Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan maganar agabanta ba,

"Yi haquri muneera, ai zancen yanda za'ayi aurenne muke tattaunawa." Inna ruqayya tafad'a had'e da riqo hannunta, turo manyan lab'b'anta tayi cike da rashin iya magana tace,

"Wallahi Inna qaryane, ai duk Ina jinku maganine zakuyi ko korar masa mata, yo a maimakon haka kuyi mani magani na auresa kurum.." da sauri tajawota had'e da toshe mata baki shi kuma baffa Ali ya dafe kai don yasan ALLAH kad'ai ke hana muneera taje ta watsa wannan magana, abunda basu sani ba hatta Yusuf idanuwansa biyu basuyi bacci ba qannensa ne kawai baccin ya d'auka. "Shiii muneera kirufa mana asiri kidena wannan zancen kada wani yajiki, yanzu da kike wannan maganar mu ba yarinyar mukeso tafara fita ba sai ke kuma ki auresa, kinjimun shashashar yarinya."
Inna ruqayya tafad'i hakan tana murgud'e mata bakin da hannu data toshe mata shi.

"Kai Inna da zafi." Muneer tafad'a itama tana jaye mata hannun sannan taci gaba da cewa, "ni ku aura munshi a haka ko mata dubu garesa ALLAH zan auresa balle d'aya, so kukeyi sai na sake shekarewa aci gaba da cemun kwancen gidansu nura wlh ALLAH ni nagaji da jira."
Taqarasa maganar tana fashewa da kuka, takaici ne yarufe baffa Ali kamar yatashi ya rufeta da duka shima, Amma yasan hakan na iyasa tafallasa komai don ba qaramar sakarya bace, lallashinta suka shigayi tare da tabbatar mata da cewa itama wannan shekarar kota halin qaqa saita auri masoyinta ya nura sannan suka samu tawuce d'akinta takwanta, fad'a baffa Ali ya shiga yiwa Inna ruqayya akan meyasa bata sanar masa da muneera na d'akinba ai da bai d'auko zancenba agabanta.

"Yo kukan da taci yau ai sanin matakin da aka d'auka akansa kad'ai zaisa taji sanyi azuciyarta shiyasa nace ta zauna har kadawo."
Tsaki yayi had'e da juyawarsa ya kwanta cike da takaicinta da ita har 'yar tata.

A 'bangaren su Nuraddeen kuwa ana gama sallar isha'i yadawo gida, d'akin baffa ya shiga ya gaishesa tare da yimasa ya jiki lokacin suna zaune shida Rashida tagama b'ab'balla masa maganinsa yasha bayan tazuba masa abinci yaci tana karanta masa wasu addu'o'in dake cikin littafin (adda'u wad dawab) littafin daya qunshi nau'o'in cutuka da kuma kalolin maganukkan da za'asha ayi amfani dasu don samun waraka, d'aya daga cikinsu take fad'awa baffa alokacin, wuri yanema a gefe ya zauna yan sauraren bayanin da take yiwa baffa. "Baffa kaga wannan addu'ar ana karantata ga duk wanda ciwo yayi masa tsanani kuma aka rasa gano kowane irin ciwone ke damunsa, sai a nemi ruwa masu kyau acikin madaidaicin kwanon shan ruwa, sai a nemo kanwa da gishiri a zuba aciki, anemo albasa itama a yayyanka ta aciki sai marar lafiyar yasa duka hannayensa acikin ruwan bayan ya saka duk wud'ancan abubuwan da aka buqata sai ya karanta qula quzzai (falaq, nasi da kuma ikhlas) kenan, sannan yakaranta ayatul kursiyu karatun na sauka acikin ruwan da hannayensa ke ciki, sannan sai ya karanta wannan addu'ar kamar haka
( _Bismillahi arqiq, wallahu yashfik, min kulli da'in mardud, wamin kulli aynin au aynil hak'k'imu ALLAHU yashfik, allahummah rabbannas, ashfi bil ba'as washfi antashshafi'i laa shifa'a illa shifa'uka, shifaa'allahu laa yugadirus saqama_).
sai atofa acikin ruwan acire hannayen daga ciki, sai a d'ebi ruwan marar lafiyar yasha sannan ya tauna albasar dake ciki, asake d'iba yayo wanka dasu sauran sai a dinga watsawa ko ina a cikin d'akin da yake ciki ana fad'in ( _ikhrij aduwwallah_) har ruwan su qare, to da yardar ALLAH duk marar lafiyar da aka dage anayi masa haka ko ya dage da kansa yanayi zai samu sauqi da ikon ALLAH, kaga zuwa gobe idan ALLAH yakai ranmu sai mufara baffa saboda ba'asan in da dace yake ba ko ba haka ba."

Cike da farinciki baffa ya dafa kanta had'e da cewa. "Hakane 'yata, ALLAH yayi maki albarka kuma yasa adace."

"Amin baffa."

Tafad'a tana rufe littafin fuskarta d'auke da murmushi, juyowa tayi gefen da Nuraddeen ke zaune ta gaishesa had'e da yimasa sannu da zuwa sannan tamik'e tabar d'akin tana yiwa baffa seda safe.

Bin bayanta da kallo baffa yayi kafin yayi ajiyar zuciya yace. "Alhamdulillahillazi bini'imatihi tatimmusswalihat, haqiqi Nuraddeen Ina tayaka murna da kuma alfaharin zab'in da kayowa 'ya'yanka, banida shakku akan cewa ALLAH yagama mallaka maka rabin addininka yanzu yarage wajenka kanemi rabin don samun kyakkyawar makoma, Ina roqon ALLAH nima daya dubi zuciyata ya shirya mani mahifiyarka, bansan meyake damunta ba da har zata d'auki karan tsana ta azawa wannan nagartacciyar yarinya wacce samunta tamkar samun zinarine acikin qasa, narasa wane irin zunubi na aikata da har iyalina ta kasance ahaka, ubangiji ALLAH kaganar da ita tun aduniya basai ranar da nadama baza tayi amfani ba." Nisawa nuraddin yayi yana d'an muskutawa sannan yace, "Amin baffa."
Sun d'an jima kad'an suna fira kafin yayi masa saida safe snadiyar baffa Usman daya shigo d'akin riqe da 'yar ledarsa wacce tazamo masa jiki duk daren ALLAH sai ya riqowa baffa ita, wani lokaci gasashshen nama ne aciki, wani lokaci kuma kifi ko kuma sharare (had'in dankali da kifi).
'Dakin Yaya hawwa yashiga itama ya gaisheta sannan ya d'auko mata zancen abunda yafaru d'azu, duk da cikin girmamawa da kuma tausasa harshe yake yimata maganar hakan bai hanata yimasa tas ba sannan ta jadda masa cewa bazata dena abunda take so ba tunda gidansa ne kuma ita ta haifesa duk yanda taga dama haka zatayi, daga qarshema korarsa tayi tace yaje yabata waje bacci take ji, haquri yabata sannan ya tashi yawuce sashensa, ruwa yafara watsowa sannan sukaci abinci bayan sun gama itama tashiga toilet ta watso ruwan had'e da yin shirinta na kwanciya tahaye gadonta, duk abunda takeyi yana zaune gefen gadon yana kallonta da gefen idanuwa saida ta kwanta ya mulmula tare dasa hannu ya jawota yana fad'in. "To ranki ya dad'e ai baki isa ba, kin manta karatu zamuyi ne?".

Jan abun rufarsu tayi had'e da rufe fuskarta "habiby kabarni bacci nakeji don ALLAH."
"Tab..ina yimasa Amma kinsan ALLAH bazaki kwantaba, kawai kitashi, Yanzu muna qarfe tara awa d'aya da rabi kacal zamuyi seki koma ki kwanta abunki kinji ko, daure kitashi mana habibtyn habibyyy." yafad'a yana d'agota daga kan filo, wartsake idanuwanta tayi don tasan tunda yafad'a to dole haka za'ayi tajuyo tana d'an harararsa. "Naji dai ko mai zaki mun bakomai." Yafad'a yana ciro littafi da biro a gefen bedside loka, murmushi tayi ta aza kanta saman kafad'arsa yace. "Karki damu, zan baki abunda kike so." Hakan daya fad'a yasa ta zauna daidai, cikin qwarewa yafar koya mata qananan kalmomin turanci da kuma hausa irinsu (I, you, she, we, he, they, them, us, e.t.c) (ni, ku, ita, shi, su, mu da sauransu.)

Gwargwado kuma ta maida hankali tana fahimta sai dai bini bini tanayi tana duba agogo, awa d'aya na bugawa tayi baya da jikinta zata kwanta ya tarota yana dariya. "A'a habibty kiji tsoron ALLAH saura rabin awafa."

"Bacci nakeji habiby."

"Kiyi haquri, rabin awar tawace addu'o'i zaki koya mun, kinga sai kema kizama malamata."
"Habiby mubarshi sai gobe." Rashida tasake fad'a tana zamewa daga riqon daya yimata tayi kwancenta, a 'yan kwanakin nan yarasa meyake damunta take yawan bacci, gyara mata kwanciyarta yayi sannan ya miqe yaje yayo arwalar bacci ya kashe masu wuta shima ya kwanta, addu'ar bacci yayi masu ya shafe mata jikinta sannn ya jawota ajikinsa ya rungumeta sosai sukaci gaba da baccinsu hankali kwance.
Misalain qarfe shabiyu biyu da rabi na dare Rashida n bacci taji wata irin qara da kururuwa na fitowa daga cikin falonta, addu'o'in data sani tafara karantowa abakinta sannan ta sauko kan gadon, fitilar d'akin ta kunna had'e da kallon yanda Nuraddeen ya qaqume abun rufarsu yana baccinsa hankli kwance, toilet tawuce tayo fitsari had'e da d'auro arwala akai tanufo falon, wani irin qugi taji yna tashi cikin dakewa takoma ta d'auko wayar Nuraddeen ta kunna karatun k'ur'ani tanufo falon dashi, tana shiga taga wata irin qatuwar mage tayo kanta tadake tana kiran sunan ALLAH tare da runtse idanuwanta, tsaye tayi tana jiran taji mezai faru da ita amma sai taji wani iska maiqarfi kamar guguwa yayi wani qugi daidai saiti kunnenta sannan yayi shuuu...yawuce ta gefen labulen tagarta.
Sautin karatun ta sake qarawa sannan ta shimfid'a abun sallah ta kabbarta sallarta cike da yaqini da kuma miqa dukkanin al'amurranta ga ALLAH, hankali kwance take gudanar da sallolin nata na nafila kamar yanda tasaba duk daren ALLAH matuqar tanada tsarki har aka kusa kiran sallar asuba, daidai lokacin Nuraddeen ya farko tare da laluba gefen da take kwance yaji ba kowa, d'an shafa goshinsa yayi cikin yanayin bacci tare da jaye mayafin da suka lullub'a ya sauko akan gadon, falon yanufo ya tarar da ita zaune ta d'aga hannayenta tana addu'o'inta kamar yanda tasaba, murmushi yayi tare da komawa toilet ya d'auro arwala shima yayi raka'o'insa biyu na raka'atanil fijir sannan ya zauna yana jiran atada sallar asuba.

Tana gama sallar asuba tayi zaunenta tana karanto azkar d'inta na safiya da marece har rana tafito sannan tawuce kitchen tad'ora dahuwar indomie kafin ta d'ora abun kari saboda yunwar da takeji shi kuma ya riqa mata gyare-gyaren uwar d'akin dana falo yana gamawa ya iskota kitchen zaune da plate gabanta tana cin indomien data gama dafawa. Cike da mamaki yake kallonta kafin yace. "Habibty lafiyarki kuwa? Qarfe shida da rabi na safe yanzu, sekace wacce takwana da yunwa..."
Bai qarasa rufe baki ba ta tashi aguje tayo waje wajen makwarara tana sheqa amai, da sauri yayo kanta ya riqeta, gaba d'aya indomien da taci saida ta amayeta abun gwanin tausayi, kujerar tsugunno ya d'auko mata a kitchen ya zaunar da ita sannan yaje ya d'ebo ruwa ya wanke mata bakinta da inda ya b'ata mata hijabin dake sanye ajikinta, d'aki ya kaita ya zaunar saman kujera had'e da cire mata hijabin sannan yadawo tsakar gidan ya wanke bakin makwararar da tayi aman ya sake d'ebo wasu ruwan ya wanke hijabin ya shanya sannan yakoma cikin falon yana jero mata sannu, kuka ta saka masa kai kace wata qaramar yarinyace sosai. "Habibty meye haka, laifinki ne fa, kinsan bama Kari dawuri don me zakici abinci yanzu beside kofa brush bakiyi ba ba dole k'wayun cutukan da suka zauna maki a baki su sakaki amai ba."
Nuraddeen yafad'a yana qoqarin jawota ajiki, k'wacewa tayi tana fad'in. "Ko ba yunwa nakeji ba, kuma cikina duk a toshe yake bana jin dad'insa."

"Ayya yi haquri habibty, amma anya wannan ci da kikeyi a kwanakinnan ba macijin cikine ke damunki ba, ga yawan bacci dana lura kinayi gaskiya yau zanyiwa baffa Usman magana idan yaje daji yasamo maki maganin macijin ciki da basir."

"Wlh kuwa habiby nima nafara jin tsoro kada yafara cimun hanji kaga yanzu banci komaiba."

Rashida tafad'a tana yamutsa fuska, daidai lokacin taji ana yimata motsi aciki, wuntsil wuntsil, da sauri tamiqe tsaye tana zaro idanuwa tare da dafe saiti inda taji motsin kamar zatayi kuka yace. "Habiby wallahi macijinnan da gaskene, kaji yafaramun motsi, wayyo ummata, wayyo zan cinyemun hanji." Da gudu takoma kitchen d'in ta d'auki sauran indomien ta qarasa cinyewa shi kuma yana tsaye yana kallon ikon ALLAH, duk Wanda yasan ciki kallo d'aya zaiyiwa Rashida ya fahimci tanada shi saboda hasken da tayi ga breast d'inta suma duk sun cicciko duk da bai sata laulayi ba yakan sata jin matsananciyar yunwa da Kuma yawan bacci wud'an gaba d'aya Nuraddeen ya ta'allaqasu da cewa yawan bacci basirne ke damunta shi kuma yawan cin abinci macijin ciki ne da ita sabod ko kad'an ransa bai kawo masa zancen cikine da ita ba, be side bema San yanda ake gane cikin mace ba idan tanada shi, ko amai da yaga tayi a tunaninsa rashin brush ne da batayi ba kafin taci abincin....






*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___30πŸ’Ž

Cike da so da qauna ya amsa mata yana tambayarta ya qarfin jikin nata, a kunyace ta amsa da taji sauqi sosai, nan yayi ta saka mata albarka bisa zuwan da baffa Usman yayi wajensu amadadin baffa suna godiya bisa tarbiyar da suka bata tare da yabon kyawawan halayenta bisa haquri da juriya da take dasu da yanda take girmama kowa acikin gidan, hakan ba qaramin jin dad'i da alfahari ta sakasu ba shi da umma bugu da qari ga albishir da suka samu cewa sun kusa samun jika nan kusa bada jimawa ba, wannan dalilinne yasa yakirata da wannan safiyar don yanuna mata tsantsar farincikin data sakashi don har seda yayi qwalla.
"Rashida Ina matuqar alfaharin kasantuwarki 'yata saboda kin janyo mani girma da kimata sun qaru a idanun duniya kin sakani farincikin da ko mai 'ya'yaye goma bai isa yanuna mun shiba, kin fahimtar Dani cewa ba ilimin boko kad'aine kesa kayi alfahari da d'anka ba matuqar kabashi tarbiya da ilimin addini, Ina mai addu'a ALLAH yakareki Kuma yafaranta zuciyarki kamar yanda kika faranta tamu nida mahaifiyarki, ki kula da kanki sosai kinga yanzu bake kad'ai kike ba, ki dage da yiwa abunda ke cikinki addu'a da neman tsari daga sharrin shed'an tun kafin yazo duniya domin shine hikimar ALLAH da yabar uwa tayi renon cikinta har na tsawon wata tara don samu isashhen lokacin yimasa addu'a badon haka ba da yanda akayiwa nana maryam kun fayakum haka za'a yiwa kowace mace saboda haka ki kula sosai kinji iko, kiqara hak'uri Kuma ki kai kukanki ga ALLAH da SANNU SANNU zai yaye mana damuwarmu, ALLAH yayi maki albarka, ga umman taki."
Baba yafad'a yana miqawa ummu wayar,

"Ummata." Rashida tafad'a hawaye na biyo kuncinta saboda tausayin kanta da halin da take ciki da basu sani ba, goge hawayenta tayi wani b'angare na zuciyarta nafad'a mata cewa bai kamata tayiwa ALLAH butulci ba tunda iyayenta nacikin farinciki Kuma ako yaushe addu'arsu natare da ita.
Muryar umma ta tsinkayo a kunnuwanta tana fad'in, "yarinyata ya kike?"

"Lafiya klw ummata ya kuke kuma da wajensu aunty marwiyya da baba balarabe, kowa duk lafiya ko umma.?" Rashida tafad'a cikin sanyin murya tana qaqaro murmushi a fuskarta tamkar tana gabanta. "Kowa lafiya klw ya qarfin jikin naki, kinacin abinci kuwa?"

"Naji sauqi ummata, abincin daine bana iyaci ummata.." saida umma ta kalli baba dake gefenta sannan yace "dama nasan za'ayi haka, ki daure kinacin abinci kada kirame shima yaron cikinki kisa yafito ba lafiyayye ba kinji ko, fad'amun me kike so inba malan Idris idan yashigo yakawo maki." Murmushi Rashida tayi aranta tana cewa, ALLAH sarki uwa, akoda yaushe kulawarta tamusamman take fiye da takowa aduniya, shiru tayi tana nazarin me zatace kafin can taji umma nafad'in "Akawo maki garin d'an wake kina so.?" nan take taji d'an waken yabiyo mata arai, "eh ummata Ina so, ahad'omun da busashshiyar zogale da kike ajiyewa kina yimana dambu shima inaso"

"To kice dai a had'o har da tsakin yin dambun ko,"

"eh umma har dana fate fate.?"

"Duk dai Rashida, wannan yaro ko yarinya anyi makwad'aita."

Umma tafad'a tana dariyar, tamkar tana agabanta haka rashidar tayi saurin rufe fuska itama tana dariya, naseeha tayi mata sosai had'e da bata 'yan shawarwarin yanda zata reni cikin sannan sukayi sallama, wani farinciki Rashida taji ya mamaye ranta cikin jin dad'i ta yane zanen gadon dake jikinta ta sauko daga kan gadon.

Falo tafito taduba bataga habibynta ba tafito tayo kitchen don tasan bai wuce can yana had'a masu breakfast, ai kuwa tana zuwa ta iskosa yana gyaran kayan miya har ya d'ora sanwar shinkafa ta tafaso saboda electric ne kuma wutar tanada qarfi sosai, qamshin shinkafar data tafaso ne yabugi hancinta lokacin data aza qafarta zata shiga kitchen da sauri takoma baya had'e da toshe hancinta amma ina tuni aman yaci qarfinta da gudu takai bakain makwarara tana sheqasa, ji Nuraddeen yayi kamar ya aza hannu akai yafashe da kuka saboda takaicin wannan abun da yaya hawwa tace ayi gashi aman datayi kusan sati da kwanaki batayi ba yau duk ta rankasa, sosai aman ya galabaitar da ita don tun tana durqushe saida takoma zaune hawaye nabimata a kunci, gashi daya matsota saita turesa saboda warin girkin da yakeyi, rufo kitchen d'in yayi da sauri ya d'ebo ruwa ya wanke mata baki zuwa lokacin batada sauran qarfin da zata iya hanasa rab'ar jikinta duk dako qamshin girkin dake jikinta da bata so, riqata yayi ya kaita d'aki ya kwantar da I bisa gado yana jero mata sannu yaje yacire kayan jikinsa ya watso ruwa sannan ya d'auko plaks d'in ruwan zafi dake kan fridge tare da kayan tea ya had'a mata mai kaurin gaske ya tadata zaune yadinga Bata tana sha, saida ta shanyesa cikin kofin tas tace yaqaro mata wani ta shanye sannan takoma ta kwanta tana fad'in "kayi haquri habiby, kagaji da rashin girkin da nake yimaka ko shiyasa kad'ora abunka yau..." Bata qarasa ba ya d'ora yatsans abakinta yana girgiza mata kai.

"Ko kad'an habibtyn habiby bazan tab'a gajiya da halin da kike ciki ba tunda nine sila, don haka kidena fad'ar haka kinji ko.?" Ya qarasa maganar yana jan karan hancinta, hannunta tasa tariqo nasa had'e da cewa.

Kaima kadena fad'ar cewa kaine sila domin yanayin wannan ibadar gidan aurence tazo mana a haka."
'Dan duqowa yayi ya sumbaceta agoshi yana murmushi ta wani lumshe idanuwa sannan ya gyara mata abun rufarta daidai qirjinta yace.

"Kiyi baccinki kada kifito har in qarasa, kwana biyu naga yadace yau akaiwa su baffa abinci shiyasa kika ga nad'ora girkin tunda ke dake dafawar bakyajin dad'i." Yana gama fad'a ya juya zai bar d'akin tariqo hannunsa alokaci d'aya tana lumshe masa idanuwa bayan ya juyo tace. "Ina sonka malamina habiby nah."

Dawowa yayi yad'an shafa cikinta d'aya d'an fara tasowa sai dai ba sosai ba saboda tsawon da take dashi. "Ina sonki so mai yawa kuma marar misaltuwa habibty."
Bai jira mezata ceba yayi saurin wucewa ransa cike da nishad'i, in dai soyayyace tsakaninsa da habibtynsa yasan basa gajiya kuma ba ranar gamata, yanzunan ne zasu qone abincinnan batare da sun ankara ba shiyasa yayi saurin baro d'akin, murmushi tayi tarufe idanuwanta nan da nan bacci yazo yayi gaba da ita, bai jima da d'aukar taba can cikin baccin aka fara nuno mata miyagun halittu kala kala suna neman firgitata amma sai taga wani glass yayi mata shamaki tsakaninta dasu sun kasa yimata komai, da wata irin kalmar shahada tafarko cikin matsananciyar qarar da tasa Nuraddeen shigowa cikin d'akin a rud'e riqe da ludayin miya a hannu, da alama ita yake motsawa yaji qarar sautin kalmar shahadarta. Saman madubi ya ajiye ludayin yanufi inda take zaune tana karanto addu'o'in data sani abaki zuciyarta cike da tsoro sai faman harbawa takeyi da sauri da sauri, tattab'a fuskarta da tayi sharkaf da zufa ya dingayi hankalinsa atashe yana fad'in "habibty lafiya?."

"Lafiya habiby." Tabashi amsa tan dafe d'an cikinta da yaji yana motsi sakamakon firgitar da tayi,

"Tashi mukoma falo." Yariqota ahankali yana kallon yanayin da take ciki, don riqotan da yayi yaji yanda qarar bugun zuciyarta ke tafiya da sauri da sauri sboda tsananin firgicin da tayi, ruwa ya d'auko a fridge yabata tasha bayan ya zaunar da ita, wayarsa ta karb'a ta kunna baqara tare da cewa yamiqo mata qillen tsamiyar dake ajiye saman fridge ta tsotsa saboda zuciyarta data fara tashi don har lokacin bai qarasa girkin da yakeyi ba.
Bayan ya miqo mata tsamiyar yafice ya nufi can cikin gida da niyar kirawo fadeela tazo taqarasa aikin dama miya ce kad'ai bai qarasa ba.
Yana fitowa yaci karo da muneera zaune bakin rumfarsu tana tsifar Kai, fiye da sati d'aya Inna ruqayya na fama da ita ta tsefesa sai yau da taga dama sannan ta zauna zaman tsifar, tana ganinsa ta dashe baki shi kuma ya d'auke kansa gefe cike da takaicinta, "ya nura."

Muneera tafad'a tare da tasowa tabiyosa har lokacin hannunta nacikin kanta tana tsifar da yatsunta, bai tankata ba har yakai bakin qofar d'akin Inna Bilkisu had'e dayin sallama, juyowar da zaiyi ya jira fitowarta sukayi karo da muneera dake biye dashi kansa yabugi nata sosai tayi baya zata fad'i yayi saurin tarota tafad'a saman hannunsa, abunka da d'an uwa duk yanda take bazaiso abunda zai cutar da itaba har takai ga taji ciwo, muneera na ganin haka ta dashe baki tare da sake sakin jikinta. "Meye haka, dalla miqe sakarai, meye kike faman bina haka." ganin ko qwakkwaran motsi takasayi sai wni kafesa takeyi da idanuwanta irin na mujiya yasa cike da takaici ya saketa, tim kakeji qasa tamkar an yarda kayan wanki.

"Wayyooo..quguna ya nura zaka karya ni."

Tafad'a tana qoqarin tashi, daidai lokacin Inna Bilkisu tafito had'e da cewa."a'a Nuraddeen shine kayi tsaye anan sai kace baqo injin dai lafiya?."
"Lafiya klw Inna Bilkisu dama fadeela nake son tazo tad'an qarasa mana wani aiki, jikin Rashidar ne yad'an motsa yau.."
"Ya nura nizan qarasa maka kowane aiki ne basai fadeela ba."

Muneera tafad'a tana wani turo lab'b'a ala tilas itaga mai kishi, "to Nuraddeen kuje ga muneera nan kaji tace zata qarasa maku." Muskutawa yayi had'e da gyara tsayuwarsa sannn yace. "Don Allah Inna Bilkisu kitaimaka kituromun fadeela." Batare daya damu da zancen muneerar da tayi masa ba,

"Nuraddeen.." Inna Bilkisu tafad'a cikin sigar lallashinsa akan muneerar taje gudun wata matsala tafaru amma yayi saurin dakatar da ita tahanyar cewa

"Don Allah Inna Bilkisu." Yana had'a hannayensa sannan yawuce ita muneera ta sake bin bayansa. Saida Inna Bilkisu ta sauke ajiyar zuciya sannan ta qwalawa fadeela kira.

"gani inna"

Fadeela tafad'a tana fitowa daga cikin d'aki da alama baccima ta farayi, "maza jeki yayanku nakiranku, kice ma Rashida Ina gaisheta da jiki."

"To Inna." Fadeela tafad'a tare da komawa d'aki ta d'auko hijabi tasaka tanufi sashensu, tana isa baki qofar shiga shiyar muneera ta riqe mata hijabi. "Wallahi babu inda zaki shiga tunda yahanani nima, munafuka kawai sai wani shishshige masa kikeyi bacin kinsan nice zan qara aurensa."

"Ha'a meye haka kuma aunty muneera, cikamun hijabina."

"Bazan cikakiba, wuce muje kikoma inda kika fito." Nan rigima ta kaure tsakaninsu muneera tayi bake bake a bakin qofar shiga sahen nasu Rashida riqe da hijabin fadeela ta kafe akan ba inda zata fadeela sai kiciniyar k'wacewa takeyi ta shiga, hakan yajawo hankalin Nuraddeen dake cikin d'aki yafito had'e da katsawa muneera tsawa yace.

"Waike wace irin marar kunya ce, zaki sake mata hijab ko sai nazo na takeki wajen." Yafad'a had'e da yowa kanta ransa ab'ace.

Da sauri ta saketa tare da komawa gefe tana fad'in "ya nura to nima in shigo?"

"In karya maki k'afa k'azama."

Turo lab'b'a tayi tana fad'in. "Badai shiyar kane baka so nashigo ba, wallahi saina fad'a inna shima akaika wajen maln ba..." Bata qarasa maganar ba sakamakon wata uwar tsawa da Inna ruqayya dake fitowa daga b'angaren yaya hawwa tayo mata jin zata tona masu asiri, "kee muneera maza kibaro wajennan kafin ranki ya b'aci, yayan naki ke fad'a kina fad'a don rashin kunya, zaki jaye ko saina iskoki." Taqarasa maganar tare da nufar wajen, qafafuwa muneera ta shiga bubbugawa tana fad'in. "Inna shifa zan aura kukace Kuma zakice nabaro wajensa, ya nura ni takace kuma ko bakaso sai ka aureni, kashirya a wannan shekarar dole muyi aure." dariya Inna Bilkisu dake kakkamta kaya a cikin rumfarta tana sauraren suruttan muneera tayi aranta tana cewa tabbas iska na wahalda mai kayan kara, Nuraddeen dake tsaye shikuma yana kallon ikon ALLAH tsaki yaja tare da shigewarsa don bai fahimci ma inda zancenta yayi ba, a fusace Inna ruqayya taqaraso wajen taja hannunta tana d'imarta a baya "ke kam anyi samna anan, shin b'angaren nasa aljannah ne da zaki nace sai kin shiga, bana fad'a maki kifita shirginsa

Please Login or Register in order to submit comment