Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana fad'in.

"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, astagfirullah ALLAH natuba kayafemun laifukana, ya ALLAH ka sauqaqamun wud'annan jarabawowin rayuwa kada sufi qarfin zuciyata susa na sab'a maka," kallon yya matram data kauda kai tana goge 'yan guntayen hawayen da suka zubo mata tayi.

"Gwaggo baifa sakeni ba, taya zaku rabamu?, Karku manta dani harshi zamu iya sake ahiga wani hali idan kuka yimana haka, kunada iko akaina ammashi sam bai kamata kununa iko akansa tahanyar tirsasashi ya sakeni ba."

"Kedai zaki shiga wani halin keda kike ganin bamu isa mutirsasaki akan abunda muke ganin shine alkahiri arayuwarki ba, amma bandashi tunda har ya iya mance awane irin hali zaki shigaba keda abunda ke cikinki ba ya tsallake qasarnan ya tafiyarsa duk da yasan abunda yafaru dake Amma saboda ya gyara rayuwarsa kuma ya farantawa iyayensa yatafi yabarki acan duniyar da bai masan inda kike ba don ya inganta gobensa, ba kekad'ai da ba kyanan ba hatta mu iyayenki da yasan muna nan ya wofantar damu ta hanyar tafiyarsa batare da saninmu ba, wannan shi kike tunanin har zai shiga wani hali idan aka rabaku.? Tir da wannan banzan tunani irin naki" tana gama fad'ar haka tafice d'auke da little da yayi bacci a hannunta

Tunda tafara magana Rashida ta dasqare a inda take tsaye, shin Anya maganganun da gwaggon tata ke fad'a gaskiya ne ko a'a?, Ko kwanto tashigayi akan cewa habibyn nata zai iya tafiya acikin yanayin da ake na b'atanta kuwa?, Inaaa hakan bazai yuyu ba , tabama kanta amsa had'e da miqewa tana goge hawayenta, dole yau sai tahad'u da mijinta koda hakan na nufin za'a rabata da lumfashinta ne, dole ta qaryata d'ayar zuciyarta dake neman gasgata kalaman da gwaggo tafad'a mata.

'Dakin da anan ne aka bata tashiga ta d'auko mayafinta da sauri tanufi qofar fita gidan, kota halin qaqa yau tanada buqatar zuwa ta had'u da masoyinta kuma mijinta, sand'a tafarayi gudun kada taganta ta hanata zuwa har ta isa bakin qofar gidan

Tana fitowa taci karo da Fatima aqofar gida ita da Dr ya kawota.

Cikin farinciki Fatima tarungumeta tana fad'in "'yar halak ina zakije ne ko kema kinyi kewar tamune kamar yanda mukayi?"

Ganin yanda idanuwanta sukayi jajir saboda kukan da tayi yasa Fatima cewa.

"Subhanallahi, maman boy meyake faruwa?" Hakan yasa Dr fitowa daga cikin motar yana kallonta had'e da qoqarin rufe marfin motar, qarasowa wajensu yayi kafin yace.

"Maman boy lafiya?" Yanda sukaga ta sake fashewa da wani kukan yasa Fatima riqo hannunta zata shiga cikin gidan da ita da sauri taja baya tare da tirjewa.

"Don ALLAH uncle ku kaini naga ya Nuraddeen, Ina son ganinsa Ina so nahad'u dashi Amma su baffa sunqi amincewa,"

"Kamar ya Rashida?" Dr.nura ya tambayeta cikin rashin sani.

"So sukeyi su raba aurena dashi uncle kuma Ina son mijina, bayada laifi, akan abunda yafaru amma gaba d'aya sun kasa fahimtar hakan! don ALLAH ko sau d'ayane kataimaka akaro nabiyu ka had'ani da mijina kamar yanda kahad'ani da iyayena."

Maganar takeyi tana kuka had'e da game hannayenta waje d'aya,

Alama yayiwa Fatima dasu shiga motar sannan yajuya shima yashiga had'e da tayarwa, hannunta Fatima tariqa tabud'e gambun bayan motar tasata ciki sannan tarufe itama tashiga yaja motar sukabar qofar gidan,

"Ina muka nufa?"

Ya tambayeta adaidai lokacin da suka fito qauyen.

"Bebeji." Tabashi amsa ataqaice tana goge hawayen da suka jiqa mata fuska sharkaf,

Tafiya mai d'an nisa sukayi kafin su iso gaba d'ayansu Babu wanda kecewa wani uffan, tuqi yakeyi da hannu d'aya, hannun d'aya kuma ya azoshi saman tagar qofar yariqe hab'arsa dashi ita kuma Fatima sai faman jujjuya kwalin wayar dake hannunta takeyi wacce dama itace dalilin zuwan nasu saboda kewarta da tayi mata yawa kullum cikin zancenta ita da little yasa Dr yasiyowa Rashida wayar don suriqa gaisawa sai gashi sun tarar da ita cikin wannan halin.

Bini bini take juyowa takalleta cike da tausayi kafin Dr yamiqo mata wayarsa.

"Kamomin Yaya maryam"

Scrolling contact d'insa ta farayi har takai ga lambar Yaya Maryam da yayi saving da Ya Maryam kano takirata.

Bugu d'aya ta d'aga muryarta a hargitse.

"Dr."

"Na'am, anwuni lafiya.?"

"Lafiya klw, yanzu nake zancen kiranka na nemi Rashida sama ko qasa narasa saboda nayi mata fad'a."

"Karki damu tana tare damu, dama shine kiran dana yimaki."

"Tirqashi Amma wannan yarinyar anyi shashasha, shine zata fita fisabillahi bazata fad'amun ba, gaba d'aya duk tabi ta tayarmun da hankali?."

"Kiyi haquri, Bata kyauta ba gaskiya amma yanzun nan zamu dawo tare in Sha ALLAH." Kasancewar akwai cikakkiyar yarda tsakaninsu yasa bata damu sosai ba duk da abun ya b'ata mata rai, asalima gaba d'aya ranta bai kawo mata cewa Rashida zatayi tunanin zuwa tahad'u da Nuraddeen ba balle har ta taka da kanta taje garin nasu,

Koda suka iso angama sallar isha'i suka samu gefen wani shago sukayi parking,

Fitowa tayi cikin motar suma suka biyo bayanta har suka iso inda za'a iya hango gidan,

"Inane gidan Rashida?"

"Wancanne uncle." Tafad'a tana nuna gidan da yatsa.

"To muje ko."

"A'a uncle bazan iya ba, kawai ni shi kad'ai nake son nahad'u dashi."

"Bari to naje nasa ayo mani sallama dashi.," Yafad'a tare da tunkarar gidan.

Tsaye kawai take duk qafafuwanta sunyi sanyi tanaji tamkar basu imata, kallon anguwar takeyi d'aya bayan d'aya,

Kafin tahango Yusuf tafe yanufo inda suke gefen wani tsoho dake saida kalanzir saman d'an teburinsa,

"Lado abani kalanzir na naira ashirin?"

"Ahhh... yusufa d'an gidan yayansa nura, Wai ina yashige ne kwana biyu nadena ganinsa.?"

"Laah...ashe lado bakasan yaje qasar waje ba?"

"Kai yusufa!, Kace wlh."

"Wlh lado da gaske nakeyi."

"Kai ALLAH ban yarda da kaiba, shi nuran d'an mahaukaciya ne da zaibar qasar nan bayan matarsa da tsohon ciki tab'ata, sai kace wanda bedamu da ita ba,"

"To ni kabani kalanzir d'ina kada innar mu tabugeni, ai sai katambyi mutane kaji, yanacan yaje k'aro karatunsa."

"Tirqashi! Amma gaskiya be kyauta ba."

Kukan da Rashida ke qoqarin dannewa ne yaci qarfinta had'e da kucce mata.

Da sauri Yusuf daya miqa hannu zai karb'i kalanzir d'in da lado kemiqo masa suka d'ago kai tare jin kukan da suka jiyo agefensu.

"Yaa rasulu manzon ALLAH, ke baiwar ALLAH lafiya.?"

Lado yafad'a had'e da sakin kalanzir d'in yana kallon Fatima da Rashida dake tsaye hasken k'wan shago na yadosu, da hannu Yusuf ya shiga nuna Rashida don fuskarta bazata tab'a b'oye masa ba aduk inda tashiga, kasa magana yayi sai faman ja da baya yana fad'in.

"Aun..aunt..auntyyy.."
Yaruga aguje yabar wajen had'e da nufar gida yana k'walawa su baffa....






*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[11/14, 22:52] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___60πŸ’Ž

Tunda Rashida ta tabbatar da cewa Nuraddeen yabar qasar taji gaba d'aya komai na duniya ya tsaya mata, Babu abunda ke mata dad'i haka kuma babu abunda ke burgeta arayuwar duniya, kallo d'aya zakayi mata kafahimci tsantsar damuwar da take ciki saboda yanda duk tabi ta susuce, batada wani aike sai kuka, na safe daban na rana daban hakama na dare daban, duk tabi tarame tayi baqi, rashin iyayenta namatuqar damunta musamman yanzu da take cikin wani hali marar misaltuwa duk da kuwa Yaya maryam da baffa sunyi qoqarin nuna mata sun sauko daga dokin naqin da suka hau saboda yanda sukaga tana nemanfita hayyacinta sai dai aransu ba haka bane.

Baffa Usman kuwa da baffa basu san abunda kefaruwa ba , gaba d'aya sun maida hankalinsu kocokom ga nemawa Yaya hawwa magani har zuwa lokacin da aka d'ibar masu nazuwa a d'auketa, ranar nayi misalin qarfe sha biyu na rana motar asibitin ta dira abakin qofar gidansu baffa, lokacin suna tsaitsaye da alamu dama suna jiran dakon isowarsune tun d'azu, wasu ma'aikatan lafiyane su biyar da kuma wani mutum yasha suit, da alama shine babbansu, Saida suka gaisa dasu sannan baffa Usman yayi masu jagora zuwa cikin gidan inda Yaya hawwa take ya bud'e masu d'akin,

Cikin qwarewar aikinsu suka shiga cikin d'akin yayainda Yaya hawwa tayi wani irin kukan kura tayo kansu.

Ba qaramar wahala suka shaba kafin su samu damar rirriqeta tana keta wani irin ihu daya karad'e ko ina tana fizge fizge, sai da sukayi da gaske sannan suka sakata cikin mota suma suka shiga.

Wajen motar baffa yatako yana hango ta glass d'in motar yanda jami'an lafiya ke qoqarin yimata allurar da zatasa tayi bacci kafin su isa yasa hannu ya goge k'wallan da suka zubo masa a idanuwansa yana mai addu'ar Allah yabata lafiya, gaban motar ya koma saiti gefen driver inda babbansu yake ya saukar da glass d'in motar yamiqa masa hannu suka sake gaisawa yayi masu godiya sannan motarsu tabar wajen, ahankali dandazon mutanen da suka taru qofar gidan suka fara watsewa cike da tausayin halin da sukaga anfito da Yaya hawwa aciki saboda yanda tayi baqi da rama sosai fiye da tunani, inba wanda yasanta sosai ba bazaka tab'a ganinta kace itace ba.

Adai dai lokacin baffa Ali yadawo daga gona rataye da fartanyarsa a kafad'a yana rera 'yan waqoqinsa, yana hango su baffa Usman ya murtuqe fuska tunkafin ya iso har zai wuce abunsa sai kuma yadawo baya had'e da kallon gungun wasu yara dake tsaye abakin gidan.

"Kai me kukeyi anan naga kun had'e kanu kamar d'iyan awaki?"

"Wlh Yaya hawwa ce akafito da ita za'a kaita asibitin mahaukata abun gwanin tausayi."

Wani yarone daga cikinsu yafad'a hannunsa na tallab'e da kuncinsa.

Batare da baffa Ali yadamu da 'yan uwansa dake wajen ba yayi tsaki had'e da cewa.

"ALLAH yaraka taki gona, ai mun huta da gayyar tsiya kullum ana hanamu bacci ana tsorata iyalinmu da yaranmu,"

Juyowa baffa yayi ransa amatuqar b'ace yace.

"Karka damu Aliyu, SANNU SANNU ai bata hana zuwa...kamar dai yanda hawwa ke girbar abunda tayi haka kaima zaka girbi naka in alkhairi in kuma sharran."

Guntun tsaki yaja batare daya damu da abunda baffa yace masa ba yashige cikin gida yana cigaba da rera 'yan waqoqinsa...

β€’β€’β€’ β€’β€’β€’ β€’β€’β€’
Kimanin satinsu Dr nura uku kenan da dawowa kano kawo Rashida, wanda sun jima hakanne sanadiyar Fatima data nace akan suyi zamansu sai qarshen wata saisu koma gaba d'aya tunda dama yakusa d'aukar hutu (annual leave), saidai hakan bazai yuyu ba saboda maganin little Nuraddeen da za'a karb'o masa gashi bayason idan yaje qarshen watan yasake dawowa har sai hutunsa yaqare,

Hakan yasa cikin satin da zasu koma kafin ranar tazo yayi sakko yaje borno ya karb'owa little maganinsa wanda idan yasha shine naqarshe,

Yana isa garin kai tsaye yawuce gidan iyayensa saboda akwai saqon da mahaifiyarsa tace yaje ya karb'owa Fatima na maganin da takesha,

Yana isa yatarar da mahaifinsa shima yadawo lokacin yana zaune kan dining table yana cin abinci, qarasawa yayi bakinsa d'auke da sallama yaje ya d'an russuna gabansa had'e da gaishesa.

Sake da fuska yamiqa masa hannu yana fad'in.

"A'a bokan turawa saukar yaushe?"

"Yanzunnan dady, mun sameku lafiya?"

"Lafiya klw dady, ya kasuwar."

"Kasuwa Alhamdulillah muna nan muna tattab'awa musanmman sabon shagon dana bud'e, abun Masha ALLAH gaskiya."

"ALLAH yaqaro bud'emai albarka, dady ammie fa?"

"Tana ciki, yanzu tabar nan inaga ankirata ne awaya."

Yana rufe baki tana fitowa, babbar mace ce mai cikar zati da kamala, farar mace ce sosai mai yawan fara'a da son mutane, kallo d'aya zakayi mata kafahimci hutu na tattare da ita, da sauri yanufi wajenta had'e da gaishesa, rungumosa tayi ajiki kai kace bashine d'anta nafarin ba suka nufo wajen dadyn tana fad'in.

"Oyoyo mutanen kano ta dabo tumbin giwa yaro koda mekazo anfika, Amma inada tabbaci akan ba'afi yaron nawa ba saidai ayi gogayya dashi ko ba haka ba alhaji?" Taqarasa maganar had'e da jawo kujera ta zaunar da Dr nura.

Dariya sukasa shida dady kafin yace.

"Mezance hajia fareeda tunda kinriga kin fad'a, ai ko ba haka bane ta zauna, uwa da d'anta kome tace akansa ai babu wanda ya isa musa mata." Suka sake sa dariya.

"Son ya hanya da 'yata Ina fatar kuna lafiya?"

"Lafiya klw ammie, tace agaisheki sosai."

"Muna amsawa, injin tana amfani da maganin yanda yakamata? Nasan halinku na 'yan boko baku fiye ba maganin nan namu na gargajiya muhimmanci ba.?"

"Ahh ammie banda Fatima tana kulawa sosai da lokutan shansa yanda yakamata,"

"ALLAH sarki baiwar ALLAH, ALLAH yasa adace, yarinyar nabani tausayi sosai, tanada matauqar juriya da haquri wlh, badon haka ba idan irin 'yan matan nan namu na zamani ne da yanxu tabi ta tayar maka da hankali dama kanta ga abunda Babu mai iya baku sai ALLAH, kuci gaba da haquri, in Sha ALLAH lokaci nazuwa da ijaba zata sauka, muna nan muna yimaku addu'a,"

"Hakane nura! Kaci gaba da haquri kana kwantarwa da iyainka hankali, da SANNU ALLAH zai duba lamurranku ya share maku hawayenku, akoda yaushe addu'ar mu natare dake."

"Dady, ammie nagode da kulawar da kuke bamu tare da addu'o'inku, koda ALLAH bai bamu aihuwa ba ku kad'ai kun isa farinciki agareni domin babu abunda yakai samun nagartaccin iyaye aduniya muhimmanci, sune kad'ai farincikin da idan katuna zaya dad'a sanyaya maka zuciya."

Daidai lokacin umma tafito daga kitchen don tagama kammala komai zata koma part d'insu, "umma gafa d'anki da d'azu nake fad'a maki cewa yana kan hanya ya iso."

Dama tuni umma tadawo wajen hajia fareeda da aiki kamar yanda dady ya umurta kuma tanajin dad'in aiki da ita sosai don kusan komai atare sukeyi cikin girmamawa, sab'anin hajia nafeesa da saidai ta nad'e qafafuwa tana bada umurni, murmushi tayi had'e da qarasowa wajen tace.

"Sannu da zuwa.." Bata qarasa ba sakamakon juyowar da yayi suka had'a ido, cikin i'ina tace.

"Kaine?"

"A'a baba kece anan kuma.?"

Yafad'a yana nuna baba da hannu, binsu da kallo su ammie sukayi cike da mamakin ganin sunsan juna, nan Dr nura yabasu labarin ynda yasanta har yana qarawa da tambayarta cewa.

"Baba ina wanda naganku tare."

"Yana can shagon da alhaji yabashi yariqa kulawa dashi, ai shi d'in mijinane"

Tafad'a akunyace tare da komawa kitchen,

Dariya su dady sukayi kafin sushiga bashi labarin zuwansu ataqaice amma basu fad'a masa cewa sanadiyar b'atan 'yarsu sukazo garin ba.

Dawowa tayi d'auke da wani qaton try da suka shirya masa abincin da yafiso ita da ammie wato tuwon semolina da miyar kub'ewa d'anye, da sauri ammie taje tariqo mata tana fad'in.

"Kai umma ai dabari kikayi nazo na d'auko masa." Sannan ta ajiye abincin agabansa, yana bud'awa yaga best food d'insa ba shiri yature jikkar gabansa yana qoqarin fara zubawa yaci, d'an mangararsa ammie tayi aqeyar kai tana fad'in.

"Bazaka bari kafara watso ruwa ba.?"

"Awshh....ammie bara nagama cin abinci tukuna, ALLAH yawuna har sun tsinke."

Yafad'a yana shafa inda ta mangaresa, dariya umma dake tsaye tana kallonsu cike da burgewa tayi tana goge 'yan hawayen da suka zubo mata tunawa da tata 'yar sannan tabar wajen.

Bayan ya kammala cin abincinsa yaje ya watso ruwa sannan yaje wajen hajia nafeesa matar babansa ya gaisheta daga can kuma yawuce wajen malamin da yake karb'o maganin Little Nuraddeen awajensa ya karb'o sannan yadawo gida lokacin kusan qarfe biyu na rana yawuce kai tsaye d'akin ammie tana zaune tana tilawar alqur'ani, Saida takai aya sannan tarufe taje ta d'auko wata leda cikin drower d'in madubi tadawo inda yake zaune gefen bedside d'inta ita kuma ta zauna agefen gado.

"Ungo wannan ka kaimata, don ALLAH kace takula da shansa tunda safe kafin taci komai, shi wannan ganyen koba don haihuwa ba yanada kyau adinga tafasashi ana sha da ruwan tea kafin aci komai da safe, yana wanke duk wata datti dake cikin jikin mutum har zuwa mara, hakama yana wanke dattin mahaifa sosai, hatta wannan tumbin da kake ganin kafara azawa idan kuna shansa tare zaya rage sosai, don haka kukula, shi magani da kuke gani dace ne bamusan ta ina ALLAH zaisa adace ba, ALLAH yabamu rayayyi masu albarka."

"Amin ammie, amma shi wannan ganyen mene ammie?"

"Ganyen guava ne."

"Guava fa kikace ammie!, Wannan guava dai dana sani."

"Eh mana, Ina tabbatar maki idan kuka gane shan tea da ita, bazaku tab'a bari ya tsinke maku va agida, da kanku zaku kirani kusanar dani amfanin da kukaji tayi maku ajiki."

"To ammie shikenan mungode."

"Yawwa ALLAH yayi albarka kuma yakiyaye hanya."

"Amin ngd."

Yafad'a had'e da miqewa ya kama hanyar komawa kano bayan yayi sallama da mahaifinsa.

β€’β€’β€’ β€’β€’β€’ β€’β€’β€’
Kimanin kwanaki uku Yusuf ya d'auka kwance yana fama da zazzab'i, baya fita ko ina daga d'aki sai d'aki har ALLAH yasa yasamu sauqi, baffansa nafita zuwa gona ya iske baba Usman a d'aki yana shiryawa zaije gidan baffa zasu koma wajen baba balarabe su sake bashi haquri akan abunda yafaru, dama Inna ruqayya tafita anguwa Inna Bilkisu kuwa tana waje tana share wajen dabbobinta da yayi datti, baffa Usman na gyara zaman hularsa akai yaji anriqo rigarsa, juyowa yayi had'e da cewa.

"A'a Yusuf ka taso? Yajikin naka da sauqi ko?"

"Eh baffa Usman naji sauqi sosai."

"Masha ALLAH, ALLAH yaqara sauqi , to ya akayi ne." Duba gefe da gefe yayi sannan ya leqa ta qofar shigowa d'aki yaga ba kowa ya matso dab da inda baffa yake zaune a gefen gado a kunnensa yace.

"Baffa aunty Rashida matar ya nura tadawo, naganta da idona Amma karka gayawa baffana."

A razane baffa Usman yamiqe had'e da cewa.

"Kai Yusuf bana son shashanci, a Ina kaganta ne?"

Hannu Yusuf yasa had'e da rufe baki yana qwalalo idanuwa ya juya yana kallon qofa,

Furzar da iska baffa Usman yayi had'e da kwantar da hankalinsa ya matso inda Yusuf ya dafa kafad'unsa.

"Yusuf ka kwantar da hankalinka, Babu wanda zaiji kaji ko?, Yimun bayani a Ina kaganeta."

"Bana son baffana yaji yace idan nafad'a nima zai b'addani kuma bazai sake bani abinci ba."

"Bazaiji ba nayi maka alqawari kaji ko?"

Nan Yusuf yayiwa bayanin baffa komai had'e da roqonsa don ALLAH kada yafad'awa baffansa shi yafad'a masa, jikinsa na rawa yabar d'akin shima baffa Usman jikinsa asanyaye yabar gidan yanufi wajen baffa yayi masa bayanin abunda Yusuf yafad'a masa, yayi matuqar shan mamakin cewa wai har yanzu baffa ali na adawa da Rashida, tsanar da yakeyi masu har takai girman da zai sake cillasu awata damuwar, tare suka fito suka nufi gidan lado mai kalanzir suka tambayesa abunda yafaru ranar tsakaninsa da Yusuf na zancen ganin matar da Yusuf ya tabbatar masu da cewa Rashida ce.

Sun samu amsa daidai da zancen Yusuf don haka ba b'ata lokaci suka nufi gidan baba balarabe.

Sai yanzu baffa yasake fahimtar dalilin fushin da baba balarabe yayi sosai, ya tabbata akwai maganganu da baffa Ali yafad'a masa marasa dad'i wud'anda sune suka tunzurasa, haqiqa ko shine malan balarabe zai d'au zafi fiyema da hakan domin d'a baifi d'a ba.

Duk qoqarin da yakamata su baffa suyi wajen yiwa baba balarabe bayani yanda zai fahimci komai sunyi amma gaba d'aya Sam yaqi saurararsu balle yafahimce su, da suka d'auko masa zancen ganin Rashi da akace anyi kuwa buga kai yayi ga qasa yace shi baima san da zancen ba, Dole suka haqura suka koma gida, kusan ko yaushe cikin kiransa suke awaya da isko shi gida suna son tabbar da zancen amma ko kad'an yaqi barin hanya ko kad'ance da zasu iya gane hakan, musamman suka turo abokanansu da mutanen da suke da kima abashi haquri ko zai sauko yafad'a masu cewa Rashi tadawo.

Amma baba balarabe yakafe akan bashida masaniyar hakan, ayanayin yanda yake sakin fuska da tarbar wud'anda suke turowa yasa bazasuqi amincewa da zancensa ba, gaba d'aya baffa yasake shiga damuwa har ya soma ramewa.

A kullum bayada lokacin kansa saina bin hanyar zuwa gidan baba balarabe, baya can baya gidan Yaya Maryam, hakama aunty marwiyya, duk inda yake sa ran zai samu tabbacin labarin zuwan Rashida yana biye dashi Amma k sunqi bud'e baki sufad'a masa gaskiya.

Duk zafin da aunty marwiyya ta d'auka akan maganar saida yasoma bata tausayi saboda irin yanda taga yana kaida komo gidanta shida d'an uwansa kawai saboda su sani ko Rashida ta dawo amma idan ta tuna cewa fada masu shine zai sake zamowa silar da Rashida zata koma acikin ahalinsu da Babu zuciyar tausayi ko Imani atattare da wasunsu sai taji zuciyarta ta karye, musamman idan ta tuna da rashin 'yar uwarta da tayi akusa da ita ta dalilin haka.

Ganin irin kai da komowar da baffa keyi a tsakankanin gidajen nasu su uku yasa suka yanke shawarar had'a Rashida dasu Dr nura su koma da ita acan borno domin hakan shi zai fimasu kwanciyar hankali tunda sunsan inda take, koba komai itama zata d'an rage damuwar da take ciki tunda har yau taqi sakin jiki kullum cikin qunci take.

Wata nakaiwa qarshe Dr nura sunzo yimasu bankwana yaya maryam takira baba balarabe da aunty marwiyya suka roqesa akan buqatarsu tasu koma da Rashi acan yafi masu kwanciyar hankali indai hakan bazai zamo takurawa agaresu ba har zuwa lokacin da ALLAH zai qaddari dawowar iyayenta,

Sun matuqar jin dad'i yanda suka basu yarda haka tare da amice masu akan 'yar tasu duk da babu wata alaqa inbata musulunci ba a tsakaninsu musamman Fatima da tunkafin Dr nura ya amsa cewa sun amince tace.

"Babu wata matsala sun amince ba komai." Har tana karb'ar little a hannun aunty marwiyya cike da farinciki.

Rashida kuwa babu yanda ta iya domin ta dad'e da tabbatarwa kanta da cewa batada wani sauran iko akanta tunda tarasa iyayenta akusa da ita, komai yanzu sai yanda akayi da ita, sunjima agidan kafin Yaya maryam taje ta har had'o mata kayanta dana little, aranar ma Rashida tasha kukan rashin iyayenta sosai tare da fawwala dukanin al'amurranta ga ALLAH tana mai addu'ar ALLAH yasa wannan qaddarar da zata d'auketa ta maidata garin da tabaro tazame mata alkhairi, ahalin yanzu ko kad'an bata ganin laifin tafiyar Nuraddeen, saidai takanji wani irin zafi da qunci azuciyarta Idan ta tuna dashi wanda batasan dalilin faruwar hakan ba.

Haka sukayita bata baki da rarrashinta sannan suka d'auki hanyar komawa borno ita dasu Dr.

Gidan iyayenta kuwa tuni Yaya Maryam da baba balarabe suka yanke shawarar saka 'yan haya aciki kafin randa ALLAH zai dawo dasu sai suna jujjuya masu kud'in...









*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[11/14, 22:52] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___61πŸ’Ž

Ba qaramar rawar gani Dr nura da Fatima ke takawa ba wajen kula da farinciki da kuma walwalar Rashida ba ita da d'anta, duk wani abu da take buqata basa bari har saita kai ga furta cewa tana so suke yimata, mutanene su day sukasan haqqin zaman takewa da kuma sanin kimar d'an Adam, ko kad'an abunsu baya rufe masu idanuwa balle ya had'a ka dasu, sosai suka nuna mata cewa dasu da ita duk abu d'aya ne babu wani banbanci don haka tanada 'yancin tayi rayuwarta yanda takeso acikin gidan ita da yaronta matuqar hakan bai sab'awa musulunci ba.

Hakan yasa tafara sakewa kamar yanda suke buqata saboda taga tasasu farinciki yanda suke qoqarin sata itama.

Sunada sati d'aya da dawowa Dr nura yaje ya sanar da iyayensa batun zaman Rashida agidansa da irin taimakon da yayi mata wanda daga qarshe har danginta suka roqesa akan tazauna wajensu nawani d'an lokaci kafin ALLAH yadawo da mijinta lafiya.

Sun jinjina al-amarin sosai har ammie nayi masa fad'an meyasa tun farkon faruwar al'amarin bai sanar dasu ba sai yanzu, gashi sanadiyar banzar tunaninsa ya haifar mata da rasa iyayenta wanda da ansanar dasu dawuri da duk haka bata faru ba, haquri yabata tare da fad'a mata iya qoqarin yin hakan da yayi alokacin amma ALLAH beyarda ba sanadiyar wannan rubutacciyar qaddarar daya tsaro masu.

Dady kuwa tunda Dr yafara bada labarin yake ganin kamancece niyarsa da nasu umma duk da dai bakomai yafad'a masu ba, jin dayayi Dr nura ya ambaci cewa ita mijin nata na qasar waje yaje karatu yasa ya janye hankalinsa daga wannan tunanin, a tsammaninsa ma yarinyar 'yar masu kud'ice don haka sai dai kawai ya nuna masa yanda yaji dad'in taimakon da yayi da kuma qara qarfafa masa wajen sanin kima da kuma darajar d'an Adam, ya sake horonsa akan ya taimaki duk wani mabuqaci shima ALLAH zai taimakesa domin shi alkhairi aduk inda kayishi to tabbas zai biyoka aduk inda kake.

Haka ammie itama ta sake gargad'insa akan yariqa sanar dasu duk wani abu dayasan yinsa zai iya basa

Please Login or Register in order to submit comment