Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata kuka yace.

"Me zan yimaki kiyafemun?, Mezan ce maki ki aminta dani, duka kalamaina babu qarya acikinsu, gaskiyace qwara d'aya nake fad'a maki habibty, bansan taya hakan tafaru dani ba, bansan meyasa qaddara tazab'amun hakan tsakanina dake ba, nayi rayuwata awaccan qasar ne tamkar wani bawan da bayada 'yanci, namanta wayeni, namanta komai nawa, abu d'ayane nakasa mantawa shine ni ruhi d'ayane mallakin gangar jiki d'aya, hakan yasa narayu tamkar maraya Kuma nakasa banbancewa tsakanin haske da duhu akan rayuwar aure balle nayi tunanin samun wani sauyi akanki, ke kad'aice tal mace d'aya da nayi alwashin rayuwa da kuma mutuwa atare da ita, ke kad'aice mace tilo dake da iko akan sarrafa zuciyar malaminta, bazan hanaki kuka ba domin ni mai girman laifine awajenki, bazan hanaki d'aukar mataki ba domin nacancanci kihukuntani iya son ranki, sai dai kuma Ina tabbatar maki da cewa ayanzu lumfashina kad'an ne, haka kuma rayuwata taqitacciyace matuqar kikace zaki ida rayuwa bada niba.."

Saida yagoge guntayen hawayen da suka zubo masa sannan yataso ya fad'i agabanta durqushe yanaci gaba da cewa.

"Wannan dai malamin daya kasa kauda idanuwansa akan rayuwarki abaya, wannan malamin da yayi alqawarin miqa rayuwarsa agareki nahar abada, wannan malamin daya d'au alwashin zai iya bada rayuwarsa fansa ga malamarsa yana miqo qoqon baransa bisa laifin daya aikata daki yafe masa, gangar jiki da kuma rouhi suna matuqar kewarki, idanuwa na mararin kallonki nahar abada, kunnuwa nason jin sautin muryarki, haka zuciya na neman tallafin chaji daga wajenki, kalmarki d'aya ta isa tagusar da baqin duhun data kasance acikinsa na tsawon shekaru, adadin zantukan kalaman bakinki kuma sun isa su gusar da duk wata tsatsa a kwakwalwata data toshe mani tunanina na tsawon lokaci, kiji tausayina don ALLAH kiyimun uzuri, na amshi laifina hannu bibbiyu kiyafemun."

Duk da tanajin dirar kowace kalma azuciyarta kuma tana son mayar masa da amsarta kasawa tayi saboda kukan da yaci qarfinta tun tanayi a hankali har tasoma yi cikin sauti, runtse idanuwa yayi da sauri saboda jin zafi da rad'ad'in sautin kukanta da yakeji a zuciyarsa.

Miqewa yayi cikin d'ari d'ari yana son ya rarrasheta amma yanajin wani irin kwarjininta da bazai iya hakan ba, sai ya miqa hannunsa ya tab'ata sai kuma ya kasa, ya sake miqawa sai yaji ya kasa, ita kuwa sai tsananta kukan takeyi yanda tasan zai iyaci gaba da hurting d'insa sosai.

Kasancewar little dadu Dr zaunensu sukayi waje saman kujerun dake gefen rumfar motocin dake a'aje bayansu dady sun tafi yasa bakajin tashin motsin kowa cikin falon inba sheshshekar kukan Rashida ba, a hankali ya sake runtse idanuwansa ya zauna kusa da ita tare da jawota ajikinsa yafara lallashi yana fad'a mata kalaman ban haquri a kunnuwa duk da bayada tabbacin zata iya fahimtars, cikin wani irin yanayi daya tsinci kansa aciki bayan tsawon wasu shekaru yake rad'a matasu a kunne kamar hakan.

" _I am really very sorry to start with habibty, Since the time you refuse to talk with me, I' m completely lost. I believe that things are not the same for me and for you. My intention was not bad, the timing was wrong. You know what I feel for you is really strong. I want to talk to you in a similar way as I did before. I want to play pranks with you as before. Please forgive me now and end this for all. Because this situation...!,"

Sai kuma yayi shiru ya kasa qarasawa sai 'yar sheshshekar kuka shima yaci gaba da sakar mata a kunne, wani iri yanayi taji tasoma shiga da zai iya skata manta abunda yafaru wanda bata buqatar hakan ayanzu, zumbur tamiqe adai dai lokacin da take fad'in.
" _I am really feeling so small for what I did, I ask for you forgiveness and hope you will do it now. Always Sorry from my side!_

Hannayenta tasa ta share fuskarta tana kallonsa cikin zafi da rad'ad'in qunar da zuciyarta keyi tunawa da kalaman da taji yayi ashekarun baya a cikin tv tace.
" _There is no place for forgiveness in this relationship, we've being separated for along time ago b'cos of so many embarrassed you couse to me and my son, always had issues but we held for too long, I do not have any more patience to be strong now, So i choose to breaking up with you peacefully, b'coz the love lost between us since!,_"

Tana gama fad'ar hakan tabar wajen batare data bari sun sake had'a idanuwa ba.

Kallo Dr yabita dashi bud'e da baki jin yanda take watso masa turanci tamkar ga bakinta aka halittosa, gaba d'aya ko kad'an kalamanta basu b'ata ransa ba, asalima farinciki yaji data bud'e baki tayi masa magana da harshen da baitab'a tsammani ba, wai matarsa Rashida, d'alibar nan tasa daya sani marar son karatu itace yau tsaye agabansa tana mayar masa da magana da kalaman dake nuna baqaramin gogewa tayi wajen karatuba kafin takai wannan matsayin da zata iya hakan, ji yayi kaso arba'in cikin damuwarsa ta ragu don ya tabbata da sannu zata haqura domin akwai banbanci tsakanin fushin mai cikakken ilimi da kuma marar ilimi matuqar zaiyi aiki dashi, murmushi yayi sannan yamiqe yafito ya samu har lokacin su Dr da little nanan waje zaunensu suna fira harda abbaty daya shigo lokacin.

Gaishesa yayi yana kallon fuskarsa sannan ya kalli ta little yana so yagano ko akwai kamanceceniyar tsakaninsu amma hakan ta cutara don shi little sak kamar mahaifiyarsa ce garesa d'an duhun fatar kad'aine ta mahaifinsa, maganar da abbaty yaji Dr Nuraddeen mahaifin little nayi da mahaifinsa yana yimasa sallama zai wuce ita tasa ya amince tabbas mahaifin nasa ne don batada banbanci data little d'insu.

Kasancewar yace nan zai kwana Amma hotel zaije ya kama kafin gobe yasa Dr da fatima suka roqesa daya kwana nan gidan amma fir yaqi amincewa, acewarsa zaifi wali acan fiye da nan don haka dole suka haqura, bayansa little yabi da zai tafi shima yace acan wajensa zai kwana abbaty nata yimasa dariya had'e da cewa.

"Yazama mayen babansa." Yace eh yadaiji,

Duk abunda akeyi Rashida na jikin window tana hangosu, sosai take kallon habibyn nata da bata samu ta kallesa da kyauba d'azun wanda little kad'aine ya hangota.

Ciro wayarsa yayi yana dariya yakirata da take tana hannunta ta d'aga batare data duba ba yace.

"Gwaggo ya kikaga habibynki?, Ki koma kadasu mama Fatima su hangoki, don babu mai rabaki dasu yau, nidai wajen baban zan kwana..."

"Marar kunyar yaro aje waya..."

Tafad'a tare da jayewa tasaki labulen,

Sosai little yasha mamaki da mahaifinsa ya fad'a masa yanda sukayi da mahaifiyarsa, murmushi yayi aransa yace lallai al_amarin Mata babba me, wato duk yanda suke son mutun sai sun ja masa aji idan yazo hannunsu, Ashe abun ma baga qanan mataba har da manya, azuci take maganar amma ashe bai sani ba tafito fili sai da yaji mahaifin nasa yajawosa ajiki had'e da laqqamosa tawuya yana dariya yace.

"Commoon my son, to meye laifin hakan, ai momynka ko makaranta taja ba aji ba ta cancanci tayi hakan, ko ka zata irin wannan a tsakaninkune kad'ai banda iyaye?."

Cikin jin kunya little ya shiga susar kai yana jin wata irin qunar mahaifin nasa aransa.

Kusan kwana Dr yayi yana kiranta taqi d'agawa, ya tura mata messages sunfi aqirga ba amsa, da safe ma sun koma shida little taqi saurarensa hakan yasa yakoma badon yanada ra'ayin hakan ba sai don ya fahimci tana buqatar lokaci kafin tahuce.

Saida akayi kusan sati ana abu guda da rarrashi Rashida taqi saukowa amma azuciyarta tuni tahaqura kawai tanayin hakan ne don tarama itama shikuwa da yariga da yasan laifin nasane sai bai damuba yaci gaba da bibiyarta,

A cikin satin ya sai wani qaton fili anan cikin bebeji aka aza masa gini part uku, kan kace me da yake ya riga daya tara kud'i nan take aka gama sashen d'aya tanadar masu shida Rashida da kuma mahaifiyarsa, shi kuma sauran akaci gaba da aiki ba dare ba rana wanda kusan little ne ke kula da komai.

A sati na biyune baaffa ya shirya da kansa shida baffa Usman suka fara zuwa gidan baba balarabe da Yaya Maryam suka roqi alfarmar da aba Rashida haquri tadawo mijinta tunda har yanzu aurensu nanan, sai alokacin baba balarabe da Yaya maryam suka san da shegantakar da Rashida keyi Wanda hakan ya matuqar basu mamaki, bayan kwana biyu suka sake shiryawa awannan karon kam booking little yasa aka yomasa na jirgi tafiyarsu da dawowarsu baffa da baba nusaiba sai Yaya balkisu da baffa Usman Wanda ahankali tuni rayuwarsu har tafara canzawa suka tafi borno wajen yamasa bikon Rashida, su kam su Dr abunma har dariya ya soma basu, musamman umma da ita kanta Rashidar wai biko tsofai tsofai da ita, a lokacinne ma su baffa suka samu damar had'uwa da Rashida da mahaifiyarta suka yimasu gaisuwar baffa tare da Basu haquri sosai kamar zasu yimasu sujada, umma da kunyar baffa takamata harda hawaye tayi na tausayin ganin yanda yakoma itama tabashi haquri, Basu koma ba saida dady yabasu tabbacin cewa in Sha ALLAH cikin satin ranar juma'a Rashida zata koma kenan idan ancire yau saura kwana hud'u, sunji dad'i sosai had'e dayin godiya sannan suka juya suka koma cike da farinciki azukatansu, musamman baffa da yakejin ko yanzu ALLAH yakarb'i rayuwarsa burinsa yagama cika aduniya.

Haba ana sanar da Dr Shire Shire suka koma sabbi yanda kukasan wanda za'a kaiwa sabiwar amarya, dama tuni ankammala duka ginin apart d'in uku har anyi fentin, part ne guda biyu plat sai d'ayan part d'in shi kuma hawa biyu wanda shine inda Dr Nuraddeen ya tanadarwa mahaifins, d'ayan plat part d'in kuma nashine, d'aya kuma na baffa Usman da baffa Ali, Amma duka an zagayesu waje d'aya anfitar masu da gate d'aya.

Hakama akwai wani qaton fili daya saya acan g.r.a dake cikin kano yasa ayi masa tsarin ginin gida biyu kowane sama da qasa, shima duka aka zagayesa amma gate d'in kowane gida aciki daban, wanda yayisu ne shi d'aya little d'aya Amma ba'a qarasa ginin ba ana kan yine.

Tuni dady yasa akazo aka zubawa Rashida kaya naji na fad'a a part d'insu ko ina Saida aka cike d'akunan tsaf da kaya masu kyau da tsada wanda tuni Dr Nuraddeen yayi niyar hakan Amma dady yace kawai yayi saving d'in kud'insa ga wasu matsalolin, Rashida kuwa abunma dariya yake Bata yanda taga anata Shire Shire sai kace za'ayi bukin amare ne, d'aukar abun takeyi tamkar wata almara don gaba d'aya ta kasa gasgata hakan wai itace yau zata koma gidan mijinta bayan wasu shekaru, wannan abu da ban mamaki tafad'a aranta duk da kuwa tuni suka daidaita da habibyn nata kullum suna maqale awaya kai ka rantse irin soyayyar nan ce ta samarin yanzu da 'yanmata, bata gasgata ba sai ana gobe zata tare, ranar kam tayi kuka sosai, haka ummanta, ba'a maganar Fatima da gaba d'aya kusan zazab'i soma kamata yayi amma babu yanda suka iya tunda dolene, roqon Dr Rashida tayi daya taimaketa yabata zainab 'yar autarsa lokacin tanada shekara goma sha 17, ko kad'an bazai iya hanata don haka yayi Mata alqawarin zai kaimata ita da kansa har gida idan lokacin yuyuwar hakan tayi Amma bada yanzu ba, Dole tahaqura tayita yimasu godiya tare da addu'ar ALLAH yabar zumunci tsakani.

Ticket d'in Jirgi d'aya Dr Nuraddeen yayi ooking ga duk wanda ke sha'awar zuwa rakiyar Rashida tun daga zuwa har dawowa don akwai gagarumar walima ta musamman da gwamna yasa aka shirya masa ranar asabar saboda rashin samun halartar ta ranar daya dawo da beyi ba, wanda hakan yayi masa dad'i yaroqi amaida masa da ita ta ganaral da kowa zai iya halarta don tayasa murnar reunion d'insa da iyalinsa, Kuma agidan gwamnati za'ayi,

Don haka gaba d'aya dady da familynsa kwai da kwarkwata manya suka hallara wajen rakiyar Rashida,

Koda suka Isa sun tarar da kayan sawa tun daga sutura mayafai takalmi man shafa, turarukka da sarqoqi masu tsada Dr Nuraddeen ya cika Mata wardrobe dasu, duk inda ka duba da akwai abunda kejere agefen.

Kowa sai murna da farinciki yakeyi tare da yimata barka da arziqi.

Batool kuwa tanajin zancen batun dawowar Rashida tabuga tsalle bazata koma ba sai angama.

Kasancewar su baffa baffa tuni suka tare tun kwana biyu da suka wuce yasa ba'a wani sha wahalar nemawa mutanen borno wajen kwana ba, wasu suka tsaya nan wasu kuma sukayi gidansu batool,

Dady da Dr da sauran maza mazan da aka zo dasu kuma suka tafiyarsu yarimawa gidan baba balarabe, umma kuma tatafi wajen 'yar uwarta aunty marwiyya, little ma tafiyarsa yayi wajen Batool d'insa don akwai d'aki na musamman da aka tanadar masu shida ita acan gidan don ya dad'e da zama d'an gida tuntuni.

Rashida kuwa aka barta ita kad'ai a part d'inta Babu Wanda ya tsaya har zuwa dare da Dr yadawo.

Saida yafara zuwa wajen mahaifiyarsa dake can pay din sama ita kad'ai sai wani d'aki dake gefe wanda anan ne aka saukar dasu zainab da hussaina da Fatima wato familyn Dr, qasa kuma nan baffa da baba nusaiba suke, gaishesu yayi tare da basu abunda ya siyo masu, Yaya hawwa ma ga baki yabata har taqoshi sannan yayi masu Saida safe yawuce part d'insa inda ya tarar da Rashida kitchen tana qoqarin dafa indomie don tasoma jin yunwa gashi dare yamiqa babusa ba labarinsa.

Tsaye yayi bakin qofar yana binta da kallo kafin yace.

"Ikon ALLAH, ni habibyn habibty yau wace irin amarya ce aka kawomun haka da zan tsinta a tsakiyar kicin."

Saida tayi dariya sannan yace.

"Amaryar da angonta ya shekara ashirin da tara batare daya sanyata a idanuwansa ba har ta tsofe, don haka metake dashi da zata tanadar masa balle har yasa ran zai iskota ad'aki Kuma a tsakiyar gado lullub'e kamar sauran amaren?."

_Gaisuwa ta musamman agareki sister *SALIHA MUSA* alkhairin ALLAH yakaimaki aduk inda kike, Ina godiya da yanda kike bibiyar littafinnan hakan yasa naga dacewar nayi maki kyautar wannan page sukutum, ngd sosai Allah yabaki aljannah da rahamarsa_πŸ‘





*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[11/14, 22:52] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️
πŸ”š *END*πŸ”š

Page___106πŸ’Ž

Daga inda yake tsaye a bakin qofar kitchen d'in yayi folding hannayensa akan qirjinsa yake kallonta yana aika mata da wasu irin saqwanni dake fitowa tun daga qasan zuciyarsa har zuwa cikin qwayar idanuwansa da itama taqurawa idanuwa tan kallo had'e da jiran amsar da zata fitowa daga bakinsa, batare daya tanka taba akan abunda tafad'a yake qoqarin ganar da ita sirrin dake kwance cikin zuciyarsa akanta, ganin haka yasa ta d'auke idanuwanta tare da juyawa taci gaba da dafa indomienta zuciyarta na qoqarin hakaito mata tarin ma'anoni da kuma fassarar saqwanninsa data hango cikin qwayar idanuwansa, wani irin murmushi mai sauti taji ya kuccikke mata batare data ankara ba wanda hakan ya tabbatar mata da gamsuwar da zuciyarta tayi na karb'ar saqwanninsa hannu biyu biyu, daidai lokacin taji motsinshi a bayanta cikin wata irin dasashshiyar murya yana fad'in.

" _I am extremely sorry for what i did habibty! at the same time, i also want to say thank you for being my wife, because you always show me the right path and correct my mistakes, i know It's hard sometimes to heal a broken soul but It's best to forget the things of the past and look forward a new life awaits you, do not think about how you were last look habibty, forward a new days dt's waiting for you, look forward beyond all the things, life is there so be certain pain will not remain in every time, So! Hope you w'll forgive me with all your holy heart_"

Yaqarasa maganar had'e dasa hannayensa ya juyo da ita suna fuskantar juna, riqo hannayenta yayi yana murza bayansu da manyan yatsun hannuwansa had'e da kallonta, murmushi tayi ta sunkuyar da kanta qasa cikin jin kunya, ita kam abubuwannan nasa da yakeyi gaba d'aya kunya suke sata, duk daya manyanta babu wani abu daya sauya daga cikin halayensa, d'abi'unsa da kuma tsarin rayuwarsa duk sunanan kmar yanda tasansu ada, dama malan bahaushe nacewa 'hali baran azaliya kuma mai hali baya fasa halinsa'.

Hura mata iska yayi a fuska ganin yanda ta antaya duniyar tunani tare da jayeta gefe yasa hannu ya d'auke indomien da take dafawa saboda qonewar da take nema tayi, zafin da yaji ga hannunsa yasashi saurin riqe hannun tare da yarfi dashi yana fad'in.

"Wash..ashe da zafi d'alibata...."

Kafin ya qarasa tayi saurin riqo hannun tana hura masa.

"Meyasa kasa hannunka ka d'auke batare da kasa qyalle ba gashi kaje ka qona kanka, sannu ku."

Tafad'a tanaci gaba da hura wajen da iskan bakinta, tsura mata idanuwa yayi yana kallo har ta d'ago kai tana riqe da hannun tace.

"Sannu"

"Nagode"

Hannu tasa ta kashe gas d'in tare da ciro d'aya daga cikin filetis d'in dake here wajen ta d'auraye ta juye indomien akai sannan ta juya riqe da ita zatabar kitchen d'in yayi saurin shan gabanta.

"Haba ranki shi dad'e ya bakice komai ba zaki wuce kibarni a tsaye.?"

"Au! Afuwan yunwa nakeji, bana kai irin wannan lokacin banyi taking dinner ba, am sorry."

Tana gama fad'a tafice, shi kuwa kamar sakarai ya sake duqawa ya d'auko ledojin daya shigo dasu tare da plate mai d'an girma da kofuka biyu ya iskota dasu akan dining area inda take zaune tanacin abincinta hankali kwance."

Tsuramata idanuwa yayi batare daya katseta ba har saida yaga tayi rabi sannan ya ture plate d'in agefenta ya aza mata wanda yazo dashi ya fiddo rousted fish d'in dake cikin d'ayar ledar da yazo da ita ya aza akai yasha source d'in tarugu sai soyayyen arish dake gefen kifin da yankakken cocumber da cabbage da kuma albasa.

"Muci wannan ko habibty!"

"Gaskiya naqoshi, kaci ni kabarni in qarasa indomie na."

Marairaice mata fuska yayi had'e da cewa.

"Don ALLAH idan wani hukuncin ne ki sassautamun tunda naga har yanzu baki yafemun ba."

"Ko kad'an yallab'ai komai yawuce aguna, _dama ni since the day i married you, i knew i don't deserve someone as great as you, and with the mistakes you have committed, I know you deserve someone better too, but with all the love in my heart that i have for you, i realized i have to accept every single of my destiny over you, wether i like or not, all I hv is to work things out, fill your life with magic again, strong our relationship till d world end up and in sha ALLAH I'll live up to my vows, to the promises i made when i said 'I do',_ so ka kwantar da hankalinka komai yawuce da yardar ALLAH."

"Sure." Yafad'a yana kallon cikin idanuwanta.

"Yes malamina."

"Oya show me and hug me if it's true madam!."

"Lalalalaaa...karufan asiri da hug d'in nan habiby we're a matured anough fa yanzu."

"Ki kace?"

"Eh man, ai gaskiya nafad'a."

"Shikenan nayarda, Amma ayi haquri aci abincinnan."

Yaqarasa maganar tare da d'ebo kifin yakai mata abaki, murmushi tayi tasa hannu ta karb'e sannan takai abakinta tanaci shi kuma ya jawo sauran indomien duk da tafara sanyi yanaci, ahankali takecin kifin tana kallonsa har ya cinye indomien tas sannan ta tura masa plate d'in kifin shima agabansa, sai daya ciro lamukkan dake cikin d'ayar ledar ya ajiye mata d'aya agabanta sannan shi kuma yaci gaba dacin sauran kifin.

Bayan sun kammala ya taimaka mata suka kwashe kayan tare ta wankesu tas tare da tukunyar da tayi amfani ta tsanesu ta goge da qyalle ta mayar da kowane inda yake, lokacin shi kuma har yafito wanka don haka itama tana shiga tawuce toilet ta watso ruwa, dama tayi sallarta ta isha'i da shafa'i da wuturi don haka alwar bacci kawai tayo tafito ta zura doguwar rigarta ta bacci tanemi waje gefen gado ta kwanta.

Tana jinsa yana jero addu'o'insa bayan yagama sallolinsa wud'anda rabinsu duk kusan akanta yakeyi da kuma mahifansa da yaronsa, bayan ya kammala ya kashe fitilar d'akin shima ya haye gadon yakwanta a rigingine yana kallon rufin d'akin duk da dai duhun daya mamaye d'akin bazai bari kafahimci me yakeyi ba yadai qurawa saman idanuwa.

Yafi mintuna biyar ahaka kafin can ya saki wata irin ajiyar zuciya had'e da cewa.

"Habibty ni kuwa abubuwa biyu sun d'aure mani kai acikin al'amurranki."

Da yake itama batayi baccin ba tajuya kwancinta kamar yanda yayi sannan tace, "kamar name kenan?"

"Kiyi haquri da abunda zan fad'a, Amma nayi mamaki sosai da nasamu labarin cewa bakiyi wani auren ba duk tsawon wud'annan shekaru da suka shud'e, na biyu yanda naji cewa kintaka wani matsayi a karatu kuma kikayi zaune ba tare da kinfara aiki ba bayan kinada damar yin hakan."

"Ikon ALLAH, ai wannan ba abun mamaki bane saboda ni nasa kaina kuma ra'ayina ne amma dai akwai lokacin dasu umma da dady sukayi qoqarin ganin annemi su baffa saboda a warware auren tunda ba'asan lokacin dawowarka ba don kada abun ya zamo akwai cutarwa aciki da ganin gaba d'aya zaman nawama ba dacewa bane amma sai na nuna masu rashin amincewata, badon komai ba sai don alokacin ni gaba d'aya aure yafice mani arai, bana sha'awarsa ko kad'an saboda ganin irin tarin matsalolin dana fuskanta aciki, da yaudara ta da nake kallon kayi, hakan yasa umma tabi ra'ayina duk da kuwa bata so zaman nawaba amma damuwowin da taga sunyi mani yawa yasa bata matsa mani ba akan dole sai ankashe auren don tasan matuqar aka kasheshi dole sai wasu sunzo neman aurena, gashi nace banida buqatar hakan, wud'annan dalilan nawa su suka iya qarfafata tare da bani qwarin guiwar iya kaiwa wannan lokaci batare da nadamu dayin aure ba, auren yariga yaficemun arai banada sha'awarsa"

"Tirqashi, Amma kinyi namijin qoqari gaskiya don awannan duniyar samun matan dake da irin wannan juriyar abune mai wahala, ubangiji ALLAH yabaki dukanin ladar da kika rayu aqarqashin inuwar aurena aduk tsawon wannan lokaci."

"Amin ya rabbi, ni nasama raina zan iya kuma nayi hakan, wanda yakamata mata da yawa da ALLAH yajarabta da rashin aure su fahimci cewa rashin yinsa is not d ended of their life, komai lokacine kuma duk nisan abu matuqar anasan ran isa garesa to tabbas za'a cimmasa, juriya, haquri da kuma qarfafa zuciya shi kawai ake buqata nan za'a tabbatar da cewa SANNU SANNU bazata hana tafiya ba, kamar yanda gashi yau ALLAH yanuna mani dawowarka duk da banyi tsammanin hakan ba kuma har mun sake komawa a inuwar da nayi tsammanin banida sauran sha'awa da ra'ayi akanta, to haka duk maccen da zataga ta dad'e agida ba aure kada tayi tsammanin lokaci bazai zoba da zatayisa matuqar ALLAH ya rubuto zatayisa d'in, to ba zato ba tsammani saidai kawai tawayi gari tana agidan mijinta, sai maganar aiki, su uncle dai sun sani karatu saboda sanin koda kana nan ALLAH bai haramta mani yinsa ba asalima haqiine akanka kabarni inje innemo ilimin, Amma shi aiki abune wanda bayada dole akanka, bazai halasta inyisa ba har saida amincewarka, shiyasa sukaga duk da baka nan babu halascin yinsa agareni tunda bamu rabuba har saida amincewarka, wannan shine dalilin."

Nan ma wata ajiyar zuciya ya sauke kafin yace.

"A gaskiya bayin ALLAHn nan sunkai qololuwa wajen sanin haqqin d'an adam tare da kyautata zamantakewa, tun lokacin da nasamu labarin irin karamcin da sukayi mana nake tunanin mezanyi na saka masu amma nakasa, wlh inada matuqar kunyarsu akaina."

"Bazaka iya biyansu ba ko kad'an habiby, abu d'aya zakayi ka kwatanta biyansu shine kadinga skasu acikin dukkanin addu'o'inka da dukkanin sallolinka na farillah, hakan shi kad'aine zaisa karage nauyin kunyarsu dake kanmu."

"In Sha ALLAH zan kiyaye hakan har iya qarshen rayuwata."

Yaqare maganar tare da jawota ajiki yana fad'a mata kalamai masu sanyi da kuma kwantar da zuciya dake tabbatar mata da irin zunzurutun qaunar da yake yimata.

β€’β€’β€’ β€’β€’β€’ β€’β€’β€’
Da safe bayan sun gama karyawa suka shirya tare suka nufi part d'insu baffa, kai tsaye sama Dr Nuraddeen yanufa wajen mahaifinsa ita kuma ta tsaya nan qasa wajen baba nusaiba suna gaisawa, bayan sun gama gaisawa takira mata baffa da alokacin

Please Login or Register in order to submit comment