Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuciya ta.

Ban ji amsan da aka bata daga 'dayan 6angaren ba sai gani nayi kawai ta koma ta zauna bisa kujera tana girgiza kanta tare da fa'din _Innalillahi wa inna ilaihi Raji'un_ 'karasawa nayi gaban ta da sauri na tambaye ta" Ammi me ya faru?" " Bakomai" Shine amsar da ta bani sai kuma naga hawaye na gangaro mata sirara, haka da na gani sai ya sake 'dage hankali na sosai take nima na saki kuka ni kam har da sheshsheka dan ganin Ammi na da kanta tana kuka...ina yi ina sake tambayar ta abinda ya faru.

" Haba Ammi da kanki...?"
Naji muryar sa kamar daga sama yana fa'din haka daga bakin parlour.

Ammi bata kula shi ba haka nima a hankali ya 'karaso ya zauna gefen Ammi sai kuma ya dafe kansa..." Ni da nake kuka ina tambayar Ammin ni dakawa tsawar inyiwa mutane shiru sannan yace in tashi maza inje in shirya in fito zamu wani wuri".
Haka yace dani yana kallo na.
Duk da nayi mamakin maganar tasa amma sam koka'dan banga fuskar da zan tambayi inda za'a je ba.


A hankali na tashi ban bar kukan ba haka kuma ban fasa mamakin shirin da yace inje inyi ba.

Sharp-sharp na shirya na fito haka ma Ammi, tare muka fito dashi babu mai cewa 'kala cikin mu duka, Yah Deen ne da kansa ya sau'ke mu a 'kofar gidan Ummah ta nan na tarar da wajen gidan duk mutane, take zuciya ta ta tsinke haka kawai naji tsoro ya shige ni sosai.

Ammi na kalla na je fa mata tambayar abinda ke faruwa anan 'din cikin ki'dima sai tace min bakomai.

Banji amsar Ammi ya gamsar da ni ba dan haka sai na bu'de motar cikin sauri nayi gaba inda na tunkari mashigar gidan mu.
Abinda kunnuwa na suka  fara cin karo da shi shine sautin koke-koke.

      Da mamaki na 'karasa cikin gidan nan tarar da Addah ta kamar ranta zai fita saboda yanda ta fita hayyacin ta tana kuka..kukan nima na fara a ki'dime na isa gare ta na zube kan gwiwoyi na" Addah.."
Nace cikin kuka..Abinda ta fara furtawa shine" Baban mu...Baban mu Hudah, Allah ya kar6i ran Baban mu da safiyar yau 'din nan".

Cak kuka na ya tsaya na bu'de baki ina kallon ta da mamaki har da 'kan'kance idanu na...lokaci guda sai kuma na jijjiga kaina nace" Kai Addah ba shi ba dai, sai dai wani, 'dazun nan fa naga 'kiran sa cikin waya ta ina ma shirin 'kiran sa ne sai wani abin ya 'dauki hankali na ta ya kuma za'a ce Allah ya kar6i ransa".

" Shine mana Hudah a asbiti fa suka kwana...."
Ta sake bani amsa da alamun tabbatarwa.

" Nayi waya da Ummah amma bata sanar da ni ba kuma..."
Ban 'karasa maganar ba nayi shiru sakamakon tuno yanayin yanda naji muryar Ummah da safennan da na 'kira ta.
" Ke nan dagaske Baban mu ne ya rasu?"
Na sake tambayar zuciya ta.
   Wani kukan ne ya 'kwace min mai tsuma zuciya...

Allah sarki rayuwa, ashe duniyar bakomai bace ga 'dan Adam...Allah ya ji'kan Ban mu da Rahama Allah yasa aljannar Firdaus ta kasance makomar sa ta har abada.

Ha'ki'ka munyi rashi babba..

A can Jos akayi jana'izar sa aka kaishi gidan sa na gaskiya da kyakkyawar shaida a bayan sa.

Su Alhaji Baba da su Yah Deen da sauran 'yan uwa duk can Jos 'din suka je sannan washegari suka dawo.

Su Zaidu ma sun zo gaisuwa inda suka shigo hatmr cikin gida suka gaida Ummah ta da sauran 'yan uwa.

Ammi kuwa dama kullum muna tare, ta kan zo da safe da yamma ta koma gida sai wata goben kuma.

Kwana na biyu a gidan mu da wata safiya da Ammi zata zo sai ta taho min da waya ta.

Ina kar6a sai naji hawaye na gangaro min a hankali musamman da na tuna 'kiran da na gani na mahaifi na na 'karshe.

Shiga nayi cikin wayar na sake dubawa wani hawayen na sake zubo min ina tuna mahaifi na da karamcin sa...Ammi ko da taga haka sai ta ce da ni da wayar zata koma ai in dai haka zan riga yi...".

Kife wayar nayi kan 'kirji na na juya mata baya na cigaba da share hawaye na.

11 da 'yan mintina na safiya lokacin ina can cikin 'dakin Ummahn mu ina kwance ina tunani, gefe na wasu ne daga cikin dangin mu yawancin su matasan 'yan mata ne kamar ni suna 'yar hira...Vibration naji waya ta nayi na neman agaji lokaci guda sai naji zuciya ta ta tsinke sanadiyan tuno Baban mu da nayi saboda da jin dirin wayar shi ya fara zuwa raina amma koda na duba sai naga ba'kuwar number ce ba ta shi ba.

Ban 'daga ba har ta tsinke ina kallon ta zuciya na dokawa, take wani 'kiran ya sake shigowa wannan ma ban 'daga sai da ya kusan yankewa kafin na 'daga.

Shiru nayi bayan na sada wayar da kunne na.
" Ya dai"
Da naji an fa'di daga 'dayan 6angaren ne ya sanyani saurin fahimtar wanda ke 'kiran nawa.

" Bakomai" nima na bashi amsa a ta'kaice ina murza idanu.
" Kina lafiya ko?"
" Umm" na bashi amsa 'kasan ma'koshi.
" Ya ha'kuri kuma?"
" Alhamdulillahi".
" Har yanzu kina kuka ko?"
" A a"
" ance min kuka kike yi kullum"..
Shiru nayi ina sake jin idanu na na tsatstsafo da hawaye..taya bazan yi kukan rashin Mahaifi na ba...na ayyana cikin zuciya ta.
" Kina yi masa addu'a kuwa".
Naji ya sake tambaya ta.
Da" Umm" na bashi amsa 'kasan ma'koshi.
Sai yace " Yauwa abinda zaki na yi masa kenan yanzu ba yawan kuka ba kinji?"

" Uhum"
" Allah ya ji'kan sa da Rahama"
" Ameen"
Nace a hankali.
" Ina Ammi?"
Ya tambaye ni sai nace
" Tana waje..bari in kai mata"
Saurin dakatar da ni yayi da fa'din
" a a barta anjima zan 'kira ki kinji".
" Uhum"

Daga haka ya yanke wayar...ni kam ri'ke ta nayi a hannu na ina binta da idanu na" _Yah Deen_ ".
Na furta cikin zuciya ta,
ji nake tamkar wani ne daban ba shi ba.







Comment
Vote
Share







*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)


By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*


_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *65*

Mamakin sa be 'kara kamani ba sai ranar da aka cika 7days da rasuwar Baban mu ranar kamar daga sama naji ana fa'din wai ga Deeni mijin Hudah sun shigo cikin gida gaisuwa.

Ina 'dakin Baban mu ni da wasu 'yan uwan mu da basu wuce sa'anni na ba, su biyun su ma suke hirar su ban fiya saka baki cikin maganar su ba, da jin abinda aka fa'din kuwa haka kawai sai naji na mi'ke tsaye ta kafan labile na le'ka nan na hango su dur'kushe suna gaisuwa shi da abokan sa guda uku, ni kam ma ban tsaya na lurako da su waye yake taren ba akan sa ka'dai na tsaida idanu na.

Tun ranar da ya 'kira ni a waya bai sake 'kira na ba, na kan yawaita tsammanin ganin 'kiran sa ya shigo cikin wayata amma shiru  kwana hudu kenan rabo na da ko jin muryar sa, ban ta6a tsammanin cewa nayi kewar sa ba sai yanzun.

Kaina na jingine daga jikin bangon gefen 'kofan na bar kallon su, ko 'yan matan da nake tare su da a 'dakin ma babu wacce ta bi ta kaina da yake dama ba wani hira sosai ke shiga tsakanin mu ba, hakan yasa suka cigaba da hirar su batare da sun kula da yanayin da nake ciki ba... ban san cewa na shiga dogon tunani tsaye a wurin ba har sai da naji ana 'ko'karin shigowa ciki daga waje sannan na dawo hayyaci na...Addah ta Maryam ce ta shigo" Yauwa ashe kina nan ma...".
Ta fa'di tana 'kare min kallo" Me ya sameki kuma Hudah?"
Ta 'kara tambaya ta da alamun mamaki 'karara kan fuskar ta.
'Kasa nayi da idanu na sannan na bata amsa da fa'din" Bakomai Addah".
Bata ce dani 'kala ba sai kawai ta bi ta 'kare min kallo sama zuwa 'kasa sannan ta saki ajiyan numfashi mai sanyi" Mijin ki yazo zasu shigo, abokan sa ne inajin suke son gaida ki".

Bata tsaya ta saurari jin amsa ta ba kawai ta juya ga sauran dake 'dakin tace" Biba ku kintsa ba'ki zasu shigo yanzu".

" Toh". Suka bata amsa da shi cikin ha'din baki daga haka naga ta juya da niyyan barin 'dakin,  yayin da naji 'kirji na ya ri'ke ni haka kawai ban san dalili ba, tsintan kaina nayi da tambayar" Wai da gaske ne zasu shigo 'din?"
Fat fat fat naji zuciya ta ta harbawa lokaci guda, ban iya nace da Addah ta komai ba har ta 'karasa barin 'dakin, a hankali na lumshe idanu na sannan na bi 'dakin da kallo a tsanake.

Ba laifi 'dakin nasan koma waye za'a iya kar6ar sa a ciki batare da damuwar komai ba, balle Yah Deen da abokan sa ka'dai.

A hankali na koma na zauna gefen su Biba tare da gyara zaman mayafin na...ba bu'katar sai na sanar da wa'danda muke tare a 'dakin domin nasan ta riga tayi musu bayanin komai dan haka ban kuma ce da su 'kala ba kawai nayi shiru.

'Dayar mai suna Fati itace ta ta jefa min tambayar" wai su mijin nawa ne zasu shigo?"

Da kai na bata amsa alamar" Erh "sai tace ita dama tana so ta ganshi dan bata ta6a ganin sa ba kuma taji ana fa'din wai 'dan gayu ne".
'Dan murmushi kawai nayi mata sai ta 'kara da fa'din" Dan Allah idan yazo ki nuna min shi kinji..juyawa tayi ga Biba tace kema Biba ba kina so ki gansa ba?"
Duka Biban ta kai mata tana fa'din" Allah ya shirye ki ke kam".
Zabura tayi gefe tace" ba wani ai gaskiya ne".
Duk yanda nake jin zuciya ta na harbawa amma hakan bai hana ni yin murmushi da jin irin maganganun nasu ba.
A fili cewa nayi da su
" Kar ku damu insha Allahu zaku ganshi". nace dasu ina mai yin 'kasa da kaina.

Kafin ta 'kara yin wata magana sai muka ji sallama daga bakin 'kofar shigowa 'dakin.

Imam ne kan gaba sai Ishaq sannan Yah Deen da wani a bayan sa da bansan sunan sa ba.

Jan Hijab 'dina na 'karayi ya rufe min rabin fuska ta yayin da su Biba suka gyara zaman su da kyau tamkar wasu manya...gaisuwa da ta'aziyar Baban mu su Ishaq suka yi min wanda cikin muryoyin nasu ko ka'dan banji tashin muryar sa ciki ba.

Duk yanda su Biba suka 'kagu da su ganshi amma kasa sakin jikin su suka yi balle su fahimci waye Mu'een 'din a cikin su, daga gaisuwar kawai naga sun mi'ke tsaye duk suka yi waje ya rage daga ni sai su Yah Deen.


Su Ishaq ke 'dan labarin sanin da suka yiwa Baban mu musamman lokacin da ya bada aure na ga Yah Deen wanda tun a lokacin kusan dukkan su suka yabawa karamci da dattakon sa,  ashe kwanaki 'kalilan suka rage masa...yanzu sai dai Fatan ubangiji Allah yayi masa Rahama yasa Aljannar firdausi ta kansace makoma agare sa...muma ya kyautata namu tafiyan...Ameen

  Daga 'karshe Ishaq ne ya 'dan 'kara yi min nasihar ha'kuri da kuma yadda da 'kaddara inda ya nuna min cewa irin su Baban mu ba iyalan su ka'dai ne ke damuwa da rashin su ba..yace kusan duk wanda ke tare da shi dole yayi alhinin rashin sa, gata 'daya da yakamata mu yi masa a yanzu itace addu'ah ka'dai...da kansa yayi masa addu'ah muka shafa wanda daga haka duk suka mi'ke tsaye suka nufi hanyar fita.

Suna masu sake maimaita Allah ya ji'kan Baba da Rahama.

Kaina 'kasa nake amsawa da" Ameen Ameen" ina wasa da yatsun hannu na yayin da nake jin siraran hawaye na gangaro min saman kunci na a hankali.

Ban yi ta6a tunanin har haka Baban mu zai samu yabo daga abokan Yah Deen ba musamman akan auran mu, ji nayi duk jiki na yayi sanyi 'kalau, cikin raina na ayyana" in dai har haka ne kuwa da iznin Allah zan yi ha'kurin zama da shi cikin kowace irin hali, in dai har akan aure na da shi mahaifi na zai ri'ka samun kya'kkyawar Addu'ah to kuwa zan 'daura 'damarar zaman aure na, Yah Allah ka mantar da ni komai, Yah Allah ka sanya fahimta tsakani na da shi.


Ban yi tsammanin akwai wanda yayi saura cikin 'dakin ba da yake naji shiru, amma haka kawai sai naji ni a tsarge tamkar ana kallo na, a  hankali na 'dan 'dago kaina ka'dan nan naci karo da shi zaune shiru ya zuba min idanu.


'Kasa na sake yi da kaina batare da na furta komai ba illah tunanin abinda ya zaunar da shi a anan 'din da na fa'da, nan na tsinkayi muryar sa yana fa'din" Har yanzu kukan kike yi ko?"

Girgiza kaina nayi a hankali sannan na fara goge hawayen dake fuska ta da hannu na 'daya.
Tsaye ya mi'ke ya sanya hannun sa 'daya cikin aljihun wandon jikin sa sannan ya kalle ni yace" Anjima zamu koma Jigawa da su Ishaq fatan ba wani abu ko?"

Da kai na bashi amsa alamun a a...sai yace" Toh Saif zai kawo miki sa'ko anjima ko zuwa gobe, in kuma akwai wata matsala ma ai ga  Ammi ko kuma ki 'ki 'kirani a waya kawai ki sanar da ni kinji".
Ya 'karashe maganar yana duban agogon dake 'daure a tsinysiyar hannun sa.
" Uhum"
Na bashi amsa da fa'din hakan batare da na kalle shi ba.
" Na tafi"
Ya sake fa'di yana me nufan bakin 'kofa cikin tafiyar sa mai birgewa....da farko rasa abinda zance da shi nayi dan haka nayi shiru ina bin bayan sa da idanu kawai...dai-dai ya isa bakin 'kofa zai fita sai na tsinci baki na da furta" Allah ya tsare".
Take kuma na sake yin 'kasa da kaina.

Cak ya tsaya sannan ya waigo ya dube ni, fuskar sa ba yabo ba fallasa ban kuma ji ya amsa addu'ar da nayi masan ba balle insan matsayin ta kawai sai naga ya sa kai ya fice daga 'dakin abin sa.

Zugum nayi kamar kurma idanun 'kyam wuri guda ina bin hanyar da yabi da kallo...ni kaina ban san me yasa nayi masa addu'ar ba, kamar yadda yanzun ma ban san me nake tunawa ba haka kuma na kasa fahimtar matsayin da zuciya ta take a yanzun da naji cewa zai tafi Jigawa ba.





*****
       Ko bayan tafiyar sa ban koma gidan Ammi ba, zama na a gidan mu nake jin ya fiye min kwanciyar hankali domin ina ganin Ummah ta da sauran 'yan uwa na sai nake jin bani da damuwar komai.

A hankali duk jama'ah na nesa da na kusa suka watse ya rage saura mu ka'dai, ko gaisuwan ma yanzu an rage zuwa sosai hatta Ammi ta kan 'dauki lokaci bata zo ba...haka ma 'kawata Binta ta kan yawaita zuwa tana tayani hira, wani lokaci har yini mukan yi tare yayin da wasu lokutan bara jimawa take komawa.

Sa'ar da naci ma 'daya ne domin duk cikin su babu wanda ya matsamin da batun cewa in koma gidan Ammi.

Baba Alhaji da kansa ya kan yawaita yin aike na ku'di ko wani abu yace akawo min bayan ko wanda Saif ya kawo min bayan tafiyar Yah Deen ma har yau ban ta6a ko sisi a ciki ba.

Waya kuwa bana 'kiran kowa daga Anty Zainab yayye na sai Ammi, ita ma idan na 'kira ta bata 'dauka sai dai ta yanke ta 'kirani daga baya...ko Yah Deen 'din ban ta6a 'kira ba ban ta6a ko tunanin 'kiran sa ba, hasalima ni ko saving number shi cikin wayar ban yi ba,  haka kuma shima banga ya sake 'kira na ko sau 'daya ba.

Har akayi 40 days 'din Baban mu aka gama ina gida..wanda tun kafin ranar su Saif suka koma school da yake hutu ya 'kare, ni kam ma ban san me yasa yanzu naji bana son zuwa makarantar ba sam naji ta fice min aka.

Ammi ce ma da kanta ta fara yi min maganar makarantar har ta tattaro min shirgin uniforms 'dina ta kawo min amma ko sau 'daya ban iya naje ba.

Lokacin da Addah Maryam zata koma ne nace zan bita Ummah ta ta hanani, nan na fara yi mata kuka sosai na 'daga hankali na kan batun tafiyar har Ammi sai da ta sani nan ta ro'ki Ummah ta da fa'din abar ni man naje tunda ba 'dadewa zanyi ba Ummah ta tace " a a ba inda zani tace hala kun manta ne cewar matar aure take yanzu ba kamar da ba".

Murmushi Ammi tayi domin sai yanzu ta fahimci Ummah da manufar hana ni tafiyan duk da bata fito fili ta bayyana ba amma hakan bai hana Ammi fahimtar ta ba.

  Cikin ranta ta bari akan cewar da ta koma gida zata 'kira Yah Deen ta gaya masa taji shi kuma me ze ce.

Hakan kuwa akayi, Ammi bata ta6a tunanin bama waya da shi ba, so a yanda tayi maganar sai ta nuna masa cewa idan munyi waya ko da na tambaye shi batun tafiya dan Allah kar ya 'ki amincewa, tanaso taje mahaifiyar ta kuma ta hana ta wai saboda tana da aure".

Yace" Gaskiya ne ai Ammi matan aure na yawo ne dama?"
" Ba yawo bane fa Mu'een sistern ta take so tabi...".
Tun kan ta rufe baki ma ya tare ta da fa'din" Sistern ta har ina kenan?"
" Ban sani ba...kana min irin wannan tambayar nice fa na haife ka ba kai ka haife ni ba".
Ta yi masa maganar a 'dan masifance.
Kansa ya sosa sannan yace" Sorry Ammi amma ai naga anyi resuming school shine kuma zata wani wuri saboda me?"
" Ka tambaye ta mana zata gaya maka ai, shikenan saboda makaranta bazata yi ziyara ba?"
Sai yace
" To Ammi taje abinda ni ba ruwa na...Allah ya bada sa'a".
Daga haka ya yanke wayar yana mai jin haushi cikin ransa amma ya danne bai bayyana ba.


Bayan tafiyar Ammi da muka ke6e da Addah Maryam sai take shan cikina akan yanayin zama na da Yah Deen dan tunda take bata ta6a ganin ko waya ma muna yi ba, tace bata ga wani alamun kulawa tattare da 'dayan mu ba...tace da alamu ma har yanzu baki san me manufar auren da akayi miki ba".

Ni kam ban 6oye mata komai ba na sanar da ita yanayin zama na da shi, abu 'daya ne ban bayyana mata ba shine ganin sa da nayi da Husnah, haka kuma ban sanar da ita cewa dalilin kenan da yasa da na dawo gidan Ammi da zama ba...na riga na yiwa kaina al'kawarin bazan ta6a sanar da kowa wannan abin ba, duk da nasan bani da ranar mantawa da shi, a kullum idan har zan zurfafa tunani na to dole sai  wannan mummunan photon ya zo raina.

Duk da hakan ma sosai naga ta nuna alamun mamaki 'karara kan fuskar ta, a fili ta furta dama ai irin wannan auren galibi haka yake kasancewa sai dai in mutun ya dage sannan yake samun kwanciyar hankali, amma kafin hakan sau an kai ruwa rana, tace shiyasa sam baku damu da junan ku ba, nan ta fara yi min fa'dan wai ai nima da laifi na, wannan ganganci ne ne na aikata, me yasa ni idan zaman ya 'daure minbaki bazan nemi shawarar kowa ba, tace mu miye amfanin mu matsayin mu na yayyanki ai dole ne muyi iya 'ko'karin.mu wajen ganin daidaituwar farin cikin gidan ki, amma kika 6oyewa kowa, nasan ko Ummah bata san komai ba game da zaman kun nan ba ko?"
Na girgiza kaina tace" Ammi fa?"
Sai nayi shiru..masifa ta hau ni da shi me yasa tunda ya tafi ni ban 'kira sa ko a waya ba? haka kika ga ake yi ne?"

Shiru na sake yi mata cuz ni kaina ban san dalilin ba.
Sai da ta daka min tsawa kafin na 6ata rai nace" Addah shima fa bai 'kira ni ko sau 'daya ba tunda ya tafi".
" 'Kaniyar ki....wallahi Hudah tun wuri ki dawo hankalin ki ki san me kike yi..tun ranar da aka 'daura miki aure fa ya kamata ace kin bar wannan shirmen a baya".
Tace dani cike da 6acin rai tana nuna ni da yatsa.

Shagwa6e fuska nayi kamar zanyi kuka nace" Addah dan Allah ni toh me zan masa?"

Shiru tayi ta zuba min idanu tana kallo na, sau'kar da murya tayi sannan ta 'kara da fa'din" Ina fatan dai ke da kanki kin san halin mijin naki ba sai an fa'da miki ba?, me kike tunanin zai yi dake shi da yake hul'da da 'yan mata da suka take ki a komai? Wannan yarinyar Ma'u ka'dai ma in kina da tunani ta isheki babbar misali Hudah, ke kina tunanin a hakan da kike yi har miji zai iya dawo da hankalin sa gare ki?"

Idanu na hawaye kawai suka fara tuno asalin halayen Yah Deen da nayi cikin zuciya ta, ni ka'dai na san me nake ji a duk lokacin da na tuno irin abinda idanu na suka gane min yana aikatawa..a gani na Yah Deen ko me zan aikata a duniyan nan hankalin sa ba zai ta6a juyowa zuwa gare ni ba, saboda naga irin matan da yake mu'amala da su, ni da kaina nasan ko cikin mafarki ban isa in kamo 'kafan Husnah a komai ba, toh dan me yasa zan dami kaina bacin nasan abu ne mai wahalar gaske ganin faruwar hakan.

Cikin muryar kuka nace da ita" Addah toh ni nace ina son hankalin sa ya dawo gare ni ne....?"
Tun kan na rufe baki na ta tare ni da fa'din" Ki min shiru 'yar 'kauye kawai, wallahi ke dai wannan karatun naki sam ban san amfanin sa ba..jibe ki kamar zaki yi abin kirki idan angan ki nan kuwa ba haka ba, Hudah ke baki san cewa kin girma ba ko? sa'annin ki nawa aka yi musu auren suka je suka zauna lafiya a 'dakin mijin su ke kin tsaya wani banzan shirme dan kin samu da ma ko?"

" Nima ai ba fa'da muke yi ba Addah".
Na bata amsa ina share hawayen idanu na.
Idanu ta zaro sannan tace" Ikon Allah! anya Hudah kina da wayo kuwa? da alamu 'kauyen cin ki ba mai 'karewa bane har abada, tun wuri fa wallahi  ki natsu ki ja mijin ki a jiki tun kafin lokaci ya 'kure miki...yanzu ina wayar ki?"

" Tana nan".
Na bata amsa ina mai tura baki na jin tace da ni 'yar 'kauye.

Sani tayi na 'dauko wayar wanda bayan na kawo wayar ta kar6a ta ajiye gefen ta.

Maganganu tayi min cikin natsuwa inda ta ringa nuna min muhimmanci da darajar da miji ke da shi a gun matar sa...manufar aure da kuma asalin dalilin da yasa ake yin sa duk sai da ta sanar da ni cikin natsuwa.

Wasu maganganun nata ma ni kunya suka bani sosai amma ganin ita bata damu ba yasa kawai nayi 'kasa da kaina na cigaba da sauraran ta.

Ta 'dauki tsawon lokaci tana yi min bayani sannan daga 'karshe tace in kwantar da hankali na indai ina son in bita can Darazo to dole sai nayi abinda zata saniyi yanzu.
Tace ke kanki kin sani ko Ummah ma bazata ta6a barin ki ki tafi ba har sai ta tabbatar da yardar Deen kafin nan dan haka ki 'kira shi yanzu ki gaishe shi sannan ki ro'ke shi batun tafiyar.
     Tace duk da tasan 'kiran da zanyi masa a yanzun bazai 'dauke shi da muhimmanci ba saboda dan kaina nayi shi ba wai dan inji ya yake acan ba amma dai still yana da kyua in 'kira shin kuma zai iya jinsa daban ta 6angaren sa.

Duk wannan bayanan da tayin kaina 'kasa ban kalle ta ba har sai da ta kai aya kafin na 'dago kaina nace da ita" Addah ai ni bani da numbern sa a wayar?"
" Kamar ya kuma bki da numbern sa Hudah?..baku ta6a waya da shi bane dama?"
" Mun ta6a yi sau 'daya".
" To ki duba cikin wayar mana...." Tayi maganar tana mi'ka min wayar tawa.

Ansa nayi na shiga inda ya nasan zan samu numbern na tafi can 'kasa ina dubawa, ni da kaina nasan babu numbern da banyi saving ba sai ta shi ka'dai, hatta Zaidu nayi saving numbern shi duk wanda na ta6a yin waya da shi to bana ajiye wayar har sai nayi saving

Please Login or Register in order to submit comment