Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lokacin zuwa kitson yayi, da taga na canza fuska sai kuma fa'din kar in damu duk abinda ya min idan na dawo in gaya mata tana dai-dai da shi.

Haka de na tashi na wuce na nemo hijab 'dina wani sky blue na sanya ajiki na kafin in fito ma har Ammi ta fito da kayan ta shirya su cikin jakar da kawo su tun ranar da ya bawa Zaidu wankin, haka na 'kar6a na tafi badan raina naso ba na kama hanyar gidan sa ina tafe ina 'ku'k'uni cikin raina, fuska ta ka'dai zaka kalla kasan cewa raina be so aiken ba.

Yah Deen na zaune a parlourn sa yana murmushi shi ka'dai, ba na komai ba sai ni sabon halayyar da Ammi ke yi masa musamman saboda ni, shi har mamakin ta yake yi wasu lokutan yadda ta fifita ni akan kowa, ai ya san babu wanda za'a turo sai ni ne shiyasa Ammi taki 'daga wayar sa...A fili ya saki ajiyar zuciya tare da fa'din" Ko cinye ta zanyi oho".
Yana cikin zancen zuci bazata kawai sai yaji tsayawar mota daga waje, cak ya tsaida hankalin sa tare da sauraren wanda zai shigo, ga mamakin sa kawai sai yaga Husnah ta shigo da fara'ar ta ba tare da tunanin komai ba kawai ta fa'da jikin sa ta rungume shi.

Ko da nazo nayi mamaki da naga mota daga waje amma ban wani damu ba nayi shigewa ta ciki da tunanin 'kila abokansa ne suka zo, duk da nasan ba amsa sallama yake ba amma hakan bai hanani yi ba har sau biyu, sai dai jin ba'a amsa ya sa kawai na cusa kaina cikin parlourn na shiga.

Cak na tsaya daga ba'kin 'kofar ban ko 'karasa sakin labilen dake hannu na ba sakamakon karo da nayi da mugun gani.

Yah Deen da wata mace kan doguwar kujera yana lalumar jikin ta.

Duk basu lura da shigowa ta, 'dan hasken da ya bayyana sakamakon rashin sake labilen da banyi ba ne ya fargar da su inda a tare suka waigo suka dube ni.

Yana gani na sai yayi saurin sakin ta ya dai-dai ta natsuwar sa gami da mi'kewa tsaye, kicin-kicin yayi da fuska sannan yana duba na yace a masifance yace"..Baki iya sallama ba ne ke?"
Ya tambaye ni cikin dakiya yana tunkaro inda nake.
Kaina 'kasa nace " ai nayi ba'a amsa ba..."
"...Shiyasa bazamu ta6a yin shiri da ke ba har abada da shegen sanyin tsiya, da kin yi da 'karfi ai da zanji ki".

Kaina na kara sau'karwa ina fa'din " Allah nayi sallama baku ji ba bane".

Tsaki yaja ni kuwa abin hannu na nayi saurin ajiye sai na fara matsawa baya da niyyar tafiya kafin yace zai ta6a lafiya ta.
Yah Deen sai ya daka min tsawa...cak na tsaya na fara rawar jiki.
Sai da ya iso gaba na ya tsaya sannan ya 'dan rage sautin muryar sa yace " Saura inji a wani wuri kinsan hali na ai, da wu'ka zan yanka ki".

Ni kam ma ina ruwa na, har cikin raina ni banga abin bada labari anan ba....sai dai sosai abin ya tsaye min araina na kasa mantawa da shi...wannan karan kashedin sa bai wani tsorata ni ba saboda nasan ba ma fa'dan zanyi ba balle har ta kai shi ga yanka ni.

Haka na juya na koma gida amma duk kotsi na abin na raina, sosai kuwa nayi jarumtar 6oyewa Ammi halin da nake ciki koda ta tambaye ni abinda ya min ma da 'karfin gwiwa ta nace mata ba abinda ya min yau kam.
" Kar fa ki 6oye min..idan na bincika naji wani abu kinsan harda ke zan zane ko?"
" Allah Ammi ba komai".
Na bata amsa da 'kwarin gwiwa ta.

'Bangaren sa kuwa tun fita ta ya kasa ta6uka komai, gaba 'daya 'kunci ya cika zuciyar sa ya cunkushe, duk wani yanayin jinda'din da yake jin sa mintina 'kalilan da suka gaba ta dun sun dakushe, zaune kawai yayi kan 1seater ya sar'ke hannun sa cikin juna ransa a matu'kar 6ace..damuwar sa ni...what if naje na sanar da Ammi abinda naga yana aikatawa.

Husnah kam bata damu ba duk da tayi zaton sister din sa ce ni, amma duk da hakan ganin nawa bai sa taji ta ha'kura da abinda ya kawo ta ba, sai dai duk yadda taso Yah Deen ya kwantar da hankalin sa su farantawa juna abin ya faskara, daga 'karshe ma da masifa suka rabu ya kora ta.

Hankalin sa yazo ya 'dan kwanta ne ganin har anyi kwanaki uku bai ga wani canji daga iyayen sa ba, wanda hakan ne yasa shi fahimtar ban sanar da su ba, tun daga lokacin ya sami natsuwa sai dai bai gushe ba a kullum yana sake Addu'ar Allah ya mantar da ni yasa kar na sake tunawa balle har inyi gigin bada labari.

Ni kuwa 6angare na ko 'kaunar sake jin muryar sa bana yi yanzu balle ganin sa...haka har ranar komawar sa tayi tun ganin sa da nayi da Husnah har zuwa ranar tafiyar tasa ban 'kara sashi cikin idanu na ba...ko ranar ma ina school ya tafi bamu ha'du dashi ba.

Tafiyar sa kuwa yafi komai yi min da'di a rayuwa ta, daga ranar da na san ya tafi shikenan na saki jiki na amma a kullum abinda na gani 'din nan baya barin kaina na kasa cire shi araina sam.


Bayan tafiyar tasa ne Imrana ya je gurin Mahaifin Ma'u da gaske wai shi son ta yake yi kuma da aure, amma mahaifin Ma'u sai yace da shi ya riga yayi mata miji tuntuni dan haka yayi ha'kuri, duk da lokacin babu wanda aka bawa auren Ma'u, amma dole a shekarun san nan badan yaso ba dan dole ya zame masa ya shirga 'karya, badan komai ba sai dan kawai ya tseratar da mutuncin 'yar sa ga fa'dawa lalataccen hannu...cuz yasan fa'dar hakan kawai shine katangar da zai iya ginawa tsakanin Imrana da Ma'u.

Ashe Imrana yaji haushin wannan maganar sosai, dan haka cikin ransa ya ku'duri aniyar 6atawa mahaifin Ma'u rai fiye da yanda yayi masa akan Ma'u, kafin yazo ai sai da ya bincika ya tabbatar ba wani a'kasa da zai kawo kasa tsaiko, ko Deeni da tace tana so bai damu bane dan yasan Deeni ba zai so irin ta ba dan shi 'dan gayu ne na 'karshe...amma bakomai " Zanyi maganin ka 'dan tsoho". 'Karshen abinda Imrana ya 'kudurta cikin ransa kenan kafin ya bar wurin mahaifin Ma'u.

Da wannan damar Imrana yayi amfani tun kafin Yah Deen ya dawo ya dinga shigar masa da Ma'u, shi da kansa ya dinga bayyana masa irin soyayyar da take yi masa tare da yawaita siffanta masa ita ya ringa 'kawata masa halittar ta, tun Yah Deen baya damuwa har yazo ya fara ri'ke zancen ta cikin ransa, bawai dan yana son ta ba a'a kawai dan yawan zancen ta da Imrana ke yawaita yi masa.

Allah sarki Mahaifin Ma'u kuwa ganin kamar ya warware matsalar Imrana ne ya sanya shi bayan wasu watanni kamar uku ya dawo da 'yar sa Ma'u gaban sa ya cigaba da kulawa da abin sa da fatan Allah ya bata miji nagari ya aurar da ita ya huta wa ransa.





Comment
Vote
Share




*Salmerh ce*😍

💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)


By
*Salmerh MD*


*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

🤞🏻

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*


🅿 *40*


Lokaci sun 'dan ja sosai, dan kusan watanni shida kenan da ganin da na yiwa Yah Deen da budurwar sa na farko, ko hutun can ma kuwa daya zo na 'kara ganin su, marasa kunya a 'kofar gida ganin dan unguwar babu mutane sosai ya sanya ko kunyar Allah basu jiba suke kissing juna ga dukkan alamu ta fito zata tafi ne.

Ni kuwa yanzu har na saba da bi ta gidan da yake matu'kar yana gari idan zani gidan Ummah ta sai nabi ta can dan kawai inga ko wannan farar motar tazo...bansan me yasa na damu da zuwan motar ba duk kuwa da cewa idan na ganin na kanji haushi sosai har cikin raina, sau tari kuwa ina ganin motar, sai dai bansan me suke aikata wa ba a cikin gidan tunda ba gani nayi da idanu na ba amma koma de miye ina da tabbacin ba abin alkhairi bane.

Ko Ammi ma yanzu kwata-kwata ta daina aika na wurin sa, idan yana son abu sai dai shi da kansa yazo ko kuma ya aiko yaro amma Ammi bata tura ni sam...musamman ma da ta fahimci irin tsoron sa da nake yi sosai.



*****

Yau 'din ma kuwa gidan Ummah ta zani gaida Addah ta Maryam da tazo tun jiya, ni ka 'dai nake tafiya ta cikin hankali kaina 'kasa, sai dai maimakon in 'dauki hanyar gidan Ummah direct a a sai na yanka na kama hanyar da zata sada ni da gidan Yah Deen.

Tun daga nesa na fara hango motar take sai naji wani iri cikin raina, sai dai duk da naga motar ban dakatar da tafiyar da nake yi ba inda nake sake tunkarar gidan ban kuma san me ke ingiza ni ba kawai dai nasan bai wuci tsabar gulma ba, cak na tsaya ganin ta fito ita ka'dai ta shiga motar ta taja tayi gaba har ta 'karasa wucewa ban ga ya fito ba ga dukkan alamu dai ranar bai yi mata rakiya ba.

Juyawa nayi da sauri na kama hanya 'kafafu na har na sar'kewa saboda yanda jiki na ke rawa da ganin Husnan.

Husnah kam yanzu hat ta saba da zuwa wajen sa ma ko ganin wahalar hakan batayi balle rashin dacewar sa, ko da shi bai 'kira ta saboda bu'katar sa ba ita da kanta ma bata iya sati batare da ta zo inda yake ba hakan yasa jama'ah da dama suka farga da zirga-zirgan da take yawan yi a garin musamnan da kowa ua san cewa gidan da take zuwa 'din gidan 'dan Alhaji Baba ne kuma shi ka'dai ke zama a gidan.

Sannan zuwan Husnah yana farawa ne da zarar ya dawo hutu gida, idan akace baya nan kuwa ba'a ta6a ganin ta tazo, wannan dalilin ya sanya jama'ah zargin wannan ala'kar tasu tare da dasa tunani a zu'katan jama'ah.

Haka na isa gida wata iri da ni sam na rasa walwala ta, su'kuku na yini ranar gaba 'daya, abin na ci na arai amma ban iya na sanar da kowa ba...koda su Addah ta suka tisani gaba da tambayar abinda ke damu na sai cewa nayi kaina ke ciwo, ai kuwa take aka nemo min magani na sha dan dole ba dan raina ya so ba.

Ana saura sati biyu zai koma school ranar da sassafe Alhaji Baba ya 'kira shi a waya inda yace yazo ya same shi....

Yanayin da yaji muryar Alhaji Baba yayi maganar ya sanya bai 6ata lokaci ba ya iso gidan dan cika umarnin Alhajin.

Bayan sun gaisa cikin sakin fuska sai Alhaji Baba ya tambaye shi cewa " Abinda yaji gaskiya ne ko kuwa, ance wata yarinya na yawan zuwa wancen gidan da kake, wacece ita?" Numfashi Alhaji Baba ya sau'ke tare da cigaba da fa'din " Ni da kaina naga tana shiga gidan rannan ko ba ita bace ke zuwa da farar mota?"
Ya 'karashe maganar yana kallon fuskar Yah Deen domin karantar yanayin sa.

Yah Deen kam zuciyar da 'karfi ta tsinke saboda ka'duwa, cike da firgici ya 'daga idanu ya kalli Alhaji sai kuma ya sake sunkuyar da kansa 'kasa nan take, baya fatan ace Alhaji Baba da kansa ya gansa da Husnah da idanun sa, in hakan ne kuwa ya shiga uku da tarin abin kunya ai.

Hakan da yayi ka'dai sai ya tabbatar wa Alhaji Baba cewa ba zargi ake wa Mu'een ba komai da yaji gaskiya ne....duk da fahimtar hakan da yayi amma sai ya 'kara tambayar sa saboda tabbatar wa duk da ya san da wuya ne Yah Deen 'din ya iya bu'dan baki ya sanar da shi gaskiyar lamari amma ua zama dole ya bincika saboda gano wace iriyar rayuwa yake yi da har mutane ke masa habaicin wai _ko 'dan Alhaji yayi aure ne bamu sani mun sanya albarka ba_ .

Cikin dakiya Yah Deen ya bu'di baki batare da ya iya kallon Alhaji Baba ba yace " Ni...Alhaji...Babu kowa da ke zuwa wuri na".
Wanda ya fa'di hakan ne bayan Alhaji Baba ya maimaita tambayar da yayi masa da farko.

Murmushin takaici Alhaji Baba yayi...yayin da Yah Deen ya ayyana irin yanda zai ci ubana a cikin ransa, tunanin sa gaba 'daya kaina ya tafi dan shi a tunanin sa ni ka'dai nasan ala'kar sa da Husnah sai kuma Imrana, shi kuwa ya san ba zai ta6a zuwa ya sanar da Alhaji wannan zancen ba.

Cikin natsuwa Alhaji Baba yayi masa fa'da ta yadda zai gane abinda yake yi 'din ba dai-dai yake aikatawa ba....inda ya 'karasa da fa'din idan aure yake son yi shi bashi da matsala zai iya yi masa jagora a kowani lokaci ko yau ko gobe sati ko wata a shirye yake kuma zai 'dau nauyin fahimtar da Uncle Ja'afar ma ba abin damuwa bane...Yace ya sanar da shi ko 'yar gidan waye shi zai je ya nema masa auren ta yafi akan a zarge ka da abinda bashi bane ko da baka aikata ba da ciwo balle ma babu mai yadda da kai tunda yarinyar ba muharramar ka bace ita.

Kansa 'kasa yace " Babu komai tsakani na da ita Alhaji ba wani batun aure.."
" Toh me yasa take zuwa gurin ka?"
"...Course mate 'dina ce..abu take zuwa kar6a".
Baya Alhaji Baba ya koma ya jinginu...sam baya son 'dan sa ya fa'da irin wannan rayuwar da jama'ah ke zargin sa da shi ko a mafarki baya son ace shike aikatawa.

Amma saboda baya son ya ja maganar sosai dan ransa 'kara yaci yake yi...ya sanya shi ta'kaita batun da fa'din " Naji...amma Muhammad ka sani.. matu'kar ka kuskura na 'kara ji ko ganin abu makamancin hakan ya faru wallahi duk matakin dana ga dama shi zan 'dauka akan ka sam bazan lamunci rashin 'da'a ba, kana jina ko?"
Da " Erh " ya amsa yana mai jin da'din rashin tsananta bincike da Alhaji bai yi ba.

Yana cikin tunanin hakan yaji Alhaji Baba na fa'din " Tashi ka bani wuri...Allah ubangiji ya shirye ka bisa tafarkin tsira".

Da 'dan hanzari ya bar gaban Alhaji Baba ya nufi wurin Ammi...
Yana shiga parlourn ni kuma sai gani na fito cikin shirin zuwa makaranta ina 'ko'karin dai-dai ta zaman jaka ta ya shigo hankalin Ammi ma duk na kaina.

Muna ha'da ido da shi sai ya wani banka min harara cike da 6acin rai, take sai nayi 'kasa da idanu na bansan me na aikata ba kuma yau 'din da aka tare ni da mugun kallo.

'Karaso wa yayi ya zauna a kujera dake facing Ammi...sai lokacin kuma Ammi ma ta ganshi...kafin tayi magana sai nace da ita " Ammi na tafi".
" Adawo lafiya mama na"
Ta bani amsa amma hankalin ta na kansa.
Sum-sum nayi ficewa ta da yake tun lokacin da ya shigo gidan mun ha'du kuma na gaishe shi a lokacin kuma banga yayi min mugun hali ba, Ammi ce dai basu ha'du ba kawai ya shiga wurin Alhaji.

Ita kam ma sam bata san da cewa yana gidan tun 'dazu ba, bata kuma san da wannan batun ba haka bata san me suka tattauna da Alhaji Baba ba ta dai gansa wani iri sai faman kau da kai yake kamar munafuki, yana gaida ta ko abinci bai tsaya ya ci ba kawai yace da ita ya tafi.

Ammi da idanu ta raka shi har ya 'karasa fita, bata damu ba cuz ta sha ba'kin halin nasa ne yau ya motsa.

Ko da ya koma gida bai iya ya sanar da Husnah cewa kar ta sake zuwa ba kamar yadda aka garga'de shi, ita kuwa yanzu sosai ta jarabtu da shi dan yana yi mata natan, ta kan yawaita shirga wa mahaifiyar ta 'karya n zata guri kaza idan ta fito sai ta nufo wurin Mu'een, sau da dama ma baya sanin zata zo sai dai kawai kwatsam ya ganta ba kuma yace mata me yasa kawai sai su shiga sha'anin su.

Shai'danin bai ta6a complaint akan hakan ba da yake shima 'din baya wuce tayi musamman idan akan Husnah ne.

Haka ranar ya wuni wani iri da shi..bai fita ko'ina ba ko neman abinci bai je yayi ba, Imrana ne ya nemo musu 'dan abin tabawa dangin drinks shima 'din ba wani na kirki ya sha ba ya bari, ko da Husna ta 'kira shi a waya kuwa sama-sama ya amsa ta, wanda jn sa wani iri ya sanya ta tambayar ko lafiya ...baka jin da'di ne? sai yace mata "Erh"
A takaice.
Take ta rikice ta fara yi mai sannu a jere...bai amsa ko 'daya ba kawai ya yanke 'kiran yama kashe wayar tasa gaba 'daya.

Duk yadda Husnah ta so jin sa amma bata same shi ba...hankalin ta ya ta shi sosai gashi bata da number kowa a garin nasu balle ta 'kira taji..hakan sai ya hana ta natsuwa ji take tamkar tayi tsutsuwa taje ta ganshi taga halin da yake ciki.

A daddafe ta 'karasa yinin ranar duk ba'a nutse ba, wani irin so take yi masa mai wuyan fassaruwa.

Shima 'bangaren sa sai da yamma ne kafin suka fita filin ball shi da Imrana dalilin kenan da ya sa shi 'dan warwarewa...har dare kuwa bai kunna wayar tasa ba cuz haushin kowa ma shi yanzu yake ji, ko gida bai koma ba dan baya son ya ganni kuma babu damar hukunta ni a gaban Ammi domin for sure ya san akaina sai ta 6ata da shi, shi kuwa akan wannan munafurcin da yake tunanin ni nayi masa bai ga mai zai sa ya bar ni na sha haka nan ba.

Banda tsantsar kunyar Alhaji Baba da ta cika shi, kunyar sake ha'da ido yake yi da shi, dan yana ganin tamkar yana kallon sa matsayin mai kawo mace gidan sa hakan yasa ko hanyar gidan bai iya ya kama ba har washe gari.

Bai sani ba ashe Alhaji Baba kusan mutane hu'du ne suka ta kai masa gulman abin...da farko baya sa zancen aka.
Dan tunanin sa Muhamad 'din sa ba zai aika ta hakan ba, amma daga baya sai abin ya dame shi yasan idan har ba dagaske bane ba yadda za'ayi ma banbamtan mutane su ta kawo masa magana iri 'daya....shiyasa ya saka ido da kansa a hankali kuwa sai Allah ya nuna masa zuwan yarinyar har tayi parking ta shiga gidan.

Ransa ya 6aci sosai da ganin hakan, yasan babu mamaki mutane zasu masa kallon mutumin banza ne da har zai bar 'dansa ya ke6e yana rayuwa shi ka'dai yana kuma aikata abinda ransa yake so wanda za'a iya 'kira da banzar rayuwa duk kuwa da cewa babu wanda yasan abinda ke kawo yarinyar gidan.

Yayi niyyan tsawatar wa Yah Deen game da zuwan yarinyar ne bawai dan yana zargin sa da aikata sa6on Allah ba illah dan kawai ya tunadar da shi anfanin kare mutunci da kuma nesan ta kai da abin Allah wadai...shi yasa ko da ya nuna shi ba komai bane ke faruwa Alhajin yayi saurin yadda da shi.

*Nasan wasu zasu ce me yasa fa'dan sa ya tsaya iya can....ba cin azahiri abinda Mu'een ya aikata abin a tsawatar masa ne sosai....toh fa nima ina son sanin dalili sai dai nasan duk bazai wuci tsananin yadda da yayi da shi ba* .

Washe gari Husnah bata samu daman fita ba dan mahaifiyar ta ta tashi da zazza6i hakan yasa ta tsaya kulawa da ita gashi ko asbiti ma basu samu ganin likita da wuri ba, damuwar ta biyu ta zama amma dole ta danne 'dayan saboda SAWUN GIWA YA TAKE NA RA'KUMI.


*****
*Bayan kwana biyu*

Tun 'karfe tara na safe Husnah tayi parking 'kofar gidan Yah Deen...yana bayi lokacin yana 'ko'karin hanzartawa ya shirya dan zuwa gaida mahaifan sa cuz ba zai iya 'daukan tsawon lokaci batare da yaje gare su ba ko ma dan ya proving innocence 'din sa ya shi yanke shawarar shiryawa yaje...duk da ya san for now Alhaji Baba ya jima a gidan gona shiyasa ya 'kudira cikin ransa cewa yau 'din har gidan gonar zaije ya bashi ha'kuri ya kuma taya shi ayyuka inda hali ma acan zai taya shi yini bazai dawo da wuri ba har alokacin kuma bai kunna wayar sa ba.

Husnah na shiga ta cire mayafin ta...ta ajiye shi anan parlour da 'yar pulse 'din ta ta tinkari cikin bedroom 'din nasa.

Tana zuwa nan ma sai taga wayam baya nan hankalin ta ya so ya 'kara tashi sai dai sakamakon 'karan ruwa da taji a bayi ya sanya ta saki ajiyan zuciya.

Da baya ta kwanta a kan gadon dake 'dakin tana jiran fitowar sa.

mintina biyar mai kyau basu cika ba kuwa sai gashi ya fito 'kugun sa 'daure da towel fari.

Yanda ta ganshin sai ta ji wani sanyi cikin ranta ya ratsa ta...zaune ta mi'ke tana sake 'kare masa kallo tana murmushi.

Shi kam turus yayi da ganin ta sam bai ji da'din ganin ta ba a wancan lokacin, sai ma haushi da ya kara ji akan wanda ke 'kunshe cikin ransa.
Wani mugun kallo ya bita da shi ya ka'da kai yayi gaba tare da 'kara murtu'ke fuskar sa...haka ya nufi inda yake ajiye 'kananun towels 'dinsa ya zari 'daya ya fara tsane jikin sa da shi...bai ko sake kallon inda take ba.

Bai zata ba kawai yaji hannun ta kan hannun sa tana 'ko'karin kar6an 'karamin towel 'din daga bayan sa, a fusace ya juyo ya hanka'da ta baya ta tafi taga-taga kamar zata fa'di sai Allah ya taimake ta drawern mirror ya tare ta.

Da mamaki ta 'daga kai take duban sa, saman la66a ta furta sunan sa " Mu'een"! Tana 'kan'kance idanu alamun mamaki 'karara ya bayyana kan fuskar ta.

Yatsa ya nuna ta da shi a fusace yace "..don't ever call my name again....and kiyi tafiyar ki, wa ma yace miki kizo...na 'kira ki nace kizo ne?"

Tsayuwan ta ta gyara cikin marairaita tace " Haba dan Allah Mu'een yau na fara zuwa ne da zaka fa'di hakan?..idan wani abin nayi maka ai sai ka sanar dani in gyara ba wai ka yi treating 'dina ba?"

.....Ido ya lumshe ya kuma bu'dewa cike da takaici ya kalle ta, 'karamin towel 'din ya rataya bisa wuyan sa ya tako gaban ta ya tsaya idanun sa cikin nata yace" Kin san wani abu?"
Husnah bata iya tace da shi komai ba sai ido da ta zuba masa sosai yake bata mamaki.

Bai damu da rashin amsawar ta ba shima kawai ya cigaba da fa'din "...Bani bu'katar sake ganin kin kusanci inda nake Husnah".


'Dago 'kafa tayi da niyyar 'karasowa kusa da shi sosai take sai ya 'daga mata hannu sannan ya girgiza mata kai tare da matsawa baya ka'dan a hankali ya cigaba da fa'din " Kin san abinda zuwan ki garin nan ya haifar min?....kinsan yanda hakan ya ta6a mutunci na Husnah, mahaifina fa da kansa yayi min maganar...kin san nauyin da naji ya kamani a lokacin?"

Kansa ya shafa da hannun sa 'daya tare da furzo iska daga bakin sa sannan ya cigaba da fa'din "....ki kama hanya ki koma inda kika fito and please kar ki kuskura ki sake zuwa gidan nan in ba ni da kaina na na neme ki ba...oyah..."

Ya nuna mata hanyar fita tare da 'kara matsawa baya.

Husnah kam maimakon ta fice a a sai ma ta taho da gudu ta shiga jikin sa ta rungume shi tana sakin kuka cikin salon yaudara....duk yadda ya so ya raba ta da jikin sa ya kasa, dole haka ya 'kyale ta...cikin kukan take fa'din Yayi ha'kuri kar yayi mata haka dan Allah....idan yayi mata katanga da kansa bata san halin da zata shiga ba..."
Da kakkausar murya yace
" Ohh ke kanki kawai kika sani baki san zancen mutunci ba ko....dallah sake ni 'katuwar banza 'katuwar wofi".

Wannan karan da 'karfi ya hanka'da ta sannan ya kamo hannun ta yaja ta zuwa parlour ya tura ta ciki ya koma abin sa ya datse 'kofan ta ciki.

Husnah haushi da ba'kin ciki sosai ya kamata dan haka a fusace ta zari mayafin ta da pause ko rufa mayafin bata yi ba kawai ta fita da 'dan gudu-gudu tana kuka.

Bata tsaya ta lura da mutumin da ke

Please Login or Register in order to submit comment