Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yafito wanka shima yagama shiryawa tsaf suka gaisa, wata irin kunyarsa ce tarufe Rashida don sai ayanzu take ganin rashin kyautawarta na waiwayarsa duk da irin tarin soyayya da qaunar daya nuna mata, daya fahimci hakan yayi murmushi tare da yimata nasiha akan ta manta da komai bawa bai Isa yakaucewa duk wani tsari da ALLAH yayi masa ba arayuwa, nan ya shiga qwalawa yaransa kira duk da kuwa kowace tagirma abunta don karatu sukeyi sosai batare da baffa yadamu da girmansu ko ganin cewa su yara bane, Rashida ma tuni ta kammala jami'a yanzu haka tana wajen sarvice, wanda sosai gwaggo Rashida taji dad'in takwarar da baffa yayi mata kuma taqara tabbatar da qaunarsa agareta, haka ma mai sunan mahaifinta auta bashar (Abba) da take kira da aminina da Rashida taganesa harda qwalla tayi jin sunan mahaifinta ya saka mashi, shima dai masha ALLAH ya girma don yanzu matakin farko take na junior secondary School, sun d'an jima ana fira kafin baba nusaiba tace tazo suje can sama wajen Yaya hawwa.

Gabanta ne yafad'i tayi saurin yin ta'awizi had'e da bin bayanta har suka isa d'akin Dr Nuraddeen na zaune yana bata ruwa abaki yana yimata firar Rashida.

"'yar halak, kingata nan tashigo innarmu, nazata ma jira takeyi sai nakoma qasa nad'auko maki ita,"

Yaqare maganar yana matsa yatsun qafar Rashida dake kusa dashi, ita dai ko kulashi batayi ba saboda yanda taga Yaya hawwa takoma, tsananin tsufan da tayi yasa ta tamuqe waje d'aya tamkar irin qananan yarannan, wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata tana Mai qara jin tsoron ALLAH yarufeta, tabbas mutum ba komai bane arayu kuma idan ka d'au duniya da zafi akwai ranar da zata qonaka da kanka, in Kuma kana kallon kanka wata tsiya da SANNU SANNU duniya zata nuna maka kai ba kowa bane.

Gaisawar da taji baba nusaiba nayi da Dr Nuraddeen yasa tadawo hayyacinta daga tashin hankalin da tashiga, cikin tausayawa ta duqa kusa da Yaya hawwa tana gaisheta, juye juye yaya hawwa ta shigayi tanabin sautin Rashida ta yanda zata iya ganinta amma inaaaa, babu ganin idanuwan balle taganeta.

Cikin kuka da muryar nadama tashiga roqon Rashida gafara tana mai nuna mata irin halin da tashiga duk saboda haqqinta data d'auka, don ALLAH tayafe mata.

Cikin kuka Rashida tace.

"Inna nayafe maki duniya da lahira, Ina roqon kema kiyafemun abubuwan dana aikata maki da sune suka jagoranci zuciyarki wajen aikata abunda yafaru."

"A'a ni bakimun komai ba, son zuciya kad'aine yasa nayi maki haka, gashi ALLAH ya nuna mani ikonsa aqoqarina naganin cewa sai kin rabu da d'ana ni anrabani dashi na tsawon shekaru, idan ma wani abunne kamar yanda baki moresa ba haka nima ALLAH yahanani moriyarsa alokacin da nake matuqar buqatarsa, shi ubangiji ba'ayi masa dubara kuma ba'a isa a Hana wanzuwar ikonsa ba a yanda yaso, gashi ALLAH yaqara had'aku a qarqashin inuwar da nayi qoqarin tunb'ukeki a qarqashinta, ni kuma an shafe mani idanuwan da zasu iya gano mani abunda yahaifar mani da shiga cikin wannan halin awancan lokacin."

Sun jima suna Abu d'aya har dai kowanensu ya yafi juna, Wanda sai alokacin taji mutuwar Inna ruqayya, tayi kuka sosai kuma tayafe mata tare da roqa mata gafarar ubangiji sannan suka baro wajenta.

'Bangaren baffa Usman tanufa ita da yarinyar baba nusaiba shi kuma ya tsaya wajen baffa su gaisa, acan ta tarar da baffa Ali aka gaggaisa shima ta tausaya masa halin da taganesa aciki sosai ya kuma roqeta gafarar abunda yayi mata tare da roqawa matarsa kuma duk ta yafe masu tana kuka, ji take aranta da gaba d'aya Bata kyauta ba da tun farko batacewa ubangiji tayafesu ba har haqqinta da na sauran mutane ya illata rayukkansu haka, koba komai tasan matuqar tayafe nata zasu samu sassaucin hukuntawa ko kad'an ne.

Tana zaune dasu Inna Bilkisu saiga muneera ta shigo, dashe baki tayi cikin farincikin ganin Rashida tana fad'in.

"Ahhh, kaga uwargidan kuma amaryar Yaya nura ashe rai kanga rai?"

Rashida na murmushi tace.

"ALLAH yanufa hajia muneera kece haka.!"

Muneera tawashe baki tare da Bata hannu suka tafe, saida suka gaisa sosai sannan Rashida tashiga yimata gaisuwar rashin mahaifiyarta Inna ruqayya itama tayi mata ta baba kowanens cike alhinin rashin mahaifan nasu, daga nan kuma fira ta canza tsakaninsu kai kace wasu aminan junane har muneera taqara roqon Rashida akan ta yafewa mahaifiyarta.

Ana haka Dr Nuraddeen ya shigo, muneera na ganinsa ta d'auke kai cike da kunya, saida suka gama gaggaisawa dasu baffa da Inna Bilkisu sannan ya kaikaita idanuwansu had'e da juyowa yana kallon Rashida ya kashe mata ido d'aya tayi saurin kauda kai gefe, dariya yayi sannan yakalli muneera data sunkuye kai qasa yace.

"Aunty muneera badai har kin shigo ba?, Ina kika baro mijin naki kika tahowarki."

"Yana wajen sauran matansa ya nura, yau nice aunty kuma?"

Tafad'a tana dariya,

"Eh mana, ai yanzu kin zama babbar aunty koba haka bane habibty."

Ita dai Rashida tsabar kunya miqewa tayi hade da yimasu sallama takoma part d'insu.

Kasancewar qarfe goma za'a gabatar da walimar da gwamna ya shiryawa Dr Nuraddeen yasa koda qarfe tara da rabi tayi har ancika gidan da wud'anda zasuje, tuni Dr Nuraddeen yasa aka d'auko wacce zata gyara masa Rashidarsa tafito kalar matar manya Wanda nan take kan kace me har anyi angama don dama matar qwararrace sosai, kallo daya zakayiwa Rashida ka d'auka itace matar gwamnan jahar gaba d'aya saboda yanda tayi kyau, ga sarqoqi masu kyau da matuqar d'aukar hankali da suka hau jikinta daidai tafito masha ALLAH abunta.

Qarfe goma da rabi aka fara gabatar da walimar wanda koda sha biyu da rabi tayi har angama, walima kam tayi kyau abun ba'a magana komai anyisa cikin tsari da tsaro saboda manya manyan mutanen da suka samu halartar wajen,

An karrama little da kambu kala biyu na farkon daga fannin sashen lafiya ne, na biyu kuma daga wajen gwamna, sannan kuma aka qaddamar dashi a matsayin kwamishinan lafiya na jahar don sun tattauna da gwamnan tun kafin yau yanuna bayada buqatarci gaba da aikin likitanci Amma zai bada gudun mawa ga dukkanin asibitotan dake buqatar taimakonsa wannan dalilinne yasa gwamna ya nad'asa matsayin kwamishinan a fannin lafiya ta jahar, Rashida itace wanda tayiwa Dr Nuraddeen jawabin godiya bisa wannan karramawar daya samu, Wanda mutane da dama taburgesu yanda sukaji tana speach agaban mutane cikin girmamawa.


Bayan an watsene Abba dasu uncle h suka sake bayyana agaban Dr Nuraddeen da matarsa Rashida suka tayasu murna, nan dai Abba ya sake daurewa suka roqi yafiyar juna da Rashida akan abunda yafaru abaya sannan suka wuce.

Kusan ranar yini su Dr sukayi suna karb'ar baquncin mutane masu zuwa tayasu murna da kuma barka da arziqi wanda saida Dr Nuraddeen yayi daqyar yasamu yaja iyalinsa suka bawa junansu kulawar daya kamata.

Da marece su Rashida na zaune dasu batool da yake itama agidan tawuni baffa yashigo shida baffa Usman bayan angaisa yaciro wasu kud'ad'e masu yawa a aljihunsa yamiqawa Rashida had'e da cewa.

"Wud'annan kud'ad'en da kike gani haqqinki ne halak malak gasu nan dubu d'ari hud'une da tamanin, bayan b'atanki da rashin dawowar mijinki mukaga kayan d'akinki na Shirin lalacewa nida Usman muka yanke shawarar saidasu mu jujjuya maki kafin ALLAH ya bayyanaki, a lokacin mun saida komai akan dubu d'ari biyu da saba'in, da muka juyasu ne suka zamo haka, sannan acan wancan gidan dana taso akwai gonar kaji da nake kiwo Ina saida su to gaba d'aya naki ne, sai wani d'an qaramin fili shima ga takardunsa duka haqqinkine,"

Yaqare maganar yana karb'ar takardun daga hannun baffa Usman yamiqa mata.

Shiru Rashida tayi tana kallon baffa, gaba d'aya Bata sanma wane irin mutunne shi da ALLAH ya halitta mai tsananin qana'a da kuma taka tsantsan, little ma sakin baki yayi yana kallon baffa, don bai tab'a fad'a masa wannan sirrinba, asalima yanada yaqinin Babu Wanda yasan da wannan sirrin idan bashi da d'an uwansa ba.

Tajima shiru kafin tahad'a kud'in da takardun ta sake mayarwa da baffa tace tabar masa su gaba d'aya duniya da lahira amma yabuga kai ga qasa yace bazai karb'a ba.

Dr Nuraddeen kam burgesa mahaifinsa yayi ya d'aga hannuwa sama yana roqa masa amincin ALLAH duniya da lahira tare da tsawon rai, tanaji tana gani baffa yaqi amsar komai sukayi tafiyarsu, acewarsa don ALLAH yayi don haka yafison ALLAHn yabiyasa da kansa.

Kiran umma tayi ta sanar da ita dasu baba balarabe, suma sun sha mamaki sosai don maganar gaskiya su har ga ALLAH sun ma manta da wasu zancen kayan d'akinta, kiransa sukayi suka roqesa akan yakarb'a tunda ita ta bashi Amma yace a'a yadai gode, ummace tayi saurin rantsewa akan to bazasu karb'i gonar kajin ba, don haka sun barmasa idan ma bayaso to shima yayi kyauta da ita.

Badon yaso hakan ba yace shikenan ya amince kuma yagode.

Godiyar da yazo yayiwa Rashida tasa Dr Nuraddeen da yaji yaquduri rushe wancan gidan na baffa ya zuba masa wasu kajin masu yawa kuma ya mayar masa dashi wajen kiwon kaji ya zuba masa wud'anda zasu dinga kula masa da wajen.

••• ••• •••
Da daddare su batool na zaune suna zancen ranar komawarta da little don ya dage akan dole gobe tabisu Dr da dady su koma saiga Abba ya shigo paloun don dama su kad'aine a zaune su hassana da hussaina suna can wajen gwaggo Rashida da sukaje zasu dawowa suka tsira rigima sai an barosu wajenta Dr Nuraddeen yace su qyalesu, dole suka haqura suka barosu,

Suna ganin Abba yashigo suka saki firar suka shiga d'auko wani sabon babi ana tayi haddashi yana dariya, SANNU SANNU falon yafara cika har dasu uncle da shurahbil da sauran matan gidan,

Cike da tsokana uncle Hussain ya shiga Basu labarin mafarkin Abba yana dariya tuno yanda ya rud'e ranar har yana cewa batool "ya kamata tad'an sakarwa sauran 'yan uwanta space a zuciyar abbanta don soyayyar da take yimata tayi yawa."

Sai alokacin tafahimci dalilinsa na ranar daya dinga cewa kada tazo ita kuma ta nace badon tasan da abunda ke faruwa ba, Wanda badon girman addu'ar iyayen nata ba data tabbata babu abunda zai hana mafarkinsa ya tabbata ko don bijirewar data yimasa da yace kada tazo, tabbas tayi kuskure Amma daga yau bazata koma bijirewa iyayenta ba da yardar ALLAH.

Ganin yanda tad'an canza yasa Abba yayi murmushi had'e da cewa.

"Ki kwantar da hankalinki dota, komai yariga daya wuce babu abunda zai faru in sha ALLAH, ni abunda ma yafi bani mamaki a mafarkin, shine wasu mutanen dana gani wanda bangansu yanzu atare daku ba cikin family d'in nasa."

Dariya su uncle h sukayi harda hajia mama tace.

"Ikon ALLAH, to alhaji ai ba lallai bane ace duk abunda kagani a mafarki dole ka ganshi azahiri ba, tunda gashi kaga batool ta haukace gata da hankalinta, little ya rasu gashi kuma raye don haka badole sai kaga komai ya bayyana ba."

"A'a hajia mama, da gaskiyar Abbana, amma dole yayi mamaki, Abbana zainab d'in daka gani a mafarkinka autace, d'iyarsu Dr da mama Fatima tazo maka a matsayin qanwarsa, qila antabayin zancenta agabanka, shi kuma wannan abokin nasa inaga dai Dr ne har yau zancen shi barrister ne shi kuma matsayin gwaggone mafarkinka ya qwace yabawa abokinsa na mafarki daka gani"

Aikuwa batool narufe baki da wannan dogon bayani nata duk aka kwashe da dariya a falon kowa na ganin wautarta ciki harda little da har yasoma hawaye, kaikaita idanuwan iyayenta tayi takai masa mintsili a gefen ciki tare da watsa masa harara, hajia mama tace,

"Ahaf! In dai shirmen batool ne ai tafiye nan, bari ni naje na kwanta don bazan iya dashi ba"

Bayan kwana biyu Abba yafara fita office said gashi ranar ya dawowa Rashida da takardar shedar samun aiki a federal high court dake nan cikin kano, ta matuqar mamakin yanda yayi neman mata aikin har ya gama batare daya sanar da ita ba, don ko takardunta batasan lokacin daya d'auka ba, shiru tayi tana tunanin ta ina ma zata fara yimasa godiya don har ga ALLAH tana sha'awaryin aikin kuma taji dad'in wannan kyautatawar da yayi mata sosai, Bata tab'a kawowa ranta cewa zai amince tayi aikin ba don gwargwado ALLAH yarufa masu asirin da koda da ita har shi basu nemi aiki ba zai ishesu arayuwa don babu abunda suka nema aduniya suka rasa sai gashi cikin ruwan sanyi da yake babba yake cikin gwamnatin kuma takardunta sunyi kyau sosai yasama mata aiki, kamar yasan abunda take tunani aranta yace.

"Kidena matsawa kanki da tunanin mme zakiyi mani akan haka ko a ina nasamu takardunki ko kuma yanda na amince dayin aikinki duk da bamu rasa komai ba domin kin cancanci inyi maki fiye da hakan, sannan zuciyarki da tawa abu d'ayane duk abunda kike so nasani kinga kuwa dole nayi makishi matuqar zai sakaki farinciki, fatana kawai kici gaba dayi mani soyayya mai yawa tare da kula dani yanda yakamata."

Murmushi tayi sannan ta kallesa had'e da cewa.

"Shi kad'ai kake buqata...?"

Kafin tarufe baki yayi saurin bud'e hannayensa had'e da cewa.

"Tare da wannan."

Cike da dattijantaka irin tamanta tayi murmushi sannan tashige tsakiyar hannayen nasa d'aya bud'e ya mayar ya rufe yana mai d'ora kansa saman kafad'arta, tace

"Hmm! Gaba d'aya kai baka tsufar da wannan soyayyar taka habiby."

"Habibty kenan, ai soyayya bata tsufa matuqar nagartacciyar ce, mutanen da keyinta kad'ai ke tsufa ni kuma awajena tsufa baya hana soyayya.

Yaqarasa maganar had'e da kissing d'inta saman kai.

" _Thank you habibty, thank you so much for your kind gesture it really made my day more special, you took time and did something magical i won't ever forget this all my life, thanks! a word is straightly from my heart for being so considerate and kind thanks a lot! and really luv you so much._"

Ta fad'a tare da qara shigewa jikinsa.

Hannu yasa cikin aljihu ya ciro makullin sabuwar motar daya siyo mata don fita aiki sannan yacirota daga jikinsa ya riqo hannunta ya aza mata akai, ware idanuwa tayi zatayi magana ya aza yatsansa abakinta had'e da cewa.

"Me zai hana kici gaba da qara yimun addu'a a maimakon wannan godiyar, wannan makullin motar kice anjima sai muje ki d'auko."

Yaqarasa maganar had'e da kashe mata ido d'aya yayi kissing forehead d'inta yana murmushi sannan yabar wajen.

Wannan karon Rashida kam harda hawayen farinciki tayi, tare da d'aga hannye sama tayi masa addu'a Mai tsawo sannan tabi bayansa.

Cikin sati d'aya Dr Nuraddeen yaje da Rashida sukayi duk abunda ya kamata wajen aikin nata sannan tasoma zuwa.

Umma tayi farinciki sosai da tasamu labari Kuma taroqi ALLAH daya tsare mata 'yarta sannan ya sanya alkhairi mai yawa acikin aikin nata, taso ace mahaifin Rashida naraye taga irin farincikin da zaiyi na cikar burinsa daya tabbata ga 'yarsa amma inaaa, mai rabawa tariga taraba saidai fatan ALLAH yajiqansa mukuma yasa mucika da imani.

*BAYAN SATI BIYU*

Bayan sati biyu da komawarsu batool borno ALLAH ya sauketa lafiya anyi mata tiyata aka fiddo mata da kyawawan yaranta gaba d'aya maza sak ita, inda murna ba'a magana awajensu Rashida da Dr Nuraddeen tamkar su tashi sama tsabar farinciki don har sunfi iyayen jariran murna, wanda kasancewar kwananta uku aka sallameta saboda tiyatar tayanzu anci gaba sosai sati na zagayowa aka rad'awa yaran suna, Hassan yaci sunan baffa Usman wato (Usman), shi kuma Hussain yaci sunan Abba mahaifin batool wato (umar faruq), batool taso abarsu da sunayensu amma little yace a'a haka yakeso adinga kiransu, tabari idan tahaifi wasu 'yan biyu maza sai abarsu Hassan da Hussain, Babu yanda ta iya dole tabi ra'ayinsa tare da fatar ALLAH yaraya matasu rayuwar musulunci, Amma azuciyarta taraya cewa itakam da haihuwa ba yanzu ba balle yace idan ta sake haihuwa kuma waima wasu 'yan biyun sai kace akuya, Sosai Abba yaji dad'in samun takwara haka ma baffa yaji dad'in takwaran da aka yiwa d'an uwansa tare da saka masu albarka.

Baba balarabe ma yamiqa dukkannin haqqin Rashida na gado da umma agaresu tare da dabbobin dake hannunsa daya jujjuaya masu da wasu kud'ad'e da ake karb'a na haya, wanda nan yayi masu bayanin cewa daga baya da yaga gidan na shirin mutuwa ne ya yanke shawarar zuba 'yan haya aciki tunda yayiwa umma magana tuntuni akan gadon tace duk yanda yayi daidaine tunda gwargwado suna cikin wadata ita da Rashida yayi amfani dashi har lokacin da buqatar karb'arsa zai taso, duk da haka saida yasa aka raba aka cire masu haqqinsu shine yasayi dabbobi yana yimasu kiwonsu, acikin kud'in hayar da ake bashine yake cida dabbobin da sauran abubuwa, yanzu kuma yamiqa komai ne agaresu saboda ganin yayi rauni ta ALLAH zata iya kasancewa kansa akoda yaushe shiyasa ya hannunta masu abinsu, sukayita yimasa godiya sosai bayan sunyi masa alkhairi.

Rashida kam kud'ad'enta da baba balarabe ya bata da wudanda baffa yakawo mata acan qauyensu tahad'asu tabayar tace agina masallaci sadaqatul jariya zuwa ga mahaifinta, da Basu isa ba Dr Nuraddeen ya qara mata wasu aka Ida kammala ginin.

Yaya hawwa kuwa cikin taimakon ALLAH da Nuraddeen ya kaita asibiti aka aunata akace bawani magani da za'a yimata idanuwanta ba zasu iya warkewa ba balle ganinta yadawo Rashida ta nace da daddare wajen yimata addua'a tana tofa mata ga ruwa ita da baffa Ali tana basu susha kuma su shafe jiki ita kuma idanuwa tun da safe kafin suci komai sai gashi duk sun warke gaba d'aya bisa yardar ALLAH, qurajen baffa sun b'ace kamar bai tab'a yi ba, ita kuma yaya hawwa ganinta yadawo tas. _('yar uwa kinada buqata ko wani abu dake damunki?, to kijure kuma kijajirce dayin wannan addu'ar👇, wlh tallahi matuqar baki gajiyaba dayi kuma kikasa yaqini akan ubangijinki to zakiga biyan buqata da waraka da yardar ALLAH, itace Rashida tayi har baffa Ali da Yaya hawwa suka samu waraka ga cutukkan da ake tsammanin sai mutuwa tsakaninsu dasu)_

A kullum takan tashi da daddare misalin qarfe uku tayi arwala saita sallaci raka'a biyu ta nafila tare da 'yan ruwa agefenta kamanin rabin kofi.
_*A raka'a ta farko tana karanta suratul ikhlas, wato qul'a'uzu birabbin nas qafa goma(10) saita tofa acikin ruwan sai tayi ruku'i, idan ta d'ago daga ruku'i saita karanta wata (suratul ikhlas) qafa ashirin(20) ta tofa cikin ruwan sannan taje sujada ta farko idan ta d'ago saita karanta suratul ikhlas d'in qafa uku(3) ta tofa saita koma sujada ta biyu, idan ta d'ago ta sake karanta qafa uku(3) ta tofa duka acikin ruwan sannan saita miqe zuwa raka'a ta biyu ta sake karanto suratul ikhlas qafa goma(10) saita tofa taje ruku'i, idan ta d'ago sai ta karanta qafa ashirin(20) ta tofa sannan taje sujada, idanta d'ago saita karanta qafa uku(3) ta tofa sannan ta sake komawa sujada, to anan idan ta d'ago bazata karanta suratul ikhlas d'in ba sai tayi tahiya tagama kafin ta sallame saita karanta qafa uku(3) ta tofa sannan tayi sallama, tana sallamewa bayan tayi istigfari saita karanta ayatul kursiyu qafa d'aya(1) ta tofa duka acikin ruwan sannan tayi salatin annabi sau d'ari(100) ta tofa aciki, idan ita keda matsala bayan tagama addu'o'inta saita rufe ruwan ta ajiye, tun da sassafe kafin taci komai saita sha ta kuma shafa a inda matsalar take idan kuma ba ciwo bane to saita shanye ruwan kawai basai ta shafa ba musamman in nacan cikin jikine daba bayyananne ba, idanma tana tsoron kada shed'an ya mantar da ita da safe zata iya tana gama sallar da daddare bayan tayi addu'o'in ta saita shanye, in kuma wani akayiwa to sai arufe ruwan a ajiye kuma ayi qoqarin bashisu yasha kafin yaci komai da safe, in Sha ALLAH ko menene damuwa ko tsananin ciwo in aka nace dayin wannan sallar to tabbas za'a samu waraka da izinin ALLAH, ammafa sai an jajirce don la'anatullahi yakan bijiro da kasala sai anyi da gaske*_ (wannan addu'a sadaka ce zuwa ga mahaifina Ina bara duk wacce ALLAH yabawa ikonyi data sakashi cikin addu'o'in ta ALLAH yajiqanshi kuma yayi masa rahama da shi da dukkanin musulmi baki d'aya, ALLAH kasa adace👏)

Hakan Rashida tayi tayi har ALLAH yasa aka cimma ijaba Yaya hawwa da baffa Ali suka warke, alokacin sun sake yin kuka sosai tare da nadamar abunda suka aikata mata gashi batare da tayi la'akari da wannan ba tayi amfani da qarfinta da ilimin da ALLAH yabata tahana kanta bacci taroqa masu samun waraka da kuma magani ga ALLAH don su samu lafiya, haka ake son zuciyar musulmi ta kasance akoda yau she mai tsananin yafiya da kuma rama alkhairi ga junansu,

Haka rayuwar ahalin ta kasance cikin farinciki da kuma zaman lafiya da girmama juna, tuni anka gudanar da auren Yusuf da Rashida 'yar baffa, manyan 'yan boko don gaba d'ayansu sunyi karatu Mai zurfi Wanda baffa ke alfahari da hakan, acan asalin family house inda su baffa Usman sukayi zama Yusuf ya saye duka shiyoyin guda uku ya rushe ya qera gidansa mai kyau irin nasu na 'yan boko wayayyi haka ma Dr Nuraddeen da kansa yasama masu aiki tunda gwamnatin jahar dashi take damawa tare da shahida da itama tuni takammalo karatun daga qasar waje suka daidaita da Uncle Hussain d'an baba balarabe aka d'aura masu aure, yanzu haka suna nan zaunensu kano wajen aikinsu guda da ita da Rashida matar yusuf, little kuwa yana can borno abunsa yayi zamanninsa acan saidai idan sunyi sha'awar zuwa nan kano suzo suyi satukka ko wata d'aya su koma musamman idan yara na hutu,

Zainab ma autarsu Dr nura tana hannunsu Rashida kamar yanda Dr ya alqawarta komai nata gaba d'aya yadawo wajensu, tana samun kulawa sosai fiye da tsammani don ba kad'an suke jin taba har cikin qoqon ransu wanda tuni itama suka daidaita da shurahbil d'an wajen uncle Hussain baffan batool, amma saita qare karatu tukuna za'ayi auren, zainaba ma 'yar baffa ta biyu itama tayi aure amma acan cikin kano take zaune da mijinta bayan ta kammala karatunta itama, asiya da Bilkisu kad'aine suka rage wud'anda suma gaba d'aya sun koma hannun Rashida tare da zainab sukeyin komai hatta karatu waje d'aya sukeyi, Babu wani banbanci tsakaninsu ko fifiko don su Dr Nuraddeen sun nuna masu abu d'aya suke awajensu saboda haka suso juna, haka ma auta basha (Abba) son da Rashida keyi masa yasa da wayo da wayo ta raboshi hannunsu baffa yadawo wajensu,

Su baffa suka koma daga shi sai baba nusaiba babu yaro ko d'aya agabansu, ga masu aiki Nuraddeen ya zuba masu, banda suci su kwanta babu abunda sukeyi, nan take tufan da yakawowa baffa hari har yana neman durqusar dashi ya gudu gaba d'aya ya murmure yayi haske sosai tamkar ba shi ba, Yaya hawwa ma ba laifi saboda Rashida nakula da ita sosai kuma tana cikin qoshin lafiya daidai gwargwado, tafiya kad'aice har yau bata iyayi wataqil hakan nada nasaba da irin wahalhalun data fuskanta alokacin da tana gidan mahaukata, Kuma hakan be dameta ba, kullum cikin zikiri take da tilawa alqur'ani, tana neman gamawa da duniya lafiya, wani lokacin ma Rashida ke koya mata karatun tayita samata albarka.

Baffa Usman ma Alhamdulillah yanzu haka sai qara habbaka yakeyi a fannin kasuwancinsa saboda gudun mawar da Dr Nuraddeen yabashi, arziqinsa sai dad'a bud'uwa yakeyi idan kaganesa zaka d'auaka wani hamshaqin d'an kasuwa ne, dama ashe talauci ne ya b'oye masa cikakkiyar sigar da ALLAH yayi masa, yanzu kuma da wadata ta sauka sai ya canza gaba d'aya tamkar ba shiba, haka Inna Bilkisu abun kam masha ALLAH sai sambarka, ga arziqin miji ga na 'ya 'yanta mata da akoda yaushe cikin aiko mata da saqwanni mazansu suke suna yimata godiyar tarbiyar data bawa 'ya'yanta, Babu mai matsala ko wata damuwa acikinsu don bayan kulawar da suke samu ga mazajensu gaba d'aya Dr Nuraddeen ya sama masu sana'o'in da sukeyi su day muneera kuma ba laifi kowace tana samu daidai gwargwado.

Tuni gidan gonar baffa da Dr Nuraddeen ya sake zuba wasu kaji aka rushe gidan aka mayar dashi wajen kula da kajin kad'ai sai kifaye da aka zuba suma ana kiwo shima ya bunqasa don har cdaga cikin gari motoci ke zuwa suna saye da kuma kamfanonan dake sana'arsu, ko yaushe saidai a qirgikke kud'i akawowa baffa ya soka aljihu yana gida zaune abunsa, (kaga haihuwa mai rana, ubangiji ALLAH kabamu masu albarka.)

Baffa Ali ma little yasa anyo masa qafar roba yanda zaijin dad'in walwala da mu'amalar yau da kullum cikin mutane, hakan kuwa yayima kowa

Please Login or Register in order to submit comment