Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Dr yaje ya dawo yamiqawa dady kud'insa had'e da cewa.

"Dady gashi su baffa sunce ayi maka godiya sosai sunayi maka ya jiki da addu'ar ALLAH yabaka lafiya, sunce agaisheki sosai."

"Madalla duk dai kasamesu lafiya ko?"

"Alhamdulillah, kowa lafiya,"

"To ya akayi ka dawomun da kud'in?"

"Eh to, lokacin da aka yanka mana sadaki dubu saba'in ina qoqarin ciro kud'in sai shi kakan little wato baffa yaciro kud'in ya bayar, kaga kuma bazai yuyu nagardan tamasa anan ba saboda yanada haqqi akan jikansa fiye damu,."

"Eh to balaifi hakan ma yayi, haka ake son mutum yakasance mai tsayawa da kuma jajircewa ga dukkanin al-amurran ahalinsa, ubangiji ALLAH yafaranta zuciyar wannan bawan ALLAH bisa nuna godiyarsa agaresa ya maido masa da d'ansa agaresa ko zai samu farinciki."

"Amin dady, wlh dattijon nan kam mutumne, yanada matuqar qana'a da kuma zuciyar yi duk kuwa da qaramcin yalwatuwar da take da ita."

"Sosai kuwa, kaga sanin little jininsa ne kuma babu wanda yake Dole agaresa kamar shi yasa bai tsaya jiran kowa ba yayi abunda yakamata, kaga yanzu sai kaje da wud'annan kud'in kakira little idan akwai wani Abu ahannunsa ka karb'a abawa ita Fatima taje tahad'o masa lefe da sauran abubuwan daya kamata, sannan Ina son gobe kuje kaida d'an uwanka da alhaji sabiu, aminina ayankawa d'an uwanku shakur sadaki shima, idan son samune ma kuroqa amadadina akan abarshi shima nan da sati biyu saboda Ina son ayishi lokaci d'aya dana little, zan kira shi alhaji sabiun in fad'a masa inyaso sai kuje ku samesa can gidansa kutafi, shima shakur d'in ka lalubesa kaji idan akwai wani abun ahannunsa sai akarb'a ahad'o masu lefen atare don bazai yuyuba ace komai yimasu za'ayi kar akashe masu zuciya."

"To dady, Nima zanbasu dubu d'ari shida, faruk kuma yabasu hud'u sai ahad'a da abunda aka samu ahannunsu aje ahad'o lefen."

"Masha ALLAH Dr, ALLAH yayi maka albarka, haka ake son babba akoda yaushe ya zamana dashi naqasanshi zasuyi koyi, ALLAH yaqara had'a mani kawunanku baki d'aya yakareku daga sharrin maqiya."

"Amin dady, bari intafi"

Dr yafad'a had'e da miqewa yana maijin dad'in addu'o'in daya yimasa,

Bayan kwana biyu kamar yanda dady yace yayi haka yayi har sun biya sadakin da aka yankawa Shakur dubu hamsin sannan ya kuma had'a kud'ad'en wajensa dana faruq, little ma dubu d'ari biyu ya bayar da taimakon mahaifiyarsa Rashida sai Shakur shima yabada dubu d'ari uku don har soma yayi abarshi ya had'a lefensa da kansa Dr yace a'a yayi haquri anriga angama magana Fatima zataje Legos tahad'o duk abunda yakamata, yabari idan tadawo yaga abunda baiyi masa ba sai yaqara da wanda yake so, da yake akwai fahimta da girmamawa tsakaninsu sai ya hanqura, Fatima na shire shiren tafiya Legos had'o kayan lefen Rashida tafiddo da sababbin akwatuna set uku tace ga nata gudum mawa nan, basai ansayi akwatunan ba kowane qwaya hud'u da jikkunan sama guda biyu, akwatunan sunyi kyau sosai har sun gaji, kowane na ukun set aciki tacikosu da kayan kwalliya da shafe shafe masu matuqar kyau da tsada, abu ga masu abun dama sana'ar da takeyi kenan. Ko kad'an su dr da Fatima basuyi mamaki ba tunda dama tanada abunyinta don haka sukayi mata godiya sosai kai kace ba d'ansu ne tayiwa hidimar duk da dai akwai qanensu aciki amma ai yiwa kaine, su ammi da dady da umma ma sun kirata ga waya suka yimata godiya sosai tare da saka mata albarka, ita kuma hajia nafeesa gaba d'aya kusan zaucewa tayi jin abunda kefaruwa, tayi bala'in tayi maseefar har tagaji akan an munafucceta anhad'a d'anta da wacce bata dace dashi ba gaba d'aya amma babu wanda ya tankata dole tahaqura itama tafara shire shiren hidimar biki tana mai ayyana abubuwan da zasu faru da sai anyi dana sanin aurawa d'anta 'yar gidan matsiyata da akayi...

_INA GODIYA WUDANDA SUKA KIRANI DA WUDANDA SUKA YIMANI FATAN ALKHAIRI TA MESSAGE DA KUMA CHART BISA QARUWAR DA ALLAH YABAMU, MASU JEGO DA BABYS SUNA GODIYA DA ADDU'OINKU NA ALKHAIRI AGAREKU ALLAH YABAR TARE, BABU KALMAR DA ZATA IYA ISAR DA BAN HAQURINA AGAREKU, AMMA INA SO KUSANI NA SAKAKU A QUNDIN ZUCIYATA DA BAZAN IYA MANTAWA DAKU BA, HIDIMOMINNE BA KADAN BA KUMA BA AGARI 'DAYA BA SHIYASA KUKAJI SHIRUN YAYI YAWA, INA FATAR ZAKUCI GABA DA AMSAR UZURUKKANA BATARE DA KUN GAJIYA BA, NGD SOSAI ALLAH YABAR TAREWA A TSAKANINMU๐Ÿ‘๐Ÿค_



*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*๐Ÿ‘๐Ÿ˜ญ
[11/14, 22:52] Billy S Fari: ๐Ÿšถโ€โ™€๏ธ๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™‚๏ธ *SANNU SANNU*๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™‚๏ธ๐Ÿšถโ€โ™€๏ธ
๐Ÿ’Ž _Bata hana zuwa..._๐Ÿ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI๐Ÿ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*๐Ÿ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*๐Ÿ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*๐Ÿ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*โค๏ธ

_Gaisuwar fatan alkhairi agareka d'an qanina M.K, *MUHAMMAD KAREEM* haqiqa bazan tab'a iya mantawa da d'imbin kyautatawarka agareni ba no matter how in life!, kadamu da sha'anina ka tayani isar da saqona saboda kyakkyawar zuciyarka, bana haufi da tantama akan cewa samun irinka adoron duniya abune mai wahala dake buqatar sai an tona, akullum addu'ata gareka shine, ALLAH yashiga cikin lamurranka kuma yasa kafi qarfin dukkannin abunda yafi qarfinka, ALLAH ya zamemaka jigon rayuwarka aduk inda kashiga kuma yasa kazamo mai cin galaba ga dukkanin abunda ke baka tsoro, ngd ngd sosai da d'imbin karamcinka agareni ALLAH yabaka aljannah da rahamarsa๐Ÿ‘ Auntyn MK na fatar zamowarka cikin alkhairan ALLAH safe, rana, dare da dukkanin lokutan da rayuwa zata aramaka, STAY BLESS๐Ÿค_

Page___88๐Ÿ’Ž

Haka akaci gaba da shire shiren buki cikin farinciki da jin dad'i ta kowane b'angare, inda tuni matan su uncle h suka d'auki harmar gyara amarya batool ciki da wajenta, haka hajia mama da kanta take zuwa har part d'in uncle Hassan don tuni batool takoma hannunsa tayi mata duk abunda yakamata sannan ta komawarta, gaba d'aya an watsar da sha'anin Abba agefe su uncle sai shire shirensu sukeyi hankali kwance suda sauran matan gida yayin da shikuma kullum yana d'akinsa cike da baqinciki da damuwar wargaza masa lissafi da Kuma buri da 'yan uwan nasa da bayanda zaiyi dasu sukayi.

Tuni ankai lefe akwatuna takwas da jikkuna qanana guda biyu, duk wanda ya kalli lefen sai yayi sha'awar sake kallo saboda yanda ya tsaru, akwatunan kad'ai ma abun kallone balle kayan dake cikinsu, don ba qaramin qoqari Fatima tayi ba wajen tsayawa kai da qafa tahad'a kayan sosai yanda zasu burge kowa, kama daga kan suturu, takalma da jikkuna, kayan shafa, sarqoqi, turarukka, mayafai da sauransu duka tsadaddi ta saka masu matuqar kyau kuma komai iri d'aya tazuba cikin kayan lefen na little da kuma na Shakur babu wani abunda ta banbanta inba colours ba, shima ita takira kowanensu tace su kira amaren nasu su tambayi kowacensu best colour d'in data fiso, wannan shine dalilin da yasa aka samu banbanci wajen colours d'in akwatunan da kuma kayan da keciki,

Su baffa kam babu wani dogon shiri da sukeyi duk da dai anan gidansa za'a wankan ango kafin yaje d'aurin aure, wanda D.r ne yaso yayi hakan dady yace a'a yabarwa baffa domin shine yafi cancanta da yayi hakan koba komai zai rage masa rad'ad'i da damuwar da yake ciki.

Batool kuwa anbuga an raya akan ta d'anyi wani program daya kamata kafin d'aurin aure amma tace ita bata buqatar yin komai inba walima ba, itama tafiso sai bayan ankaita da kwana d'aya sai agudanar da ita acan kamar yanda annabi keyi wanda hakanma yayi daidai da ra'ayin little shima, acewarsa yafi buqatar yayiwa ALLAH godiya bisa mallaka masa abunda bai tab'a tsammanin cewa halin daya shiga ciki zai iya bari ya samesa ba da yaje garin murna su aiwatar da abubuwan da zasu jawo masu fushin ALLAH acikin rayuwar aurensu.

Suma su uncle sun amince da hakan duk da dai akwai su 'yar walimar da suka shirya bayan angama d'aurin aure wacce itace matsayin taron yinin biki da za'ayi, both ango da amarya zasu halarci walimar ana gama d'aurin auren a babban gidan gwamnati da d'aya daga cikin aminan Abba ne ya d'auki nauyinta gaba d'aya, taron zai kasance mata da maza, manya da yara zasu iya halartarsa batare da wata damuwa ba don akwai qwaqqwaran tsaro da aka tanada awajen kuma walimace da aka tanadi b'angaren mata daban na maza daban inda malamai da dama zau halarci walimar wacce za'a fara qarfe goma sha biyu na safe bayan angama d'aurin aure zuwa qarfe d'aya na rana.

Shakur kuwa da amaryarsa iman tuni sun fara gudanar da programs d'insu inda kamu suka farayi sannan dinner sai kuma walima da zasuyi ranar juma'a Dr yace suyi haquri ita ahad'a data little da za'ayi bayan ankawo amarya, basuso hakan ba amma dole suka haqura, hajia nafeesa kuwa tun tana kumburi har tagaji tadena tashige itama uwar ango Shakur ana damawa da ita.

Rashida kuwa kusan halin da baffa yashiga itama cikinsa take don a 'yan kwanankin nan da suka rage batada aiki kullum sai kuka, taso ace wannan ranar zata riske sune tare da habibynta amma sai gashi yau ita kad'ai ke gudanar da shagalin d'ansu alhalin yana raye ba mutuwa yayi ba, lura da hakan yasa Fatima ta dinga qoqarin janta cikin mutane 'yan buki da suka zo saboda takawar mata da damuwar amma duk da hakan bai hana cikin dare tazauna tayi kukanta mai isarta sannan tamiqawa ALLAH al_amurranta tare da addu'ar ko meye akan habibynta ALLAH ya yaye masa shi yakarkato hankalinshi izuwa garesu, musamman Fatima tasa aka d'unkawa little kayan cin buki kusan kala goma tsadaddi masu kyau ta d'unka masa ga wasu da Rashida itama tayi masa, shi kansa kusan kala biyar ya d'unka sai gashi ana gobe d'aurin aure Dr yazo masa da wasu shaddodi bugaggi masu shegen kyau da tsada kusan kala uku d'unkin babbar riga shida Shakur da zasu saka wajen d'aurin aure amma kowanensu kalar nasa daban, qwaya d'aya ne wata farar shadda gizna da tasha aiki har tagaji yayi masu kala d'aya da alamu su zasu saka wajen d'aurin auren, aikuwa murna da farinciki agun little ba'a magana kamar zai taka kan jariri, ji yakeyi yazama d'an gata gaba da baya baya da inyace yana fama da maraicin rashin uba akusa dashi yayi qarya saidai kawai yace yana fama da kewar rashin ganinsa ne kawai, godiya shada Rashida suka taru sunata yiwa Dr da fatima har ba adadi, Dr yayi murmushi had'e da cewa.

"Haba maman little ai inaga izuwa wannan lokacin godiya bata kamata ba a tsakaninmu saidai addu'ar ALLAH yaqara mana danqon zumunci, inhar godiya tazamo dole a tsakankaninmu to mune yadace muyi maku ita domin kun zamo mana haske acikin gida, tunda kuka shigo rayuwarmu ALLAH yaqara bud'a mana tare da saukar mana da ni'imar 'ya'ya da muka dad'e d'auke da quncin rashinsu tattare a zukatanmu, haqiqa komai na duniya yanada sanadi gashi asanadiyarku rayuwa tazo mana da sauqi, don haka dole mufaranta zukatan da suka zamo silar farincikinmu don nuna godiyarmu ga ALLAH, don haka bana buqatar irin wannan godiyar agareku ko kad'an, addu'arku kawai ta isa kumata wadatar."

"Shikenan uncle mundena, ALLAH yayi maku sakayya da farincikin duniya da kuma na lahira, mungode sosai."

Murmushi Dr yayi had'e da d'ora kansa saman kan kujera fuskarsa na kallon rufin falon yace.

"A haf! Indai kece nasani bazaki dena wannan godiyar ba data riga ta aurar maki baki."

Duk suka kwashe da dariya har da Fatima.

"Nagode Abba, ALLAH yaqara bud'a da tsawon rai" shima little yafad'a yana kallonsa yana dariya.

Miqewa Dr yayi kamar zai fita yariqo kafad'ar little dake qoqarin tashi shima had'e da d'an matsesa kad'an ya d'aga hannu kamar zai dokesa yana cewa

"Kai ko!"

'yar qara little yayi had'e da cewa.

"Awwsshh...mama!" Irin yad'anji zafi kenan!

Fatima na dariya tace,

"A'a'a'ahhh.. Dr cikamun yaro kada ka b'allashi yana shirin zama ango gobe."

"Haba matar, ina ni Ina karya wannan zabgegen saurayin naki, ko bakiga yanda yake neman kereni da tsawoba?, Anya ma tuwon gidannan kawai yake ci bada na gidan umma ba?, kodai d'aki kike sashi kina qara masa da wani bamu sani ba?"

"Eh tam, kodai nayi ai banyi laifi ba, naga wasu yini sukeyi suna d'urawa yaran nasu abinci ba dare ba rana, to meye don nima nayiwa nawa d'an jaririn haka? Ka cikashi tsautsayin angwanci nake tsoro ga yarona ko little.?"

Ba kunya little ya d'aga kai Rashida tayi murmushi had'e da d'auke kai tana qoqarin barin wajen tace.

"Wayaga god'ai god'ai, ALLAH yatsari jariri idan haka yake!,"

Yanda tayi yasa Dr sakinsa tare da bushewa da dariya yana fad'in.

"A'a maman little banda cin gira fa kusa ga ido, har yanzu takwarana jaririne, zo muje kafad'amun idan akwai sauran abubuwan da kake buqata kafin gobe." Yaja hannunsa tare da ficewa.

Rashida kuwa girgiza kai kawai tayi tana 'yar dariya taqarasa shigewarta batare da tabi takansu ba.

Gidan amare kam yasha kyau musamman na batool da gaba d'aya saida su uncle suka cika mata d'akunan da kayan d'aki masu kyau don duka kayan nawajene hatta kayan kitchens d'inta suma daga waje su Uncle h sukasa akayo odarsu, duk wata gata da suke tunanin mahaifinta nada niyar yimata sunyi mata fiye da hakan, babban falonta kad'ai saitin kujeru biyu aka zuba mata aciki, qarami kuma saiti d'aya, sai kayan gado d'aki biyu aka samata su tare da wata qatuwar katifa a d'an qaramin d'akin dake cikin gidan Wanda kamar an tanadesa ne saboda yara ko baqi da doguwar wadrobe had'e da cheat of drawer aciki, komai dai yaji Masha ALLAH, nera tasha kashi sosai don su uncle sun bud'e bakin aljifansu duk da ba itace 'ya tafarko da suka fara aurarwa agidan ba, amma amatsayinta na 'yar gaban goshin yayan nasu sun nunama duniya cewa tabbas itad'in 'yar gatace, duk wanda ya shiga gidan yafito sai kaji yana fad'in albarkacin bakinsa, wasuma har suna kiran little ya tako arziqi, hakama a b'angaren iman iyayenta sunyi qoqari matuqa sunsa mata komai daidai qarfinsu, inda Shakur ya sake zage damtse wajen ganin yasa duk abunda yaga batada shi saboda gudun 'yan gutsuri tsoma musamman da yaji mahaifiyarsa na zancen irin kayan da aka narkawa batool agidan little, har tana fad'in da yanzu suke dasu ankayi masu baqinciki saboda sonkai.

Kwanci tashi ba wuya awajen ALLAH haka ita SANNU SANNU bata hana zuwa saidai adad'e ba akai ba, abunda duk aka sawa rana kuma to tabbas qararrene, yau misalin qarfe 12:30 na rana dubban mutane suka sheda d'aurin auren NURADDEEN NURADDEEN IDRIS ALIYU (LITTLE) DA AMARYARSA FATIMA UMAR FARI, a nan anguwar sharad'a phase 1 dake cikin kano inda yasamu halartar manya manyan baqi ciki harda mataimakin gwamna jahar da ciyamoma da manyan 'yan kasuwa na cikin gida da waje don babu wanda su uncle h basu gayyato ba, kama daga kan abokanan yayan nasu(Abba) har zuwa nasu abokanan, 'yan uwa da abokan arziqi, mutanen anguwa, mutanen gari nakusa dana nesa hakan yasa anguwar tacika maqil ko masokar tsintsiya babu, duk inda ka duba manyan motocine sai huci sukeyi tamkar ana cidasu, abunka ga sanannen mutum wanda akasan dashi nan take 'yan gidan redio da television suka isa wajen suna d'aukar rahoton yanda ake gudanar da d'aurin auren, duban irin karamci da halaccin dasu dady suka yiwa jininsa yasa baffa yaroqi dady daya zamo wakilin ango ma'ana ya karb'ar masa auren batool a hannun iyayenta, shi kuma dady sai yace yabarwa baba balarabe, nan shima yace a'a yabar masa ya amsa kawai, ganin abun nasu yakoma jayayya yasa baffa Usman yace, Dr nura yaje yakarb'o masa auren sun nad'asa waliyin ango dama shiyafi dacewa don shine ubansa su duka karambanine zasuyi, ba tare da bata lokaciba kuwa nan take yaje aka gudanar da d'aurin auren dama tuni anbada sadaki don haka sai abun bai wani d'auki dogon lokaci ba.

Ana kammalawa motoci suka fara kwasar mutane zuwa d'akin taron da za'a gudanar da walima, sai dai shi baba balarabe da baffa Usman da bashar(abbaty) d'and'an Dr wanda shine babban abokin ango tunda bawani girme masa yayi ba dasu Hassan da Hussain 'ya'yan baba balarabe su suka tsaya wajen gudanar da walimar tare da ango, su kuma su dady, Dr, baffa, juyawa sukayi suka koma borno don misalin qarfe 2:30 na rana za'a d'aura auren Shakur da amaryarsa hafsat (iman) dama booking d'in jirgi sukayi ya kawosu Kuma shi zasubi su koma saboda yanayin lokaci mota bazata bari su isa dawuri ba, da da baba balarabe za'aje sai dady yace akwai buqatar ace iyayen ango sun halarci walimar, don haka sai ya tsaya akaje da baffa da mijin aunty marwiyya.

Suna Isa kai tsaye suka nufi wajen d'aurin auren Shakur don har lokaci yasoma qurewa dama dady yabar amininsa da faruk su tsaya tare da Shakur koda sunyi lattin dawowa, suna zuwa aka fara gudanar da d'aurin auren wanda anan ma Dr shiya karb'arwa qanensa shakur auren iman.

Bayan an kammala d'aurin auren mutane suka hallara zuwa qofar gidan Dr wanda sai alokacin Rashida takira Dr tafad'a masa akwai reception d'in data had'awa 'yan d'aurin aure anan gidansa idan an kammala, wanda ita ta shiryashi da kud'inta batare da sanin kowa ba si Fatima data fad'awa don komai odarsa tayo a restaurant, nan take Dr ya sanar da dady akayi sanarwa akwai reception a anguwarsu Dr. dama dakon mutane kenan kamar yanda abun yasoma zama al'ada yanzu don haka suka nufi gidan Dr wanda tuni ankafa qatuwar rumfa da kujeru awajen, wasu kuma mutanen suka tafiyarsu saboda wasu uzurukka nasu, bayan kowa yaci yasha ya qoshi shakur yashiga har cikin gida yayiwa Rashida godiya sannan shida abokanansa suka nufi gidansu iman don d'aukar hotuna.

โ€ขโ€ขโ€ข โ€ขโ€ขโ€ข โ€ขโ€ขโ€ข
A can kano kuwa saida aka gama kwashe kowa aka kai can inda za'ayi walima sannan su Uncle h suka zo suka d'auki amarya batool, matar uncle Hussain da amaryar Abba wato kishiyar hajia mama su suka riqota har zuwa cikin mota, sanye take da royal blue lace yasha fararen fulawowi masu fad'i ajikinsa anyi mata d'unkin riga da sket, sai wata qatuwar alkibba fara tas itama daga saman kai ayi mata aiki da royal blue d'in zare haka agaban rigar da bayanta an qawatashi shima, kallo d'aya zakayi mata ka hango tsantsar farincikin dake tattare da ita don takasa b'oye hakan, kasancewar ita d'in kyakkyawa ce ta ajin farko yasa bata wani bari aka cika mata fuska da irin kwalliyar nan da ake yayi ba sai dai 'yar kad'an data qara fiddo mata da kyanta na asali sai qamshi take zubawa tayi matuqar kyau tubarkallah masha ALLAH abunka ga farar macce da blue d'in abu ke matuqar amsa.

Batare da b'ata lokaci ba uncle Hussain yaja motar suka bar wajen, Abba kuwa dake can bayan corridor d'akinsa zaune bisa resting chair idanuwansa arufe miqewa yayi yakoma cikin d'aki yarufe yanajin wani irin rad'ad'i azuciyarsa, tabbas yau ya yarda da bahaushe dake cewa son zuciya b'acin zuciya..Wai yau 'yarsa da yafi so fiye da komai aduniya itace ke farinciki bayan baqin cikinsa, itace tazab'i bijire masa akan zab'inta, ta yarda tarasa gatar da yake bata taje ta zauna da wani marar asali matsiyaci da baisan darajarta ba, ta zauna da mutanen da basuda wata kima da daraja a idanuwan mutane, idan kuwa hakane dole a matsayin sa na mahaifi daya reneta cikin kulawa har takawo wannan girman yanuna mata kuskurenta na fifita wasu akansa.

A can wajen walima kuwa tunda aka shiga da ita idanuwan little ke kanta ko qyabtawa bayayi, ganin an nufo wajen da ita yasa little qoqarin miqewa da sauri abbaty yaja rigarsa yakoma ya zauna.

"Little meye haka?, Duk idanuwan taron nan fa na akanka, ina zakaje idan katashi?"

Sai alokacinma little yafahimci ko meyake son yayi yayi saurin duba gefe da gefensa yana murmushi tare da sunkuyar da kansa qasa yana sosa qeyar kansa, qasa yayi da muryarsa had'e da cewa.

"Old man." Don haka yake kiransa saboda sunan marigayi baba dake garesa.

"Ya akayi?, in baka waje zaka tafine?"

"Haba! Bahaka nake nufi ba, bakaga yanda gimbiya tayi kyau bane!, Sak tafito a gimbiyarta wanda kamata yayi ace awannan lokacin nazama srki, ya kake tunanin abun zai kasance."

Saida abbaty yaui dariya sannan yakai bakinsa wajen kunnensa had'e da cewa.

"Abun zai matuqar burgewa, Amma kayi qoqarin farkawo daga mafarkin da kakeyi inba haka ba ko yanzu kazamo sarkin marasa kunyoyi awajen nan!"

Da sauri ya juyo suka had'a ido dashi ya kad'a masa kai alamun tabbatar masa da abunda yafad'a had'e da d'an turo masa idanuwansa.

Hakan yasa yayi saurin tattaro natsuwarsa zuwa ga sauraren wa'azin, bini bini yake juyawa ya kalli batool dake can kan kujera saiti dashi a gefen da mata suke, malamai sunyi wa'azi sosai akan zamantakewar aure da kuma neman aljannah, mutuntaka da kuma girmama rayuwar d'an Adam, muhimmancin riqo da addinin da kuma kariyar da take bayarwa acikin aure, tausayi tsakanin ma'aurata da taimakekeniyar juna, yiwa juna uzuri tare da fahimtar juna, kyakkyawar zamantakewa da iyaye da kuma 'yan uwa had'i da mutanen gari, haquri, juriya da Kuma yiwa juna uzuri acikin rayuwar aure, duk da ba awaje d'aya suke zaune ba alokaci d'aya zukatansu sun quduri riqe junansu amana bisa wud'annan kyawawan nasihu da suka fito daga bakin manyan malamai tare dayin alwashin aiki da duka nasihohin da suka saurara.

Ana kammalawa mutanen da aka tanada saboda su kula da jin dad'in baqin da suka halarci taron had'e da ci da shansu suka fara zagayawa da abintayye kala kala suna a'ajiyewa tare da gorunan ruwan sha masu sanyi da kwalayen lemuna kala kala, ga kaji da snacks suma sai abunda mutum kesonci zai zab'a yaci, _๐Ÿ˜…acan nahango mutanena su aunty fareeda da meamah dasu teemah gabs anbaje anata Jan gara, aunty fareeda kam sai tura kaji takeyi acikin jikka wai zata riqawasu arfatu, gani awaje an hanani shiga sai ta taga nake samun d'auko maku rahoto, nahadiyi yawu yafi a qirga amma babu wanda yakulani sai aunty maijidda data hangoni a jikin taga ta taso saye da hijab d'inta tundaga sama har qasa riqe da take away guda biyu duka naman kajine aciki ta miqomun tana fad'in, My billy ungo kirage zafi da wannan tunda sun hanaki shigowa, kece da naci komai sai kice sai kin d'au rahoto kin fad'awa mutane shiyasa suka saka maki idanuwa suka hanaki shigowa, ALLAH idan bakibi hattaraba ko motar kai amaryar ma baza'a bari kigani ba sai dai kawai kiji ance ta haihu nace, to aunty Maijidda taimakon da ruwa da lemun mana, ga samosa can da tsinken tsire guda hud'u ki had'omun dasu, dariya tayi had'e da d'aukomun tace, yo my Billy kice ke kinfima wud'anda suka samu shigowa murewa_

Saida kowa yaci yaqoshi hani'an mari'a sannan motocin suka sake kwashesu suka mayar dasu gida wasu kuma daga nan suka wuce gidajensu suna masu yiwa ango da amarya fatan alkhairi da kuma samun zaman lafiya da zuri'a masu albarka.

Batool nakomawa gida su uncle sukace aje agyarata yanzu za'a wuce da ita gidan mijinta, ai nan take jikinta yafara rawa hawaye suka soma zubo mata tashiga dube duben inda zataga mahaifinta ahankali tana kiran sunansa.

"Abba, abba, abbanah, momy Ina abbana?"

Tafad'a tana kallon matar mahaifin nata, dafata tayi sannan tace

"Ki kwantar da hankalinki kizo muje kigyara zan kaiki har inda yake kinji ko?"

Kamar wata samna batool tace.

"To.." tare da bin bayanta.

Bayan angyarota tana tashin qamshi tako Ina ajikinta mom takaita indasu uncle h suke tanzaunar da ita, hud'uba suka sake yimata kamar yanda iyaye keyiwa 'ya'yansu idan zasuyi aure sannan sukasa aka kira hajia mama ta sake yimata.

Cikin dakiya tace.

"Batool haqiqa yau kin samu cikar burinki duk da kin sab'awa mahifinki awani b'angare, Amma Ina roqon ALLAH kada yakamaki da wannan laifin ya yafe maki, Ina roqonki da kibi mijinki sau da qafa fiye da yanda nake yiwa mahifinki, ki girmama masa iyayensa fiye da yanda kike girmama naki, kishiga gidanki da niyar bautar aure ba kasuwanci ba, kaji tsoron ALLAH, kiji tsoron ALLAH, kiji tsoron ALLAH Kuma kiriqe ibada da kuma addininki, wannan shine nasihata agareki, du abunda kika yimani kuwa nayafe maki duniya da lahira, ALLAH yayi maki albarka yabaki zuri'a d'ayyaba yakareki da sharrin mutum dana aljani da kowace irin halitta, dafa kanta tayi had'e da karanto mata addu'a ta tofa mata sannan tabar d'akin da sauri saboda kukan dake neman kuccikke mata, batool kuwa tsananin kukan da takeyi ko

Please Login or Register in order to submit comment