Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

A lokacin sosai tsigar jikin ta taji ya tashi ashe daga lokacin Baby bazata sake rarrashin ta ba, shiyasa ma ta yi ta kallon idanun ta amma bata gane komai ba duk da kallon da baby ke ta binta da shi...Ashe amsar tambayar da ta bata bata yi kuskure ba lokacin da ta tambaye ta cewa tana so su koma gida ne Baby sai tace da ita" Ni ba dake zanje ba...".
Allah sarki rayuwa gashi ta dawo gidan kuma bata dawo da ni ba...shikenan bazan sake kallon ki ba  Mama na? Shikenan kema kin tafi?"
"... _ban yi Pupu ba a school kuma ko fitsari ma banyi ba amma ya min tsarki mai zafi_ ..."
Wannan maganar da ta tuno ne ya toni asirin kukan ta, sosai take jin ciwon wannan abin, gani take har abada babu wanda zai 'kara yi mata cutar da zata kai mata wannan abin, Sani da Ubangidan sa sun cuceta, cuce mafi tsananin ciwi a zuci, gashi sanadin su ta rasa Baby, rashi na har abada..."..
Kuka sosai take yi sahf ta mance da cewar dare ne ba rana ba.
Ammi ce ta ta shi ta cigaba da kwantar mata da hankali ha'de da nasiha mai ratsa jiki. Wanda tun faruwar lamarinbsai yanzu ta iya yi mata magana mai tsayi har ma da Nasiha mai sanyi.

Kwana tayi tana tunane-tunane batare da ta iya rintsawa ba, ko gaisuwa idan anzo sai dai su Hafsat su amsa da su Ammi amma ita kam bata iya fa'din komai.

Cikin Alhaji Baba da Ammi kuwa babu wanda ya sake waiwayen inda Yah Deen yake ko su damu da halin da yake ciki, tausayin sa ko misqala zarratin babu shi a zuciyoyin su.

Da yamman ranar su  Zaidu suka iso, a bakin Safwan suka ji halin da yake ciki take kuwa sai hankalin su ya 'kara tashi, sosai suka ji mutuwar Baby har cikin jinin su, dan kuwa babu wanda be zubda 'kwalla ba, ganin basu ga 'dan uwan su bane ya sa suka tambayi Alhaji Baba sai yace da su shima be sani ba.
Safwan ne ya girgiza kansa sannan yayi musu bayanin komai ganin kamar hankalin su ya tatshi da rashin ganin san, zaton sa ko sanar da su in zai sa su samu natsuwa.

Ai kuwa take ya 'karya ta batun sa dan kuwa kuka suka ringa yi kamar 'kananun yara, abin duk ya musu bazata, da yake su sun taho ne kawai jin cewa Jasmine tayi accident amma har suka iso basu san cewa already ta rasu ba, basu gama wancan jimamin ba kuma ak 'kara musu da wani sai kuma 'dan uwan su na can jikin na'urori bai ma san da batun rasuwar Baby ba.

Zaid kam bai iya ya motsa zuwa ko ina ba,  ya zauna a wurin karban gaisuwa, cikin ransa yake ro'kon Allah akan ya tausayawa Yah Deen ya sassauta masa wannan abin, gani yake tamkar sun yi masa yawa damuwan dole zai illata shi, tun ma bai san da batun jinyar baby ba gashi ya shiga coma ina ga yasan cewa Precious Babyn sa ta tafi ta bar shi...tausayin sa sosai Zaid yake ji yayin da wani 6angare na zuciyar da ke  jin haushin Yayan nasa da ya 'dauki drivern da be iya tu'ki sosai ba gashi ya salwantar musu da rayuwar Yarinya a banza...a ganin Zaid kamar rashin iya tu'ki ne ya kawo accident in.

Saif kam kasa natsuwa yayi domin dauriya yasawa zuciyar sa ya danne komai ya danne damuwar rashin Baby musamman da yasan cewa ko ya damu kansa ma Jasmine ba dawowa zatayi ba so da me rai ake yi dan haka hankalin sa duk ya tattara ya dawo da shi kan 'dan uwan sa...cikin zuciyar sa yake juya amsan da Alhaji Baba ya basu game da Yah Deen in, dole yasan akwai wani abu amma haka kawai Alhaji Babab bazai ce bai san inda yake ba bacin zaman kar6an gaisuwan 'yar sa ake yi, babu ammaki akwai laifin da yai masa shiyasa har ya fa'di hakan game da shi.

Abin sosai ya dame shi, Zaid kam ma ko aka bai sa ba, balle yayi wani tunani akai.

Saif ne ka'dai yaje har asbitin ya dubo shi a daren ranar batarecda ya bari ya kwana ba, wanda har a lokacin ma ya tarar da shi ne bai san waye akan sa ba...duk yanda ya so ya danne batun rashin Baby amma ya kasa, sosai yake ji da Jasmine yake sonta fiye da yanda yake son kansa, hakan yasa tunanin ta kan yawaita zuwa brain 'dinsa lokaci kan lokaci zaki ga yana share hawaye da fatan Allah ya ji'kan ta, ashe haka rayuwa take?"

Sani ma tuni ya farfa'do yayin da Dr.Felix ya cigaba da bashi kulawa,  cikin sa'a akayi aikin kuma anyi nasara sai fatan Allah ya kiyaye na gaba...sani.ya zama mai hannu 'daya, sa'an sa 'daya ma hannun hagun aka cire aka bar shi da dama.

Tunda ya farka kuwa hawaye yake zubdawa,.nadama sosai ya shige shi matsannanci, da kansa yake Allah wadai da halayyar sa, yasan idan Umman sa taji abinda ya aikata ma da 'kyar ne idan zata yafe masa...kaico na...na bi son zuciya gashi ta kaini ta baro ni...sai gashi tun a duniya naga sakamako na ..Yah Allah ka yafe min, Yah Allah ka ji 'kaina, ka bani lafiya ka kuma bani 'kwarin gwiwar da zan iya dur'kusawa gaban oga Deeni in nemi yafiyar sa bisa cin amanar da nayi masa, in ce Maman Baby ta yafe min raina mata hankali da nayi, In ro'ki Jasmine tai min afuwa badan hali na ba, nayi al'kawarin zame mata bawa har 'karshen.rayuwa ta matu'kar zata yi min afuwa ta yafe min abinda na yi mata.."
Kuka yake yi sosai wanda ya rasa mai lallashin sa, bashi da kowa da zai ce masa kayi ha'kuri daga shi zai tarin nadamar sa a zuci.

Washe gari Sai ga Su Ishaq tun daga Maiduguri inda sun taho dan Alhaji Baba da kansa ya sanar da Ishaq rasuwar Jasmine cus duk cikin abokan Deen Ishaq yafi kwanta masa sosai.
Tare suka taho da su Imam, Anas da wasu daga cikin abokan su na makaranta da duk ya sanar mawa.

Kowa yaji labarin rasuwar Baby da kuma rashin lafiyan Mu'een Noor ake fara tausayi,  saboda dole ansan sai ta shiga wani hali sakamakon rashin 'yar ta ga kuma ga Miji can kwance shima rai a hannun Allah.

Kwanan sa biyu kafin ya dawo hayyacin sa..da salati abakin sa, abu na biyu da ya ambata shine sunan Noor followed by 'yar sa Jasmine...

Safwan aka yi saurin nemowa yazo lokacin da ya iso hannun Yah Deen dafe kansa yana yayyamutsa fuska duk jikin sa wani iri yake jin sa...yana jin muryar Safwan sai yace"...Kaina Safwan ciwo".

Matsawa Safwan yayi kusa da shi yana yi mar sannu tare da nema masa sau'ki daga wurin Ubangiji.

Bai jima da farkawan ba sai ga Saif ma yazo dam baya iya yin awa biyar masu kyau batare da yazo yaga halin da 'dan uwan sa yake ciki ba.

Sosai yake bashi tausayi dan yasan a zahiri Yah Deen sai yafi kowa jin ciwon mutuwar Baby Jasmine.

Tausayin 'dan uwan nasa ne ya sanya shi kuka yana tsaye daga bakin 'kofa yake share hawaye, Yah Deen sai tsura masa idanu yana kallon sa da lumsassun idanun sa amma bai furta masa komai ba.

Ganin hakan ne yasa a hankali Saif ya 'karaso ya matso kusa da shi sannu yayi masa cikin tausayawa yana me kawar da kai dan baya so ya fahimci halin da ake ciki tun yanzu.

Baya jin ciwin komai sai 'kirjin sa ka'dai da yayi masa nawi sai kuma kansa jikin sa dake ciwo kuwa yasan ba komai bane face gajiya da kwanciya wuri guda da yayi, dan haka da kansa ya yun'kura ya tashi ya zauna, cire zcannular dake hannun sa yayi...Likitan sa da Safwan na yi masa fa'dan baya bin ka'ida kamar be san dokar aiki ba.
Ko tanka su bai yi ba, a fa'dar su ma wai ya tsaya tukunna a gama tabbatar da sau'kan ciwon kafin ya tashi..." Kaina ka'dai ke min ciwo..".
Daga fa'din hakan bai damu ba kawai ya tambayi Safwab iya kwanakin da yayi a kwance Safwan yayi masa bayani sai ya jinjina kai tare da mi'kewa tsaye ya nufi bayi da dubara ya 'dauro alwala ya fito.

Haka yayi sallolin sa batare da jan dogin surori ba dan jiri baya barin sa 'kafar sa ma rawa take yi masa sosai...idan yayi sai ya tsaya ya huta kafin yake cigaba da jerowa.

Saif ne ya tsiyaya masa fresh milk mai 'dan sanyi ka'dan amma ya 'ki sha shi wai Coffee zai sha, duk yanda Safwan yayi 'ko'karin nuna masa muhimmancin shan fresh milk in ammaYah Deen 'kin amincewa yayi..sai da yaga Saif na hawaye kafin ya ansa ya 'dan sha yana kawar da kansa.

Dole tasa Safwan ya aika  aka kawo masa Coffee 'din dan ya lura Mu'een taurin kai ne da shi da kafiya, yanayin abinsa kamar Noor, itama haka bata jin magana wani lokacin, wanda duk bai san hakan ba sai yanzu da zama ya ha'da su a asbiti yasa ya 'dan fahimci wasu halayyan ta, sosai take da taurin kai irin na Mu'een, gashi ba ta jin lallami idan ranta ya 6aci.

Cikin sa'a kuma ma ba'a jima ba sai gashi an kawo masa kafin hakan kuwa 'karasar da jerin sallolin dake kasan yayi.

Sai da ya idar kafin Saif ya gabatar masa da Coffee 'din ya kar6a ya sha abin sa cikin kwanciyar hankali, banda 'yar rama da yayi babu abinda zaka gani ajikin sa kace shine marar lafiyan..domin ya 'dan warware.

A hankali yake sipping yana tunanin halin da iyalan sa ke ciki, Saif kam ba 'karamin farin ciki yayi da farkawar 'dan uwan nasa ba sai dai ta wani 6angaren tausayin sa yake ji matu'ka, yasan jin labarin mutuwar Baby shine zai zame masa wani babban illar kuma idan ba ayi sa'a ba...gashi Safwan ya garga'de shi da cewa kar ya sanar da shi tun yanzu su bari tukunna sai ya 'kara samun natsuwa.

Yana cikin sipping Coffee 'din ya dubi Safwan yace" Ya jikin Baby ne..Allah yasa dai ta warware yanzu...".

Shiru Safwan yayi yama rasa ta inda zai fara yi masa bayani.
Saif kam 'kasa yayi da idanun sa kafin Safwan yayi magana kuma sai ga su Ishaq sun shigo da sallamar su.
Cikin natsuwa duk yake duban su, har cikin ransa ya ji da'din zuwan su.
Yayin da suma sukai matu'kar farin ciki da ganin sa a zaune cus jiya bayan isowan su sun zo amma a lokacin bai tashi ba sai gashi kuma yanzu cikin sa'a yana zaune had da cup a hannun sa da alamu jiki yayi sau'ki.

Hannu suka zo suka bashi suna yi masa ya jiki tare da gaisawa da Safwan.
Deen yana murmushi yace" Lalle Maman Daddy 'yar gata ce, kardai duk saboda duba jikin Baby kawai kuka zo all the way from Borno State?..".

Murmushi Ishaq yayi tare da zama gefen sa yana cire hular kansa.

Ganin yana shirin zama ne ya sanya Yah Deen saurin fa'din" A a ku tashi muje Please nima nan da kuke gani ba 'karamin 'kaguwa nayi da ganin su ba...".
Hakan da ya fa'da ne ya sanya Ishaq saurin fahimtar cewa har yanzun bai san halin da ake ciki ba kenan...
Fuskar sa ya kalla sannan yace" Kar ka damu ai zamu...amma gama cin abincin naka tukunna".
Yamutsa fuska Deen yayi yana fa'din" Ai na gama..ya ishe ni fa dama, tun 'dazun su Saif ke 'duramin madara kamar wani 'karamin yaro..."
Yayi maganar yana murmushi tare da ajiye cup in hannun sa a gefen sa.

Maganin sa Safwan ya 6allo ya bashi inda shi kuma yana murmushin yace" Safwan sarkin dubara so dai kake sai na 'kara sha kenan..?".
Da haka ya kar6i maganin ya sa abaki sannan yabi bayan sa da Coffee 'din, dire cup 'din yayi yana sau'ke ajiyan zuciya...yana duban hannun sa inda aka 'daura masa canular ya shafa a hankali cuz 'kai'kayi wurin ke masa.

Yun'kuri yayi yana shirin mi'kewa amma sai Ishaq ya dakatar da shi...da fa'din" Magana fa nazo muyi da kai".
Koma wa yayi ya zauna yana fa'din" Okay ka hanzar ta, na 'kagu inga iyali na..".
Cikin ransa ya ayyana ba mamaki shima yaji labarin abinda ya faru ne, nasan kowa ma tsana ta zai yi yanzu".

Nasiha Ishaq ya fara yi masa cikin natsuwa har ya gangaro kan batun rasuwar Baby...Yah Deen kam tsura masa idanu yayi ganin kamar da gaske yake yi bada wasa ba ya sanya Yah Deen juyawa ya ringa binsu da kallo 'daya bayan 'daya.

Kansa yaji yana juya masa sai ya lumshe idanu" Ishaq kasan bama irin wannan wasan da kai ko?"
" Ana wasa da mutuwa ne Mu'een?"
Imam ya bashi amsar tambayar sa da wata tambayar.
Bai damu ba da wata raunanniyar murya yana dafe da kansa yace" Safwan dagaske Jasmine ta rasu? Dagaske Baby ta tafi ta barni?"
Safwan matsowa yayi daf dashi dan yayi masa bayani cikin natsuwa yace" Jasmine ta rasu Mu'een, tun ranar da su Ammi suka zo bata 'kara kwana da rai ba, idan baka manta ba ranar shine kaima aka kwantar da kai anan 2days kenan yanzu...".
Jajayen idanun sa ya bu'de ya sau'ke su kan fuskar Safwan yayin da ya cigaba da fa'din" ha'kuri zaka yi Mu'een ha'ki'ka rasa Jasmine babban rashi ne mai ta6a zuciya amma babu wani abinda zamu iya aikatawa tunda muma 'din duk shi muke jira..."
A fizge ya furta Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un...kansa ya fara girgizawa a hankali da sanyin murya yace" Ishaq...Nuree fa wani hali take ciki? Ku tashi ku kaini gida please..zan je in duba ta, nasan hankalin ta tashe yake sosai yanzu, kuma ina so in ro'ki Ammi ta yafe min Alhaji ma yayi fushi da ni..yace babu shi babu ni.."

Kuka Saif ya fara a hankali dama yasan dole akwai wani abin tsakanin sa da mahaifin su, Yah Deen duban sa yayi da riannanun idanun sa yace" Saif dagaske ne Jasmine ta rasu..?"
Bai iya ya bashi amsa ba dan kuka da yaci 'karfin sa.
Yayin da Yah Deen ya maida idanun sa ya rufe..ko ina jikin sa ji yayai yana masa gudu, yayin da bugun zuciyar sa ya tsananta ya sosai...amma duk da hakan fa'di yake su kaishi wurin ahalin sa, yana so yaga iyalan sa.

Basu yadda sun tafi ba har sai da liktan sa ya basu dama domin yace ciwon nasa tashi yake yi idan ya riga ya sau'ka kuma shikenan dan haka discharging nasu yayi ya 'kara da fa'din idan akwai wata matsala suyi saurin tuntu6ar sa.

Godiya suka yi tare da kamo hanyar gida dukkan su hadda Safwan dan shima tun lokacin da aka kwantar da Jasmine har zuwa yau 'din bai huta ba.

Cikin motar yake gayawa Ishaq cewa" Nuree tace wai har abada bazata yafe masa ba, ka taimake ni Ishaq wallahi bazan iya rayuwa babu ita ba..itace farin ciki na bana so in rasa ta kamar yadda na rasa Baby Ishaq".

"Kar ka 'daga hankalin ka please Mu'een, Noor mai ha'kuri ce na tabbata zata yafe maka duk abinda kayi mata Insha Allahu".
Abinda kawai Ishaq yace kenan har suka isa gida, yayin da Saif ke share hawaye a 6oye, tausayin 'dan uwan sa yake ji sosai...aganin sa abubuwan sun yi masa yawa ma.

Da isar su 'kofan gidan nasa sai jikin sa yayi sanyi 'kalau bai iya ya sake furta komai ba har suka fiffito daga motan, a hankali ya ringa bin mutanen dake zaune da idanu, hadda abokin Uncle Ja'afar ya gani a wurin zaune wanda ya bashi aiki anan asbitin da ya bari a bauchi, Babban mutun ne mai fa'da aji amma gashi zaune 'kofar gifan sa tare da mahaifin sa wurin kar6an gaisuwar 'yar sa Jasmine, da 'kyar yake 'daga 'kafafun sa amma ya daure suka 'karasa wurin jama'ar, da yawa sun yi farin ciki da ganin ya taho da 'kafafun sa domin duk sun san halin da yake ciki a gadon asbitin...cuz Safwan na kawo musu labarin halin da ake ciki dan su kwantar da hankalin su.

Kowa gaisuwa ya ringa mi'ka masa yayin da shima ya mi'ka gaisuwa ga manyan sa su Alhaji da sauran su, Alhaji Baba a takaice ya amsa masa gaisuwar batare da yako nuna kulawa ba, shi da kansa ya sani shi mai laifi ne a wurin Alhajin dan haka bai damu ba, so yake su ke6e ya samu daman da zai 'kara neman afuwar su.

Bai samu ya shiga cikin gida ba sai da yamma lis wannan ma Safwan ne ya matsa masa akan su shiga ya watsa ruwa ya canza kaya, haka ya shiga ya watsa ya canza wasu kayan sannan ya fito suka yi sallar maghrib da Isha'i...fuksar sa fayau jin kansa yake yi kamar bashi ba, sam baya jin wani nauyi tattare da jikin sa, illah 'kafafun sa dake yi mai nauyi.

Cikin gida suka koma wanda sai a lokacin ya shiga ya gaida su Ammi, itama 'din babu yabo babu fallasa ta amsa shi, haka ma Nuree, abin kuma sai ya fara sashi yana jin wani iri, me yasa bazasu tausaya masa ba ko dan rasa Baby da yayi? Antyn sa Zainab ita ka'dai ce ta amsa masa gaisuwa da tausa sashshiyar murya har ta 'kara da kwanatr masa da hankali... haka ya tashi sum-sum ya fita yana jin babu da'di cikin ransa, itama Anty Zainab in may be da tasan halin da ake ciki yasan da 'kyar ne idan zata kula shi..

Wahshegari akayi sadakan uku da bakwai aranar kuma Alhaji Baba suka koma gida shi da wa'danda suka zo daga Shuwarin gaisuwa..wanda kafin tafiyar sa sai da ya bawa Ammi umarnin ta tafi masa da 'yar sa bai amince Noor ta 'kara ko da kwana guda ba ne  tare yake so su koma gida.

Ammi jinjina kai kawai tayi bata sanar da kowa batun Alhajin ba kawai ta ri'ke cikin ranta, dama ko be fa'da ba bata da niyyan sake barin Noor zama tare da Deen yanzu.

Duk mazan sun tafi Illah 'yan biyun Ammi suka rage.
Gidan sai ya zama daga ni, Ammi, Anty Zainab, Ummah ta sai Addah Maryam da suka daga baya.

'Yan biyun Ammi ma washegari suka koma dayake suna makaranta ne dama daga can suka taho...Ummah ta ma ranar da su 'yan biyu suka tafi a ranar su Ummah ta ma suka koma wanda da kuka muka rabu rabu da su, Ummah ta na ta yi min nasiha akan tawakkali, ita kanta cikin idanun ta idan ka kalla damuwa ce fal, tausayi na take ji sosai.
    Dan ma har suk koma basu ji labarin abinda ya faru ba, an dai sanar da su gaskiyan case in Baby  wanda hakan ne yasa Ummah ta tsanannin tausayi na, shiyasa ma take min nasiha da tawakkali a ganin ta Allah ya jarabce mi da auren mutun irin Yah Deen, dan kowa idan yaji abinda ya samu Baby ya kuma san asalin waye Mu'een cewa yake yi sakayya ce kawai Allah ya nuna masa ba komai ba.
Shiyasa da dama ke tausayi na.

Anty ma da farko bata san ainahin abinda ya faru ba ita dai kawai jimamin rasa Baby ne yafi damun ta dan sosai rasuwar Baby ya ta6a ta.

Kuma Ammi bata sanar da ita saboda taga hankalin ta atashe yake sosai, duk sai ranar da ta sanar da su Ummah ta kafin itama taji abinda ya faru.







Comment
Vote
Share




*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *80*

Rungume ni tayi tana hawaye, Anty yanzu ko dogon magana bata iya yi, ko ina ka ganta shiru zaka ganta a zaune tana tunani, sosai take jin mutuwar Baby cikin ranta.

Sati guda naji Ammi na fa'din zasu yi kafin su koma, dan haka tun daga lokacin nima na fara kimtsa kaya na a 6oye batare da na bari sun sani sani ba, tunani idan su ka san niyyata 'kila su dakatar da ni d wannan kalmar ta ha'kuri, ni kuwa a yanzun sam bazan iya ba na riga na yanke abinda nake ganin ya fimin.

  Ana gobe su Ammi zasu tafi na je na bu'de akwati guda ina jera kaya na,  'ko'karin zugewa nake yi sai ga Anty Zainab ta shigo ta same ni.
Da mamaki ta tsura min idanu tana kallo na dan ita bata san dalilin da zai sani shirya kaya ba.

Tambaya ta tayi" Me zakiyi da kaya har haka kuma?" Ina tayi maganar da alamun mamaki 'karara kan fuskar ta.

Tun lokacin da naji motsin shigowan ta sau 'daya tak na 'daga idanu na na kalle ta daga hakan ban sake ba, sai ma na fara jin hawaye na taruwa min.

Ko yanzun ma da tayi min tambayar ban 'daga kaina na dube ta ba nace" Gida zan koma Anty...tare zamu tafi da ku...".
Na 'karasa maganar da muryar kuka.

Shiru Anty Zainab tayi tana duba na jikin ta sanyi 'kalau a hankali ta mi'ke ta fita, bansan me taje ta gayawa Ammi ba sai ganin ta nayi ta shigo bayan fitan Anty Zainab bada jimawa ba.
Lokacin har na gama harha'da kayan ina tattare kayan dake kan mirror na.

Sunana Ammi ta 'kira da raunanniyar murya sai na waigo na dube ta batare da na amsa ba, 'lasa nayi da idanu na kawai wanda take naji zuciya ya fara dukan uku-uku, Addu'a nake a raina Allah yasa Ammi kar ta hanani barin wannan gidan, a hankali na 'karasa gaban ta na dur'kusa tuni idanu na sun cika da hawaye, 'kasa nayi da kaina batarexda iya duban fuskar ta ba, hawayen da suka taru min ne suka yi saurin gangarowa na kai hannu na share su, duk abinda nake yi Ammi bina kawai take da idanu bata cecda ni 'kala ba.
Hawaye na ne suka dinga gudu akai-akai ina share su na fara ro'kon ta" Dan girman Allah kar ki hanani tafiya tare da ku, Ammi ban jin zan iya sake rayuwa a garin nan  kar ki dakatar da ni dan Allah.
Ammi ban ta6a neman wani abu na rasa ba tun tasowa ta saboda baki rage ni da komai ba girma na har kuwa yau 'din nan Ammi nasan kin wadata ni da komai, amma yau ka'dai ina neman alfarmar ki Ammi, yau ka'dai ina ro'kon ki  ba wai dan kin kasa ba sai dan ki cika min buri na kawai dan Allah ki barni in tafi.
Wallahi Ammi bazan iya sake rayuwa inyi farin ciki ba matu'kar ina tare da Yah Deen...ban tsane shi ba amma na tsani rayuwa ta tare da shi, na tsani in sake gani na 'kar'kashin inuwar gidan sa, idan nace zanci gaba da zama anan wata'kila nima gawata zaki zo ki tarar Ammi...dan girman Allah badan ni ba ba dan bana son Yah Deen ba ki ce ya sake ni..Ammi".

Kuka sosai ne ya ci 'karfin ta ta kwantar da kanta kan 'kafafun Ammin tana kuka sosai.

Ita kanta Ammin ji tayi zuciyar ta ya karye sosai, ha'kika ha'kurin ta ya kai ma'kura tunda har ta iya bu'dan baki ta sanar da ita abinda ke ranta, a hankali Ammi ta dur'kusa sannan ta 'dagota ta rungume ta ajikin ta tana bata ha'kuri tace" Daina kuka kina damun kanki...da kaina ma ko baki ro'ke ni ba ba iya tafiya zan yi in sake barin ki tare da shi ba, shakka nake ji kar ki 'ki amincewa shiyasa na kasa fa'da miki amma ni na riga na yanke hukuncin raba shi da ke....domin hankali na zai fi kwanciya idan nasan cewa baki tare da auren sa, ha'kurin da kika yi masa abaya ma ka'dai ya isa bana fatan ki sake kwatanta irin wannan zaman har abada, tsananin tausayin ki ke hana ni magana 'yata shekarun ki sunyi ka'dan da wa'dannan abubuwan..."

Da haka ta ringa lallashi na har ta samu nayi shiru yayin da tsananin farin ciki ya lullu6e ni jin cewar Ammi na ma ta amince da tafiya ta.

Har sallar Isha'i a 'daki na muka yi shi ni da Ammi, da kanta ta nemo Biro da Memo ta ajiye akan side drawer sannan ta 'daga wayar ta ta 'kira Yah Deen..fuskar ta ka'dai idan ka kalla zaka san ranta 6ace yake da shi.

Daga can 6angaren da yake ba 'karamin da'di yaji ba

Please Login or Register in order to submit comment