Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kanshi yabani damar zuwa wajensa?, don Abu sumayya ka kaini wajen Abbana Ina son ko sau d'ayane na sake ganinsa kafin ayimun wannan aikin! Ina matuqar kewar abbana sosai." Ta sake saka mashi wani kukan had'e da tusa kanta cikin qirjinsa.

A wannan karon kasa cewa komai yayi don tabbas yasan tanada gaskiya, musamman daya tuna shekarun data d'iba bata ganesa ba bayan tsananin shaquwar dake tsakaninsu, wani irin tausayinta ya rufesa tare dashi kansa da tunda yazo duniya sau d'aya yatab'a ganin mahaifinsa shima d'in ga tv ne bawai a zahiriba, bubbuga bayanta ya shigayi a hankali alamun rarrashi amma kamar yana qara cewa tayi kukan, bai tab'a sanin haka batool d'insa take da rigima ba sai yau, gaba d'aya tazame masa stubborn tayanda bama zai iya shawo kanta ba,

Sallamar mahaifiyar da yaji tasa sashi saurin cire batool d'in ajikinsa da sai faman reren kukanta takeyi ko gajiya batayi.

Da sauri yaje ya tarbota daga bakin qofar falo da take qoqarin shigowa tana fad'in.

"A'ah, a'ah Fatima har yanzu kukan kikeyi baki daina ba?, Subhanallahi meyayi zafi haka kekuwa?, Nan da lokacin da Zaki haihu ai kamar gobene ga ALLAH, don ALLAH kiyi haquri kidena wannan kukan hakan."

Rashida ta qare maganar tana qoqarin zaunawa kusa gareta.

Gaisheta little yayi ta amsa tare dasa hannuwa ta d'ago batool, yanda take kukan baqaramin tayar mata da hankali yayiba musamman da taga yanda fuskar tata tayi ja had'e da kumbure sundul.

"Ya Salam maman biyu, yau kece ahaka?, Kiyi haquri ni ban sanki da haka ba ko so kikeyi kitayar mana da hankali?"

"To yi shiru kinji ko, ya isa haka, wannan kukan naki bana sonsa yana d'aga mani hankali"

Tafad'i hakan tana share mata hawaye tare da d'ago fuskarta, "kinga yanda idanuwanki suka kumbura kuwa fatima?, Ai mugode ALLAH tunda har abban naki ya haqura ya sauko, kinga inda rabo bayan kin haihu ai zaku gana ko?"

"Gwaggo idan namutu wajen haihuwar fa?, shikenan narabu da Abbana kenan na har abada?, Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun gwaggo don ALLAH kubarni inje inga Abbana tunda haihuwar nan da sauran lokaci.."

Batool tafad'i hakan cikin wata irin disashshiyar muryar da ko fita batayi da kyau saboda kukan da takeyi.

Shiru Rashida tayi tana nazarin maganarta kafin can taji tariqo hannuwan biyu tare da durqushewa gabanta.

"Gwaggo inajin wani abu mai tsananin rad'ad'i yana kokuwa da lumfashina saboda son ganin Abbana da nakeyi, nasan irin yanda kika damu dani da d'awainiyar da kikeyi akaina a matsayinki na uwa kuma nasan bazaki gaza fahimtar irin kewa da shauqin dake tattare dani na son ganin mahaifina ba aduk tsawon shkarun nan da suka shud'e, a yau Ina roqonki daki amince mani kibada damar da zata saka nahad'u da mahaifina ko sau d'ayane kafin lokacin dazan haihe abunda ke cikina, nasan koda ta ALLAH tafaru kaina alokacin kunyimun alfarma mafi girma arayuwata."

Kallon little daya noce kai qasa hawaye na zubar masa Rashida tayi, tabbas tasan yau shima dole yatuna da nasa mahaifin wanda ko shakka babu ta tabbatar shi yasashi zubarda qwalla.

Cikin sanyin muryar dake nuna itama zuciyarta tagama karyewa tace.

"Shikenan batool, tashi ki goge hawayenki kije ki watso ruwa, ni zantafi nabar 'yan biyu su kad'ai ad'aki suna bacci kada su tashi suyimun b'arnar daba daidai ba, zanyi tunani akan haka kafin anjima kinji ko."

Taqarasa maganar had'e da dafa kanta sannan tamiqe, d'ago kan da batool zatayi sai taga itama kukan takeyi da sauri tace.

"Don Allah gwaggo kiyi haquri Idan na b'ata maki rai..."

"Ko d'aya Fatima, kije kiyi abunda nace kuma ki tabbata kinci abinci kuma kinsha maganinki."

Tana gama fad'ar haka tajuya tafita tana sharar qwalla, yau little ya matuqar bata tausayin da tana buqatar taje tayi dogon nazari koda dangin mahaifinsa ne tahad'asa dasu, idan ma zai iya daga dubu d'ari har zuwa ko nawane zata bashi yaje koda qasar da mahaifinsa yazab'i zamane ya dubosa, tabbas tasan shi yarone mai matuqar biyayya da haquri badon haka ba da tuni shi da kansa yafara neman sanin yanda zai binciko mahaifinsa.

Da yake da drivern gidan Dr tazo bata jira fitowar little ba ta shigewarta mota suka nufi gida zuciyarta namai qarfafa mata akan abunda ta quduri yi,

Little kam gaba d'aya baima san fitar taba balle yabiyota baya har saida batool ta tab'asa yayi firgigit tare da fitowa daga dogon tunanin d'aya shiga yana goge hawayen idanuwansa.

"Gwaggo fa ta tafi!"

Da sauri yamiqe yafita amma koda yaje har motar data kawota ta jima da fita ya juyo yadawo cikin gida jikinsa sanyaye.

••• ••• •••
Tuni baffa da baffa Usman suka iso gida da gawar Inna ruqayya, 'yan uwa da abokanan arziqi sai kuka sukeyi musamman idan sukaji ta hanyar data mutu, muneera kam da sauran 'yan uwanta kam sunsha kuka har sun gaji, ba'a maganar Yusuf da alokacin yana makaranta yana zana jarabawarsa ta qarshe, saida su baffa suka yita bashi baki akan ya haqura ya zauna tunda zuwansa bazai iya canza komai ba, kuma zai iyasa ya rasa damarsa awannan shekarar sannan ya haqura amma yayi kuka kamar ransa zai fita da duk wanda yagani sai ya tausaya masa,

Yaya hawwa ma kuka tayitayi tana nema mata gafarar ALLAH tare da tausayin kanta da batasan lokacin da itama tata zata risketa ba, haka gida yacika anata koke koke, Inna Bilkisu da wata maqwabciyarsu su suka yimata wanka, sunga tashin hankali matuqa wajen wankan domin wani wari gawarta ta dingayi gashi duk inda suka taba ajikinta sai fatarta tabiyosu tamkar kazar da akasa ga wuta tanine, gaba d'aya jikinta ya zimame nan take saika rantse gawarta tayi kwanakkine tasoma lalacewa, haka suka samu suka lallab'a sukayi mata wankan suka yimata sutura kowaccensu hawaye kwance da fuskarta.

Haka aka d'auki gawarta akaje akayi mata sallah akaje kaita gidanta na gaskiya, ana saka gawarta akaga wani qaton maciji baqiqirin yafito daga qasanta tare da nad'id'iye gawar gaba d'aya, kan kace me kusan mutanen da sukazo wajen sun fice aguje saboda tsananin tashin hankali, baffa ne kad'ai da baffa Usman da wasu mutane qalilan suka tsaya, haka akayita qoqarin korar macijin har aka gaji amma yaqi fita daga qarshe baffa na hawaye yace.

"Ya ubangiji kaine ka halicci bayinka kuma kai kake da iko akansu, ba'a shiga tsakaninka da bawanka akan duk hukuncin daka zartar akansa amma kai mai yafiyane tsakaninka dasu, rahamarka wadatacciya ce ga dukkanin wanda kaso sannan gafararka mai yawace ga bayinka, bamusan tsakaninka da wannan baiwar taka ba amma ALLAH kasheda duk abunda ke tsakaninmu muda ita musamman ni da nake da ikon kaina ALLAH nayafe mata duniya da lahira, ALLAH na yafe mata duniya da lahira ALLAH nayafe mata duniya da lahira Ina roqon kaima daka yafemata ya ubangijin sammai da qassai badon halinmu ba."

Yana gama fad'ar hakan yabada umurnin a rufeta haka dashi saboda basuda ikon hana abunda ALLAH ya tsaro, haka sunaji suna gani aka ida kakkad'a itace da ganyayyakin da za'a saka don babu Wanda zai iya shiga yajerasu yanda akeyi sannan aka ida tura qasa aka binneta sannan sauran mutanen suka watse kowa nafad'in albarkacin bakinsa akanta.

Baffa da baffa Usman sunjima bakin kabarin nata suna kuka tare da yimata addu'a sosai kafin sutafi,

Gari kam ko Ina ya d'auka irin yanayin mutuwar da Inna ruqayya tayi da abunda aka tarar kabarinta, wasu su tausaya mata, wasu suce haqqin baffane da suka d'auka da mijinta wasu suce haqqin jama'ane da tayita zalunta wasu kuma suce haqqin mijinta, koma dai meye musulmi bazai fidda rai ga rahamar ALLAH ba ana yimata addu'ar ALLAH ya gafarta mata.

Baffa Ali ma daya farka ka sanar dashi cewa yayi hukuncin da yadace kenan da ita tunda taqi ALLAH bayan gaskiya ta bayyana agareta, bazaice komai ba sai masu irin halinta su d'auki darasi tun kafin lokaci ya qure masu kuma su tubarwa ALLAH, kana ganin yanayin da take magana kasan cike take da baqinciki da kuma takaicinta, Saida su baffa sukayi da gaske suna bashi haquri ya yafe mata kuma ya nema mata gafarar ALLAH sannan yana kuka yace.

"Shikenan, nayafe mata a matsayina na mijinta Ina roqon dani da ita duka ALLAH kayafe mana, ALLAH ya sassauta mata ya lullub'eta da rahamarsa."

Kwanansa d'aya a asibitin aka sallamesa suka koma gida, alokacinne yayi kuka sosai don ya tabbata mai rabawa tariga tarabashi da ita musamman daya shiga d'akin sai yaji gaba d'aya kewarta takamasa dama mata da miji sai ALLAH, aranar kam baiyi bacci ba kwana yayi yana roqa mata gafarar ALLAH da kuma rahamarsa duk kuwa da rad'ad'in qurajen dake jikinsa dake damunsa.

••• ••• •••
Dr Nuraddeen kuwa kusan awarsu d'aya a filin jirgin kafin ya samu yaji ankira matafiya 'yan qasar tasa wato nageria, cike da farinciki ya isa bakin matattakalar jirgin yana d'agawa abokin nasa d'an qasar Thailand hannu don tunda ya kawosa cewa yayi bazai tafi ba sai yaga tashinsa.

Dama kai tsaye jirgin daya shiga kano zai sauka sai gashi gashi anyi sanarwa cikin jirgin cewa anaba dukkanin passinjojin ciki haquri saboda an samu matsala jirgin bazai iya qarasawa ba acan sanadiyar hazo da iska da suka yiwa sararin samaniya qawanya don haka ana bada haquri jirgin bazai iya sauka acan ba saidai a jahar borno, ko kad'an hakan beyi masa dad'i ba gashi da alama sai dare zasu sauka kuma babu wanda ya sani acan jahar balle yakwana awajensa kafin safe, tsaki yaja tare da aza kansa saman sit d'in jirgin da yake zaune yana furzar da wani iska ta bakinsa dake bayyanar da yanayin damuwar daya shiga.

Haka kuwa akayi jirgin nasu bai sauka ba sai misalin qarfe goma da rabi na dare ya fito agajiye had'e da ware hannuwansa yana shaqar iskan qasarsa, a hankali yace.

"Alhamdulillah, home sweet home!" Yanajin wani farinciki azuciyarsa alokaci d'aya kuma yanaji tana buga masa da sauri da sauri.

••• ••• •••
Rashida kuwa kusan yini tayi tana tunani had'e da kai da kawowa akan hukuncin da zuciyarta ke qoqarin yankewa, daga qarshe dai ta amince da little ya d'auki batool gobe yakaita taga mahaifinta saboda ba'asan halin ta rayuwa ba, kada suzo wani abun yafaru daga baya yayita damun zukatansu aqoqarinsu na ganin sun tirsasa zuciyarta akan abunda batada natsuwa dashi.

'Dauko wayarta tayi takira little tace yazo shida batool tana son ganinsu, cikin mintunan da basu fiye ashirin ba sai gasu sun iso kowanensu cikin yanayin da Bata so ba,

Murmushi tayi had'e da yimasu nasiha sosai akan yadda da dukkanin qaddarowar da ALLAH ya tsarowa bawansa sannan taroqi little daya yafemata akan hukuncin data yimasa na batason yayi mata maganar mahaifinsa da duk wani abun daya shafesa, tana hawaye ta kalli Batool tace.

"'yatah nafahimci damuwarki da kuma yanda kikeji a zuciyarki akan mahaifinki sanadiyar hakan yasa nima nafahimci irin jarumtar da d'ana yayi wajen yimani biyayya wacce natabbata idan kece bazaki iyaba saboda ke yarinya ce da bakisan ya ake b'oye zafi, rad'ad'i da kuma damuwa arai ba, sau da yawa nakanyi mamakin irin tsattsauran ra'ayin da kike dashi da kuma kafiya wanda yau sune suka lurar dani adalcin daya kamata nayiwa d'ana arayuwa, nagode maki sosai ALLAH yayi maki albarka ya kuma saukeki lafiya, ki kwantar da hankalinki in Sha ALLAH gobe zakije kiga mahaifinki"

"Kai kuma little Ina so yau kasani a matsayina na mahaifiyarka na amince maka uma na baka dama idan kukaje kacewa baba balarabe nace yakaika wajen dangin mahaifinka, kaje garesu na tabbata zaka rage damuwar da kakeji a zuciyarka kuma idan kundawo kanada zab'i kaje qasar malesia kanemo mahaifinka idan kanada ra'ayi idan kuma bakada nadai had'aka da danginsa kuma natabbata zasu rage maka kewarsa sosai. Suna can awani qauye da ake kira bebeji koda baba balarabe bazai samu damar kaika wajensu ba saboda yayarsa data hana tuntuni to kai kaje da kanka, idan kaje katambaya gidan marigayi aliyu gadanga, kakanka malan Idris Aliyu da 'yan uwansa naciki sai kace akaika wajensa kayi masa bayani, na tabbata zai ganeka sosai don bazai tab'a mantawa da fuskata ba, kuma kayi qoqarin had'ani dashi awaya kafin kadawo."

Atare shida Batool suka rungumeta cikin jin dad'i suna godiya musamman little dake jin tamkar ya tashi sama don jin dad'i, duk dako yasan cewa yadad'e da saninsu amma amincewar da mahaifiyarsa tayi yaje da izininta ya bayyana agaresu shiya yimasa dad'in daya tabbata akwai nasara biye a bayan hakan, batool ma harda qwallan farinciki tayi amma tad'au alwashin bazata bari asan da zuwan nata ba sai sun bar garin don kar Abba yahana.

Sun jima suna fira kafin suyi sallama da ita lokacin qarfe goma daidai na dare, dama tunda rana tayiwa su Dr bayanin komai wanda sud'inma suka qara qarfafa mata zuciyarta harta amince, hakama dady da umma takirasu ta sanar dasu, umma dai bata so hakan ba aranta amma jin dady ya qarfafawa Rashidar cewa taba little d'in dama yahad'u da dangin mahaifin nasa tunda dama shi yariga da yasan komai yasa tahaqura tace ALLAH yasa hakan shi yafi zama alkhairi,

Saida suka biya wajen Dr da fatima sukayi masu sallama suka yimasu fatan alkhairi sannan suka tafi gidan dady nanma albarka sukayita saka masu hadda ammi da hajia nafeesa sannan suka kama hanyar zuwa gida zuciyoyinsu cike fal da farinciki,

A daidai kan hanyarsu da zata kaisu gida idan sunyi yuton ta d'ayan titin sukaga mutum tsaye abakin titi da mita gefensa anbud'e gabanta da alama ta lalacene ana yimasu hannu, har zasu wuce sai kuma little ya tsaya mutumen ya d'an leqo ta gefensa had'e da cewa.

"Don ALLAH ko zaka taimaka ka ajiye wani bawan ALLAH d'aya daga cikin hotels d'in dake kan hanyar nan? Babban mutumne na d'auko daga airport yace yau yafara shigowa garinnan sai kuma taxi d'ina ta lalace."

Kallon batool yayi sannan yace.

"Ahh gaskiya da matsala, kace fa baqone agarinnan? kar fa muzo daga taimako kasaka mu a matsala."

"Haba bawan ALLAH, ALLAH dai yatsare, in Sha ALLAH babu abunda zai faru, nayarda da mutumen wlh sosai."

"Shikenan kace yazo, mudai da zuciya d'aya zamuyi."

Da gudu mutumen yaje yakira Dr Nuraddeen dake zaune cikin motar har baccin gajiya ya soma d'aukarsa, ya riqo masa jikkarsa har suka iso wajen motar su little ya bud'e masa baya ya shiga, kud'i Dr Nuraddeen yaciro aljihunsa da baisan ko nawa bane ya miqama drivern taxin cikin muryarsa mai sanyi yace.

"Gashi bawan ALLAH, nagode ALLAH yasaka da alkhairi,"

Baki bud'e drivern yasa hannu ya karb'a yana yimasa godiya tare da leqa inda little yake shima yayi masa godiyar yana cewa.

"Don ALLAH kuyi haquri ku saukesa ko hotel d'in can tacan gaba."

"Bakomai in Sha ALLAH"

Little yafad'a tare da Jan motar yabar wajen yana fad'in.

"Barka da isowa yallab'ai, awace hotel kakeso mukaika, mai sauqin kud'i ko mai tsada?"

"Duk wacce tasamu Alhamdulillah."

Dr Nuraddeen yafad'a yanajin wani irin fad'uwar gaba a tattare dashi haka shima little Saida gabansa yayi mugun fad'uwa da yaji muryarsa.

Batool ma kasa haquri tayi Saida tajuyo da qarfi tana kallon sit d'in na baya saboda yanda taji kamanceceniyar muryar tasu duk data Dr Nuraddeen tafi kauri amma da yake duhu ya mamaye motar bata iya ganin fuskar mutumenba saidai ta juya cike da mamaki aranta....






*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___101💎

A bakin wata katafariyar hotel naga little ya tsaida motarsa had'e dayin horn da sauri mai gadin dake zaune saman wata kujera a bakin gate d'in yana magana da wane dake tsaye gefensa ya ruga ya bud'e suka shiga, Saida ya daidaita tsayuwar motar tasa ya kashe sannan cikin girmamawa yace.

"Alhamdulillah maigida mun iso, Ina fatan kuma zatayi maka?"

Saida yayi Dr Nuraddeen yayi murmushi sannan yace.

"To masha ALLAH, zatayi da yardar ALLAH." Yafad'a tare da bud'e gambun qofar gefen nasa yafito had'e da jawo jikkarsa dake ajiye ya sagala a kafad'a ba tare daya damu da nauyin da take da shiba sannan ya rufe qofar yazo daidai saiti glass d'in qofar da little ke zaune had'e da miqa masa hannu, yana fad'in.

"Madallah fa, nagode sosai ALLAH yasaka da alkhairi kuma yayi albarka."

Cikin rashin kulawa little dake amsa kiran da Rashida tayi masa daidai lokacin daya tsaya shima yamiqa masa hannu sukayi musabiha tare da cewa.

"Ah ba komai maigida, ahuta lafiya saida safe" tare da tada motar yanaci gaba da amsa kiran mahaifiyarsa.

"Little badai har yanzu baku Isa gida ba bayan kasan gobe akwai tafiya mai tsawo a gabanku?"

Rashida tafad'a ranta a d'an b'ace.

"Yanzun nan can muka nufa wani bawan ALLAH ne natsaya naragewa hanya, shine ma kikaji yana yimana godiya."

"To ba laifi, adai dinga kulawa ALLAH yasa ku Isa lafiya, kudaure don ALLAH ka riqamata kuyi duk shirin daya kamata kafin safe, yanda zakuji dad'in yin sakko kaji ko?"

"To gwaggo in sha ALLAH."
Sannan ya kashe wayar daidai lokacin da take fitowa daga cikin hotel d'in.

Dr kuwa yajima tsaye yana bin motarsu da kallo aransa yanajin kamar yasan bayin ALLAHn nan, koma dai meye yaron nada kirki sosai don ya kwanta masa arai fiye da tunani, Sam bayada rawar kai irinta samarin yanzu da rashin girmamawa, ya fahimci hakanne ganin tunda ya shigo motar baiga wani abun ya had'asa da iyalinsa koda kuwa magana ce balle sayesayen kide kiden da zakaga anayi a mota ankai volume qarshe anayi ana canza batare da andamu da wud'anda ke cikin motar ba, haka yanayin yanda yake magana dashi cikin girmamawa da martabawa shiyasa yaron yaqara burgeshi sosai aransa.

Murmushi yayi sannan yasa kai yanufi cikin hotel d'in bayan yaga fitarsu don har saida motar tasu ta b'ace masa da gani sannan yabar wajen.

Akan hanyarsu tazuwa gida batool ta kalli little tace.

"Wai kasan wani abu Abu sumayya?."

"A'a gimbiyata sai kin fad'a."

Ya bata amsa had'e da juyowa yana sakar Mata murmushi,

"Wlh muryar bawan ALLAHn nan yanda kasan taka, ni da farko ma da yayi magana saida natsorata bakaga sanda najuya baya Ina son naga fuskar saba?"

Mangareta yayi ga kai had'e da cewa.

"Yawwa ai kin tuna mani, wato don kinibibi mijin wata kike qoqarin kalla, to da izinin wa kikayi hakan?, Ai tun lokacin naso mangareki albarkacinsa kikaci don kar yaga rashin kunyata shiyasa na qyaleki."

Dariya ta dingayi sosai har tana kwantar da kanta saman kujerar kafin tace.

"Oh ni batoolun Abbana!, Ashe kace abun yayi maka zafi haka, to i hak'uri ranka ya dad'e Abu sumayya abban hasssana da hussaina, gimbiyarka natuba ka yafeta bazata sake ba, Amma maganar gaskiya muryarku na yanayi sosai."

"Ko?"

Yafad'a tare da danna hancin motarsa cikin gidansu da tuni mai gadi yana ganin isowarsu taso ya wangale masu gate d'in."

Saida ya kashe motar bayan yayi parking sannan ya juyo ya kalleta had'e da cewa.

"Kinsan yanda ikon ALLAH yake, qilan qasar muce guda, hakan zata iya kasancewa amma dai ni banji hakan ba, kawai dai naji kamar na tab'a jin muryar awani wajen ne"

Ya qarasa maganar yana dariya had'e da mintsilar mata kumatu.

Dariyar itama tayi kafin tace.

"Ahaf! Ai tara na tare da goma , wani wajen yafi muryarka da kakeji kullum."

"Bawani gimbiya kindai zama mayyata kamar yanda nake mayenki shiyasa kikejin muryar kowa na shige da tawa."

Yafice yana dariya don yasan yasan ya tsokalota tunda yafad'i hakan.

Ita dai bata tankasa ba itama tasa qafa ta fito bayan ya zagayo ya bud'e mata gambun.

Kusan kwana sukayi suna shiri tare da imagining yanda tafiyar tasu zata kasance gobe zukatansu cike da farinciki.

••• ••• •••
A can qasar malesia kuwa tuni gidan labaransu na redio da talevision suka d'auki harmar labaran komawar shahararren likitannan da akafi sani da Dr N.I Aliyu qasarsa, wanda hakan baqaramin jawo hankulan manema labaran qasar yayi ba, gashi gaba d'aya bayada lambar wayar da za'a iya samunsa hannunsa balle su tuntub'esa da kanun labaran don suji dalilinsa nayin hakan bayan yafurta cewa bayada alaqa da qasar ashekarun da suka gabata, hakan kuwa ba qaramin cece kuce yajawo ba ga mutanen qasar da kuma su kansu 'yan jarida, Wanda daga qarshe har saida suka dangana da shugaban asibitin daya baro da kuma shugabar makarantar daya yayi wacce itace tazame masa tamkar uwa kuma uba aqasar, duk da dogon jawabai da bayanonan da suka samu hakan bai hanasu cigaba da yayata labaranba da kuma tofa albarkacin bakinsu ba akan hakan, aganinsu hakan da yayi tamkar butulcine yayi wa qasar tasu.

Kan kace me itama qasar tasa ta nageria sun fara qoqarin mauar masu da raddi tare da son ganin lallai sai sun gana dashi ta kowace hanya kafin isowarsa, haka wani jami'in labarai yaci gaba da bin diddigi har saida yasamu sanin ko wane jirgi ya shigo daga nan yatuntub'i jami'an jirgin suka yimasa bayanin cewa, sanadiyar hazo da gajimare da suka yima sama qawanya yasa Basu samu damar sauke pasinjojin nasu a jahar kano ba suka saukesu a jahar borno, kuma sun bashi tabbacin yana cikin jahar tunda isowar dare sukayi, idan har zai bar jahar to sai zuwa wayewar safiyar gobe idan ALLAH yakai mana rai,

Haka wannan d'an jaridar ya bawa abokanan aikinsa duk wani rahoton daya samu kafin safiyar gobe saboda shi d'an jahar adamawa ne.

Wannan daren ya zamo wani irin dare dake cike da ban al'ajabi domin kuwa a b'angaren su batool farinciki bai barsu suka runtsa idanuwa ba haka ma Rashida kwana tayi tana salloli akan ALLAH ya qaddara wannan tafiyar tasu little ta zamo alkhairi saboda yanda ta koma jin jikinta ba daidai ba, Dr Nuraddeen ma haka, d'oki da fargabar yanda zai riski iyayensa gobe basu bari ya runtsa ba, ga b'angaren' 'ya jaridu da 'yan gidan redio da talevision da sauran manema labarai suma kwana sukayi suna Shire shiren yanda zasu tarbi isowar wannan shahararren likita da labarinsa ya karad'e ko ina. Kowane b'an gare matse yake kuma qagare yake safiya tawaye don cimma cikar burin zukatansu.

••• ••• •••
A b'angaren Abba kuwa Yana gama waya da little yafad'a zaune saman katafaren gadon dake cikin d'akin tare dasa hannayensa ya dafe kai,

Kallonsa su uncle h d'aya tsayar tun d'azu sukayi had'e da tambayarsa ko lafiya.

Cikin raunin murya yace.

"Batool ce, ta dage lallai sai tazo, Kuma bana buqatar wani abun ya sameta, don haka dole nabar garin nan gobe."

"Ka natsu da kayi hakan a ranka?" Uncle Hassan yafad'a tare da zaunawa kusa dashi, jinjina masu kai kai yayi uncle Hussain dake qoqarin zama kusa dashi a d'ayan gefen yace.

"Shikenan ka kwantar da hankalinka, in Sha ALLAH gobe damu dakai duka zamu tafi, Amma Kuma kasa aranka cewa idan ALLAH yana nufin wanzuwar wani abunne akansu koda basu zoba to tabbas zai faru atawani sanadin daban saboda bawa bai isa ya kaucewa qaddararsa ba, Wanda muminin kwarai yazama dole yayi Imani da ita ya ALLAH mai kyau ko marar kyau."

Saida sukaga yad'an rage damuwa sosai sannan suka bar wajen suma suna masu addu'ar ALLAH ya kauda fitinar zamowar mafarki gaskiya.

Ita kuwa hajia mama kwana tayi tana kuka tana addu'a da Abba ya sanar da ita yanda sukayi da batool, don ta tabbata yanda take da kafiya da tsattsauran ra'ayin irin nashi ALLAH kad'aine ya isa yahana zuwan nata gobe kamar yanda tafad'a don haka ta dage wajen roqon ALLAH daya sauqa masu duk wata jarabawa da zai yimasu yanda zasu iya canyeta, haka kuma tayiwa Abba tambihi sosai akan kuskuren da yayi nafad'ar mafarki marar kyau baiyi yanda annabi yace ayiba, sosai yasake shiga damu don ta fahimtar dashi cewa alqawarin ALLAH ne duk wanda ya sab'awa umurnin manzon ALLAH yabi son zuciyarsa to tabbas zaiga ba daidaiba, wanda hakan yasa tanace da addu'a tare da qasqantar da kai ga ubangiji akan idan zai jarabcesu to yayi masu wacce imaninsu ke iya d'auka don haka sai shima Abba yayi nadamar hakan daya aikata yaci gaba da roqon yafiyar ALLAH akan sab'awa karantarwar annabi da yayi cikin rashin sani da kuma neman saussauci acikin wud'annan al-amurran.

••• ••• •••
Tun da asubar fari batool ta tashi ko nauyin cikin jikinta bataji tayi dukkanin abunda ya kamata, sannan ta tadashi suka hau shirin tafiya, koda qarfe takwas da rabi tayi

Please Login or Register in order to submit comment