Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, daga qarshe kuma tasaki taroqi ALLAH yasa hakan shiyafi zama alkhairi,

Hajia nafeesa kuwa da taji Babu irin maseefar da batayi ba da habaice habaice tun umma batasan abunda kefaruwa ba don bai riga ya sanar da ita ba har tasani, ta matuqar girgiza had'e da nuna qin amincewarta amma ammie tayita lurar da ita da lallashinta har saida ta amince, ba'a wata samu matsala ta b'angaren 'yan uwanta dana baba ba sboda ganin dattako da cancantar dady suma suka amince, nan take dady yasa aka rushe sashen da take da wasu wurare cikin gidan itama aka fitar mata da part d'inta abunka ga mai arziqi cikin sati biyu aka kammala komai har d'aurin aure ta tare abinta,

Duk wannan abun daya faru bisa amincewar Dr da taimakonsa dady yayis hakan kuma dashi har Fatima sunyi farinciki sosai ba tare da wata hiyana ba, Rashida ce kawai kullum take cikin jin kunya tana ganin kamar hakan da akayi ba'a kyautawa ammie ba, bayan duk taimako da halaccin da tayi masu ita da d'anta har saida ammie tazaunar da ita tanuna mata hakan ba illa bane tunda musulunci bai hana ba sannan tafara samun sakewa daidai, duk da ako yaushe idan hajia nafeesa tahad'u da ita har mahaifiyarta cikin jifarsu take da miyagun kalamai cewa wai Rashida tayi cikin shegene shiyasa tagudo suma da abun kunya ya ishesu sun kasa gano uban d'and'an dake cikinta sai suka biyo bayanta, hatta ma little da baisan komai ba kullum cikin kyararsa take tana aibantasa agaban 'ya'yanta tana kiransa da shege wanda ba'asan ubansa ba, hakan yasa har 'ya'yanta ma ke kiransa da haka amma da yake baisan komai ba baya damuwa.

Haka rayuwa taci gaba Rashida nasamun kulawa da kuma gudun mawa sosai wajen karatunta da ita har d'anta ta b'angare biyu wato dady da kuma Dr, don tuni shima little Dr yasashi makaranta lokacin itama Fatima har tahaihu tasamu qaton d'and'anta suka rad'a masa suna basheer wato sukawa baba takwara, wannan ba qaramar kima da daraja yaqara jawo masuba a idanuwan umma da Rashida harma da 'yan uwansa, sunyi matuqar farinciki da jin dad'i sosai aransu harma suna ganin aduniya yanzu basuda masoya da suka fimasu su dady da Dr nura ba.

Rashida kuwa tun tana dakon dawowar mijinta izuwa gareta ita da d'anta har tacire rai, gaba d'aya ta tattara wata rayuwar aure data tab'ayi abaya dama auren ta ajiyesu gefe taci gaba da karatunta ita da yaronta, saidai duk da hakan daidai da rana d'aya Bata tab'a yarda tayi wani abun da zaya keta mata marta da kuma darajar auren taba har ta kammala secondary lokacin little na primary 2 amma babu wani labarinsa, a lokacin fatima har tayaye basheer da suke kira (abbaty) tasake samun ciki ta haifi 'yan biyu duka mata saidai rurrutsa ce tayi a tsakaninsu, inda aka barsu da sunayensu na asali wato hassana da hussaina, murna kam awajen Dr da fatima bata misaltuwa, gashi dai SANNU SANNU cikin iyawar ALLAH suma sunfara tara nasu 'ya'yan da suke matuqar qauna a cikin shekaru uku kacal ALLAH ya arzuttasu da 'ya'ya uku, Babu wata wahalar reno da fatima kesha saboda Rashida nanan, duk wata kulawa da yaran zasu buqata tana basu tamkar ita tahaifesu.

Shekarar Rashida d'aya tana jiran saka makon jarabawar tasu tafito kuma cikin taimakon ALLAH tayi nasarar lashe kowane darasin da kyakkyawan sakamako wato exelent gaba d'aya, ranar da ita har umma sunyi kuka sosai cike da son inama baba nada rai yaga yanda tafara taka mataki na biyu akaratu da kyakkyawan sakamako, godiya kuwa sunyiwa Dr da dady da ammie ba adadi har saida suka farajin kunya.

Umma da ammie kuwa bazaka tab'a ganinsu kace kishiyoyi bane domin akwai tsantsar fahimta da mutunta juna atsakaninsu, hakan yaqarawa hajia nafeesa tsanar umma da rashida dama little gaba d'aya.

••• ••• •••
A b'angarensu baffama acikin shekarunne ALLAH ya sauki nusaiba matarsa lafiya saidai ba'a samu namiji ba kamar yanda yaso ALLAH ya arzuttasu dai da samun 'ya mace kyakkyawa kamarta sak da nusaiba baffa ya rad'a mata suna Rashida, yana matuqar son yarinyar fiye da tunani saboda sunan data zauna, sau da dama yakan tuna da baba da Kuma 'yarsa Rashida aduk sadda aka ambaci sunan 'yar tasa da taci sunan Rashida, wannan yasa ko kad'an baya son jin kukanta balle abunda zai b'ata mata rai, hakama gaba d'aya yakasa mantawa da gudan jininsa daya kasa samun labarinsa, lokacin daya tuntubi ma'aikatar da aka turasu qasar waje don qaro karatu akan labarinsa sai suka b'oye masa ainahin halin da d'an nasa ke ciki, domin koda Nuraddeen suka isa qasae waje bayan anbasu wajen zama sai yanemi wayarsa sama da qasa yarasa, gashi gaba d'aya wud'an da aka had'asa dasu zama 'yan jahohin kudu ne acan nageria babu wanda yasani acikinsu, asalima gaba d'ayansu babu ruwansu dashi saboda shikad'aine bahaushe sai suka nuna mashi halinsu qarara na qyamar jinsin da banasu ba musamman ma ga musulmi d'an arewa duk da kuwa qasarsu d'aya, hakan yasake jefasa acikin wata damuwar akan wacce yake ciki yana son yasan halin da ake ciki anan gida nageria amma bayada waya, kud'ad'ensa ma daya zo dasu gaba d'aya an sace balle yasamu ya sayi wata, wata irin wahalalliyar rayuwa yafarayi aqasar da kud'in ma da zai samu yayi amfani dasu babu, ana haka d'aya daga cikin qabilun da yake tare dasu yafara qoqarin jawosa jiki yana son taimaka masa da sunan tausaya masa, amma azuciyarsa bashine dalilin silar taimakon da yake yimasa ba kawai yana so ya d'orasa akan hanyar da zata hanasa karatune balle yasamu yayi abunda yakawosa har yakoma qasarsa ana alfahari dashi sai dai duk da haka Nuraddeen bai tab'a wasa da karatunsa da tuni suka fara yiba a fannin koyon likitanci na psychiatric musamman idan yatuna da halin daya baro mahaifiyarsa aciki sai yaji yaqara samun qwarin guiwar maida hankali sosai, hakan yasa yazamo kusan shine zakara kuma zaqwaqurin da yafi kowane d'alibi amakarantar, tun daga kan fararen fata har zuwa 'yan uwansa baqaqe, wannan abun yaqara baqantawa natare dashi rai ganin shi bakowa bane acikinsu amma ace ya zartasu qoqari acikin aji, don haka suka sake d'aukar d'amara wajen ganin sun durqushesa tahanyar jansa ga jiki, sunyi amfani da yawan damuwar da yake shiga wajen ganin sun jawo ra'ayinsa tahanyar zagayawa dashi wajaje masu ban sha'awa da d'aukar hankali aqasar wanda nan take suka fara zuwa club club dashi suna nuna masa hanyoyin shaye shayen qwayoyi da barasa da sunan zasu taimaka masa wajen rage damuwar da take ciki, yau da gobe babu abunda tabari, tun Nuraddeen najin bazai iyayin hakanba har yafara sha'awar aikatawa batare daya ankara ba, akoda yaushe yakan zauna yana qoqarin tunano gida da abunda yafaru sai yaji yakasa tuna komai, sab'anin da da kullum cikin tunaninsa da abunda yafaru tsakaninsa da matarsa yake, wani abu daya sake d'aure masa kai shine yanda bayason tuna qasarsa gaba d'aya balle ahalinsa shiyasa nan take suka samu nasarar juyar dashi yanda suke so, idanma yace zai zauna yatuna wani abu akansa sai yaji kansa na matuqar sara masa da yimasa ciwo, bazaiji yasamu sauqin hakan ba har sai ya d'auki barasar da tuni ya amince da takan rage masa damuwa yasha.

Gaba d'aya rayuwarsa tagurb'ace amma wani ikon ALLAH babu abunda ya sauya ta b'angaren karatunsa, zai iya sha yabugu sosai sannan yaje aji suyita yimasa dariya yana wartsakewa zaije yanemi topic d'in da akayi yayi reasarch akai kuma nan take yafahimta, idanma yakasa zaije yanemi malamin duk inda yake ya sake yimasa bayani, malamai da yawa na mamakin halin da yaron yajefa kansa aciki wanda shi da kansa idan an tambayesa bazai iya fad'ar daliliba, iya abunda zai iya fad'a akai shine baya son tuna komai akansa, ahalinsa da kuma qasarsa, idan kuma yayi yunqurin hakan to halin da zai tsinci kansa aciki shine zai haifar masa da shan barasa don yasamu magancesa..






*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___71💎

Sunana Nuraddeen Idris Aliyu wanda akafi sani da Dr N.I Aliyu wato qwararren likita a fannin lafiya daya shafi matsalolin qwaqwalwa...

Waro idanuwa Rashida tayi had'e da qurawa masa idanuwa cike da farinciki, alokaci d'aya tashiga qwalawasu Fatima kira, aunty, aunty, aunty kufito kuzo kugani ga abban little a tv ana fira dashi, pls aunty kufito kugansa, habiby ne wlh, kufito don ALLAH kada agama firar dashi.

Tadinga fad'a tana k'walamasu kira, ayanda take kiran nasu yasasu fitowa da sauri ba shiri, musamman Dr. Nura har yana shirin fad'uwa sanadiyar tuntub'en da yayi, ita kuma Fatima daqyar take takawa saboda nauyin da tayi, gashidai girma nadad'a tarar masu amma har lokacin haihuwa bata tsaya masu ba tasamu daqyar ta qaraso ciki, Saida takai jikin tv tasa yatsa adaidai gefen da aka nuno hotonsa tana fad'in uncle wannan shine mijina, shine abban little aunty,

Dawowa tayi tariqa Fatima tana cewa, kuzauna aunty kusaurari firar da za'ayi dashi, gaba d'aya ya canza saida nakallesa da kyau da sunan sa daya fad'a sannan zuciyata ta gamsu da cewa shid'inne, taqare maganar had'e da zaunar ita saman kujera, kaima uncle kazauna tafad'a lokacin da take qoqarin zaunawa itama had'e da qura masa ido, wani irin farinciki take jin kanta aciki marar misaltuwa, addu'a tadingayi azuciyarta akan ALLAH yasa yafad'i cewa zai dawo garesu nan kusa bada jimawa ba,

Wayarta tajawo ta lalubo lambar umma lokacin tarako dady zai fita riqe da hularsa tana yimasa addu'a, kasancewar wayar na nan falo saman kujera yasa umma tad'auko tare da d'agawa, Saida tayi murmushi sannan tace Rashida kuna lafiya, cikin zumud'i ta amsa mata tana cewa umma ku kunna tv a tashar BBC ana fira da mijina, gaba d'aya tamanta da umma take magana saboda hankalinta gaba d'aya na wajen firar da akeyi da Nuraddeen yana bada amsa, jin da tayi umma tayi tsaki had'e da cewa marar kunya yasa takashe wayar tana girgiza kai yasa tayi saurin toshe baki tana dariyar da da zaran ka kalleta zaka fahimci tsantsar farincikin dake tattare da ita taci gaba da kallonta

Dady ne yatambayi umma ko lafiya yaga tayi tsaki, tace kabarni da yarinyarnan marar kunya wai ni take fad'awa na kunna tv tashar BBC ana fira da mijinta inba tsabar rashin ta ido ba sai kace mijin nata yadamu da itane, dariya yayi tare da matsawa ya d'auki remote d'in tv dake kunne yana fad'in, to meye abun kunya aciki, idan bata fad'a maki ba wa kikeso tafad'awa?, ko Qaryane tafad'a shid'in ba mijinta bane? yaqare maganar daidai lokacin da yakamo tashar BBC, juyawa tayi zatabar wajen don batasonma ganinsa gaba d'aya dady yariqo hannunta had'e da cewa don ALLAH tsaya suji ko zasu samu wata hujja acikin firar da akeyi dashi wacce tahanasa dawowa, dama tuni ita umma tafara jin haushinsa tun lokacin da suka tsinci labarin cewa yace bazai dawo qasar ba yafiso yayi zamansa acan, shene abun yaqona mata rai har take ganin kamar yayine don yacutar mata da yarinya data kafe kai da qafa saishi duk da yashafe shekaru masu yawa acan batare daya tab'a tunanin waiwayo taba.

Babu yanda ta iya dole suka zauna suna kallon fira.

Gaba d'aya b'angaroran biyu sun shagala da irin firar da akeyi dashi har zuwa lokacin da ake tambayarsa dalilin daya hanasa komawa qasarsa yabada gudun mawarsa duk da zamowar gwamnatin qasarce ta d'auki nauyin karatunsa da komai nasa har zuwa lokacin daya kammala, yajima shiru yana tunanin amsar da zai bayar amma daga qarshe yace bayada wani dalili, kawai yafi sha'awar yayi zaunensa acan ne, da aka sake tambayarsa cewa ko yayi hakanne saboda kud'in da can qasar za'a bashi anan qasar baza'a tab'a iya bashi koda makamancinsu bane amma bud'ar bakinsa sai cewa yayi koda qasar bazata biyashi ko sisi ba yafiso ya zauna acan, shi kawai baisan abunda yasa hakanba amma yafi son zama acan har iya qarshen rayuwarsa fiye da yakoma qasarsa.

Tirqashi! Nan take Rashida taji wani dimmmm! akanta tanajin gaba d'aya duniyar tayi mata nauyi saboda maganganun da taji suna fitowa daga bakin wanda zuciyarta tagama bashi aminci da yarda, d'ago kai tayi tana kallon irin yanda yake b'ata rai da nuna damuwarsa qarara afuska adaidai wannan gab'ar wanda farkon fara firar dashi ba haka yake ba duk da akwai sauyesuyen da tagani atattare dashi alokacin na rashin walwala da sakin fuska da ada Bata sanshi daau ba, amma da akazo daidai wannan gab'ar sai taga sauyin yasake lunkuwa atattare dashi, nan take jikinta yayi sanyi tashiga jerowa kanta tambayoyi akan me hakan kalamansa ke nufi?, shin ko yamanta da ita ne?, meye ma'anar zai zauna acan har abada?, Shin a Ina ya ajiye auren nasu?, Idan kuma zancensa ya tabbata meye makomarta?, Meye makomar rayuwarta?, wane hali zata kasance aciki?.

Kafin ta lalubo amsar wud'annan tambayoyin sai taji ansake jefo mata wata tambayar da tayi daidai da d'ai daga cikin tambayoyin da tayiwa kanta, shin kamar yanda kafad'a kafi son kazauna acan qasar nahar abada to ya zancen iyalinka da kuma sauran ahalinka?, Sai daya murza goshinsa da yatsun hannuwansa na tsawon daqiqu biyu sannan ya d'ago kansa idanuwansa sunyi jawur yana kallon wanda keyi masa tambayoyin yace iyali? Ahali?, Kamar ya?,

Abokin firar nasa yayi d'an murmushi yana jujjuyawa akan kujerar da yake zaune akai sannan yace Ina nufin matarka da 'ya'yanka, iyaye harma da 'yan uwa, bud'ar bakinsa ba abunda yace sai iyaye, 'yan uwa? bansani ba, yaqare maganar cikin yanayin ko inkula.

Wata irin razana Rashida tayi had'e da miqewa tana girgiza kai tana ja da baya, tsaye tayi cak lokacin da taji yana cewa mata da 'ya'ya shi bayada ko d'aya bayan ansake jefa masa wata tambayar akansu, durqushewa tayi wajen tare da fashewa da kuka tana fad'in, Kada kayi hakan malamina, iyaye,
mata, 'ya'ya, ahali duka kana dasu, idan har zaka manta dani baici kamanta da iyaye da kuma d'anka da muka rabu ina d'auke dashi, safe, rana, dare soyayyarka bata tab'a fita azuciyata ba, idan kuwa zakayimun halacci ban cancanci kamanta dani ba balle har kafurta babuni acikin rayuwarka gaba d'aya, duk iya shekarunnan narayune da igiyoyin aurenka akaina batare da nadamu da qananan shekaruna ba ina dakon jiran dawowarka agaremu, na b'ata duka lokacina wajen baka yardata da kuma soyayyata amma acikin qananan mintuna gaba d'aya ka rosamunsu.

Wani irin kuka tasaki tare da rugawa tashige d'akinta tasa makulli, adaidai lokacin little Nuraddeen yadawo daga makaranta, ya isko su Dr da gaba d'aya sun kasa motsawa daga inda suke zaune yayi sallama, ganin hawaye daga idanuwan Fatima da tausayin mamansa yasata kuka yasa ya jefar da jikkarsa abakin qofar shigowa falon yazo ya duqa agabanta yana goge mata hawayen tare da tambayarta meyasata kuka, riqo hannunsa tayi tana shafa kansa had'e da kallon tv tana hango kamarsa acikin fuskar Nuraddeen da ake concluding firar da akeyi dashi, tabbas jini jini ne duk da kamannin little gaba d'aya na mahaifiyarsa ne amma akwai na mahaifinsa kad'an atare dashi, ganin tana kallon tv yasa shima yamaida hankalinsa ga tv, qurawa Nuraddeen idanuwa da ake nuno qaton hotonsa had'e dayin d'an taqaitaccen sharhi akan bayanin da yayi cikin firar da akayi dashi, maido kallonsa yayi ga fatima had'e da cewa, wayeshi mama?, Meya samesa naga ana nunosa kina kuka?, Kasa amsa masa tayi saidai Dr nura yace yamaza yaje yacire uniform d'insa yayi wanka sai yazo yaci abinci.

A lokacin little nada shekaru goma sha biyar aduniya kuma yana matakin aji na hud'u a makarantar secondary.

Umma kuwa murmushin da yafi kuka ciwo tayi had'e da kallon dady tace kagani, kawai ita kad'aice ke hauka akansa, gaba d'aya ya manta da ita balle abunda ke cikinta, dafari na d'auka yanda suka nuna damuwa akanta koda tabbaci suka samu akan tamutu bazasu manta da itaba, nayi tunanin son da suka nuna mata zaisa susamu tawayar farinciki atatattare dasu don nuna damuwarsu akai, amma sai gashi cikin wannan yanayin da ake ciki yasamu qwarin guiwar barin qasar, naji ba dad'i lokacin da aka sanar damu amma marigayi yalurar dani na fahimci hakan ba laifi bane, sai gashi akaro nabiyu da ranta bata mutuba sun wofantar da ita kuma nasan cewa dole zasusan cewa anganeta daga wajensu balarabe da sauran mutanen gari, hakan da sukayi shima babu kyautawa aciki, sai kuma gashi anxo mana da labarin yace bazai dawo qasar saba alokacin da tagama sa burin cewa zai dawo zuwa wajensa, shima d'in banji dad'i ba araina don Babu uwar dake burin ta zauna tana kallon 'yarta agabanta kuma da sunan tanada aure musamman yanda ake sheganta mata yaro, amma kazauna ka lurar dani cewa ba lallene abunda aka fad'a yatabbata ba, ka hana zuciyata ta gasgata zancen sai gashi yau agabanka, da kunnuwanka ka gani kuma kaji abunda yafad'a da bakinsa, Wai bayada mata da 'ya'ya gaba d'aya saboda rud'in duniya da abun duniya daya d'ebesa, alhaji shin shima wannan ba gaskiya bane?, shima suruttaine it na mutane kada I gasgata?,

Sau d'aya kabani gamsashiyar amsa amatsayina na uwa kuma macce dake d'auke da zuciya irin ta d'an adam da batada qashi shin yakamata raina yab'aci kuma naji zafi akan wud'annan abubuwan ko kuwa?,






*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___72💎

Shiru Dady yayi gaba d'aya yakasa yin magana saboda yanda jikinsa yayi sanyi akan kalaman da Dr Nuraddeen yayi, yajima zaune yana nazarin maganganunsa dana umma yanaso yagano dalilin da zaisa Dr Nuraddeen yayi hakan, amma duk iya nazarinsa da zurfin tunaninsa kasa samun dalili d'aya yayi da yasa ya aikata hakan, abu d'aya zai iya cewa shine kodai k'wakwalwarsa tasamu matsalane ko kuma rud'in duniya, Amma wane irin abune zaisamu aduniya da sukafi iyayensa da iyalansa da sauran 'yan uwansa aduniya, yatabbata dole dai akwai abunda ba daidai ba acikin wannan al-amarin, wanda qoqarin gyarashi izuwa daidai d'in baqaramar wahala zaiyiba, dole koma meye yazamo d'aya daga cikin wud'anda zasu fahimci rad'ad'in da umma keji aranta fiye da yace zaiyi qoqarin fahimtar da ita kuma awannan karon, domin hakan zai saka mata wani shakku arai tayi tunanin kondon bashi yahaifi Rashida ba tunda ranta yariga da yagama b'aci, Saida ya sauke wata irin gwauruwar ajiyar zuciya sannan ya kashe tv had'e da kallon umma dake sharar qwalla da gefen hannunta yafara qoqarin bata maganada kuma kwantar mata da hankali,

A matsayinki na mahaifiya tabbas nasani dole zakiji badad'i bisa abubuwan dake faruwa domin UWA DA 'DA sai ALLAH, ayanayin daya fitar da lafuzzansa babu kyautawa aciki ko kad'an kuma beyi adalci ba, mussamman ga iyayen da suka haifesa, anan yakamata kiyi tunani,abubuwane marasa dad'i kefaruwa akan Rashida kikaji ba dad'i aranki to mekike tunani ga iyayensa da suka haifesa daya nunama duniya baisan komai akansu ba alokacin da akayi masa zancensu, wannan abu mai girmane da akwai buqatar ace anbinciki qwaqwalwarsa da zuciyarsa kafin a amince da kalaman da yayi, anawa tsammanin indai wud'annan maganganu da yayi dagaskenke yakeyi to tabbas yarasa hankalinsa ne, idan kuma da hankalinsa yayisu to rud'in duniya ne kuma zaiyi nadama akai ko yaushene, don haka Ina so kiyima Allah kicire komai aranki uma ki kwantar da hankalinki muje can garin iyayen nasa muji ko meye kefaruwa don asamu maslaha aciki.

Maslaha! Maslaha dadynsu? Wace irin maslaha za'aje nema awurin iyayen da suka cutar da 'yar wasu kuma suka nemi gyara rayuwar nasu d'an don ALLAH yamayar masu da aniyarsu?, ai shi ALLAH baya zalinci kuma abunda duk kayi sai anyi maka, saboda haka babu inda zamuje tunda hatta su kansu yanuna baya buqatarsu balle suyi darajar da zasu iyayin wani abu akansa, umma tafad'a cikin b'acin rai da nuna tsantsar baqincikin daya tarar mata azuciya, ganin haka yasa dady ya d'auki hularsa dake gefenta had'e da cewa ALLAH yasawaqe yabar gidan don yasan duk bayanin da zaiyi mata alokacin bazata fahimceshi ba, asalima zai dad'a qaramata wani rad'ad'ine azuciya idan ya matsa mata, duk da shima wani sashe nazuciyarsa nafad'a masa Nuraddeen yayi kuskure mai girma amma acan qasan zuciyarsa yahanasa gasgata hakan domin shi mutumne mai yawan yiwa mutane uzuri.

ALLAH sarki rayuwa kenan, shi rashin sani yafi dare duhu, kuma sanin gaibi sai ALLAH duk jarumtar umma da alkunyarta dole zata ajiyesu agefe tayi duk abunda take ganin ya dace akan 'yar tata tilo da take kallo amatsayin sauran farincikin da yarage mata aduniya, saboda rashin sanin ainahin abunda kefaruwa ga Nuraddeen da batayi ba , ba itaba hatta iyayen nasa dake tare da wud'anda suka aikata son ransu akansa basu san abunda kefaruwa ba, Basu san abunda akayi masa ba har yakoma haka balle ita, abune gaibi dabai bayyana agaresu ba, amma komai nisan dare gari zai waye kuma SANNU SANNU bata Hana zuwa...in Sha ALLAH da sannu ALLAH zai bayyana komai kuma yawarware dukkanin wani qullin da basuda masaniya akansa, ya haskake duhun dake gabansu suka kasa ganosa kuma ya yaye masu duk wani shamakin daya zamo silar wanzuwar wannan qaddararriyar matsalar data cutar masu da d'a.

A b'angarensu Rashida kuwa little nawucewa Fatima tanufi d'akinta tana bubbuga mata qofa tana kiran sunanta, tanajin yanda sautin kukanta ke tashi alamun tana jinta amma taqi zuwa tabud'e qofar, tasowa Dr nura yayi yadafa kafad'arta ta juyo ya girgiza mata kai alamun ta qyaleta tace amma Dr tana buqatar wani akusa gareta dazai rarrasheta kuma kasan tana fama da matsalar bp nan kada yazo ya tasar mata, jawota Dr yayi yana fad'in, ki k'yaleta babu abunda zai sameta, ahalin yanzu tafi buqatar kad'aici fiye da komai, mubarta tazubar da hawayen shine zai sama mata sassauci azuciya fiye da ace anhanata fitar dasu, wallahi matar Ina tausayin rayuwar yarinyar nan, tun daga lokacin datayi qoqarin sauya ra'ayin mahaifinta akanta yayi mata abunda takeso ALLAH ke jarabtarta har zuwa wannan lokacin, idan tafita wannan saita shiga waccan kuma duka adalilin rayuwar auren da tayi iqirarin cewa tana so, ubangiji nayi mata hakanne saboda yagwada qarfin imaninta agaresa, kinga kuwa tanada dalilin zubar da hawayenta ko don tasamu qarfin canye jarabawarta, sau da dama kukan da mukeyi akan damuwarmu yana taimaka mana wajen yaqi da ita sab'anin shirunmu dake mummukar zuciya har yasanya mana raunin da zamu iya yaqi da damuwar tamu balle mucanye jarabawowin mu.

Suna nan zaune afalo har little yayo wanka yadawo fatima tasa shahida da alokacin tanada shekaru goma sha biyu ta zibo masa abinci, Saida yaci yaqoshi sannan yafara dube dube yana tambayar Fatima ina gwoggonsa wato Rashida, don yasan idan tana nan to tabbas bazataji dawowarsa daga makaranta ba kuma taqi fitowa, kasancewar har lokacin bata fitoba balle taci abincin rana yasa Dr yace yaje ya had'a mata abincin ranarta yakai mata tana d'aki, yayi hakanne don yasan ahalin yanzu shikad'aine zata iya saurara kuma ya kusanceta taji sanyi aranta.

Shahida ce tayi saurin riqa masa tray d'in daya d'auko da abinci tabi bayansa dashi, sau kusan uku yana qwanqwasa mata bata bud'e ba kafin can yasoma kiranta, gwaggo, gwaggo kibud'e qofa yaci gaba da fad'a yana dukan qofar, tanajin murayarsa da sauri ta taso tabud'e qofar, qura mata idanuwa yayi ganin yanda sukayi ja had'e da kumburewa kafin yajuyo yakarb'i tray d'in ahannun shahida yana fad'in sannu sister, sannan yashiga daga ciki had'e da sake tura qofar da qafa tarufe, Saida ya ajiye tray d'in a saman gado daga gefe sannan yadawo ta gabanta ya zauna, yanaci gaba da kallonta cikin natsuwa yanason karanto damuwarta, little yarone Mai matuqar natsuwa da sanyin hali, koda yatashi baiyi irin qiriniyar nan ta yara ba saboda rashin son hayaniyarsa,

Please Login or Register in order to submit comment