Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Baba shine matsayin wakilin amarya yayin da Uncle Ja'afar ya wakilci ango...abin mamaki kuwa sai ya fahimci aure na da Yah Deen 'din yafi kwantawa Alhaji Baba arai fiye da wanda aka so yi a farko.

Ya fahimci hakan ne lokacin da Alhaji Baba yazo gaban sa ya rin'ka zuba masa godiya kamar wanda yayi masa wani gagarumin abu...tun a wurin ma ya fara bayyana masa abinda shi bai ta6a sani ba, wato soyayyar Deen ga Marigayiya Nannen mu...a lokacin ba 'karamin mamaki yayi ba da yaji wannan labarin sai dai ya fahimci komai Allah ne da shi kuma shike tsara komai...shiyasa ya yi sanadin ha'duwar aure tsakani na da Deen,ย  kenan dama can ba Nanne bace matar sa ni 'din ce...tun daga ranar ya san cewa aure na Da Yah Deen ha'din Allah ne.

Alhajin da kansa ya nemi a rufe zancen saboda wani dalilin sa a lokacin yace da kansa zai bayyana idan yaga dacewar lokacin....wannan dalilin ne ya sa ba kowa yaji zancen ba har yanzu...sai dai duk da haka 'yan bani na iya na nan ma'kale suna juya zancen.

Yace kwatsam yana zaune sai yaga ana ta 'kiran sa awaya ana sanar da shi abinda ke faruwa...da farko ma bai yadda ba amma daga baya daya da yaga kusan mutane hu'du sun 'kira shi da batun kuma iri 'daya sai jikin sa yayi sanyi gankalin sa ya fara tashi, daga 'karshe ma kashe wayar sa yayi na tsawon kwanaki biyu yana nazari kan lamarin.

Yace yasan wasu daga ciki ba wai haka kawai suke 'kira dan su sanar da shi ba, ya fahimci harda munafukai masu nuna cewa kwa'dayin su yayi kai harda 'kafafu tunda gashi halin yaron ya bayyana a fili kowa ya sani...ransa ya 6aci sosai amma duk da haka bai ga wata mafita ba illah ya nemi a mi'ka ni 'dakin mijina wata'kila hakan ka'dai shine mafita shiyasa ya yanke wannan hukuncin.

Yace da ace ma wani daban da bai sani ba ne da babu yadda za'ayi bayan sanin mummunan halayyar sa still ya sake 'daukan aure ya bashi...amma Alhaji Baba yafi 'karfin haka a wurin sa darajar sa kuma Muhamnad ya ci saboda karamcin sa a wurin jama'ah da kuma mahalicci...yace Allah ne ka'dai shaidar sa kan haka bai ta6a yin niyya ko aikata wani abu saboda kwa'dayi ko son abin hannun su ba duk da yasan ba kowa ne zai fahimci hakan ba amma Allah ya sani... yana so kuma nima inyi ha'kuri...inyi ha'kuri inyi masa biyayya..in zauna da mijina lafiya yace duk abinda zai faru tsakanin mu kafin in kai 'karar sa wurin wani in fara kaiwa wurin mahalicci saboda shine babban gata na...Allah ya sani shi kansa a yanzu ba son zama na da yaron yake ba dayake lokacin da ya bada auren bai san cewa haka halayyar sa take ba sai daga baya, so ba yadda zaiyi domin raba aure bashi ne mafita ba...ya yi tawakalli ne kawai saboda Allah kuma fatan sa Allah ya dubi niyyar sa...idan ya so sai yasa sanadin aurena da shi ya shirya shi ya daina abinda yake yi...Addu'ar saxgare mu kawai itace ubangiji Allah ya bamu zaman lafiya ya saka fahimta tsakanin mu....".

Ni kam kuka nake yi sosai har ban iya amsa addu'ar da yai 'din ba shi kansa Baban mu jikin sa sanyi yayi daga yanayin muryar sa zaka fahimci damuwar da yake ciki.

Ummah ta da kanta ta ringa lallashi na har nayi shiru bacci ya 'dauke ni ajikin ta...tausayi na take ji amma babu yadda zatayi, ita dai bata san me zata je da su Ammi ba...duk abin nan tarasa matsayin da ya kamata ta bashi..shin so ne ko kuwa...ta wani fannin akwai wani haske tattare da kasancewar mu tare da su amma wani 6angaren sai dai ace Alhamdulillah kawai...sau tari ta kan hango tsagwaron son kai cikin lamarin su amma sam hakan baya bayyana kansa a fili 'kauna ta zahiri kan lullu6e komai...dan duk abinda ke faruwa da tsigar zallar so suke bayyanuwa..ji take
da tana da iko da bazata ta6a yadda da batun zama na da Mu'een ba amma babu yadda zatayi ha'kurin nan dai sai addu'ah kuma....fatan taย  Allah Ubangiji ya shirya shi yasa Hudah ta kasance Haske cikin rayuwar sa".


Ana gobe zan koma gidan Ammi aka kawo kayan lefen aure na akwati set biyu masu kyau da 'daukan hankali, ni kam ma ko kallo kayan ba su ishe ni ba inaji anata zuzuta kyan kayan da kuma yada habaicin wai _dama haka ake so kuma an samu_ inji mutane...Babu wanda ya tanka su haka kowa yazo zai gani ya fita da maganar kayan a bakin sa.





Comment
Vote
Share






*Salmerh ce* ๐Ÿ˜

๐Ÿ’• *NOORUL* ๐Ÿ’•
ย  ย  ย  (Haske nah)


By
*Salmerh MD*
ย 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


๐Ÿ’ซ *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
๐Ÿ’ซ
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

๐Ÿ’•๐Ÿ’• ~*This page is 4u Dear Zainab Kabir Ingawa...Alkhairin Allah ya kai mk duk inda kike...nagode sosai da 'kaunar ki gare ni.*~๐Ÿ’•๐Ÿ’•


*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*


๐Ÿ…ฟ *59*


Addah ta Maryam ma tazo da wasu 'yan uwan mu a hakan ma abin yazo ne cikin lokaci 'kan'kani amma duk da haka ba laifi gidan mu ya tara jama'ah ka'dan.

Itama Addah Maryam tayi mamakin faruwar lamarin yanda yazo agaggauce, ta yi 'ko'karin ganin ta samu cikakken bayani daga bakin Ummahn mu amma hakan bai samu ba, sai da suka zauna da Addah Saudah shine tayi mata bayani gamsashshe a fahimtar ta, tace Baban mu ne ya matsa akan dole sai an kai ni 'dakin na saboda labari ya iske shi cewa Mijinnawa shine ke da alhakin cikin dake jikin Ma'u 'yar gidan malam Barau shiyasa Baban mu yace agaggauta kai masa matar sa a tunanin sa ko laifin nasu ne da tun farko ba su bashi matar sa ba suka bar ya a gida..inda ta 'kara da fa'din ni.nama yi mamaki wallahi ban zaci Baban mu zai kuma amincewa da zaman Hudah tare da yaron ba bayan jin abinda ya faru sai ga shi da kansa kuma yayi umarni da akaita gidan sa batare da ya koyi tunanin me hakan zai haifar ba".

Baki kawai Addah Maryam ta ta6e tare da kawar da kanta gefe bata iya ta furta komai ba, sai dai har cikin ranta bata ji da'din maganar ba sam...aganin ta ba haka ya dace ayi ba..kamata yayi a bar Hudahn agida tukunna inma ba zasu iya raba auren ba har sai an tabbatar da shiryuwar sa kafin abrta zama dashi baya ga haka taya za'ayi a 'dauki yarinya 'karama kamar ni abawa mutumin da bai san ciwon kansa ba Baban mu yana nufin bai damu da abinda ya farun bane ko me? ..taso su tattauna maganar da Ummahn mu amma bata samu fuska ba hakan yasa dole ta ha'kura tayi shiru da bakin ta.

Ana gobe za'a kaini gidan Yah Deen Saif yazo gidan mu shi ka'dai hr naso ma nayi msmskin ganinsa shi ka'dai 'din amma sanin ba'kin hali irin na Zaidu yasa mamaki na ya kau ...y Saif yasha Jumpa milk colour da hula kamar wani babba, fuskar sa fayau sai 'dan 'kasumba da ya fara tarawa, yayi kyau sosai abin sa...a 'dakin Baban mu aka masa masau'ki inda aka yi 'kirana bayan sun gama gaisuwa da Ummahn mu.


Jin cewa Saif necyazo ya sani tahowa cikin tsananin farin ciki, jiki na da doguwar rigar material sai 'dan 'karamin ba'kin mayafi da na yane kaina da shi...fuska ta da fara'a muka gaisa da shi na tambayi su Ammi da Zaidu..yace min lafiyan su qalau.

" Meya sameka kai in kuma?"
Na tambaye shi ina kallon fuskar sa.
Take ya amsa ni shima da tambayar" Me kika gani?"
Nace" Kamar baka da lafiya".
Yace" Ni lafiya ta qalau".
Ya 'karashe maganar yana suman shafo kansa.

Shiru nayi ban kuma fa'din komai ba cikin rains nake tunanin abinda zai iya sashi canzawa haka cikin sau'ki dan nasan Saif ba haka yake ba...tashin farko tunanin na kan Yah Deen ya sau'ka cuz a sani na shi ka'dai ne ke takurawa su Saif a gidan..baki na ta6e cikin raina nake fa'din" Har yanxu ba zai canza hali ba".

Lallen dake zane a hannu na naga yana kallo ban damu ba sai ma nayi murmushi da fara'a ta nace 'dazu da safe aka zana min yayi kyau ko?..har an min kitso ma 'kanana zafi ma kaina yake min har yanzu".

Ido ya tsura min yana kallon fuska ta kamar wanda ke son gano wani abin acikin idanu na....Nima 'din sai nayi shiru ban kuma cewa komai ba.

Cikin sanyi ya ambaci sunana sai na amsa nima a hankali jin yanda yanayin muryar sa ya koma.
Yace
" Hudah dagaske Yah Deen mijinki ne yanzu?"

" Nima haka naji an fa'da...amma bansan lokacin da akayi auren ba".
Na bashi.masa bayan yanayi na na canza izuwa na damuwa.

Idanu ya lumshe tare da yin 'kasa da kansa hannun sa cikin gashin kansa, kamar an tsikare shi kuma sai naga ya mi'ke tsaye hannun sa ri'ke da hular sa yana duba agogon dake 'daure a tsintsiyar hannun sa yake ce min" Zan tafi gida...dama nazo ne kawai in dan ganki inga matar Yaya na".
Yayi maganar yana me 'ka'kalo murmushi.

" To bazaka tsaya in kawo maka ko ruwa ba?"
Na fa'di ina mi'kewa tsaye da hanzari na.

'Daga idanu yayi ya kalle ni, sai da ya juya ya fara tafiya sannan ya furta..." Karki damu Matar Yayah.. am ok.."

Biyo shi nayi abaya ina 'kun'kunin sunan da yake 'kira na da shi, a fili kuwa cewa nayi" Sai nagaya ka da Ammi tunda ka'ki zama ka ci komai".

Murmushi yayi ta'kaitacce sannan ya waigo idanun sa yasa cikin nawa idanun yana murmushi yace" Idan naje gidan ki ai zan ci".

Dajin haka sai na fara buga 'kafafu na a 'kasa tare da tura baki.na gaba...zan yi magana yayi saurin tara na da fa'din" Common..me hakan kuma...ke fa yanzu kin girma...gobe-gobe za'a kaiki 'dakin mijin ki ko so kike ace yarinyar Ammi shagwa6a66iyace".

Daina abinda nake yi na cigaba da kallon sa..sai ya juyo da kyau ya fuskance ni gira ya 'dage sama sannan yace"ย  Kinsan me nake so dake 'yar gidan Ammi?"

Kai na girgiza alamar a a sai yace" Ha'kuri zakiyi...ai nasan kinsan halin Yah Deen da kyau ko?"
Wannan karon kam shiru nayi ina mai cigaba da kallon sa.
" Kiyi ha'kuri ki zauna lafiya da mijin ki kinji?...kuma nayi al'kawari kullum zan rin'ka taya ki Addu'ar Allah ubangiji Kar ya bashi ikon cutar mana dake kuma ya daidaita miki hankalin sa...ko baki so?"

Ban bashi amsa ba still nayi shiru ina jin yanda cikin idanu na ke tsatstsafo da ruwa ...Saif sai yayi murmushi ka'dan sannan ya cigaba da fa'din" Kar kiyi min kuka ni...ai nasan kina so ko...to ubangiji Allah ya baki ha'kurin zama da shi...Allah ya baku zaman lafiya ya sanya muku albarka cikin auran ku..ki kwantar da hankalin ki insha Allahu bazaki yi danasanin auren Yayah ba".

Daga haka ya juya tare da sanya hular sa akansa ya fita batare da ya jira jin amsar da zan bashi ba...yana saka takalmin sa ya ke sake fa'din kice da Ummah na wuce kawai dan naga tana cikin hidima kar mu raba mata hankali".

Ganin dagaske tafiyar zaiyi ya sani saurin fa'din"ย  Ka gaida min Ammi na" Abinda kawai na iya fa'di kenan ban kuma san dalili ba sai naji zuciya ta gaba 'daya ta karaya kafinvna ankara sai jin idanu na nayi suna tsiyayar da hawaye.


Saif bai sake yadda mun ha'da idanu ba yayi gaba abinsa, har ya 'karasa fita daga gidan kuwa ban kuma cewa komai ba illah bin bayan sa da na tsaya yi da kallo ina tsaye daga bakin 'kofa ina share hawaye na.


Saif yaro ne ba wani babba ba amma yana da nagartar da idan ka zauna da shi sai ya birke ka..wani lokaci har zaka iya mantawa da 'karancin shekarun sa, musamman ma idan magana ta fahimta ta ha'da ka da shi...ko cikin yaran Alhaji Baba Saif ne wanda yafi jin natsuwa da shi sosai...da suke je boarding school 'dinnan ma sai abin nasa ya 'karu, halin girma da mutuntaka duk suka shige shi ga su dama akwai jikin girma ba laifi.


Ni dai 'dan maganar nan da muka yi da shi sai naji wani iri tamkar wanda akace min daga yau 'din bazan sake ganin su ba...tun daga yanzu har na fara missing presence na su..hakan yasa na koma cikin 'dakin Baban mu na kwanta na dinga rizgar kuka na wanda babu mai lallashi na...da 'kyar na samu kukan ya tafi har bacci 6arawo ya sace ni.





*****
ย ย  Washe gari da yamma aka zo aka tafi dani gidan Ammi..bayan an min kwalliya ta na gani a bada labari...ko kafin atafi da ni sai da aka ha'da ni da Baban mu awaya ya sake kwantar min da hankali gami da nasihar ha'kuri da kuma kawar da kai...duk wannan abin bai sa na sake zubda hawaye na ba...har sai da mukaje gidan Ammi aka ha'da ni da Yah Deen wuri guda lokacin bayan sallar Isha'i ne, Alhaji Baba da kansa ya zauna yayi mana Nasiha mai shiga jiki tun anan nafara kuka na harda shashshe'ka cus yanzu na fahimci kowa nasihar zama da Yah Deen yake min...kenan dagaske daga yau zama tare da shi zan koma yi...kamar yadda Saif ma ya fa'di.

Ammi ce ta fitar dani rungume ajikin ta bayan Alhaji Baba ya sallame mu sai ta wuce dani 'dakin ta muka bar Yah Deen ka'dai da Alhaji Baba, bansan me suka tattauna tsakanin su ba amma sun shafe a'kalla kusan mintina ashirin suna tare da shi.

Nima 'din Ammi lallashi na take yi a 'dakin ta tana sake lalla6ani yayinvda nake mata shagwa6ar ni bana son zama da shi tace kar akaini gidan sa...Ammi kam lalla6ani ta ringa yi da kalamai masu da'di har na rage kukan da nake yi, cikin hakan tasa na 'daukan mata al'kawarin duk abinda yamin wanda banji da'din sa ba ko kuma na cutarwa bazan 6oye mata ba...tace in kwantar da hankali na insha Allahu bazata ta6a bari ya cutar da ni ba matu'kar numfashin ta na aiki...ni dai kawai in masa biyayya matsayin sa na miji na kar na raina shi...saboda shine tsanin aljannah ta daga yanzu....tace aure na dashi ya riga ya zama rubutaccen 'kaddara ne baya ga da ko ita da kanta bazata ta6a bari hakan ta kasance ba...sai dai yanzu kam babu yadda zatayi tunda ba'a jayayya da yin ubangiji kuma shi yasan dalilin faruwar komai...tace min idan na kwantar da hankali na na zauna dakanta zata sa ya siya min waya mai kyau wanda zan na 'kiranta kullum muna gaisawa.."

Jin hakan da ta fa'di ne ma ya 'dan sanyayar min da hankali na har na kwantar da kaina kan cinyar ta ina maida numfashi yayin da ta ringa shafa min kaina tana sake lalla6a ni.

" Ammi" na 'kira sunan ta a hankali.
Sai ta amsani tare da bada hankalin ta gare ni..
Nace " Banga su Saif ba Ammi.."
Tace
" Kar ki damu zaki gansu ai uwata har gidan ki zasu je su gaida ki kinji?"

" To"..nace 'kasan ma'koshi na ina sake tunanin rabuwar mu da Saif ta jiya.

'Karfe tara da 'yan mintina aka tafi dani gidan Yah Deen da sunan gidan aure na, bansan me yasa ba amma sai na kasa tsaida hawaye na...sanda za'a shigar dani gidan kuwa fargaba ce ta shige ni mai tsanani musamman saboda sanin halin sa da nayi hakan yasa kuka na ya tsananta.

Gashi babu wanda zai kwana tare dani dan haka koda suka kawo nin ma basu zauna ba shiga suka yi suka lalle'ka cikin gidan sannan daga bisani suka dawo nan kuma suka fara niyyar tafiya, nan kuka kuwa naji hankali na ya tashi sosai...tunanina ta yanda zan iya zama tare da shi a gida 'daya.

Addah ta Maryam na rungume ina ro'kon ta kar ta tafi ta barni tsoro nake ji..haka ta dinga yimin nasiha tana sake tuna min kalaman Baban mu da Ummah ta...still ban sake ta ba na cigaba da kuka na..wayo tamin tace in bari ta tafi tunda dare yayi yanzu amma gobe insha Allahu da sassafe zata dawo mu yini.
Nace mata ni tsoro nake ji ni ka'dai dan Allah kar ta barni..sai tace min to bari ta dubo Mu'een idan baya nan sai ta kulle 'kofa ta dawo...da jin haka sai na sake ta ina share hawaye na.

Daga haka ban kuma jin motsin ta ba.

Allah ma ta taimake ni dan tamkar ha'din baki da fitar su basu jima ba sai ga shi shima ya shigo gidan da farko ma da naji motsin 'kofa nayi tunanin ko Addah Maryam 'din ce..but jin sallamar sa da nayi wanda yayi ta daga bakin parlour 'kasa-'kasa tamkar ma bazaiyi ba hakan ne ya sani fahimtar shine.

Ai kuwa ban ko amsa ba na cigaba da kuka na..sai ma ganin san ya sake tada tsimin kukan nawa na fara yi tamkar an doke ni ne.

'Karamin tsaki yaja da jin irin kukan da nake yi...ko kulani bai yi ba balle in saka ran ya san da zama na, abin hannun sa ya ajiye kan center table dake tsakiyar parlourn daga haka ya sa kai ya wucewar sa ciki.


Tsawon mintina kusan biyar sannan na sake jin muryar sa daga baya na a tsawace yace " Ki min shiru...".

Yi nayi kamar banji ba na cigaba da kuka na ina share hawaye...'dan takowa yayi ka'dan yana sake ha'de fuska yace " Wallahi 6allaki zanyi idan kika dame ni banson hauka ni".

Ji da ganin hakan ne yasani saurin mi'kewa tsaye ina yarfa hannuwa na cikin kukan nake fa'din" Ni dai Ammi na.."
Tsakani na da Allah nake bu'katar komawa wurin Ammi har zuciya ta...yaushe zan zauna da mutumin da ko dariyar kirki ma zan iya irga sau nawa naga yayi ta tsawon zama na a gidan su..kwatsam kawai ace yau gani ga shi matsayin ma'aurata.
Da wani tsawan naji ya sake fa'din
" Dan ubanki na 'daure ki ne ko ni ne na kawo ki gidan da zaki dame ni?"

Dalili guda biyu kacal ne suka hana ni nufan hanyan fita saboda nasan already ya rufe 'kofar bayan da ya shigo, sannan kuma nasan a lokacin dare yayi, wa'dannan dalilan ne suka sanya ni cigaba da rera kuka na kawai batare da na nufi hanyar waje ba.

Tsaki yaja sannan ya sake komawa ciki...da shigar shi sai ya rage kayan jikin sa cikin hanzari dan duk ji yayi ransa ya 6aci, bayi ya shiga sai dai bai jima ba ya sake fitowa.


Da yake lokacin da za'a kawo kaya na kaf aka fitar da kayan sa a gidan aka kai gidan Alhaji Babaย  so bashi da ko da kayan bacci ne yanzu anan dan haka kawai sai ya zauna da boxern dake jikin sa da nufin bacci da shi.

A hakan kuma ya dawo parlour inda nake da yake ya saba da zama hakan tun asali.

'Bangare na kuwa a lokacin na daina kuka sai dai ajiyan numfashi zaune nake kan gwiwoyina nake a 'kasan parlour sai faman murzan idanu kawai nake yi...a haka naga ya fito ya nufo inda nake.

Da ganin sa hakan sai nayi 'kasa da kaina tare daย  saurin rintse idanu na cuz ni baya ga shi ban ta6a ganin wani namiji cikin irin wannan yanayin ba...cikin raina nake mitar halin sa.

Yanda zuciya ta ke harbawa ya sanya nake jin wani sabon tsoron sa na sake kamani da ban na menene ba...daga nesa dani ka'dan ya zauna yana sake ha'de ransa cikin ba'kin hali ya ce..." Kin yi sallah ne?" Da sauri na 'dage masa kaina alamar " Erh" ...sai yace " Abinci fa?"
Nace " Naci" Still idanu na a rufe.

" To maza ki tashi ki je ki kwanta banson sake jin wata rigima kuma in ba haka ba zane ki zanyi...".

Daga fa'din hakan ya tashi ya koma ciki ya bar ni zaune a wurin kamar yadda ya samo ni.

Sai da na tabbatar ya fita sannan na bu'de idanu na ina sake kallon inda ya tashi.

Baki na ta6e na kawar da kaina gefe...na 'dauki a'kalla kimanin mintina sha uku kafin na mi'ke na cire mayafi da 'dan kwalin kaina nayi kwanciya ta kan doguwar kujera






Comment
Vote
Share











*Salmerh ce* ๐Ÿ˜

๐Ÿ’• *NOORUL* ๐Ÿ’•
ย  ย  ย  (Haske nah)


By
*Salmerh MD*
ย 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


๐Ÿ’ซ *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
๐Ÿ’ซ
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

๐Ÿ…ฟ *60*


Baki na ta6e na na kawar da kaina gefe....na 'dauki a 'kalla kimanin kusan mintina sha uku kafin na mi'ke, mayafi da 'dankwalin da ke kaina na cire daga nan nayi kwanciya ta kan doguwar kujera.

Take kuwa bacci yayi awon gaba da ni....Yah Deen ma bai sake bi ta kaina ba har sai da gari ya waye bayan ya 'dauro alwala sannan yazo ya tashe ni inda ya bubbuba 'kafafuna yana fa'din" Ke..."
Firgigi na tashi na zauna ina ha'de raina cuz ni ban saba da irin wannan tashin ba..Ammi na ba haka take tashi na daga bacci ba.

Tuno cewa wai yanzu da shi zan zauna a gidan ya sani na sake jin wani iri har cikin zuciya ta..bansan ranar da zan saba da Yah Deen ba ni.kam a rayuwa ta.
" Ta shi kije kiyi sallah?"
Abinda kawai yace dani kenan sannan ya juya ya koma ciki.

Ko motsawa ban yi ba daga inda ya bar ni har ya idar da tasa sallar ya kuma fitowa ina nan na takure wuri guda tamkar almajira abin a tausaya min.

Ga shi fitsari nake ji sosai kuma na kasa zuwa inyi saboda fargaba...tamkar daga sama naji muryar sa akaina yana sake fa'din" Har kinyi sallar ne?"
Saurin girgiza kaina nayi ina sake matse fitsarin da ke damuna.
" Lokacin kuma jiran ki yake yi ko?.."
Ya sake fa'da daga inda yake tsaye.

Ban san me zan ce da shi ba dan haka sai na 'dan waigo ka'dan na kalle shi, tsaye yake ya ri'ke labile a hannun sa daga bakin 'kofar shiga cikin, fuskar sa ba yabo ba fallasa amma ban wani tsaya na 'kareย  masa kallo ba na kawar da kaina cikin raina nake 'kun'kunin" ta ina zan wuce to bayan ka tare hanyar"..

Tsaye na mi'ke hannu na ri'ke da shirgin kaya na mayafi da 'dan kwali na...shahada kawai nayiย  na nufi bakin 'kofan bedroom 'din cikin sanyin jiki kaina a 'kasa...nasan duk tsiya ai idan anzo zai matsa in shiga.

Tsaki ya ja guntu sannan ya saki labilen ganin na tunkaro sa...nasan bai wuci yayi tunanin zamana da shi zqi takura masa ba shiyasa naga ya wuce ni a 'dan fusace ya 'karasa shiga cikin parlourn batare da ya ko sake kallon inda nake ba.


Yayin da ni kuwa hakan shi yafi komai yimin da'di cuz dan da ganin ya bar bakin 'kofan nayi saurin shigewa ciki, da yake dama ri'ke nake da fitsari...ai su mayafin ma duk watsasu nayi kan bed nayi saurin shigewa bathroom.


Ko da na fito rasa yadda zanyi nayi sallar nayi, gashi sai da na tsaya na watsa ruwa ban kuma son maida kayan da na cire cuz suna da nauyi, gashi ba wasu ban san kayan da zan saka ba a wannan lokacin.

Tsaye nayi ina tunani gami da kalle-kalle cikin 'dakin tamkar zanyi kuka 'kasa-'kasa nace" Waiyo Ammi na dan Allah kizo ki tafi dani...wardrobe na nufa duk da banda tabbacin samun abinda zai min amma sai naji raina ya kwanta da in bu'de 'din, kamar wasa kuwa da na duba sai naga kaya ne jere aciki.

Duk da bansan na wanene ba amma take sai naji farin ciki ya lullu6e ni, abaya ba'ka na ciro na sanya tare da Hijab babba pitch colour da na gani shima cikin kayan rigar kuwa daidai tsayi na tayi min dai-dai, daga haka na wuce kn dadduma na tada sallah ta.


Har na idar na zauna kan daddumar ina karanto Azkar 'din da muka saba yi da Ammi har a lokacin kuma Yah Deen bai dawo 'dakin ba...sai dai banyi mamaki ba cuz daga inda nake zaune ina iya jiyo sautin T.V na tashi nasan babu mamaki abinda ya 'dauki hankalin sa kenan.

Na 'dauki a'kalla kusan mintina ashirin zaune a wurin kafin na mi'ke izuwa parlourn dan na gaida shi.


Kishingi'de na same shi 'kafafun sar'ke da juna 'daya kan 'daya yayin da ya 'dago su saman kujeran yayi musu masau'ki, hannun sa

Please Login or Register in order to submit comment