ha'da da ro'kon kar Baban mu yace a a, dan Ammi ta damu sosai.

Cikin gida ma Ammi zaune tayi cikin natsuwa take ro'kon Ummah ta akan tayi ha'kuri bawai raba ta da 'yar ta take son yi ba kawai tsananin sha'kuwa zata duba dan girman Allah ta bar mata ni, tace hankalin ta kasa kwanciya yayi yau ka'dai da bata ganni kusa da ita ba, tasan badai-dai bane hakan bai kamata ta nuna damuwar ta ba tunda hannun iyaye na nake amma duk da haka ta kasa jurewa sai da tazo ta ganni.

Ina lafe gefen ta take maganar tana shafa kaina a hankali dan nima tunda naji muryar ta fito da gudu na rungume ta... daga yanda take maganar zaka fahimci cewa daga can cikin zuciyar ta maganar ke fitowa kuma babu zancen wasa a ciki.

'Dan takaitaccen tunani Ummah tayi....tun zama na agidan ban ta6a kawo 'karar abinda aka min wanda bai kama ta ba, ban ta6a zuwa nayi complaint ba akan wani abu da ba dai-dai ba, zama na nake a sake tamkar gidan mahaifina wanda ko makaho ya ganni zai san cewa hankali na kwance yake bani da wata damuwa a gidan


Comment.
Vote
Share




*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)


By
*Salmerh MD*

 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Wannan shafin naki ne Antyn mu ( Anty MAIMOUNATH O.G MAHNOOR)*
*Allah ya 'kare mana ke a duk inda kike.* 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*


🅿 *36*


   ........Dan haka dan me zata hana ni?...dan me zata raba ni da jin da'di na?..ina ma laifin mai son naka?..ai wanda yaso naka ma tamkar kai yaso, in ba mai 'kaunar ka ba waye zai yi maka hakan....idan maganar mutane kuma zaka biye zaka da'de bakayi abin kirki ba, dan su mutane komai ka aikata to a wajen su kuskure ne dole sai ka samu masu zagin ka, in zaka yi abu to kawai saki ranka kayi abu saboda Allahn ka ba wai dan gudun abinda za'a fa'di ba tunda ba haramun a ciki..."

Muryar Ammi ne ya katse tunanin da Ummah ta ke yi...inda Ammi tace " Dan Allah Umman Saudah karki ce a'a..kinga gidan yanzu bakowa sai ni ka'dai, idan ma bazaki bar min ita ba to ki bani aron ta  mu cigaba da zama zuwa wani lokacin insha Allahu da kaina zan dawo miki da ita...i ll bring her back to u safely kamar yadda kika bani ita insha Allahu.."
Ammi tayi maganar cikin kwantar da muryar ta.

  Murmushi kawai Ummah ta tayi sannan ta biyo bayan sa da fa'din " haba karki damu Ammi, ai 'da na kowa ne...Hudah kam yanzu 'yar ki ce, ga tanan Allah ubangiji ya baki ikon kulawa da ita..Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi".
Iya abinda Ummah ta fa'di kenan daga haka kuwa taja bakin ta tayi shiru.

Take Ammi ta washe baki ta fara godiya wa Ummah ta gami da 'kara janyo ni jikin ta ta rungume ni sosai.

Alhaji Baba yau har cikin gidan mu suka shigo shi da Baban mu, shima Alhajin 'kara mi'ka godiyar sa ga Ummah yayi cike da jin da'di, haka ma Ammi ta ringa zuba godiya.

Kafin su tafi ya ciro ku'di ya ajiye wa Ummah ta duk yadda tayi kan ya bar ku'din amma Alhaji Baba ko kulawa bai ba, Ammi ce tace " Haba Ummahn Saudah...idan kina haka kuma ai sai ya zama tamkar ba'a zama 'daya ba...dan Allah ki bar shi ki siyawa jikokin ki alawa dashi".
Su kam su Alhaji tuni sunyi waje inda suka sake fita tare da Baban mu.


Ko ranar kuwa ban kwana a gida ba muka wuce da su Ammi...sai 'kara jana ajiki ma da takeyi kamar zata maida ni cikin ta.

Tun daga ranar Ammi ta ninka komai da take yi min ada, komai nawa sai da ya fita daban, ta shagwa6ani ta riritani tamkar ni ka'dai ce abu mai sunan 'da data fara gani a fa'din duniya, sosai Ammi ta 'kaunace ni ta nuna min soyayya na zahiri, sai dai duk abin nan bai sa na zama mara kunya ba, sai ma shiru-shiru da na 'kara zama a ko'ina...Ammi ta hanani yawan surutu sosai take kwa6a ta a fa'dar ta wai tafi so in dinga yin komai da 'kwa'kwalwa ta.


Ma'kwabtan mu kuwa da yake ranar da abin ya faru kan idanun wasun su ne sai hakan ya sanya suka canza akalar zancen su da fa'din wai su Ummah ta saida ni sukayi ganin Alhaji Baba ya bawa Ummah ta ku'di...mutanen duniya sam ba'a iya musu wallahi...(na lura abin ma harda hassada a ciki).



     *****
     Zaune suke, Ummah ta, Baban mu, Yaya Usman dan shima wannan karan yazo gida har Addah ta Saudah dake gidan mijin ta...

Baban mu ne yake neman shawarar su game da sabon gidan gona da suka bu'de a can Jos wanda Alhaji Baba yake so ya 'dora shi akai amma shi yana ganin tamkar shekarun sa sunja ya kuma manyan ta yana ganin kamar bazai iya ba.

Yah Usman ne ya dinga bashi 'kwarin gwiwa da nuna masa irin babban cigaban da hakan zai kawo a rayuwar su, yace hakan ai hanyar alkhairi ne kuma ya yadda da kai ne shiyasa karka watsa masa 'kasa a idanu Baba".

" Allah ya tabbatar da Alkahiri yasa hakan shine mafi Alkhairi ga rayuwar mu gaba 'daya"
Ummahn mu abinda kawai tace kenan sai dai batun zama acan ne tace ita kam a a babu inda zataje tsofai-tsofai da ita ga 'ya'ya da jikoki..tace gara shi namiji ne, kuma ai dama su maza da nema aka sansu duk namijin 'kwarai baya zama...kuma komai nisan wuri matu'kar ka kyautata niyyar ka to Allah zai isan maka".

Da haka suka rabu da Yah Usman ya koma gidan sa ya barsu nan zaune Baban mu dumu-dumu cikin tunani.

Haka ma Addah Saudah da ta kasa fa'din komai har taron ya watse, farga take yi na yadda abin zai kasance a bakunan mutane...anya ba'a yi kuskuren saurin amincewa ba kuwa?"

Shi kam Baban mu  tunanin sa na can batun da Ummah ta tayi ne, yana ga hakan cigaba zai kawo a rayuwar sa, to amma ai zama zai iya kuwa, a wannan shekarun nasa yana ga ba mutuncin sa bane yin rayuwa shika'dai a wani wuri daban da ba cikin iyalan sa ba...kuma Alhaji yace an gama komai hatta muhalli an tanadar acan.

Ummah kamar tasan meke cikin ransa kawai tayi 'karfin halin bashi shawarar cewa ya samu wata kawai ya aura sai su tafi tare tace kaga ko ba komai bazaka rasa abincin da zaka ci ba duk sanda zaka bu'kata.

Bece da ita 'kala ba kawai ya tashi ya wuce 'dakin sa.


Hakan kuwa akayi kafin cikar sati biyu har an 'daura auren Baban mu da wata mai suna Jamila,  mijinta rasuwa yayi ya barta da yara biyar....ana 'daura auren da sati guda suka tattara suka koma Jihar Plateau da zama.

Umman mu kam ita ka'dai ta san yanda take ji har azuciyar ta ba ta san me zata ce da familyn Alhaji Baba ba, 'kauna ce wannan ko kuwa akasin haka, komai yana faruwa ne da mutuntaka,  girmama juna da kuma zumunci, amma daga 'karshe duk ciwon abin kanta yake komawa, farko Hudah, 'karfin abinda yasa ta bar ni da Ammi kawai yawan damuwa ta ne ita kanta tana so in daina a wancan lokacin, zaton ta ko ri'keni da Ammi zatayi na 'dan wani lokaci ne, amma sai gashi abin ya juya ya koma zaman da bashi da iyaka dai-dai yake da a 'kira shi na dindindin dan bata san ranar dawowa ta gare ta ba...and ita ka'dai ta san ciwon hakan da taji.

   Sai gashi kuma karo na biyu abin kan Baban mu ya

Please Login or Register in order to submit comment