Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta zubawa sai da imrana ya riga ta isa abinku da namiji ga shi da dogon 'kafa.

'Kafar Ma'u kam duk tayi futu-futu da ita ga zufa shar'kaf, kwalliyar da tayi ma duk ta dame ta kwa6e mata a fuska kaca-kaca ta koma wata iri da yake da yawa ta shafa powdern gasu jan lipstick da sauran su.

kallo Imrana ya 'kare mata daga sama zuwa 'kasa sannan yace" Kina jina ko?"
Sai ta 'dage kanta sama.
Yace ciro 'dan kwalin kinnan ki goge fuskar ki, shi fa Deeni baya son mace mai yawan kwalliya..."
Ya fa'di hakan ne saboda ganin da yayi kwalliyar tata ta fita a hayyacin ta, kuma yasan matu'kar Deeni ya ganta cikin wannan yanayin ba zai amince da ita ba shiyasa yayi mata dabara.

Ma'u kuwa tana jin haka take sai ta fara goge fuskar ta, kafin kace Kobo har kwalliyar ta yi hanyar ta fuskar ta tayi fayau shine ya ringa nuna mata inda basu 'karasa goguwa ba duk ta goge su, take fuskar ta dawo dai-dai.

Duba mai kyau zaka yiwa Imran ka fahimcj murmushin mugunta yake yi, amma ga Ma'u da gankalin ta baj je can ba hakan sai ya sa bata fahimci komai game da shi ba, yana murmushin  yake fa'din" Yauwa koke fa 'yan mata, kinga ma kin fi kyau haka nan fiye da 'dazun.."

Murmushi Ma'u tayi yayin da Imran ya cigaba da fa'din" Idan mun shiga ciki ki natsu kinji, kuma ki tabbatar bakiyi masa gardama ba, duk abinda yace miki kiyi to kar kiyi masa musu sam baya son taurin kai shi ai ke da kanki kin sani ma ko? nima nan da nake abokin sa ai kinga bana yi masa wargi ko?"

Kai kawai ta 'daga sama alamar" Erh"
Duk da bata tabbatar da maganar tasa ba amma yanayin da tayi mata tambayar yasa she hv no choice than to ansawer him yes.

" Balle ma ke baki na son shi ba..?" Imrana ya sake tambayar ta.

Sai ta sake 'daga kanta sama kamar wawuya.
Sai yace" Kuma kema kina so ya so ki ya aure ki ko?"
Wannan karan kam ido ta zuba mishi tana kallon sa, sai da ya sake maimaita tambayar kafin ra bashi amsa da
" umm" 'kasan ma'koshi.

Sai yace
"Gud toh banda taurin kai, yau ranar ki ce yarinya kiji da'din ki kinji?"
" Uhumm"
Ta sake fa'di batare da tasan ainahin manufar sa kan fa'din hakan ba.

"Bismillah" yace tare da juyawa ya shiga gidan, a hankali ta 'daga 'kafafu ta bishi a baya suka shiga ciki.

Can cikin bedroom Deeni yake yana duba sake duba kayayyakin da Uncle ya 'din ka mai sai yaji sallamar Imrana.

Yana daga wurin ya amsa wanda hakan ya bawa Imrana damar 'karasawa ciki ya same shi, yana daga tsaye ya 'dage masa gira yana murmushi ya nuno parlour da babban 'dan yatsan sa yayin da sauran yatsun ya tan'kwashe su.

Yah Deen bai wani sha wahala fahimtar manufar sa ba dayake bai manta akan abinda suka rabu ba, dan haka sai ya mi'ke tsaye fuskar sa wasai saboda farin cikin da yake ciki na fasa auren sa da akayi da Husnah.

Murmushi ne ya bayyana kan fuskar sa yana kallon Imrana yace " Haba dagaske Imran ka kawo min?"

Kai ya jinijna masa tare da juyawa yake fa'din" Wancen ajiyar da kwanaki nake baka labarin nace, yarinyar na tsananin 'kaunar ka tun ba yau ba so ka more abinka, amma please kar ka yi abinda zai sa asirin mu ya tonu kasan wannan ba Husnah bace..ni zanje in dawo nan da 40mins".

Bai ce da shi komai ba har ya 'karasa fita illah bayan sa da yabi da kallo hannayen sa duk na ri'ke da 'kugun sa.

Dai-dai yaji 'karan rufe 'kofar parlour at sane time Ma'u ta bayyana bakin bedroom 'din sa idanun ta 'kasa, wanda shigowan nata ya samo asali ne daga umarnin da Imrana yayi mata kafin ya fita.


Taki uku tayi ta tsaya daga inda take tsayen bata 'karaso ba haka kuma bata 'daga kai ta kalle shi ba illah" Ina yini" da ta furta.

Yayin da Yah Deen ya dinga bin ta kallo kawai batare da ya amsa gaisuwar tata ba.

Sosai ganin ta gaban san ya sake tada masa tsimin sa, ya jima da mura'din yarinyar cikin ransa sai gashi yau Allah ya bashi dama har cikin gidan sa.

Kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya 'dan matsa baya ka'dan bayan ya cire hannayen sa daga 'kugun sa, da sanyin murya yace' 'Karaso mana ki zauna ko?"

Yayi maganar yana nuna mat bakin gadon sa.

Sai da ta kalle shi sai kuma ta kalli inda yake nuna matan, Mu'een kuwa 'dauke kabsa yayi tamkar ba shine yayi maganar ba kawai ya cigqba da abinda yake yi.


A hankali ta 'karasa ta zauna bakin gadon tana mai wasa 'yan yatsun hannun ta sam sai taji ta kasa sakewa..it kanta bata san me yasa take matu'kar son wannan mutumin ba.



Cigaba yayi da abinda yake yi, sai da ya kammala ya maida kayan mazaunin su bayan ya cire wanda yake son sanyawa ya ajiye gefe kafin ya dawo inda take.

Gefen ta ya zauna yana sakin sassanyar ajiyar zuciya.

" Ya sunanki?"
Ya tambaya yana kallon fuskar ta.
Kanta 'kasa tace" Ma'u".
" Miye kuma Ma'u? sunan ki Asma'u dai ko?"
'Kasan ma'koshi tace" Umm".
Sai yace" Gud!...kina sona wai dagaske?"
Ya tambaya still yana kallon ta.

Shiru tayi bata iya ta bashi amsa ba saboda kwarjinin da yake yi mata...Mu'een kam bai damu da shirun nata ba kawai ya cigaba da fa'din" Anyways..baki da matsala, ko da 'din ma bansani bane..amma kinga yanzu da na sani ai har aure na fasa saboda ke..fatan kin shiryawa jarrabawar da zan miki?"

Kai ta 'dage sama alamar " Erh".
Tsaye ya mi'ke sannan yace" Ki shiga ki watsa ruwa jikin ki..in kin fito zan gaya miki what is next".
Ya 'karashe da nuna mata bathroom 'din sa.

A tsare da furta hakan saboda baya son tayi masa gardama sam, ai kuwa sai ta 'daga kai ta kalle shi sannan tace " Nayi wanka a gida..."

Tun kam ma ta 'karasa yace" Banson musu ni..a haka ne zan aure kin?"

Tana jin haka ta mi'ke ta nufi bayin nasa kafin ta 'karasa shiga ne ya sake ce da ita" 5mins please ina jiran ki yanzu akwai inda zani".


Ranta fari 'kal ta shiga bayin, bata sha wani wahala wurin fahimtar yanda zata yi ba cuz akwai tap, taran ruwan tayi a bucket tayi wankan ta tasa ta maida kayan jikin ta sannan ta fito tana wani sussune kai 'kasa.

Ko da ta fito bata gansa cikin 'dakin ba danchaka sai ta koma inda ta tashi 'dazun ta sake zama tana rarraba idanu da tunanin jarabawar da yace zai mata...farin cikin ta bai wuce auren ta da yace zai yi ba.

Tana cikin tunanin taga ya dawo 'dakin direct inda take ya nufo yana binta da kallon sha'awa..." Kayan basa damun ki ne?"
abinda ya fara fa'di kenan lokacin da ya isa wurin ta.

Kai ta jijjiga masa alamar" a a basu damin ta.

Zama yayi daf da ita tare da 'dago 'kafar sa 'daya ya 'dora daga saman cinyoyin ta...cikin murya mai 'daukan hankali yace" Ni banson ganin ki da su to..ko baki son cin jarabawar tawa?"

Muryar ta na rawa dan jin abinda ya fa'di 'din ga kuma wani sabon al'amari da ta gani 'kafafun sa kan nata ba ta saba hakan ba shiyasa duk sai taji hankalin ta ya fara tashi, zuciyar ta na harbawa da sauri, amma duk da haka sai da tayi dauriyar amsa masa da fa'din" Ina..so".

Ido ya lumshe ya kuma bu'de su nan take sannan yace
" To ki nutsu..banson taurin kai kinji? Ni kaina ma inaso ki ci jarabawa ta saboda ki aure ni".
Yana maganar ne yana tafiyar da hannun sa kan fuskar ta zuwa saman wuyan ta..daga nan ya nufi bayan ta da shi..a hankali yake yawo da hannun nasa yana kuma bin cikin idanun ta da kallo.

Ba wani lokaci yake so ya 6ata da ita ba, abu biyu ne kawai burin sa game da ita, na farko burin sa yaga yayi tozali da Boobs 'din ta da suka da'de zane cikin zuciyar sa, yayin da burin sa na biyun ya kasance na matu'kar son jinsa cikin jikin ta ne.

Duk abinda yake yi mata Ma'u bata hana shi ba, zaton ta ko dagasken duk jarabawar ce hakan ma...idanu ta lumshe jikin ta na faman kakkarwa amma bata hana shi ba har lokacin da ta taji ya zuge mata zip 'din rigar ta baya lokacin ne tayi saurin bu'de idanun ta tare yun'kurin tashi tsaye cuz har yanzu a zaune take.

" Relax mana gani kawai zanyi".
Yayi maganar cike da bada umarni yana wani yatsina fuska tare da maida ta baya ya kwantar, take ya zare rigar tata yayi gefe da shi.

Hankalin Ma'u sosai ya tashi jin jikin ta babu komai, dama rigar ce kawaj ta sanya sa sai mayafin ta, ko bra bata fara sanyawa ba tukunna, wasu lokutan ne dai take amfani da vest in ta ga dama yau 'din kuwa bata sa ba sam.


Yanda ya haukace da ganin halittar jikin ta yasa ya kasa controlling kansa take ya fara yi mata wasu irin wasanni da bata ta6a sanin akwai su a rayuwar duniya ba.


Har ma sai ta ji bata damu ba wanda hakan yasa ta bashi dama sosai da jikin ta, bata tashi sanin jikin ta babu komai ba sai lokacin da taji zafi na ratsata lokacin ne ta ankara tayi saurin 'daga kanta dan ganin me ke faruwa nan ta ci karo da yanayib da jikin ta take, tana shirin bu'de baki tayi kuka Mu'een ya yi saurin danne bakin tare da maida kanta 'kasa ya hana ta motsi.

Ko da wasa bai gwada yin kissing 'din ta ba illah jikin ta da yayi ta sarrafawa son ransa batare da ko tsoron Allah ba ballantana yaji tausayin ta a hakan ya afka mata.


Ma'u kamar zata mutu haka take ji, gashi bata da bakin kuka illah hawayen ta dake zuba ta gefe da gefen idanun ta na azaba...'kwayar idanun ta ka'dai idan ka kalla zaka fahimci cewa tana cikin tashin hankali.


Sai da ya gama fitar da ita a hayyacin ta kafin ya 'kyaleta, taimako 'daya da Allah yayi masa kuma shine Ma'u irin matan nan ne masu 'kwari sam batayi masa langwami ba, ta dai sha kukan ta ta 'koshi taf, amma ko bayi da yace taje ta wanke jikin ta ma da kanta ta taka ta shiga.

Shi ya bata ruwan zafi tayi amfani da shi sannan ta fito yace ta shirya ta koma gida amma karta fa'dawa kowa abinda ya faru yace duk ranar da ya shirya auren ta da kansa zai zo gidan su ya sami mahaifinta".


Tana share hawaye ta fita saboda azaban da take ji cikin jikin ta...ko 'kafar ta ma nauyi sosai take mata kafin ta 'daga shi amma a hakan ta daure take tafiyar cikin hankali yanda bazai dameta sosai ba.


Ganin yanda take tafiya da dabara ne yasa Yah Deen tsaida ta kuma ma sai alokacin yayi wani tunani kan rashin amfani da tsarin da be yi ba kafin ya kusance ta, magani guda biyu ya 'dauko ya bata yace ta sha...Ma'u kam bata son ha'diyan magani dan haka data kar6a sai ta ri'ke cikin hannun ta kawai ta sha ruwan ta ajiye kofin sannan ta juya ta fita, da fitar ta wajen gida kuwa ta watsar da su tana mai sake share hawayen ta da ya kasa tsayawa.

Shi kam cike da jinda'di yayi tsalle ya fa'da kan kujera yana 'daukan remote zuciyar sa fari 'kal yau ya samu abinda yake so...gani yake yau 'din da babbar sa'a ya tashi, jumma'ar yau 'din da hasken ta tazo masa...an fasa auren sa da Husnah gashi kuma ya samu biyan bu'katar sa wurin Ma'u.

Bai damu sam da halin da zata shiga ba ita da iyaten ta balle yayi tunanin babban zunubi ya aikata wanda Allah ke hukunta bawa a kansa..sksai zuciyar sa ta nutse cikin kogin da ba'a gane illar da zurfin sa ke haddasawa har sai anyi nisa cikin sa.

Tana cikin share hawayen bata bar ko 'kofan gidan ba sai ga Imrana da shima isowar sa kenan yana 'ko'karin shiga ciki.


Da ganin ta da yanayin ta sai ya saki dariyar mugunta a fili ya furta" Aiki ya kammala kenan...Asma'u ta Deeni komai dozen..".

Shiru tayi kawai tana cigaba da share hawayen ta..sai yace" Me ya faru kuma kike ta faman kuka haka...cewa yayi bazai aure ki ba ne?"

Sai ta jijjiga kanta alamar a a batare da ta ha'da ido da shi ba.
Kai ya rausayar gefe sannan yana duban ta yana mata kallon tsaf a 'dan yatsine yake kuma fa'din" Yarinya kwantar da hankalin ki ki daina kukan nan kinji...sakamakon soyayyar Deeni dama kenan..kyauta yake bada tukuici..dan haka ki saki ranki..kukan ki shi zai sa kowa ya san abinda kika aikata harda 'yan gidan ku ma, in kuwa kika yi shiru kika daina kukan babu wanda zai gane abinda ya faru ko a gidan na ku ma.."

D gama fa'din hakan sai ya juya ya nufi mashigar gidan yana sake fa'din" Sai mun zo zance...".


Yana shiga parlourn ya saki fuska da dariya ya tunkari wajen da Yah Deen ke zaune yana 'dan tsalle irin na tsokana ya bashi hannu suka kashe kowa fuskar sa cike da fara'a sosai.

Imrana ne yace" Harfa ka canza nawa".

" Sai kace yau na fara".
Ya bashi amsa yana murmushi.

" a a kaide kayi shiru kawai kafa san 'yan yaran nan fa bala'i ne".

Hannu Mu'een ya sake bashi kawai yana murmushi, cuz shi sam be iya fallasa sirrin gadon sa ga kowa duk dama ba ta hanyar da ta dace yake yi amma bai iya fa'di ma kowa tun asali haka yake yanzun kuwa ya lura abinda Imrana ke son ji daga bakin sa kenan..shiyasa kawai ya mi'ka masa hannun suka sake tafawa irin na gogaggun gayu..ya 'dauke masa hankali da hakan sai dai tun kafin su raba hannaye Imrana yace" Gaskiya abani nawa tukuicin nima dan na lura ba 'karamar liyafa ka sha yau 'din nan ba".
Yana gyara zaman sa yace" Je ka za6i kaya guda cikin na Anty".
Haka kawai yace da shi a takaice, yayin da Imrana ya tashi yana murna yake yi mai kirari da" Alhaji 'dan Alhaji, yaro mai abin mamaki...da haka ya wuce ciki dan 'dauko kayan da aka bashi kyautar su.


Imrana na fitowa daga bedroom 'din Deeni hnnun sa da kayan da ya za6o sai suka ji tsayuwar mota daga waje, babu wanda ya damu cikin su dan sun san babu mamaki 'yan 'daurin aure ne suka dawo, Imrana 'karasowa yayi ya zaune nesa ka'dan da Mu'een yana sake godiya yana kuma warware kayan domin dubawa.

Yah Deen bai ce da shi komai ba dan duk hankalin sa ya tafi ne ga tsayuwar motar da yaji..murmushi gefen baki yayi da ya tuna cewa Ishaq bai zo ya tarar da shi da yarinyar can ba da ya shiga uku wurin sa yasan, yanzu kam ransa wasai bashi jin wata fargaba tunda yana da tabbacin babu wani mummunan labarin da suka yo masa guzurin sa daga can tunda an riga an raba tsakanin sa da Husnah shi yanzu bashi da wata damuwa.

Ai kuwa su 'din ne kamar yadda tunanin sa ya basa, dan yana cikin tunanin yaji sallamar su...Ishaq ne ya fara shigowa sai sauran a bayan sa.


Zama yayi kan kujera yana sakin ajiyar zuciya tare da cire hulan da ke kansa.

Yayin da sauran ma suka yiwa kansu mazauni kan sauran kujerun duk suka zazzauna Anas nema yana zaman yake fa'din" Ango mai abin mamaki, ango kasha mai'ko, ango mijin amarya".

Murmushi Yah Deen yayi yana kallon sa tare da bashi amsar" A da kenan Anas..yanzu single nake kamar kowa"
Anas sai yace" Hmm ai shiyasa nace ma maj abin mamaki domin har gobe ango kake mijin amarya kuma".
Bai damu da zancen Anas 'din ba sai ya 'dauki abin wasa dan haka kansa ya kauda gefe yana fa'din" Erh daga goben har zuwa ranar da na shiryawa kaina yin wani auren kenan..."
Ya 'karashe maganar yana dawo da kallon sa kan Ishaq dake kallon TV ana hasko wasanni yace masa" Kayi shiru Ishaq ko duk gajiyan tafiyan ne?"
Kansa ya shafo a hankali tare da bashi amsar
" Bari kawai kaina har ciwo yake min wallahi..an tara jama'ah ba laifi".

Dariya Yah Deen yayi tare da fa'din" Shine ai da nima kake so inje in kwaso ciwon kan abanza ko?...ni bani labari ma me ya faru ne da yasa har aka fasa?"
Ya 'karashe maganar yana gyara zaman sa izuwa fuskan tar Ishaq dake gefe da shi.

Ishaq Babbar rigar jikin sa ya cire ya ajiye agefe sannan yace" Ai ka bari mutanen nan 'kananun 'yan gabas ne wallahi...




_Kuyi min afuwan ji na da kukayi shiru kwana biyu al'amura ne suka sha kaina...kunsan rayuwa sai a hankali... hada-hada...._




Comment
Vote
Share






*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)


By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *53*

Ishaq Babbar rigar jikin sa ya cire ya ajiye agefen sa sannan yace" Ai ka bari kawai mutanen nan 'kananun 'yan gabas ne wallahi...sai da fa muka gama shiri mun baza kunnuwa zamu ji an 'daura auren ka kawai sai ji akayi ya wakilci auren Husnah da wani daban, ashe ma wai wancen Hisham 'din 'dan sa ne na cikin sa, in ba rainin hankali ba yau ne yasan da zaman 'dan nasa da bai yi tunanin aura masa ita tun farko ba sai da ya bada ta ga wani ?...abin takaici ma wai sai daga baya bacin har an gama komai kafin ya zo yana bawa su Alhaji ha'kuri...a lokacin ji nayi tamkar in mare sa..."

Anas ne ya tare maganar tashi da fa'din.." Ai Alhaji ba 'karamin birge ni yayi ba, kai baka ga yanda ya nuna masa bai damu ba, sai ma wata kwantacciyar fara'a da fuskar sa ke haskawa...jikin Mutanen ai har sai da yayi sanyi 'yan rainin sense..".

Baki Yah Deen ya ta6e, cikin nuna halin ko in kula da batun ya furta" can musu su suka sani...ni dai Alhamdulillah kawai zance tunda an raba ni da ita".

Babu wanda ya ko kwatanta sanar da shi cewa an sake 'daura masa auren da wata  kawai suka bar shi da murnar sa na bai auri Husnah ba.



*****
   'Bangaren Husnah kam tunda taji cewa da Hisham aka 'daura auren ta bada Mu'een ba sai ta ringa kuka gwanin tausayi idan ka ganta, hawayen ta sam ya kasa tsayuwa, sai dai ita kanta bata san ainahin me take yiwa kukan ba, shin kukan an raba ta da Deeni ne ko kuwa kukan auren da akayi mata da Hisham?
A yanzu baza ta ce akwai soyayyar Mu'een cikin zuciyar ta ba balle tace taji haushin rabuwa da shi, sannan ta san Hisahm 'dan uwanta kuma mai 'kaunar ta amma me yasa ta kasa jin farin ciki da jin labarin aure tsakanin su? Ta riga ta shiryawa zama da Mu'een tuntuni, ta yiwa kanta al'kawarin zama da shi cikin ko wani irin hali.

Mahaifiyar ta kam jikin ta sanyi yayi da jin wani juyin da aka kuma yi, sam ta rasa me yake damun Alhaji Mamman a dauniyar nan, tsananin son kansa ya fiye masa yawa, wancan karon da ya bada auren Husnah batare da neman yardar ta ba ta yi masa uzuri da tunanin ko abokan sa ne iyayen yaron shiyasa amma duk da haka hankalin ta bai kwanta ba, wanda bata samu natsuwa ba sam har sai da ta tabbatar da cewa Husnah na son yaron sannan hankalin ta ya kwanta da auren, yanzu kuma bacin sun gama kwantar da hankalin su kan hakan sun kar6i auren sai ya kuma 6ullowa da wata sabuwar zance...wai auren Hisham da Husnah...she is totally speechless kan hakan

Husnah kam kukan ta na 'kara yawaita ne a duk lokacin da ta tuno da mahaifin ta, tasan da ace yana raye da duk hakan ba zai faru da ita ba, ta san da babu wanda ya isa ya ringa juya mata rayuwa batare da yardar ta ba, balle irin wannan juyi irin na rashin mutunci da 'kas'kanci 'karara hatta mahaifiyar ta ba'a bawa darajar da za'a shawara da ita ba, tasan ba kowa ne zai iya 'daukan hakan ba duk kuwa rashin gatan mutum.

Yini ta yi tana kuka, yayin da kanta ke tsananin yi mata ciwo amma sam bata damu ba, kafin maghrib kuwa ko motsin kirki bata iya yi da jikin ta saboda yanda kanta ke sarawa, idanun ta ma nawi sosai suka yi mata.


Lokacin da Mummyn ta fahimci halin da Husnah take ciki kuka ta sanya kawai itama, gani take kamar bata kula da maraicin Husnah ba, a 'yan kwanakin nan Husnah tayi kukan da be kamata ace tayi sa ba duba da yanayin shekarun ta, gani take kamar Allah zai tambaye ta akan hakan,  haka ta zauna gefen Husnahn tana faman sheshshe'ka itama, wata 'yar uwar tace dake tsaye dafe da kafa'dar ta take bata baki akan taya Husnah kukan bashi da amfani sam, bata ce da ita komai ba illah ro'kon ta da tayi akan ta 'dauko mata wayar ta.

Family Doctor 'din su ta 'kira inda ta sanar da ita abinda ke faruwa da Husnah cikin rawar murya.

Husnah kam hawaye ta gefe da gefen idanun ta yake sau'ka, ko iya bu'de idanun da kyau ma bata yi yanzu, tana kyautata zaton Allah ne kawai yake jarabtan ta kan abinda ta aikata abaya, shiyasa yake ha'dawa da abubuwan 'daga hankali a duk sa'in da yaga dama batare da ta zata ba, a  hankali ta furta" Mummy...mutuwa zanyi ko?"

Saurin kamo hannun ta mahaifiyar ta tayi ta ri'ke cikin nata tana girgiza kanta idanun ta hawaye tace" Bazaki mutu ba Husnah, idan kika tafi ni da wa zan zaki barni a duniyar nan...?"
Husnah rintse idanu tayi tana jin ciwo a 'kirjin ta, ga kunyar mummyn ta da yabi ya cika mata zuciya, tasan babu wanda zai so yaji cewa 'dansa ya aikata irin abinda ita ta aikata, amma duk da haka tana ganin dole ne ta sanar da mahaifiyar ta, dole ne ta gaya mata rayuwar da tayi bayan idanunta, 'kila idan mahaifiyar ta yafe mata Allah ma zai ji 'kanta ya yafe mata, gani take duk abin nan dake faruwa da ita alhakin mahaifiyar ta ne yake binta...she have to end it here kar abin ya zarce haka, da jimawa farin ciki yayi mata 'kaura, rayuwar ta shiga garari ne tun lokacin da batun auren ta da Mu'een ya fara, yanzu kuma ga yadda abin ya kasance.

Idan tace haka zata cigaba bata san agaba me kuma zai sake faruwa da ita ba...idanun ta a rintsen wani hawayen ya sake gangaro mata mai matu'kar 'dumi....a hankali cikin sanyin murya ta furta" Mummy ki yafe min...na ci amanar ki..naci amanar tarbiyar da kika da'de kina bani mummy..."
Kuka take yi mai tsuma zuciya mai ha'de da shashshe'ka..bata iya bu'de idanu ta ha'da ido da Mummyn nata ba a lokacin.

Yayin da Mummyn ta tsura mata idanu tana kallon fuskar ta zuciyar ta duk ta karaya, bata son tana kukan nan, tana so ta dakatar da ita haka nan amma sam ta kasa sai ma taji ta karaya gaba 'daya musamman da taji irin kalaman nata da mamakin ta tsaya kallon ta.
Husnah kam tana cikin kukan tayi tunanin rashin sanar da Mummyn yafi saboda gudun halin da itama zata shiga sanadin hakan, take sai tayi ma'am da wannan batun dan haka ko da ta bu'di baki dan cigaba da ro'kon Mummyn sai tace
" Mummy...dan Allah ki yafe min insha Allahu bazan sake 'daga hankali na ba...nayi al'kawarin zan zauna da Yah Hisham da amana....nasan 'kaddara ce ta ha'da aure na da shi auren mu ha'din Allah ne..dan haka na amince Mummy.."
Ta 'karashe da sheshshe'ka, sam ba haka ta so fa'di ba amma nawin maganar yasa ta kasa furtawa mummyn ta, ta ya za'ayi ta dubi tsabar idanun Mummy tace da ita ta aikata zina sau ba adadi a rayuwar ta, sannan daga 'karshe wanda ta yadda da shi ta mallaka masa jikin tan shine kuma yazo ya nuna mata tsana mafi muni a rayuwar ta?...Tasan jin hakan ba komai zai haifar ba face 'dagawa mahaifiyar ta

Please Login or Register in order to submit comment