Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na kalla naga irin zubin da ubangiji yayi maka na salihhan bayi dake da matuqar hangen nesa amma kai ka kasa fahimtar hakan balle har ka hango abunda nake son lusar da kai nan gaba, fisabillahi amatsayina na mahaifiya nagaji da irin hukuncin da kakeyiwa 'yata, na d'au tsawon shekaru ina yimaka biyayya batare dana damu da akan daidai kake ba ko akasin hakan, nayita addu'a nayita jiran ranar da kai da kanka zaka fahimci kuskurenka ka gyara amma ka kasa, asalin sahabin manzon ALLAH (s.a.w) dake da sunanka tabbas yanada zuciya sosai amma ya kasance mai tsananin fahimta da saurin sauka da uzuri koda kuwa ga yarone balle babba, akwai qissarsa da aka kawo cewa wata rana yana zaune masallaci sai yaji wani bawan ALLAH na sallah a raka'ar farko ya karanta fatiha sai yakaranta qul a'uzu birabbin nas, yana jin haka ya tashi da sauri yaje gida ya d'auko takobinsa ya tsaya bayan wannan mutumen yana jiran yaji mezai karantawa a raka'a ta biyu idan ya karanta fatiha, sai yaji ya sake karanta qul a'uzu birabbinnas kamar yanda yayi d'azu."

"Mutumen na sallamewa sayyida umar ya kallesa yace wlh ka kuru, daka karanta wata sura bayan qul'auzu birabbinas dana sare kanka da wannan takobin nawa mai tsananin kaifi, sai mutumen ya tambayesa dalili sai yace baya halatta mutum ya karanta fatiha da wata surah a raka'ar farko idan ya tashi yin raka'a tabiyu yace yakaranto wata surar data yimasa dad'i sai kace mai karatun jarida, dolene yakaranta surar dake bima wacce yakaranta a raka'a tafarko ko kuma aya araka'a tabiyun, shiyasa nasan daga qul'a'uzu birabbinnas babu wata surah nazata zakayi wasa da alqur'anin ALLAH ne na d'auke maka kai sai naji ka maimaita surar wannan dalilin shiya qwaceka daga mutuwa a hannuna yau". _(to sai mu kula yin hakan laifine acikin sallah, idan ka karanta surah araka'ar farko idan zakayi ta biyu to surah dake bimata zaka karanta ma'ana ta qasanta, idan kuma ayoyine to cigabansu zaka karanta, ubangiji ALLAH yasa mudace๐Ÿ‘)_ kaga anan sayyidina umar yayi zuciya sosai da tasashi zuwa ya d'auko makami akan abunda yaji kuma yayi hasalar da tasa har yake tunanin zai iyayin kisa, amma da yayi haquri yabi abun ahankali har zuwa qarshen sallar bawan ALLAHn nan sai ya sauka daga fushinsa tunda yaji abunda yake tsammanin zai faru ba haka bane kuma abun bai faru ba, sai ya janye hukuncin da yayi niyar d'auka akan wannan bawan ALLAHn tare da yimasa bayanin da zai ilmantar dashi anan gaba, to don me kaima bazakayi koyi dashi ba?, Kayi haquri alokacin da kaji cewa abunda kake tsammani ba haka bane?, don mi bazaka janye hukuncinka ba tunda abunda kake gudun faruwarsa bai faru ba?, Don mi baza kayi uzuri ga 'yarka ba kajawota ga jiki kafahimtar da ita dalilinka na rashin son aurenta da yaron wanda kagano hakan wataqil zaisa ta ilmantu akan girman soyayyar iyaye ga 'ya'yansu ita kesa su yanke masu hukunci cikin b'acin rai saboda qaunar da suke yimasu don tsoron karsu fad'awa halaka.?, Maganar gaskiya ni baka kyauta mani kuma baka yimani adalci, idan kai baka buqatarta akusa dakai ni Ina son na ganeta akusa dani mu zauna tare muyi fira irinta uwa da d'iya, tafad'a mani damuwarta inbata shawara akai Amma duk saboda kai narasa wannan damar, wannan wane irin son kaine kake dashi haka, kullum kai kanka baka damuwa da damuwar kowa idan ba taka ba."

"idan ma hukunci ne kake yimata ai ya isa haka, izuwa yanzu itama tasan me ake cewa d'a da mahaifi, bana tantama duk yana cikin jarabawarta da ALLAH ya karb'e mata rayuwar 'yarta saboda tafahimci irin girman soyayyar dake tsakanin iyaye da d'ansu ta fahimci pain d'in da iyaye ke shiga alokacin da wani abun da basa so zai sami d'ansu, b'acin haka ALLAH ya sake jarabtata tahanyar fasa jikinta aciro mata 'ya'ya duk da kasancewar alokacin zata iya rasa rayuwarta, Ina tsammanin ta wannan fannin kad'ai izuwa yanzu tasan me ake cewa iyaye kuma tasan girmansu, to don me bazaka yafe mata ba, ko kafiso sai ranar da akazo aka cemaka tamutu ko kuma shi mijin nata daka tsana ya mutu sannan kafashe da kuka kace kayafe mata?, Alhaji umar" tafad'i ainahin sunansa wanda ya sashi d'agowa da qarfi yana kallonta, tabbas yau yakaita qul don bazai iya kawo rana d'aya ba d'aya tab'aji ta furta sunansa haka kai tsaye, Saida ta share hawayenta da tafin hannuwanta sannan taci gaba da cewa.

"Ka rabu da mugun nama, ka rabu da dokin qarfe, ka yafi 'yarka tazo garemu na roqeka da ALLAH da girmansa, idan kuma ba haka ba wlh wannan zuciyar taka bazata kaika ko Ina ba kuma zata sa kayi nadama mai yawa arayuwa don na tabbata har yanzu kana sonta kuma kana tsananin qaunarta fiye dani, yanzu haka 'yarka nada tsohon ciki kuma shima tiyata za'a yimata akaro na biyu yarage gareka ka sauko daga fushin da kakeyi da ita ko kuma akasin haka, ita dai mutuwa rigar kowace kuma zata riskemu aduk lokacin da taga dama, ba lallaine afito maka da ita da raiba domin ba ahannunmu rayuwarta take ba don haka kana da damar canza abunda yakasa canzuwa cikin shekaru bakwai a cikin daqiqa d'aya idan kaso."

Tana gama fad'ar haka tamiqe ta lunke dardumar da tayi sallah akai sannan take ta watso ruwa ta dawo tanemi gefe ta kwanta, shi kuwa gaba d'aya yau kalamanta sun kashe masa jiki cikin sanyin murya yakira sunanta had'e da cewa.

"A yanzu na fahimci cewa a cikin hukuncin da nayi nine mai laifi, a duk tsawon wannan lokacin Ina d'aukar 'yata a matsayin ita keda laifi shiyasa na koreta daga gidannan, Amma yanzu Dana fahimci nine mai laifin yakamata nahukunta kaina tahanyar barin wannan gidan tunda shine hukuncin da nake zartarwa ga mai laifi, ALLAH shine sheda tuni nayafewa batool bana fushinda ita amma sai nakejin matuqar zanci gaba da ganinta wannan baqinciki data jefani aciki awancan lokacin zai iya cigaba da addabar zuciyata har iya qarshen rayuwata, shiyasa nakasa cewa tadawo gareni."

Ita dai Bata sake tankasa ba saboda ayanzu ta gama yanke hukunci akan zataje ta zauna da 'yarta matuqar wud'annan maganganun da sukayi basusa ya haqura ba bazata sake cemasa ya haquran ba, dolene itama tagwada masa irin tata zuciyar awannan karon don tagaji, ganin taqi tankasa yasa shima ya juya ya kwanta kalamanta nayi masa yawo a qwaqwalwa, har akayi kiran sallar asuba Abba bainsamu ya runtsa ba daya rufe idanuwa batool yake gani, gaba d'aya hankalinsa yabi duk ya tashi babu wacce take so da gani idan ba itaba gashi dare yayi balle yakirata awaya yaji muryarta ko zai samu sassauci, ALLAH ALLAH ya dingayi safiya tawaye yakira ta har aka kira asuba, haka ya daure yayo sallah yadawo yayi zaune yana jiran har gari yafara haske yakira yanda hankalinta bazai tashi ba idan taga kiran amma da yake jiya bai samu wani isasshen bacci ba sai baccin yayi awon gaba dashi.

A can cikin barcin nasa ya soma yin mafarkin daya matuqar tayar masa da hankali wanda bayan mintuna talatin da kwantawarsa ya farka cike da tashin hankali ya saki wata irin qarar da tasa hajia mama dake kitchen rugowa wacce saida ta karad'e gidan gaba d'aya, a yanayin data ganesa yana faman zufa duk da a.c dake kunne yasata ajiye fushin da takeyi dashi ta matso kusa garesa sosai tana fad'in,

"Lafiy alhaji?.." ko rufe baki batayi ba saiga su uncle h da dawowarsu daga masallaci kenan sukajiyo sautin qararsa suka shigo sugani ko lafiya,

Kasa magana yayi inbanda hawaye da zufan dake keto masa babu abunda yakeyi, a gefe gefensa su uncle h suka zauna suna goge masa zufan tare da sake tambayarsa, daqyar ya iya sake bud'e baki yace....

_Hi gusz, me yafaru ne da Abba?, Wane mafarkine yayi daya jefasa acikin wannan yanayin?, try and find it by your self๐Ÿคฃ the first person dana fara karanta comments d'insa naga yabada amsa daidai da mafarkin Abba to tabbas shi keda page d'in gobe sukutum in sha ALLAH, wannan alqawarinane in ALLAH yabani Aron rayuwa๐Ÿ˜…a kafta my fans๐Ÿคž๐Ÿปluv you much๐Ÿ˜˜_






*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*๐Ÿ‘๐Ÿ˜ญ
[11/14, 22:52] Billy S Fari: ๐Ÿšถโ€โ™€๏ธ๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™‚๏ธ *SANNU SANNU*๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™‚๏ธ๐Ÿšถโ€โ™€๏ธ
๐Ÿ’Ž _Bata hana zuwa..._๐Ÿ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI๐Ÿ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*๐Ÿ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*๐Ÿ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*๐Ÿ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*โค๏ธ

_Masha ALLAH, jinjina agareki tare da gaisuwa ta musamman had'e da fatan alkhairan ALLAH sutabbata agareki aduk inda kike gwanaty๐Ÿ˜… *SARATU UKASHATU ISAH (MUM NUSAIBA)* Ina godiya bisa yanda kike bibiyar wannan littafi da yanda kika hakaito inda mafarkin Abba yanufa, a gaskiya naji dad'i kuma kin burgeni sosai, though akwai da yawa wud'anda suka amsa tambayar daidai da taki amma kece wacce cikar alqawarina ya tabbata agareki kasan cewar ke kika rigasu bada amsa, namatuqar jin dad'i da nishad'antuwa yanda naga comment d'in fans na playing ta ko'ina sanadiyar hakan kuma nagode maku sosai jaxakumullahu bikhair, tabbas kud'in abun alfaharina ne saboda yanda kuka juri bibiyar wannan littafi nawa duk da tsawon nisan zangon da yayi batare da gajiyawa ba, ubangiji ALLAH yabaku aljannarsa da rahamarsa bigairi iqabin wala hisabin๐Ÿ‘THANK YOU ALL ONCE AGAIN๐Ÿค_

Page___99๐Ÿ’Ž

Da qyar Abba ya iya bud'e bakinsa yace hajia mama tamiqo masa ruwa, fridge taje ta bud'e ta d'auko gorar ruwa mai sanyi takawo masa ya karb'a ya bud'e marfin yafara sha da sauri da sauri tamkar wanda yakwana da yini bai sha ruwa ba har saida ya shanye ruwan tas sannan ya ajiye gorar saman bed side had'e da goge bakinsa, duqar da kansa yayi na mintota tamkar mai nazarin wani abun kafin ya d'ago kai yace.

"Na shiga uku ni da kaina zan jawowa yarinyata shiga cikin wani hali da zan gwammaci mutuwata akan rayuwata, na tabka kuskuren da ayanzu ni da kaina nake tsoron qoqarin gyaransa saboda gudun kar abunda nagani yafaru."

Cikin rashin fahimtar wasu daga cikin maganganunsa hajia mama tace.

"Kamar ya alhaji?, Taya bawa zaiyi kuskure kuma yayi nadamar aikatasa ace kuma yana tsoron gyaransa?."

Hawaya kwance a fuskarsa wanda ganinsu ya matuqar tayarwa da 'yan uwan nasa da hankali ya sake d'agowa yana kallon ta had'e da cewa.

"Sosai ina jin tsoron gyarasa kar mafarkin da nayi yanzu ya tabbata.."

Kusan atare kafin ya rufe bakinsa su uncle h suka had'a baki wajen cewa.

"Mafarki!"

"Eh mafarki."

"Ikon ALLAH, to Yaya ai kai shi mafarki ba gaskiya bane, don haka bama tsammanin zai faru don ka gyara kuskuren daka aikata,"

"A'a hussain, sau da dama mafarkin bayan sallar asuba ance yana zama gaskiya, bana son wani abu yafaru da batool domin bako shakka itace rayuwata, nasan zakuyi mamakin hakan dana fad'a lura da yanda nawofantar da ita na tsawon shekaru saidai abunda baku sani ba shine, duk tsawon shekarunnan narayune bisa d'imbin tunaninta safe, rana da kuma dare, nayi nasarar cin galabar zuciyata wajen korarta gidannan duk da irin son da nake yimata amma nakasa yaqi da qwaqwalwata da kuma ruhina wajen dena tunaninta, adaren jiya mahaifiyarta taganar dani abunda nagagara ganewa balle har na saurari gaskiyar da kuka yita qoqarin ganar dani, nayi nadamar abunda nayiwa 'yata ta cikina kuma naquduri gyara laifina yau Amma kash nayi mafarkin daya girgizani kuma ya raunata zuciyata har nake tunanin bazan iya ba."

"Haba alhaji sai kace ba musulmi ba!, Kayi Imani da ALLAHnka kayi abunda ya kamata, kada kayi Imani da abunda kagani a mafarki, tun d'azu sai kambama al'amarin nan kakeyi kaqi ka sanar damu ko meye?" Uncle Hassan yafad'a cike da damuwa, juyawa hajia mama tayi don bata son yafad'i ko mafarkin meye don annabi yace idan anyi mafarki mai kyau babu laifi afad'a idan kuma akayi marar kyau to ayi shiru ayi sadaka sannan kada afad'awa kowa, gashi 'yan uwan nasa na neman ya bayyana masu mafarkin da yayi Wanda ta tabbatar ba ai kyau bane tunda har ya shiga cikin irin wannan yanayin, wasu hawaye taji sun zubo mata tayi saurin sharesu don kada su karya mata zuciya ta wuce d'akinta tafad'a toilet ta d'auro arwala sannan ta shimfid'a abun sallah ta fuskanci ubangijinta tare da roqon ALLAH ya sauqaqa duk abunda yayi nufin zai jarabcesu dashi kuma kada ya d'ora masu abunda bazasu iya ba ko zai kautar masu da Imani,

Shi kuwa Abba shiru yayi kafin ya d'ago kai ya kalli 'yan uwansa had'e da cewa.

_"Acikin baccina dana farka a yanzu cikin wannan yanayi nayi mafarkin batool ita da mijinta sun kamo hanya zasuzo nan kano suda yaransu 'yan biyun data haifa sunyi accident, mijin nata ya mutu ita kuma ankaita asibiti anyi mata tiyata anfidda mata wasu jariran 'yan biyu macce da namiji, babban tashin hankali ko data farko tasamu mental problem akanta sanadiyar buguwar da tayi, ankiramu bayan faruwar had'arin anbamu yaran nasu basuyi komai ba, Babu abunda ya samesu d'ayar kawaice ta yanke a gefen fuskarta, gaba d'aya na rud'e batool d'ina ta haukace acikin mafarkina, duk abunda nayi mata amma Bata yadda da kowa saini, hatta likitoci da mahaifiyarta dukansu takeyi, Babu wanda take ambata bakinta saini, Babu wanda take saurara saini, nikad'ai ke iya kusantarta Bata jimani ciwo ba, hakan yasa soyayyar da nake yimata naqi bari akula da ita yanda ya kamata a asibiti, da kaina na d'aukota na dawo da ita gida Ina kula da ita hatta yaran data haifa in bani na riqasuba nakais tabasu nono bata tab'a shayar dasu , ni daku munyi magani har angaji amma batool d'ina takasa dawowa hankalinta, ga mijinta ya mutu, ga qananan yaranta tabar mana da duk inda muka kallesu sai mun zubar da qwallan tausayinsu, gashi mahaifiyar mijinta ta kasa mantawa da abunda nayi mata wanda ku baku sani ba har tana kuka dani akan laifin dana aikata tare da tabbatar mani da kowaye ubansa, na matuqar girgiza daa mafarkina ya nuna mani mahaifin yaron dana tsana aduniya kuma nake shegan tasa duk da anfad'a mani shine mahaifinsa yazo a daidai lokacin da nake buqatar taimakon tawa yarinyar da zimmar taimakonmu ba tare dana san shine mahaifin mijin batool ba, inajin tsoro kar wannan mafarki ya zamo tamkar isharace akeyi mani da abunda zai faru da 'yata da kuma mijinta...."_

Haka yaci gaba da basu labarin mafarkinsa da yayi wanda tun a farkon littafi ya zamo shine shimfid'ar wannan labarin har yakai qarshe yana Mai fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi, hatta su kansu saida sukaji jikinsu yayi sanyi don tabbas mafarkin nasa akwai ban tsoro da firgitarwa acikinsa, ganin yanda duk yabi ya sare yayi loosing hop d'insa yasasu qarfafa nasu zukatan ta hanyar rarrashinsa tare da maganganu masu dad'i da zasu kwantar masa da zuciya, suka nuna masa shi cewa mafarki fa ba gaskiya bane in sha ALLAH babu abunda zai faru, binsu yayi da kallo suka jinjina masa kai alamun tabbatar masa da abunda suka fad'a, don ya sake samun natsuwar zuciya uncle hassan yace uncle Hussain yakira masa shurahbil ya d'auko masa wayarsa d'aki, shiru yabiyo bayan na wasu mintuna sanadiyar wayar da uncle Hussain keyi sai ga shurahbil wanda shine d'an uncle Hassan na biyu yashigo sanye da doguwar rigarsa jalabiya riqe da wayar uncle Hassan da alama bacci ya tashi,

Yana shigowa gaban Abba ya sake fad'uwa don bazai mantaba haddashi yagani cikin mafarkin don shine ma yayita kula da yaran batool kuma sanadiyar yaranne ya had'u da mutumen da shine mahaifin mijin batool har yakawo masu shi a matsayin wanda zai taimaki rayuwar 'yarsa, har yaqaraso cikin d'akin ya gaishesu ya miqawa uncle Hassan wayarsa yafita idon Abba na akansa.

Bugu d'aya uncle Hassan yayiwa wayar batool tashiga tafara ruri, cikin jin dad'i batool dake zaune tana karyawa little ya kawo mata wayar ta d'aga had'e da cewa.

"Uncle h barka da safiya, antashi lafiya?"

"Lafiya klw batool d'in Abba, ya kike ya nauyi?"

Akunyace ta amsa da Alhamdulillah tana cigaba da cewa.

"Uncle ya abbana yake, yana dai lafiya ko?"

Kallon Abba yayi daya runtse idanuwa wasu zafafan hawaye na zubo masa jin shine mutum na farko da tafara tambaya kaf acikin ahalinsu wanda dama hakan yazame mata jiki aduk lokacin da tayi waya da d'aya daga cikin gidan shine take fara tambayar ya yake kafin kowa sannan yace.

"Lafiya klw abbanki yake batool, 'yan matayen namu suke?"

"Suna wajen gwaggo uncle, kowa dai lafiya ko?"

"Eh batool, ya maigidan naki?."

"Muna lafiya uncle, Wai yaushe Abbana zai yafemun nadawo areku uncle, Ina matuqar kewarsa da kuma 'yan uwana sosai, kuroqamun yafiyarsa uncle kunga awannan karon ma likitoci sunce bazan iya haihuwa da kaina ba, Ina tsoron kada nakoma ga ubangijina abbana nafushi Dani don Allah kuce ya yafemun." Taqare maganar tare dasa yatsa tagoge 'yan qwallan da suka zubo mata tana kallon little dake faman mammatsa mata qafafuwanta, tsananin tausayin da taba uncle hassan yasa bai tsaya yin komai ba ya mannawa Abba da tun d'azu sautin muryarta da yake saurare tasashi rufe idanuwa qwalla na zuba wayar akunne.

"Hello, uncle!." Data fad'a daidai lokacin da wayar ta sauka akunnensa ya sashi saurin bud'e idanuwansa had'e da cewa.

"He..he.hello Fatima!"

Wata irin zabura tayi had'e da miqewa tsaye lokaci d'aya wanda seda abun cikinta ya juya tayi saurin dafe mararta tana qoqarin kiran sunan mahaifinta don gasgata abunda kunnuwanta suka jiyo mata, cikin rawar murya tace.

"A.a.abbana!"

"Na'am batool" yafad'a yana share hawayen idonsa, yanajin tashin sautin muryarta sadda take furta Alhamdulillah da qarfi tare da juyawa cikin qarfin hali ta kalli gabas tayi sujudush shukur sannan cikin muryar dake nuna kukan farinciki takeyi taci gaba da cewa.

"Natuba Abbana ka yafemun, gaba d'aya rayuwa babu kai Abba wahalane da ita, nayi kuskure matuqa wajen kafiyawa abunda zuciyata keso duk da kuwa alkhairine sanadiyar nisan tani da kayi da kanka, bazan qaraba Abbana kayafeni."

"Ki kwantar da hankalinki batool nayafe maki, ni kaina tirsasa zuciyata kawai nakeyi akan saita haqura dake amma Ina matuqar shan wahala adalilin kewarki da akoda yaushe ke addabar zuciyata, idanuwana cike suke da mararin son qaninki akoda yaushe amma son zuciya da kuma sharrin iblis la'anannen Allah ya sani barinsu cikin qishirwar son ganinki, kiyafemun 'yata bisa tsattsauran hukuncin da nayi agareki, kiyafemun haqqinki dana tauye tsakaninki da mahaifiyarki da kuma 'yan uwanki, nayi nadama sosai kuma ina buqatar na kasance tare dake har iya qarshen rayuwata, kimanta da waccan hukuncin da nayi agareki domin mahaifiyarki ta nuna mani kuskuren yin hakan, ni mahaifinki ne kuma nan gidan kune bakida wani shamaki tsakaninki dashi har iya qarshen rayuwarki kinji ko 'yatah!"

"Eh Abbana, Ina sonka, Ina matuqar sonka Abbana don haka bazan tab'a kallonka a matsayin mai kuskure agareni ba balle har kanemi yafiyata, nice mai laifi gareka da bazan dena roqon yafiyar kaba har qarshen rayuwata, ka yafemun Abbana Ina matuqar qaunarka sosai."

"Nayafe maki 'yatah nima ina qaunarki sosai." Yafad'a yana dariya lokaci d'aya hawayen nasa na qara kwaranya, wanda ga dukkan alama wud'annan sun banbanta da wud'ancan don su na farinciki ne.

Tun suna wayar a zaune har yamiqe sunaci gaba da wayar yana dariya, kallo d'aya zakayi masa kagano tsantsar farincikin dake tattare dashi saboda yanda wani annuri ke fita a fuskarsa, murmushi su Uncle h sukayi had'e da miqewa zasu bar d'akin yayi d'aga masu hannu alamun su tsaya wanda seda hakan yaso basu dariya, batool kuwa tuni tasamu qafafuwan little da shima farincikinsa ya kasa b'oyuwa tayi matashi dasu tanaci gaba da waya da mahaifin nata hankali kwance,

Cikin sanyin murya tace.

"Abbana Ina so nazo naganka, Ina matuqar kewarka sosai."

Wani irin fad'uwar gaba Abba yaji jin abunda ta fad'a da sauri yace.

"A'a batool!, Don ALLAH kada kuzo kinji ko?, Ina ance tsohon cikine dake ko?, to kibari bayan kin haihu sai kizo kinji ko?"

Shagwab'e fuska tayi tamkar tana gabansa had'e da cewa,

"Abbana da sauran lokaci fa!, Sai 13 ga wani watan tukuna za'ayi aikin, nidai zanzo naganka abbana."

"A'a batool kada kizo kinji ko?"

"A'a Abbana nidai kabarni inzo inyaso ko kwana ukune kad'ai sai nayi."

"Batool.."

"A'a Abba nidai zanzo, ko baka yafemun ne ba?"

Cikin rud'ewa da rashin sanin yanda zai fahimtar da ita ta gane me yake nufi, cikin wata irin qarfin murya yace.

"Aaaaaa..., kada kizo nace batool kinji ko?."

Tashi tayi zaune a tsorace kamar zatayi kuka had'e da cewa.

"To Abbana shikenan bazan zoba.."

Tafad'i haka cikin muryar dake nuna hakan baiyi mata dad'i ba, d'an sassauta muryarsa yayi cikin sigar lallashi yace.

"Sorry my dota kinji ko, kinga cikinki ya tsufa bai kamata ace kinyi doguwar tafiya ba, ki zaunawarki gidanki in sha ALLAH ni da kaina zanzo nadubaki."

"To Abbana Amma meyasa?"

"Bakomai, ina shi mijin naki." Yafad'i hakan don yabasar da maganar saboda baya son tayi masu tsawon da dole sai tasa ya amince mata da tazo d'in.

Miqawa little wayar tayi tare da tashi tabar wajen tana kuka, meyasa abbanta zai hanata zuwa alokacin da take son ganinsa, halama ya manta da tsawon shekarun data kwashe tana jiran ganin wannan ranar? Kodai wani abun yafaru agidan da ba'aso tasani shiyasa abbanta saukowa daga fushin da yakeyi da ita?, gaskiya akwai boyayyen al'amarin dake faruwa da bata san dashi ba, badon haka ba yakamata ace shima zaiyi farinciki idan taje tunda yana son ganinta, wud'annan tambayoyin da wasuwasi ta dingayi azuciyarta tana kuka har zuwa lokacin da little yagama waya da Abba ya biyo bayanta,

Sosai little yayi farinciki da zuwan wannan ranar da hawayen gimbiyarsa zasu dena zuba saboda kewar mahaifinta kuma yaji dad'in yanda mahaifinta ya nuna masa ba komai yanzu aransa akan auren 'yar tasa da yayi ya fahimci abunda ada yakasa fahimta kuma ya roqesa yafuwa tare dasa masa albarka sosai....










*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*๐Ÿ‘๐Ÿ˜ญ
[11/14, 22:52] Billy S Fari: ๐Ÿšถโ€โ™€๏ธ๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™‚๏ธ *SANNU SANNU*๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™‚๏ธ๐Ÿšถโ€โ™€๏ธ
๐Ÿ’Ž _Bata hana zuwa..._๐Ÿ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI๐Ÿ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*๐Ÿ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*๐Ÿ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*๐Ÿ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*โค๏ธ

_i will like to extend my gratitude in dis page to you my dear sister, *FATIMA UMAR ANKA (MOMYN J)* you're truly among the most important people i have ever gotten in my life, you're such a kind and very nice person dt i will never be able to forget, you did so much things to me sister!, the way you care, luv, respect, advice and so on to me is beyond the expected, all I pray, is ALLAH to protect you, guide you, luv you and take very good care of you every where you are, may he hills all your worries and put so many smile on your face, give you what ever you want in dis dunya wal akhira and make his jannatul firdaus to be your finale abode๐Ÿ‘, thank you so much sister, FILLAH am rilly luv you more than how words can say๐Ÿ˜_


Page___100๐Ÿ’Ž

Yana shiga d'akin batool ta sake fashewa da kuka sosai ta yanda duk yanda yaso rarrashinta bazai iyaba, gaba d'aya tabi ta tayar masa da hankali, tun yana d'aukar abun zata gaji tagama har ya fahimci da hasken gaske takeyi bazata dena ba, hakan yasa ya d'auki wayarsa yakira mahaifiyar tasa ya sanar da ita halin da ake ciki, ita da kanta ta tabbatar da hakan lokacin da suke waya don tanajin sautin qarar kukanta, don haka tace masa yabata mintuna gatanan tafe.

Ajiye wayar yayi gefe had'e da komawa inda take kwance idanuwanta sunyi lutulutu saboda kukan data dad'e tanayi ga fuskarta gaba d'aya tayi jajir abunka ga farin mutum, d'agota yayi tare da rungumota ajikinsa har lokacin tana kuka yace.

"Gimbiya wai meyene haka!, Kina son jefa kankine keda babynmu cikin wani yanayine da bazaki haqura kidena wannan kukan hakan ba?, Ko kina so ne kiyiwa ALLAH butulci bisa baiwar da yayi maki ta juyo da hankalin mahaifinki akanki a lokacin da baki tab'a tsammaaanin hakan ba?, Ko so kikeyi ni kijefani cikin damuwa saboda kawai natsani ganin kukanki?"

"Ni Ina son kawaine inga Abbana, karka manta wannan kukan bashine karo nafarko ba da nakeyi akan mahaifina, idan har zanyi kuka alokacin daya yimani kashedin zuwa inda yake make tunani idan aka hanani zuwa alokacin da

Please Login or Register in order to submit comment