Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka so ni ayanda nake d'innan koda bazan samu ilimin bokon da kake muradi ba sannan kayi hak'uri da raunina alokacin dana gaza, ni kuwa nayi alk'awarin riqeka kai kad'ai acikin zuciyata batare dana had'aka da kowa ba, zanyi jarumta wajen kula da kai da kuma baka farinciki har iya qarshen rayuwata." Shiru yayi yana sauraren kalamanta da yakeji tamkar karta dena, tabbas yayarda kowane bawa da irin baiwar da ALLAH yayi masa, Rashida batada ilimin boko amma duka kalamanta cike suke da fikrah da kuma ma'ana, a 'yan shekarunta baiyi tsammanin zai iya samun nagartaccin kalamai daga wajen taba, asali ma yad'auka wayayyiyar mace 'yar boko ita kad'ai tasan yanda ake sarrafa harshe wajen furta kalmomin soyayya, murmushi yayi sannan yace

"Indai wannan ne muradinki da Kuma burinki to ki kwantar da hankalinki, ni Nuraddeen nayi alqawari zan soki so mai tsanani Kuma zan d'aukaka darajarki acikin 'yan uwanki mata."

"Ina godiya da hakan malamina" tafad'a cike da farinciki, firarsu sukasha sosai kafin ya canxa akalar firra zuwa wajen koya mata yanda zatayi amfani da wayar, dariya tayi sannan tace.

"Malamina kahutar da kanka don bana fahimtar komai ahaka, inda ma ace a ikacene kake nuna mun to da zanfi fahimta amma wannan left da right da kake fad'a awajen asambuli kawai nake ganesa."

Dariya yayi sosai kafin yace "shikenan gobe kifito da wayar sai innuna maki wasu abubuwan a aikace kinji ko?."

"To shikenan, seda safe naji motsi qila su baba ne suka dawo"

"Ok. To kigaishesu."

"Zasuji in sha ALLAH malamina." murmushi yayi ahankali ya furta mata "I love you so much Rashida."

Dariya kawai tayi had'e da ajiye wayar tayi tsakar gida, "hello, hello." Yadinaga fad'a amma ga mamakinsa yaji shiru, yatabbata ajiye wayar tayi batare data kashe ba ta tafiyarta, dariyar shima yayi sannan yakashe wayar ya ajiye, ji yakeyi Ina ma rashidarsa zata iya karanta message day tura mata dad'ad'an kalaman da zasu dad'a sanyaya mata zuciya kuma suqara mata qaunarsa, amma kash yasan dole soyayyarsa tasamu tawaya tawannan gefe.

••• ••• •••
Baffa kuwa tuni yaba baffa usman shanunsa guda biyu yace aje asayar dasu kud'in afara sawo kayan aikin da za'a fitarwa da Nuraddeen sashen da zai ajiye matars, kafin kace me tuni baffa Usman yayi yanda yace har anfara aza gini mai kyau, wanda duka baffa Usman ne yakira wud'anda suka fitar da zanen yanda za'ayi ginin, ciki da falo sai toilet da kitchen duk acikin sashen da aka d'ibar masa tsakankanin shiyar mahaifinsa data baffa Ali....








*_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU👏😭_*
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___13💎


Jin kamar motsi abakin k'ofar ajin yasa malamin dake cikin juyowa, "A'a malan Idris barka da safiya" yafad'a tare da qarasowa wajen ya mik'a masa hannu suka gaisa,

"Yawwa malan sale an shigo?"

"Eh wlh, wani abu kake nema ne?"

"Eh kusan haka dai Amma bari naje zuwa anjima na dawo saboda inada aji yanzu."

"Ok to, Masha Allah" suka sake gaisawa sannan yawuce, yana wucewa tasaki wata irin ajiyar zuciya tare da fitowa a qarqashin kujerar data b'uya tana watsawa nakusa da sit d'insu wani mugun kallo saboda yanda taga sun maido hankalinsu gaba d'aya akanta, da sauri suka d'auke idanuwansu daga kallon da sukeyi mata gudun karta tata masu rashin mutunci, wani juya idanuwanta tayi had'e da aza kanta saman bencin dake gabanta tayi kwancenta,

malan Idris nafita yanufi ajin da yake da period ransa duk ajagule, yaso ace yana shigowa yayi tozali da fuskarta saboda yanda yayi matuqar kewarta sai gashi hakan yacutara, haka nan ya daure yana koyarda d'aliban nasa sama sama amma gaba d'ayan tunaninsa da natsuwarta na wajen d'alibar tasa akan dalilin daya hanata zuwa makaranta yau duk da dai wani gefe na zuciyarsa na tabbatar masa da cewa tana cikin makarantar kawai biyi nasarar ganinta bane, adaddafe yasamu period d'insa ta k'are yafice daga ajin, wata d'aliba yakira yace taje ajinsu Rashida tace yana kiranta duk dako agaban idonsa wani malamin ya sake shiga cikin ajin nasu bayan nafarkon yafita.

Daidai bakin qofar yarinyar ta tsaya tare da cewa "escuse sir, malan idris yace yana kiran Rashida bashar." ai Bata rufe baki ba rashida tasake shigewa qarqashin kujerar, dube dube malamin yafara yana kiran sunanta amma taqi amsawa, sukuwa ajin gaba d'aya tsoronta sukeyi saboda sanin halinta shiyasa babu wanda yayi yunqurin tonata gudun kada ta taresaidan antashi tabashi kashi don haka takeyiwa duk Wanda ya takaleta acikin aji.

Juyowa malamin yayi had'e da cemata, "kije kifad'a masa bata zo ba."

Yana nan a inda take zaune yarinyar tadawo tafad'a masa cewa, "malan ance bata zoba" yace

"Ok wuce aji Kuma karki sake ink'ara ganinki waje kafin afito breakfast kinaji na ko."

"Eh malan" tafad'a tare da rugawa tashige ajinsu,

Tunanin zuwa gidansu yayi ya dubota, sai kuma yaga kamar hakan ba daidai bane tunda bai tabbatar da batazo ba d'in, don shi har yanzu jikinsa nafad'a masa tana cikin makarantar saidai in akwai wani abu dake faruwa, hanyar clinic d'insu ya nufa ko tana can Amma ga mamakinsa bai iskota ba hakan yasa yawuce dining hall d'insu da kitchen duk bata can, wasa wasa malan idris ya zagaye duk wasu building na makarantar amma baiga Rashida ba, hankalinsa ya matuqar tashi da hakan, don bai tab'a ganin tayi fashin zuwa makaranta ba duk da rashin son karatunta saboda yanda baba keson tayi karatun shiyasa baya d'aukar mata hakan, office d'insa yakoma ya zauna tare da aza kansa saman jikin kujerar yana jin rayuwarsa duk ba dad'i, tun lokacin bai sake leqawo wajen harabar makarantar ba sai da yaji antashi breakfast, miqewa yayi da sauri yakoma jikin tagar office d'in nasa yana kallon qofar ajinsu yanda d'aliban kefitowa d'aya bayan d'aya Amma har suka gama fitowo ko mai kama da ita bai gani tafito ba balle itad'in, cike da takaici yakaiwa jikin bangon naushi had'e da juya zai bar wajen, kamar ance ya sake juyowa ta tagar ya hango ta azo qafarta sannan yaga ta leqo da kanta tana kalle kalle kamar mai neman wani abun, ganin yayi tana yiwa meenah qawarta magana ga kunne had'e nuno office d'insa wanda yasa aransa yaji dad'i atunninsa maganarsa takeyi, abunda bai sani ba Rashida tasa aduba matane idan yana cikin office don tasamu tafito ta sayi abunda zata saya kafin ya rutsar mata, yana kallo tafito tana d'an waige waige har ta isa inda zatayi sayayyar tasaya da sauri kuma tajuya tabar wajen, a maimakon takoma cikin aji sai yaga tanufi bayan class d'in da sauri meenah na biye da ita.

Murmushi yayi had'e da sauke wata irin ajiyar zuciya sannan yakoma bisan kujerarsa ya zauna yana dariya saboda yagano dalilin da yasa tab'uya bai gane taba, dariya yasakeyi had'e da cewa, "kunyata Rashida keji kenan!?" Jikkar da yazo da ita yajawo yaciro kwalin wayar daya siyo mata yana kallo sai kace shine ita, a hankali yafurta da taimakon wannan wayar zan tabbatar matar maki da irin soyayyar da nakeyi maki, zanyi iya qoqarina wajen yakice maki wannan matsananciyar kunyar dake nema tazama shamakin da zaya zamo silar takurawa rayuwar aurenmu, maida kwalin wayar yayi cikin jikka ya rufe sannan yamik'e yafito daga office d'in, Saida yad'an jawosa sannan yamik'e ta d'ayar hanyar da zata sadashi da bayan ajinsu Rashida, zaune ya iskota saman wani dutse sunacin dankali da awara sai zob'o da ruwan sanyi dake ajiye gefensu ita da meenah qawarta dake fad'in,

"Waike Rashida lafiya malan Idris yazo nemanki d'azu kika b'uya kuma ya sake aikawa akiraki kikaqi zuwa? Naga dai kuna shiri dashi balle ace wani abun, kodai laifi kika yimasa." Saida ta d'auki ledar ruwan tafasa tasha sannan tace, "wlh meenah babu wani abun dana yimasa kawai Ina cikin damuwane kuma kinsan halinsa ko kad'an baya son ganin d'alibinsa cikin damuwa, bansan irin amsar da zan bashi bane idan ya tambayeni."

"To amma ai wannan shiya Aiko kiranki ma'ana shike nemanki, bakya tunin ko akwai dalilin da yasa yake nemanki?." Tana rufe baki kamar ance ta d'ago kanta tahangosa tsaye ajikin bangon ajin ya nad'e hanneyensa akan qirjinsa yana kallonsu, k'ok'arin yin magana tayi ad'an tsorace yabud'e mata idanuwa had'e dasa yatsansa akan bakinsa alamun tayi shiru, ita kuwa Rashida dama kanta naduk'e tana cin abincinta don haka bata masan abunda ke faruwa ba, alama ya sakeyiwa meenah da hannu ta tashi ta tafi, cikin tarin qarya data k'irk'iro tace

"Emm...Rashida Bari naje naqaro mana ruwa qwaya biyu don wud'annan bazasu ishemu ba" takarb'i sauran nahannunta data fasa tasha tabar wajen, tana wucewa yayi gyaran murya had'e da dawowa tagabanta ya tsaye, a tsorace ta d'ago kai jin murya da qafafuwan data gani agabanta wanda bako shakka ta tabbatar namijine, suna had'a ido dashi tayi saurin mik'ewa tsaye tare da duqar da kanta tana qoqarin rab'awa ta gefenshi tawuce, hannunsa ya d'ora ajikin bangon ya tare ta inda zata wucewa had'e da cewa.

"Ina kuma zaki jene?"

"Aji zan koma." Tafad'a har lokacin kanta na sunkuye a qasa, gyara tsayuwarsa yayi sannan yaci gaba da cewa, "to ki zauna ki qarasa cin abincinki mana."

"Naqoshi."

"Saboda nazo?"

"A'a"

"To meyasa?, Bakya son ganina anan ne?."

"A'a" tasake bashi amsa atak'aice,

"Meyasa naje nemanki kika b'uya kuma na aika akiraki kikak'i zuwa?." Shiru tayi saboda bata san ta Ina zata fara bashi amsa ba, har zai sake jefo mata tambayar yaji anbuga qararrawar komawa aji hakan yasa yace, "ki tabbatar kin jirani idan aka tashi ina son magana dake kinji ko?," yafad'a yana kallonta, kad'a masa kai tayi alamar eh sannan ya koma tahanyar daya biyo ya wuce, ahankali tajuyo tana kallonsa har ya b'ace kafin takoma saman dutsen data tashi ta zauna, hannuwanta tasa ta dafe kanta dasu wasu zaffan hawaye na zubo mata, tambayar kanta tashigayi akan meyasa malan idris ya shigo rayuwarta a daidai wannan lokacin, meyasa yafurta mata kalmar da zata saurin narkar mata da zuciya alokacin da batayi zato ko tsammani ba?, Meyasa tabari zuciyarta tafara sonsa bayan tasan batada iko akan zab'awa kanta abokin zaman da zatayi rayuwa dashi alokin?, Wani irin kuka ta fashe dashi tana mai jin rad'ad'i da kuma zugi acikin zuciyarta,

Tafi mintuna biyar zaune ahaka tana kuka har saida tayi mai isarta sannan ta tashi tawanke fuskarta da sauran ruwan dake wajen ajiye takoma cikin aji.

Ana tashi tayi saurin d'aukar jikkarta tagudu don batasan abunda yake son fad'a mata ba, Bata so yasake jifarta da wasu kalamai da zasu tunzura zuciyarta har sukaita ga bijirewa zab'in da mahaifinta yayi mata, Amma sai dai kash! cikin rashin sa'a tasamu yana nan tsaye abakin k'ofar ajinsu yana jiranta, k'ok'arin shigewa cikin 'yan uwanta d'alibai tayi tagudu yayi saurin riqo jikkarta dake sagale a kafad'arta, tsaye tayi cak batare data juyoba yace,

"Ina kuma zaki je?" Juyowa tayi saboda d'aliban dake wucewa kada suyi zargin wani abun ta jaye jikkarta ahankali daya rik'e sannan tace,

"Gida zanje." Yanda yaga wasu d'alibban sunyi tsaye suna kallonsu yasa ya shafa kansa yana fad'in muje inrakaki dama tuni ya d rufikke office d'insa ya tsaya nan zaman jiranta don yasan zata iya guduwa, babu yanda ta iya dole tabisa suka nufi gate d'in zuciyarta na harbawa da sauri da sauri, meenah dake can gefe tana jiranta na ganin haka tawuce abinta zuciyarta cike da tambayoyi akan meye tsakanin qawar tata Rashida da kuma malan Idris.

Tafiya yakeyi ahankli tamkar wanda baya son su isa gidan yana tambayarta meye dalilin da yasa gaba d'aya yau ta sauya masa ba kamar yanda suka saba ba amma takasa cemasa komai, adaidai bakin wata bushiya dake kan hanyar ya tsaya tare da cewa,

"Rashida meyasa inata yimaki magana kika yimun shiru? shin ko bakya sona ne shiyasa kika zab'i wannan hukunci a matsayin amsar da zaki bani don tabbatar mani da cewa bakya sona d'in." Yaqarasa maganar cike da damuwa a fuskarsa, da sauri ta d'ago kanta tana girgiza masa idanuwanta cike da k'walla kafin tace,

"Ko kad'an malam ba haka bane, asalima azuciyata babu wani namiji da nake so kuma nake burin qare rayuwata atare dashi kamarsa, Amma kash kazomun a qurarren lokaci, kazo alokacin da banida ikon zab'awa zuciyata abunda take so face wanda aka zab'o mata, tabbas ina sonka amma nasan wahalace kurum zansha don bazamu tab'a kasan cewa a inuwa d'aya ba" taqarasa maganar tana share hawayen da suka zubo mata a fuska, cike da mamaki yake sauraren kalamanta kafin yace

"Rashida ban fahimceki ba, kamarya bazamu lasance a inuwa d'aya dani dake ba bacin kince kina sona kuma kinsan nima Ina sonki, to meye kuma zai dakatar damu daga cimma burukanmu."

"Nauyin bakin da kayi wajen sanar dani soyayyarka har sai dana sallamawa mahaifina akan duk zab'in daya yimun, wannan shine dalilina domin jiya mahifina yazab'o mun wanda zai aura mani kuma har yabiya sadakina, yanzu haka kwanaki goma sha biyune suka ragemun nazamo mallakinsa kuma ni bazan iya hana hakan ba." Dariya yafara mata har yana riqe ciki don gaba d'aya ya fahimci batasan cewa shine mijin da take iqirarin mahaifinta ya zab'a mata ba, yana kallon yanda ranta yab'aci amma yakasa tsaida kansa har saida yayi mai isarsa sannan yace " yi hak'uri ranki shidad'e abunne dole inyi dariya.." yaqarasa maganar had'e da d'ago kansa amma ga mamakinsa sai ya hangota ashe tuni har tabar wajen tana gab da isa gida,

Da sauri ya cimmata yana kiran sunanta, tsayawa tayi tanajin zuciyarta kamar tafad'o saboda takaicin fad'a masa sirrinta da tayi Ashe dama shi ba sonta yakeyi ba tunda har ya iya yimata dariya a daidai wannan lokacin daya kamata ace dukkanin su suna cikin damuwa, qarasowa wajen yayi had'e da rik'e kunnuwansa yana gumtse dariyar dake neman sake fito masa yace "yi hak'uri matata natuba kinji"

K'walalo idanuwa awaje tayi had'e da girgiza kai irin bakasan abunda kakeyi ba tace "malan matar kafa kace? Karka manta yanzu nagama fad'a maka cewa antsayar mani da mijin da zan aura kuma har yabiya sadaki kwanaki kad'an suka rage a d'aura mana aure amma ka aza mani dariya saboda kasan Kai d'in bada gaske kake sona ba shiyasa bak damu ba, dama nasan bazaka iya aurena ba tunda banida ilimin boko kawai kafad'i hakanne don ka yaudareni."

"Subhanallahi Rashida mekike cewa hakan, nifa Ina mamakine akan yanda bakisan cewa nine mijin da zai aureki ba, kituna ke d'alibata ce, idan babu soyayya taya kike tunanin zan iya zaunawa ina bibiyarki haka? Ni da kike gani bantab'a soyayya ba kuma ban tab'a bawa wata mace dama ba tashiga rayuwata sai ke, to don me da zan yaudareki Rashida, ita soyayya Babu ruwanta da ilimi ko akasinsa kawai shiga takeyi a zukatan da ALLAH yaga cancantarsu da juna, kiyi hak'uri da banjira amsar da zaki bani ba na gabatar da kaina awajen iyayenki, wlh Rashida sonki nakeyi da gaskiya Kuma aurenki nakeso nayi kizamo mallakina kuma uwar 'ya'yana"

"Don ALLAH malan kadena fad'ar haka, kadena k'ok'arin cusamun sonka azuciya, wud'annan kalaman naka zasu iya sake jefani cikin maraicin rashinka alokacin dana zamo mallakin wani, tun ranar daka furta mani kalmar so nake shan wahala domin duk motsin da zanyi Ina tsinkayo sautin kalmomin a kunnuwana, meyasa zaka nemi sake turani cikin damuwa da wud'annan zantuka naka."

"Amma Rashida meyasa baki tambayi baba kowaye yazab'a maki?"

"Saboda bana son nasan koshi waye?"

"Koda nine Rashida?."

"Taya zaya zamana cewa kaine" tunanin fad'a mata komai yayi saboda yakawo k'arshen wannan jayayyar tasu tunda ya fahimci batada wata masaniya akan komai gyara tsayuwarsa yayi sannan yashiga labarta mata abunda yafaru ranar da yazo gidansu wanda shine silar daya kai mahaifinta aranar makarantarsu daga nanne ya gano shid'in abokin mahaifinsa da bashida lafiyane har zuwa jiya da sukaje dubosa shi kuma dama ya sanar da mahaifinsa cewa yana son yanema masa aurenta Kuma kasancewar aminaine sosai yasa mahaifinta ya amince, nan take akayi komai aka gama bisa amincewar iyayenta da kuma nasa, yana kaiwa nan ya lumfasa had'e da cewa, "to Rashida kinji abunda yafaru kuma Ina fatar zaki amince dani d'ari bisa d'ari ki aureni, cike da mamaki wata irin kunya tarufe Rashida don gaba d'aya yanda yabata labarin haka taji baba yana bawa ummashi amma arayuwarta bata tab'a kawowa shi d'inne ba, wani irin farinciki takeji aranta marar misaltuwa, ahankali tabud'e baki tare da sunkuyar da kanta k'asa tace,

"Kayi hak'uri malamina" sannan tabar wajen aguje, dariya yayi yana binta da kallo har tashige gida, wani yaro yakira tare da bashi ledar dake hannunsa yace yashiga wancan gidan yakaima Rashida sannan shi kuma yawuce zuciyarsa fal cike da farinciki.

••• ••• •••
A b'angaren yaya hawwa kuwa wato mahaifiyar Nuraddeen kasa amincewa da kuma natsuwa tayi akan komawar yaronta garin saboda yarinyar da zaya aura se take ganin kamar duk abunda yasamu yanzu ita da iyayenta zai baiwa, hakan yasa tayanke shawarar zuwa wajen wani malamin tsibbo tace tana son tunkafin ayi auren a tabashi da ita a saka mashi tsanarta ta yanda koda ranar d'aurin aurensu ne bazai yarda ya aureta ba sai a maye soyayyar da yake yimita akan 'yar qanen mahaifinsa wato muneerat, duk iya tsibbo da bugun k'asar da malamin zaiyi yayi don ganin kozai iya cin nasara Amma ya kasayi daga k'arshe sema cemata da yayi ta tashi tatafi don babu abunda zai iya, domin wannan auren ko tana so ko bataso dole sai anyisa saboda arubuce yake acikin qundin qaddarar yaronta da babu wanda ya isa ya hana ko kuma ya sauyasa hakan, Wanda kuma duk yayi yunqurin hanawa to tabbas babu ko shakka dole zai mutu don bazai iya ja da alqawarin ALLAH ba.







*_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU👏😭_*
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___15💎

Wasa wasa gini yafara girma saboda aikin akeyi ba dare ba rana, duk wani tanadi da baffa yayi sai daya fiddosa yabawa baffa usman yace ayi duk abunda yakamata kafin lokaci yayi don baya son aikin yakai har lokacin da za'a kawo amarya, acewarsa hakan yafi da ace ankawo yarinyar mutane cikin matsuwa inda bazata samu sakewa ba, sosai duk wanda ya kalli baffa cikin natsuwa zai fahimci bakad'an yake matuqar jin jiki ba, ammasaboda qarfin hali akoda yaushe qoqarin b'oye hakan yakeyi don gudun kada adakatar da auren.

Ita kuwa yaya hawwa kullum cikin masifa take wai ama faman kashewa k'asa kud'i a banza anqi atanada Amma tun daga baffa har zuwa baffa Usman Babu wanda ya tankata inba baffa Ali dake sake zugata akan ccewa inbatayi da gaskeba duk nan baffa zai qarar da kud'in gashi yana jinya abarta da wahala, sake rufe idanuwa tayi ita ala tilasa a ajiye ginin inyaso Nuraddeen d'auki shigihwa guda a cikin shigihun dake sashen nasu a gyarawa yarinyar, nan ma baris baffa yayi da ita saima cigaba da bada kud'i da yakeyi ana cigaba da aikin, tayi masifar tayi har tagaji don kanta tabari amma babu abunda ke dad'a b'ata mata rai irin yanda taga ana narkewa wajen kud'i da irin manyan shanun da yasa aka kama aka sayar, hakan ba k'aramin takaici da bak'inciki yake sata ba idan ta tuna, gashi har yanzu takasa had'a kud'in da malam bakada imani yace tahad'o wajen yimata aiki balle tasan ko meye madafarta, wata shawara ta yanke aranta na zuwa wjen baffa ko zata samu cikon kud'in da take nema wajensa, kwance ta iskoshi duk ya had'a zufa saboda wutar da aka d'auke sai zafi ya taso masa,

"A'a malan kaid'ai kake a d'akin ba kowa? Sukuma 'yan albarka sun d'auke wutar duk zafi yataso, kai ALLAH dai ya rangwanta mana" tafad'a tana jaye labulayyen taga saboda iska yashigo sannan taqaraso wajensa ta tallabosa ya tashi zaune yana fad'in "wash! bi ahankali hawwa, bayannan inajin yana yimun zafi sosai"

"Sannu malan, sai hak'uri kasan dama shi sauqi ahankali yake shiga, ALLAH dai yabaka lafiya."

"Amin hawwa." Yafad'a yana kallonta cike da mamaki don yasan wani abun take so, bai qarasa tunanin da yakeyiba yaga ta d'auko mafefeci tafara yimasa fiffita had'e da cewa, "malan kaga aurennan ya matso gashi babu fashi sai anyisa kuma inada buqatar inyi wasu 'yan gyare gyare, shine nace mezai hana ko 'yar dubu goma ka qara mani insamu in gyaggyara kafin lokacin ya qaraso" murmushi yayi don dama uasan za'a rina, indai hawwar daya sani ce Babu yanda za'ayi kaga tana yimasa wud'annan abubuwan batare da tana son wani abu daga garesa ba, d'an nisawa yayi sannan yace,

"Hawwa dubu gomafa kikace?, Yanzu ke ko hidimar gyaran inda yaronnan zai zauna da nakeyi bakya gani har zaki zomun da wannan zance, haba hawwa ai kamata yayi ace kinkawo nahannunki anqara dasu bawai kinemi karb'a ba"

"Amma naga ainima duk hidimarce zanyi ko malan, ko kafiso akawo yarinyar nan babu wani abun kirki da aka tsinana agidan?."

"To meza'ayi tunda dai naga ba kishiyarki bace balle kice haka, in Kuma maganar abubuwan da za'aci a rarrabane to kibari lokaci yayi ina sane dasu, mufa wajen ango muke ba amarya ba balle muce wata hidima zamuyi."

"Dakata malan kawai idan bazaka bayar bane kafad'amun Amma bazai yuyu kazauna kana fad'amun yanda ranka keso ba." Taqarasa maganar had'e da miqewa ta jefar da mafefecin gefe,

"Meyayi zafi haka daga magana hawwa karki manta yaronnan d'an mune mu muka haifesa kinga kuwa gaba d'aya hidimar tamuce dani dake kuma yakamata ace kema kin kawo taki gudun mawar, ni nazatama kina can kina qoqarin had'a masa lefe ashe aiki nizai qararwa." Ya iyar da zancen yana dariya, wani irin mugun tsaki taja sannan tabar d'akin, girgiza kai yayi yace "ALLAH ya shiryeki hawwa."

••• ••• •••
Ta b'angaren baba kuwa tuni yaga yakammala had'a kayan d'akin Rashida da taimakon d'an uwansa malan balarabe, haka itama umma bisa amincewar Rashida tasa 'yan uwanta sukazo tabasu sadakin Rashida da kuma abunda ALLAH ya hore mata da wanda suka kawo mata tace suje tare da rashidar duk abunda takeso ta fannin kayan kici dana aikace aikacen gida asawo mata, tun safe suka fita basu dawo ba har sai qarfe biyar na marece, sosai umma taji dad'in sayayyar da sukayo mata don Babu abunda basu siyoba sai wanda aka manta, shire shiren auren sukeyi sosai don tuni sun fara rabon minti da cingwam, soyayya kuwa tsakanin Rashida da Nuraddeen sai wanda yagani, cikin sati d'aya suka d'inke waje d'aya tamkar wasu masoyan da suka jima da shekaru suna soyayya, kullum cikin satin sai yaje wajenta fira da daddare wani lokacin kuma da marece, tuni d'aliban makaranta da kuma malamai suka sanda alaqar dake tsakanin malam Idris da Rashida wanda mafi yawansu sunsha mamakin yanda malam idris yake d'an kwalisa kuma wayayye da yasha boka zai auri Rashida wacce kaf makarantar babu wanda baisan da zaman taba saboda tsabar takkwalci, wasu kanyi fatan alkhairi gareta akan ALLAH yasa ta sanadiyarsa tamaida hankali ga karatu wasu kuma kanyi dariya had'e da cewa ya kwasarwa kansa daqiqiyar yarinya kuma jahila, duk abubuwan da mutane kefad'a suna dawo masa a kunne amma ko sau d'aya bai tab'a jin damuwa akan haka ba, yariga yaji ya gani aduk yanda Rashidarsa take yana sonta kuma yana qaunarta ahaka, ana gobe juma'a da zai koma gida yazo fira wajen Rashida da daddare bayan tafito tayi masa shimfid'a a zaure ya zauna takoma cikin gida ta kawo masa ruwa yasha sannan itama tazauna saman kujera irin tazaman gida dake facing d'insa,

"Sannu da zuwa malamina." Tafad'a tana jujjuya wayarta dake hannunta kafin shi kuma ya amsa mata da "yawwa habibty, kina lafiya?."

"Lafiya klau alhamdulillah, ya shire shiren tafiya?, gobe sai gida ko?"

"In sha ALLAH, ko Zaki rakani?." K'walalo idanuwa tayi waje had'e da cewa "na shiga uku ni 'yar babanta, rufan asiri kada kasa abugani ajaridu"

"Saboda kinje gidanmu ana saura sati d'aya bukinmu?, Ai ni kuwa sai nake ganin da nan da can duka d'ayane Babu wani abun aciki!."

"Hakane, Amma dai

Please Login or Register in order to submit comment